Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kirki ba karya mata fada, maida kofan tayi ahankali tarufe tace "thank you Uncle" dan haka take kiranshi sanan tajuya tafara tafiya zuwa entrance sanan tashiga ciki, Sharif tagani tsaye gaban kantan reception yana sanye cikin cooperate kaya ba suit ba amman wando da riga yay tucking ga belt dayasa mai kyau yana duba Rolex din dake daure a wrist dinshi kaman akwai abinda yake jira, kaman yaji ajikinshi kallonshi ake yasa yadago kanshi yakalli entrance hada idanu sukayi ajiyan zuciya yasauki sanan yasakin mata wani irin cute smile yana dumfaro ta, saida yakai gabanta ya tsaya ahankali yace "you look ahhhhh mema zance"? Yay dan shiru yana kallon sama yadaura yatsanshi daya kan kumatunshi kaman mai tunani saikuma yakalleta ganin yanda take kallonshi irin ta kosa taji mezaice dinan yasa cikeda tsokana da wasa yace "you look like indon kauye" gabaki dayan murmushin datakeyi bacewa yayi tai raurau da idanu kaman zata fashemai da kuka hakan yasa yay dan dariya yace "just teasing you" saikuma ya tsareta da idanunshi da for the first time tunda tasanshi suke shiri sosai tana kallonshi kaman yayanta taji wani iri hakan yasa tadauke kanta, murya chan kasa yace "you look damn cute Du'a kaman in saceki in gudu" murmushi tadanyi kanta akasa dan tasanshi da wasa still tana wasada yatsunta, for a moment yamanta inda suke tsaye all yake gani wasa her tsaye agabanshi, ahankali yadan waiga yabi wajen da kallo sanan yajuyo yakalleta yace "I've been calling you baki dauka maisa" dago kanta tayi takalleshi ita bamatasan tayaya yasami number taba, saikuma tanunamai wayannata dake hannunta tace "anan ka kirani"? Wayan ya kalla yace "yes, I gave u about 3 to 4 calls I think" wayan tajujjuya takalla dan ko kadan bataji ringing ba ahankali tace "banji ringing ba" hannunshi yamika mata yace "let's see maybe kintaba wani waje ne" bashi wayan tayi yakarba yabude ganin ba key saikuma ya kalleta yace "bari zan miki setting nashi anjima wayan nason update, yanzu dai our Boss yazo he's in his office, maisa kikai latti, our Boss is such a wired dude fa" yay maganan kaman mai whispering din gulma da hakan ma yasa tai murmushi, tsayawa yayi yana kallonta yace "instead of kifara tsoro kinyi latti murmushi kike ko zaiyi deducting a salary ki sanan yau saikin biya bashi time din dakikaci by adding extra hours kan lokacin tashinki, oya let's get going" yay maganan yana tafiya tana biyedashi abaya yace "zai miki tambaya, so yanzu idan kinje as normal yanda any boss zaiyi he will ask u few questions ma sababbin staff nashi, yadan miki tambaya karkiji tsoro be very bold and answer him kinji" gyadamaikai tayi suna hawa stairs, yace "and idan yace maisa kikai latti me zakice? Uhmmm kuma banaso nakoya miki karya"? yay maganan yana tunani yadaura yatsanshi akai yana tafiya, dasauri tana kallonshi itama tana tafiya tace "zance mai nakone akafa" kwalalo idanu yayi ya tsaya yana kallonta, gyadamai kai tayi kaman wata yar yarinya tace "wlh dazu nadebo ruwan tea shine yazube akafana yay zafi sosai saisa nai latti" tunda take maganan yake kallonta saida tagama ahankali calmly yace "kinyi kuka"? Gyadamai kai tayi da zuciya daya tana raurau da idanu tana tafiya, chak yatsaya heart dinshi nawani irin racing he feels kaman yajawota ya rungumeta ya lallasheta, jin shiru yasa tawaigo ganinshi abayanta yasa tadan zaro ido tace "menene, ka manta dawani abu ne" dan murmushi yayi yataho da saurinshi yace "no, how's the leg now? Yadena zafi?" gyadamai kai tayi tace " yadena" daidai nan sukakai 5th floor, tsayawa yayi daganan yace "our Boss is a bit harsh but don't get scared okay" gyadamai kai tayi