Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*🗯️MADADI!!💍*
_(Ba Haram Bane!!)_

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
~~~~~~~
*MANAZARTA WRITES ASSO*📚🖊️
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~
~~~~~~~

*'Kir'kirarren labari ne kuma ba'ayi dan aci zarafin wani ko wata ba. Wanda yaga yayi dai-dai da yanayi na labarinsa to a rashin sani ne*
~~~~
*Ban yarda a sauya min salon labari ta kowace siga ba, wanda ya sanja min labari na ta wata hanya daban to ban yafe ba*
~~~~~~

*NASIHA*
```A wasu lokotan sauyi na rayuwa yakan zowa mutum. misali da farko kana cikin 'kunci sai Allah ya saukar maka da farin ciki wanda zai sa ka manta ba'kin cikin ka na baya. Idan kaga haka ya kasance da kai/ki to tabbas ka/ki ji'banta dukkanin al'amuranka ga Allah. Na biyu kuma kana cikin farin ciki katsaham! Ubangiji sai ya saukar maka da ibtila'i na rayuwa gabad'aya al'amuran ka su dagule! To idan irin haka ta kasance da kai sai ka nutsu kayi tunanin shin wane laifi kayi wanda Allah ya saukar maka da ibtila'in rayuwa, kada ka/ki ce bari kaje gurin malaman duba su duba maka ko wani ne yayi maka asiri daga ka/kin aikata hakan shikkenan ta'bewa da lalacewa ta tattara a kanka ko a kanki, idan ka/ki fad'a ko wane irin bala'i na duniya Ubangiji kad'ai zaka/zaki fuskanta da matsalarka lokaci guda zai magance maka/miki, Allah ba'a had'ashi da abokin tarayya! Idan ka kuskura ka had'a Ubangiji da wani to zaka/zaki dawwama cikin 'kunci da lalacewa har 'karshen rayuwar ka/ki.```


*SADAUKARWA GARE KU*
'Yan Uwa Rabin Jiki♥️

*SADDIQA UMAR ABBALE*
*HALIMATU UMAR ABBALE*
*NAJA'ATU UMAR ABBALE*
~~~~~~~~~~~~~


*1*
"Innalillahi wa'ina ilaihi rajiun."! Abinda Baba Talatu tafad'a kenan ta kalli Saddiqa dake gefe a tsaye tana hawaye tace" Yi sauri ki d'ebo ruwa suma tayi." Saddiqa ta futa daga d'akin da sauri, karo suka ci da Baba Malam da Babban d'ansa Alhaji Magaji." Baba Malam yace." wato dai har yanzu Kuka kuke yi ko da alama dai kuna so ku hana Halima ta kwanta lafiya a kabarin ta." Tana girgiza kai had'e da 'kokarin mayar da hawayen idonta tace"Baba Malam mun daina kuka Yaya Naja'atu ce tafad'i ta suma shine Baba Talatu tace na d'ebo ruwa." Da sauri Baba Malam da Alhaji Magaji suka shiga d'akin. ita kuma ta futa da saurin gaske, ruwa ta d'ebo cikin kofi ta shigo d'akin dashi.
Baba Malam dake tsugune kusa da Naja'atu yana mata addua ya kar'bi ruwa ya shiga yayyafa mata a fuska, Baba Talatu hawaye kawai take sharewa tana girgixa kanta.
Baba malam sai da ya yayyafa mata ruwan sau uku sannan ta saki wata ajiyar zuciya mai kar'fi! idanunta ta shiga kiftawa, sai ta mi'ke zaune da sauri ta shiga rarraba idanunta a kansu.
Baba Talatu ta ri'ke hannunta tana fad'in "Naja'atu kiyi hakuri kada ki jazawa kanki lalura." Ihu! ta zumduma! tasa hannu ta toshe kunnuwanta jikinta na wata iriyar kyarma! tace"Baba Talatu kunnuwa ba zasu iya d'aukar wannan maganar taki ba! a ina aka ta'ba haka *Uba ya Auri 'Yarsa* ashe dama dake da Baba malam dashi kansa Abban nawa dukkanin ku maguzawa ne ku baku san addin........Kafin ta 'karasa Alhaji Magaji ya kwad'a mata mari! yace."Ke ki nutsu ki shiga hankalin ki bama son shirme da shashanci ki saurara ayi miki bayanin yanda al'amura suke."

