Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

馃ウ?COMPILED BY
ESHHAT SMILER HOM OF HAUSA NOVLS DOCUMNTS
WASAPP 08066360176 FOR MORE?馃ウ馃ウ馃ウ馃ウ馃ウ馃ウ馃ウ馃ウ

*AUREN BAUTA*

馃嵎馃嵔馃


馃懇馃徑鈥嶐煃硚(the amazing cook)~馃懇馃徑鈥嶐煃�




馃嵆馃崪馃馃嵅馃崨馃崫馃馃尟馃崲馃馃崶馃崵馃崳馃嵄馃嵅馃崱



By mmn walid and walida (mrs aliyu)



Marubuciyar
*tawa kaddarar*
*dangin sa*
*uwata*
*rabo na ce* to be continued in shaa Allah



Page 1馃尮




"Sai yanzu kika dawo 拼ar iska tun 蓷azu da aka aike ki 蓷ebo ruwan sai yanzu kika ga daman dawo wa kuma kina ji na nace miki sanwar wake da shinkafa zan 蓷aura da ruwan shine kika je kikai zaman ki don kina min ba茩in cikin ku蓷in da zan samu ko, shegiya da fuskar kamar ta aljan"



Duk wannan fa蓷an da inna harira bata taimakawa 拼ar yarinyar da take 蓷auke da ruwa akan ta, duk kuwa da ganin cewar yarinyar ta gaji sosai



sai da tayi ta gama sannan ta sauke,
"kuma kije gonar malam ki wo min in kin ga dama ki da蓷e kamar kinje lahira gaida iyayen ki"


茒an 蓷ankwalin da take 蓷auro karar ta 蓷auka tayi waje da shi, directly gonar ta nufa wanda bashi da nisa da gidan ta 蓷ebo karar sannan ta kama hanyar gida tana yi tana nishi daga gani yunwa ce da kuma gajiya a tattare da yarinyar



Da sallamar ta ta shiga gidan ta ajiye karar sannan ta zundumi ruwa a randa ta 蓷an sha ka蓷an bata san ta cikawa cikin ta ruwa



"shiga madafi ki 蓷auko ragowar 蓷umame ki don yadda kike zaro min idandinan nan naki a cikin wannan ba茩ar fuskar taki ai wannan sai in mummunan mafarki"




Abincin ta 蓷auko zata fara ci kenan inna harira ta kuma saka ta aikin hura wuta na wake da shinkafar da take saidawa



A bakin murhun ta zauna tana hura iccen tana cin sandararran tuwon dawan da idan aka jefe ka da shi sai kaji ciwo saboda tsabar taurinsa



Sai da ta gama girka wake da shinkafar tsab sannan ta kwashe a 拼ar fantekar da ake kwashewa sannan ta gayaws inna harira ta gama


"lantana lantana", inna harira ta kira 拼ar ta da ke yi mata talla don kuwa asmau bata da kan inna harira tace yadda fuskar ta take ba茩a haka ma kwakwalwar take sam babu haske a tattare da ita



Asma'u ce ta 蓷au fantekar inda lantana ta shige gaba suka tafi tallan haka suke yi kullum ita lantana itace me kan talla amma ban da asma'u



Sai bayan sallah la'asar sannan suka dawo inda suka tarar da inna harira da ba茩uwa a zaune a tsakar gida akan tabarma



茦walawa asmau kira tayi ta 茩arasa inda take sannan ta nuna wa matar asmau

"hjy kina ganin zatayi, don ni 拼ar nan babu abinda take min anan, kullum sai dai taci tayi kashi kan talla babu shi yanzu in ta tashi aure wazai mata kayan 蓷aki, ga shegen ba茩i kamar kwalta"



Matar da aka kira da hjy ta dubi asmau sannan tace

"to ba wai baza tayi ba kamar yadda na fa蓷a miki abuja ni fa nake kai yara aikatau, wannan kuma kamar yarinya ce"


"ahap haka kike gani ai wannan in ta kama aiki kamar jaka haka take, reno shara wanki wanke wanke duk ta iya"



Hjyr ta kuma kai duba asmau wacce kan ta yake a 茩asa sannan ita sam bata fahimci inda zancen su ya dosa ba


"ni dai da waccen ce" ta fa蓷a tana nuna lantana 拼ar inna harira, inna harira sai tayi dariya irin ta basarwan nan