tanadan zaro manyan idanunta, dan yatsine fuska yayi yace "naaaay! I don't like that face, now smile and go you got this" 👍 yamata thumbs up da hannu dayasa tai murmushi sanan tawuce tafara tafiya mutanen dake wajen sai kallonta suke, gaban office dinshi da aka rubuta CEO taje ta tsaya, ga secretary dinshi awajen zaune gaban table tana aiki, ganin ta tsaya yasa tace "you can go in Mrs Du'a" gyadamata kai tayi batare datai magana ba sanan ahankali tadaura hannunta kan handle na kofan harwani kalan sanyi takeji sanan gently tabude kofan kanta akasa, wani irin kamshi da sanyi ne suka wani daki fuskanta dayasa tadan lumshe ido kadan sanan tabude idon kafin ahankali tasa kafanta tashigo sanan tamaida kofan tarufe ta jingina da kofan kanta akasa still hannunta duka biyun kan hannun handbag dinta data kankame gam gam tanajin wani irin sanyi tundaga kafanta har tsakiyan kanta dan sanyin office din yabaci kaman ankure AC gabaki, takai kusan 1min tsaye awurin tana kankame da igiyan handbag dinta kaman her whole life depend on it sanan ta daure still kanta akasa kaman wata munafuka tashigo har zuwa gaban hadadden table din office din ta tsaya gaban kujeran guest tana kara kankame hannun jakan tama rasa takamaimen mezatace a office din mai kamfanin nan, tunawa da maganan Sharif na kartaji tsoron yasa tahadiye tsoron ahankali tabude bakinta cikin muryanta data kara wani irin kankancewa sabida yanda ke faduwa tace "good morning Sir" takai kusan 30sec dagaidashi jin shiru yasa gently kaman wacce idanunta ke shirin fitowa sabida tsabagen rawan dasukeyi tadago kanta takalli kujeran zaman mai office, ido hudu sukayi da Asad dake zaune yana yasanya wani hadadden Italian suit white da blue, wanda keda wani monkey jacket da farin riga ke kasanshi, babu jacket ajikinshi ya rataya kan maratayan da ake ijiyewa a office dan hanging kaya monkey jacket da farin riganne kawai ajikinshi yana zaune kan kujeranshi hannunshi rikeda wasu papers dayake reviewing ga coffee agabanshi yana sipping, sai dayan hannunshi rikeda byro ko kallonta baiyiba, wani irin rawa jikinta yafara ganin Asad mutumin daya cirota daga rijiya a kano, mutumin data gani a TV, mutumin datagani a hotel hall, same mutumin da dazun nan taganshi agidansu shine kuma still take gani anan shine mai kampanin nan, the CEO boss dinta to kodai aljani ne, jitayi cikinta yawani irin murda kawai taji wani fitsari yataso mata yacika mata mara yana shirin zubowa duka acikin yan sakannin data dago kanta ta kalleshi, daurewa tayi ta harde kafafunta gam but still jikinta rawa yake takara kankame jikinta, saida yagama reviewing document din hannunshi yay signing tsaf sanan ya yunkuro ya ijiye papers din kan table sanan ya gyara zama da kyau ahankali yadago kanshi yazuba mata mayun idanunshi akanta, dawani irin sauri tadauke kanta tana kallon gefe tana kara harde kafanta sabida wani irin fitsari datakeji dake neman fin karfinta, cikin muryan nan nashi dababu alamun wasa cikinshi yace "kinyi latti awa daya da minti biyar da sakan lalatin, bayan kinzo aiki latti kika tsaya kina chatting da wani ma'aikaci anan did you know the gravity of laifin nan"? gizgiza mai kai tayi still kanta na kallon gefe, tsawa yadaka mata yace "nobody answers me with motion speak up" wanan karan batasan lokacin data saki hannayenta dake kan jakaba takai tadaura Ata wajajen abdomen dinta dan tana neman sakin fitsarin sosai, lips dinta narawa sosai tace "I am sorry sir......." yana kallonta still yace "well your salary will tell u if I accept the sorry or not, have a sit" gyadamai kai tayi saikuma da sauri tace "okay" kafin ahankali tasa hannunta taja kujeran gaban table din tazauna jikinta na bari.

