Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

din yace "is she a kidnapper"? Dasauri Sharif yace "how am I suppose to know eh? Ammi saida tace inzo da security indaukeka kace kai bakason azo daukanka da kowa, yanzu in kidnappers ne Yaya zamuyi"? daidai lokacin tarinmata kusan su shidda suka fito daga gidansu Du'a da gate kenan abude, Babban cikinsu ne ta bubbuga motan dan tinted class ne tagefe dasauri Asad yace "don't open the door" bude motan Sharif yayi yafita ganin matan aure kamilallu, Matar tace "Malam dan Allah kataimaka mana kakap anguwan nan babu maza yarinya kuma tafada rijiya kusan minti takwas da rabi kenan bamu samu nasaran ciro ta ba kuma iyayenta basa nan sunje kauyen su chan Ikara dan Allah kataimaka mana maganan rai ake anan" shiru Sharif yayi yana kallonsu saikuma yakalli gidan dasuke nunamai yanda aka taru yara da manya gawasu na kuka dan abin abin tausayi yasa yace "Ina zuwa" shiga motan yayi dasauri yakalli Asad dake binshi da kallo yana jiran bayani yace "Asad zomuje muyi taimako" dasauri Asad yace "taimakon mene" dasauri yace "yarinya ce tafada rijiya and parents dinta are not around tayi about 8min a rijiyan kuma kasan ni ban iya ruwaba pls muje kacirota" Wani kalan matsiyacin kallo Asad yamai yace "you must be joking, na iya ruwa yes na iya ruwa kataba ganin na shiga rijiya ne? I don't think namataba ganin rijiya, common key this car mubace daga anguwan nan" dasauri Sharif yace "common Asad maganan rai akefa anan what if yarinya tamutu right before our eyes when munada chance na saving life dinta mezamu fadama God" maida kanshi yayi jikin kujera yace "sannu superman, tunda kanada relation ne da yarinya ai kaje kai saving nata nidai count me out" dasauri Sharif dake kallonshi cikeda mamaki yace "haka kace" tabe baki yayi yace "saikuma kayi" yay maganan yana lumshe ido danshi bacci ma yakeji fita daga motan Sharif yayi yakalli matan yace "muje ingani" dasauri daga Uwani har sauran matan sukai gidansu Du'a tareda Sharif din dake biyeda su, almost 1min yayi idanunshi a lumshe saikuma yabude idanunshi dasauri yajuya yakalli gate din su Du'a, wani irin banzan tsaki yayi sanan yabude kofan bayan yafito yana maida kofan yarufe yace "you are messing with my mind Sherif" sanan yawuce ahankali yabisu, kafanshi nadama yasa yashiga gidan wani irin sanyi yaji yay wani irin cringing acikin bones nashi dasauri ya tsaya chak yanabin duka gidan da kallo yanda yaga duka matan gidan sun juyo suna kallonshi kaman sunga wani hero ko celebrity na movie, juyawa yayi dasauri zai fice daga Gate din yaji muryan Sharif yace "yauwa gashinan yazo, the well is here Asad" dasauri yajuyo yakalli Sherif din dake gaban rijiyan kusada Bala direba yana nunamai rijiyan, wani kallo yama Sherif irin zamu ganmu dinnan sanan yashigo cikin gidan zuwa gaban rijiyan, necktie dinshi yacire yabama Sharif din yakarba, sanan yacire takalminshi dakuma jacket dinshi, igiyan dayagani hannun Bala ne ya karba wani irin dauri yama igiyan a waist dinshi da sanan ya kallesu yace "zan shiga ciki idan Nagano ta zan muku sign ku jawota" duka gyadamai kai akayi, juyawa yayi yakalli rijiyan baitaba shiga rijiya ba, kallon Sharif yayi dake kallonshi irin kallon nan na u caused all this sanan yay wani irin tsalle yafada rijiyan jikake tsundum.!!!




