Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sama nazo nayi waya, koma bansan yazo ba gidan nan ba Bakin Sharif bane har sama zai iya zuwa wajena, Sharif zo dan Allah kadubamin kafarta kotasami targade ne, kosu Razika basu kadai ba duk wanda zaizo gidan nan hanashi gudu nake akan bene dan hatsari ne da bene yanzu jibi", karasowa wajen Sharif yayi dawani irin sauri takai hannunta ta share hawayen daya bata fuskanta, Hajiya data matsa gefe tace "au uban kukan dayagamaji kinayi dan yazo nanne zaki wani goge hawaye" turo baki tayi ta dauke kai, Hajiya tace "kaji Sharif dubamin kafan kagani" ahankali yakai yatsunshi biyu yadaura kan kafar datai ja sabida turgudewan yanabin dogayen feet dinta da kallo yace "does it hurt" yadan dagakai yana kallon fuskanta, hadiye zafin tayi tagirgiza mai kai alamun a'a hakan yasa Hajiya tace "kafan dakika gamawa kuka ne kike cewa baya zafi"? Murmushi yadanyi yace "buguwace kawai tashafa man zafi zai daina mata zafi" yay maganan yana sauka kasa abinshi, hararanta Hajiya tayi tace "wuce kije kishafa robb akai Allah kika karamin gudu agidan nan saina saba miki Du'a, kidena guje guje kinji" gyadamata kai tayi ashagwabe tace "tom" "wuce kitafi dakin ki, wani aiki Sharif ketayani yi" gyadamata kai tayi tawuce ta tafi tana tafiya ahankali Hajiya tabita da kallo saida taga tabude daki tashiga sanan tasauko tace "Allah kyauta" karasowa tayi tazauna kusada Sharif tace "wai shi gogan bazaizo yagaidani bane" dariya Sharif yayi yana abinda yakeyi yace "finally kinyi admitting kinyi kewan Asad" hannu tadaga kaman zata dakeshi ya kyalkyace da dariya yace "wlh aiki sosai ne aikin nan dayakeyi shi kanshi yagaji kinsan Asad ya tsani takura shida yasaba saidai yatakurama mutane shi baiso atakuramai Allah Allah yake gobe tayi yagama, da sassafe fa yake fita kullum" murmushi Hajiya tayi tace "Allah sarki Asad, kana ganinshi haka akwai kwazo da zuciya" murmushi Sharif yayi yace "nidai idan yazo kicemai wlh yafito da mata yay aure inba hakaba dudda ina kanninshi aure abuna ni zanyi na barshi" yay maganan yana batarai, wani irin baki Hajiya tasaki tana kallonshi tace "ohhh jama'a yauni naga takaina, kaiwai mara kunyan inane Sharif, yoo dan kaniyan kama duka duka da wata nawa ya girmeka wata uku ne fa tsakaninku haka Amminku tagayamini, Asad nada wata uku aduniya aka haifoka" dan dariya Sharif yayi yaturo baki cikeda rashin kunya yace "nidai gaskiya nafadi muku aiko Ammi nagayamata ni wlh aure nakeso kuma shi Asad banga alamun ya shirya aure ba Hajiya wlh yaron nan kaman aljani shi yama tsani mata, basa gabanshi the only matan dayakema murmushi yayi hira yay wasa dasu aduka fadin duniyan nan guda biyu ne daga ke sai Ammi, kinsan ko Anty Turai kanwar Abban mu bayama murmushi cewa ma yake he hates her, to ina zan tsaya jiran irin wanan saiyay aure zanyi ai namutu tuzuru hakanan Hajiya wlh a'a" wanan karan hannu Hajiya takai ta dakamai duka abaya dayasa yakusan sakin laptop din yace "aashhh" dauke laptop din tayi tace " naga alama kwana biyu ban jibgeka ba saisa bakada kunya, mugama aikin dakakemin Allah sa ba shirme kakeba dan naga hankalinka baikai" tai maganan tana saka glasses a idanunta tana kanne idanu danta karanta report din daya rubuta mata, karban system din yayi yace "ni dai tsaya na karanta miki natafi gida nai waya da budurwa ta kuma saina gayamata kece duk kika cinye mata time" dariya tayi tace "kagaya mata hala tamadan soka sabida yanda ba'acin kudinka at least ni Kakar ka ina moreka" dariya yayi sosai sanan ya shiga karantamata.....
wa.me/+2347012181461



💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫



✍️ M SHAKUR

Free Page
EPISODE 2️⃣4️⃣
yauma kaman kullum suka tashi suna breakfast malamin su yazo ta tafi wajen nata su Razika ma haka, as usual by 1 yatafi, daki takoma ta kunna TV tunani kala kala aranta, wanan sanarwan nan na iya tasake saurara rasa abinda zatayi yasa tabude kofa tafice daga dakin, dakin Hajiya tabude tashiga dake meeting a zoom na retired lawyers, ita kebada report din ga glasses akan idanunta, kallon Du'a dake kallonta tayi hakan yasa Du'a tashigo wani book dake kusada ita tadauka rubutu tamata sanan tabata kallon rubutun Hajiya tayi ta gyadamata kai tareda daukan purse dinta ta zaro 10k tabata, karba tayi cikeda jin dadi tafito daga dakin sanan tasauko kasa da sauri tana murna tai wajen Razika dake dakinsu tace "Grandma tace kirakani saloon jeki shirya nima bari na shirya" gyadamai kai Razika tayi tace "kinbar wayan ki a dinning tun jiya" murmushi tayi tace "zan dauka nasan Su Aneesa ne bari naje na shirya" sama tayi, shiryawa tayi cikin wani black abaya mai kyan gaske, sanan tazauna tai rolling veils dinta dayay kyau shima ta feffesa turare tafito rikeda handbag, a falo tasami Razika tace "yauwa kin shirya muje to" gyadamata kai Razika tayi suka fice, driver Hajiya ya kwashe su zuwa wani saloon daba na ranan nan ba dantace dagaske bazata wanan ba, tsife mata kalaban akayi sanan aka wanke mata kan sai murmushi take ta kosa agama, gamawa akayi aka mata blowing hair din yabushe tass sanan matan tace "Hajiya wani style za'a miki" dasauri Razika tace "asake mata kalba amman yan kanana kanana this time" dasauri Du'a tace "a'a ayi manya manya" dasauri Razika tace "please amiki kanana Du'a ai tanada sauri" dagakai Du'a tayi takalli matan tace "idan kikai kanana zaki gama kafin 4" kasa magana da kyau matan tayi sabida idanun da Du'a ta zubamata yarinya kaman ita tai kanta. "eh bakice komiba zaki gamamin kafin 4" kasa magana matan tayi sai kawai gyadamata kai datayi murmushi sosai Razika tayi tace "kingani na gayamiki za'a gama, afara to amata mai kyau mai style" fara mata kalaban matan tayi tana mamakin yawan gashin Du'a dakeda tsayi, tsayin shikecin lokaci ma ba asalin kitson ba, wajajen 3 Du'a takalli uban tulin gashinta da ba'ayi ba tace "3 yayi sai yanzu mukai rabi" kallon fuskanta matan tayi ganin Du'a tayi kaman zatai kuka yasa dasauri tace "yakuri gashinki nada tsayi sosai ne gashi robber hair, I am going as fast as I can, zan gama dawuri" gyadamata kai kawai Du'a tayi matan tacigaba da kitson da saurinta, tanaji tana gani 4 yayi ana kan kalaban ba'a gama gamaba sosai taji hawaye yazo mata amman ta daure tahana kanta wuraren 5 matan tagama, tashi tayi tsaye da sauri tana parking kitson da ribbon dinta tadau gyalen ta ta tafa wanan karan batama tsaya rolling ba duka kudin da Hajiya tabata tabama matar sanan takalli Razika tace "muje" tashi Razika tayi suka fito tace "wai ina kike sauri zakije ba gida zamuba" girgixa mata kai tayi suka shiga mota, tace "dan Allah transcorp hotel zaka kaimu" sanan tajuya takalli Razika tace "program liyafa akeyi na matasa kan fara sana'a tun karfe hudu aka fara" gyadamata kai kawai Razika tayi dan batasan wani program bane ba akeyi ba but yanda taga Du'a tasan it must be something very important to her.