Anatse yace "look up and introduce yourself" yay maganan bayabo ba fallasa as usual, gently tadago idanunta tadaura akanshi kaman yanda shima yake kallonta, kasa jure kalan idanun dayake dashi tayi hakan yasa tana kallonshi ne amman tadan karkata kwayan idanunta gefe sanan ahankali tace "My name is Du'a, I am 21yrs old, an haifeni a kano, Babana nada mata biyu awajen Mama na I am the first child, nayi school from nursery zuwa JSS 2 a makarantan Royal, that's were I stopped a school".


💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫



✍️ M SHAKUR

Free page
EPISODE 3️⃣0️⃣

Tai maganan tanadan moving da jikinta sabida yanda cinyanta ke rawa tanajin fitsari, jin shiru yasa kaman wata barauniya tadawo da idanunta back saitinshi hada idanu sukayi yana kallonta har lokacin wanan karan kasa rike fitsarin tayi batasan lokacin datawani zabura tamike kaman mahaukaciya ba tana yarfe hannunta dayan hannun kuma takai wajen abdomen dinta tadan kalleshi tana rawa rawa tace "I.....wan......pee...." bamata karasa maganan ba jin fitsarin yazo tasa tawani saki handbag dinta datake rikedashi kan table dinshi kayan ciki duka suka zubo kan table dinshi sanan tawani kwasa a guje tai kofan kofanshi tabude tafice dagudu.....

Wani mugun tsaki yasaki yanabin table din nashi da kallo da kayan cikin jakanta dasuka zubo, the first thing da idanunshi suka sauka akai was pad, dauke kanshi yayi yay tsaki, yana kokarin dauka wayanshi aka bude kofan aka shigo itane kanta akasa, maida kofan tayi ahankali tarufe sanan takaraso har gaban table din, ganin yanda kayan jakanta suka fito kan table din yasa tadan kalleshi ganin yana daddanna wayan yasa takwashe dasauri tazuba a jakan sanan tadaga jakan tarike kaman wacce zatai sata ta lallaba tazauna akan table din.

