Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gidan nan da family mu gabaki daya matsala, jibi duka su Baffa dazu sunce duk akoreta ni I think inhar hakane zan dauki Du'a natafi da ita chan Jaji tai zamanta a apartment dina" dasauri Mami tace "Hamad duk randa mahaifiyar ka tasan kaika tafi da Du’a abin bazai muku kyau ba, kuma Du'a mace ce bazaiyi kyau tayi rayuwa dakai kai kadaiba dama kanada mata ne, ni kaina ayanzu all I want is peace, tunda Du'a ce matsalan afitarda ita daga gidan saisa na yanke shawaran kaita wajen Mama na achan Abuja" kallon Abba tayi ahankali tace "Dadyn Hamad" kallonta yayi yay shiru batare dayace komiba, ahankali tazo kusadashi zama tayi sanan takama hannunshi tarike tace "I know tunanin dakake da abinda ke ranka, mu dinan bamuke kula da Du'a ba wlh Allah ne, so it's high time we free this girl mu mikama Allah komi and I assure u idan tana hannun Mama she's safe nasan Mama na, I don't want u to be stubborn, u are a family man, ba Du'a ce kadai yarka ba, sauran ma dole ka kalli yanda rayuwan su zata cigaba da gudana, sabida Du'a kar peace da family ka ya wargaje just look at what Nana is going through now itama ai yarka ce, the way u look out for Du'a itama haka kake looking out for her, kayakuri kaduba lamarin kaji" tunda take maganan yake kallonta harta gama, ajiyan zuciya yasauke sanan yace "I will think about it, kubani waje yanzu" gyadamai kai kawai Mami tayi ta tashi tawuce tafice, yakalli Hamad yace "ka kira Dr na yazo yadubata tashi katafi" tashi yayi ahankali yafice shikuma Abba ya kishin gida da kujera ya lumshe idanu Allah kadai yasan meke going azuciyanshi.



Wuraren magrib likita abokin Abba wanda shine likitanta tun tana yar karama yazo yadubata allura yamata sanan yabata magunguna Abba ya sallameshi yatafi.

"she's alive! she's alive I can feel her pulse" sama sama takejin maganganun nan kaman a eco saikuma chan tabude idanunta sukai clocking da nashi......tarrrr tabude idanunta daga baccin datake tanabin inda take da ko'ina na dakin da kallo, ganin tana dakinsu kan gadonta ne an lullubeta da bargo, mafarki take kenan, mutumin data bude ido tagani dazu yacirota daga cikin rijiya tagani yanzun nan amafarki, ahankali ta yunkura ta tashi zaune ta jingina da bango tana kallon ko'ina ganin gari yama soma wayewa, saukowa tayi daga gado sai alokacin taga wani jibgegiyan akwati da batasan daga ina yazo ba baka kwara daya atsaye gaban wardrobe dinsu, bathroom dinsu tawuce tashiga wanka tayi da ruwan zafi sosai tana karajin karfi ajikinta sanan tafito daga wankan daidai lokacin Mami nabude kofan dakinsu tana shigowa hada ido sukayi da Mami ahankali ta sunnarda kanta kasa tana tuna all maganganun data gayama Mami jiya suna dawomata fresh a memory dinta kasa motsi tayi itama Mami tadauke kai tawuce wardrobe wasu kaya taciro mata tajuyo ta ijiyesu kan gado tace "ki shirya kiyi salla bari naje nakawo miki breakfast".



