Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

we are finally about to get married, dan Allah karkamin haka, kataimakama rayuwana Muhsin kasan yanda nake sonka please Baby" fizge hannunshi yayi yace "stop talking nonsense, wlh bazan aureki ba kinjima na rantse, ni Du'a nakeso ita zan aura" yajuya zai tafi dawani irin sauri tasha gabanshi ta zube ta hanyar kneeling down tahade hannayenta tana kuka tace "please stop saying kanwata zaka aura, please stop saying that, wlh karabu dani zan iya mutuwa Allah kuwa Muhsin dan Allah karkamin haka, you know how much u mean to me eh, me zakayi da ita? babu abinda banfitaba kawai saidai ta nunamin haske" zaro ido yayi yace "what! are you crazy, karki kara comparing kanki da yarinyar nan dan wlh tafiki komi, nima daman zan aureki ne because u are full dan banson mace ramamma, kinada big boobs da ass you know that's what I like, but damn!!!! Du'a shape is bura'uba! her shape is life threatening, idan bansami yarinyar nan namore rayuwa da itaba I can die, ke kinga ass da boobs wane naki, see maddd flat tummy, see snatched waist, I don't think kugunta yakai 10, ke abeg go gefe we are talking about Kim Kardashian anan danko Kim taga Du'a she go run go hide" dasauri tashiga hade hannayenta zatai magana hankadeta yayi yabita gefenta yawuce yace "saikuma kiyi bayan nagama rantsuwa cewa bazan aureki ba kome zakiyi saidai kuma kiyi ni kanwarki nakeso wlh, am off zanturo Dad anjima da night" yana maganan yay gaba zuwa compound dinsu yaje yashige hadaddiyar jeep dinshi mai gadi yabudemai gate yawuce yafita abinshi.




Takai morethan 15min awajen kuka take sanan wani irin zuciya yadibeta ta tashi tai ciki ta kofan kitchen tabi Mami na kitchen tana kwashe abinci amman ko kallonsu batayiba tana kuka tawuce fuuu ta tafi falo tashiga Mum dake zaune tareda Hawwa suna magana ne sukaga shigowan Nana tana kuka sosai bamata luradasuba tai hanyar stairs dasauri Mum tamike tace "Nana ke lafiya gani nan anan, menene kike kuka haka"? dawani irin sauri tajuyo tadawo batai wata wataba tafada jikin Mum tazube sai kuka, daga Mum har Hawwa rudewa sukayi, Hawwa tace "Ya Nana menene fada kukayi da Muhsin ne" cikin kuka sosai tace "Mum Muhsin yace yafasa aurena wai Du'a zai aura" chak Mami datafito rikeda kula ta ijiye kan dinning ta tsaya dubus awajen tana mamakin mekuma yakawo sunan Du'a a zancen su. Mum dama tarude sabida yanda yarinyar ke kuka tace "Du'a kuma, ta ina Muhsin yasan wata Du'a dahar zaice miki zai aureta iyye, kinsan mekike fadi kuwa"? Mum tai tambayan sounding so confuse and shocked dan batagane kan zancen yartataba, cikin kuka sosai Nana tace "Mum bayan nadauki zobo naje kaimai ajikinshi naga Du'a suna hira haryanama tabamata gashi taciremai dankwali, kuma idan karya nayi kije garden tama barmai dankwalin ta har novel dinta awajen ma" cikin wani irin mugun zuciya jikin Mum har kyarma yake tashiga kwalama Du'a kira.


"Du'a! Du'a!!! ki sauko kasan nan dakanki kafin nazo dakin nan wlh dan na lahira zai fiki jin dadi" bude kofa tayi ahankali tashiga saukowa idanunta sunyija sabida kuka tashiga saukowa daga stairs hada ido tayida Mami dake tsaye a dinning tana kallonta kaman yanda itama take kallon Mami, kasa karasa saukowa tayi Mum tace "zaman lafiyanki shine ki amsa tambayan dazan miki batare dakinmin karyaba inba hakaba yau saina kusan nakasaki wlh, kin sauka kasa ko baki sauka kasaba"? kama jikin skirt din lace dinta tayi gam gam tsabagen tsoro tana kallon Mami tsabagen tsoro sanan ta kalli Mum tace "bayan nai salla shine ta window na leka naga su Aneela nawasa a compound shine nasaci hanya ta kitchen nafita, to naji muryanku a kitchen shine na kwasa da gudu sabida kada ku ganni wlh wlh ni bansan da mutum a garden ba tuntube nayi dashi zan fadi shine yataroni" fashewa da kuka tasakeyi sosai tace "wlh wlh ni banma sanshi ba Allah kuwan Mum"