Ijye wayan dayake tabawa yayi tadau wani file yabude batare daya kalleta ba yace "I learned that HR dept basu karbi any of your detailed ba ID Card na this company kawai MD yasa amiki" gyadamai kai tayi kanta akasa tace "yes sir" still yana duba rubuce ruvuce yace "can I have ur personal ID Card?" dan dagokai tayi takalleshi hada ido suka sakeyi dasauri ta girgizamai kai tace "uhm bandashi" danjim kafin cikin wanan muryan nashi yace "voters card or national identity card dinki that's what I mean" sake dago idanunta tayi takalleshi ganin yana kallonta still yasa tadauke kai murya chan kasa kaman wacce ke tsoro tace "bandasu" cikeda haushi yace "what nonsense! Are you even a Nigerian citizen"? Yay maganan da fushi cikeda kuma fada, doguwan riganta takama tarike gam tawajajen cinya batasan maisa ba fada ko magana da ita da fushi sosai yana tuna mata da memory na gidansu, kuka ne taji yazo mata tadaure da kyar tace "ba....ba'a barina fita agidane saisa bandasu" tai karashe maganan tanakai bayan hannunta kan idanunta tana danne hawayen dake shirin zubomata tanajan hanci, Yatsine fuska yayi kaman irin dan dole yake mata magana dinan yace "give me ur account details we need to attache it to your file for ur salary pension, Sigma pension zasuzo subude miki pension account dinki, now ur bank details" dan dago kanta tayi takalleshi idanunta sunyi ja, hada ido sukayi dan har lokacin kallonta yake murya chan kasa tace "I don't have an account" goshhhh! yawani irin buga table din dayake kai dasaida tama firgita, cikeda bacin rai yace "what kind of a girl Ammi tasa nakawo into my company eh? How can I hire a person who doesn't have any identity card dazai nuna she's a Nigerian and a citizen, please get out of my office, and don't come back to this company saikin bude account sanan kinsami ID card, understood?" Gyadamai kai tayi ahankali hawaye yacika mata idanu fall, yatsine fuska yayi yace "now get out of here" ahankali ta tashi jikinta har bari yake irin na wanda ke shirin yin kukan nan, dawani irin sauri sauri tafita daga office din nashi tai stairs dasauri sauri take sauka kasa kanta akasa ta daure iya daurewa karta bari tai kuka tana kaiwa kasa tai hanyar fita, receptionist dinsu nabinta da kallo cikeda mamaki dan tasan kullum wanan yarinyar da duk suke kirada Matar MD Sharif ta shigo bata sake fita sia lokacin tashi.


Tana fita tai hanyar parking space, sai alokacin tafashe da kuka sosai ganin babu motar direban Grandma yasa ta tuna lokacin tashi baiyiba, ga wayanta bayama hannunta yana hannun Sharif dawani irin gudu tafita tana kuka sosai tana share fuskarta da bayan hannunta, bakin titi ta tsaya tana kalle kalle.




Idanunta sunyi jajir takasa daina kuka, taxi dayazo wucewa ta tare dan bataga keke napep ba kaman yanda lokacin nan kafin asa tadaina fita take gani akan titinsu, tsayawa yayi ba bahaushe bane yakalleta tsayarda hawayen tayi tashiga sanan tarufe yace "madam ba drop u want" gyadamai kai tayi tace "eh" sosai take kuka cikin keken kawai memory gidansu dakomi yake dawomata da yanda yawani korata kaman yana koran kare, jin yanda take kuka yasa mai taxi yakalleta ta cikin mirror yace "hope all is well o Madam, u no tell me where I go carry you go" murya chan kasa cikin kuka sosai dan daura hannayenta tayi akan fuskanta tana kukan tace "estate" dasauri yace "which estate" kasa amsashi tayi sabida kuka hakan yasa yace "eh which estate" ko kadan batasan sunan estate dinsu ba bama hakaba ita bamatasan ko estate din nada suna ba dan bata taba luraba ahankali tace "just go if we get there I will show you" gyadamai kai mai taxi yayi daba bahaushe ba yacigaba da sharara gudu tana kuka hardaga baya ta lallashi kanta tai shiru tajuya tana kallon hanya ganin bataga estate dinsu ba, sunyi tafiya fin awa biyu suna zagaye zagaye yana tambayanta duk wani estate dazasu gani a hanya konasu ne tace a'a, gajiya yayi yay parking akan wani titi cikin fushi yace "abeg give me my money and leave my car u donno where u dey go" girgizamai kai tayi cikin muryanta data dishashe tace "I know is estate, idan akabi titi ake kaiwa" tsayawa yayi baki bude yana kallonta ta glass din motar ganin kaman ma yarinyar batada hankali dan inba hakaba tayaya babban mace haka zata wani cemai idan akabi titi ne za'azo estate dinsu batasan ina zata bane, harzuka yayi yace "just give me my money find another taxi, the little petrol wey remain make i manage am go home" kalan titi dasuke tayi dababu ma mutane sosai babu motoci sosai dan irin titin sabuwar hanya dinan ne yasa cikeda tsoro tace "but this is not my estate, I don't know anybody here" cikeda nakan magana yace "me I no, see Madam gimme my money comot for my car" ganin yana magana kaman zai daketa yasa tashiga bude jakanta, she's not even sure kotanada kudi, kudaden dake cikin jakan taciro hakan yasa yace "my money na 5000, na drop u carry we almost round Abuja finish" gyadamai kai tayi tashiga kirga kudin jakan duka duka 4900 nema, ahankali tamikamai ganin baida mutunci tace "is 4900 sorry" fizgan kudin yayi yace "witch even if na send they send u my papa spirit still dey protect me, comot for my car" yay maganan yana wani irin bude kofa yafita yabude baya yana kallonta yace "I said comot for my car" fitowa tayi ahankali tana gyara rikon jakanta maida kofan yayi yarufe sanan yakoma gaba yazauna yarufe kofan lekowa tayi ta window yace "I pass ur power tell them u no fit do me anything witch" yay maganan yanajan mota shi duk kallon mayya yakema Du'a sabida yanda takeda bala'in kyau gashi tagama zagaye Abuja dashi zarginshi shine zatakaishi ashamai jini ne.