Fita Mami tayi daga dakin itakuma tashiga shiryawa agurguje sanan tahau kan dadduma tai salollin dake kanta saida tai azkar sanan ta tashi ta cire hijabin tazauna akan gado, bude kofa Mami tayi tashigo dauke da tray na abinci sanan takaraso cikin dakin ajiye abincin tayi kan side drawer gadonsu sanan tadawo tazauna ahankali kan gadon kusada Du'a da kanta ke kasa har lokacin dan wani irin kunyan Mami taji tanaji, murya chan kasa tace "Mami ina kwana" shiru Mami tayi tana kallonta batare data amsa ba saikuma gently takai hannunta kan fuskarta ta tallabo habarta hakan yasa tadago idanunta ahankali takalli Mami, murya chan kasa Mami tace "Du'a" ahankali tace "Mami I'm sorry Kinji" murmushi Mami tayi tace "shiiii I want you to listen to me" gyadama Mami kai tayi, Mami tadan numfasa tace "all abubuwan dakikaga nida mahaifinki namiki badan mun tsaneki bane saidan we are all trying to protect you Du'a, Du'a nasan kinsan wanan abin dan nasan kinsha jin yan uwan Abban ku nafadi, dana haifoki babu kalan maganan da ba'a fadiba akanki, ance ke ba yar Abba bace, naje na nemi ubanki nahadaki dashi, ke mayya ce ke yar ruwace" shiru Mami tayi tana sauke ijiyan zuciya sanan tace "Du'a akwai many things which u don't know kuma banmason kisani, I fought mahaifinki, we fought hard muka samu yan uwanshi da Maman shi suka barki kika zauna agidan nan left to them koranki sukaso ayi" Mami tasakeyin shiru sanan ahankali takai hannunta tadaura kan kumatun Du'a dake kallonta ahankali tace "Du'a you are special! tun ranan damuka haifeki mukasan hakan, you are special saisa kikaga muna boyeki, Du'a ke dabance! muna boyeki ne cus munyi tunani ta hakan zamu iya kareki and protect you, but u got it all wrong kin zaci mun tsaneki ne amman bamu tsaneki ba, kintuna abinda yafaru dake a JSS2 dayasa Abba yahanaki fita at all kinaso yakara faruwa dakene" girgixa ma Mami kai tayi dasauri hawaye nacika mata idanu. Ahankali Mami tasauke ijiyan zuciya tace "nakira Mama, Grandma dinki tariga tasan komi dama, yanzu da safen nan Hamad zai kaiki chan wurin ta a Abuja harsai komi nagidan nan ya daidaita, I think kema is best for u, your childhood has been terrible, kin taso cikin kyaran kowa is high time kije inda nasan u will receive d best care batare da an kyareki ko an ware ki ba, kinason kije wajen Mama na ko" ahankali ta gyadama Mami kai hawaye na zubomata, hannu Mami takai tashare mata hawayen tace "nasan namiki laifi, I've wronged you in so many ways just to please yan gidan nan but bazan karaba, nina daukeki na raineki for 9 months I can never hate you, abinda nakeso dake is take very good care of yourself, kizama yarinya mai wayau da basira, know when u are in danger and when u are not, kidage da addu'a, ki rike Allah danshi kadai ya isarmiki, I want you to be a good girl, karki sake kima grandma dinki ko any of your uncles rashin kunya kinji Du'a, I know u are in a good hands this is the first time dazaakije wani wuri da hankalina ya mugun natsu, now eat your food saiki fito ki gaida Abban ki kuyi sallama bari nakai jakan I waje" gyadama Mami kai tayi Mami ta tashi jakan taja tawuce tafita daga dakin, shiru Du'a tayi Allah ma yasan har cikin ranta tana farin ciki zatabar gidan nan sabida tasan yanda Maman Mami kesonta lokacin tana yarinya idan sukaje gidan kaman zata cinyeta, koba komi bazata kara ganin Muhsin ba, mugun mutum, koba komi idan baiganta ba zai hakura ya auri ya Nana, Hawwa zata huta da hararanta kullum Mum ma tahuta babu wanda zai kara kiranta yar aljanu, and at the same time yau saitaji wanan bakin cikin da kunci na haushin Mami dayakeji dukya fita daga zuciyanta sabida fir the first time Mami ta zaunar da ita tamata bayanin abinda bata taba mataba kenan. hannu tamika tadauki tray abincin ta abincin taci bama tawani ci sosai ba ta ture ta ijiye, shigowa dakin Mami tayi takalleta tace "tasoto muje kiyi sallama da mahaifinki" gyadama Mami kai tayi gabanta nafaduwa hijabinta tasaka sanan tabi bayan Mami suka fito, Abba na zaune akasa yana karanta jarida hangita yasa ya tsayar da karatun yana kallonta harta karaso, dan nesada shi ta tsugunna ahankali tace "ina kwana Abba" "ya jikinki akwai abinda ke miki ciwo"? Abba yamata tambayan bayabo ba fallasa wanda idan tasabo tasaba dan Abba naturally he's not that kind of a friendly father dake wasa da yaranshi, gyadamai kai tayi ahankali tace "babu ko'ina Abba" gyadakai yayi cikeda gamsuwa yana kallonta, batare data dagokai ba tace "Abba kayakuri bazan kara abinda nayiba" ahankali yace "l know" dagokai tayi ta kalleshi, hannu yasa a aljihu yaciro bandir nayan 200 20k yace "zo" tashi tayi ahankali takarasa gabanshi karba tayi ahankali tace "nagode Abba" "Allah kiyaye hanya, jeki Hamad na jiranki a mota ta" hakanan batasan mesaba kawai taji kuka yazo mata dasauri tajuya tana daura hijabinta kan fuska Abba kuma yabita da kallo, fita tayi daga falon, Mami ta biyota abaya rikeda hadadden kula na abinci.



