Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baya muka sami cikakken bayanin an ganshi ya hau wata mota ta haya da akwatin xai nufi wani kauye ya boye acan" kafin yara subi motar yayi nisa" amma an samu sa'a sunxo mana dashi yana can gidan tuhuma munce su boyeshi sai sunji daga garemu" Ga akwatin kudin munzo dashi
Suka ajiye akwatin a gaban kwamishina Dan masani" sannan suka bushe a tsaye suna jiran umarni daga wurinshi" da farko yaso nan take ya ciro bindigar ya gama dasu" to amma kuma saiya canxa shawara" ya kamata ya bude akwatin domin ya dauke hankalinsu" idan suka mayar da hankalinsu wajen kallon kudin sai ya harbesu a tsanake"
Dan Masani ya ciro wani siririn mabudi a aljihunshi ya saka a cikin kwadon akwatin ya dade yana mirxawa" xuwa can sai kwadon ya bude" kwamishina yayi murmushin farin ciki tun kafin yasa hannu ya bude murfin yaga abinda yake ciki" ya dubi 'yan sandan dake a tsaye a gabanshi suna ta zufa yace dasu"
"to ina fatan dai kowa a cikinku ya gama tunanin abubuwan da xaiyi da wadannan kudi" domin kuwa da xarar mun kammala rabasu" xamuyi ritaya" sai kowa ya nemi kwakkwaran kasuwanci ya fara" nidai dama na gama nawa tunanin kasar ingila zan koma da zama" ban sani ba ko kuma kun kammala taku shawarar"
A-C-P bilya yace dashi"
"mu dukanmu yallabai mun gama shirya inda zamu nufa" samun kudin dama ai yafi sarrafasu wahala"
suka tuntsire da dariya a lokaci guda"
.
Kwamishina Danmasani yayi dariyar mugunta" sannan ya bude murfin akwatin" manyan 'yan sandan uku suka ja da baya a tsorace cikin tsananin rudani" a yayin da suka ci karo da abinda ke cunkushe a cikin akwatin" wasu jibgin kaya ne an kimshesu suna ta faman tsami" da kuma littafan karatu da takalma" a kusa da wani kallabi wani katin shaida ne na jami'a wanda ke dauke da hoton kyakkyawar budurwa tana ta fara'a a gefen hoton an rubuta sunanta da manyan baki RALIYA
.
=======>*****^*****<======
.
Naziru ya farfado daga suman tsayen" yayi sauri ya rupe murfin akwatin domin kada wani yaxo wucewa ya hango makudan kudin dake a ciki" Shegen sama yayi ajiyar xuciya ya tambaya"
"A ina ka samo wannan akwatin naziru?" A ina ka samo wadannan kudi haka...?"
Naziru ya daga kai ya dubeshi cikin tsananin firgici yace dashi"
"Wallahi nima wurin Raliya kanwata na amsoshi ita ta bani da hannunta tace inxo in bude mata" ina kyautata xaton ita kanta bata san abinda ke cikin akwatin ba"
Shegen Sama yayi murmushin farin ciki yacewa Naziru"
"Allah ne ya bamu wannan makudan kudi Naziru" domin kuwa babu wanda yasan daga ina suke" Abinda yafi kawai shine mu rabasu ni da kai kowa ya gudu yabar garin" muje can wata duniya mu boye ba wanda zai sake jin labarinmu har abada"
Naziru ya harareshi sannan yace
"Baka da hankali Shegen Sama kana tsammanin akwai rabonka a cikin wadannan kudin?" to wannan kudi nawa ne ni da kanwata" sai naga dama in dauko wani abu a ciki in dan tsakura maka domin kuwa ka riga ka gani"
.
