Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

AZIZA-01

BABI NA DAYA

KANO
RANAR LAHADI, UKU GA JANAIRU
12:00AM NA DARE.

Yana Zaune shi kadai acikin duhu akan kujera daya jal dake dakin yayi zuru baya ko motsi kamar mutum-mutumi.

Daga inda yake zaune acikin duhun daren fuskarsa na duban katuwar tagar dakin ta katako wacce ke fuskantar farfajiyar gidan hakanan kusan duk wani katako na tagar dakin a cinye yake da Gara.

Haka din nan dayake zaune yafi sa'o'i hudu ahaka idanunsa na duban saman dakin batareda shi kansa yasan abunda yake kallo ba.

Sawu ya dauke duk kusan wadanda ke gidan sun shiga barci bakajin sautin komai ko motsin wani abu sai sautin bugun agogo mai gwaiwa tsohon yayi wanda ke makale yana reto kamar allon sha amma dan karfin hali sai aiki yake abin sa tik tik tik banda wannan sautin kuma akwai jefi jefin kukan gyare nan da can to amma ko kusa ko alama wannan saututtuka basu dami SUNUSI ba domin babu abunda take gani ko ji a halin yanzu sai sakon da aka zo aka tsurkunta masa a yammacin ranar...
Kodai ka yarda ko kada ka yarda nidai na fada ma AUREN AZIZA YA MUTU.......

Wannan kalma ita ke ta faman kai kawo da kururuwa acikin kwakwalwarsa ita ta hana shi ji da gani takuma sa shi shigowa cikin wannan dakin ya zauna hakanan baya ko kwakkwaran motsi kamar gunki domin ya kasa imani da hakan.

Dakin ya gauraye da haske ba zato ba tsammani kanwar sa ASMA'U ce ke tsaye a kofar dakin hannunta akan makunnar lantarkin dakin tana dubansa cikin mamaki.
Me.....ne ne? Sunusi ya tambaye ta a firgice domin baisan da shigowar ta ba saida ta kunna kwan wutar.

Sunusi me kake yi haka tun dazu kai kadai acikin duhu kuma ba barci kake ba? Sunusi ya harareta fuskarsa murtuk yace
Me ya shafe ki da zamana? Bance dake bana son yawan tambayoyi ba yan kwanakin nan.....

Yi hakuri...... Asma'u tace dashi cikin sauri domin tuntuni ta gama tsorata dashi kai ba ita ba duk sauran dangin su ma ayanzu haka tsoron sa akeyi domin rabon da aga hakoransa afili yana dariya tun ba'a yi auren AZIZA ba yau kuwa shekara uku kenan daidai

Uhm.... Daman...... Daman Samira ce tazo yanzun nan tace wai tana son kuyi sallama domin wai taji ance gobe da sassafe zaku tafi... Sunusi ya dubi kanwar sa cikin mamaki - mamaki fushi-fushi.
Kina nufin kice Samira ce tazo nemana cikin wannan uban daren?

Asma'u ta gyada kai Sunusi yayi shiru zuciyarsa na bugawa har tsawon minti guda sannan saiya dago kai yace kice da ita bana bukatar ganinta.

Asma'u ta juya a tsorace zata fice daga dakin.
Ki kuma kashe min wutar kafin ki fice Sunusi ya sake cewa da ita nan da nan dakin yasake komawa cikin Duhu.

********** ********* *********** ****************

Ko da Dakin ya sake komawa cikin duhu sai Sunusi yasake dulmiya cikin tunaninsa koda yake Awannan karon yana motsi ba kamar wancan lokacin ba.
Wannan..... Samira da naci take.. Kamar mayya yace da kansa sannan ahankali saiya lalubi gefen sa acikin duhun daren hannunsa ya taba katuwar jakar dake dauke da duk wani abu dayake bukata domin acikin jakar akwai siturunsa takalma agogo man wanke baki burushin wanke wando da dai sauran tarkace wanda acikinsa har da takardarsa ta shaidar daukarsa amatsayin SOJA.

Saidai nan da yan sa'o'i ne yake sa ran zuwan sauran Abokan tafiyarsa wanda da asubahin gobe ne suke sa ran tashi zuwa zariya makarantar horon sojoji kurata.