Hamad na tsaye gaban motan sienna Abba yaga fitowanta yana kuka, murmushi yayi yabude mata gaban motan tana karasowa tashiga ta zauna, karasowa itama Mami tayi tana murmushi tace "bazakama kanwarka magana tarage kuka ba tadauka yarinya ce ita" murmushi yama Mami baice komiba, Mami ta ijiye mata kulan akan cinyanta tace "ga abinci inkinji yunwa kici naga baki waniyi break da kyau ba and stop crying" gyadama Mami kai tayi, tashi tayi takalli Hamad tace "kutafi Allah kiyaye hanya" rufe kofan yayi sanan yazagaya yashiga yatada motan yaja Mami namusu bye bye suka fice daga Gate din. ajiyan zuciya Mami tasauke ahankali tace "Allah ya azurtaki da farin cikin rayuwa Du'a, I love you so much y'ata, zan dinga miki addu'a kinji Du'a"


💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫



✍️M SHAKUR



Free page
EPISODE 1️⃣ 2️⃣
Sosai Hamad ke zuba gudu akan titi, har cikin ranshi he is happy for Du'a na barin gidansu datayi, bini bini yake kallonta yanda saibin hanya da komi take da kallo kana gani kasan bata saba fitowa ba, dan juyowa yayi yakalleta ganin yanda take kalle kalle yasa yay dan murmushi yace "iyye basaban ba yau anfito waje" juyoda kanta tayi takalleshi washemai baki tayi tana murmushin nan mai tafiyar da imanin mutum tace "Ya Hamad rabon dana fito waje wlh harna manta nafi shekaru" murmushi yamata yace "this is a chance da Allah yabaki, remember abinda nafada miki duk wanda yadogara ga Allah to Allah ya isar masa, cikin sauki tashi daya Allah yacireki daga kuncin gidan mu, so babu abinda yagagari Allah muddin ki kayi imani, just always thank Allah kinji and be a good girl" gyadamaikai tayi kaman mai tunani tace "Ya Hamad nifa nama manta kamannin Maman Mami fa Grandma, tun ina karama da Mami ta taba zuwa dani ban kara zuwa ba, saidai muyi magana awaya, su Aneela ne suka santa" dan murmushi yayi hankalinshi nakan hanya yace "grandma dinki is one of the nicest person I know in this world, tanada kirki gatada son mutane, duk naje Abuja sainaje na gaidata, you are so lucky to have her as grandmother" shiru Du'a tayi kaman tana tunanin maganan shi saikuma chan ta kalleshi tace "Ya Hamad maisa kai u are different agidan mu? baka biyema su Mum da Ya Nana, kafisu kirki duka" yana kallon hanya still yace "let's say sabida ni namiji ne I see life differently daga yanda mata keganin life, and Abba yabani tarbiyan da nakan iya banbance right from wrong" murmushi tayi takalli kulan kan cinyarta tashiga budewa name ne soyayye da Irish da plantain. "bani nama naci" turo baki tayi tadauko nama daya takai tasamai akan hannunshi dayake bata, murmushi yayi ya wurga abaki yana taunawa yace "wow girkin Mami always taste different" nama daya itama ta dauka tamaida kulan tarufe sanan tahauci tanamai hira kadan kadan harta cinye sai bacci, kallonta yayi ganin yanda take bacci yasa yay murmushi gabgarawa gefen hanya yayi yay parking Sana yadan taso yasaukar mata da kujeran sanan yakoma mazaunin shi yatada motan yana bata wuta.