Leka rijiyan dukansu sukayi Bala yace "kace ya iya ruwa sosai ko" gyadamai kai Sharif da kirjinshi ke dukan uku uku yayi yace "eh ya iya amman baitaba shiga rijiya ba" wani irin salati duka gidan aka dauka, wata mata cikinsu takalli Bala tace "incedai ka kira mahaifinta ka sanarda su inma barin ikaran nan subaro sutaho fa dan wanan yarinyar inhar ta rayu to Allah yace kawai kwanan ta nagaba ne" ahankali Bala yace "nariga na sanar dashi" "jama'a Qulhuwallahu kafa bakwai" nan aka fara karatu fa, ganin yayi kusan 2min a ruwan ruwan ma yadena motsi yasa dasauri Sharif ya tsugunna yana leka rijiyan. "Asad Asad can u hear me are you okay? Asad" kana ganinshi kasan hankalinshi atashe yake, kusan 20sec dagama kiranshi saigashi yawani bullo da kanshi daga ruwan yay ihu yace "I got her!" dasauri daga Sharif har duka yan gidan sukahau hamdala, dasauri Sharif yace "what about u are you okay Asad" yana kokarin janyo Du'a kanta yafito daga ruwan gabaki daya yace "we will talk about that when am up there" cirokanta yayi daga ruwan sanan yadaura kanta akirjinshi ya rungumeta ahaka, igiyan dake waist dinshi ya shiga warwarewa sanan yadaura shi kan waist dinta duk acikin ruwan dan kansu ne kawai ke sama sanan yace "Sharif I don't know if she's still alive but she is unconscious, na daura igiya a waist dinta, ni zan dingabin matattakala while am holding her kukuma kunajan igiyan waje am I clear" dasauri Sharif yace "yes Asad sanan yatashi dasauri yarike igiyan tagaban Bala yakama ta bayanshi sanan yacilla matan ragowan igiyan yace kuyi layi ku kama igiyan mujawosu waje, duka rike wa sukayi Sharif yace "give us go ahead we are read Asad" hawa matakala daya Asad yayi yana rungume da ita har lokacin sanan yadago kanshi yakalli sama yace "pull us Sharif" jawo igiyan suka shiga yi yana rikeda ita yanabin matattakala har sukakai sama Tsugunnawa Sharif yayi yamikamai hannu da taimakonsu yafito rikeda Du'a akan kafadan shi sanan ahankali yacirota daga kafadarshi ya shinfidar da ita akasa sai alokacin yamaga fuskarta yanda yake kallonta haka kowadake compound dinan ke kallonta, Uwani ce ta rarrafo tana kuka sosai tace "mun shiga uku mun lalace Bala ta mutu jibi yanda takara haske, Innalillahi wa innailaihi raji'un" ahankali Sharif dake gefen Asad yace "Asad tamutu ne"? "I dont know" Asad yabashi amsa atakaice yana dauke idanunshi daga kanta, yace "let's go" dasauri Sharif yace "check ko she's alive common Asad, are you this heartless" wani mugun kallo yama Sharif zaiyi magana wata yar tsohuwan dake cikinsu tace "bawan Allah matsamata ciki in ruwa tafito tanada rai idan baifi
to ba ba rai" kaman bazaiyi ba saikuma ya matsa inda take kwance dasauri Uwani ta matsa hannunta ya kalla saikuma yakai hannunshi yakama hannunta yana duba pulse dinta bai sami pulse a hannun ba sai uban sanyi da hannunta yayi kaman kan kara, hakan yasa ya ijiye hannun yakai yatsunshi biyu kan jijiyan dake gefen wuya anan yasami wani very very weak pulse dasauri yazare hannunshi yace "she's alive" "Alhamdulillahi Rabbil Alameen" yan gidan suka fadi hannayenshi biyu yasa akan cikinta yashiga matse mata cikin da karfi yana kallon fuskanta sai chan ya tsaya yakalli Uwani dake gefensu tana kukan murna ganin tana raye yace "bude bakinta kihura mata iska aciki" dasauri Uwani tazo bude bakinta tayi tahura iska ciki yace "ya isa" daina wa tayi shikuma yacigaba da matsa mata cikin, ruwan gashinshi nabin fuskanshi har zuwa hanci, amman shiru saida yasa Uwani tahura mata iska harsau uku amman shiru hakan yasa Sharif yace "common kai kasan komk nakan harkan ruwa, ka asalin this thing ba kahura mata iskan dakanka mana, let's help the poor girl" ko kallon Sharif baiyiba yakalli Uwani yace "sake huramata" dasauri tsohuwan tace "bawan Allah kayakuri dan Allah kataimaka mata tafarfado hankalinmu duk ya kwanta inda mahaifiyar ta na nan datakusan mutuwa dan Allah kataimakama marainiyan yarinyar nan da iyayenta basu anan" kaman ya kurma ihu yakeji amman yadai daure da kyar dan matsowa wajen kanta yayi yana kallon pink lips da dan karamin bakinta dazai daura nashi akai, kaman wanda ke tsoro yakai bakinshi gently yana kallon fuskanta yadaura kan nata ko mugun sanyin da jikinta yayine yake shiga nashi oho jiyayi jikinshi yadauki wani mugun sanyi daurewa yayi ahankali yahuramata iskan bakinshi zuwa cikin nata kaman wani magic tarrrr yaga tabude idanunta dasukai wani masifan haske sai cikin nashi suna kallon juna saikuma wani uban tari datayi white tana kallonshi duka ruwan daya taho daga bakinta sai nashi dawani irin mugun sauri yacire bakinshi daga nata yaciro kanshi yajuya yana wani irin kakarin amai babuma wanda ya lurada shi sai wani irin ihu da hamdala da duka mutane keyi na ta farfado tana uban aman ruwa aka zagayeta, ganin yakasa aman yasa ya yunkura zai tashi jiyayi an kama hannunshi gam dasauri yajuyo yakalli hannunshi gani yayi Du'a dake amai sosai tarike hannunshi gam tana kallonshi har lokacin da idanun nan nata da kaman bata hayyacinta, dasauri yajanye idanunshi dagakan hannun yakalli fuskanta idanunta kadan suka budu amman shi take kallo saikuma jikinta yafara bari tana kakkarwa, fizge hannunshi yayi daga nata dasauri yana yarfewa danjjn hannun yayi kaman ya sandare yakalli Uwani dake kanta yace "ku chanza mata kaya ku rufeta shes cold a kaita asibiti" sanan yawuce wanshi batare daya kalli Sharif ba yace "wlh nakai mota baka zona saidai kadawo gida da kafa" dawani irin gudu Sharif yatashi yabishi abaya yana kara waigen Du'a da aka zagaye, mota suka shiga Sharif yaja motan da gudu.