Shegen Sama ya hade fuska yace da Naziru"
"kai ma kasan cewar wannan bazai taba yiwuwa ba" dole ne mu raba wannan kudin mu biyu" in ba haka ba daga nan zan hau keke inje in sanarwa 'yan sanda acan gari suzo su amshi kudin da hannunsu"
Naziru ya kurawa shegen sama idanu cikin tsananin kulewa" ya dade da sanin halinshi na rashin sabo" akan dan abu kankani zai iya yiwa koda uwarshi rashin mutunci ne" kuma Naziru ya tabbatar idan har bai yarda sun raba kudin ba" to ko shakka babu shima yayi asararsu" domin kuwa kai tsaye shegen sama zai wuce zuwa wurin 'yan sanda
Naziru yace dashi "to naji zamu raba kudin" amma uku zamu raba duk da kanwata Raliya kowa ya dauki kaso dai-dai"
Shegen Sama ya sake murtuke fuskarshi" duk yayi sharkaf da zufa kamar kuturu yace da Naziru"
"Bazan taba amincewa ka ha'inceni ba Naziru" domin kuwa ba yau ka fara yi min irin wannan hadamar ba" kudi mu biyu muka tsince su ni da kai" kuma mu biyu xamu rabasu" idan baka amince ba" sai dai kowa ya hakura akaiwa 'yan sanda su raba
Naziru ya kidime yana durkushe ya dafa akwatin kudin da hannunshi" hakika shegen sama ba abokin amana bane" domin kuwa irin wannan ta taba faruwa a tsakaninsu" a lokacin da suka shiga gidan fulani dake a bayan gari suka sato agwagi biyar suka zuba a cikin buhu" Naziru ya barwa shegen sama agwagin kafin jama'a su tafi gona su tafi dasu gari su sayar a kasuwa"
Lokacin da Naziru ya biyo ta gidansu shegen sama" tuni har yakai gari ya sayar da agwagin" haka sukayi ta rigima akan kudin har yanzu bai gama biyanshi nashi kason ba"
Don haka a wannan karon Naziru yasan cewar koda ace amincewa yayi su raba kudin biyu da shegen sama" dole ne saiya ha'inceshi" saboda tsabar hadama" don haka ya xama dole yayi kokari yayi maganin shegen sama" a wannan karon
Naziru yace dashi "Naji na amince xamu raba kudin mu biyu" to amma bazai yiwu mu raba wadannan kudin yanxu ba" saidai mu boye su xuwa nan da kwana biyu idan babu wani abu da ya faru" saimu ciro abinmu sun xama namu"
shegen sama ya xaro idanu cikin rashin yarda" yace da Naziru"
"A ina xamu boye wadannan makudan kudi?"
Naziru yace
"muje can fadamarmu mana mu boye su" mu gina rami mu binne akwatin bayan komai ya lafa saimu tono abinmu mu raba"
Shegen Sama yayi shiru cikin xargi" xuwa can yace" zan amince muyi hakan" amma kai ma ka amince idan muka binne wadannan kudin to baxan yarda ka matsa daga inda nake ba" sai dai ka dawo nan dakina mu rika kwana tare" ko bayi xaka shiga sai dai mu shiga tare" domin nasan ha'incinka Naziru so kake yi ka ha'inceni ban yarda dakai ba"
Naziru yace dashi
"Na amince" zomu tafi bakin rafi mu binne akwatin nan shegen sama" domin kuwa idan tsautsayi ya ratsa sai kaga wani shegen ya karu mun zama mu uku
shekiyan samarin biyu suka fito daga cikin zauren Naziru yana rungume da akwatin a hannunshi" shegen sama yana binshi a baya" suna tafiya zugum-zugum sai kace zasuje jana'iza bayan sunje bakin fadamar ne" inda ke cunkushe da shuke shuke" dangin kabewa da kuma tumatir" wani bangaren kuma gonakin rake ne da kuma kubewa 'yar damina"
Naziru ya nuna gindin wata bishiyar dorawa dake a saman tudu kafin a gangara cikin fadamun a nufi bakin rafi
"A gindin bishiyar can ya kamata mu boye kudin nan" ya cewa shegen sama yana nan cikin zargi ko fara'a baya yi" ya girgixa kai bai cewa Naziru komai ba" yana ta kaffa-kaffa dashi domin kada ya tsere da akwatin yabar shi" xuwa can sai suka samo magirbi a cikin fadamar tumatirin wadanda masu aiki suke ajiyewa kafin su dawo washegari
Naziru ya mikawa shegen sama daya ya ajiye akwatin a gefe daya" shima ya dauki magirni daya" nan da nan suka fara gina rami sam-Sam!! Kamar suna gina kabari" bayan sunyi nisa da aiki" ramin yayi fadi sai suka dawo suna haka cikin ramin daya bayan daya" idan wanna ya gina ya gaji" sai ya fito ya bar dayan shima ya gina" a haka har suka kammala gina dogon ramin"
Naziru ya dauki akwatin ya saka a ciki yabar shi a tsaye" suka sa hannu suka tura kasar ta cike ramin" sannu a hankali suka rufe saman akwatin suka haye saman ramin suna tattakawa domin wurin ya saje da sauran kasar fadamar"
Bayan sun kammala ne sai Naziru ya kwashe magirban ya rike daya a kowanne hannunshi" ya daga kanshi sama a tsorace ya cewa shegen sama"
"waccan jirgin menene"
shegen sama" anya kuwa bamu suka biyo ba?"
