Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da motar tayi
fakin a kofar gidan" shekaran jiya wanda ke zaune a gidan ya tashi"
wani yaron mu ne da ya sami karayar arziki ya
dawo daga birni" mai suna Abashe ba wata
matsala kuyi zamanku tun da dai sana'a ta kawo ku"
Alabashi idan an sami abinda aka zo nema daga baya sai ku canza wani wajen wanda yafi wannan sukuni"
Rufa'i yayiwa mutumin godiya" nan da nan ya
taimakesu suka fara shiga da kayan cikin gida"
ba wasu kaya bane dama na azo a gani ba katifa ce da sauran kayan tarkacen kwanonin abinci dana aiki"
Bayan direban ya tafi tare da mutumin da ya
nuna musu hanyar gidan" sai rufa'i da Raliya
matarshi suka fara shiga da kayansu cikin dakin"
Sai a lokacin suka lura da rufin dakin inda silin ya kusa ruguzowa mai tsautsayi kawai yake jira" Rufa'i ya tsaya ya kalli silin yace da Raliya dake a bakin kofa" "Kai!! Raliya wannan dakin zai zaunu kuwa" dubi silin din yadda ya kusa ruftowa anya bazamu canza gida ba"
Raliya dake rike da hannun dan su idrisu tace da mijin nata"
"Ba komai Rufa'i mu zauna hakan nan Allah zai
kare mu" kada ka manta akan abin nema muka
fito" ko ina muka tsuguna yayi tunda ba'a garin
mu" muke ba"
Rufa'i ya daga kai ya kalli silin din yace
"Bazamu zauna a dakin nan ba sai mun gyara
silin din nan" bari in dauko turmi a waje in hau in gani ko zan iya gyara wa" Raliya tace dashi
"Baka rabuwa da jawo aiki Rufa'i don Allah kada ka taba musu daki iya gani iya kyalewa"
Rufa'i ya wuce ta" ya fita waje cikin sauri yana
cewa" masu gidan ne zasu kwana ciki ko kuwa mu!" idan dakin ya kashemu wa gari ya waya bamu ba?
Ya kinkimo wani tsohon turmi da suka gani a
tsakar gidan" Raliya ta shige cikin dakin ta bashi hanya ya shigo ya ajiye turmin a tsakar dakin ya kifa bayan shi ya fara kokarin hawa"
Raliya ta kalli tozon silin din tace
"Gaskiya wannan wauta ne Rufa'i ina jin tsoron
ka taba silin din nan" ya haye saman turmin yace da ita
"idan bazaki iya tsayawa ba ki fita waje ki jirani in gama raliya tayi dariya tace dashi............RALIYA-28
.
Ya Haye saman turmin yace da ita" "Idan bazaki iya tsaywa ba ki fita waje ki jirani in gama"
tayi dariya tace dashi"
"Ina fa zan iya fita in barka banga halin da kake
ciki ba Rufa'i sai dai in fita da Idrisu" ko dakin ya tusashemu mun kasa fitowa" mun bar wa 'yan baya wanda zasu gani su rika tunawa damu"
Raliya ta janye danta suka fita waje da yake bai
san abin da ake cki ba" sai ya fara korafin da ya
dameta dashi" tun da safe tun suna gida"
Mama ina keken da kika ce zaki sai mun yau?
Raliya tace "Ai fa yau na shiga uku da wannan keke" to zauna anjima ka tuna mun zan sai maka ta zaunar dashi a jikin bangon ta koma ciki da sauri" A lokacin har Rufa'i ya fara tura rubabben silin din" don ya koma" Raliya ta tsaya tana kallon shi yana akan turmi dogo" zuwa can sai yace da ita cikin mamaki"
Raliya ina jin akwai wani abu a cikin rufin dakin
nan" na danna silin naji kamar da wani abu mai
nauyi kamar dutse Raliya tace
"Dutsen lafiya" Rufa'i me zai kawo dutse cikin
silif ? Zuwa can Rufa'i yana danna silin din don yakoma ya hadu da dan uwanshi" cire hannunshi keda wuya sai abinda yake ciki ya dawo da karfi ya fasa ragowar kwalin da katakon dake rike dashi Shekara da shekaru " ya ruguzowa rufa'i akai" sannan ya fadi kasa tas!!