Agaban wani gida mai kama da mansion sukai horn bude musu akayi suka shiga, Sharif na parking yabude mota yafito yana attishawa, daidai wata kyakkyawan mata tana sanye dawani hadadden lace tafito kana ganinta kaga mamanshi sabida kamanninsu tana ganin dan nata ta tsaya turus tana kallonshi ganin yanda yay sharkap daidai nan shima Sharif yafito yana murmushi dasauri takaraso wajen tace "what on earth happen daka jike haka son" ranshi abace yace "lemme shower Ammi" yay wucewan shi, tabishi da kallo saikuma tajuyo takalli Sharif dataga yana murmushi tace "maiya faru yaji ke haka Sharif kaima jibi yanda kai daka daka kaman kai wasa a mud"? Dan dariya yayi yace "aikin Allah mukayi Ammi" aikin Allah? ta maimaita gyadamata kai yayi yace "Ammi we just saved a girl dabadan muba data mutu arijiya wlh, Asad yacirota daga rijiyan nikuma na ciro both Asad and the girl, nima bari naje nai wanka" shima yawuce yabar Ammi awajen baki bude.


💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫



✍️M SHAKUR

free page
EPISODE 🔟
Gban wani hadadden flat yayi ya bude kofa ahankali yashiga, kaga flat din zaka dauka a turai kake, sama yayi yabude wani daki da komi nacike kenan blue, bathroom yabude yashiga danyay wanka, koda yafito shiryawa yayi cikin 3 quarter da singlet fara, sanan yafito anan falon sama yaga Asad zaune dagashi sai towel daya daura a waist dinshi fari, tulin gashin kanshi ajike da ruwa yana tsiyayar da ruwa, ruwan nabin fuskanshi yana diddiga akan kirjinshi gwanin ban sha'awa, dark skin dinshi nawani irin glowing dankomai bai shafaba yana fitowa daga wanka yatuna da abinda yakeyi dazu a mota yazo yazauna yacigaba, kirjinshi kaman zai fashe acike tsabagen work out gashi da uban hair akirjin dasuka kwanta sukai lub lub har wajen cibiyanshi da maranshi, hakama muscle dinshi amurtuke yadaura MacBook din akan cinya nashi yana danne danne ya mikarda kafafun shi yadaura kan wata cushion. "katashi kasa kaya Asad yanzun nan fa kabar cikin rijiya kayi wanka basaikasa kayaba" kaman ba dashi ake magana ba yamai banza dan haushin shi yakeji sabida abinda yamai dazu, tabe baki Sharif yayi yace "koba komi dai after such a long time nasa kayi taimako u just save a life today wired dude kawai" dago kanshi yayi yawani kalli Sharif din irin kallon nan na dani kake, dagamai gira daya Sharif yayi sanan yawuce yace "am starving idan kagama come down muje ka gaida Dadda, nidai natafi wajen Ammi naci abinci" yawuce yasauka kasa abinshi batare daya karabi tanan Asad dinba tunda yaga fitina yakeji, baitaba ganin fitinannen yaro dan bala'i irin Asad ba.


