Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sanda domin a nemo musu
JARMAI babu wanda yayi ma wani mgana" domin
kuwa tunanin wadannan makudan kudi ta gama
rudasu" kowanne yana tunanin abinda xae fara yi
da xarar kudin sun xo" suna cikin tafiya ne a
mota xasu dawo gida" sai ACP aminu ya bugi
kafadar abokin aikinshi bilyaminu yace dahi"
mutumin naga kayi shiru ne! Tunanin me kake
yi?"
Bilya yayi ajiyar xuciya"
"tunanin wadannan kudin nake yi" Ina ta lissafa
abubuwan da xanyi dasu ne"
"Wata xuciyar tana raya min inje kasar rum in
gina kamfanin karafa acan"
"Amma kuma nafi so in koma kasar japan in hada
hannun jari da wani kamfanin kera bindigogi"
.
ACP Aminu yace dashi"
"Ni kuma tuni na yanke shawarar komawa kasar
swizilan in gina otal nawa na kaina" Daga nan
kuma ni da wannan kasar har abada Allah ya
rabani da talauci"
'yan sandan biyu suka fashe da dariya lokaci
guda" abinda basu sani ba shine tuni har
kwamishina ya gama shirya irin kisan da xaiyi
musu a boye" da xarar kudin sunxo hannunshi"
.
======>*****^*****<========
:
"SURI?" Raliya ta tambayi mutumin cikin
mamaki" ya akayi kasan kawata suri malam?"
jarmai yayi mata murmushi yace"
"masoyiyata ce" bata taba baki labarina ba?"
RALIYA ta girgixa kanta alamar bata taba ji ba"
Hakika wannan xobe dake a yatsanta suri ta
mallaka mata shi a daren jiya domin ta rika
tunawa da ita" gashi yanxu kuma ta hadu da
masoyin suri a mota kuma ya gane xoben shi" daya ba masoyiyarsa"
RALIYA ta tuno maganar da sukayi ita da suri a
yammacin jiya inda take shaida mata cewar"
AKWAI WANI SAURAYINTA RIKAKKEN BARAWO MAI SUNA JARMAI
raliya taji gabanta ya fadi ta dafe kirjinta" a
tsorace sannan ta sake kallon Jarmai wanda ke xaune a cikin fasinjojin motar yana yi mata
murmushi" taji tsoro ya kamata" to amma kuma
da yake taci sa'a ta kusa sauka daidai hanyar da xa'a bi a nufi kauyensu bata damu ba"
Jarmai ya mayar da hankalinshi a wajen nashi
tunanin da yaga raliya bata son hirar" domin
kuwa shima yana da nashi tunanin da ya dame shi a xuciyarshi" to akalla dai yanxu yana kyautata
xaton yayiwa kawunshi Elbashir nisa" domin
kuwa koda ace Elbashir ya sanarwa 'yan sanda"
bazasu taba kawowa a ransu cewar xai gudu ya boye a wani kauye ba" xasu bishi can wani waje
ne inda suke tsammanin ya nufa" kamar tashar
jirgin sama"
"to amma kuma gashi ya shammacesu ya dauko
murgugujen akwatinshi wanda ya cika FAL da
miliyoyin kudi na dalar amurka" ya shiga motar
haya xaije wani kauye ya labe sai kura ta lafa"
sannan sai ya biyo dare ya dawo ya dauki
masoyiyarshi suri su gudu da kudin su"
Jarmai yayi murmushin farin ciki da ya tuna irin
holewar da xaiyi a duniya da wadannan kudi bai
san cewar suri ta gama shirya hanyar da xata bi
tayi mashi wayo ba ta amshe akwatin ta gudu da kudin ba"
.
SURI tana can makaranta tana ta duba agogo
tana tsaki" domin kuwa ta kosa taga Jarmai" ta
kosa ta amshe kudin ta koma garinsu ta dauke
tsohuwar kakarta gurguwa su gudu xuwa wata
duniya inda xasu more kudinsu hankalinsu a
kwance ba tare da 'yan sanda sunbi sawunsu sun takura musu ba"
.
Motar taci gaba da sheka gudu akan titi" xuwa
can RALIYA ta hango lambar kauyensu dake a
bakin titi an rubuta DAN MARKE nan da nan tayi sauri ta taba yaron dake gyangyadi"
"Akwai wajen lambar can! Akwai......."