"haba bazaki so ki蓷au wannan ba ai alan茩osa ake ce miki indai lantana ce ba abunda zata iya, yanzu tallan wake da shinkafar da take kai min ma tace zata dena tunda 蓷an me gari yace yana sonta shi yasa nake neman hanyar da ku蓷i zasu dinga shigo min, ga bikin lantana ban ajiye ba ban ba wani ajiya ba, kuma auren 蓷an me gari kashe ku蓷i gare" ta fa蓷a tana ajiyar zuciya


"to shike nan indai kince wannan 蓷in zatayi ai shike nan, amma idan na tafi da ita kuma aka 茩i 蓷aukar ta zan dawo miki da ita"


"na yadda amma kice su fara gwadata tukunna kafin su yanke hukunci da wannan 蓷an 茩aramin jikin nata shine yake sawa mutane suna yi mata kallon yarinya ce"



Sukai sallama kan kashegari da asuba zata zo 蓷aukar asmau zuwa garin abuja aikatau



***********************



Asmau sunana na kasance ni ka蓷ai a wajen iyaye na babana 蓷an nan garin ne azore wanda yake a 茩aramar hukumar minjibir ta jihar kano,



Garin fulani ne sosai don gida tsilli tsilli zaku dinga gani in kun shigo sannan sai kuma gonar mutum a jikin gidan sa, irin dai ginin fulani, in kaga gida 蓷aya sai kayi tafiyar mill kafin kaga wani



Ban san iyaye na ba kasancewar sun rasu, mahaifiyata ta rasu lkcn haihuwar 茩anina, inda aka rasa aka rasa 蓷an,



Shi kuma mahaifina sai da na 蓷an tasa ka蓷an sannan Allah yayi masa rasuwa, sai kulawata ta koma hannun wan mahaifina



Inda yake min rikon sakainar kashi, don kuwa babu ruwan shi da duk wani daya shafe ni duk abinda matar shi zatai min baya cewa komai wannan shine ta茩aitaccen tarihi na


******************




Da sassafe hjy ta zo mukai sallama sannan muka kama hanya inda naci karo da wasu 拼ammata wa蓷anda zamu tafi da su, amma duk sun girme ni don ni sai na zama kamar wata 拼ar tsana a ciki su



Sai da muka je gezawa sannan muka samu 茩aramar mota inda zata kaimu abuja, haka aka cunkusa mu a motar nan kamar dabbobi inda ita kuma hjyr ta zauna a gaba ita ka蓷ai



Tafiya ce kamar ta yada shege ba 茩a茩茩autawa sai da muka je kaduna sannan direban ya tsaya muka fito muka 蓷an huta, sannan muka kama hanyar abuja




Lfy 茩alau muka isa abuja inda muka sauka a kubuwa, anan gidan hjy yake, 蓷aki ta bamu guda, tace duk mu sauke kayan mu




Ni dai kamar an min duka haka nake ji don kuwa a gajiye nake, kwanciya nayi sai bacci, inda 拼ammatan da muka zo da su kowacce take ta buri tare da fatan irin gidan da za a kaita, ni dai tunda na samu bacci ya kwashe ni sai nace saba'ul khairi



馃懇馃徑鈥嶐煃� menu of d day馃懇馃徑鈥嶐煃�
*wake da shinkafa served with local salad & zobo drink*


馃嵅 ```wake da shinkafa```馃嵅


```ingredients```

```wake```
```shinkafa```
```gishiri```
```man gya蓷a```
```ha蓷in salad```


```method```


1) bayan kin gyara waken ki saki ki wanke ki 蓷aura akan wuta, sannan ki bishi da ruwan kanwa (optional)

2)sai waken ya dahu, sannan ki 蓷auko wankakkiyar shinkafar ki ki zuba ki juya ki saka 蓷an gishiri sannan ki rufe


3) idan ya dahu sai ki sauke ki yi serving da soyayyan man gya蓷a, ko tankwa, da yaji sai kiyi ganishing da salad aci lfy


*LOCAL SALAD*

```ingredients```

cabbage
lettuce
carrot
cucumber
green pepper
lemun tsami
man gya蓷a
maggi


```method```

1) ki wanke lettuce, cabbage, cucumber, green pepper 蓷inki, ki barsu su tsane sannan sai ki yanka su irin yankan da kike so




2)ki kankare bayan carrot sannan ki wanke shi daga nan sai ki gurza shi


3) ki 蓷auko kayan ha蓷in da kika yayyanka ki ha蓷a da carrot sannan ki ha蓷e su waje 蓷aya, ki 蓷auko lemun tsami ki 蓷iga ka蓷an ba dagawa ba yadda dai zai miki sannan ki zuba mai ki zuba maggi ki juya sai ki juye a salad bowl sai ci




*zobo drink*

