Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dauke da dakon
itatuwan duka ya sauke da kyar sannan ya duke
yana kwance igiyar da suka daure itacen"
Dama haka suke yi idan suka fita aiki kowa da
irin matsayin da yake takawa"
Bangis mai sare kofar gida" komai karfin kofa sai ya watsar da ita" a duka daya"
shi kuma bala shine ke daukar itatuwan duka"
musamman tunda rana zaije daji ya saro icen
koyar aduwa" ya tara wuri guda ya dauko"
Sai dare yayi idan sun fita aiki saiya sauke kowa ya zabi nashi" Amma aikin duka tare sukeyi" idan itatuwan sun kare a jikin mutum daya" sai su sake fita tsakar gida kowa ya sake zabo sabon icen su rufarwa wani"
kuma basu damu da mace ba" tun da dai
sha'anin sana'a ya kawo haka" ko mace suka
rufarwa a ka'ida sai itatuwan sun kare a jikinta
bayan sun yi mata lilis" kamar suna fyadin
shinkafa" ko dawa.
.
A wannan karon ma haka sukayi" bayan kowa
yazabi icce daya" ya shake a hannunsa sun bar
ragowar itacen a kasa" sai bangis yaja baya a
fusace" ya ruga a guje yasa kafa ya banke kofar
dakin farko wanda ke kusa da zaure" kofar ta
fashe a lokaci guda" sannan ta karkace tabar jikin ginin ita bata fadi ba" kuma bata tsaya ba"
Bangis yasa hannu ya fizgo kofar kwanon ta fadi kasa" karuwan dake ciki su biyu da kuma dan daudun suka taso a tsorace suna ihu" bangis ya kara shiga ciki da yake babu haske a cikin dakin sun kashe wuta"
Sai yakai hannu jikin bango a kusa da kofar dakin ya lalubo inda makunnin yake" ya kunna wuta haske ya gauraye ko ina a cikin dakin"
jiniya da kuma Idon Gwal suna a makure a jikin
bango daga su sai wasu guntayen shimi na barci masu hade da karamin siket" shi kuma daya gayyar tsiyar yana tsugunne ya makure a gefe daya ya lullube jikinshi da zani yana sanye da gajeren wando"
Da shigar bangis cikin dakin bai tsaya jiran komai ba" sai ya nufi inda karuwan biyu suke" bala ya biyoshi a baya dauke da nashi iccen" shi kuma lado niga" shugaban tafiyarsu" ya tsaya a waje yana gadi" don kada wani a cikin sauran dakunan ya bude ya fita a guje ya tona masu asiri"
Bala da bangis suka fara jibgar idon gwal da
jiniya kowanne idan ya daga nashi iccen sai ya
kure karfinshi" tun na bara waccan da kuma na
badi" wanda baizo ba" sannan su kimawa
kowacce a baya wani lokaci kuma ko ina suka
samu duka kawai suke yi" karuwan suka birkice
suna ihu" kowacce jikinta yayi kala-kala da jini
saboda kayayuwan dake a jikin itatuwan"sai da
Bala yaga jiniya ta sandare zata suma" sannan
ya tsaya fara tambayarta"
"Ina kudi da sarkoki suke?"
Idon gwal ce take da dan sauran rai" ita ce tayi
kokarin nuna musu wata jakarsu karama dake
sagale a jikin bango" ita ma karfin halin tayi
shine domin ta kwaci kanta kada su kashe ta"
amma duk jini ne a goshinta da fuskarta"
Bala yayi saurin zuwa" inda jakar take ya ciro ta
ya zage zip din ya leka ciki" babu wanda yasan
komai a ciki sai shi kadai bangis daya tsaya da duke" shima yana jiran bala
ya ciro jakar" sai ya tambaye shi da ido" bala ya
girgiza kai alamar ya gamsu da abinda ke cikin
jakar!
Bangis ya harari mata biyu dake zube a kasa"
cikin jini suna murkususu" sannan sai suka hada ganinsu wuri guda akan dan daudun wanda duk abinda akeyi yana makure yana rusa kuka" Bil hakki da gaskiya tamkar wani karamin yaro" bala yana rike da jakar a hannun hagu" dauke da katon ice a hannun dama"
Bangis ya rike nashi iccen da hannuwa biyu"
kamar zaiyi faskare" suka tararwa katon
shu'umin dan daudun suna ta jibgarsa baji ba
gani" ya jefar da zanin daga shi sai gajeren
wando fari" kafin kiftawar ido da bismilla duk sun farfasa masa fata" jini yana zuba" kamar ruwan leda" a wannan karon bangis ya tambayeshi
"Ina kudinka suke?"