Wuraren 1 suka kai Abuja, tadata yayi ta hanyar kiran sunanta. "Du'a, Du'a" bude idanunta tayi kadan, hararanta yayi yace "duk uban baccin dakikayi jiya bai isheki ba yarinya saison bacci" tashi tayi yace "gyara kujeran" gyara kujeran tayi yataso sanan takalli hanya yace "kinga yanda Abuja keda kyau kalli titi ba irin na Kanon Kuba" murmushi tayi tace "mun kuwa kaiwa gidan" gyadamata kai yayi yace "takirani yafi sau uku duk kina bacci" shiru tayi tana kallon ko'ina kaman zata hadiye garin da idanunta saiwani irin sanyi da shauki takeji har sukakai wani estate mai suna Presidential Estate. zaro ido tayi tana kara kallon ko'ina ganin gidaje masu suna gidaje ba muna gidaje ba, tasha ji idan su Mum na gulman su tana yawan cewa ai Abba sabida ya rainata yar gidan masu kudi yaje ya auro mata, itama yarinyar kaman mayya itace kawai ta auri talaka mahaifiyarta tabarta ne sabida ita kadaice yarta mace, ita bazata iya tuna gidan dasuke zuwa a dan memory dinta na Grandma sonta lokacin tana yarinya akazo kuma aka dena zuwa da ita saidai su Aneela da Muhammad da Mudasir.


Shiga Estate din yayi yana tafiya ahankali ganin yanda Du'a is enjoying the view din, agaban wani lafiyayyen gida Hamad yay horn, wani security yafito ganin Hamad yasa yace "barka da zuwa yallabai Hajiya ta sanar dani zuwanka" gyadamai mai kai Hamad yayi yana murmushi shikuma yakoma ciki yabude musu Gate din, Jan motar ciki yayi Du'a ta kwalalo idanu tace "nan ne gidan Grandma Ya Hamad" murmushi kawai yamata yana karasa parking motansu acikin jerin motocin dakenan gidan wanda babu mate din seinna su, bude motan yayi yafito sanan yamata alamu data fito gyadamai kai tayi daidai security yagama kulle gate yazo yace "akwai akwati ne Yallabai" "oh yeah" Hamad yafadi yana budemai booth daidai lokacin Du'a takaraso wajen tsayawa chak security yayi yana kallonta ganin haka yasa Hamad yace "ga akwatin" dasauri yajuyo yakalli Hamad hannu yasa yadauki akwatin yawuce Hamad kuma yarufe booth din yajuyo daidai lokacin wata hadaddiyar mata wacce kana ganinta kasan ba yarinya bace dan ta ijiye jikoki tafito, tana sanye da bubun atampa ajikinta gatanan black beauty da akalla zatakai 70.


"oyoyo oyoyo, su maigida an iso" jin muryanta yasa dasauri Hamad yajuya washe baki yayi yace "Hajiya wanan kwalliya haka, bazaki barma yara ba" dakuwa tamai tace "kaci gidanku, yanzu dani dasu idan akaje gasan kyau basai akwasheni sau dari baza'a kwashe suba" karasawa yayi har inda take sanan cikeda girmamawa yadan runtsuna yace "ina yini Hajiya" hannu tasa tashafa kanshi tace "kasha hanya Soja na maigida, jekai wanka kahuta kaida komawa kano sai gobe" tai maganan tana kallon Du'a dake bayan Hamad kanta akasa tana wasa da hijabinta kunya yahanata dago kai. "Du'a" matar takirata ahankali, ahankali Du'a kaman wacce ke tsoro tadago kanta takalli kakanta fess tagane ta danga kamanninta da Mami nan, black beauty abinta yar gayu, ganin takasa magana yasa dasauri tabude mata hannu tace "zonan zoki rungumeni, taho taho" ahankali Du'a taje dasauri tashige jikinta takankameta kankameta Hajiya tayi tace "Alhamdulillah Alhamdulillah, Du'a sannu, sannu kinji, akwai abinda ke miki ciwo"?girgizamai kakan nata kai tayi, dagota Hajiya tayi tasa hannu tai cupping face nata tana kallonta kaman yanda Du'a me kallonta ahankali rasama mezatama yarinyar tayi hakan yasa ta manna mata kiss a goshi sanan takama hannunta tarike tace "muje nakaiki dakinki kiyi wanka"