Yadade yana danne danne sannan yarufe system din yatashi daidai lokacin iPhone 13pro max dinshi tahau ringing kobai kalli screen dinba yasan Ammi ce hakan yasa yadauki wayan yakara a kunne cikin muryanshi dakeda dan sanyi yace "Ammi gani nan zuwa" katse wayan yayi ya jefar kan kujera sanan yashiga wani daki, shi dakin komi off white ne ba kaman na Sharif ba, hoton dake jikin bango nashi zaisa kagane wanan dakinshine, gaban madubi ya tsaya dayacika da kayan shafa sanan yadau cream ya shafe jikinshi kafin yabude wardrobe yadauko wani 3quater maroon da white t-shirt yasaka dasukamai kyau sosai sanan yakoma gaban madubi wani man gashi yabude sanan yalukata yashafa akanshi kafin kaceme gashin su kara wani kanannadewa bakinsu na shinning kaman wani gashin jariri sanan yadau turarukanshi ya feffesa yadau yazura wani crock na maza yafito falon saman, wayanshi yadauka sanan yawuce yafice daga flat din, yana fita wani rana yadaki fuskanshi tsaki yayi yace "I hate this damn country" Babban flat din gidan yayi kofa yabude ahankali yashiga Sharif ne ke zaune afalo sai wasu yan mata guda uku Aneesa, Rahima, da Mariya duk suna zaune kusada Sharif din suna hira, suna ganinshi tsit kakeji wani irin batarai yayi kaman baitaba murmushi tunda yazo duniya yazo zai wuce tagaban su dasauri suka shiga gaidashi. "Ya Asad welcome ya hanya" da kyar ya iya bude baki ya amsa batare daya kallesu ba. "fine" that's the only thing yafadi sanan yay dinning Sharif nabinshi da kallo saikuma ya kalli Aneesa data bishi da kallo kaman zata hadiyeshi.
Zama yayi kan kujera daidai lokacin Ammi tafito daga kitchen rikeda flask tana kallon fuskanshi tace "sannu da aiki superman mai shiga rijiya, yanzun nan nagama hadamaka tea dinan zokasha koya kori sanyin daya shiga jikinka" dan murmushi yamata daidai tamikomai cup din shayin dayaji kayan kamshi karba yayi itakuma taja kujera kusadashi tace "Ya hanya" ahankali yace "Ammi yaushe zamu koma gidanmu"? "to marason zumunci anan kano zaku cigaba da zama" dasauri yadago kanshi wata hadaddiyar mata ce kyakkyawan gaske tana sanye da bakin jallabiya kesaukowa, ahankali yace "ina yini Anty" hararan shi tayi sosai tace "kai yaron nan ina kanwar mahaifinka kana kirana da Anty, abinda kike koyamai kenan Maryama? Kaf family nan bamuda yaro mara tarbiya irin Asad" sanin halinta yasa Ammi tace "stand up and greet her properly Asad" kallon Ammi yayi yanda ta gyadamai idanu yasa yatashi ahankali yana kallon kasa yace "ina yini M...um" washebaki tayi takaraso inda yake hannunta takai kan fuskanshi tace "ko kaifa Asad, kadawo lpy" kanshi akasa yace "lpy" murmushi tayi tace "ance kadawo kayi aikin nanne na youth start up forum ko da government sukai establishing right?" gyadamata kai yayi batare daya kalleta ba, cikeda gamsuwa tace "awani tasha zakuyi Channels television news" murya chan kasa yace "kowani TV station zasusa har nagama na 7days" gyadamai kai tayi tace "Masha Allah, Allah yataimaka, saikuma batun aure ko" shiru yayi sakinshi tayi tace "anyway nadawo mayi maganan da kyau, let's go girls" tashi matan sukayi suka bita suka fice.