Yaron motar ya cewa direban cikin sauri"
"In kaje Dan marke akwai mai sauka"
Motar ta fara saranda nan da nan ta silale ta
tsaya a saitin hanyar kauyen su RALIYA" wasu
matan fulani su hudu sun dauko koren nonon
suna ta sauri sun kama hanyar kauyen" A kusa
dasu kuma wani saurayi ne ya tasa manyan
shanun huda a gaba sun dawo daga aiki duk ya
jike da raba a kafafuwan wandonshi da ya yage" raliya tayi ajiyar xuciya domin kuwa taga gida"
tayi sauri ta fita daga motar bayan yaron ya bude
kofar" ya nufi bayan motar cikin sauri domin ya
bude ya dauko mata akwatinta
Jarmai ya cewa raliya "sai anjima 'yan mata" idan kin ga suri kice ina
gaisheta"
RALIYA tayi banxa dashi domin kuwa ta tsaneshi
duk ta kosa dama ta sauka su rabu" yaron motar
ya ajiye mata akwatin a kasa" ya rufe bayan
motar ya dawo a guje ya shiga direban ya ja
motar suka tafi"
yaron motar ya daburce bai san akwatin da ya
ciro ba a cikin kwatinan biyu" domin kuwa irinsu
daya" wannan ba matsalarshi bace" yace a
xuciyarshi sannan yaci gaba da gyangyadin shi
motar tana ta sheka gudu
RALIYA ta gyara lullubinta da tsohon gyalenta"
sannan ta dauki akwatin domin ta kama hanya ta nufi kauyensu" to amma kuma ga mamakinta sai
taji akwatin yayi mata nauyi jigim!
Sai kace an xuba mata duwatsu a ciki" ta
yunkura dakyar ta raba akwatin da kasa" sannan
ta fara tafiya dashi batayi nisa ba ta tsaya domin
ta huta" me ya sami akwatinta kuma?"
RALITA ta tambayi kanta" to amma kuma
watakila laifinta ne domin kuwa yunwa take ji
bata karya ba ta fito daga makaranta" gashi
yanxu daukar akwati xai gagareta"
RALIYA tayi murmushi tace a xuciyarta"Dana sani
dana tsaya na karya domin kuwa suri ta gama
abinci" to amma kuma ta kosa ta dawo gida taga masoyinta rufa'i
RALIYA tana kan tafiya ne da kyar dauke da
akwati" sai ga wani mutum makwabcinsu mai
suna malam Dan kano" ya taho da amalanken
shanu yana turata da hannunshi" ya cewa
raliya "yan makaranta an dawo ne?" Raliya ta...RALIYA-07
.
Yan Makaranta An Dawo Ne?
"RALIYA ta gaisheshi cikin ladabi ya
amsa" ganin tana ta fama da katuwar akwatin sai ya mayar
mata ya dora akan amalanken ya tura
mata"
Raliya tayi mashi godiya tabi shi a
baya" suna ta
sauri" suna wuce manoma a gonakin
dawa da
masara" suna ta faman aiki" Raliya
taso ace ta
rage kudi a hannunta data ba
mutumin ko naira
ashirin ne" domin kuwa ya taimaka
mata wajen
daukar mata wannan akwati mai
nauyin tsiya" to
amma kuma bata da sauran ko
kwabo a
hannunta" su kenan ta bada su kudin
mota" to
saidai kuma da ace raliya zata
bude akwatin da
mutumin ke tura mata data sami
kudin da xata
bashi lada masu yawa"
Abin da raliya da mutumin basu
sani ba" shine
wannan akwatin dake gabansu ba
tsummokara da
littatafai bane a cikin shi" Dalar
amurka ne har
kimanin miliyan hamsin"
.
=====>******^*******<=====
.
FARAR motar tana cikin tafiya da
fasinjojinta
guda shida sunyi shiru" ba zato da
tsammani sai
suka ji jiniyar motar 'yan sanda a
bayansu"
direban ya kalli madubin motar yaga
bakar motar
yan sanda ta cika Fal da kwalawa
suna rike da
bindigogi" nan da nan ya rage gudu
daya ga 'yan
sandan suna tsayar dashi"
Tsayawar motar keda wuya" sai
motar 'yan
sandan taci taya a bayanta" 'yan
sanda shida
suka firfito a gurguje suka xagaye
motar suna
xare idanu" Jarmai dake xaune yayi
mutuwar
tsohuwa domin kuwa yasan cewar
asirinshi ya
tonu" shiyasa suka biyoshi"
Yaron motar ya bude kofar motar"
'yan sanda
suka leka ciki biyu daga ciki suka
cakumo Jarmai kamar dan wake a lokacin ne
wani dan
sanda ya bude bayan motar ya
sungumo akwatin
ya kankame ta yana ta baraxana da
bindigar dake
a hannunshi" wani a cikin 'yan sanda
ya dakawa Jarmai tsawa"
"wannan shine akwatin?"