Ciki tashiga da Du'a falon wani irin hadadden gaske gashinan Duplex sai yan aiki guda biyu dataga suna gyara dinning suna ganin Du'a duk suka bitada kallo suna gaidata. "welcome Du'a" murmushi Hajiya tayi tace "kingan su suke tayani aikace aikacen gida, wanan sunanta Shema'u, dayan kuma sunanta Razika, duk sun sanki, jeki musu sallama" gabansu taje ahankali sai kallonta suke kaman basu taba ganin mutum ba, hannu tamika musu cikin muryanta mai dadi tace "Assalamu Alaykum, nice to meet you" dasauri suka karbi hannunta suna murmushi Razika tace "you are so beautiful" tsayawa tayi turus tana kallonsu Hajiya dake kallonsu tace "tell them thank u sunce kinada kyau" ahankali tace "thank u" sakinta sukayi itakuma Hajiya tasauke ijiyan zuciya sanan tace "taho mutafi" dasauri tajuyo kaman jira take dama stairs sukayi sukai sama saitaga ashema kasan baida kyau wani daki tabude dakin mai kyau sosai saiga hoton ta datana yarinya tana rarrafe kusada Hajiyan dasauri tashiga dakin tana kallon hoton, murmushi Hajiya tayi tace "lokacin kina yar tatsitsiya keda Mamanki kunzl ganin gida, little Du'a, jeki yi wanka kizo kici abinci zan baki labarin anjima" gyadamata kai tayi sanan tacire hijabi ahankali tawuce zuwa kofan datagani wanda ta tabbata bathroom ne saida tashiga sanan Hajiya tafita daga dakin.


Saida tayi wanka sanan tafito daure da towel, akwatin ta dataga anshigo dashi tabude tadauki wata doguwan riga wanda yawanci kayanta dogayen riguna ne daidaikune riga da skirt, saka rigan tayi sky blue ce mai kyau sanan tasaka hijabi salla tayi sanan tazauna tana tunanin maganan Hajiya datace tasauko, tashi tayi ahankali tacire hijabinta ta ijiye sanan tabude kofa tafito, ahankali take sauka daga stairs tana karabin gidan da kallo, daga sama sama takejin maganan Hajiya da Hamad saikuma takarasa suna ganinta sukai shiru. "kin idar tahonan" tauna mata kusada ita akan dinning hakan yasa ta taho zama tayi wajen Hajiya tace "debi abincin ki kici" dasauri Hamad yace "kafin namanta banfada mikiba kuran nama tazo gidan nan ba" turo baki tayi Hajiya ta harareshi tace "karkaga kana maigida kanemi samin jika kuka sama zamu hau nidakai, ci abinci ki kinji kome kikeso" gyadama Hajiya kai tayi sanan tadebi rice da stew da plantain da fish tanaci, bini bini Hajiya ke kallonta hartaci rabin abincin sanan tasha ruwa haka



💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫


✍️M SHAKUR

EPISODE 1️⃣3️⃣
Har dare hira suke Hajiya da Hamad, kagansu zaka dauka Hamad jikan ta ne, Hajiya wata irin mace da idan kana tareda ita you have no reason or what so ever to hate her ne, kodan sabida yaranta biyu kachal aduniya saisa takeda son mutane haka oho, danta na farko yaranshi uku dukansu Maza kuma kanana dan Mami tariga shi aure yana UK achan yake aiki sai Mami dakeda yara hudu tana aure a kano, Bayan Mami ta haifi wata tarasu, Hajiya is very very educated, lawyer ce babban gaske amman yanzu tai retire saidai she's still an advocate na Human right, batun yauba taso tadauki Du'a, akwai lokacin data kusan kulle Maman Abba wato Kaka, sabida kukan da Mami tamata ne tana rokonta yasa tahakura daga lokacin tai fushi da Mami ta shareta, saisa koda wasa bata taba taka kafarta agidan Abba ba dan batada daukan nonsense and zasuga yanda zata maida yarinyar nan, Du'a tariga tabar gidan nan kenan har abada saidai in bata raye.


Ganin Du'a na gyangyadi akan kujera yasa ta tadata. "Du'a Du'a tashi kije ki kwanta adaki" ahankali ta tashi murya chan kasa tace "saida safe Grandma" murmushi tamata tace "kiyi alwala sanan kiyi addu'a kafin ki kwanta kinji" gyadamata kai tayi sanan tawuce, dakinta tabude tashiga tamaida kofan tarufe, bayi tashiga tadauro alwala kaman yanda aka umurceta sanan tafito, fadawa kan gadon tayi tana karanto addu'an bacci sanan taja bargo ta lulluba tana rufe ido fuskan mutumin nan tagani yay flashing a idanunta dasauri tabude idanunta tana yaye bargon tafito da kanta waje tanabin dakin da kallo, mutumin daya ciro ta daga rijiya she just saw fuskanshi, lumshe ido tayi ahankali still tana ganinshi saikuma ta girgixa kanta kaman tana kokarin koran abin dan bataso tana ganinshi, ahaka bacci yay awon gaba da ita......


Hajiya tashigo dakin da asuba ganin wutan dakin A kunne, karasawa gaban gadon tayi, zama tayi atabaki bakin gadon tana kallon fuskanta, Du'a is just different! ahankali takai hannunta ta kwashe gashin daya sauka a gefen fuskanta, shafa gefen fuskanta tayi tana kiranta ahankali. "Du'a, Du'a atashi daga bacci asuba tayi" bude idanunta tayi ganin kakanta yasa taji kunya murmushi tayi dasauri Hajiya tace "na tabbata yau zata yalwatu da ni'ima a gareni, wanan kayataccen murmushi dakika gaisheni dashi Du'a, Masha Allah jikata is very beautiful, barakallahu fiki, tashi kiyi alwala kizo kiyi salla kifito kuyi sallama da Hamad yashirya zai tafi" gyadamata kai tayi Sanna tasauka daga gadon ahankali bathroom tashiga itakuma Hajiya tawuce tafita.


Saida tai salla sanan tafito sanye da hijabi, a falo tagansu suna zaune Hamad na rike da mug yanashan coffee, karasowa tayi ta tsugunna ahankali tace "ina kwana Grandma" "kintashi lpy Du'a ya kwanan Abuja" murmushi tayi tace "I love here Grandma, Ya Hamad good morning" "morning dama ke nake jira zantafi" yatashi bayan ya ijiye cup dinshi, Hajiya tace "sa takalmin ki kiraka yayanki" tashi tayi tasaka slippers din da Hajiya ke nuna mata sanan tabi bayan Hamad suka fita daga falon sauka suke daga matattakala kaman daga sama yace "ya akayi kika fada rijiya Du'a" dawani irin sauri takalleshi ta tsaya batare data cigaba da tafiya ba hakan yasa shima ya tsaya yana kallonta yace "answer me" murya chan kasa tace "Muhsin din Ya Nana ne yazo" dawani irin sauri cikeda mamaki yace "Muhsin"gyadamai kai tayi tabashi labarin komi iya wanda tasani, shiru yayi saikawai yay kwafa yace "muje" binshi tayi harwajen mota, sanan ya tsaya yace "be a good girl kinji, kinga yanda rayuwanki take kasancewa awajena maza so be careful kinji" gyadamai kai tayi shafa gefen fuskanta yayi yace "wuce ki koma ciki bye" waving hannu tamai tawuce shikuma yashiga mota yatada yabar gidan bayan security yabudemai gate.