Daure fuska yayi sosai yanajan cup din tea dinshi zaikai baki yace "saisa banason zuwa gidan nan I don't like her Ammi, this Anty Turai" shareshi Ammi tayi tajuya takalli Sharif dakecin abincin shi tace "you want more Sharif" "Ammi am full" kallon Asad din tayi tace "mezakaci"? kallon abincin data bubbudemai yayi sanan idanunshi suka sauka kan spaghetti da meat balls da hannu yanuna mata zubamai tayi ya karba yashiga ci ahankali bin dan nata take da kallo take, anytime taganshi mahaifinshi kawai take gani halinshi sak dana ubanshi, juyowa tayi takalli Sharif tace "baku bani labarin ciro yarinyar dakukayi daga rijiya ba" kaman jira Sharif yake yace " Ammi I was driving fa kawai wata mata tasha gabanmu tana kuka wai mutaimaketa yarinya tafada rijiya, Ammi I was begging Asad fa yaje mucirota wai bazaiyiba gashi ba maza sai tulin uban mata kaman gidan biki duk suna kuka, shine nace musu mujeni nacirota dan nasan that's the only thing dazai fitoda Asad daga cikin motan nan danni kadai nasan irin mugun halinshi, aiko ina shiga saigashi yataho ashedai yana sona yasan ban iya ruwaba fear of my death yasa yazo bawaidan he meant to save the girl ba, shine yashiga fa yacirota, Ammi kinsan menene" yay maganan yanajan kujera da sauri yana zama sanan yakalli Ammi dake kallonshi yace "Ammi nifa dasuketa yarinya I thought small girl ce fa tafada rijiyan saigashi Asad yafito da zankadediyan budurwa innalillahi Ammi kinga kyanta kuwa" Ammi dake sauraronshi tace "haba" dasauri yakalli Asad dake cin abincin anatse yana danna waya yace "Asad isn't the girl beautiful" batare daya kallesu ba yace "I don't know bankalleta ba" wani mugun tsaki yaja yace "Ammi wlh Asad dan rainin wayau ne" dan dariya Ammi tayi ganin yanda Sharif ya tunzura sosai tace "don't mind him kaji cigaba da bani labarin" murmushi yama Ammi yace "wlh Ammi tunda nake Allah Ammi harna gama yawona across the globe ni bantaba ganin kyakkyawa irin yarinyar nanba Ammi she don't even look Nigerian, hala half cast ce, Ammi she's so pretty gashinta har waist, she's so pretty I wish I can even see her again" ture plate din abincin dayagama ci Asad yayi yamike Ammi dasauri ta kalleshi tace "harka koshi? Baka cinye ba ai" gyadamata kai yayi yace "ya isheni, natafi wajen Dadda" dasauri Sharif yatashi yace "wait for me Asad" ko kallonshi baiyiba yawuce Ammi tabisu da kallo tana murmushi, Sharif is such a gentle man with a very very forgiven spirit, shikuma Asad is opposite na hakan, churarren mutum ne baka gane gabanshi da bayanshi ko itama sabida ita tahaifeshi ne saisa take iya fahimtan halinshi tass,.