Shegen sama ya daga kanshi a tsorace ya kalli sama" yana kokarin ganin jirgin da Naziru ke nuna mashi" ba xato da tsammani sai yaji wani abu mai kama da guduma ya tsaga mashi kokon kai tas!!
Shegen sama yayi kururuwa sannan ya zube a kasa yana kokarin ya dafe kanshi ne" sai naziru ya sake daga magirbin ya dankara mashi a kokon kai kan shegen sama ya sake tarwatsewa" idanuwanshi suka kakkafe.........
.
LAHIRA MOST GO
SHEGEN SAMA KUMA SAI MUN TAHO BARZAHURALIYA-10
.
Shegen Sama yayi kururwa sannan ya zube a kasa yana kokarin ya dafe kanshi ne" sai naziru ya sake daga magirbin ya dankara mashi a kokon kai" kan shegen sama ya sake tarwatsewa" idanuwanshi suka kakkafe" nan take ya birkice ko motsi bai sake yi ba"
naziru ya tattara magirban ya mayar dasu inda ya daukosu sannan ya dawo inda gawar shegen sama take" yasa hannu dakyar ya ciccibeshi ya saba a kafadarshi jini yana tsiyaya" daga kanshi kamar an huda ledar ruwan sanyi"
Ya daukeshi yaraf-yaraf kamar mushen rakumi" ya nufi bakin kogin inda ba kasafai mutane ke zuwa ba saida yamma" Da isarshi ya iske fararen belbelu sunyi sansani a gefen katafaren ruwan suna ta tsattsagar kwari da kananan kifaye" Naziru ya yunkura da karfi ya jefar da gawar Babban abokinshi a cikin ruwan tsundum! Fararen belbelun suka tashi sama fir!! A tsorace suna shawagi a sararin samaniya
.
=====>******^******<======
.
LITTAFI NA BIYU
BABI NA UKU"
.
Idan aka dauke sautin bugawar agogon dake kafe a bangon dakin" ba wani sauti dake tasowa sai numfashin mutane uku da suke a cikin dakin sunyi jugum-jugum kamar wadanda ke amsar gaisuwa" suna nan kamar yadda suke tun mintoci ashirin da suka wuce" sun tasa tsummokaran kayan 'yar budurwar da kuma littatafanta da hotunanta wadanda ta dauka tare da kawarta wacce tafi shakuwa da ita wato Suri
kwamishina Danmasani ya fara kawar da shirun dake cikin dakin ya dakawa tsofaffin mukarrabanshi tsawa"
"Wai wacece wannan yarinyar?
Wacece Raliya?"