Jarmai ya girgixa kai "yace shine"
'dan sandan
yasa gindin bindiga ya kwada mishi a
gepen
bakinshi" hakora uku suka yi tsalle
suka fito
waje" wata mace dake a cikin motar
ta rusa
kururuwa"
Jarmai ya xube kasa yana shure
shure" jini yana
kwararowa ta bakinshi da hancinshi"
nan da nan
suka tattarashi suka hada da kawatin
suka nufi
cikin motarsu" ba laifin su bane"
domin kuwa tun
cikin daren an basu umarni in har
sunga Jarmai
kada suxo dashi da kamanninshi" su
canxa mashi
halitta yadda ko uwarshi ta ganshi
baxata iya
ganeshi ba"
To amma kuma har 'yan sandan suka
ja motarsu
sukayi kwana suka tafi bata Jarmai
suke yi ba
da yake kwance magashiya" ta
akwatin kudin
suke yi dake a tsakiyar su" domin
kuwa su kansu
basu yarda da junansu ba" suna jin
tsoron kada
wani a cikinsu ya harbesu ya gudu
da miliyoyin
kudin shi kadai"
Da ace xasuyi karambanin bude
akwatin da
sunsha mamaki domin kuwa xasuyi
nasarar
tsintuwar littatafan karatu da kuma
rigunan
mama da tsofaffin takalma
.
=======>*****^*****<======
.
Kauyen dan marke wanda yake da
nisan kilomita
daya da rabi daga bakin titi" yana
cikin karamar
hukumar garun malam" dake a jihar
kano" dan
marke kauye ne dake da dimbin tarihi
domin
kuwa akwai tsofaffin dake a raye a
cikinshi"
wadanda suke ba yara tarihin kafuwar
wannan
kauye" tun xamanin mulkin mallakar
turawar
ingila" kafin a sami yancin kai"
ALLAH ya albarkaci kauyen dan
marke da
manyan manoma na rani da kuma na
damina"
kusan a kowanne yanayi mutum ya
shiga cikin
kauyen da wahala ya sami mutane a
xube suna
xaune" koda yaushe mutane suna
gonaki da kuma
fadamu"
Akwai kuma masu xuwa kamun kifi"
domin kuwa
a xagaye da kauyen dan marke
manyan koguna ne da ba'a taba ganin sun kafe ba atarihin da za'a iya tunawa"
Kasancewar yankin karkarar da
kauyen dan
marke kewaye yake akwai yalwatacciyar
ciyawa a gepen
fadamu rani da damina" shiyasa
fulani suka kafa
rigaye jefi-jefi a kusa da kauyen"
wannan ya sake
taimakawa maxauna yanki yajen
samun isassun
dabbobi da kuma samun takin
gargajiya da arahar nono da man shanu"
.
Duk da wannan albarka da ubangiji
yayiwa yankin
karkarar na samun abubuwan dogaro
da kai"
hakan bai hana samun matasan dake
xaman
kashe wando ba" tun sape har xuwa
dare" naziru yana daya daga cikin irin
wadannan
hatsabiban matasa majiya karfi dake
a kauyen
dan marke" wadanda sau daya idan za'a yi fada
tsakanin fulani" makiyaya da kuma
manoman
kauyen dan marke su Naziru ake
sawa a gaba"
suyi ta ife-ife da makamai a hannu"
domin kuwa
duk cikin samarin dake wannan
kauye babu
wanda ya kama kafar Naziru " wajen
hatsabibanci da kuma son tada
xaune tsaye"
Mahaifinshi malam muntari shine
ladanin dake
kiran sallah a kauyen" sannan kuma
shine na'ibin
babban limamnin dake yankin
karkarar" kowa
yana ganin mutuncinshi badon halin
'ya'yanshi
biyu sun bayar da shi ba"
Malam Muntari shine mahaifin
Naziru da kuma raliya 'yar makaranta" da
Naziru da
kanwarsa raliya sunyi matukar yin
kaurin suna
a wannan gari nasu" Naziru yayi
bakin jini ne
badon komai ba saboda kowa yana
da labarin
baya xuwa gona domin taya
mahaifinshi aiki".