```ingredients```

Ganyen zobo
Citta
Kanunfari
Abarba
Cucumber
Sugar
Flavour


```method```

1) ki 蓷auko zobo sai ki wanke shi ki zuba masa ruwa ya sha kansa sannan ki 蓷aura a wuta, tare da citta, 蓳awon abarba, sai dakakken kanunfari ( ```sirrin daka kanunfari shine 茩amshin shi ya fi fitowa idan an daka shi akan a watsa shi haka```)


2) idan zobo ya tafasa ya dahu sai ki sauke shi ki juye a babban mazubi yadda zai sha iska, kafin ya huce kuma bari mu ha蓷a ragowar

3) ki fere yanka abarbar da cucumber ki 茩anana yadda dai zasu miki da蓷i wajen blending sai ki marka蓷a su kina yi kina tacewa kina 茩ara marka蓷awa har dai a samu yadda ake so

4) sai ki 蓷auko wannan zobon naki ki tace ki 蓷auraye ganyen ki kuma tace wa har sai maa shaa Allah, sannan ki ha蓷a da ruwan cucumber & abarbar nan


5) ki zuba sugar, flavour ki zuba a jug a saka shi a fridge yayi sanyi sai shaa


馃懇馃徑鈥嶐煃� *Bon appetit*馃懇馃徑鈥嶐煃�


*ASMA'UN SABIT*
🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛


👩🏽‍🍳~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩🏽‍🍳




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠



ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)



page 2 🌹






Kashegari da sassafe aka tashe mu, koko da ƙosai aka bamu, muka karya sannan hjy ta tasa mu a gaba domin neman wa kowa gidan aiki



Muka dinga zagaya gari zuwa gidajen masu hannu da shuni da kuma masu matsakaita ƙarfi ana ajiye mu da ɗai ɗai,



Sai da ya rage mu biyu sannan muka hau mota muka nufi wuse zone 4 kamar yadda naji hjyr tace wa driver taxi ɗin da muka shiga



A ƙofar wani restuarant muna sauka inda muka shiga ciki,




Hjy ce ta nuna mana wani ɗan loko wai mu zauna a can kafin ta dawo, kusan minti biyu ta ɗauka sai gata inda ta kira mu muka bi ta cikin gidan



Wata mata ce muka samu tana zaune a saman wata three sitter daga gani itace me wurin

"gasu nan kamar yadda na faɗa miki su biyu ne" matar da ke zaune a ɗakin ta gyara ɗan glass ɗin da ke fuskar ta sannan ta kalle mu kamar ta ga wasu kashi ko abun ƙyanƙyami



"me zanyi da waɗannan jariran" ta faɗa a wulaƙance

"na faɗa miki indai zaki kawo min ƴar aiki babba nake so amma me zan yi da waɗan nan, gwara ma waccen amma wannan kamar ba a daɗe da yaye ta ba"


Ta ƙarashe zancen ta idon ta akaina


"wallahi hjy munnira ƙaramin jiki gareta amma da shekarun ta"




Mahawara suka fara yi inda hjyr da ta kawo mu ta fi hjy munnira baki don haka dole hjy munnira ta yadda ta ɗauke mu bayan an sani shara nayi



Sai da suka gama cinikin abinda za a dinga biyan mu a shekara sannan hjy tai sallama da mu, ita kuma hjy munnira ta kira wata laure wai ta tafi da mu ta nuna mana aikin daya dace mu



Can bayan gidan muka je inda anan ake duk wani hada hada na girki, ƙaton kitchen ne, sai kuma wajen wanke wanke sai kuma wasu ɗakuna guda biyu da ke can gefen daga ƙarshen katangar inda anan akace mu ajiye kayan mu



Kowaccen mu aka haɗa ta da aikin daya dace da ita, ni dai kitchen aka kai ni inda wacce muka zo da ita aka kai ta wajen wanke wanke




Ina shiga kitchen, naga girman kitchen ɗin, ban taɓa ganin irin wannan kitchen ɗin ba sai yanzu



Girki ake yi kamar ba gobe, tsayawa kawai nayi ina kallon ikon Allah tare da ƙarewa kitchen ɗin kallo,



"ke ya sunan ki" naji wata ta faɗa

"asmau" na faɗa a hankali, kallon banza naga ta bini da shi

"ke amina waye yace a kawo mana ƴar jaririyar nan kitchen mu da muke aikin wuta" ta faɗa kamar taga kashi


"hjy ce tace a kawo ta nan" inji wacce aka ƙira da aminar

"to sai sa ta tsabtace jikin ta don nan bama gayyata ƙazanta" sim sim sim na fice inda na nemi hanyar da ɗakunan kwana suke



Ƴar jaka ta na ɗauko, sam babu wasu kayan arziƙi don duk kayan da nawan yawancin su ba wanki, wasu kuma a yayyage


Zama nayi ina kallon ikon Allah, ban jima da zama ba sai ga wata ta shigo

"me kike yi a ɗakin nan bayan kowa yana waje yana aiki, kar dai bincike kike mana a kayan mu"


"wallahi ba haka bane, wanka akace inzo inyi in canza kaya kuma naga kayan nawan duk babu wanki" na faɗa d ido na duk ya kawo ruwa saboda banji daɗi zargin da tai min ba


Jakar tawa ta zazzage a ƙasa ta fara duba kayan cikin ta, bakin ta a taɓe

"kije wajen wanke wanke ki samu ƙananan sabulai ki haɗa ki zo kiyi wanki"

Miƙewa nayi na fita, nai mamakin dana ƙarasa wajen wanke wanke na samu sabulai, kamar ba da kuɗi a ka siye su ba, tsinta na fara yi har na haɗa iya wanda nasan zai ishe ni sannan na tafi ɗakin