Tunda suka shiga hotel din gabanta ke faduwa sosai parking yayi hakan yasa suka bude suka fito suna kallon kofan dazai sadasu to asalin cikin hotel din da wani security guard dake sanye da uniform ke tsaye yana kallonsu, kallon Du'a dataga ta tsaya sakakau Razika tayi yanda take kalle kalle tace "a ina akeyin abun" dan zaro idanu Du'a tayi irin na asalin wanda doesn't have any idea akan abu tayi tace "nima bansani ba" ganin haka yasa Razika tadan matso kusada ita murya chan ciki tace "to ki tambayi wanan security daman gashinan yanata kallonki" dan zaro idanu tayi saikuma tajuya takalli mutumin dake kallonsu har lokacin kafin Du'a tai magana yace "are you here for the program"? Gyadamai kai Du'a tayi batare datai magana ba, yace "to ku shiga hall din ma 8th floor" gyadamai kai tasakeyi sanan tawuce tafara tafiya tana kama hannun Razika suka shiga ciki tare, tunda taji 8th floor yasa tasan akwai elevator hakan yasa sukai hanyar stairs suka farabin bene, da sauri sauri gudu gudu take hawa stairs din, sosai sukai nisa dafa bango Razika tayi tana nishi sosai tace "wayyo Allah na kafana, Du'a nagaji wlh" kaman zata fashe da kuka tace "nima wlh nagaji kinga ankusan gamawa dan Allah muje" tashi Razika tayi tana nishi suka cigaba dabin stairs din ita karan kanta Du'a daurewa tayi kaman kaman kafafunta zasu tsinke, ahaka suka kai floor din tundaga tsayin corridor wajen sukaga mutane sunyi layi hadaddun yammata da maza anyi layi har zuwa hall din da cikin hall din da ake asalin abun, ganin anbisu da kallo yasa Du'a tabi Razika da kallo saikuma takoma tabayan Razika tana sussunar dakai kaman mara gaskiya dan wani iri takeji idan ana kallonta, murya chan kasa kaman mai whispering tace "Razika tambaya mana inane hall din me akeyi anan" dan Jim Razika tayi saikuma ta kalli wata mata dake tsaye alayi tana sanye da hijabi tace "dan Allah inane hall din" hall din dake gabansu matan ta nuna mata tace "ga hall dinan" ahankali Razika cikeda tausasa murya sabida karta gaji da ita tace "angama ne me kukeyi alayi dayawa haka"? File din dake hannunta matan ta nunama Razika tace "anriga angama liyafan, layin nan kuma na masu son irin su email dinshi ne sanan muna using opportunity din muna submitting CV dinmu akwai possibility na zaiyi recruitment koma baiyiba tunda gwamnati sunsan da zamanshi zaya iya sama mana aiki kingane, long layi ne about 100 people naciki duk sunata bashi kuma ya karba" gyadamata kai Razika tayi tace " nagode sosai, sanan tadan matsa baya still Du'a na labe abayanta tace "kinji ko, ina zamu iya jiran this plenty mutane dasunkai 200, Hajiya tasan kinzo nan" girgixa mata kai tayi alamun a'a, hakan yasa Razika tace "to gaskiya ki wuce mutane tunda anriga angama bazamu kafin akawo kanmu goman dare tayi" gyadamata kai Du'a tayi asanyaye Razika tace "muje" juyawa tayi ahankali suka fara tafiya saikuma ta tsaya Razika takalleta tace "menene?" ahankali tace "I want to say thank u" bata jira amsan Razika ba tawuce wajen da saurinta tai gaban hall din tana sussunnar dakai batai wata wataba kawai ta danna kanta ta kutsa tacikin mutanen dake layi tashiga hall din, tana shiga yan waje sukahau ihu chaaa barinma matan wasu suka biyota ciki ganin haka yasa tawani irin kwasa da gudu dan hall din nada makeken girma sunachan kan stage, dagudu itama Razika tashigo tana kwala mata kira. "Du'a, Du'a, Du'a ina zaki".....