Acp Bilya yayi sauri ya tattara hankalinshi daga daburcewar da yayi ya cewa kwamishina"
"yallabai wallahi bamu santa ba" bamu san yadda akayi wannan al'amari ya faru ba" wannan shine akwatin da suka xo mana dashi" kuma mun tabbatar ba xasu ha'incemu ba"
kwamishina ya cije lebenshi idanunshi sun koma kamar garwashin wuta" yasa hannu ya ture tunbujejen gashin bakinshi wanda ya toshe ramukan hancinshi" domin kuwa a halin yanxun yana bukatar wadatacciyar iska ya dubi jami'an tsoron dake tsaye suna jiran umarninshi yace dasu"
Dole ne mu gano yadda akayi wannan matsalar ta faru" dole ne mu gano ko wacece wannan Raliyar idan ma ita ce ta misanya akwatin kudin ta ajiye mana wannan to dole ne mu bita duk inda take don ta bamu kudinmu"
Dan masani" ya kwashi hotunanta daya zakulo a cikin akwatin yaga kyakkyawar budurwace kowane hoto da ta dauka murmushi take yi" maimakon abin ya bashi sha'awa sai yaji kamar murmushin da takeyi a cikin hotonan" tana yi mashi dariyar mugunta ne" ta tafi da
Dala Miliyan Hamsin Dan masani yaji kamar ta yafa mashi garwashin wuta a fuskarshi" ya zaro mata kananan idanunshi yana kallonta, a hoton yace
Ki daina saurin murmushi yarinya baki ci bulus ba" zamu bi ki duk inda kika shiga a duniya" zamu dawo da kudinmu dake wurinki" ba zamu amshi wadannan tsummokaran kayan ba"
Ragowar 'yan sandan biyu dake a tsaye suna kallonshi" suka dubi juna a tsorace su kansu sun dade da sanin halin kwamishina wajen rashin hakuri musamman bangaren da ya shafi kudi" zuwa can ya dan sassauta zuciyarshi sannan ya tattara hankalinshi a kansu yace
"kuje kuyi min binciken gaggawa akan wannan yarinyar" ku fara tuhumar Jarmai yadda akayi ya sami wannan akwatin maimakon akwatin kudin da ya sato a wurin kawunshi" sannan kuma kuyi hanzarihanzarin zuwa makarantar da wannan yarinyar take ku kamo mana ita"
Kwamishina dan masani" ya sake dauko wani hoto da Raliya ta dauka ita da kawarta ya dubi hoton sannan yace dashi
"idan baka ganta ba a makarantar" ku kamo wannan kawarta ta" dole ne ita tasan inda take"
Ya juya bayan hoton yaga anyi rubutu da biro cikin siraran harrufa kamar haka
(NI DA KAWATA SURI) kwamishina ya mukawa Acp Bilya hoton ya amsa cikin ladabi" ya gyara zama sannan ya dubi razanannun fuskokinsu yace dasu cikin bacin rai
Bazaku sha wahala wajen gano 'yan matan ba" domin kuwa Raliya ta rubuta sunan kawarta a bayan hoton" duk wacce kuka gani a cikinsu ku kamo mana ita" kada ku dawo nan ba tare da daya daga cikin wadannan 'yan matan ba"
"RALIYA ko kawarta SURI"
tsofaffin jami.an tsaron suka fice da sauri suka bar dakin kamar iska
.
======>******^*****<=======
.
Kamar kowacce rana idan akayi sallar la'asar yamma tayi wani yanki dake a bayan labirari" dakin karatun dake a jami'ar bayero yakan cika da dalibai Fal domin kuwa wajen yana kunshe da yalwatacciyar inuwar bishiyoyin dorawar turawa da madaci sannan kuma akwai kujerun da aka gina na siminti dake a warwatse a ko ina a harabar inda samari da 'yan matan ke zawa su zazzauna wadansu suna karatu" wadansu kuma suna zaman soyayya" babu wanda ya damu da abinda wani yake yi"
A wannan karon ma wurin ya cika makil da dalibai" suna zazzaune mafi yawa daga cikinsu karatu sukeyi" domin kuwa zuwan wannan jarrabawa da za'ayi a kwana kwanan nan" yana matukar tsorata dalibai" sai kace ba'a saba da ita ba
Dalibain suna zaune suna karau kamar daga sama sai sukaji karar wani abu ya tashi ya fashe fas!!
Sai kace balo-balo nan da nan kowa yayi saurin dago kanshi a fusace" wata bayerabiyar daliba" sanye da farin tabarau tace a fusace"
(fuck you bastard)
A lokacin ne wani dalibi bahaushe sanye da kayan nasara yace
Don Allah wanne bakauye ne ya fasa mana balo-balo anan muna karatu?" kada ku mayar mana da (compound) kamar filin wasa mana"
'Daliban suka mayar da hankalinsu akan inda karar ya fito" wani saurayi ne gajere mai manya manyan kumatu yana kallon wata madaidaiciyar budurwa wanda ke tsaye a gabanshi tana faman huci" yace da ita a fusace"
"Ni kika mara Nafisa?"
Budurwar ta hayayyake mishi kamar zata cinyeshi danye"
An mareka din" an mare ka" duk abinda kaga zaka iyayi kayi na mareka"
Saurayin ya girgiza kanshi a fusace sannan ya saki kumatun shi yace da ita cikin damuwa"
Yanzu Nafisa saboda kawai na damu dake" na nuna ina kaunar ki shine zaki mareni a bainar jama'a?"
