Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

karfi" reshikan
bishiyoyin dake makarantar suka rausaya a lokaci
guda" sannan ganyaye suka farfado kasa"
Suri ta lumshe idanunta cikin jin dadi" a lokacin
da iskar ta doki fuskarta tare da watso mata
kwayoyin ruwan dake makale a sararin samaniya
wadanda tun lokacin da ana ruwan Allah bai basu
ikon fadiwa tare da 'yan uwansu ba"
Suri tayi murmushi data tuno abinda ta tabbatar
yana can yana faruwa a wani wuri" a daidai
wannan lokaci" tun lokacin da Jarmai ya
gwangwadawa Suri labarin wannan dukiya da
xai sato daga wurin kawunshi ta fara
tunanin abinda xatayi da dukiyar" domin kuwa
tasan cewar indai sunxo to sun xama nata har
abada"
ta riga ta gama shirya duk yadda xatayi ta
yaudari masoyinta Jarmai ta kwace dukiyar ta
gudu da ita cikin uwa duniya"
Daga nan ba wanda zai sake jin duriyar inda
take" sai dai in ana labarinta idan ta fara gina
kampanoni" tasan cewar mutane da dama xasu
tsananta binciken yadda akayi ta xama biloniya
tun tana budurwa ko karatu bata gama ba" tace
a xuciyarta" Idan na sami kudin dole ne ayi
shakkar tabani" suri ta sake murmushi"
Dole ne suri ta riga girmama kudi da dala a
duniya
Domin kuwa taci bakar wahala a rayuwarta
kamar 'yar mahauniya" tun lokacin da aka yaye
ta a hannun wata azababbiyar kakarta ta girma"
wacce kullum idan xa.ayi lissafin gaskiya bana
dokin rano ba" to sai ta lakada mata shegen
duka sau bakwai ko sau tara a rana"
kuma ba wani laifi ma take yi ba" laifin dai kenan
idan ta dora mata talla bata sayar ba" kuma a
kullum kakar suri takan dora tukwanen shinkafa
gudu uku manya-manya kamar mai saida kan
awaki" Haka suri ta rika daukar su a bangaji daya bayan daya" duk sai sun kare"
Idan dare yayi aka xo kan lissafin ribar da aka ci"
kullum kafin suri ta kwanta barci sai kakarta ta
nemi lafiyayyen itace tayi mata dukan ala-tashemu lafiya" domin kuwa a ka"ida indai akayi lissafi ba.a ci ribar jaka uku ba" to suri ta banu ta lalace"
.
SAI lokacin da ta samu ta gama sakandire ta
shiga jami'a sannan ne Allah ya raba suri da
masifar wannan kaka tata" domin kuwa tun
lokacin da ta kawo karpi suka fara sa"insa da
tsohuwar"
Watarana suri ta koma gida hutu daga jami'a tayi
xanxaro da jaket mai ruwan kasa" wadanda
samarinta na jami'a 'yan duniya suke saya mata"
xaman ta keda wuya" ko ruwa bata sha ba" sai
kakarta ta nufi murhu ta fara neman itatuwa tana cewa"
"Ai naji dadi da wannan hutu da kuka samu suri"
dama duk na kosa ki dawo wallahi" haka nan
nake xaune ba cas ba as" tun da kin dawo da
wuri yanxu bari in dora maki shinkipa ko tiya
hudu ne" tunda rana tayi" ala bashi gobe sai mu
tashii da shiri" mu girka shinkafa tiya takwas
wake tiya uku"
SURI tayi banxa da tsohuwar tana ta kicin kicin
ragar shinkafa" bayan taci aikinta ta gama
shinkapa ta nuna cike da tukunya" sai kakar suri
ta leka daki" ta sameta tana duba alban din
hotunan da suka yi ita da kawayenta da kuma
samarinta a jami'a" kakarta ta daka mata tsawa
tace"
"ke nake jira ga shinkapar can xan kwashe" so
nake kiyi hanxari shinkafar tayi rana in kinje can saiki ci taki"
SURI tayi murmushi sannan tacewa tsohuwar"
"kaka ai wannan xamanin kuma ya wuce" yanxu
ni 'yar jami'a ce ba 'yar sakandire ba ce!"