Chak ya tsayar da rubutun dayake ma wata a littafin data bashi, yau yana sanye cikin wani gray suit dayafi na kullum mai kyau, yana zaune yadaura kafa daya kan daya agaban wani hadadden table, both sides dinshi bodyguards ne tsaye rike da gun, sai wasu manyan mutane dake kan stage din suma a zazzaune da suit, tsayar da rubutun chak yayi batare daya dago kanshi ba jin ana ihu da hayaniya a hall din amman suna daya kunnenshi ya iya karba Du'a!


Dawani irin gudu Du'a takaraso gaban hall din daidai inda mutum zai fara hawa yan kirgaggun stairs din dazai sadaka to stage din wanda anan line din yafara duk wanda yazo kanshi xaihau stage ne yaje yasauko, wani irin tsayawa Du'a tayi tana nishi sama sama kaman kirjinta zai fashe sabida gudun datayi tana kallonshi ganin yes yes tabbas shine, daidai lokacin matan dasuka biyota suka karaso cikeda fada sukace. "ke waye dazaki baromu alayi ki gudo ki shigo ciki" juyawa tayi tasake kallonshi cikin muryanta mai shegen zagin nan da dadi dake rawa kuma sabida tsabagen tsoro dakuma gudun datayi tana kallonshi still tace "thank u" duk binta akai da kallo ganin yanda take kallonshi tacemai thank you, wani mutum dakebinta da kallo ne dakekan stage din yace "Pretty lady ki koma kibi layi idan akazo kanki then you now tell him thank u, as it is so many people sun cemai thank you yours is not first kinga he is busy" yanuna mata Asad dayama cigaba da attending to mutane kaman ma baisan something is going on ba, gyadama mutumin kaitayi hawaye na neman zubomata amman ta daure tana kallonshi ahankali tace "thank you for saving my life" daya daga cikin matayen dasuka biyota ne tawani finciketa tace "dalla malama kizo kifita" dasauri Razika takama hannun matan tace "kisaketa dalla kema ai tafiya zamuyi, muje Du'a" kasa daga kafa daga wajen Du'a tayi tana tsaye kaman an dasata tana kallonshi, muryanta wanan karan narawa sosai hawaye yacika idanunta sosai tace "thank you for saving my life" fincikanta matan tasakeyi hakan yasa Razika tace "malama dalla kisaketa, Du'a let's go" kin motsi Du'a tayi kaman ba ita akeja ba, nan hall din yadau hayaniya, ahankali ya sallami guy din dake gabanshi sanan yajuyo da kanshi ahankali yadaura fararen idanunshi akan na Du'a da akeja taki tafiya tana kallonshi, faduwa gabanta yayi yanda yanda ya kalleta, wani irin yatsine fuska yayi sanan yadauke kanshi daga kanta yajuya yakalli security dake gefen damanshi batare daya kalleta ba yana jiran next person dake kan line yanuna Du'a da yatsanshi a wulakanci yace "fitarmin da yarinyar nan daga hall dinan please and throw her outside this premises".