Budurwar tace
"sau nawa kake so in fadi maka" shamsuddeen na fadi maka bana kaunarka" bana sonka" bana ra'ayin ka amma ka nace min duk inda na nufa kana nan like dani" to ana yin soyayya dole ne tunda nace bana yi saika rabu dani" wannan shine gargadi na" na karshe da zanyi maka" ka fita daga harkata" shasuddeen kada ka sake yi min magana" banza kawai shashasha"
Budurwar ta juya a fusace ta tafi" tabar saurayin yana shafa manya-manyan kumatunshi 'yan matan dake wurin suna kallon diramar dake faruwa tsakanin saurayin da budurwar suka fashe da dariya hade da tafa hannuwansu" Bayeribiyar dake zage zage dazun ta buga kafarta a kasa saboda murna tace
("very good baby" treat men like this")
samarin dake wurin ganin an wulakanta namiji dan uwansu akan soyayya acikin jama'a sai suka fara kunkuni" wani dalibi yayi tsaki yace a fusace
"Laifin shi ne sakarai" ne me Zanyi da waccan bebin din amma dubeshi ya bari har tana marinshi"
wani dalibin dake a karshen harabar yace
"matsalar soyayya ce taya iya faruwa da kowa anan" ku daina ganin laifinsa don ya sha mari" babu mamaki wata rana sai ta dawo tana binshi yana shareta" badai soyayya bace tayi mu gani
Dalibai suka yita dariya suna mayar da martanin abubuwan da suka faru a cikin dan kankanin lokacin" irin wannan diramar takan faru ako ina a cikin makarantar a tsakanin samari da 'yan mata" wadansu kuma da yake sun saba da ganin irin wannan shirirtar" ko dago kai basu yi ba" balantana kuma har abin ya basu dariya"
.
Daliba Suri tana daya daga cikin wadannan dalibai" amma kuma ita sabanin sauran daliban da karatu ya hanasu su dago kansu suyi kallon fadan" ita tunanin wani abu ya hanata ta dago kanta" tayi shiru a zaune tayi tagumi akan kujera tun dazun take zaune a wajen" ta zurfafa a cikin kogin tunani mai zurfi" duk wanda ya ganta yasan cewar hankalinta ba'a kwance yake ba
Suri ta dago kanta bayan taji dalibai dake dariya sunyi shiru" domin kuwa ita bata ga wani abin dariya ba" don budurwa ta mari saurayin ta a cikin jama'a me yiwuwa kuma abin dariya ne" to amma kuma bakin cikin dake damunta a halin yanzun bazai taba barinta tayi dariya ba" tun tashinta da safe take a cikin wannan hali na damuwa" wadansu a cikin kawayenta suna tsammanin a dalilin tafiyar Raliya babbar aminiyarta tasa ta cikin wannan hali" idan ma akwai wannan to ko shakka babu akwai wani abu bayan wannan
Suri ta kurawa reshen wani madaci idanu" ko kiftawa bata yi" a zuciyarta tana ambaton sunan masoyinta Jarmai shin me ya faru da Jarman har yanzu bai zo ba?" wannan itace tambayar da suke take faman tambayar kanta tun safe" to amma kuma har zuwa yanzu bata samo amsar wannan tambayar ba" tasan cewar inba wata matsala ce ta faru ba" to dole ne Jarmai yazo ya dauketa su gudu" kamar yadda yayi alkawari idan har yayi nasarar sato Milliyoyin Kudin " anya kuwa ba'a kama masoyinta Jarmai ba
Suri taji hawaye sun zubo mata" tayi sauri ta share hawayen domin kuwa bata so wani ya gane tana kuka" bata so a dame ta da yawan tambayoyi"
Suri tayi ajiyar zuciya" tuntuni ta gama shirya yadda zata kashe Miliyan Hamsin din da Jarmai saurayinta zai sato.
Ta fitar da motocin da zata saya ta gina katafaren gida na alfarma mai dauke da tsararren kwatamin wanka a cikinshi
Gashi yanzu Jarmai baixo ba" babu Miliyan Hamsin " babu Jarmai
.