Dan daudun yace a tsorace yana magiya"
"kudina suna wajen yayata" kuje ku tambayeta
Ita ke da sarkoki masu tsada" kuyi mani rai babu kudi a wajena" bala yayi mamakin yadda muryarshi ta dawo ta namiji garas" kamar bai taba rangwada ba" ya
dubi fuskarshi yaga tasha shegen kalangu da
kuma jan baki da kwalli radau"
Idanunshi har sun rabu dashi" sai ya sake daga
iccen ya maka mashi akai tas!! Icen ya karye yayi tsalle ya hadu da rufin dakin" dan daudun ya fasa kururuwa ya dafe kanshi" sannan ya kife kasa yana haure-hauren mutuwa" jini yana tsiyaya agoshin shi" bangis ya fashe da dariya yana cewa bala
Kada ka bata masa kwalliya mana" ko kana so
ne ta rage tsada wajen samarinta?"
Bala ya jefar da ragowar guntun iccen daya karye yace da bangis a fusace"
"Ai wannan dama kashe shi mukayi" ko banza
mun rage mugun iri"
suka fice waje suna dariya" da zuwan su inda
lado yake tsaye suka mika mashi jakar ya amsa araine" kamar abin wasa" tun kafin yayi magana bangis yace dashi
"Kada ka damu oga sunce mu tambayi hajiyarsu za'a samu alheri sosai a wajenta kudin suna cikin dakinta"
Lado yace dashi"
"to me kake jira ba aikinka bane..?
Bangis ya dauko gatarinshi na fasa kofa ya daga shi" sannan ya gabzawa kofar ta yanke ya fadi kasa"
to amma kuma ga mamakinsu maimakon su sami Hajiya tabawa a tsaye tana jiran tsammanin bala'in dake zuwa gareta" sai suka sameta asume a kasa ko numfashi bata yi"
Abinda basu sani ba" shine tun lokacin da ta
farka barci a tsorace taji burarin yaranta 'yan
fashi suna casa su a daki"
Kafin suzo kan nata dakin" nan take hawan jininta ya taso" bata san lokacin da ta silale kasa ta fadi ba
Me yiyuwa tafiyar kenan.....RALIYA-23
.
Batasan lokacin da ta silale kasa ta fadi ba"
me yiwuwa tafiyar kenan" watakila kuma ta sake farfadowa to amma wannan matsalarta ce! Barayi uku suka shiga cikin dakin bata kashe wuta ba" bangis ba yason yawan surutu idan ana aiki yace
Ita wannan rasuwa ma tayi" tun kafin tajira mu
muzo mu kashe ta da kanmu...?"
Lado ya harare ta a fusace tana kwance shirim
kamar giwa a kasa fuskarta ta cunkushe tayi
murtuk yace dasu
taci sa'a da ta mutu tun kafin tasha wahala"
domin ya fiye mata sauki"
Duk da haka saida ya sa kafa ya take hannunta
dake malale a gefe guda" hannun ya bayar da
wani sauti karass!!