Su shida ne suke sa ran tafiya Sojan hakan nan kowa yanada dalilin tafiyar sa soja biyu daga ciki dai suna son tafiya ne saboda kawai suna sha'awa yayinda biyu kuma suke son tafiya kawai wai don wani soja ya wulakanta su shiyasa suma suke son tafiya soja na cikin biyar dinsu kuwa shi ya shiga soja ne saboda wani babban buri dake zuciyar sa wai yana tsammanin zai iya zama shugaban kasa na mulkin soja. To amma dalilin Sunusi yasha bambam matuka dana yan uwansa dan haka sa'ar da ya sami sakon cewa.

...... Auren Aziza ya mutu sai duk yaji kamar duniya ta ruguzo masa a tsakiyar baya dalilin tafiyar sa soja ya raunana domin tafiyar tasa sojan tanada alaka da sakon daya samu a yammacin ranar koda Sunusi ya sake taba jakar dake cikin duhu da hannunsa saiya ji hawaye yafara kwarara akan fuskarsa ta wani Bangaren hawayen farin cikine awani bangaren kuwa kuwa na bakin ciki.
Bakin cikin daya birkita shi ya zarar dashi ya maida shi mahaukaci kiri kiri wanda hakan shi ya sa zuciyarsa takoma can baya wani lokaci kuma acan wani zamani daya shude da dukkan wani farin ciki na Sunusi.

Abun yafara ne kawai daga gaisuwa ta al'ada koda yake a kasar hausa idan aka ga gaisuwa ta tsananta tsakanin mace da namiji marasa aure wani lokacin akan zargi cewa lallai akwai wani abu a tsakani.
TO da irin wannan ne aka fara tsakanin Aziza da Sunusi tsautsayi da Kaddara ce suka hadasu akalla dai ko da kowa bai ce haka ba to shi Sunusi yace tsautsayi ne domin idan Allah ya yanka ma kazar wahala to dole ne saika fige ta.

Amma in bahaka ba me zai kai wanda karatun sakandire kawai yayi zuwa bikin yaye daliban jami'ar bayero..?

Awata Asabar da aka tara manyan farfesoshi da kananan malaman jami'a gamida manyan masu fada aji dakuma masu tarin kudi da adadin sifilin su yafara daga shida domin hallara agurin bikin yaye daliban jami'ar bayero.

Yakamata mu tafi da kai Sunusi. SHEHU BARAU yace dashi. dan ajinsu Sunusu ne tun suna firamare to amma shi Allah yasa yanada rabon wucewa zuwa jami'a har ya gama shi kuwa Sunusi da kyar ma ya kammala sakandire a daddafe.AZIZA-02

Shi Sunusi da kyar ma ya kammala sakandire a daddafe.

Har suka shiga tsohuwar jami'ar bayero inda za'a yi bikin jikin Sunusu na bari domin bai taba shiga ba hakanan kuma gani yakeyi kamar idan an je kowa zai dauke shi ne amatsayin bagidaje tunda shi karatun sa baiyi zurfi ba gashi kuma na sakandiren ma dayayi bada wani sakamako na kirki yafita ba abu na biyu kuma daya dada firgita Sunusi shine duk wanda ya kalla acikin daliban saiya ganshi tsaf tsaf kowa yaci diresin kamar an ɓarasu daga kwali fuskokin sa sai sheki sukeyi musamman ma YAN MATA.

Sunusi ya shafi fuskarsa sa'ar da suka karasa gindin wata bishiya wacce ke dab da dakin karatun da za'a yi bikin
Sunusi ya tuna da ko mai bai shafa ba ya fito gashi kuma lokacin sanyi ne duk jikinsa yayi fururu kamar an tono shi daga kabari bakuma wannan bace kawai ke damunsa ba hatta kayan dake jikinsa ko goge su baiyi ba ya taho musamman ma Wandonsa kore ne fatau gashi duk ya tattare kamar Asabari toh wannan ita ta sa Sunusi ya dunga rabe rabe abaya hoto ma dakyar abokinsa SHEHU BARAU ya takura shi suka dauka tare domin idan ya shiga cikin jama'a saiyaji shi kamar duk wari yakeyi.

Har aka tashi daga taron Sunusi na boye boye da biki yayi buki ma sai Sunusi yakoma can gefe guda yayi zaman sa akan benci yana yan waige waige ko ina dalibai ne suna ta daddaukan hotuna kungiya kungiya tun Sunusi na tsoron gurin har dai ya warware yaci gaba da kallon daliban sannan ne to tsautsayi yafada masa domin lokacin ne yafara hangen AZIZA.