Suri taji wani hawayen zai sake zubo mata" tayi sauri" ta tashi daga kan kujerar da take zaune" ta wuce daliban dake zazzaune suna karatu" ta kama hanya ta tafi katafaren ginin dakin kwanansu" farin bene hawa uku dake cike da tagogi barkatai masu ruwan ganye na gilashi"
suri ta gangara ta wata siririyar hanya dake cike da ciyayi ta zagaya ta bayan wasu ajuiuwa" domin kuwa tafi so har takai dakin kwanansu kada ta hadu da wani dalibi ko daliba data santa"
Domin kuwa batason magana daidai wannan lokaci" suri ta gama zagaye zagayenta ta dawo kan babbar hanyar da motoci ke wuce a cikin makarantar sashin wurin kwanansu na mata..
.
.
TANA KAN TAFIYA SAI........RALIYA-11
.
Raliya Tana kan tafiya ne ta hango wasu dattawan mutane biyu sanye da bakaken kaya a jikin wata
bakar mota fijo" sun kura mata idanu" suna ta
kallonta tun daga nesa" akwai wani yanayi dake
tattare da mutanen wanda bai kwantawa suri Arai ba" tazo daidai inda suke zata sabasu ta wuce" sai taji wani mutum ya daga murya yace da ita" "ke muke zaman jira anan suri"
.
Suri taja birki ta tsaya a tsorace ta sake duban
mutanen sai a lokacin ne ta fahimci kayan
jami'an tsaro ke jikinsu" suri taji gabanta ya fadi
tayi sauri taja baya
Me zanyi muku malamai...... Me kuke nema a
wurina?" Wanda yayi magana da farko ya sake cewa da ita a tsanake"
"wasu bayanai muke nema a wurinki acan
ofishinmu" shigo cikin mota mu tafi" ba abinda
Zai sameki 'yan mata"
Suri ta sake ja da baya zata yi tirjiya ta ruga da
gudu" sai ta dubi hannun daya tsohon jami'in
tsaron taga yana rike da guntuwar bindiga
saitinta" ta dubi fuskokinsu taga babu alamar
wasa ko yaudara" mai rike da bindigar yace da
ita "kina iya guduwa idan kina bukatar yin hakan" to
amma kada ki zargeni idan kikaji harsashin
bindiga ya karairaya kafafuwanki 'yan mata"
Nan da nan mara bindiga ya bude kofar motar yashiga ya zauna akan kujerar direban" wanda ke rike da bindigar ya bude kofar baya na motar" ya
yiwa suri murmushi sannan yace da ita"
"zaki iya shigowa yanzu 'yan mata sunana Aminu Jangwarzo" wannan abokin aikina ne bilya" mu dukanmu jami'an tsaro ne" idan kika bamu hadin
kai ba abinda zai sameki" amma idan kika bamu wahala wajen binciken da zamu yi maki" ina
faragabar sanar dake koke kanki bazaki gane
kanki ba nan da wani dan lokaci mai zuwa"
Suri ta fashe da kuka" tayi saurin rufe bakinta
ganin har yanzu mutumin bai dauke bindigarshi
daga saitin inda take a tsaye ba" suri ta taho a
tsorace kamar kwai ya fashe mata a ciki" ta shiga
cikin motar" jami'in tsaron yabi bayanta cikin
sauri sannan ya rufe kofar" direban yaci taya
suka fice daga harabar makarantar" suka doshi
hanyar ficewa daga babbar kofar da suke
fuskanta"
Wadansu yara dake gara taya a kusa da wajen
suka dagawa motar hannu" lokacin da ta wuce
kamar kibiya" a karo na farko direban motar yayi murmushi tun zuwansu makarantar neman suri" sannan ya dagawa yaran hannu"
Lokacin da su bilya da Aminu jangwarzo suka kai suri gidan tuhuma na sirri" C-P Dan masani yana ciki yana jiransu" a cikin gidan ne suka kulle Jarmai a wani faffadan daki mai duhu wanda ke cike da kyankyasai da kuma zarnin fitsari da masu laifi da ake kawowa a kulle su a ciki suyi sati ba'a waiwayesu ba"