Alamar karyewar kashi" yasan cewar idan ma
likimo tayi to dole ne ta farko" ganin ko motsi
bata yi ba" sai ya basu umarni suka fara birkice
kayan dakin" A cikin 'yan tsirarun mintoci suka kwaso duk wata tsohuwar ajiya da matar tayi" kudinta da sarkokinta masu daraja" duk sunzo hannu" Ganin cewar lokaci yana kara nisa" sai Lado yaduba agogo yace
"mu fita hakan nan tunda mun sami abinda muke so"
ya zuba tarkacen da suka kwasa a dakin hajiya
tabawa a cikin jakar da suka dauko a dakin su
jiniya da idon gwal" suka fice har zasu kama
gabansu sai bala ya nuna dakin da bakuwa
Asabe take"
"bamu caje wannan dakin ba"
Bangis ya kalli dakin a kulle" yace dasu"
ba sauran wata tsiya da zamu samu iyakar yaranta kenan su uku kuma duk mun caje su"
Bala yace"
"Duk da haka ya kamata mu karashe aikin mu
tunda dai munzo daki na karshe" ko babu komai a ciki ya kamata mu tabbatar kafin mu tafi" Lado ya sake duba agogo" sannan yace da su cikin kosawa"
"lokaci yayi nisa" in zaku shiga ku bude mana
menene kuma na wani tsayawa jayayya"
Bangis yasa kafa ya banki kofar a fusace yana
kunkuni" domin kuwa ya gaji kuma tsammaninsa
baza'a sami wani abu ba" tunda dai ba sauran
wani mutum wanda bai caje ba" baya so ya balle kofa ba'a samu komai a ciki ba"
Balle kofar keda wuya sai Asabe ta kwatsama ihu iyakar karfinta" dama tana tsaye tana sauraren hirar da suke yi ta jikin kofar" ihun da tayi shiyafi basu haushi" domin kuwa sun tsani kwarmato da tonon asiri" idan suna aiki" nan da nan lado yayi sauri yaje inda ragowar itacen suke ya zabo nashi
Bala da ya karya nashi tuni shima yaje ya kara
daya" suka wuce bangis wanda ya dawo baya"
domin dauko nashi sabon icen"
Barayin uku suka taru waje daya" suka sa Asabe a tsakiya suka fara casa ta" daga waje wadanda ke a cikin gidajensu suna jiwo karar duka tim!! Tim!!! Kamar sun sami katifar ciyawa 'yar sale"
tunanin dake a zuciyar Asabe a lokacin da barayin ke farfasa mata jiki" shine akwatin kudinta dake tsakar dakin" ta kai hannu domin ta sake dafa akwatin kafin ta mutu"
Ganin haka sai kartin uku suka tsaya cikin
mamaki suna kallonta" domin kuwa sun san
cewar indai ba wani abin arziki ke cikin akwatin
ba" to zaiyi wahala ace ana yiwa mutum caji
yakai hannu yana kokarin ya taba wani abu"
Asabe ta yunkura duk da karairayewar da jikinta yayi" domin kuwa a cikin minti daya da sukayi da fara lallasata" sun karya mata cinyoyi da kuma hakarkari guda shida" sai kuma lado wanda ya karya mata hanci" a wani wawan duka na farko da ya fara kai mata a fuska"
A haka kamar wacce suka ciro daga hadarin jirgin sama" ta ko'ina a jikinta sai barar da jini yake yi ta dafe akwatin" sannan ta fashe da kukan nadama"
A lokaci guda ta tuno da mijinta balarabe" Adalin mutum mai hankuri" wanda ke gudun haram da duk wani kyale-kyalen duniya" hakika balarabe yayi gaskiya da yasha sanar da ita cewar Samun duniya ba wani abin dogoro bane" saboda koka samu sauran bil'adama bazasu taba barinka ka huta hankalinka ya kwanta ba" ga barayi a ko'ina ga 'yan damfara" ga talakawa 'yan maula dake zagin wanda baya alheri" ga ciwo da matsalolin rayuwa"
Babu shakka samun lahira da kuma guzurin alheri shine mafita ga dan adam!!
Asabe ta janye hannunta daga kan akwatin a
daidai lokacin ne kuma ranta ya janye da sauri
yabar jikinta" ta tarwatse tayi dai dai a gaban
barayin kowanne dauke da iccen aiki" suna ta
numfashi domin kuwa sun sha wahalar aikin duka a wajen Asabe fiye da sauran mutanen gidan" Barayin suka kalli juna cikin kaduwa" domin kuwa a iya shekarun da suka yi suna wannan muguwar sana'a basu taba ganin wani dan adam ko mace ko namiji wanda yayi irin wannan mutuwa mai cike da ban tausayi ba" irin na Asabe"
kukan da tayi a daidai lokacin da zata mutu da
kuma wani tunani da suka ga tayi shiru tana yi"
shiyafi komai sanyaya jikin su"
"menene a cikin akwatin wanda har ya sata
nadamar rabuwa dashi?"
Lado wanda ya fisu jan hali da karfin zuciya"
shiya fara dukawa ya kama akwatin nan da nan
ya bude" sannan ya wangame murfin"
Barayin uku suka ja baya a tsorace a lokacin da
suka ci karo da sababbin Dalolin Amurka
wadanda ke ta walwali a daure bandir bandir sai kace gilasai a cikin ruwa.