Abu na farko daya fara zuwa zuciyarsa lokacin daya hangeta shine balarabiya ce to amma sa'ar daya nutsu dakyau saiyaga ashe dai bakace amma ba kamar shi ba fatar jikinta launin kofi ce tana sheki luwai-luwai kamar nunanniyar tufa hakanan tunda Sunusi yake bai taba ganin idanu ba fari irin na aziza ba ya tabbata duk tsananin duhu bazai Hana shi ganin kwayar idanun aziza ba saboda farinsa.

Akwai wani digon baki a kuncin ta na dama wanda ya dada mata kyau doguwa ce ba can ba hakanan ta hada fari uku
1 Fari Na haƙori
2 Fari Na idanu
3 Fari Na fatar jiki

Tana kuma da siririn abu uku
1 Siraran gashin kanta da suka zuba ta cikin bakar hular dake kanta wacce kusan kowane dalibi yana da ita gami da rigarta tana kuma da
2 Siririn wuya dogo dakuma
3 Siriri cikon na uku wato siraran yan yatsu na hannu dana kafa

Tana kuma da baki uku
1 baki na idanu
2 gashin kai da
3 baki na adon fatar baki

Tanada kauri uku wani malamin arabiyya yatab cewa da Sunusi duk macen data hada kauri uku baki uku fari uku to hakika wannan mata ita ya kamata a kira kyakkyawa
Koda Sunusi ya sake dubanta saiyaga duk ta hada wadannan abubuwan.

Abincin wani bana wani ba gadon ari sai fanna ramin kura sai ya'yanta Sunusi yace a ransa sannan saiya dauke kansa domin abunda ido bai gani ba zuciya bata darsuwa a kansa.

Yana nan kansa a sunkuye saiyaji an dafa kafadarsa
Tunanin me kake yi ne? Shehu barau ya tambaye shi Sunusi ya dago kai sannan ne to ya sake yin ido biyu da tsautsayinsa akaro ba biyu atsaye a kansa shehu ne abokinsa shida wasu dalibai yan uwansa guda hudu sannan tare da AZIZA.

Tashi mu dauki hoto. Shehu yace dashi sannan saiya dubi sauran daliban wadanda duk sanye suke da bakaken riguna dogaye masu faffadan hannaye yace.
Wannan abokina ne Sunusi sannan ya dubi Sunusi yace wadannan kuma abokaina ne wannan dogon sunansa ALIYU wancan KABIR wannan HILAL wannan dan guntun kuma HABU DUKUS kenan daliban duk suka fashe da dariya gaba dayansu harda Sunusi. suka mikawa Sunusu hannu duk aka gaggaisa ana fara'a Sunusi yaso su a zuciyarsa nan da nan saiyaji duk rashin sabon da ya Dame shi adazu yafara Barin jikinsa

Wannan kuma ita ma yar ajinmuce sunanta AZIZA shehu yace da Sunusi yana dubansa Aziza ta haskake shi da murmushi.
Sannu malam ina kwana
La....lafiya lau... Wani abu ya toshe masa makogwaro dakyar yake numfashi ida tayi murmushi ashe tafi kyau. Sunusi yace cikin zuciyarsa.

Idan Kuma kaso kana iya kiranta da aziza
(THE FIRST LADY) Shehu yace yana dariya Aziza ta Harare shi cikin wasa.
Kai rabu dashi malam Sunusi aziza dai.
Sunusi bai iya amsawa ba baikuma iya hada idanu da ita ba akwai wani abu dake kokarin huda masa kirji.

Bayan angama daukar hotuna sai kowa yafara watsewa Sunusi ya sake komawa gefe guda ya zauna akan bencinsa na dazu shehu kuma ya tafi yana sallama da dalibai yan uwansa.

Yau na shiga uku zan kamu da son abunda yafi karfina Sunusi yace da kansa ya kifa kansa akan cinyarsa zuciyarsa ta dulmiya baya ganin kowa sai hoton aziza cikin zuciyarsa..

Sannu...malam wata daddadar murya tace dashi sannan sai daddadan kamshin turaren dake jikinta ya doki hancin Sunusu ya dago kai zuciyarsa na bugawa daf-daf kamar zata tsaga kirjinsa.

Aziza ce tsaye a kansa tana murmushi
Me yasa kake son zama kai...kadai? In bazaka damu ba zo mu je ka rakani can cikin makaranta kafin su shehu su dawo

Me take nufi? Sona take.? Tausayina take ji? Kokuwa mafarki nakeyi?..... Wannan ai sai shugaban kasa.....