A zabure! ta mi'ke tsaye! kamar wacce zata tada iska tace"Baba Magaji ni bazan fuskanci komai ba ba kuma zan nutsu ba, saboda ni ba kafura bace wallahi sai na kashe kaina idan kuka d'aura min aure da Ubana, wai baku ji sunansa bane Abban Naja'atu fa sunansa amma shine zaku daura mun aure dashi! to dukkaninku sai na kaiku *Hizbah!.* Ta'karashe maganar tana wani irin kuka mai cin rai.

Baba Malam ya goge guntin hawayen idonsa ya ri'ke hannunta da fad'in "Auta zauna ni da kaina zan warware miki abunda baki sani ba." Fuzge hannunta tayi tana 'kokarin tsallakeshi ta wuce! Alhaji Magaji yayi sauri tare mata hanya Yace."Naja bakya jin magana ko? To shikkenan idan baki kaimu *Hizbah* bakya 'kaunar Allah." Yafad'a babu wasa a tare dashi.
Hannunsa ta ri'ke jikinta sai mazari yake tace"Abba Magaji ka duba maganar nan da kyau fa! Kayi duba na tsanaki! ya za'ayi dan kawai Mamanmu ta mutu sai suce zasu d'aura min aure da Ubana wace irin rayuwa ce wannan."!!! Tafada cikin wani irin sauti!! Shima a fusace! Yace."Wai ke waye ya fad'a miki Alhaji Abbas Ubanki ne."!? Shuru tayi tana binsa da wani irin kallo! bakinta sai rawa yake yi. da kyar ta iya bud'e bakinta tayi magana....."Baba Magaji bangane maganar ka ba."! murya na rawa tayi maganar, Baba Malam ya zaunar da ita kusa dashi hannunsa cikin nata ya rike sosai yana kallonta, tausayi take bashi sosai, tabbas yasan dole ne ta shiga rud'ani da tashin hankali sakamakon bayyanuwar abinda yake rufe tsayin shekaru goma sha shida! da suka wuce. Wanda ta d'auka a matsayin mahaifinta dashi ake maganar d'aurin aure a tsakaninsu, babu shakka duk wanda ko yaji wannan lamarin dole ya shiga halin d'imuwa da tashin hankali

'Dakin ne yayi shuru na tsayin mintina uku kowa jikinsa yayi sanyi mussaman Naja'atu wacce take jin wata irin fargaba da fad'uwar gaba, tunda Abba Magaji yayi furucin cewar ba Abba Abbas ne mahaifinta ba take wata zabura tana rarraba idonta a kansu bakinta motsi kawai yake tana so tayi magana amma ta rasa me za tace! fashewa tayi da wani kukan tana kallon Baba Malam da kansa yake sunkuye sai zufa yake gogewa, tace"Baba malam kuna so nima na mutu ko? kuna so kamar yanda kuka rasa mamana nima ku rasa ni ko ? zuciyata daf take data daina aiki sakamakon bala'in da kuka jefata a ciki! Baba Magaji yace wai Abbana bashi ne Ubana to shikkenan sai ku fad'a min wanene ya haifeni."? Murya na rawa ta 'karasa maganar.
Baba Malam ya d'ago kansa a nutse yace."Naja'atu Nine Ubanki ni na haife ki Alhaji Abbas Uban ri'kon ki ne kuma miji ga 'yar uwarki Halimatu." wani irin kallo ta shiga yi masa tana girgixa kanta sai hawaye ya wanke mata fuska! murya a sanyaye tace"Baba malam ya akayi haka? ya kuka yi mun wasa da hankalina? ni ban yarda kaine mahaifina ba, Abba Abbas shine Ubana shi na sani tunda na taso shine yaci dani yasha dani ya tufartar dani ya tsaya a kaina nayi karatu kuma shi nake so ya aurar dani ga mijin dana za'bawa kaina."! Ta'karasa maganar cikin yarda da abinda take fad'a.
Abba Magaji ya fusata! sosai ya bud'e baki zaiyi magana Baba malam ya d'aga masa hannu yace."Kada kayi mata tsawa ko ka hantare ta, dole ne dama haka ta kasance da ita damu bakid'aya, ha'kika mutuwa itace ta janyo mana wannan tashin hankalin dan da Halimatu na raye to babu shakka Naja'atu zata cigaba da zama a matsayin 'yar data haifa alhalin kuma 'kanwa take a gareta, Yanzu zamu bari ta nutsu tukkuna zuwa dare sai mu sake wani zaman domin mu sanar da ita abinda ya faru a baya wanda bata sani ba." Abba Magaji ya sauke ajiyar zuciya a nutse yace."Shikeenan Allah ya za'ba abinda yafi alkairi." Baba Malam ya amsa da amin kana ya mi'ke suka futa a tare.