Sannan kuma jifa-jifa na cewa wai ya
fara shan taba" a tarihin kauyen dan marke ba a taba samun wani saurayi da ya taso yasha taba ba sai akan NAZIRU"
.
Yawancin matan garin har gargadin 'ya'yansu
sukeyi idan sun dora masu talla" ko Naziru ya
kirasu zai saya kada su sayar mashi" suce an
hanasu"
Akwai wata mata dake dorawa 'yarta tallar tubani
da manja" wacce Naziru ya kira yarinyar ta ya
sayi kwano biyu" da matar ta sami labari" da
kyar makwabta suka xo suka cece yarinyar"
matar tana ta jibgarta tana cewa"
"kullum idan zata fita saina ja mata kunne" ko
hanya ta biyo taga Naziru tayi sauri ta shige
wani gidan sai ya wuce" amma shine ya kirata
taje har ya sayi tubani ya taba min kwano"
Ance saida matar tayi kwana bakwai tana wanke
kwanonin da tokar makaranta da kuma kasar
masallaci kafin a sake xuba abinci a ciki" saboda
Naziru mai shan taba ya taba kwanonin da
hannunshi"
.
Ita kuma RALIYA an tsaneta ne a garin saboda
tayi shirgegiya amma kuma mahaifinta yaki aurar
da ita" tsararrakinta sun haifi 'ya'ya hudu xuwa
biyar" shiyasa da xarar ta dawo hutun makaranta
matan garin xasuyi ta gulmace-gulmace"
wadansu suna cewa ai anji labarin tana da
wannan ciwon na kanjamau da ake kwasowa a
birni"
wadansu kuma sunce duk wata sai an xubar
mata da cikin shege"
To amma kuma a bangaren malam muntari"
shidai yasan hakika yana da matsala babba a
bangaren danshi Naziru" kuma shidin ma ba'a
xaune yake ba" duk sati sai ya sa an sauke mashi Ashafa" sannan kuma yana da wata bara daya sa
ana rubuta mishi ita kafa saba'in duk karshen
wata yana tsare Naziru yana sha domin a samu
ya daina wannan lalata da ya sawa kanshi" ta
barin suma akai da kuma shaye-shaye da xuwa
bakin rapi suna yin karta shi da lalatattun
abokanshi"
Sannan kuma malam muntari ya sami wani
lakani a wajen wani bafillatani wande ake
barbadawa a tsire aba yaro ya cinye tsiren a
xaune" a cewar bafillatanin komai ibilishin da
yaro ya xama indai aka barbada garin sau biyu"
to an sami sauki har abada" sai ya koma waliyyi"
Malam muntari ya barbada wannan magani a
tsinkayen tsire yafi sau goma koda yaushe ya
kira
danshi Naziru saiya zare mishi idanu yace ya
xauna ya cinye tsiren"
to amma kuma har yanxun babu alamar nadama"
Naziru sai kara gaba yake yi" maimakon yayi dan
dama dama" ko sati biyu ba'a yi ba ya saci wata
tunkiya tun daga lokacin malam muntari ya fara
karaya da lamarin Naziru domin kuwa
hatsabibancin shi ya wuce duk inda ake
tsammani"
To amma kuma a game da raliya yarshi
wannan
sai dai ayi mashi sam barka" domin kuwa bai
taba kamata da wani laifi da zaice mata tir ba" ta
tsare mutuncinta tana karatunta" kafin ta
kammala kuma ta fito da masoyinta ayi mata
aure"
A ka'ida a kowacce safiya idan an tafi gona"
Naziru tare da shakiyan abokansa su SHEGEN
SAMA basu da wani aiki saisu nufi bakin kogin
dake bayan garin su xauna a gindin wani
mangwaro su nada mandula su sha suyi karta"
kamar kullum a karon bayan duk mutane sun tafi
gona" sai Naziru ya hau tsohon babur dinshi
(SUZUKI) wanda ya taba yin gobara ya kone"