Wannan shine inda hadarin ya afku tun daga ranar sunusi ya daina ganin komai sai aziza ya daina jin komai sai muryar aziza ya daina karatun komai sai na kyawun surar aziza ko a kwance ko a farke bashida wani tunani saina aziza to in ba tsautsayi ba menene wannan?

******** ******** ********* *********************

Kwanakin da suka biyo bayan bikin yaye daliban jami'ar bayero da suka fi dukkan shekarun Sunusi aduniya farantawa saidai kuma ashe kash..........AZIZA-03

Kwance ko a farke bashida wani tunani saina aziza to in ba tsautsayi ba menene wannan?

******** ******** ********* ******** **********

Kwanakin da suka biyo bayan bikin yaye daliban jami'ar bayero da suka fi dukkan shekarun Sunusi aduniya farantawa sannu ahankali kwanaki shuka shude makwanni suka shude watanni suka tsawaita har akayi shekara guda.

Abubuwa dayawa sun faru tun acikin shekara gudannan data shude wannan kuwa yau faru ne tun daga washegarin ranar da aka kammala bikin yaye daliban.

Yaro mai sa'a sunusi ka bani mamaki don Allah meyafaru tsakaninka da aziza jiya a makaranta shehu ya tambaye shi.

Bakomai wallahi nidai kawai tace na rakata can cikin makaranta kafin ku dawo abin kenan dana sani

Shehu yayi shiru yana duban Sunusi cikin zargi sannan sai yace bari nafada maka ko wacece aziza domin al'amarin ku jiya ya gama rudani.

AZIZA itace yarinyar da ake tsammanin duk jami'ar bayero babu sa'ar ta a kyau kowa ka gani sonta yakeyi hatta yan mata yan uwanta suna kinta ne kawai don kishi da kyawunta maza kuwa ba'a magana domin babu wani malami ko dalibi da zaice baya kaunar aziza koda kuwa a boye ne.
Yayi shiru na dan lokaci yana duban Sunusi sannan saiyaci gaba duk wannan abunda akeyi ba'a taba yarda wata dangantakar soyayya ta shiga tsakanin ta da wani a makarantar ba saidai mutunci amma sai... Gashi jiya tana tambayata kwatancen inda kake.

Sunusi yaji gabansa yafadi wani farin ciki ya lullubeshi shin Daman ashe mutum zai iya mafarkin yana dauke da kudi ahannu yakuma farka ya ganshi da kudin ? Wannan shine yadda ya kwatanta alakar sa da aziza

Tace dani yau zata zo da yamma shehu yayi shiru sa'ar daya dubi kamannin Sunusi yaga sun canza.

Ni... Abun dai yabani mamaki abun kawai da Sunusu yace kenan.

A inda suke tsaye a kofar gidansu Sunusi ne dake kan titin gidan zoo suna jingine ajikin motar shehu kirar Marsandi mai launin makuba samarin biyu sukayi shiru na dan lokaci kowa na jujjuya maganar aziza cikin zuciyarsa.

Dama ace ajina yakai na shehu... Sunusi yace cikin zuciyarsa amma yanzu ai nayi KARANBANI... Ina ni ina kyakkyawa mai kyawu kamar yar ruwa ba a banza yake tunanin hakan ba.

Tuntuni tun suna firamare Sunusi ya dade da sanin cewa mahaifin shehu alhaji sadauki barau ba karamin attajiri bane domin tun a wannan lokacin shehu yake zuwa makaranta a mota duk kuwa da cewa yayi kankanta sosai a wancan lokacin tsakanin gidan su Sunusi da shehu layi shida ne a tsakani amma duk da haka zaiyi wuya shehu yazo gidan su Sunusu ba'a cikin mota ba irin kawancen shehu da mota shiyasa da yawa daga cikin Abokan su da dama suke kiran sa da shehu barau mai mota

Sunusi yasan cewa da shike yake da arzikin gidan su shehu dakuma shine da ilmin shehu da ko dar dar din tunkarar aziza kyakkyawa bazaiyi ba to amma ayanzu babu ko kobo dukun-dukun dashi kullun yana warin talauci kamar beran masallaci ga kuma uban jahilci karatun addini ko izu daya bai gama ba ya watsar daga nan babu kari tun dayake bai taba zuwa Islamiyya ba da zummar karatu to amma ya kanje a buga mandiri dashi hakanan yar sakandiren ma da kyar ya gama kuma shine karshen baya domin sakamakon daya samu KAFI BABU NE dan haka koda ya tsaya yanzun nan kusa da abokinsa shehu yana karatun wasikar jaki sai ya yankewa kansa da kansa hukuncin cewa lallai tunkarar aziza da soyayya agare shi ayanzu tamkar taran kwarankwatsa ne da tsakiyar kai.