Tsohuwar ta matso kusa da ita ta rike kugu tace"
"suri ubanki nace" ko bakya jina" nace ubanki!!"
wato har kin fara koyo fitsara daga xuwanki
jami'ar ?" to bara in fada maki" wallahi tallahi ko
ferfesa kika xama a gidan nan sai kin daukar min
tallata" xaki tashi kije ki nada gammo ko saina ci ubanki?"
Suri ta sake yin murmushi sannan taci gaba da
bude alban din hotunanta" bata ko daga kai ta
kalli tsohuwar ba" kakar tace"
"Au! To nasan abinda kike so" kin rabi da samu
ne shiyasa" tayi sauri ta fita waje ta nufi inda
take ajiye itacen konawa" ta xabo wani mukeken
faskare tana ta sumbatu tana ce"
"Ina amfanin abaka rikon maraya" tun kina
jaririya da iyayenki suka yanke jiki suka fadi"
shegiya nina daukoki ina ta wahala dake" wato
yanxu kin girma kin shiga jami.a" shine xaki yi
min ixkanci" to baki isa ba yarinya"
Tsohuwar ta fada cikin dakin rike da faskarenta"
suri ta mike a fusace ta rike itacen a lokacin da
tsohuwar take shirin kawo mata duka tace"
"Gaskiya fa kaka wallahi baxan yarda kullum kice
xaki rika dukana kamar kin sami jaka ba" yaya
kawai na girma zaki rika takura wa rayuwata"
yakamata ki rika wayewa" ki gane cewar da fa"
ba yanxu bane"
Tsohuwar ta xaro idanu cikin mamaki tace"
"Ni ai banyi ilmi ba" bansan komai ba sai talla da
duka" kuma tunda kince min kin girma kin wuce
duka da talla" to mu xuba ni dake shege ka fasa"
dan halak sai yanka"
Tsohuwar ta kama jikarta da kokawa kici-kici" da
yake irin mutanen da ne" tasha sauyoyi da jike-
jike tana nan garas da karfinta" ta dauki suri ta
buga da kasa" ta shake mata wuya da kumbunan
hannunta"
Da suri taga tshohuwar xatayi mata lahani" saita
xame jikinta" sannan ta tashi ta ruga a guje ta
nufi kofar gida"
tsohuwar tabi ta a guje cikin tsautsayi sai taci
tuntube da tukunyar miya a kafafuwa ta fadi ta
sake wuntsilawa" kakar suri ta fara kururuwa
mutane suka shigo suka kawo mata dauki" bayan
an duba tane aka ga ta karye guri biyu a kafarta" ta dama sannan ta goce a hannunta na hagu"
Tun daga wannan rana ta xama gurguwa" kuma
tun daga nan suri ta sami sauki" dole sai dai ita
ke dawainiya da ita" shiyasa suri take bin samari
'yan duniya suna kashe mata makudan kudi" rabi
tayi hidimar karatunta" rabi kuma ta aikawa
kakarta gurguwa wacce ke xuwa yawon bara da sanda"
.
A halin yanxu da suri take tsaye a saman benen
cikin duhu" tana shakar daddadar iska mai cike
da kamshin damina" kuma mai sanyaya xuciya"
saida ta tuno da axababbiyar kakarta dake acan
gida tana yawon bara" daga gobe kakarta ta
daina xuwa bara" suri tace a xuciyarta tana
murmushi a bayyane" domin kuwa gobe ne xan
xama miloniya" daga ni har dangina mun gama
shan wahala a rayuwarmu ta duniya" Allah yasa
Jarmai yayi nasara yaxo mana da kudin"
.
Suri ta bar jikin karpen benen cikin fara.a ta
nufi
dakinsu ita da Raliya" da kuma wata iyamura mai suna MARY
Da xuwa ta sami Raliya xaune gaban kyandir din
dake a jikin teburin karatun su" ta bude
wargajejen akwatinta mai taya baki" tana ta
kimtsa kayanta a ciki wasu ma basu bushe ba"
haka nan take ta faman cusasu" suri ta matsa
kusa da ita" ta dafa kafadar Raliya tace-;
"Allah sarki kawata" shike nan xaki tafi ki barni"
Raliya tayi murmushi" sannan ta dubeta"
"Kada kidamu suri" tace da ita" sannan ta dauko
wata rigar mama ta jepa a cikin akwatin kayanta"
wata rana ai xamu sake haduwa" in dai bake ce
kika jepar dani ba"
Suri tace
"Baxan taba jepar dake ba Raliya" duk da yake
xan xama miloniya baxan mance dake ba" da
karpe nawa xaki tafi goben?"
Sammako xanyi tun da sassafe" Raliya tace da
suri" sannan ta koma kan littatafanta dake xube
akan katifarta" suri ta dafa kawarta sannan tace da ita cikin murmushi...
.
.
LOADING PAGE 04RALIYA-04
.
"SAMMAKO xanyi tunda sassafe" Raliya tace da suri. Sannan ta koma kan littatafanta dake xube
akan katifarta" suri ta dafa kawarta sannan tace
da ita cikin murmushi"
"zuwa lokacin kudina sunxo" in da rabonki kema
xan dan yaga maki ko dubu dari ne" kawata ko
kuwa me kika gani?"
Raliya tayi tsaki" sannan ta debo littatafan ta
xuba a akwatinta"
.
=======>*******<========
LOKACIN da abokan Elbashir suka shiga cikin
falon ne" suka same shi a tsaye!!
"ku nake ta xaman jira" tun daxun. Na dauka
cewar baxa ku sami xuwa bane"
Daya daga cikin bakin uku ya hade fuska yace"
"Haba Alhaji me xai hanamu xuwa kuwa?"
maganar kudi ba maganar wasa bace" yi sauri ka fito mana dasu kowa ya dauki kasonshi"
Elbashir ya dubi fuskokinsu yaga ko wanne a
murtuke yake basa fara'a yasan cewar tuntuni
tun lokacin da suka mara mishi baya ya wawuro wadannan kudade" dama suna xargin da wahala idan bai ha'incesu ba a wurin kasafin da xa'ayi to amma kuma da ace ma anan kadai abin xai tsaya to da da sauki"
"Ina fatan dai ba wanda yasan wannan magana"
domin kuwa wannan sirrine tsakaninmu mu hudu"
wani mai katon kai a cikin bakin yace a fusace"
"Haba Alhaji sau nawa xakayi mana wannan
tambayar?" kada ka daukemu kananan yara
mana" duk duniyar nan wa xamu fadawa irin
wannan sirri mai girma" yanxu maganar kasafi takawo mu" ka gaggauta don mu gama da wuri
kaga dare na kara yi"
Elbashir yayi murmushi" maimakon ya shiga cikin
dakin ya kinkimo akwatin kudin" sai suka ga ya
tafa hannayenshi fas!!
Bakin suka dubeshi a tsorace cikin rashin yarda
domin kuwa sun san cikakken ibilishiii ne" yanxu
haka wata makarkashiya yake so ya kulla musu"
kafin su san me yake faruwa ne" sai suka ji karar
harbin bindiga a bayansu" mutum biyu a cikinsu
suka yi koli-koli a cikin falon suka fado kasa
cikin
jini ko shurawa basu yi ba" dayan kuma yana
inda-inda a rude" sai wani harsashi ya sheko a
guje ya fada cikin malum-malum din da ya jibga" ba wanda yasan inda harsashin ya nufa da gana nan" sun dai ga mutumin yayi tsalle ya hadu da
bango" daga nan wurin yayi tsit kamar anyi ruwa an dauke" gaba daya mutanen sun tafi barxahu"
.
A gaisheku jarumai"
Elbashir yace da ifiritan samarin biyu wadanda ke
tsaye a bakin kofar falon" bindigogin su na fitar
da tiriri" suka matso xuwa cikin falon" suka dubi
gawarwakin mutanen da suka kashe"
Mai bakar rigar yace a fusace"
"Akwai wani aikin da xamu sake yi maka kuma
Alhaji?
Elbashir yace dasu"
"Ina so ku kwashe su ku sakasu a mota" nabar
muku su kyauta idan kuna so" Nidai ku kwashe
min su daga nan" Amma ku tabbatar kun batar
dasu ta yadda har abada baxa a gano su ba"
bayan kun gama sai ku dawo in sallameku
ragowar kudinku"
Nan da nan Ifiritan biyu suka fara kinkimar
gawarwakin bakin da suka kashe daya bayan
daya" suna kaisu cikin motar da suka xo da ita"
awaje"
.
Wadannan ifiritai biyu da basu dauko
rayukan mutane a bakin komai ba" suna da
tarihin rayuwarsu kamar yadda ko wanne dan
adam yake da nashi tarihin"
Matsalar kawai itace su nasu baiyi kama dana
sauran mutane dake a duniyar mutanen kirki ba"
Mai bakar rigar wacce ke da hoton damisa a
baya" sunanshi DUMFANA" mahaifiyarshi ce
kawai data rage masa a duniya" ita kadai tasan
sunanshi na gaskiya" ita ma kuma rabon da ta
sakashi a idanunta bana shekara goma sha biyu (12) cif-cif" tun wani ciwo da yayi a wajen
yawon
duniyar shi aka mayar dashi garin su" bayan ya
warke sai ya sake baxama ya fito" tun lokacin
bata kara jin duriyar shi ba" don haka babu
wanda xai ce yasan sunanshi"
.
Shi kuma dayan mai shudiyar singileti sunanshi GAMBO" amma kuma shi a iya cewa sam barka
ansan sunanshi na lakabin rana wato DANLITI saidai kuma idan mutum ya shekara yana neman shi
indai ba Gambo yace ba" to da wahala ya samu
wanda xaice ya sanshi"
Wannan shakiyan samari guda biyu abokan juna
ne na GANI KASHE NI" domin kuwa a wajen
yawon dambe suka hadu" daga sana'ar dambe
kuma sai suka koma satar kekuna"
Bayan nan sunyi sana'o'i da dama" daya bayan
daya dukansu na alatsine da tir!!
Daga bisani ne suka ci birki a guda daya wato
sana'ar kisa da gangan" Idan kuma sun dauki
lokaci mai tsawo basu sami wanda xa'a kawo su kashe ba" sukan tuna baya suje suyi fashi da makami"
.
GAMBO DA DUMFANA" suna kammala kwashe
mushikan barayin" suka xubasu a mota suka tuka
a cikin daren suka tafi" su kadai suka san inda
xasu kaisu su watsar" Elbashir yayi ajiyar xuciya daya ji sun tafi da motar"
ya shiga cikin daki ya jawo bakar akwati mai
tayoyi wacce ke cika FAL da makudan kudin" ya
xauna dirshan a falon kamar dan shayi" ya bude akwatin a tsanake ya dubi sababbin dalolin amurka suna ta sheki a ciki"
Yayi murmushin farin ciki" domin kuwa duk
duniya shi kadai yasan wannan lamarin a halin
yanxu babu wanda xai tona mashi asiri"
Elbashir yayi jugum a xaune yana kallon kudin" alokaci guda yana tunanin abubuwan da xaiyi
dasu a duniya"
.
Abu na farko daya fara xuwa mashi a rai
shine.....RALIYA-05
.
RALIYA ta shiga cikin motar ta xauna
tare da sauran fasinjojin" yaron ya shigo ya
rufe kofar direban yaja suka tafi" Ga al'adar
xaman mota ba wanda ya damu da wani" fasinjoji ne duk da raliya baya a gaba biyu na a
kujerar tsakiya"
mutum hudu sun warwatsu" a sauran
kujerun
baya" kowa yana ta tunanin da ya
dameshi"
kamar yadda raliya ta dukufa yin
nata tunanin"
bayan ta ciro kudin mota ta bayar"
Ba a fi minti biyar ba da fara
tafiyar su ba sai wani
fasinja ya sake tare su cikin sauri"
yana sanye da
gajerar riga da wando mai ruwan
kasa" yana
dauke da nashi murgujejen akwatin a
hannunshi"
yaron motar ya bude kofar bayan
motar ya tsaya"
Sannan ya bude but din motar yakai
hannu ya
amshi akwatin fasinjan" da farko
mutumin bai so
ya bashi akwatin ba" domin kuwa yafi
so ko ina
xai xauna ya kasancee tare da
akwatinshi domin
kuwa ba abin wasa bane a ciki"
to amma don kada mutane su
xargeshi saiya
mikawa yaron motar ya saka a cikin
but din
motar" tare da akwatin Raliya wacce
xata koma
kauyensu" shi kanshi yaron motar
saida abin ya
bashi sha'awa daya ga an jera
Akwatina biyu irin
su daya a bayan motar" kowanne
yana ta sheki ajikinshi an rubuta
(Japan Express )
.
Yaron motar ya dawo cikin motar ya
xauna"
direban yaja suka tafi" wannan
fasinja daya shigo
motar yanxu" mai akwati irin na
raliya 'yar
makaranta" akwai alamar damuwa
mai yawa a
tare dashi" domin kuwa shima tun
sanda ya shigo
yayi tagumi" motar tana tafiya yana ta
faman
waige-waige sai kace yana
tsammanin wasu
suna biye dashi"
TO amma kuma idan ma har yayi
wannan xato ba
laifi bane domin kuwa shi kanshi
yasan cewar ya
kinkimowa kanshi uwar rigima"
wacce idan ba
wata kwakkwarar sa'a ya taka ba" to
xai yi wahala idan bai bar baya da kura ba"
mutumin yayi ajiyar xuciya sannan ya dubi
budurwar dake
xaune kusa dashi mai yiwuwa irinshi
ce" duk abin
duniya ya isheta" to amma kuma
matsalarta
tasha banban da irin nashi" gashi dai
sun shigo
mota daya" sannan kuma akwatinan
da suka
shigo dasu cikin motar duk irinsu
daya" amma
kuma basu damu da suyiwa juna
magana ba"
Lokacin da mutumin ya dubi yatsun
Raliya ne sai
yaga wani xobe a dan yatsanta
wanda yayi kama
da xoben da ya taba ba masoyiyarshi
dake jami'a baiyi kawaici ba saiya
tambayeta cikin tausasa murya"
"Yan mata ina kika samu wannan
xuben don Allah?"
Raliya ta dube shi a karo na farko
tun
shigowarshi cikin motar" sannan tace
dashi cikin
mamaki"
"Kamar yaya ina na samu wannan
xoben" malam
wannan wacce irin tambaya ce
haka?"
RALIYA tayi tsaki sannan ta kawar da
kanta xuwa
wani bangare tana kallon bishiyoyin
dake wucewa
a gepen titi" domin kuwa tasan cewar
dama
akwai irin wadannan mutanen masu
karambanin
yiwa 'yan mata magana a mota"
Gashi kuma ita ba a irin wannan
surutun da ita in
har tahau mota to da xarar ta biya
har a sauka
ba wanda xaiji muryarta" Ralita tayi
tsammanin
mutumin ya rabu da ita" to amma
kuma xuwa
can sai taji ya sake yafitota a
hankali" lokacin da
ta juyo ne a fusace ta dubeshi sai ya
dukar da
kanshi kusa da kunnenta yace da ita"
"Kiyi hankuri 'yan mata dama ba wani
dalili yasa
nayi maki wannan tambayar ba" ina
da wata
masoyiyata ce dake jami'a wacce na
taba bata
irin wannan xoben" sunanta SURI ni
kuma sunana JARMAI"
.
======>*****()******<=======
ALHAJI ELBASHIR ya dauki tsawon
lokaci akwance bai san inda kanshi yake ba"
jinin dake
xubowa kadan" kadan" daga cikin
raunin dake a
kanshi ya gangaro yana malala a
fuskarshi"
bayan ya kwashe kwararan awoyi
biyu a haka"
xuwa can sai numfashinshi ya dawo"
sannan ya
fara motsa yatsun kafarshi da kuma
hannayenshi"
ya dauki lokaci mai tsawo yana haka
kafin ya fara
yunkuron tashi ya xauna"
Duk wannan abu dake faruwa
hankalin Elbashir
yana kan akwatin kudinshi da ya
bari a bude a
tsakar falon" har xuwa lokacin da ya
tuno cewar
an sami akasi wata matsala ta faru"
bai amince
da xargin da yake rayawa a ranshi ba
na tunanin
wani ya shigo ya tafi da akwatin"
Yasan cewar hakika an shigo bai
sani ba" kuma
ya tuno cewar an kwada mashi wani
abu mai
kamar karfe akai" to amma kuma duk
da wannan
yana saran idan ya farfado xai laluba
yaji ba su"
to tabbas dole ne ya amince da
xargin da baya
so" wanine ya shigo yayi awon gaba
dasu" wanda
kuma idan har haka din ta kasance to
dole ya
dauki mataki kwakkwara"
Elbashir ya samu da kyar ya tattara
karfinshi wuri
guda" ya fara kokarin tashi ya xauna"
to amma
kuma juya tana dibarshi" da xarar ya
kusa
xaunawa sai kuma ya koma ya sake
faduwa yaraf! Sai kace yasha barasa"
Bayan yaga wahala yana kokartawa"
xuwa can
saiya samu sa'a ya xauna" tun baya
iya ganin
komai sai duhu" har ya share
fuskarshi da
hannun rigarshi" sannan ya fara
ganin abubuwa
dake a cikin dakin"
to amma kuma cikin rashin sa'a sai
yaga wayam"
babu katon akwati" nan da nan sai
yaji gabanshi
ya fadi" ya sake waigawa ko ina a
cikin falon" babu akwatin kudi ba dalilinshi"
"DALA MILIYAN HAMSHIN" shinkenan sunbi ruwa" Amma kuma dole ne
ma ya nemo su ko ina suka shiga a duniya"
Elbashir yace a fusace" ko xan rasa raina saina
dawo da abina!" ya karashe maganar cikin daga
murya"
Yana nan cikin falon yana ta surutai shi kadai
saiya kai ganinshi xuwa tsakar dakin inda yayi
male-male a lokacin da hadarin ya faru" Elbashir yaga wani dan mabudin mota a kasa akan
darduma" nan da nan yayi hanxari yakai
hannunshi ya dauki mabudin" dubawarshi keda
wuya sai yaga hoton Jarmai a cikin gilashi a
baya kuma hoton wata budurwa ne" to amma
kuma bata hoton budurwar yake yi ba" Ganin
hoton Jarmai da yayi shiyafi komai tayar mishi
da hankali" domin kuwa a halin yanxu ya
tabbatar da abin da ya faru ko shakka babu
Jarmai ne ya shigo yayi mishi wannan muguwar ta'asa"
"JARMAI..!!!" Elbashir ya tambayi kanshi cikin
mamaki" bai taba tsammanin Jarmai yasan da
wannan sirri ba" na wadannan makudan kudi da suka sata daga gwamnatin tarayya" Gashi yanxun
ya biyo sawunsu kuma yayi nasara" tabbas
Jarmai ne ya shigo ya doke shi" ya dauke
akwatin kudin ya gudu abinshi"
Tun Jarmai yana karami Elbashir ke rike dashi"
wannan ya samo asali ne a lokacin da yayar
Elbashir mai suna LANTANA taxo ta sameshi da
maganar hatsabibancin da danta Jarmai yake yi mata" baban Jarmai ya dade da mutuwa yabarta
da rigima" mahaifiyar Jarmai ta kaishi karatun
allo can wani gari mai nisa" domin ta huta da
axabarshi" acan makarantar ko sati ba'a yi ba
jarmai ya rotsa kan almajirai uku da allo suna
fada" da malamin yasa a kamo shi ne ya gudu" akasa ya dawo gida bayan ya kwana biyu yana
tafiya"
A ranar da ya dawo ya kwashe tiramen xannuwan
mahaifiyar shi Lantana ya sayar yaje aka cinye
kudin a wajen caca" Da Lantana ta kwashe duk
wannan labari ta shaidawa dan uwanta Elbashir sai yace ta kwantar da hankalinta xai yi mata maganin Jarmai zai daukoshi su xauna tare" tun
daga wannan lokaci shekaru ashirin kenan xuwa yanxu" Jarmai yana hannun Elbashir " ya sashi a makaranta tun yana karami amma yaki karatu"
ganin haka saiya mayar dashi boyi-boyin gidanshi
yana aikenshi wurare daban-daban" yana taka
tsan-tsan da halinshi" Daga lokacin da Alhaji
Elbashir ya fara xama da wannan hatsabibin da
nashi Jarmai ya kamashi da laifuka da dama"
kadan daga ciki sun hada da dauko matan banxa
yana kawosu gidanshi" da kuma shaye-shayen
kayan maye"
To amma kuma duk wadannan laifuka basa
damun Elbashir " abban abinda ya tsana a
rayuwarshi ta duniya shine ayi mishi sata" daka
daukar mashi kwandala daya ya gwammace kayi
tatul da giya kaxo ka xaxxageshi kayi ta kwara
mishi amai a jikinshi"
shiyasa suka dade tare da Jarmai basu bata ba
shekara da shekaru" domin kuwa Jarmai baya
daukar mashi ko anini" idan yana son kudi yakan xo ya tambayeshi"
To amma gashi yanxu ba xato ba tsammani
Jarmai ya sake hali" ya fara sata gawurtacciya"
babu mamaki dama can kwanton bauna yayi"
hakika ya shammaci kawunshi Elbashir to amma kuma baiyi nasara ba" Elbashir yace a xuciyarshi"
xan nemoshi duk inda ya shiga" ya daga mabudin
motar a saitin fuskarshi ya dubi hoton Jarmai
cikin tsananin fushi kamar ya jawoshi a cikin
hoton ya kashehi" yace dashi cikin kunan rai a
bayyane"
"Asirinka ya tonu munafuki" saina kamaka duk
inda ka shiga" kuma saika dawo min da kudina"
DALA MILIYAN HAMSIN" baxa su taba kubce
mani ba"! Saina ganoka yaro"
.
Elbashir ya mayar da numfashi sannan ya shiga
cikin wani daki dake jone da falon" da shigarshi
yakai hannu inda wayarshi ta sadarwa take akan
wani teburi karami" ya danna lambobin wayar"
sannan ya saurara yana rike da hannun wayar a
kunnenshi" xuwa can ya fara magana a fusace"
"Hello! Nine Alhaji Elbashir
"Yi maxa ka kira min kwamishinan 'yan sanda
kace nine ke magana" akwai muhimmiyar
maganar da xamu tattauna dashi"
"Zuwa can Elbashir ya dakawa wanda suke
magana tare tsawa sai da dakin ta masa kuwwa"
"Yayi barci?" kace a tasheshi babu lafiya ne" bana
so kana bata min lokaci"
A daidai lokacin ne akayi walkiya mai haske a
sararin samaniya" sannan akayi tsawa" yayyafi
mai sanyi ya biyo bayan haka"
.
=======>******^*****<======
.
Kwamishinan 'yan sanda C.P RAIYANU
DANMASANI yana xaune yana fuskantar
mataimakan aikinshi su biyu sun yi mishi tsuru"
suna sauraron abinda xaice dasu" domin kuwa
tun lokacin da ya buga masu waya a gidajensu
yasa matansu suka tattashesu a cikin wannan
talatainin dare yace su hanxarta xuwa su
sameshi yana a gida yana jiransu"
Sun san cewar babu lafiya inma kuma da lafiyar
to akwai wani babban al'amari daya faru mai
Zafi-zafi wanda yake bukatar jan damarar yaki"
Kwamishina 'Danmasani dogo ne dan kimanin
shekaru hamsin a duniya" fuskarshi ta fara
tattarewa kadan" sannan kuma furfura ta fito jefi-jefi a cikin sajenshi da kuma tumbujejen gashin bakinshi" kullum kanshi a aske yake kamar tulu"
tun lokacin da yana karamin ma'aikaci yana
matukar alfahari da..............RALIYA-06
.
TUN lokacin da yana karamin ma.aikaci yana
matukar alfahari da jajayen idanunshi dake boye a cikin loko kamar idanun maciji" da kuma
faskeken hancinshi da ya tsare rabin fuskarshi"
sau da yawa idan ya hade fuska ya kalli mai laifi" tun kafin yace wani abu wasu ke fara kuka" domin kuwa har gara mutum ya hada idanu da namijin zaki a daji da ya hada ido da DAN MASANI
.
Mataimakanshi biyu da yafi shakuwa da su A.C.P AMINU JAN ZAKI" da kuma ACP BILYA dukan su suma tsofaffin Ma'aikatane da suke dade suna shan damara tun a xamanin yakin basasa"
Har yanxu a ckinsu babu wanda ya mallaki
abinda ya wuce gida da kuma tsohuwar mota
banda motar ofishi da ake xuwa da ita a
daukesu" har gara kwamishina yana da 'yan
kadarori da ba'a rasa ba" to amma kuma idan
aka kwatantasu da hidimar da yake yi da
bila'adadin 'yan'yanshi sai dai ayi hamdala amma kuma baxa ace an samu yadda ake so ba"
Kwamishinan 'yan sanda ya dubi fuskokin
mataimakanshi dake xaman jiran yace dasu wani abu" ya gyara xama sannan yace"
Nasan cewar xakuyi matukar mamaki a dalilin
wannan kira da nayi maku" wata magana ce ta
taso mai girma a tsakanina da ku" Ina so ku
tattara hankalinku wuri guda" domin kuwa mun
sami dukiya mai yawa wacce xata amfanemu da 'ya'yanmu da jikokinmu har karshen rayuwarmu
Amma sai kun bani goyon baya" mun hada kai
sannan xamu cimma wannan dama data fado
hannunmu"
Tsofaffin 'yan sandan sukayi saurin gyara xama
da sukaji maganar da kwamishina ya fada" nan
da nan suka girgiza kawunan su domin su
karfafa mashi gwiwa yaci gaba
"Yanxun nan bada dadewa ba" kwamishina yaci
gaba" Alhaji Elbashir ya kirani a waya" har nayi
barci yasa aka tasheni" dana dauka ne yake
sanar dani gaskiyar abinda ya faru a tsakaninshi da wani dan uwanshi" wani yaro mai suna JARMAI
Elbashir ya sanar dani cewar Jarmai ya sace
mishi kudi har dala miliyan hamsin" ya gudu dasu a cikin daren nan" ya sanar dani ne domin mu taimaka mishi cikin gaggawa a samu a kamo barawon tun kafin yabar garin" yace zai bamu ladan dala miliyan daya" idan har muka taimaka mishi muka kamo Jarmai
Tsofaffin dake sauraron kwamishinan suka kalli juna cikin murmushi" domin kuwa ladan aikin yana da yawa" akalla zasu sami kudi mai tsoka
ACP Aminu jan Gwarzo yace cikin doki"
"Ya kamata mu gaggauta mu kamo barawon
domin kuwa dala miliyan daya kudi ne masu
yawa yallabai
ACP Bilya yace"
"Kwarai kuwa yallabai indai xai cika mana
wannan alkawarin lallai ya kamata mu kokarta
mu kamo barawon cikin hanxari"
Kwamishinan 'Dan masani yayi murmushii sannan ya dawo cikin kankanin lokaci ya murtuke fuskarshi" mataimakanshi biyu suka yi ajiyar zuciya" domin kuwa murmushinsa yafi xama abin tsoro fiye da abin sha'awa yawancin murmushin yafi kama da yanayin da xaka gani a fuskar busasshen tsohon da aka tsirawa allura
.
Har yanxun baku fahimci inda bayanina yasa
gaba ba" kwamishinan yace dasu" wadannan kudi
da yake so mu kwato mishi kada ku taba
tsammanin idan suka xo hannunmu xamu mayar
masa" domin kuwa shima ba nasa bane" kuyi
tunani xaku fahimci abinda nake nufi" a ina
Elbashir xai samu dala miliyan hamsin a kasar
nan"?"
Nasan cewar shima sato su yayi a asusun
matatar man fetur yana so ne mu rufa mashi asiri
da xarar kudin sunxo hannunmu sun xama namu
wannan rabo ne daga sama ya fado a hannunmu"
Tsofaffin 'yan sandan suka dubi junansu" cikin
tsananin rudewa da murna" domin kuwa indai har
abinda kwamishina ya fadi gaskiya ne" to hakika
sun gama hayewa" kwamishina yace dasu"
"Ina so kuyi hanxari kuje can ofis ku sami yara
hudu ko biyar na amana wadanda xasu yi mana
wannan aikin" ina so kafin nan gari ya waye su
nemo mana shi Jarmai din" suxo mana dashi
nan" kun ga da xarar sun kamo mana shi sai mu amshe kudin mu boyeshi a inda baxai kara
fitowa ba har abada" balantana ya tona mana
asiri" kun ga sai mu kasa wannan kudi kowanne a cikin mu ya adana abinshi domin akwai hadari idan muka ce xamu kai banki" yafi kyau musan inda xamu boyesu a gidajenmu" ko me kuka gani?"
.
Wannan haka yake yallabai" suka ce a lokaci
guda a cikin biyayya" a cikin dan lokaci kankani
har sunyi sharkaf da xufa duk da yake cewar
yayyafi akayi a waje" nan da nan suka tashi a
cikin daren suka baxama domin xuwa ofishinsu
su nemi 'yan sandan da xasu yi masu wannan
aikin cikin gaggawa"
Har xuwa lokacin da tsofaffin 'yan sandan suka
tura rundunar 'yan

Please Login or Register in order to submit comment