idan zai tada babur din saiya xungura shi a guje
sannan sai yayi tsalle ya haye" gashi kuma babur
din bashi da salansa idan ya fara burari sai yaran
kauyen suyi ta koke-koke" wasu kuma suna
shigewa gida a guje" domin kuwa kafin a saba da
babur din a lokacin da Naziru ya fara tadashi a
kauyen mata duk suka bi suka rude suna salati"
sun dauka cewar girgixar kasa ake yi"
NAZIRU ya xungura babur din a guje yayi tsalle
yasa giya" amma kuma a wannan karon baici
sa'a ba" haka yayi ta dama dashi har yakai bakin
kogin" yana sanye da kodadden wandonshi na
sojoji daya fashe a gwiwa" da kuma bakar riga
wacce ta dauki shekara biyu bata ga ruwa ba" in aka dauke ruwan saman da ya jikata bara" Naziru
bazai taba mancewa da wannan rigar ba" domin
kuwa a caca ya ciwota tare da wani takalmi"
Bayan yaje bakin kogin bai iske abokan
shekiyancin shi ba" sai yayi fushi ya gunguro
babur din ya kamo hanyar dawowa gida" yana
cikin gungura babur din" sai kuma wata xuciyar
ta raya mashi cewar ya sake jarraba tayar dashi
me yiyuwa yaci sa'a ta tashi"
Naziru ya ingixa tsohon babur din a guje" sannan
yayi tsalle yahau yasa giya" babur din ya sarke
da ihu" saida tsaunukan garin suka amsa kuwwa"
sannan ya cilla da shi a guje Naziru ya nufi gida
yana murxa babur din"
A daidai lokacin da yake kan tafiya ne kafin
yasha
kwana ya shiga garin" wasu bakin mata tsofaffi
sun biyo ta hanyar xasu nufi wani kauye" suna
tafiya suna labarin jirgin da suka sami labari ya
fado a birnin kano a watan da ya wuce" wanda
ya kone gidaje da mutane bil adadin" sai kuma
sukaji rugugin wani abu ya tunkarosu kamar zai tsaga kasa"
saboda tsananin burari nan da nan tsofaffin
matan suka juya cikin kauyen a guje domin kuwa
sun dauka cewar jirgin ne irin wanda suke jin
labarin ya fado a kauyen a halin yanxu"
Matan suka watsar da kullin kayayyakin su . . . .RALIYA-08
.
Matan suka watsar da kullin kayayyakin su
daya kakkaura ce mai kiba" daya
kuma doguwa ce dakayar take iya tafiya" to amma kuma da
sukaji burarin yana kara matsowa
kusa dasu" nan
da nan suka xage dantse doguwar ta
wuce
kakkaurar tayi mata nisa" ita kuma
kakkaurar
tana biye da ita tana salati" domin
kuwa sun
gama tsinkewa mutuwa ce ta zo
.
Suna cikin gudu suna numfashi sai
suka ci karo
da wasu mata su uku dauke da
tuluna" sun debo
ruwa a wata rijiya" matan suka tsaya
tambayarsu
a tsorace" ganin tsofaffin sun wuce
su a guje
kamar iska suna haki sai matan suka
ajijjiye
tulunansu suka rufawa tsofaffin baya"
wadanda
aka tserewa sunata ihu suna cewa a
jira su"
A dai dai lokacin ne wani dan koli
dake bin
kauyuka da keken shi yana tallar 'yan
kunne da
sarka ya shawo kwana da tsohon
keken shi" ba zato da tsammani sai yaci karo da mata ridi-ridi
su biyar suna cin gudu" dan kolin
yayi iyakar
kokarin shi domin ya tsayar da keken
amma yaki
tsayawa" gashi kuma ya jiyo karar
wani abu
shima kamar jirgin kasa ya biyo
matan" nan da
nan yayi tsalle ya jefar da keken yabi
matan a
baya yana nannade malum-malum
dinshi data dabaibayeshi a kafa
.
Mata biyar da Dan koli suka keto
kauyen
danmarke a guje kamar sunga
mutuwa" wani
mutum da ake cewa tsalha mai jaki"
ya hawo
wani tsohon jakinshi mai shegen
gardama" ganin
mutane suna cin gudu" sai ya kada
kan jakin
domin su koma gida" amma kuma
jakin ya ruga
guje" ya tunkari inda burarin nan ke
tasowa"
wanda ba'a san ko menene ba" ganin
haka sai
yayi tsalle ya sauka daga kan jakin ya
dawo baya
ya rufawa matan baya suka yi cikin
gari raf! Raf!! A guje
Bayan sun kai bakin dandalin garin
ne sai suka ji shiru rugugin ya wuce" tsofaffin biyu suka fara
tsayawa suka dafa bangon wani gida"
suna share zufa" matan dake biye dasu da dan
koli da kuma tsalha mai jaki suka cimmasu"
kakkaurar tsohuwar ta dubi ragowar abokan
tseren tace dasu"
"Sannun mu jama'a barka da arziki
Dan koli yace"
"Lallai Allah ya auna mana arziki
sannunmu"
malam tsalha ashe haka wannan
al'amari yafaru"
Malam tsalha ya mikawa dan kolin
hannu suka gaisa"
ragowar matan uku masu tuluna suka
fara yiwa juna jaje
Matan makeri sannunmu da tsira"
wata a cikinsu tace
"Barka dai matar mai unguwa
sannunku"
"wannan bala'i dame yayi kama a
duniya?"
tsalha mai jaki ya cewa dan koli"
"wai me ya faru ne dan koli ni nayi
tsammanin
harin da akace jaji bush zai kawo
shine suka
jeho mana nakiya anan kauyen" jiya
matata taji
ana fadi a rediyo?
Dan koli ya share zufa yace da
malam tsalha"
"Eh, to nidai na taho naga wadannan
mata suna
gudu" ina jin maganar dai kenan koba
haka akayi ba?
Ya tambayi matan biyar" matan makeri
tace"
muma dai mun debo ruwa ne" muka
ci karo da
wadannan tsofaffi suna gudu" mun
tambayesu ko
lafiya basu ce mana komai ba" shine
muka biyo
bayansu
Dan koli ya bata rai yace"
Zancen banza kenan" kawai kuma
daga ganin
mutane suna gudu sai ku kama yi" to
ku baba me kuke yiwa gudu?"
Doguwar tsohuwar tace"
"mu baki ne muna tafiya ne zamuje
kauyen
kwananduke" daga magaji wando
muke" shine sai
muka ji karar wani abu kamar na
jirgin sama zai
fado" to munji labarin abinda ya faru a
birni kwanan nan shine mukayi ta kanmu"
.
Malam tsalha yayi tsaki yace da
tsofaffin"
"Amma wallahi kun cucemu tsohuwa"
haka kawai
daga kunji karar wani abu sai ku
kama gudu"
Yanzu haka ma babur din yaron can
NAZIRU dan gidan mai kiran sallah kuka ji"
Dan koli yace"
"shine mana!! Kawai kunja mana
tashin hankali
muna gudun banza ni banma san
inda na ajiye keken kayana ba"
Ya wuce gaba yana zage-zage" afusace ya koma
inda ya baro kekenshi" malam tsalha
yabi
bayanshi yana share zufa" yana ta
tsaki domin
kuwa matan sun gama bata mashi rai"
Matar mai unguwa ta shiga gaba suna
ta fada
domin su koma su dauki tulunansu"
"wannan sakarcin ma dame yayi kama
a duniya"
indai lalatar Naziru ne wanene bai
saba dashi ba
a wannan kauyen" haka yake tada
wannan babur
din ya tsorata mana yara" kuma kawai
ku da
girmanku sai ku kama cin gudu?"
Kakkaurar tsohuwar tace a fusace
"to mu ina xamu sani tunda mu baki
ne?" kawai
muna cikin tafiya malam" sai muka ji
abu ya taho
rugu-rugu ba arxiki" ina xamu tsaya
kawai-kawai ya cim mana?
matan suka yi ayari suka koma suna
ta musayar
maganganu" malam tsalha mai jaki
bai waiwayi
inda jakinshi yake ba" da xuwanshi
saiya shige
cikin gida" domin kuwa ranshi ya riga ya baci"
Duk lokacin da ranshi ya baci haka
kawai sai yaji
yana jin gudawa ya shiga cikin gidan
a fusace
yana ta xupa" matanshi suka fara
tambayarshi
abinda ya faru" ko daga kai baiyi ya
kallesu ba"
yayi sauri ya wawuri buta ya fada
bayi" da
shigarshi ya turo kofar ta rufe a
fusace"
.
=====>******^*******<======
.
NAZIRU ya shiga cikin gidansu" yana
gangara
babur dinsa" da shigarshi ya hango
kanwarshi
Raliya ta dawo tana xaune a kasa da
kakarsu tare
naziru ya jingine akwalar babur dinshi" sannan
ya nufi wajen kakarsu da kuma Raliya yana
fara'a "yan makaranta yaushe aka dawo ne?"