.
Sautin harbe-harben dindigogin dake amsa
kuwwa a cikin daren shiya farfado da barayin
daga suman tsayen da sukayi" nan da nan suka
dawo hayyacinsu harbin dake tasowa a waje
shiya ganar dasu cewar 'yan sanda aka yiwa
waya suka zo" gashi kuma sunyi sakaci 'yan
sanda sun ritsa su a cikin gidan"
to amma kuma ba harbe-harben yafi damunsu
ba" wadannan makudan kudi dake cike da akwati sune abin damuwar" domin abin yazo musu abazata" suda suka zo neman 'yan sarkoki da kuma 'yan kudin da mata ke ajiyewa sai gashi sa'a ta hau kai" wannan ma ya wuce sa'a ya zama fatahi"
domin wadannan kudi sunyi yawa ko gwamnati
ta same su" sun isheta kasafin wani bangare na aikin raya kasa dazai taimaki miliyoyin mutane" sai gashi mutum uku sun tsince su ba zato" ba tsammani"
Suka dubi gawar matar dake a kwance a
gabansu" basu ga laifinta ba a halin yanzu da
take kokarin sake taba akwatin kafin ta mutu"
tana kuka domin kuwa ita kadai tasan abinda ke ciki" menene abin yi yanzun ?
"A lokaci guda suka kai hannu kowa yana kokarin ya rufe akwatin ya dauka" to amma kuma Lado yafi su zalama kuma tunda shine madugun tafiyar" dole suka bar mishi ya rufe akwatin ya sungumeshi ya kankame suka kalli juna" kamar suna tsammanin zai tashi da kudin sama"
"Aka sake harba bindiga a waje" sai a lokacin
suka tuna cewar akwai fa 'yan sanda a waje suna jiran fitowarsu
Bala ya fara bude baki yayi magana tun ganin
abin al'ajabi amma sauran sai zufa (gumi) suke
yi suna ajiyar zuciya"
"Akwai 'yan sanda a waje suna jiranmu" ta wacce hanya zamu bi mu gudu?"
Lado yace da su
"kowa yayi kokarin yasha da kafarsa" ni dai
nasan cewar ko ruwan harsashi zasu yi mani saina sha da wannan akwatin" don haka wanda
yakai labari ya sameni a gida mu raba kudin" idan kuna da sauran shan ruwa a gaba" idan kuma kwananku ya kare kunga shinkenan bama bukatar kason kudi" sun zama nawa ni kadai"
Basu san abinda Lado ya dogara dashi ba" da yafadi haka" domin kuwa har wani murmushin
yadda dakai yake yi" to koma dai wacce hanya
Zaibi ya gudu" suma zasu bi duk da basu dogara da komai ba"
su dukansu kowanne yana da bindiga" to amma kuma idan zasu fito aikin dare basu cika daukar bindiga ba" kuma musamman idan mace zasu kaiwa ziyara"
sau da yawa aiki da bindiga yakan zo da
matsaloli" domin kuwa wata mace idan aka nuna mata bindiga tsoro da rudewa yakan sa ta
dabirce ta kasa ciro kudi ko sarka ta bayar"
kuma ba lallai bane a san inda ta boye su" wata
kuma da taji an harba bindigar zata suma ko
bango aka harba tun mafin ma azo kanta" kuma idan bata a cikin hayyacinta" babu yadda za'ayi ta ciro Alheri ta bayar"
Akwai lokutan da basu san suyi kisa a wajen aiki" shiyasa basu dauko bindiga akai-akai" sun fi jin dadin aiki da danyen icce mai kaya" duk wanda suka sashi a tsakiya suka fara caji" dole ne ya fadi inda kudi suke" kuma ba maganar kisa" indai ba kwanan mutum ya kare ba" zasu bar mutum da ranshi" amma kuma tsamin jiki wannan kuma ba'a magana"