To amma duk fa da wannan tunanin akwai wata zuciya mai taurin kai da ke cewa dashi bi ahankali Sunusi duniya da sannu aziza zata kauna ce ka in bahaka menene zata ke neman ka?

Af na manta ma ban fada maka ba muryar shehu ta ratsa shirun. Sunusi yayi firgigit sannan ya dubi motocin dake ta faman kai kawo kamar tururuwa akan titin yace.

Me kenan Shehu? Shehu ya dafa saman Marsandin sannan yace da Sunusi
Jibi fa zamu kauracewa unguwar nan Sunusi ya dube shi cikin mamaki yace.

A'a iko sai Allah ina kuma zaku koma? Shehu ya sosa keya.
Abuja zamu koma kasan (boss) din mu ya sayi gida acan kum......
falleliyar bakar Hondar da ta tsallako titin ta nufo inda suke tana walwali kamar madubi ita ta katse kalaman shehu lokaci guda kuma sai ta tsaida numfashin Sunusi domin tun kafin ma motar ta tsaya shi yasan ko wacece aciki.

Kofar motar ta bude sannan aziza ta jeho doguwar kafar ta waje fara sol....Kwatsam.........AZIZA-04

Kofar motar ta bude sannan aziza ta jeho doguwar kafar ta waje fara sol kamar ka taba jini ya tsatstsatso tana sheki kai kace bata taba taka kasa da ita ba.

Sanye take da doguwar riga baka sidik mai gashi-gashi akwai wasu taurari na azurfa guda biyu dake dinke a saman rigar daf da kirjinta suna daukar idanu kamar idanun kyanwa acikin duhun dare kyakkyawan gashinta dan siriri ya dan leko ya dan zubo akan dogon wuyanta dan siriri amma sauran adadin gashin suna boye acikin wata bakar hula malafa ta farar miski a saman ta akwai irin tauraron dake jikin rigar guda daya na azurfa yana walwali a kasan sa kuma an rubuta da karfe shima launin azurfa kamar haka HONEY.
Lokacin data gama fitowa daga cikin motar ta nufo inda suke duk sai walwalin da motar keyi ta dusashe domin aziza tafi motar walwali

Sunusi... Tayi yar dariya da zazzakar muryar ta kayi hakuri dan Allah na ajje ka kanata zaman jirana ko? Wallahi wata yayar mu ce ta haihu anan asibitin Nassarawa shine to na biyo ta can kafin nazo nan ta danyi shiru sannan saita sake cewa
Ina wunin ku...?

Lafiya lau shehu ya amsa yana murmushi.
yaya gajiyar shagalin jiya?

BA gajiya....shehu yaushe zaku wanko mana hotunan mu ne?

Za'a kawo miki naki har gida shehu yace da ita

Sunusi yayi mutuwar tsohuwa baya ko kwakkwaran motsi hakanan bai gaskata sautin muryarsa ba ballantana ya shiga cikin hirar. Wannan hira yan boko ce ya dada jaddadawa zuciyarsa.

Shehu yajuyo ya dube shi yace da aziza cikin murmushi
Ga mutumin naki ni zantafi, aziza ta dan dauke kai gefe guda cikin jin kunya sannan tace kaji shehu da tsokana meye kuma na tafiya kayi zamanka mana shehu ya girgiza kai yace ai damunar bana bata kwado bace kedai gara ni nayi gaba zan kawo miki hotunan ki har gida shehu ya bude kofar motarsa cikin sauri.

TO nagode shehu aziza tace da shehu ya dubi Sunusu yayi masa dariya yace kabi da ita ahankali domin haryanzu bata iya ruwa sosai ba da haka yaja motarsa yabar su nan tsaye shiru tsawon dakiku suna duban juna koda yake Sunusi bai ko iya kallon ta sosai ba.

Mu koma cikin mota ko....?
Tace dashi tana dubansa to...

Sunusi yace kamar mai koyon magana sannan ya bita abaya simi simi kamar tana jansa da akala.
Ga sauran mutanen dake da Karancin sanin Abunda ke gudana a tsakani idan suka dubi aziza da Sunusi sa'ar da suke nufi motar sai su rantse da Allah almajiri ne ke binta abaya zata dora masa dako.