Cikin wani irin bakin zuciya Nana tai inda take a stairs wani irin finciko gaban riganta tayi ta chakumeta tace "karya kike baki sanshi ba, kinji ina waya dashi jiya da daddare munyi zaizo yau saisa yau harda cin kwalliya haka sabida ki kwacemin wanda zan aura ko, baki sanshi ba ubanme mikikeyi ajikinshi"? Cikin kuka sosai tace "wlh Ya Nana niban shiga jikinshi ba hannuna yarike kuma inata kokarin na kwace yaki sakina, shine yazo zai tabamin gash......" wani irin kishine ya kwashi Nana tawani kaimata mugun duka abaki bata cire hannu ba sai jini bakinta tasake fashewa da kuka, kimarta Nana tashiga yi baji bagani Mum tace "yima shegiyar yar Aljanun mugun duka Nana, yimata jina jina, itada uwarta sunga kinyi miji daga gidan arziki shine aka turata tayomiki kwace tarabaki dashi, duniya inhar baka mutuba baka gama ganin abin kallo ba, kimeta da kyau kyan datake takama dashi ki chanza mata halitta" yanda Nana ke dukanta tana bubbugata da kome tasamu yasa tafara ihu tana mika hannu tana kwalama Mami kira dan bata iya fadaba bamatasan yanda zata fara dukan yartaba kwata kwata, ahankali Mami tajuya tacigaba da arranging dinning table din datake, kannensu dake wasa ihun dasukaji yasa duk suka shigo ciki suka cika falon, Aneela tafashe da kuka sosai ganin yanda ake dukan yayarta.



Juyawa Mum tayi takalli dining ganin Mami tajuya tacigaba da arranging dinning abinta yasa tai wani irin murmushin mugunta tace "barka mata shegen rigan nan dataje tana kokarin kwacemiki miji dashi kannenta suganta taji kunyan duniya" wani irin bugata da tiles Nana tayi jikake kum Nana tawani juyarda ita tawani yage zip din riganta tanajan rigan zata ciremata, rike rigantayi tana kuka sosai tace "Ya Nana yakuri, Mamiii" tasake kwalama Mami kira dan mugun kunya take aganta, Mum da ranta fess dan tadade tanason gumama Mami amman tarasa ta yanda zatayi saiyau Allah yabata dalili mai kyau tace "fizge rigan duniya da kannenta suga abinda take boyewa, haka akema yan iskan yara masu son kacema yayyinsu mazajen dazasu aura, fizge rigan kannenta suga nonuwan marasa fasali" fizge rigan Nana tayi tayar Mum tace "yara ku kalleta kumata woyiiii" su Muhammad sukahau woyiiii dan basusan meke faruwaba yarane, throw pillow kan kujera taja takankame tana boye kirjinta, Nana tawani sake dauketa da mari tahau ruwan cikinta tana nausa daidai lokacin Abba da Hamad suka shigo dakin, shiru yaran dake woyi sukayi jikake dakin kaman andauke wuta sai muryan Du'a da baima fitowa da kyau tana kiran Mami Mami take, awani irin zuciye Abba yay wajen wani irin dago Nana yayi tsaye sanan yakai mata lafiyayyen mari Pau!!!!!!