Hawaye tagoge daga fuskanta da sauri bayau aka saba kiranta da mayya ba, ahankali takalli gabas, kudu yamma da arewa tana tunani inane hanyan zuwa gidansu, gashi babu wasu mutane a hanya sosai, hakan yasa ta yanke shawaran bin hanyar da mai motan yabi da kafa, dan batada ragowan kudi kuma koma tanada shi bataga taxi ko keke napep dazata tare anan ba ga cikinta dayake ciwo dan bataci abinci ba gakuma MP datakeyi datakejin alamun na yakamata ta chanza pad dan kaman yajike.


💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫


✍️ M SHAKUR

LAST FREE PAGE
EPISODE 3️⃣1️⃣

Sosai take tafiya Instead of taga tana shigowa cikin mutane amman saitaga kaman tana kara komawa inda ba mutane ne, one one motoci ke gittawa, tun wuraren 1 da direban nan yasauketa itace har uku saura tafiya take kafanta yay budu budu sabida a bayanta dakejan kasa ga shegen kishin dayakeji ga yunwa ga gajiya, tsayawa tayi abakin titi duk motan dazaizo yawuce take tarewa amman basa tsayawa hakan yasa takoma gefen titi dan daji da bishiyoyin dake wajen tasamu ahankali tazauna akan wani dan dutse dake wajen tana maida ijiyan zuciya tanajin wani shegen kishi tana kalle kalle bataga komiba, daura jakanta tayi akan kafafunta kafin ahankali tadaura kanta akan jakan kawai tafashe dakuka ahaka akife kafin daga bisani wani wahalallen bacci yay awon gaba da ita awajen.