wanna talk to me no problem just click on this link wa.me/+2347012181461


💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫



Chat me up directly by clicking on this link wa.me/+2347012181461
✍️ M SHAKUR

Free page
EPISODE 2️⃣5️⃣
Ko karasa maganan baiyiba katon bodyguard dinshi yataho hakan yasa Razika tawani ja hannun Du'a da duka karfinta, fashewa da kuka sosai Du'a tayi Guard din nabinsu Razika najanta da sauri tana kuka mutanen wajen namata dariya suka fita daga wajen sukai hanyar staircase suka farabi, sai alokacin bodyguard din ya tsaya ata gaban stairs din yace "idan kuka dawo cikin wajen nan saina bindigeku" dasauri Razika kejanta suna sauka sai alokacin tasan ashe kafafunta sun gaji, sosai take kuka Razika tace "waike bakida wayaune Du'a saikace wata karaman yarinya, jibi yanda kikasa akai embarrassing namu" da kyar ta iya karasa sauka daga stairs din kaman kafafunta zasu cire daga cinyanta suka fito waje, wani Alhaji ne suka gani tsaye awajen yana gyara zaman malum malum dinshi yana kallonsu, hannu Du'a tasa tai wiping hawayen dake kan fuskanta tass, wani irin murmushi mutumin yasakin mata yace "common pretty girls basa kuka, daina kuka" dasauri Razika tacigaba da janta da sauri dan magrib yayi, da dan gudinshi ko kunyan mutanen dake wuce su baiyiba yasha gabansu yakalli Razika yace "I guess ke kawarta ce ko dan Allah sakin mata hannu kibani minti daya nai magana da ita" yakalli Du'a data dauke kai yace "Pretty dance mata tasakin mata hannu" cigaba da tafita sukayi yana binsu har sukakai mota, bude motan Razika tayi Du'a tafara sawa aciki sanan tashiga itama taja kofa mutumin na bubbuga kofa takalli driver Hajiya tace "muje wanan mutumin na binmu" kunna motar yayi yaja shikuma mutumin yadaga hannunshi sama kaman mai kiran mutane saiga wata hadaddiyar jeep yazo baya yabude yashiga yace "mubi wanchan motan Auwallu amman ahankali zamubi motan sabida karsu sani suboye inaso nasan mahaifin yarinyar nan" yana biyedasu har suka shigo estate dinsu, nesa dasu yasa aka kashe motan ya gyara zama yana kallonsu, gate aka bude musu suka shiga ciki sanan aka maida gate din aka rufe, dasauri yace "tada motan kaga Auwallu" tasa motar driver shi yayi zuwa gidan da Du'a ta shiga, parking yayi akofar gidan sanan yabude bayan motan yafito yana gyara zaman malum malum yana leken gefen gate din kaman wanda yasami matsalan tabin hankali, ahankali yakai hannunshi zaiyi knocking gate din aka bude gate din aka fito, Sharif ne yafito daure da alwala dan masallaci zaije sallan isha'i, tsayawa yayi yabi mutumin da kallo, dasauri mutumin ya shiga leka gidan kaman zaiga Du'a ta gefen Sharif, ganin haka yasa Sharif yarufo gate din ahankali yace "lpy" wani irin murmushi Alhaji yayi tareda shafa kanshi saikuma yace "wai mugaisa wlh duk na rude ne naga abinda raina ke matukar so" yamikama Sharif hannu, kin bashi hannu Sharif yayi yana kallonshi still yace "lpy maikazo nema? Kokuma nace wakake nema?" sake sosa meya Alhajin yayi yace "wlh naje ba wata yarinya yar fara haka nabiyo naga tashiga gidan nan, inataso namata magana tun achan amman dayan datake tareda ita taja hannunta tahanata magana dani wlh, dan Allah ko zan iya ganinta kokuma zaka hadani da mahaifinku dan naga kaman kai yayanta ne naganka fari kaman ita dudda tafika fari da kyau" yay maganan yana lashe baki yace "Allah yayi mace awurin nan wlh" wani irin daure fuska Sharif yayi ganin tsohon banza ne, hakan yasa yace "sunana Sharif, kuma yarinyar dakake magana matata ce, ka kama girmanka ka tattara inaka inaka kabarmin kofar gida kafin nahadaka da hukuma" wani irin kwalalo idanu yayi saikuma yadaura hannu akan saman bakinshi yace "assha ai bansan matarka bace, bansan matan aure bace wlh nagayamaka bata kulani ba inda ace takulani tagayamin tanada aure daban biyota ba wlh, amin afuwa nabarka lafiya" yajuya yashiga mota dasauri sukabar wajen wani irin tsaki Sharif yaja yabi motan da kallo yace "tsohon banza kawai" saida yaga su fita daga estate din sanan yawuce yatafi masallaci.