Dasauri Mum tace "idan duka zakayi Alhaji ni zaka daka danni nasa Nana tama shegiyan makiran yarinyar nan duka tacire mata riga kannenta sumata ihu" wani irin kallon Mum yake kafin yabi kowana dakin one by one da kallo sanan idanunshi suka sauka kan Mami dake dining tana arranging kula cikin kakkausan murya yace "Zainab kina nan wajen kina tsaye zasu kashe Du'a can't you intervene, wani irin banzan hali ne wanan" juyowa tayi takalli Abba idanunta sunyi ja sosai cike da tsananin kunci tace "Dadyn Hamad mekakeso nayi eh? mekakeso nayi? Ya zanyi da raina?Tun ranan dana tsugunna na haifo wanan yarinyar duniya nake shiga bala'i kala kala? Babu kalan shairin da ba'a yimin ba kan haifo yarinyar nan, tunda na haifi Du'a ban kara samin kwanciyan hankali ba, kome yasameta ita tajama kanta kahanata fita waje ubanme yakaita garden? Gasu gatanan idan suka kasheta kaga kowama yahuta daman tun ranan dana haifota tazamema kowa kashi a wuya ankasa taunata, ankasa fitoda ita, ankasa hadiyeta, nima nagaji I am tired of everything, I'm tired" kawai saiga kuka yazo mata dasauri tabar dinning din tawuce sama tabude dakinta tashiga abinta.


Juyoda kanshi Abba yayi yakalli Mum da Nana dake kuka itama yace "kuwuce kuje kujirani adakina" wucewa sukayi sama, sanan ya kalli yaran yawani daka musu tsawa yace "to your room dukan ku" dasauri kowa na falon ya watse, Abba yajuyo yakalli Hamad yanunamai riganta yace "bani riganta" wucewa yayi yadauko rigan shikuma Abba ya tsugunna yatallabota zuwa jikinshi yana kallon fuskanta yanda goshinta ya kumbura ga bakinta jini, gefen fuskanta yay ja sosai, bashi rigan Hamad yayi Abba ya karba sanan yakama hannunta yasamata rigan kafin yarufe mata kirjinta dashi sanan yaja throw pillow data rufe kanta dashi ya yar sanan yasamata dayan hannun rigan yadagota zai saka mata zip tafashe dawani wahalallen kuka sosai ahankali Abba yace "ina ke miki ciwo"? Cikinta ta nunamai, daga riganta yayi yakalli cikin ga alamun naushi nan duk sunyi jajja, Hamad dake tsaye kansu yace "Abba bazamu kaita hospital ba kuwa what if tanada internal bleeding" girgiza mai kai Abba yayi yace "get me a towel and hot water da rob" wucewan kitchen yayi dasauri yakawo ruwan zafi da towel.


Karba towel din Abba yayi sanan yasa a ruwan zafi yaciro yadaura kan cikinta yana matsamata fashewa da mugun kuka tayi tarike Abba tace "wayyo Abba zafi, Abbbaaaa" sosai ran Abba yabaci kuma yay alkawari saiya mugun sabamata, tun tana kuka yana fitowa harya dena saidai hawaye, saida yagasa harda goshinta da bakinta sanan yashafa mata rub din tass, sanan yakalli Hamad yace "kaje phamarcy and get drugs for her she can't go to hospital" gyadamaikai Hamad yayi sanan yawuce yafita shikuma Abba yatashi daukanta yayi tana jikinshi dantamayi bacci kwantar da ita yayi kan gadonta sanan yasa bargo ya lullubeta yadade tsaye akanta sanan yawuce yafita daga dakin.


💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫



✍️M SHAKUR


Free page
EPISODE 5️⃣
Dakinshi yawuce, bude kofa yayi yashiga dakin Mum na zaune kan kujera itakuma Nana tana zaune akasa tana share hawaye danhar lokacin kuka take ganin Abba yashigo yasa gabanta yacigaba da faduwa dan gabaki dayansu suna tsoron mahaifinsu danko kadan baida wasa sanan yanada zafi.