Wuraren 1 as usual Sharif yazo floor dinsu rikeda wayanta daya saita mata komi, knocking office dinta yayi tareda budewa duka at the same time, ganin babu kowa a office din babu jakanta yasa yadanyi kwafa yace "yauma ta tafi masallacin bata jirani ba ko" jan kofan yayi yamaida yarufe yafito daidai Asad yadawo shima daga mosque din yana tafiya ahankali yana gyara zaman necktie dinshi yana kallon Sharif din, tsayawa kusadashi Sharif yayi cikeda tsokana yace "how far kamana order pizzan" hararan Sharif din yayi yace " order with ur money" yay maganan yana wucewa office abinshi shikuma Sharif yahau dariya yawuce elevator yashiga zuwa kasa masallaci yashiga yay alwala yay salla sanan yafito yana kallon wajen ganin babu ita yasa yawuce Canteen dinsu, ganin babu ita awajen ma yasa yay fushi kawai baima tsaya cin abincin ba yawuce floor dinsu yace "nizata share yau duk tai abubuwan ta ita kadai" wayanta ya kalla dake hannunshi yace "she will come get it by her self" ijiye wayan yayi agefe kan table dinshi yacigaba da aikinshi...... Wuraren 3 yakasa hakuri rabon daya ganta tun safe tashi yayi yafito yay sama, office dinta yasake budewa ganin bata ciki yasa yafito yabi ma'aikatan wajen da kallo wucewa yayi yakarasa wajen receptionist din gaban office din Asad yace "have u seen Miss Du'a Patience"? Cikeda girmamawa tace "yes sir naga saukanta" juyawa yayi da sauri yashiga elevator yasauka kasa, shi yasan bata yawo iya kanta masallaci sai Canteen kuma duk tare suke zuwa toko tana restroom din mata ne, hanyar bayi yayi ya tsaya gaban macen security dake wajen yace "dan dubamin miss Du'a aciki" tashi matan tayi tac3 yes sir tashiga taduba tafito tace "babu kowa a rest room sir" shiru yayi yana tunani dan this is strange, daga kai yayi yana kalle kalle ganin receptionist din wajen yasa yakarasa yace "have u seen Miss Du'a"? Gyadamai kai tayi tace "yes Sir dazu naga tazo tawuce tafita tana kaman ma kuka take" dan tsayawa yayi yana kallonta saikuma chan yace "around what time kenan"? Dan shiru tayi kaman tana tunani tace "around eleven na safe" juyawa yayi dasauri cikin fushi yace "Assssadd! What have u done this time" elevator yahsiga zuwa 5th floor, direct office din Asad yashiga dake magana dawani employee dinsu daya kawonai report, kallon employee Sharif yayi yace "excuse us Mr Bashir" "sure sir" yafadi yana tashi yafita sauda yarufo kofan sanan Sharif yakalli Asad babu alamun wasa kaman bashiba yace "ina Du'a Asad? Inaka turata" dan yatsine fuska Asad yayi yana jawo MacBook dinshi zuwa gabanshi yace "wace Du'a"? Cikin fushi Sharif yace "you know what am talking about, yarinyar dakai saving daga rijiya, jikan Hajiya, yarinyar da Ammi tasa kabata aiki, ina take"? Typing abu yashigayi a system dinshi abinci cikin halin I don't care yace "batada any means of identity sanan batada account so I asked her to leave my company duk randa tasamesu she can come back" cikin wani irin bala'in mamaki Sharif yace "you ask her to mene?" yay shiru yana kallon Asad dake harkan gabanshi, cikin wani irin bacin rai yace "Asad kakosan mekayi? Did you know that yarinyar nan batasan ko'ina ba a Abuja ko good 3weeks batayi a Abujan nan ba, tayaya zata koma gida? Look her phone is with me" yanuna wayanta dake hannunshi, dan tabe baki Asad yayi yana aikin dayakeyi a system yace "she's an adult she can take herself home" yanda yake maganan ma yafi komi cima Sharif rai irin ko ajikinshi dinan baimasan yayi wani abuba, cikin mugun fushi dabazai iya tuna the last time dayay irinshi ba yace "wlh katashi kanemo yarinyar nan ina gayama" wanan karan ko kalloma Sharif bai isheshi ba saima hannunshi dayakai yana taba screen din system din yana magana ahankali yace "there's an error in this FIFO calculation......" irin baimasan Sharif nayiba, sosai ran Sharif yabaci wayanshi yaciro ya danna ma Ammi kira yadaura a kunne ringing biyu Ammi tadaga kafinma tai magana yace "Ammi kina ina yanzu haka" cikeda rashin fahimtan abinda Sharif keyi tace "ganinan gidan Hajiya, takirani gwuiwanta naciwo shine na shigo" ahankali yace "Ammi Du'a na gidan" dasauri tace "Du'a kuma, Du'a dake office basai 4 kuke tashi ba, wai yau bakaje office bane" wani irin lumshe ido yayi yabude kirjinshi na bugawa yace "Ammi listen to me zangaya miki wani magana amman banson kice komi dan kar Hajiya tagane dan abinda kunya ace mune mukama jikanta haka" nan yakorama Ammi magana daga A to Z, tsabagen tashin hankali batasan lokacin data fito tsakar gida ba, cikin bala'in bacinrai tace "ina Asad din"? cikin bacinrai Sharif yace "yana zaune anan Ammi ko ajikinshi baimasan yayi abu" cikin fushi sosai tace "bashi wayan" cikin bacin rai yace "ni wlh bazan bashi wayataba saidai ki kirashi ta wayanshi bari naje naduba Nabi hanya kozan ganta" yay maganan yana katse wayan yawuce yafice daga office din straight waje yayi yashiga motanshi yabi hanya.