Kaya na na ɗiba sannan na je bayan ɗakin inda banɗakin mu yake na wanke kayana tas sannan na shanya



Wanka na shiga da ragowar sabulun na saɓi jikina kamar ba gobe, don a



Don kuwa a azore ban isa in samu wannan damar ba, sai dana gama wanka na sannan na fito



Sai yamma sannan kayana suka bushe na kwashe, a ranar dai ban koma kitchen ba sai kashe gari


Cikin hukuncin Allah na fara aiki a kitchen amma ba abinda nake yi sai aike, dauko wannan ɗauko wancen haka dai



Kafin ka ce me wannan har na zama ƴar gidan, na son komai na kitchen, sannan na san inda ake ajiye komai


Gidan cin abincin hjy munnira gidane da a kullum a ke dafa kusan buhu biyu na shinkafa da ta tuwo


Babu irin variety na abincin da ba a yi, waina sinasir, alkubus fankaso, ta ɓangaren shinkafa ma


Jollof rice fried rice, duk dai wasu sunfari na dafa abinci ana yi, ba wai duka a ke ci anan ba, akwai waɗanda ake fita da su,


Don kuwa akwai certain hotels ɗin da suke zuwa suna yin order abinci anan gidan, ga kuma costomers da suke zuwa suna siya su tafi da shi



Ga waɗanda suke siya su ci anan, akwai wasu mutane ma da ake musu abincin gidajrn su anan, kullum akwai abincin da za a dafa na certain gida akai masa



Nakan yi mamaki amma dana ji cewar yawanci gidanjen ministers ne da house of reps da senators ake kai musu waɗanan abincin saboda mutanen da suke tarawa sai na daina mamaki duk da dai ban san ko su waye ba



don haka aiki a gidan nan in aka tashi tun safe sai mukai ƙarfe 10 :00pm bamu gama ba


Amma kuma mu girki ne kawai akwai ƴan wanke wanke, akwai kuma ƴan service, akwai masu kaiwa gidaje, group group ne kowa da group ɗin sa kuma kowa ya san aikin sa



******************



*b̫a̫y̫a̫n̫ s̫h̫e̫k̫a̫r̫a̫ b̫i̫y̫u̫*




Na zama ƴar gida yanzu don kuwa ba abinda bana shiga ayi da ni ta ɓangaren girki,


A lokcn ne hjy munnira ta ƙara buɗa restuarant ɗinta inda yanzu babu abinda ba a yi, snacks ne ɗrinks ne, duk daia abinda kake so idan ka zo restuarant ɗin mu,


Kuma kullum cikin hukuncin Allah ƙara samun costomers muke yi, yanzu ba a shakkar bani girki ko ya yake don kuwa a gaskiya na iya



Kasancewar ni ce ƙarama a kitchen yasa kowa sai kaji yace asmau don Allah juya min kaza, kwashe kaza, wannan ne ya sa ni ko wane ɓangare na kitchen ina shiga


Ba kamar cooks ɗin kitchen ɗin ba, yadda in a ɓangaren sarrafa shinkafa kake to ana zaka zauna, in a ɓangaren snacks kake to anan zaka zauna, haka ma in a ɓangare drinks kake ko miya ko salad ko wani abu na kitchen



Ma'aikatan a rarrabe suke kowa yasan aikinsa, amma banda ni, ni ina kowane ɓangare kuma duk inda naje sai na tabbatar da cewar na koyi abunda suke


Wannan ne yasa a kitchen ɗin nai fice tunda komai aka bani zan iya kuma zan yi shi kamar ba ƴar ƙaramar yarinya ce tayi ba



*****************


Sabit yana zaune a office ɗinsa cikin fararen yadinsa waɗanda kana kallon su kasan ba ƙananan kuɗi aka sa wajen siyan su ba, wayace a hannunsa yana ta danna wa


Tun ɗazu yake kiran ta amma bata ɗauka ba, tsaki ya ja tare da ajiye wayar

"wallahi sam banga amfanin wayar mata ba ace mutum sai yai ta kiran ki a waya amma wai bakya kusa da wayar" be gama mitar sa ba sai wayar tashi ta fara ringing


Tune ɗin daya saka mata kenan don haka wayar tana fara ringing ya gane ita ce, idon shi ya kai kan screen ɗin wayar inda aka rubutu *only u*


Ɗan tsaki ya kuma sannan ya ɗauka a yangance kamar wani mace

" *SD* don Allah kayi haƙuri wallahi ina sallah ne ka kira" duban shi ya kai kan agogon bangon ɗakin inda ya ƙarfe 03 :15pm


*only u sallah me kike yanzu kar dai kice min azahar"

" wallahi *SD* na shiga meeting ne shiyasa ban samu nayi sallah akan kari ba, ya kake "


"amma meeting sai ya hana ki sallah wai sai yaushe zaki san mahimman cin sallah haba only yanzu haka zamu yi aure ki dinga nuna wa yaran mu, yanzu lkcn sallah bazaiyi ba a bar abinda ake yi a tafi ai sallah ba"

" *SD* kasan matsalar bank fa su koman su a ka'idance yake kar ka damu in shaa Allah tarbiyya me kyau zan muyi wa ƴaƴan mu, kaji"


Ta shiga kalailaye shi da kalaman da tasan suna kwantar masa da hankali kafin kace meye wannan har sun koma kamar ba abinda ya faru,



Sai da suka gama shan soyayyar su sannan sukai sallama akan zai zo da daddare, daga nan sukai sallama kowannen su zuciyar su tana alfahari da kuma ƙaunar junan su





👩🏽‍🍳 *Menu of d day* 👩🏽‍🍳

🍲```Veg cous cous with kidney sauce``` 🍲