Ahankali da sallama tabude falonsu tashiga, Hajiya na zaune kan kujera tanacin fruits dake cikin bowl akan cinyanta, ganin Du'a ta shigo yasa tanuna mata gefenta tace "zoki zauna anan Du'a" murmushi tayi takaraso wajen tazauna, bowl din tanuna mata tace "zaki sha fruits"? gizgiza mata kai tayi tace "na koshi" murmushi tamata tace "karki damu nariga namiki friends sunje kano ne but maybe tsakanin yau ko gobe zasu dawo zaki gansu yanmata kaman ke zadan su girma miki but I'm sure u will like them" murmushi tayi tace "thank you Grandma" murmushi tamata sanan tace "yanzu abinda ke mind dina is school, banso kishiga secondary school dan kinyi girma saidai lessons, koda wasa bazakiyi rayuwan kullen nan dakikayi agidan ubanki ba, don't worry I will think of what to do akanki, yanzu dai zansa driver na yadauke ki Razika zata biki kije saloon ama gashin nan lafiyayyen gyara ko amiki kalba ko kitso duk wanda kikeso, sanan amiki gyaran farce right" gyadamai mata kai tayi tana murmushi, Murmushi itama Hajiya tayi tace "answer da naki stop nodding head be acting like a big girl okay" murmushi tayi sosai wanan karan tace "okay Grandma" "good girl, jeki shirya kiduba wardrobe dinki akwai kaya awajen kisa daga nan" harzata gyadamata kai saida sauri tace "Tom" wuce wa sama tayi Grandma tabita da kallo harta bace mata.



Wardrobe din dakin tabude hadaddun karyane wanda mostly abaya ne, dogayen riguna kala kala daban daban, ahankali tadaura hannunta kan wani baki fitodashi tayi daga leda tana kallon rigan kaman Grandma ta aunata shiryawa tayi cikin rigan saikuma dagudu tai wajen madubi tana kallon kanta yanda taga tayi kyau ko Nana su bata taba ganin tasaka doguwan riga mai tsada nan ba, murmushi tayi tadaura dan kwalin saman tadauki hijabinta akai tasaka tafito tasauko kasa Hajiya na ganinta tace "ina gyalen abayan Du'a" dasauri tace "nadaura akai Grandma" dan dariya Hajiya tayi saikuma ta mike tace "zokiga" karasowa gabanta tayi Hajiya ta yaye hijabin dan kwalin ta warware sanan ta gyaramata parking gashin, takalli Razika dake wajen tace "he daukomata handbag a dakinta Razika" da sauri tai sama, taimata rolling gyalen saitai kaman wata balarabiya, saukowa Razika tayi da jaka mai kyau, Hajiya ya karba tabata tace "perfect oya kutafi to driver na waje yana jiranku" takalli Razika tace "stay by her side, saikun dawo, bye Du'a" juyowa Du'a tayi tamata waving hannu alamun bye sanan suka wuce suka fita sai murna take basabamba, mota suka shiga direban yajasu.



💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫


✍️ M SHAKUR

Free page
EPISODE 1️⃣4️⃣
Bini bini direban Hajiya dake sanye da uniform ke kallonta tamadubi, hakan yasa Razika takalleta, ganin yanda take kalle kallen hanya tana murmushin nan dake karamata wani kalan kyau nadaban yasa Razika tace "is this ur first time a Abuja Du'a?" juyowa tayi tazubama Razika mayun idanunta dakesa mutum yaji wani kwanciyan hankali harzata gyadamata kai ta tuna maganan Hajiya hakan yasa tace "eh" murmushi sosai Razika tayi tace "Abuja ai nada kyau, nima Hajiya tadaukoni daga kauyen mu takawo ni nan, sanan akwai lesson teacher dake zuwa mana karatu duk asabar da lahadi, Hajiya nason yara, kinga tunda nake a Abuja bantaba ganin yarinya mai kyau kaman keba" dan murmushi tayi saikuma tadauke kanta tamaidashi kan titi tana

Please Login or Register in order to submit comment