Wayan Ammi tabida kallo tunda take bata tabajin Sharif yayi fushi hakaba duk cikin yaran shi kadaine baida matsala gashida ban dariya, dialing number Asad tayi, yana zaune ganin Ammi na kiranshi yasa yature system din dake gabanshi yana kallon wayan harta katse bai daukaba, akaro nabiyu ne yamika hannunshi kaman mai tsoron wayan yadauka yakara a kunne baice komiba, cikin fushi sosai Ammi tace "aida itama wanan kiran baka dauka ba goga kaji" taidan shiru hakan yasa ahankali yace "Ammi I just told her to go idan tai national ID da bank saita da......""shut up Asad!" Ammi tadakamai mugun tsawan dashi zai iyacewaka tunda yake arayuwanshi Ammi bata tabamai tsawa hakaba, tace "Asad this is not how I train u wlh billahil azim, Asad where is your heart, Asad how can u asked that girl ta tafi gida yarinyar dabatasan ko'ina ba, kasan yarinyar nan kuwa? Kasan wacece ita? Eh? kasan mesa aka kawota wajen kakanta kasan labarin Du'a kuwa? Do you know what that girl has been through? Asad is this how I trained you? Duk duniyan nan banda Maman data wuce Hajiya Asad you know this morethan anyone matan nan babu abinda batamin ba aduniyan nan, Asad jikan ta zaka wulakanta eh?" jin yanda ran Ammin shi yabaci sai maganganu take awaya yasa yaji duk badadi, ahankali yace "Ammi" cikin fushi tace "don't you dare call me Asad, idan wani abu yasami yarinyar nan tayaya zankalli Hajiya nagayamata d'ane sila eh? Mezata cema iyayen yarinyar nan kasan case din dake kan yarinyar nan kuwa, Asad why are u like this? Maisa baka da imani bakada tausayin mata eh? kanada kannai mata idan wani yakorasu haka kaibamai zuwa kayi fada dashi bane, Asad listen to me if anything should happen to that girl wlh wlh bazan yafemaka ba dan bazan taba iya kara kallon idanun Hajiya ba..." dawani irin sauri yace "Ammi!" cikin fushi tace "yes Asad nasan kalman dana gayamaka, katashi duk inda yarinyar nan tashiga aduniya ka nemota kadawo da ita gida nan dakanka safe and sound inba hakaba wlh saina mugun sabamaka Asad dabazaka gane kaina ba mai bakin hali kawai" Ammi ta katse wayanta cikeda bacin rai tana kallon agogo dan tasan hudu nayi direban Hajiya zaitafi daukota.

TOH GGM DINA🥰🥰🥰 ANAN NAKAWO KARSHEN FREE PAGES THIS LABARI NADA TSAYI YANZU NAMA FARA.
SUBSCRIPTION IS 500 PAY INTO 3107021073 AISHA MUHAMMAD FIRST BANK.

KUJI TSORON ALLAH KUBIYA KADA KU KARANTA BATARE DAKUN BIYABA DAN GASKIYA ALLAH ZAI SAKAMIN.

THANK YOU ❤


Assalamu Alaykum, inaso mu gina al'umma masu tsoron Allah da tsoron hakkin dan uwanshi musulmi, I was very kind and generous nayi pages talatin da daya (31) pages awanan littafin as free, dan Allah kudubi

Please Login or Register in order to submit comment