Raliya tace dashi
"tun daxun na dawo yaya Naziru" ina ka shiga
ne?"
Naziru yace da ita yana shafa tarin sumarshi"
"Na dan fita nan bayan gari ne" yaya karatun
naku Raliya?"
"kafin tabashi amsa ne kakarsu tace dashi"
"An fita yin sana'ar da aka sabo ko?" ai kai dai
wallahi Naziru har abada baxaka rika jin magana ba"
Naziru yayi saurin canxa hirar domin kuwa
yasan halin kakarsu idan ta fara yi mashi
bambami sai ta wuni bata gaji ba"
"Raliya ina fatan dai a wannan karon kin cika
min alkawarina" tuntuni nasha tuna miki idan xaki
dawo ki sayo mani tabarau irin mai dan fadin
nan" irin na SHEGEN SAMA abokina"
Raliya tayi murmushi"
"Ban mance ba yaya Naziru" tace dashi sannan
takai ganinta inda ta jepar da akwatinta tun
dawowarta anan ta sake shi a tsakar gida"
'ya'yan awakai suna ta hawa kai suna tsalle bata
damu ba" domin kuwa tasan cewar ba wata tsiya
ke a ciki ba" daya wuce tsummokara da littatafan
karatunta" yaunxun nan da xarar ta gama hutawa
dama take so ta amshi kudi a wajen mahaifiyasu
taje ta sawo omo tayi sukola
Raliya ta cewa yayanta Naziru
Yana cikin akwati ka bari sai anjima idan na bude
sai in baka yanxun nan xan tashi" dama in ciro
kayana wanki xanyi"
Naziru ya bata rai yace da ita"
"sauri nake yi tashi ki bani yanxu Raliya" wajen
abokina zan tafi Shegen Sama yana can gida
yana jirana"
kakarsu dake sauraronshi tace"
"kadai xama sangwamemen katon banxa Naziru"
ace kai ba xaka tsinanawa kanwarka komai a
duniya ba" sai dai ita ta samu ta baka kaji kunya kayi girman kwabo"
naziru yayi dariya ya cewa kakarsu"
"In banda abinki kaka menene to don taxo mini
da tsaraba" Daga birni fa take" tinda mu muna
nan a kauye" ai yakamata ace ta danyo mana
siyayyar birni" nima idan aurenta da rufa'i ya
tashi ai dole ne inyi mata
Raliya taji farin ciki ya lullubeta" data ji Naziru
ya ambaci sunan masoyinta Rufa"i da shigowar
ta ta aiki wani yaro domin gidan su domin a
sanar dashi cewar ta dawo" amma kuma taci
rashin sa'a Rufa"i ya tafi gona tunda safe sai ya
dawo " Anjima nan zaizo ya sameta su raba dare
suna hirar yaushe gamo"
Raliya ta tashi cikin tsananin farin ciki domin ta
dauko wa Naziru tabaronshi data sawo mishi a
kano" ta ciro dan makullin akwatin ta kori
awakan dake xaune akai ta daga akwatin tsaye
ta fara kicin kicin budewa" Raliya ta dage tana
dama da akwatin ya budu amma kuma yayi gam
yaki budewa"
wannan abu ya bata mamaki" daxun nan tahi
akwatin ya kara nauyi data sauko a mota" yanxu
kuma gashi ya kulle tayi-tayi ya bude yaki
budewa" anya kuwa wannan akwatin shine nata?
Raliya ta tambayi kanta cikin fushi" Naziru dake
a tsaye yana jiranta ta bude ta ciro mishi
tabaronshi yace da ita"
"kawo mabudin mu gani don Allah" sai kace wani aiki?"
Raliya ta mika mashi mabudin yayi nashi kokarin
amma akwatin yake buduwa" kakarsu dake xaune
tana yagar rama tace"
"to wai dole sai an bude" a hankura mana sai an
huta xuwa anjima" wannan naci har ina?" bana
son kana takurawa yarinyar nan Naziru" kai baka
san ka girma ba wallahi"
Naziru ya hauri akwatin cikin fushi da
gwandolarshi"
"Duk bukulunka saina sai tabarau yau akwati"
yace yana xaro idanuwa" sannan ya dauki
akwatin da hannu daya yace da Raliya"
"Kada ki dama Raliya bari inje dashi wurin
abokina Shegen Sama yana da karfen bude
kwatuna" idan ya bude kwadon sai in dawo miki
dashi ki ciro ki bani"
Raliya tace dashi"
"ba komai yaya Naziru kaje dashi ku bude"
Naziru yayi waje da akwatin kakarsu tace"
"wannan masifar naci naka Allah ya rabamu da
irinshi"
Naziru ya fito daga cikin gidansu" Abokinshi
Shegen Sama wanda suke takadarcinsu tare"
kamar Naziru dashi a gidansu" su biyu ne dama
suka gagari kowa a kauyen danmarke"
to amma kuma har dama-dama Shegen sama
shi ance yana xuwa gona idan ta raya mashi" to
sai dai kuma ko sati daya ba ayi ba daga kawai
mahaifinsh yace ya daina kawo mishi tuwo tunda
bayason xuwa aiki" kishiyar mahaifiyarshi ce keda
aiki" data gama abinci bata sa mishi ba" saida ya
bari babanshi ya fita masallaci ya fada cikin
dakinta" yayi mata dukan tsiya da bel" tsawon
lokacin mahaifinshi yayi yana tsine mashi
albarka"
Naziru ya sami shegen sama a xaune akan
gungume a kofar gidansu yana hamma" shegen
sama gajere mai fadin kirji kamar kofar gareji"
yana da murgujejen kai da kuma faskeken tafin
hannu kamar faranti" yana sanye da kodaddun
kaya irin dan madina" wanda ya zazzare ya koma kamar kyallen tatar koko
Naziru ya kunduma mashi zagi tun kafin ya
karasa wajen shegen sama.
.
ZANSO KUYI HANKURI SHAFIN DA NA SHIGO
YANA DA MATSALA" BANA GANE RUBUTUN"
AMMA SHAFI DAYA NE KAWAI"
.
Ayarin 'yan sandan da suka kamo jarmai suka ci birki a daidai ofishin ACP Aminu jangwarxo"
tsayawarsu keda wuya suka fito dashi nannade
da ankwa a hannayenshi tare da murgujejen
akwatin kudin...RALIYA-09
.
Ayarin 'yan sandan da suka kamo jarmai suka ci birki a daidai ofishin A-C-P AMINU JANGWARZO"
tsayawarsu keda wuya suka fito da shi" nannade da ankwa a hannayenshi tare da murgujejen akwatin kudin" Dan sandan da yake dauke da akwatin sun shashi a tsakiya rike da bindigogi" domin kuwa suna fargabar wata kila yana da layar bata"
Da shigarsu ofishin jangwarzo suka sameshi tare da A-C-P bilya" 'yan sandan suka sara ma tsofaffin sannan babban cikinsu yace
"An gama aiki yallabai gashi nan mun kamoshi a motar haya xai gudu xuwa wani kauye" ga akwatin da ya sato
A-C-P Jangwarzo yayi saurin amshe akwatin a hannunsu" sannan ya daka masu tsawa yace"
"ku daukeshi ku kaishi gidan tuhuma ku kulleshi" kada a bari wani ya kusanci inda yake har xuwa nan da lokacin da xan baku umarni nan gaba"
'Yan sandan suka cakumi jarmai wanda bakinshi ya karkace ya koma gefe daya" yana ta xubar da jini" kamar gilmawar walkiya" nan da nan har sunyi ciki dashi sun bace" tsofaffin 'yan sandan biyu suka kalli juna cikin tsananin murna" sannan suka fice da sauri domin su kaiwa kwamishina ya bude ya basu nasu kason"
Cikin minti uku har sun garxaya a mota sun sami dan masani yana ta kai da kawowa a wani kebantaccen gida na sirri da ya ce su sameshi acan idan sun amso akwatin kudin"
Yana tsaya yana kallonsu suka tunkareshi da akwatin suna fara'a ganin haka saiya shiga cikin wani daki na sirri" tsofaffin 'yan sandan suka bishi ciki suka sameshi har ya xauna akan kujera ya dora hannuwanshi akan teburin dake a gaban kujerar fara'a akan fuskarshi da kuma murnar ganinsu"
"Me kuka tsaya jira tun daxun ina xama jiranku?"
Dan Masani ya tambaye su yana shafa bindigarshi dake a boye a kugunshi domin ya tabbatar tana nan"
sai jangwarxo yace
"mun sami matsala ne a wurin nemanshi" domin kuwa da farko tashar jirgin sama da kuma na kasa muka tura yara su nemoshi" sai daga

Please Login or Register in order to submit comment