Maida kofan yayi yarufe sanan yashigo ciki har lokacin kanta nakasa sanan yawuce yazauna kan kujeranshi yana facing bata, cikin kakkausan murya yace "maiya hadaki da kanwarki Du'a Nana"?Hawayenta tashare cikin sheshekan kuka tace "Abba dazu Muhsin yazo na shimfida mai dadduma a garden shine nakoma nadauko zobo ina zuwa naganshi tareda Du'a....." yanketa Mum tayi tace "fadama Babanku komi kina bobboyemai kikaga dai Du'a ajikinshi" wani irin kallo yama Mum sanan yace "kika kara magana batare danabaki izinin kiyiba wlh saikinyi mamakin abinda zan miki" yajuya yakalli Nana yace "ina jinki" sake share hawaye tayi tace "Abba tarena ganshi da Du'a babuma dan kwali akanta yarikemata hannu yana kokarin tabamata gashi, shine Du'a na ganina tahau kuka wainace yasaken mata hannu, sakinta yayi ta tafi shine yacemin waishi bazai aureni ba wai Du'a yakeso ita zai aura yanzu bayasona waizaije yagayama babanshi" shiru tayi takai bayan hannunta ta goge wasu sababbin hawayen dasuka zubomata.
Gyara zama Abba yayi ranshi amugun bace yana kallonta yace "dago fuskanki ki kalleni nan" girgixa mai kai tayi takasa, hakan yasa yadaka mata tsawa yace "I said look at me" dasauri tadago kanta takalleshi jikinta har bari yake tsabagen tsoro da shakkan Abban ta yace "so sabida namiji ne kike neman kashe blood sister ki, da Allah bai kawoni gidan nanba dayau kinyi kisan kai eh!" yasake dakamata tsawa kana ganin yanda yake maganan kasan ranshi abace yake, yace "to the extend kina ciremata riga exposing your fellow sister body kannenku su ganta, Nana is that how I train you eh answer me" fashewa tayi da kuka sosai tace "Abba kayakuri bazan karaba" girgixa mata kai yayi yace "kece y'ata mace tafarko yau idan namutu I believe kece zaki kula dasauran kannenki u will be their mother but look at what you did today, sabida namiji eh? sabida yace bazai aureki ba and so what zaki kashe yar uwarki ur blood sabida wani eh? Saina hukuntaki sosai Nana, stand up jeki kawomin wayanki, your laptop ki kawomin ATM card dina danabaki" fashewa tayi dakuka sosai dan babu abinda yafi tadamata da hankali irin wayan dawani wayazata kira Muhsin su shirya, ita karan kanta Mum saida ta girgixa amman takasa magana dan taga ranshi inyay dubu yabaci. cikin kuka Nana tace "Abba dan Allah kayakuri nayi kuskure amman namaka alkawari bazan karaba" wani kallo yamata yace "you know my principle bana dukan yara, but kika bari natashi daga wajen nan batare dakinje kin kawo what I asked for ba sainamiki jina jina" wani kallo Mum tamata na alamun taje takawo hakan yasata tashi tafita bata bata lokaci ba tadawo takawo komai kujera yanuna mata yace "keep them there and leave this room, sanan dagayau!" yajuya yakalli Mum yace"ki sallami Uwani duk wani aikin Uwani ita zata dingayi bazatabar gidan nanba saita gama kodako zatai lattin lectures get out" dasauri tajuya tafita tarufo musu kofan.




Wani kallo yabi Mum dashi yace "I am so disappointed in you Hajara, halinki nabani mamaki and ki sauraren kiji bazan zauna inaji ina gani ki rabamin kan yarana ba, wlh duk randa kika kara attempting abinda kikayi yau kinasa anacirema yarana mata kaya kina kiran yara suyi ihu wlh wlh saina rabu dake take this as a warning" cikin kwantar da murya tace "kayakuri Alhaji na yarda nasan nai kuskure I know I took everything far, but raina abace ne maganan da Kaka keyawan fadi duk yadawomin kai, wlh Alhaji da gaske Du'a yar aljanu ce to inba hakaba ya za'ayi Muhsin dake tareda Nana kusan sjekaru biyu kenan yau kawai daga ganin Du'a yace ita yakeso yafasa auren wacce yasani for years, dududu bikinsu saura wata daya, tuntuni Kaka tace ka tattara yarinyar nan ke korata chan duniya inba hakaba bala'i da masifu iri iri sundinga samunta gidan nan kenan, yanzu maganan Muhsin baiwani dadani da kasaba amman what if dagaske yake eh? da gasken gaske yake shi yafasa auren Nana Du'a yakeso bahakan ya tabbatar mana itadin yar Aljanu bace ba kenan, wlh indai aka fasa auren nan saina kira Kaka na sanar da ita komi gwara tun yanzu nagaya maka sabida kar bayan kaji nayi kaga kaman na yaudareka ne" "tashi kifita daga dakin nan" Abba yay maganan cikeda fada, tashi tayi tace "narasa me kakeyi da yarinyar dakai karan kanka kasan bataka bace agidan nanba saisama baka ambato sunanta cikin y'ayan ka, hakanan wlh koma mezai faru saidai yafaru I am a mother bazan zauna inada zankada zankadanyanmata ba sukasa aure ba sabida yar aljanun da aka haifa maka agidan nan, gaskiya nake fadi I can go to any limit dannai protecting yarana, grounding nata adaki doesn't solve anything dan gashinan fita take causing trouble, the best thing is tabar family mu takoma chan family su na aljanu" tai maganan tana bude kofa tafice abinta, gabaki daya duka abinda tafadi yajisu.