Suka dubi juna sa'ar da suka zauna acikin motar sannan ne to aziza tace dashi so nake mu tafi wani kanti dakai ka zabi duk irin suturar da kake so domin daga yau bana son kara ganin ka cikin wadannan kayan.

Hakan da tace shiyasa Sunusi ya dubi rigar dake jikinsa mai launin ruwan goro koda ya shinshina rigar saiyaji kamar tana wari-warin gawa.

Amma....... Sunusi yafara magana aziza ta katse shi tana haskake shi da murmushi kada kace komai Sunusi... Allah ne ya hadamu babu kuma mai raba mu sai shi.... Sanin kanka ne kuma Hausawa sunce wai ME SON DAN TSUNTSU SHIKE BINSA DA JIFA wannan itace kalma mafi dadi da Sunusi ya taba ji tunda yazo duniya.

Wannan shine farko tun daga wannan rana al'amura suka ci gaba da faruwa akan Sunusi kamar a mafarki Kusan kullun suna tare da aziza soyayya tayi karfi aziza itace cin Sunusi itace kuma shan sa, suturarsa da duk wata bukatarsa ta duniya ko a barci ne ko a farke Sunusi bashida wata magana saita aziza domin tagama sauya rayuwar sa kwata kwata ta tsame shi daga cikin talauci takuma bashi dukkan soyayyar ta agare shi kullum acikin farin ciki yake to amma fa duk da haka haryanzu yana nan a cikin JAHILNCIN SA .

Kadan-kadan shekara guda ta shude abokinsa shehu tuni sun shekara a Abuja amma lokaci lokaci yakan aiko masa da wasikar gaisuwa Yakuma tambaye shi aziza wani lokaci har yakan ce
Kabita ahankali Sunusi bana ko shakka aziza matar mu ce

To amma fa duk irin wannan soyayya da aka shekara guda anayi Sunusi bai taba zuwa gidansu aziza da zummar hira ba.

Ta taba kaishi ta nuna masa wani katon gida mai tangamemen kofa kamar kofar gari sau daya amma ko fitowa basu yi daga motar ba suka juya tace dashi babana ne.. Wallahi ya takura min ko kadan baya son ya ganni da samari to amma in Allah yaso zan sha kansa Sunusi.... Kaine mijina in Allah yaso... Oh Darling haka kullum takan ce dashi ita ke zuwa hira ta dauke shi a mota ta kaishi guraren shakatawa daban daban suyi hirar su

ABU DAYA DAKE DAMUN JIN DADIN SOYAYYAR SUNUSI SHINE......AZIZA-05

Abu daya dake damun jin dadin soyayyar sunusi shine mahaifiyarsa kullum batada aiki sai fada akan soyayyarsa da aziza.

Duk abinda takeyi maka ni ba burgeni takeyi ba domin yarinyar ba sa'ar ka bace ta ko'ina abunda nake so dakai tun wuri ka bar yarinyar nan ka nemi daidai dakai yar talaka ƙwarya tabi ƙwarya Sunusi in tabi akushi fashewa takeyi ga yarinyar nan yar uwar ka yar gidan MALAM BABA dama ita ka nema tunda yarinyar nan SAMIRA ta dade tana nuna maka kauna amma kayi biris da ita.
Kanata bin kyalkyal banza.
Harta gama fada Sunusu bazaice uffan ba domin shi yasan Allah ne kawai zai raba shi da aziza dan haka bai ma taba bata lokacin sa ba kan Samira sau da yawa takan yi kwalliya ta zo har cikin dakinsa amma da sun gaisa sai Sunusi ya fice ya barta a dakin.

TSAUTSAYI kamar yadda Sunusi ya kira abun daga baya yafara ne bayan sun kai shekara daya daidai da aziza suna soyayya kamar su hadiye juna a ka'ida duk bayan kwana uku aziza take zuwa ta dauke shi.
Watarana sai aka wayi wari

2 Comments On AZIZA
avatar
mustapha-6-6

2 months ago

Reply

Gaskiya naji dadin samun taskar nan sabida akwai dinbin littafai masu debe kewa Ina godiya da fatan alkhairi

avatar
taskar

2 months ago

Reply

Replying to mustapha-6-6

Mu ma muna godiya kwarai, ka samu ka yi subscribtioon na mu koda na 1k ne domin ka fi jin dadin samun littatafan tunda zaka samu daman downloading na su

Please Login or Register in order to submit comment