```ingredients```

_Cous cous_
_Butter_
_Cabbage_
_Peas_
_Carrot_
_Canned sweet corn_


```recipe```

1) ki wanke carrot ki yanka shi size ɗin da kike so, sai ki wanke peas sai ki haɗa su ki tafasa su da ɗan gishiri, tafasa ɗaya sai ki sauke ki wanke su da ruwan pampo wannan wankewar zai sa su suyi shar kuma su rike kalar su sai ki ajiye a gefe


2) a wanke cabbage a yanka sannan a ajiye shi aside, sweet corn ɗin shima a tsane ruwan shi a ajiye shi gefe


3) ki ɗaura ruwan zafi, idan ya tafasa, sai ki ɗauko cous cous ɗinki a cikin bowl, sai ki ɗan zuba masa dan ruwan zafin, ba dayawa ba ya ɗan sha, *a zuba yadda bazai yi wa cous cous yawa ba* sai ki ɗan bari ruwan ya tsotse

4) ragowar ruwan daya ke tasafa a kan wuta sai ki saka colander ```(in babu colander zaki iya yin na buhu amma a tabbatar da buhun be taɓa ruwan ba)```a kan sa, sannan ki kawo jiƙaƙƙen cous cous ɗin ki, ki zuba, ki kawo kayan peas da carrot ki zuba ki rufe ya turara


5) idan ya ɗanyi wani lkc kika buɗe kika ya dahu sai ki sauke, ki juye cous cous ɗin a wata roba, ki zuba melted butter, da sweet corn da kuma cabbage sannan a juya a zuba a food flask
~bon appétit~


```kidney sauce```


```ingredients```

_Kidney_
_Attaruhu_
_Albasa_
_Maggi_
_Man gyaɗa_
_Tomato paste_
_Curry_
_thyme_


```recipe```

1) a wanke kidney a cire tsakiyar nan don kuwa wataran har tsakuwa ake gani


2)sannan sai ki tafasa ta da albasa da maggi da thyme, idan ya tafasa sai ki tsame ta a gefe


3) a grating attaruhu da albasa, ki saka

Please Login or Register in order to submit comment