Suna futa, Naja'atu ta kalli Baba Talatu tace"Baba dan Allah dan annabi kada ki bari al'amarin nan ya tabbata, ke macace ce mai hankali da sanin ya kamata kuma kina zuwa isilamiyya kin san dai haramun ne Uba ya auri 'yar sa ko."? A zauce! take maganar.

Baba Talatu tace"Naja'atu Alhaji Abbas ba Ubanki bane an fad'a miki Mijin Yayar ki ne Halimatu Allah ya ji'kanta, Alhaji Abbas kinga wacce ya haifa nan ita da 'yan uwanta su Mussadiq.'' Ta nuna mata Saddiqa dake zaune a kusa da ita.

Wani irin kallo ta shiga binsu dashi tana girgiza kanta, ta rasa a'ina zata ajiye wannan babban al'amari a cikin zuciyarta, *Abbah Abbas* ba shine ya haife ta ba *Baba malam* ya haife ta? anya kuwa da gaske suke wannan maganar ko dai kawai suna so bukatarsu ta biya ne gurin ganin sun d'aura mata aure da *Ubanta* tabbas dole ne ta nemawa kanta mafita dan ita kam bata yarda da wannan maganar da suke ba.
Tana kallon Baba Talatu da Saddiqa suka suka futa daga d'akin, ta shiga girgiza kanta tana masifar mamakin a'lamarin, kwanciya tayi kan tabarmar dake shimfid'e a dakin ta shiga tunano rayuwar ta ta baya tare da mutanan data dauka a matsayin iyayenta.




*GA MASU BUKATAR KARANTA BOOK DIN ZASU TURA #400 SINGLE, VIP GROUP #600 GA ACCONT D'IN DA ZA'A TURA KUDIN.......0542382124.....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATIN WAYA ZAKI TURA KIYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBAR......07084653262.....IDAN KIN SAN BA BIYAN KUDIN LITTAFIN NAN ZAKI YI BA DON ALLAH KADA KI KIRA WAYA TA KO KIYI MIN WATA MAGANA TA WHASAP*

*MUTANAN MU NA NIJAR IDAN KUNA SO KU BIYA KUDIN LITTAFIN ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN NUMBARS.........90899076_88137740 KATIN AIRTAL KO ORANGE.*
[10/15, 1:05 PM] Gagarabadau👺: a