shiyasa suke fargabar fita su doshi jami'an tsoro basu da makami a hannunsu" to amma kuma da suka ga Lado yayi waje bai damu ba" dauke da akwatin kudin sai suka bi bayanshi babu wanda yake waiwaiyar karamar jakar da suka amsa awajen karuwan" suka barta a yashe a tsakiyar
gidan suka yi waje da gudu"
A daidai lokacin ne sukaji an sake yin harbi sau
daya a waje" suka bi ta kofar gidan suka fadi kasa" suna
rarrafa a lokacin da suka fita" sunyi baifi taku
biyar ba sai wani harsashin bindiga ya fado a
cikinsu tare da tartsatsin wuta" nan da nan suka tarwatse kowa ya kama nashi wajen"
"Yan sanda dake a boye a jikin bangon
makwabtan Hajiya tabawa suka firfito da gudu
suka bi barayin uku"
Ganin sun warwartsu kowa yabi hanyarshi sai
'yan sanda biyu suka bi bangis" 'yan sanda uku
suka bi bala" daya kuma yabi lado"
'yan sandan dake biye da bangis suka fara daka mashi tsawa" sai wani ya sakar mashi wuta akafa" kafin ya fadi ne kuma sai wani mara hakuri a cikin 'yan sandan ya saki tashi bindigar ta sami bangis a fankacecen bayan shi" harsashin ya huda shi ya fita da gudu yaje can gaba ya sami wata falwaya a bakin hanya ya fasata ya shiga ciki" bangis yayi koli-koli ya fado kasa" A lokacin babu wani abu dake dauke da sauran rai ajikinshi"
"yan sandan dake biye da bala suma sun
cimmashi" amma kuma ganin yaki tsayawa kuma yana tayi masu yawo da hankali a cikin wani lungu" sai suka ji haushi suka sakar mashi harsasan bindigogin dake hannunsu"
A lokaci guda kuma suka same shi" harsashi na daya ya sameshi a kafada" harsashi na biyu ya same shi a kokon kai" harsashi na uku yabi ta jikin wuyanshi yayi awon gaba da wata jijiya suka kara gaba tare"
Gawar bala ta juya sau biyu ta fada cikin wata
katuwar kwata" a lokacin da 'yan sandan suka zo har ta kusa nutsewa"
Dan sanda dake biye da Lado kuma...........RALIYA-24
.
Dan Sandan dake biye da lado sabon shiga ne
bai kware ba" kuma bai dade da fara aiki ba"
dakyar aka matsa mashi ya biyo tawagar jami'an tsaron da zasu zo aikin kama barayin" don haka a lokacin tsoro yake bin lado yana jin tsoro kada lado ya juyo ya harbeshi"
Dan sandan wani saurayi ne dogo mara jiki"
watanshi biyu da fara aiki" kuma yayi alkawarin
da ya cika shekara daya zaiyi murabus" ya koma makaranta dama kudin shiga jami'a yake nema shiyasa ya gwammace ya nemi aikin dan sanda don haka yayi alkawarin bazai taba sa kan shi cikin hadari a kashe shi a banza ba"
Da gangan yabar lado yayi mishi nisa" da yaga
ya bace ya daina hangoshi" sai ya dawo baya"
yana numfashi dakyar haka ya koma ya sami
ragowar jami'an tsaron su bakwai duk da wani
sajan madugun tafiyar"
ya sharara masu karyar" fada sukayi hannu da
hannu shida barayon da yabi" kuma har ya buge barawon zaisa mashi ankwa ya kamo shi" sai wani a cikin barayin ya biyo ta baya ya kada mishi gindin bindiga akai" da suka ga ya fadi sai suka barshi" daga baya ya taso juwa na dibarshi" dakyar ya iya dawowa".
Sauran 'yan sandan sukayi tayi mashi godiya da jinjina" domin kuwa shi ma yayi iya bakin kokarinsa" a lokacin tuni lado niga yakai gida" kuma harya shiga dakin shi ya fara yunkurin adana kudin shi Dala miliyan hamsin
.
======>++++++++++<=======
.