Wani flat suka shiga kayataccen falo ne da kujera ke ciki sai lallausan carpet da aka rufe ko ina na kasan dakin dashi sabida sanyi sai wani tsohon dattijo da akalla zaikai shekara 90 ko fin haka ke zaune kan wata kujera mai ultra taushi wacce kanagani kasan musamman sabida shi akayita yana zaune gashinan tsaf tsaf sai wani bakin glasses a idanunshi hannunshi rikeda ayaba yanaci da aka yayyankamai awani clean bowl, tunda yashigo gidan this is the first time yayi kayataccen murmushi yace "Dadda" da sauri tsohon dake tauna ayaba abaki ya tsaya chak saikuma da sauri yasake gyara zaman glass dinshi a idanunshi yakalli kofa sabida haske kofa yasa baiganesu ba cikin muryanshi ta tsufa da still kuma take fitada kyau yace "amaida kofan arufe" dasauri Sharif dake hadiye dariyan shi yamaida kofan yarufe hakan yabashi daman ganinsu ahankali yanuna Asad da yatsa yace "Sharif Asad nake gani" dawani irin sauri Asad yaje bowl din jikinshi yacire ya ijiye agefe sanan yawani rungume kakanshi tsam tsam yace "Dadda kai kadai nayi missing wlh, kaga Sharif tunda na shigo garin nan yake batamin rai Dadda" washe bakinshi da hakora sun fiffita yayi yace "to wlh su kiyayeni aina gayamusu duk wanda yataba Asad toni yataba kona mutu bazan yafemai ba" dariya sukayi duka Sharif yazo yace "Dadda kai bazakamai fadaba mugun halinshi yay yawa" hannu yamika ya kamo hannun Sharif yace "banace ku hada kanku ba kome yayi kamai hakuri, shi hali zanen dutse ne ko mutum zai rabu dashi saidai da kadan kadan, halin mahaifinshi Abdullahi yagado sak" kankameshi sosai Asad yayi yace "i love you Dadda na"


💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫


✍️ M SHAKUR

wa.me/+2347012181461


Free page
EPISODE 1️⃣1️⃣
Da taimakon Matan dake compound din aka kwasheta akai falonsu da ita jikinta na mugun barin sanyi daidai lokacin motarsu Abba tai parking akofar gida wani irin azababben gudu sukayi dayake Hamad shiya tukasu da Mami da Abba ne kadai sauran duk sun barsu awajen Kaka achan Ikara, dawani irin gudu Mami tashigo gidan idanunta sunyi jajir, this is the first time data iya cire koma meke sata yima yarta wani kala tanuna tsantsan damuwa da so akan yartata tadubi matan tace "ancirota ancirota daga rijiyan? jama'a kufadamin ina y'ata Du'a, ina take"? Tai maganan tana kama kirjinta dataji yana wani irin bugawa tsabagen fargaba, daki matan gidan suka nunamata sukace "tana daki, yanzun nan aka shiga da ita ciki" dawani irin gudu Mami tai flat dinsu Abba ma dayashigo yabita dasauri Hamad shima dagudu yabisu da shine last na shigowa sabida parking mota dayake, tana shiga falo taga some few mata akan Du'a dahar lokacin take ajike akasa tana wani irin rawan sanyi hakoranta na karkar kar kaman ana hada kacha ana gwarasu, wani irin ihu Mami tayi. "Du'a! Du'a" yanda Mami tayi baya kaman zata sume yasa dasauri Abba yatareta yace "calm down" juyawa Matan dakin sukayi suka fice ganin maigida, daidai Uwani tasauko kasa dawasu kaya da bargo daban daban a hannunta, tashi tayi daga jikin Abba dasauri takarasa wajen Uwani, karban kayan hannunta tayi sanan takoma inda take, dagota tayi dasauri takalli Hamad tace "Hamad bani wuka" dagudu yay kitchen wuka yadauko yafito yaga rigan jikinta Mami tayi Abba da Hamad duk suka juyar dakai chanza mata kayan Mami tayi agurguje sanan tawani irin rungume yarinyar dasauri tarufeta da bargo tana kuka. "I am sorry Du'a sorry" matsowa wajen Abba yayi hannunshi yakai yadaura kan wuyanta jin sanyi yasa yakalli Uwani yace "jeki hado garwashi" sanan yaciro hannun Du'a daya yana murza tafi hannun dasauri Hamad shima yazo yakama dayan hannunta yana murzawa duk tana jikin Mami data kankameta sosai, ba'a wani dauki lokaci ba saiga Uwani da uban rushi a kasko dan makota taje tasamo, ajiye wa sukai agabanta still suna murza hannunta ahaka suka samu kadan kadan tarage rawan sanyin hartazo tada ina gabaki daya kallon fuskanta tayi yanda idanunta ke a lumshe shafa fuskanta Mami tayi ahankali takira sunanta.