Sharif na tsakar gida yana alwala yaga shigowansu itada Razika tana goge fuskanta da gyalen abayan dake kanta idanunta sunyi ja sosai, bama su luradashi ba suka wuce ciki, falo suka shiga kallo daya Hajiya dake zaune akan kujera tana magana awaya tamata tagano wani abu dasauri tacire wayan daga kunnenta tace "zan kiraki Hajara" katse wayan tayi takalli Du'a da Razikan da duk suke atsaye sun kasa karasowa gani suke kaman tana ganinsu zata gane abinda yafaru, yunkurowa tayi tana kallonta still tace "why did you cry Du'a? Maiya sameki?" Dan zaro ido tayi this is the first time datasan tama Grandma dinta laifi sosai, Grandma data taimaketa tabata freedom shine daga fara fita ta hartaje hotel ita maiyama kaita taje, duk ta tsaya tana tunanin nan zuciyanta fall da tsoro batare databama Grandma dinta amsaba, juyakai Grandma tayi takalli Razika tace "maiya sameta take kuka"? Baki Razika tabude zatai maganan da sauri ta tattaro duka karfinta ta tari numfashin Razika ahankali tace "Grandma hannun matan zafi sosai kuma gashi tadade kaina ke ciwo" sosai Grandma ke kallonta, ga idanun nan nata sundan kumbura alamun tasha kukan tace "to dan kanki na ciwon kitso sai kiyita kuka banace kidena all this abubuwan ba keba yarinya bace"? Gyadama Grandma kai tayi hawaye nasake taruwa a idanunta tace "sorry" ganin tana neman sake kuka yasa taidan murmushi dan she looks damn cute tace "zonaga kitson" tahowa tayi ahankali gabanta nafaduwa sosai ko kadan bataso tama Grandma dinta karya ba, zama tayi gefenta, Grandma tabude kan tana kallon kalaban dayay bala'in kyau tace "wow daman abu mai kyau yafi bada wahala, kinga yanda yay kyau kuwa, wow oya jekiyi salla kiyi wanka kizo nabaki abinci da paracetamol kisha" gyadamata kai tayi ta tashi ahankali sama, Grandma takalli Razika dake tsaye itama tace "sannu kinji Razika, Du'a dukta wahalar dake, jeki daki kiyi salla kihuta" ahankali tace "to" tawuce, tashi tayi itama dayake hijabinta nakusada ita dan tariga tai salla yasa ta tashi ta shimfida dadduma danyin salla.