Alhaji Hashimu " fitaccen manomi ne a garin
kwanar tsamiya" sau da yawa duk lokacin da
Za'a fadi sunanshi anfi hadawa da kirarin da akeyi mashi wato "MAI Abinci Har Bayan Rai dole ne mutane su rika yi mashi wannan kirarin" domin kuwa ance duk shekara yakan noma hatsi buhu dubu takwas da dari biyar"
wata shekarar kuma idan damina tayi albarka
sosai ance har dubu goma yana cikashewa" don haka babu mamaki don ance mashi "Mai Abinci Har bayan Rai domin kuwa ansan cewar indai abinci yake nema" to bai isa yaga bayan buhunan hatsi dubu takwas ba" in da ba mutanen jihar su zai rika ciyarwa ba"
Alhaji Hashimu yana da 'ya'ya majiya karfi" kuma mafi yawancinsu mazane lafiyayyu" a haka sun kai guda ashirin da shida" domin kuwa matan shi hudu" kuma biyu da suka gama haihuwa basu fasa kwatanniya ba" saida kowacce ta dire 'ya'ya goma sha uku a dakinta" kamar suna gasa tara maza hudu mata" su kuma sauran matan biyu wato amare daya tana da 'ya'ya bakwai biyar maxza mata biyu" daya kuma tana da guda biyar maza" biyu mata uku
Wadannan 'ya'ya basu taba tsorata wannan
tsohon manomi ba" domin kuwa kowacce safiya sai an cika wani karamin diro da tuwo" da kuma wato gabjejiyar tukunyar miya" wacce matan shi ke bashi labari idan suna so ya karo kudin magi cewar guga uku tukunyar keci" kuma kullum sai an cika ta fal har baki indai ana so miyar ta ishi kowa da safe
Da rana kuma da yake ana kaiwa 'yan gona
abinci Alhaji Hashimu yafi so a rika yin dambu
akai akai" domin yafi auki" shima dambun sai ancika diro duk da wanda za'a diba a kaiwa manyan 'ya'yanshi dake kaiwa rana fadowa a gona"
Amma kuma a yadda matan shi ke korafi wani
lokacin sunce ko dambun tiya shida akayi Dakyar suke samun sa'a yabasu kudin mai rabin kwalba daya a zuba"
Idan kuma bai ga dama ba" sai a dauki kwanaki
ana abinci babu mai a ciki" hakan an kirga adadin 'ya'yanshi suke rububi suna ci don maganin yunwa"
Babu abinda Alhaji Hashimu yafi so a duniya irin yaga yayi wa 'ya'yansa maza aure" tun suna
shekara sha bakwai a duniya" wani lokaci har
alfahari yake yiwa mutanen yankin cewar" yafi
duk wani mai kudi nunawa yara gatanci" domin
kuwa idan yaro yana dagewa aiki a gona yana
sawa kartin yayyenshi yana wuce su" to dole ne ashekarar ya bashi izni yaje ya nemo aure a kara mishi ta biyu" kota uku" wasu sunce yana da wani matashin saurayi dan shekara ashirin da biyu wanda ke da mata hudu duk yara masu jini ajika. Babu abinda Alhaji Hashimu ya tsana a duniya irin karatun boko" domin kuwa yasha fadawa 'ya'yanshi idan suna aiki a gona cewar da wani ya guji aikin gona ya koma boko" to gara su mutu kowa ya huta"
"boko karyar banza ce yara" ku rabu da wannan
hanyar ku koma gona itace rufin asirin ku a
duniya" wannan shine abinda wannan manomi yayi imani dashi"
A haka 'ya'yanshi da jikokinshi suka taso ba ilmin addini" babu na zamani" idan abokanshi masu banbancin ra'ayi irin nashi suka bashi shawara ya rika mayar da hankali wajen ilmin 'ya'yanshi sai ya kira 'ya'yan yace idan dare yayi su rika daukar alluna suna zuwa wajen wani malami dake da almajirai a kusa da gidanshi"
Domin kuwa daga safe har yamma lokacin gona ne" yana ganin asara ce mutum mai lafiya a gida yana karance karance ga aiki can a gona ba iyaka"
Su kuma 'ya'yan basa tsayawa yin wani karatu
da daddare" suna gama cin abinci zasu bazama gidajen bidiyon dake a kauyen"
Alhaji Hashimu bai damu da haka ba domin kuwa shi a ganin shi indai namiji zai auri mata hudu" kuma indai zai iya zuwa gona tunda asuba ya dukufa aiki saidai a bishi can da abinci"