"Du'a" bude idanunta kadan tayi saikuma tabudesu gabaki daya tana kallon fuskan Mami, dasauri Hamad yataso kansu yana kallonta yace "Du'a taya kika fada rijiya"?zubamishi idanu tayi shima tana kallonshi saikuma ahankali tamaida idanun kan Mami tana kallonta asanyaye, Mami hakanan taji jikinta yay sanyi sabida yanda yarinyar ke kallonta, hawaye taga sun zulalo ta gefen idanunta kafin ahankali tabude bakinta cikin muryanta dabata fita sosai tace "maisa aka cironi daga rijiyan eh? Mami inaso namutu kowa yahuta saisa kodana fada saidai nadinga lumawa cikin ruwan ko tsoro daya banji ba saima kwanciyan hankali danaji domin ajalina yazo, Mami naso namutu sabida kihuta hankalinki ya kwanta kince tundaga randa kika haifeni baki karasamin kwanciyan hankali ba, yau dana fada rijiya all I could thought of was yanzu zaki fara samin kwanciyan hankali, bazan kara jawo matsala agidan nanba, bazan kara saki ko Abba a matsalan Kaka ba, Ya Nana zata auri Muhsin dinta, bazan kara zamema kowa matsala ba, Abba bazai kara wahalan boyeni ba dan nariga namutu" yanda take maganan tana kuka mara sauti sai hawaye kobakada imani sai zuciyanka ta sosu, ahankali tace "Mami akwai wata tambaya dana dade inaso namuku keda Abba" taidan shiru saikuma ahankali tace "bayan kun haifeni maisa tun a asibiti dakuka ganni daban bakusan yanda kukai dani ba maybe ko kuce baku sona a kaini gidan marayu kokuma kuce a chanza muku yarinya bani kuka haifa ba, maisa kuka daukeni still kuka raineni maisa kukamin haka, wanan kalan rayuwan dakukasa inayi kullum zaban mutuwa nakeyi akanta dan tafimin alkhairi I just want to die nahuta, dan Allah kubarni na mutu" tafashe da kuka sosai dayasa daga Abba Mami da Hamad were damn speechless itako Uwani dake gefe kuka tadingayi, tadade tana kuka ajikin Mami babu wanda yay attempting hanata ahaka bacci yay awon gaba da ita, ahankali suka kwantar da ita akan kujera suka lullubeta sanan Mami tazauna gaban kujeran tana kallon fuskanta, Tashi Hamad yayi yakalli Abba da Mami yace "Abba I want to see you both" yay sama tashi Mami tayo takalli Uwani da jajayen idanunta tace "ki zauna da ita" gyadamata kai Uwani tayi Mami tawuce sama itama, Abba yadade tsaye awajen sanan yawuce yay sama, dakinshi Hamad yabude ya shiga Mami tashigo Abba dashine na karshe shima yashigo yasami waje yazauna, kallon Abba Hamad yayi yace "Abba what are you going to do? Yaya zakayi da maganan Kaka?" kallon Hamad yayi yama kasa magana saikuma chan yace "all I know is bazan taba iya koran y'ata daga gidan nan ba" dasauri Hamad yace "Abba yazakayi da bakin Kaka, tace inhar yarinyar nan batabar gidan nan ba bata yafemaka ba, itaba mahaifiyarka bace kaza kaza kaza, Abba Kaka ta tsufa and we all know yanda tsofaffi sukai believing akan all this superstition, Du'a tazaman ma

Please Login or Register in order to submit comment