Kamar an kayar da katanga" Raliya tayi baya ta
fasa kururuwa ta dafe kanta" a lokacin ne kuma
bayan ta ruguzowa Rufa'i wanda yake kokarin
barin turmin a tsorace" Rufa'i ya tsallako bangaren da Raliya take a rude
sai da kura ta lafa" sannan suka ga abinda ya
fado wani katon akwati ne" duk yanar gizo ya
lullube shi" da kuma majinar bango"
Akwatin ya fashe daga gefe" kuma murfin har ya karye" a dalilin dadewa da kuma buguwar da yayi a halin yanzun da ya sulmiyo tun daga koli"
Tsawon mintu daya ma'auratan biyu suna kallon akwatin a tsorace" kamar wadanda suke kallon maciji" Rufa'i ne yayi karfin hali yakai hannu don dauke murfin akwatin wanda ya murgude" Shima baiyi haka ba" sai da ya karanta ayatul kursiyu har sau uku a jere"
Rufa'i ya daga murfin Akwatin cikin zullumi nan
take sababbin Dalolin Amurka sukayi mishi lale
marhabin"
Rufa'i ya saki murfin akwatin ya dawo da baya
cikin mamaki" Raliya ta fashe da kuka" sannan
tayi salati" ta ce Rufa'i mafarki nake yi ko gaskiya ne?" Don Allah mafarki nake yi Rufa'i ?
yayi saurin dafata don kada ta sume a tsaye yace da ita"
"ki kwantar da hankalinki Raliya ba mafarki kike
yi ba.. Ki tattara hankalinki guri guda kada ki
Zautu"
Raliya tace dashi a rude
"Rufa'i wannan wanne irin abu ne?" wannan
shine fa akwatin kudin da nake tsammanin ya
jefamu a cikin hadari tun zamanin da ina
makaranta" kafin muyi aure kasancewar nayi
misayar akwati da wani barawo a mota" Rufa'i shine wannan akwatin" na shiga uku Rufa'i ya
Zamu yi?
Raliya ta sake fashewa da kuka a tsorace"
"ba komai ki daina kuka Raliya" ya isa hakan
nan
Ya lallasheta sai zufa ke ta faman wanke mashi
fuska" kamar ya ci karo da mataccen da ya
dawo" Rufa'i yace da ita cikin nutsuwa"
Kadan kenan daga cikin kudurar Ubangiji" Raliya wannan wata ishara ce da ya kamata ta zama darasi a gare mu da duk wani wanda zai sami wannan labari" domin kuwa akan wannan akwati an zalunce mu an so a raba mu da ran mu" Allah kadai yasan iya shekarun da yayi a wajen" kuma Allah kadai yasan iya adadin mutanen da suka zauna a dakin nan tare da wannan akwati" to amma da yake ba rabon su ba ne" kinga bai fado ba sai yanzu da wani sanadi ya kawo mu wannan gari"
.
Raliya ta share hawayenta tace da mijinta"
"Gaskiya ni ba na son wadannan kudin" zama
lafiya a duniya yafi zama da irin wadannan kudi
Rufa'i sai a lokacin ya saki ranshi ya kalli kudin yace wannan kudi naki ne Raliya tun farko dama naki ne" wasu mutan ne masu hadama suka kwace miki" amma gashi Allah ya dawo maki da abinki"
don haka ni a ganina kowa muka kaiwa
wadannan kudi to wata rana sai sun sake
dawowa wurinki" tun da dai naki ne ba na wani
bane" Raliya tayi karfin halin dukawa ta durkusa gaban akwatin tayi ajiyar zuciya"
"Rufa'i mu dauki kudin nan mu kaiwa 'yan sanda sunyi mana yawa" me zamuyi da irin wadannan kudi a duniya?
Mijin nata ya durkusa kusa da ita" shima ya kalli tulin kudin tari guda cike a cikin akwatin yace "basu yi mana yawa ba matata" yanzun
gwamnan kasar ta mu akwai mutum daya daya
mallaki dubun wannan kudin" kuma har yanzu
wasu yake nema kari basu ishe shi ba" saboda
haka bazamu kaiwa 'yan sanda ba" mu zamu rike su sun zama namu"
Raliya taji ajiyar zuciya bata sake cewa komai
ba" taci gaba da kallon kudin tana tuno wahalar
da tasha a rayuwarta tun zamanin da tana
makaranta tare da kawarta "Suri har zuwa
wannan zamanin da take zaune da fakirin mijinta Rufa'i
Suna nan a haka sai dan su Idrisu ya fado cikin
dakin yana shagwaba ya cewa Raliya"
"mama ina keken da kika ce zaki sayo min?
Rufa'i ya mika hannu ya kamo dan shi yana
murmushi" yace dashi" "kada
ka damu idrissu ba keke kawai za'a sayama ba har mota ma za'a sayama.

ALHAMDULILLAH.
Godiya nake gareku kusantuwar bisa goyon bayanku wanga littafi yazo ƙarshe.
.
NI
SADEEQ SHEHU SHARIFF
( JARMAN TASKA )Nake Cewa
ALLAH YABAR ZUMUNCI
- sai kuma mun sake haɗuwa a wani littafin.
.
THE END
.
KARSHE
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment