Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hau ka ciro min shi mu gani" watakila rabona ne ya gifta
Balarabe ya kama bishiyar ya hau" sannu a
hankali har yakai reshen da akwatin yake"
Asabe tana . . . . . .RALIYA-20
.
Balarabe ya kama bishiyar ya hau" sannu a
hankali har ya kai reshen da akwatin yake"
Asabe tana kasa tana kallonshi" da zuwanshi
yakai hannu a tsorace ya jawo akwatin jingim da nauyi zuwa can sai yayi ta maza ya dora shi akan kirjinshi" yaga duk ya fara tsatsa saboda yawan laimar da ruwan da ya dade yana dukanshi" ga alama akwatin ya dade a saman bishiyar mutane basu sani ba
Balarabe ya sauko da akwatin kasa" Asabe tayi
saurin amsarshi taji shi da nauyi kamar an zuba duwatsu a ciki" nan da nan ta fara kici kicin budewa"
Balarabe dake tsaye a kanta yace da ita"
Bai kamata ki bude ba Asabe" mutumin da yayi
tsintuwa irin wannan kamata yayi yaje ya kaiwa
hukuma tukunna sai suyi bincike da kansu" Amma bai kamata mu rigasu budewa muga abinda yake ciki ba
Asabe taci gaba da saita tayoyin kwadon
akwatin" zuwa can ta danna mabudan dake a
kowane gefe nan da nan akwatin ta bude cikin
sauri tare da fitar da wani sauti kamar an balla
sillan kara" budewar akwatin keda wuya sai
Asabe ta kwantar dashi akan cinyarta dake wajen sannan ta bude murfin cikin sauri"
Balarabe dake tsaye yana kallonta yaja baya a
tsorace a sakamakon abinda ya gani a cikin
akwatin" ita kanta Asabe dake durkushe a gaban akwatin saida ta suma" ta bushe na dan wani lokaci" idanuwanta ko kiftawa basa yi zuwa can kuma saita dawo hayyacinta"
Bayan tahi ajiyar zuciya" balarabe yayi karfin hali ya matso kusa da matar shi Asabe" yana kallon Makudan kudin" dake cikin akwatin yace da ita a tsorace"
"yi sauri ki rufe Asabe kada wani yazo ya samemu da wadannan kudi mu jawowa kanmu
bala'i watakila ajiya wasu mutane sukazo sukayi a saman bishiyar" don Allah ki rufe in dauka in mayar dashi inda na daukoshi
Asabe ta harari mijinta balarabe cikin kankanin
lokaci idanunta sun canza kama" sun koma launin toka toka" yawanci idan ranta ya baci ko kuma idan zatayi wani wata doguwar masifa wacce zata kwana bata gaji ba" to daga idanuwanta balarabe yake ganewa" idan yaga sun canza launi" Asabe tace dashi a fusace
"Baza'a mayar din ba" sakaran banza ragon
maza kawai" in banda kai mahaukaci ne wa kake tsammanin zai tsinci akwati irin wannan cike da Dalolin Amurka yace zai mayar dasu inda ya dauko su?" wannan tsintuwa tawa ce" idan baka so" ni ina so
Balarabe ya sake matsowa kusa da ita a tsorace jikinshi yana tsima"
"kada kiyi haka Asabe" wannan ba karamin hadari bane muka tsinci kanmu a ciki" ki rufe akwatin nan" mu gudu mu bar wajen nan na fada maki wannan ajiya ce wasu sukayi" babu mamaki barayi ne kizo mu gudu kada suzo su same mu anan su karkashe mu
"Asabe tace da balarabe a fusace
"kayi tafiyarka kai kadai balarabe" daga yau
rabuwarmu tazo na fada maka" wannan akwati ta zama nawa" duk duniya babu mai rabani dashi ka "Sake ni kawai kayi tafiyarka ka koma gida na fasa zuwa unguwar da zaka kaini" dama wasu kudin zan je nema acan gashi kuma yanzu na same su anan
Balarabe yayi sauri ya waiga kowanne bangare
don ya tabbatar babu wanda yake ganinsu" babu kowa a dajin mutane basu fara zuwa gonakinsu ba
Asabe ta rufe akwatin cikin sauri" ta mike ta
kinkimeshi da kyar ta rungumeshi a kirjinta"
Duk da nauyinshi sai faman zufa take yi saboda tsananin rudewa da tayi da ganin wadannan milyoyin kudin tace da balarabe mijinta dake tsaye yana kallonta cikin fargaba
"kai nake jira balarabe" na fada ma cewar
rabuwarmu tazo bazan iya zama da kai ba a
halin yanzu babu maganar aure a tsakanina
dakai "saboda me Asabe?
Balarabe ya tambayeta a tsorace"
"saboda me?
"Asabe tayi murmushin ta na izgilanci tace
dashi "saboda yanzu ni miloniya ce" balarabe nafi karfinka" zama tsakanin miloniya da beran
masallaci bazai yiwu ba
Balarabe zai sake yi mata magana kenan" sai ta
murtuke fuskarta a fusace ta daka mashi tsawa "Ba na son wa'azinka balarabe kada ka bata mini lokaci" kayi sauri ka sallameni in tafi" kada ka jawo inci mutuncinka a dajin nan....."
Balarabe yaji duk da masifar Asabe yana sonta
baya son rabuwarsu" to amma kuma yaya zaiyi
da ranshi tunda dai ta matsa mashi dole saiya
saketa" bai san lokacin da ya fashe da kuka ba"
yace da ita
Shikenan Asabe" na sakeki saki daya" amma ina sonki" banso kiyimun haka ba" banso rabuwarmu dake ba"
Asabe tayi dariyar shekiyanci tace dashi"
"Sai wata rana mijina kada ka damu" nasan
bazaka taba mancewa dani ba a rayuwarka" bana bukatar kayan dakina" ka daukesu na bar maka kaci gaba da zama kai da momi kace mata Nina tafi sai watarana"
Asabe tayi saurin garzayawa cikin gudu-gudu
tana rike da akwatin tabar tsohon mijinta balarabe tsaye yana kallonta.." har tayi nisa sai ya daga murya yace da ita
Yanzu ina kika nufa Asabe" ina zaki je a cikin
dajin nan? Asabe bata waigo ba tace dashi tana sauri
Wurin zuwa ba mai wahala bane balarabe"
musamman idan kana da Milyoyin Kudi a tare
dakai kada ka dami nina san inda zanje sai
watarana...
Asabe tayi nisa balarabe yana tsaye yana
kallonta har ta bace ya daina ganinta
.
=======>******************<========
.
HAJIYA TABAWA ta fito daga cikin
fashashshiyar rumfarta inda take sayar da
abinci" wacce rufin kwanonta ya huhhuje kamar rariya" sai kadangaru da tsaka ke kai da komowa a jikin rumfar da kuma jirwayen ruwan sama na shekara da shekaru
Da fitowarta ta kalli kwastomominta dake a
Zazzaune akan benci wadanda yawancinsu
leburori ne" da kuma 'yan tasha sai kuma dan
abinda baza'a rasa ba na matafiya masu safara
suna kai kaya kasuwannin karkara Ganin wasu suna a zaune ba'a kawo musu abinci
ba" saita dakawa yaranta uku tsawa" karuwai
biyu da kuma dan daudu daya"
Nan da nan suka mayar da hankalinsu akan
uwargidansu ta tsaya a bakin rumfar shirim da
ita kamar bukka" 'yar gajeriya ce baka" mai
mulmulallen kai wacce ta matse shi da dankwali sai kace wani karamin tulu" sau da yawa bata tashi masifarta" sai taga kwastomomi sun hadu awajen" saboda tayi musu burga A san cewar ita ce babba" haka kawai sai ta fada karuwan da fada wasu lokutan hade da zagi" da yake tuntuni zuciyarsu ta mutu" kuma da yake tuni sun kaucewa tafarkin gaskiya na manzon tsira da aminci su tabbata agareshi" wannan
baya damun su" to amma kuma a boye idan sun kebe sukan dade suna gulmar mafadaciyar matar wacce take rike da su yau da gobe" tana neman arziki a tunaninta"
Shi dan daudun ba kasafai yake jin tsoronta ba"
da yake shine dan lelen ta" sau da yawa tafi
bashi amana fiye da karuwan yaran nata" domin kuwa ko ba komai takan sanar dashi wasu kadarorinta data saya" ta boye a gidanta
wadanda zasu taimaketa ako da yaushe" duk
lokacin da bukatar kudi ta taso mata"
Abubuwan da take bashi labarin ta saya ta boye sun hada da sarkokin daham masu tsada"
wadanda a yanzu haka a cewarta kudinsu sun kai kimanin Rabin miliyan kuma in banda
wadannan sarkoki da 'yan kunnaye da zobina
bata tanadi komai ba" a wannan sana'a ta dafa
abinci a bakin tashar mota" tun tsawon shekara
goma sha hudu da suka shude"
Ganin sun kura mata ido" suna jiran umarninta"
sai ta bude wagegiyar muryarta mai kama da
lasifikar garmaho tace dasu a fusace
me kuke yi kuka bar mutane a zaune baku basu
abinci ba? Daya daga cikin karuwan wacce suke ce mata Jiniya ta taso tana rangwada da siririn wuyan ta kamar na tsohuwar belbela" tasha damara da gyalenta kafarta babu takalmi" ta nufi inda daya daga cikin tukwane biyar din da ke kan wuta suna tiriri" ta bude daya da sauri ta jefar da murfin agefen murhun saboda zafi taja da baya" sannan ta ce wa uwargidan tasu Doya suke jira" kuma har yanzu bata karasa nuna ba Hajiya tabawa tace dasu
"Ai laifinku ne tuntuni naso ku fara dora doyar
nan to da yake ku bakwa jin magana sai
da kuka ga dama sannan kuka dora" gashi lokaci yayi har mutane sun fara tambaya ina amfanin wannan rashin mutuncin ace mutum yazo cin abinci sai yayi zaman jira
Ta dubi kwastomomin dake a zazzaune da jajayen idanunta" sannan ta washe wagegen bakinta wanda ke kama da barnar wuka" kuma wanda ke tona asirin shekarunta data dauka a baya tana kurbar barasa" kafin shari'a tazo ta daidaita sahun duk wani takadari dake zaune a birni da kewaye
Bayan ta gama tsorata kwastomominta da
abinta a tsammaninta za'a kirashi da murmushi
sai tace dasu "kuyi hankuri kada yanzun nan zata nuna" basu dora da wuri ba ne yau"
Kwastomomin da suke cin abinci suka dubi
wadanda ke a zaune suna jiran doyar" wasu
samari ne majiya karfi su uku wadanda da
ganinsu ko ba'ayi tambaya ba" idan mutum yayi
la'akari da tabon dake a fuskokinsu to zai iya
gane cewar in dai ba hadarin mota aka tabayi da su ba to babu shakka sunyi zaman daba" ko kuma yawon farauta" to amma kuma da'ace anan abin ya tsaya da anyi san barka" Lamarin rayuwarsu duk ya zarce nan a halin yanzu.
Hajiya tabawa ta dubi daya karuwar dake a zaune wacce ake cewa "Idon Gwal wata kakkaura ce wacce bata mori man canza fata na shafe-shafen zamani ba"
maimakon ta koma fara mai dan kyan gani" sai
tayi kala biyu" kamar zabuwa" wani sashi na
faffadar fuskarta dake kama da faranti" tayi fari
fegen idanunta kuma yayi duhu" da kuma wani
sashi na kunnuwanta
Duk da haka bata damu ba" domin kuwa mijinta
na bariki bai damu da ganinta a haka ba kullum
idan yayi kamasho a tasha ita yake fara zuwa ya zubewa kudin da ya samu" wani lokacin ta dauki wani abu ta bashi" wanda zai sayi taba da abinci" wani lokaci kuma idan taga dama saita hanashi ko sisi" kuma ta zazzagi iyayenshi har sai an bata hakuri saboda bai kawo mata kudi masu yawa ba" da zasu isheta cefane
Hajiya tabawa ta harareta" sannan tace da ita
"ke kuma kin zauna nan kina kallon mutane da
wadannan shegun tulu-tulun idanunta naki da ke kama dana mujiya" bazaki tashi ki taimake ta ku iza wutar a samu abincin ya nuna ba?"
Idon Gwal din ko kuma idon mujiya cewar
Hajiya tabawa mai abinci" ta taso cikin fushi..RALIYA-21
.
Idon Gwal din ko kuma idan mujiya a cewar
tabawa mai abinci" ta taso cikin fushi ta nufi
inda 'yar fingililiyar kawarta take" suka taru suna iza wuta tare suka kalli juna suka yatsina fuska domin kuwa sun tsani wannan dunkulalliyar matar tana bada su a gaban kwastomomi baki" tana zaginsu don ta ga ita ce shugaba" to amma kuma da ace sun shirya sun zauna a dakunan aurensu domin raya sunnar fiyayyen halitta" anya kuwa irin wannan cin mutuncin zai same su?
Daga nan sai ta mayar da hankali akan dan
daudun yana zaune akan kujera ya juya musu
baya" yana fere kabewa ya kima wani katon zani akan shi kaya guda yana rangwada sannu ahankali yana rera wata waka ta garaya da yake
yawan cashewa da ita a duk lokacin da biki ya
tashi" aka gayyace shi hawa bori" tabawa tace
dashi "ke kuma idan kin gama wannan fera kabewar ki shigo ina son ganin ki zan aike ki wani wuri
"Gamsameman katon wanda zai iya kayar da
bajimin sa" ya lankwashe bayanshi bai waigo ba ya matse muryarshi kafin yace da ita cikin
girmamawa. "Gani nan zuwa idan na gama yaya.
Samari ukun dake jiran a sauke doya a cikin
kwastomomin suka harari dan daudun a lokaci
guda" su kadai suka san dalilin zuwansu wajen
wadannan gayyar tsiyar karuwai da 'yan daudu"
amma ba abinci ya kawo su ba.
Hajiya Tabawa ta koma cikin tsohuwar rumfar
kwanon inda take shimfida tabarma ta zauna da muhimman bakinta na sirri" wadanda ke zuwa kullum" yawancinsu tsofaffin bariki ne" da suke nemanta da kuma watsatstsun kawayen ta wadanda suka gujewa shiriya tun tali-tali
Bata dade da komawa cikin rumfar ba" kamar
daga sama sai ga wata bakuwa tazo wajen" ga
alama taci uban tafiya wujiya-wujiga da ita" duk
tayi zufa" tasha rana" amma kuma duk da haka
tana dauke da wani murgujejen akwati a
hannunta" da ganinta tafi kama da sababbin
shigowa bariki" ko kuma babu mamaki tsohuwar hannu ce
tayi canjin gari ne shine ta fado wajen sayar da
abinci" domin kuwa tasan cewar a irin wadannan wuraren suke samun helkwatar da za'a amshesu
Don haka kowa yayi tsammanin wannan katon
akwati dake a hannunta duk barazana ce babu
wata tsiya ke a cikin shi ba" sai 'yan
tsummokaranta na sawa da kayan kwalliya da
ba'a rasa mata dasu a jaka duk wuya"
"to amma kuma da ace wannan bakuwa zata dan bude akwatin ko kadan" kwastomomin da kuma karuwan su leka suga abinda ke a ciki" to da babu mamaki wasu zasu sume a wajen saboda tsananin kaduwa"
Bayan da bakuwar ta gaishesu sai tace kai tsaye "Nazo wajen Hajiya tabawa ne"
"Jiniya ta dago kai daga inda take a bakin
murhun tana hura wuta" duk hayaki ya cika mata idanu" tace da bakuwar"
"ki shiga cikin rumfar tana nan
Bakuwar ta shiga cikin rumfar dauke da katon
akwatin ta" wasu daga cikin kwastamomin sai
kallon hadarin kaji suke yi mata" domin kuwa
yawanci sun bada cewar ita ma ai 'yar zaman
kanta ce" wacce tazo neman taro da sisi daga
garin su"
"yan matan karuwan biyu da kuma dan daudun
suma a wulakance suke kallonta" domin kuwa
basu san a kawo musu wata bakuwa ta zauna acikinsu" Abinda duk wadannan mutane basu sani ba shine Wannan bakuwar wata tsohuwar aminiyar Hajiya tabawa ce" wacce suka dade da shakuwa tun awani yawon bariki da ya hadasu" kuma wannan akwatin dake a hannunta idan aka zazzaage
abinda ke a ciki zai iya samar da tituna da
makarantu da asibitoci da fanfuna da wutan
lantarki a duk fadin wannan karamar hukuma tasu
Gabaki daya mutanen sunyi mamaki da sukaji
Hajiya tabawa da ke a cikin rumfar ta taso cikin
farin ciki ta tarbi bakuwarta tana cewa cikin
Zumudi
"Ashe rai kanga rai Asabe?" sannu da zuwa
kawata" ashe kina nan a raye ina kika shiga
shekara da shekaru?" sannan kowacce ta kama
hannun kawarta suka tafa suna dariya da shewa
.
=====>+++++++++++++++++++<=====
.
Minti talatin bayan haka lokacin da doyar ta
karasa nuna aka zubawa samari ukun dake zaune suna jira sai suka fara kaiwa baki, hannu baka hannu kwarya. Suna cin abincin suna sauraren
duk wata hira da karuwan keyi da dan daudun"
Bayan sun gana an kawo musu ruwa" sai babban cikinsu wanda kuma ga alama shine jagoran tafiyar su yace da jiniya nawa ne kudin ku? tace dashi tana juya dan firirin wuyanta"
"dari biyu da arba'in ne
Saurayin yayi murmushi kafin ya ciro kudin ya
bata" ita a tsammaninta kwarkwasar da tayiwa
saurayin ya burgeshi" har yake yi mata fara'a
Abinda bata sani ba" shine siririn wuyanta da yagani shi ya tuno masa da wata mata da ya
darzama wuka a wuya wata uku da suka wuce"
lokacin da suka shiga gidanta yin fashi taki basu hadin kai" ta fito musu da gwal-gwalan da aka basu labarin ita ma ta boye a gidanta
Yanzu da saurayin ya kalli wuyan jiniya saiya fara tunanin abubuwan mamaki" itama tana bukatar wukar zuwa anjima da daddare"
Idan har suka shigo gidan Hajiya tabawa yin fashi da makami kamar yadda suka kudiri aniya ba wani dalili da yasa suka zo cin abinci awajen matar ba" sai don su fahimci yadda take gudanar da al'amuranta" da kuma lokacin da take tashi daga kasuwa ta koma gida"
wannan ya zame musu kamar al'ada duk lokacin da zasu je sata sai sun bi mutum sannu a hankali sun ga yadda yake gudanar da sha'anin rayuwarshi" sannan sai suyi mishi dirar mikiya idan dare yayi
Koda yake a tarihin wannan muguwar sana'a tasu basu yiwa maza sata" sai dai mata" domin kuwa sun fahimci mata sunfi maza bada hadin kai cikin sauri idan suka ga barayi"
sau da yawa bayan sun dawo daga sata idan
suka zauna sai su rika tuno abinda ya faru" su
duka ukun sun sha cewa! "mata basu da matsala da zaran ka nunawa mace bindiga zatayi sauri jikinta na rawa ta baka kudi da sarka" to amma kuma abinda yasha bamban a wurin maza" a da can kafin su fahimci haka" sun sha tsare hanya wasu mazan ko kashe su za'ayi bazasu taba fadin inda kudin suke ba" saboda tsabar taurin kai
Amma mace ko ido ka zare mata yanzun nan
Zaka sami sarka mai tsada kasa a cikin aljihu
kayi gaba abin ka ba wani wahala"
A wannan karon Hajiya tabawa itace sabuwar
wacce zata amshi bakuncin su" idan dare yayi"
an sanar dasu cewar matar tana da kudi sosai"
kuma bata yin ajiya a banki" don haka in gaskiya zasu gani anjima Domin kuwa duk da wannan jajayen idanu da take yiwa yaranta barazana dasu tana banbami" sun
san cewar da zarar sun nuna mata bindiga zata
lafa ta basu abinda suke so"
Domin kuwa su ba 'yan daudu bane da ta
rainasu da wuka suke wasa da bindigogi bada
ludayin miya ko askar fere doya da kabewa ba"
Jagoran samarin uku mai suna LADO NIGA ya
ciro kudin abincin ya bata" jiniya ta amsa tana
fari da busassun idanunta tace
"muna fatan wata tana zaku sake dawowa"
Lado yayi murmushi a zuciyarshi yace
"kada ki damu zaki sake ganinmu bada jimawa
ba Daga nan ya mike ragowar abokan tafiyashi su biyu suka tashi" akwai alamar dariya a fuskarsu da suka ji irin hirar da lado keyi da wannan bushashshiyar mata"
Daya a cikin su sunanshi BALA" daya kuma
sunanshi BANGIS" dukkansu karti ne majiya
karfi" wadanda iskar duniyar bushasha ta kado su wuri guda suka hadu suka zama abokan juna kuma masu yin sana'a daya
Bayan sun bar inda rumfar Hajiya tabawa ke
sayar da abinci da suka dan matsa nesa kadan"
sai suka zauna akan wani karfen injin birtsatsai
na ruwa" lado ya dubi bangis dake fuskantar shi ajere akan nasu karfen yace dasu
"Ina ganin bamu da wani haufi tana a gari babu
inda zata je yau" kawai mu dirar mata anjima"
Bangis yace dashi "musamman kuma naga kamar tayi bakuwa" ina jin koda yana da niyar fita zaiyi wahala ace bata dawo ba" komai dare"
Bala yace da bangis"
"Don tayi bakuwa wannan ba wata hujja bace da zaisa mu daga kafa" yau ko tana a gida ko kuma zata fita wani waje" baka ganin bakuwar ba" wata mai maiko bace" ina tsammanin irin
tsofaffin 'yan hannu ne data fara karewa shine ta sake gari" ta zo wajenta" wannan ba wata
bakuwar harkar arziki bace" kawai indai zamu
dira mu dira" kamar yadda mukayi niya"
Lado niga" yayi fito zuwa can yace
"mu dira kawai" komai ma muka samu yafi babu"
A haka dai mun rage na tabawa kafin wata
hanyar ta sake buduwa"
"sukayi dariya" a lokacin ne suka sake mayar da
hankalinsu acan inda rumfar matar take hayaki
ya turnuke a wani murhu Idon gwal ta duka tana faman fifita" a daidai lokacin ne kuma Hajiya tabawa suka fito ita da bakuwarta" tace da yaranta
"baku san idan kunga bakuwa tazo ku gaisheta
ba?"
wannan aminiya tace" mun dade bamu hadu ba"
sunanta Asabe ku dauki akwatinta ku rakata
gida tayi wanka ta huta kafin in dawo" tazo ne ta dan yi mani kwana uku kafin ta koma"
Karuwan biyu da gabjejen katon dan daudun suka zube cikin girmamawa suka gaishe da bakuwar"
sannan jiniya ta amshi akwatinta suka tafi gida"
Lado Niga da abokan tafiyarshi suka kawar da
kansu bayan matan biyun sun bace!"
.
=========************==========
.
'Dakin da aka sauke Asabe a gidan Hajiya
tabawa" yana cikin dakuna uku dake a jere da
juna" kuma dama ta tanade su ne musamman
don irin wannan ranar idan tayi baki" sauran
dakuna biyu inda yaranta uku ke kwana ne"
wadanda take cewa 'yan mata baki dayan su"
tare da shakiyin katon da ya mayar da kanshi
mace" saboda tsananin bala'in da ya fadowa
rayuwarshi a duniya
Wani abinda Hajiya tabawa ta kasa fahimta a
game da wannan ziyara da Asabe ta kawo mata shine" ganin yadda take faman nuku-nuku da katon akwatin da tazo dashi" sai kace ta ajiye wata tsiyar azo a gani a ciki"
to amma kuma bata tambayeta abinda ke ciki ba" tasan dai bai wuce tiramen zannuwa da tsofaffin takalma ba"
Hajiya tabawa ta dade da sanin Asabe tun a wani zaman sayar da abinci da tayi a cikin birni"
To amma kuma bambancin rayuwarta da kuma
Rayuwar Asabe shine ita tabawa ta dade da yin
murabus da . . . .RALIYA-22
.
Hajiya Tabawa ta dade da sanin Asabe tun a
wani zaman sayar da abinci da tayi a cikin birni
to amma kuma bambancin rayuwarta da kuma
rayuwar Asabe shine ita tabawa ta dade da yin
murabus da sha'anin zaman aure
Rayuwarta gabaki daya ta dogara ne a tashoshin garuruwa na motoci" inda take kafa rumfunan sayar da abinci ita da yaranta na bariki" idan ta fahimci wannan garin yayi mata zafi ciniki ya cushe sai kuma ta canza sheka ta koma wani gari"
Amma ita Asabe bata shiga ruwa tsundum ba"
asha ruwan tsuntsaye take yi da harkar bariki"
tana dan tsayawa tayi aure" amma da zarar anyi auren to in har akaci sa'a yayi tsawon rai takanyi wata takwas zuwa wata tara" kuma in har ta fito to bata da wasu abokan arziki sai ire-iren. wadannan karuwai 'yan tasha"
wata majiya tace Asabe tana jin tsoron
mahaifinta ne shiyasa bata shiga harkar bariki
tsundum ba" Amma in har ta wayi gari watarana taga bashi a raye to ita ma bangaren Zaman aure sai dai a bar wa 'yan baya tarihi"
A can cikin dakin Asabe ita ma tana a kwance
batayi barci ba" ko da yake dama in ma aka
kawo mata zancen barci ai kamar anyi wauta ne Domin kuwa a yadd take kankame da wannan uwar akwati dake cike da Dalolin Amurka to bata da karfin imanin da zata iya runtsa idanu tayi barci bata kallonshi"
Lokaci-lokaci bayan ta tabbatar ta kulle ko ina a
cikin dakin ta zage labule" sai ta bude akwatin"
domin ta kara tabbatar da abinda ke a ciki ba
budar ido bane" kuma da gaske ne ba mafarki
take yi ba
Hakika kudin suna nan kamar yadda suka tsince su a daji ita da tsohon Mijinta za'a ce
Yanzu wato balarabe sarkin tsoro" domin ita dai
Asabe tana mamakin yadda za'ace dan adam mai rai da lafiya a jiki ya tsinci akwati cike da kudi" kuma wai har ya tsaya yana wani bata lokaci da wasi-wasi.
Kudi duk inda suke kudi ne Kuma ba abin
wasa bane" samun su kawai ke da wahala"
amma in har ka samesu" to duk matsalolin da
Zasu biyo baya masu saukin warwarewa ne"
kamar yadda Asabe tayi imani
Da ganin kudin tun a lokacin tasan cewar ba
kudin nageriya bane" to amma kuma tasan inda
ake canjin kudin a kano" domin kuwa ita 'yar
birni ce gaba da bayanta shiyasa ta yanke shawarar ta samu wuri ta boye
kanta da kuma kudin a lokaci guda"
Idan ta huta kuma ta gama shirya yadda zatayi
da kudin" daga nan sai ta debi wasu a ciki ko ba yawa koda a cikin habar zaninta ne ta nufi birni acanza mata su taga shin miliyan nawa zasu koma
Ko miliyan uku ta fara canzawa a kudin najeriya sun isheta ta sayi gida a birni" ta koma can kudin kuma sun isheta ta bude akawun a banki ta sami wata 'yar sana'a ta karya tana yi" tana canza kudin sannu a hankali yau da gobe wata rana duk sai ta mayar dasu kudin nageriya"
tasan cewar zuwa lokacin ta zama biloniya"
wacce za'a rika jin labarinta ako ina" kuma indai har kudin sun taru to tasan cewar ba kowanne mutum bane zai sa mata ido ya zargi inda ta same su"
Babu wata sana'a kwakkwara dan lokaci kankani ba" tasan matsalar wannan zamani" kuma tasan abinda mutane ke so" in dai zaka rika yiwa mutane alheri a wannan zamani kana basu kudi to komai laifin ka sai ka zama babban mutum"
Haka kawai sai ayi ta girmamaka ana yi maka
fadanci" komai ka fadi babu wanda zai karyataka" kuma abinda kake so shi za'ayi maka" don haka menene abin wahala?"
Tun da dai ga kudin nan tsaba a cikin akwati"
kuma duk nata ne ita kadae"
Asabe ta sake mika hannu tana zaune ta taba
akwatin ta sake bude shi" domin ta sake
tabbatarwa kudin sunanan"
A daidai lokacin da tayi murmushi ne bayan kudin sun haska mata idanunta sai taji wani abu a waje kamar faduwar nakiya ya cika ko ina a gidan" to amma kuma ba nakiya bace karar fadowar kofar gidan ne" wacce bangis ya kwadawa wani murgujejen gatari" ta tsage gida biyu ta tarwatse sai kace kofar gilashi bata jan katako na madaci ba"
Asabe taji gabanta ya fadi" tayi sauri jikinta yana kyarma ta mayar da murfin akwatin ta rufe shi da kyau" A sannan ne kuma taji sautin shigowar kartin a fusace cikin gidan" Asabe ta dafe kirjinta a tsora ce"
"me yake faruwa?" ta tambayi kanta"
me ya kawo barayi cikin gidan" kuma ya akayi
suka san akwai kudi a boye a cikin akwatin ta?"
Asabe ta fara safa da marwa a cikin dakin" gashi kuma babu hanyar guduwa nan da nan ta fara sheshshekar kuka tace a zuciyarta"
"Na shiga uku a ina zan boye kudina?"
A daidai lokacin da take inda-indar inda zata
boye kudinta ne" bala dake

Please Login or Register in order to submit comment