Sau da yawa idan ba irin wannan bincike na sirri ya taso ba" ba kasafai ake kawo mai laifi wannan kebentaccen gida ba da kwamishina ya ware domin wasu bukatunshi na musamman" tun dazun yana nan a cikin gidan" tun lokacin da su bilya suka tafi jami'a domin nemo Raliya ko kawarta Suri bayan sun tafi ne ya shiga cikin dakin da aka kulle Jarmai ya sameshi a nannade da ankwa hannu da kafa" yayi iyakar kokarinshi wajen ganawa Jarmai azaba iri iri domi ya fada masa inda ya boye jakar kudin da suke nema"
Amma kuma Jarmai ba abinda yake iya fadi sai dai bai sani ba"
Danmasani bai rabu dashi ba saida yaga ya suma" sannan ya fito daga cikin dakin yana huci idanunshi sunyi jawur kamar gauta"
Lokacin da su ACP bilya suke fito daga cikin mota suka iza kyeyar suri zuwa cikin gidan" Dan masani yana tsaye a bakin dogayen dakunan tuhumar inda Jarmai yake" suri taji gabanta ya fadi" ta sake tsurewa a lokacin da taci karo da kwamishina " yanayin fuskarshi kawai ya isheta fahimtar azabar dake yi mata lale marhabin a cikin gidan"
Tun kafin su gabatar da ita" kwamishina ya daka mata tsawa a fusace" "Ke.... Ina kawarki Raliya? Suri ta firgice ta fara in-ina cikin tsananin kaduwa"
"Raliya?" ban san....... Ta koma garinsu" Wallahi bata nan ta koma gida"
kwamishina Danmasani ya harareta" yakai hannu ya cakumo kwalar rigarta da hannu daya" ya dagata sama kamar 'yar tsana sannan ya wanke ta da mari tas!! Sai da kuncinta ya tsage kamar an yanka ta da reza"
Suri ta fasa kururuwa iyakar karfinta" kwamishinan 'yan sanda ya jefar da ita kamar totuwar masara ta hadu da bangon dakunan tuhumar nan take ta watse a kasa"
ya matsa kusa da inda take a kwance tana juye-juyen mutuwa" jini ya wanke 'yar matsakaiciyar fuskarta" ya duka yace da ita a sanyaye
Ba kasheki zamuyi ba" ballantana ki huta" zamuci gaba da karairayaki ne har sai kin koma tsumma" ki fada mana gaskiyar abinda muka tambayeki" ina kawarki Raliya ta tafi?"
Suri ta bude baki dakyar jini yana zuba tace dashi "ta koma gida dazu da sassafe" ta koma garinsu
kwamishina ya zare idanu yace
ina ne garinsu" a ina yake?"
Suri ta yunkura ta matsa baya kadan a tsorace tace" "Dan marke ne garinsu" wani kauye ne Dan marke acan take"
Kwamishina ya daka mata tsawa"
Me taje yi ana tsakiyar karatu" kuma yaushe zata dawo! suri tace "ta koma ne domin ayi mata aure" tace bazata iya ci gaba da karatu ba" tana da wani masoyi da take so sunanshi" RUFA'I tace donshi zata bar karatu" domin yace bazaici gaba da jiranta ba" zai auri wata budurwa.
Kwamishina ya daka mata tsawa saida hanjin cikinta ya motsa"
"Dame ta tafi lokacin da zata bar makarantar" baki ganta da wani akwatin kudi ba?
Suri ta girgiza kanta a tsorace"
"wallahi ban ganta da akwatin kudi ba" da akwatin kayanta ta tafi wanda take zuwa dashi ko yaushe" Raliya bata da kudi ni na bata kudin motar komawa gida"
kwamishina ya mike tsaye yana mayar da numfashi ya dubi mukarrabanshi biyu dake tsaye suna kallon yadda yake tuhumar 'yar budurwar" fuskokinsu sunyi sharkaf da zufa sun koma kamar dodanni" yace dasu a fusace
"ku hada ta da waccan ku kulle mana su" zasuyi mana amfani nan gaba kadan"
tun kafin su rufe baki Aminu jangwarzo yayi sauri ya taho yasa hannu daya ya cafi gashin kan suri dake a hargiste a waje kamar shekar ungulu" ya mikar da ita tsaye" sannan ya jata zuwa dakin da Jarmai yake tana binshi da digirgire tana kukan azaba"
Da zuwanshi yasa kafa ya haure kofar dakin ta bude" bai shiga ciki ba" kafin kofar ta sake dawowa ta kulle ne ya

Please Login or Register in order to submit comment