Ajiyan zuciya yasauke ahankali tareda fuzarda iska daga bakinshi yadade ahaka zaune sanan yatashi kaman an tsikareshi, bude kofa yayi yafice, hanyar dakin Mami yayi, ahankali yasa hannu yabude dakinta wani kamshi ne yamai sallama, shiga ciki yayi tareda maida kofan yarufe, tashi tayi tsaye daga kan gadon datake zaune idanunta sunyi jajir takakalo murmushi tace "sorry Dadyn Hamad bankawo maka abincinka ba" tazo da sauri zatabi ta gefenshi tawuce hannunta yakamo sanan yajawota jikinshi fuskanta ya tallabe yace "you've been crying ko jibi yanda idanunki suka kukkumbura" girgizamai kai tayi zatai magana saiga wani kukan kuma hakan yasa dasauri yasata ajikinshi yana bubbuga bayanta batare dayayi magana ba, tadade ahaka sanan tadago ta kalleshi tace "Abban Hamad kafin muyi aure ai kokai saida aka tabbatar maka dana warke ko naji sauki, babu any form of jinn ajikina, bana wasa da azkar safe rana da dare, yau shekara nawa muna tare ba kara having any form of attack ko mafarki ba, but yau nafara tunanin kodai sune baban Du'a di......." hannu yadaura mata akan baki yace "shiiiiii banson maganan nan, kintaba ganin jinn sun haifi mutum? nine mahaifin Du'a, kawai Allah yabamu y'ace daban damu nothing more nothing less" girgizamai kai tayi tace "what if Muhsin da gasken yafasa auren Nana Yaya zamuyi? how are we going to explain this to the family Yaya zamuyi" saiga wasu sababbin hawayen, yatsanshi yakai yasharemata hawayen daya zubomata yace "when we get to the bridge we will know ta yanda zamu tsallaka shi karki damu kanki kinji" gyadamaikai tayi ahankali wasu hawayen na zubo mata tace "Dadyn Hamad Du'a batajin magana, we've grounded her for years now tundaga JSS3 har zuwa yau, amman kwanan nan tasoma sneaking tana fitowa, hakanan inaji araina something is about to happen, what if tasake samin attem........." hannunshi yadaura kan lips dinta yace "stop talking, and stop thinking negative, idan tafarka nida ita we will have some serious talk, yanzu all abinda nake bukata is natsuwa dan banda ita ko kadan, ina bukatan natsuwa sanan nasamu nayi tunani, bari nasami natsuwa dake" yana maganan yadauketa zuwa gado bashi yafito daga dakinba sai wuraren 5 ya chanza kaya zuwa jallabiya fuskanshi tayi wani annuri alamun akwai full natsuwa taredashi yasauka zuwa falo, Mum na zaune a falo tadauke kai kaman bata ganshi ba.



Saukowa Mami tayi taci sabon kwalliya Mum tabita da harara tace "kidaiyi kigama gobe zan karbi girkin" serving Abba tayi sanan tazauna gefenshi tana bashi duk wani abu dayake bukata.



💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫



✍️M SHAKUR

Free page
EPISODE 6️⃣

Bayan sallan isha'i Abba baima dade da dawowa daga masallaci ba shida Hamad dasu Muhammad ba mai gadi yayi sallama izini Hamad yabashi yashigo, shigowa yayi har gaban Abba yace "barka da hutawa Alhaji, kanada baki, sunce wai Alhaji Ibrahim mai tabarau ne" kallon Abba Hamad yayi yace "Baban su Muhsin ne Abba" tashi Mum dake zaune afalon tayi ta kalli su Muhammad tace "yara kuwuce mutafi sama Abban ku yay baki" binta yaran sukayi sukai sama, kallon mai gadi Abba yayi yace "kamusu iso" Maigadi yawuce yatafi, Hamad yakalli Abba dayaganshi anatse yace "Abba yaya zamuyi idan dagaske Muhsin yake"? Murmushi Abba yayi bai bashi amsaba yace "just stay here and learn, duk randa bani kaine zakai making decision akan kannenka mata" gyadama Abba kai yayi daidai lokacin mai gadi yay sallama yabude kofa yashigo dasu hakan yasa Abba da Hamad suka tashi don agaisa, wasu Manya manyan attajirai ne su uku sai Muhsin dake taredasu kana ganinsu you don't even need an explanation kasan masu hannu da shuni ne, hannu Abba yamika musu cikeda girmamawa suka gaida dan mahaifin Muhsin ne Alhaji Ibrahim maitabarau sai kannenshi guda biyu Alhaji Isyaka Maitabarau sai Alhaji Mubarak Maitabarau, sosai Abba yagaisa dasu cikin mutuntawa yasa suka zazzzauna Muhsin shima ya gaida Abba cikeda girmamawa ya amsa, Hamad ma yagaidasu suka zauna cikeda girmamawa, shigowa Uwani tayi takawo drinks da ruwa sanan tawuce falon yay shiru.



Gyaran murya Mahaifin Muhsin yayi yace "To bari mufara da kalamai mafi kyawu wato da Sunan Allah Mai Rahama Maikuma Jinkai, Alhaji kaganmu agidanka da dare haka kuma unannounced ko, bawani yakawomu nan ba sai wanan yaron" yanuna Muhsin dake gefenshi da kanshi ke kasa, sanan yakara sauke ijiyan zuciya yace "wlh Alhaji idan nace namasan ta yanda zanmaka bayanin nan kafahimta tonamaka karya amman bari nafara da tantance gaskiyan lamarin kafin nakoro bayani" yay dan shiru kafin yanisa yakalli Abba kaman yanda shima yake kallonsu yace "Alhaji wai dan Allah kanada y'a mai sunan Du'a ne? Danni wayanda muka sani shine wanan Baban dan naka wato Hamad, Aisha, Hawwa, Amal, Aneela, Asiya da Muhammad da Mudasir, dan Allah katabbatar min da gaskiyan lamarin nan kanada y'a mai sunan Du'a ne wacce duk bamusanta ba"? Shiru Abba yayi yana kallonsu kaman bazaice komiba danhar dagakai Hamad yayi yana kallonshi sanan yadan nisa yace "eh inada y'a mai sunan Du'a" ahankali Baban Muhsin yace "to Alhamdulillah, nasan banida wanan hurumin dazan tambayeka maisa baka taba ambato mana itaba ko wani abuba dan nasan kanada dalilinka nayin hakan, daman tabbatarwan kawai ita nake bukata tunda yanzu ka tabbatarmana kanada y'a mai sunan Du'a toga dalilin da yakawomu wurin ka da daddaren nan" ya sakeyin shiru sanan ya numfasa yace "shi so hallitan ubangiji ne, danhaka so gaskiya ce hakama ki, Alhaji d'ana yazo gidanka jiya sai cikin iko irin na Ubangiji yaci karoda yarka Du'a kuma Allah ya jarabceshi da sonta ainun aranshi danyau haukace mana kawai ne baiyiba ga kannina nan katambayesu kaji, yace shiyabarma Nana duka abubuwan dayamata amman yafasa aurenta dan baya sonta Allah yahadashi da Du'a ita yakeso itakuma yakeson Ya aura inhar ka yarda zaka bamu" tunda suke maganan Abba yake kallonsu babu ko kyafta ido, yakai kusan minti biyar ahaka baice komiba dakin tsit kakeji sanan yay gyaran murya yace "to Alhamdulillah naji dadi yanda kukazo kukasamen, shi gaskiya dayace koda batada dadin ji, naji dadin yanda kuka sanardani gaskiya batare da kwana kwana ba ko kuma boyeboye ba danhaka nima zan sanardaku gaskiya Alhaji" yay maganan cikin mugun hikima da ilimi sanan yace "it's very okay idan danku Muhsin yaji bayason y'ata bazai aureta ba shi aure daman yagaji haka ko anyi ana rabuwa, amman gaskiya itace bazan iya bama Muhsin wacce yaji yakeso dinba wato Du'a" dasauri Muhsin yadago kanshi yakalli Abba idanunshi sunyi jaaa sosai.