Takwas daidai yabaro uban mutanen dake kan layi yafito dan yagaji iya gajiya, juyawa yayi yakalli security dake biyedashi abaya yamika musu hannu yace "car keys, u can go" daya daga cikinsu ne yadauko key daga aljihunshi yamikamai yace "Sir daka bari mun maidaka gida is not safe for you to be driving alone" dan yatsine fuska yayi yace "it's okay" juyawa yayi yakunna mad ride dinshi yabude kofa yashiga sanan yatada motar, tafiya mai tsawo yayi sanan yakai gaban wani eatry, shiga ciki yayi sanan yay parking inda ake parking ya kashe motar, wayanshi yadauka ya daddanna sanan ya ijiye wayan kan cinyanshi ya jinginar da fuskanshi jikin kujera tareda lumshe ido yana fuzarda iska, Asad wani irin mutumne da idan zaka kwana kana kallonshi bazaka taba tantance wani yanayi yake ciki ba sai idan kai mai lurane.
Knocking motarshi da akayi yasa yabude idanunshi ahankali yadago kanshi, wata doguwan fara mace ce tsaye gaban kofan tana sanye dawani arnen half gown daya tsaya daidai gwuiwanta sanan an tsaga tagaban da kadan yarage ba'a ganin pant dinta, kanta sanyeda attachment daya zubo har waist dinta taci uban makeup a fuska dayamata kyau ba laifi ga hill akafanta mai tsinin gaske, yarinyan dan kyau Allah yayi kyau ga hips ga boobs duka, danna lock din motar yayi kofan yabude hakan yasa tabude kofan ta shigo ta zauna tareda maida kofan tarufe sanan tajuyo takalli Asad din dake kallonta bayabo ba fallasa murmushi tamai tadan juya idanu tana chewing gum dinta tace "why call me wajen gari haka, wajen garin ma this local place, you are so lucky ma danazo" shiru yayi yana kallonta ta duhun harta gama tana wani yatsine yatsine, jin shiru yasa takunna flash din iPhone 11 pro max dinta tadaga ta haska fuskanshi tana kallonshi kaman yanda ko gezau baiyiba kallonta yake tace "woooww, bansan cewa mahaifinka nada kyakkyawan thick sexy boy hakaba, so you are the famous Asad da mahaifinka always talks about, only son, his father's pride, wowwww" cikin thick voice dinshi yace "would you mind turning that off" wani irin lumshe ido tayi kafin ahankali tasauke wayan ta kashe flash din tasan Alhaji yana yawan bata labarin Asad dinshi but bata taba sanin babban Matashi saurayi haka bane mai jini ajika ba gashi kyakkyawa yafi baban shi kyau sosai, ahankali tace "why did u call me here" shiru yamata yakai kusan 3min sanan yace "inaso kirabu da mahaifina ne!" dawani irin sauri takalleshi saikuma tanuna kanta tace "ni Zinariya kake cema narabu da mahaifinka? Sugar Dady nawa? Anya kasan girman abinda kake fadi kuwa, dakakirani cemin kayi we will talk business zakamin proposing offer da I can't resist saisa nazo, is this the offer"? Dauke kai yayi daga kallonta yajuya yana kallon waje yace "sunanki Zainab Garba Habu from kano, anguwan uku layin Murtala hamisu house number 3, mahaifinki yarasu, mahaifiyarki nada rai ita ke kulamiki da yaronki mara uba kekuma kina nan Abuja kina karuwanci dan kisami kudi kidinga turamusu....." yanda yake maganan komai waye sai wani kalan natsuwa yashigeka, batare daya kalleta ba yace "kaman yanda nagayamiki awaya I have an offer for you bana karya is true I have that offer, inaso kirabu da mahaifina is exchange ma 10million naira, gida akowani kasa kikeso acikin kasashen waje da visa da passport miki da mahaifiyarki da kannenki dakuma danki inkin yarda" tunda yake maganan jikinta ke tsuma amman tadaure tahana kanta tanuna tadai daure takalleshi tace "sabida 10million ne zan rabuda Alhaji shikemin komi, yabani kudi naturama yan uwana akan me zan rabudashi sabida yan chicken change dinan naka da balallai ne kabani ba" hannunshi yamika yadauko wani envelope daga kujeran baya yadawo dashi gabanta yabude yazaro takardan ciki yamika mata karba tayi ahankali tana kunna hasken wayanta tana dubawa maida kanshi yayi kan hanya yace "I am sure u can read, wanan agreement ne da lawyer na yarubuta nariga nayi signing inhar kin yarda zaki rabu da mahaifina kibarshi har abada without having any form of contact dashi aboye to komi dana fadamiki nakine sanan inda daga baya kikazo kika saba alkawari to inada right na na kulle ki agidan yari but all this saikin yarda ne zaki iya signing" duka abinda yafadi haka yake arubuce awajen, Alhaji nabata kudi but baitaba bata kudin dayafi 500k ba, yana bata kudi 50k 60k tasaima gidansu abinci, yasata awani gidanshi kullum ya ijiyeta cinta kawai yake amman yaki aurenta kotamai maganan aure saiya cemata shi bayida ra'ayin kara aure amman komi yamata, ga motanshi daya daya ijiye mata dudda bai bataba amman tana hawa, yanzu ga kudi malala har 10mil da rayuwa kasan waje manta manta, ubanme Alhajin ke tsinana mata banda uban jaraba yacita kusan sai shidda arana duka baya wuce 1min, sai bakin jaraba bakarfi kaman ammai baki anya bazata karbi wanan offer ba.




Anjiyan zuciya tasauke dashi kanshi saida

Please Login or Register in order to submit comment