Kuma ace bazai dawo ba sai rana ta fadi" to
menene matsalar ai rayuwa tayi kyau" mutum
ya wuce gori indai ba zana karya za'ayi ba"
Sannu a hankali zamani yaci gaba da tafiya" sai
kuma aka fara samun 'yan tawaye a cikin
'ya'yanshi da wadanda ke so su shiga
makarantar boko" da kuma wadanda basu son
Zuwa gona" masu son suyi karatun sun dan fara gane dadin ilmi ne a dalilin wani saurayin da ya bude ajin yaki da jahilci na manya a kauyen duk sati kowanne mutum yana bada naira goma ladan aji"
Ba wani nisa akayi da karatun ba" kawai bakake
ya koya musu hadawa" duk wanda ya iya rubuta sunanshi da kuma sunan garinsu" kuma duk wanda ya iya karanta sunan fim a jikin kwalin kaset din da ake kafewa a gidan bidiyo" sai ya kama murna da tsalle"
Nan da nan 'ya'yan manomin hudu suka dinka
kayan makaranta suka shigar da kansu firamaren dake kuyen" basu damu da girman da sukayi acikin yara ba" domin kuwa karatu suke nema ido rufe"
A ranar da aka je gona ba tare da su ba" sai da
Alhaji Hashimu yabi kowannensu da gora zai
buge da kyar mutane suka rike shi suna bashi
hankuri"
Su kuma bangaren wadanda basu son zuwa
gonar sune irin su Ladoga Niga " da kuma wasu yayyenshi biyu" su kuma abokai ke zuga su"
suna nuna musu cewar ya za'ayi babansu yana
da kudi ga gonaki da motoci" ga gidajen da ya
gina lafiyayyu ana haya a kauyen" kuma su rika
wahalar zuwa gona?"
Don haka sai suka zama 'yan tawaye sai dai su
ci tuwo da safe" suyi kwanciyarsu suna jin wakar fina finan Hausa" a rikoda wasu kuma suna wasan karta da kuma kokuwa da abokai.
Da Alhaji Hashimu yayi tarkonsu bai sami sa.ar
kama ko yaro daya a cikinsu ba" sai ya bada
doka a gidanshi cewar duk wacce ta kara basu abinci a bakin aurenta" daga baya da ya sami
labarin kowacce idan uwarshi ke da aiki taba
bashi abinci a boye" sai manomin yasa wata
ranar Juma'a da safe ya gayyaci" 'yan uwa da
abokan arziki aka daka gumbar sadaka da kuma koko da waina da suga" ya tsinewa 'ya'yan baki dayansu"
tsinuwar da yayi musu ai itace ta bisu" domin
kuwa ba' a jima ba Kungiyar su Lado wadanda
basa zuwa gona suka fara shaye shaye da daukar kayan mutane" da kuma miyagun dabi'u na tir da Allah wadai kafin wani lokaci duk suka kori matansu na ladan noma.
Ana kan haka kuma a wata ranar lahadi da yamma Alhaji Hashimu mai Abinci Har bayan
Rai yaje gona da yammaci" ko sallar la'asar
baiyi ba" yana can har dare yayi" ba magriba ba
isha'i yana faman kaftun inda zai dasa wani irin
rake" yana cikin aikin kenan farsin wata na
dibarshi da haske" bai san lokacin da ya dora
kafarshi a jikin wutsiyar wani bakin maciji ba"
wanda ya fito neman abincin dare"
macijin ya juyo da kanshi a fusace ya kaftawa
Alhaji Hashimu sara sau biyu a jere" sannan ya
sulale a guje bayan ya ga tsohon ya fasa
kururuwa ya dafe kafarshi yana dingishi zuwa
inda ya ajiya wani tsohon babur dinshi
(Kawasaki) bai isa wajen babur din ba" ya fadi
kasa kuma bai sake tashi ba daga nan
Sai da safiya tayi da mutane suka fara
sammakon zuwa gonaki sannan aka ganshi a
bakin hanya kiyasai sun cika bakin shi da hancinshi" tuni ya dade da zuwa garin da ba'a dawowa Lokacin da 'ya'yanshi da matanshi suka gama 'yan koke koken al'ada bayan anje anyi jana'idar shi an dawo sai kuma suka fara cuku-cukun lissafin buhunan dake ajiye" domin kada wani yaje ya dauka ba'a sani ba"
A satin da suka fara rigima akan dukiyar da ya
bari" su Lado sune a gaba wajen tayar da jijiyar
wuya suna zage-zage"
kwana goma bayan mutuwarshi aka gaggauta
aka raba gado" babu wanda ya sake komawa
takan wani

Please Login or Register in order to submit comment