Abba yacigaba. "Alhaji kai mahaifine haka nima mahaifine, yanzu wani yazo yana tareda yarka har a kusa bikinsu sai yaga kanwarta yace yafasa aurenta kanwar yakeso zaka yarda kabashi"? Abba yamai tambayan shiru Baban Muhsin yayi yakasa amsa tambayan, Abba yace "duk wani abinda zai raba kan y'ay'ana ko family na bazan taba yinshiba, gwara afasa auren gabadaya da inbaka wata, dan haka I am sorry idan maganata ko amsata bata kuma dadi ba amman bazan iya baku auren Du'a ba, as for kayayyakin dakuka kawo duka in sha Allah zamu aiko muku dashi, Allah yasa hakan ne yafi alkhairi"


Kafinma Baban Muhsin yayi magana Muhsin ya rarrafa da gudu zuwa gaban Abba, kneeling yayi yahade hannayenshi biyu muryanshi narawa kaman wanda zai fasheda kuka yace "Abba Abba wlh wlh wlh na rantse da Allah bawai dan cin mutunci ko toxarci kodan inci zarafin Nana nai hakaba, wlh kawai Abba azuciyata naji bana sonta wlh tunda nasa Du'a a idanuna nake so ko kulkewa nayi saina ganta, Abba kataimakamin dan Girman Ubangiji" tunda yake maganan daga Abba har Hamad kallonshi sukeji, ahankali Abba yasa hannayenshi yakama hannun Muhsin dayake rokonsu dashi yace "Son kayakuri kotayaya zaka roken I don't think I can risk my family for this, I can't stand naga kan family na ya rabu sabida one bad decision dazanyi ba, bazan iya baka Du'a ba, it's final" to Abba biggest suprise kawai yaga Muhsin yafashe da kuka sosai, daura kanshi yayi kan cinyan Abba cikin kuka yace "Abba wlh idan baka bani Du'a ba zan iya mutuwa dan Allah kayakuri, I am sorry if I hurt you sabida nace banson Nana...."



Iyayenshi kasa koda motsi sukayi, sunsan Abba made the right decision dankosu basuso sunzo ba mugun so da gatan dasukema Muhsin dinne yasa sukazo su gwada luck dinsu.


Ganin yanda Muhsin ke kuka yasa zuciyan Babanshi yafara breaking shifa baida wanda yakeso kaman Muhsin aduniyan nan, kallon Abba yayi yace "Alhaji name anything dakakeso wlh zan maka indai zaka bama dana Du'a dinan dayakeso, kaga wlh zan iyasa acireka daga matsayin HOD dinan abaka Deen na BUK gabaki daya, idan bakaso zan baka aiki akasan waje, wanan gidan na chanza maka nabaka lafiyayyen gida anan GRA kano, mota kudi koma mekakeso just name it zan baka inda zaka hakura kabama yarona wacce yakeso kaganshi nan shikadai gareni kataimakamin please" sake tashi Muhsin yayi daga jikin Abba fuskarnan nashi hawaye ya wankeshi yahade hannayenshi yana kallon Abba, dan murmushin manya Abba yayi yace "I am happy da position da dukiyan da Allah yamin a rayuwa bana bukatan kari, nariga nayi maganata idan babu matsala zan haura sama inada y'a mara lafiya naduba, Hamad you can see them off okay" gyadamai kai Hamad yayi Abba yatashi, sosai Muhsin yafashe da kuka, kanin Baban Muhsin Alhaji Mubarak yatashi yay wajen Muhsin yace "Kato dakai kana kuka, ga matanan agari kaman ledan pure water kodaga kasan waje kakeso kayi aure Babanka

Please Login or Register in order to submit comment