*🗯️MADADI!!!💍*
_(Ba Haram Bane!!!)_

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
~~~~~~~~
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi._
~~~~~~~~
~~~~~~~~


*SADAUKARWA GA DUK WANI A HALINA DAKE CIKIN WANNAN UNGUWA♥️*


*2*
*'Kofar Na'isa* Unguwa ce mai cike da d'umbun tarihi, duk wanda ya kwana ya tashi a cikin birnin kano ya san da zaman unguwar. 'kofar na isa unguwa ce ta malamai masana addini da kuma 'yan boko masu aiki da iliminsu, duk wanda yake mu'amula da d'an cikin unguwar zai gane cewar suna da wani irin quality wanda Allah yayi musu, saboda sun iya mu'amula da mutane sosai! akwai masu kudi a unguwar akwai marasa karfi a ciki, dai-dai gwargwado masu rufin asirin dake cikin unguwar suna taimakawa marasa shi mussaman da azimi suna hidima sosai da sosai da wuya kaji ance maka ga wata hatsaniya ta tashi a unguwar irin ta *Daba!* ko kuma *Sace-sace* dai-dai gwargwado suna bawa yaransu tarbiya had'e da ilimin addini dana boko!

Alhaji Sama'ila mai kwano wani attajirin mai kudi ne a cikin unguwar wanda yayi suna sosai dan idan kana neman gidansa daga bakin titi ka ambaci sunansa za'a nuna maka Alhaji Sama'ila mai kwano mutum ne mara ganin 'kyashi mai kaunar dan uwansa da ma'kotansa, Yana da 'yaya Uku kacal wanda matarsa Hajiya Abu ta haifa masa su, Biyu maza mace d'aya, amaryarsa mai suna Hajia Rabi bata ta'ba haihuwa ba tsayin shekarun da sukayi a tare! Yana zaune da ita haka dan shi mutum ne mai mi'ka al'amuransa ga Allah yasan tabbas Allah ne ke bada haihuwa kuma shine yake hanawa.
*Ramlatu* itace babba a cikin 'yayansa sai wanda yake bin ta, Abbas sai Alhasan shine na karshe! tunda su Abbas suka taso a cikin unguwar nan suka ga yanda mahaifinsu ke mu'amula arziki da makotansa sai suma suka fara kwantantawa, hakan yayi wa mahaifin nasu dadi sosai ya kuma 'kara nuna musu cewar hakan da sukeyi shine dai-dai dan cikin jinsin mutunan da Allah ya hallita a duniya babu wanda yafi wani a gurinsa sai wanda yafi bauta masa, kada su nuna sunfi karfin yin mu'amula da wanda suka fi rufin asiri, to babu shakka watarana Allah zai iya 'kwace damar dake hannunsu ya mi'kawa wanda suke ganin bai isa ba......Wannan dalilin ya sanya suka saki jikinsu da kowa suke mu'amula a cikin unguwar tamkar sauran mutane.

'Karamin gida ne madaidaici mai kofa gami da dakalin siminti a kofar gidan, gidan na kallon gate din gidan Alhaji Sama'ila hanya ce kawai ta raba tsakaninsu! Malam Baba shine mai wannan gidan, kamilin mutum nitsatstse mai kamala da dattako, malam baba mutum ne shi mai yawan ibadah da karatun al'kur'ani kusan duk azimin yana zaman tafsiri a kofar gidansa, inda Alhaji Sama'ila ke sawa ana fito da sadaka daga gidansa, akwai jituwa mai kyau a tsakaninsu dan sai nace halinsu ne yazo daya na gudun duniya shiyasa suke zaune lafiya da kowa, Alhaji Sama'ila ya dauki ragamar gidan Malam Baba a hannunsa ba wai dan shi malam din ya gaza ba Malam na futa sana'arsa kuma sa'i da lokaci al'amajiransa na kawo masa abun arziki gidansa babu yunwa ko kad'an! malam nada 'Yaya Uku wanda suka haifa tare da matarsa Baba Talatu Babban cikinsu shine Adamu wanda yaci sunan mahaifinsa sai suke kiransa da Magaji, Halimatu itace ta biyu sai kuma Naja'atu da tazo a karshe! Lokacin da suka haifeta har sun cire tsammani da sake haihuwa sai kuma Allah ya kawo cikinta, lokacin Halimatu na daf da kammala secondary skuul lokacin tana da shekara goma sha shida a duniya.

Tsakanin Abbas da Magaji akwai jituwa sosai suna abota mai kyau da tsabta komai nasu tare sukeyi karatu tare su d'inka kaya iri daya hula iri d'aya takalmi iri daya kai hatta da agogo iri daya suke daurawa! Sai kuma Allah yasa shekarunsu suka zo daya da juna yanzu haka suna matakin shekaru talatin da d'aya koda biyu Lokacin ne kuma iyayensu suka fara yi musu maganar aure dan sun riga sun mallaki hankalin kansu! kuma suna zuwa kasuwa suna harkokinsu, Alhaji Sama'ila yanzu ba ya fita kasuwa sosai su ya d'ora kan harkokinsa na yau da gobe! Alhaji Sama'ila nada shaguna sama da talatin a cikin kasuwar sabon gari kuma dukkanin rumfunan sa harkar siye da siyarwa akeyi a ciki, suna harkar kayan rufin gida da kofofi da ta gogi sannan kuma yana da gidajen bulo suna buga bulo da harhad'a intar lock da ties, mutane da yawa naci da sha a karkashin wannan bawan Allahn, to ganin 'Yayansa sun kai munzali ne yasa ya d'ora su kan harkokinsa na kasuwa kwata-kwata baya nuna bambanci tsakanin Abbas da Magaji Abinda zaiyi wa d'ansa Abbas shi yake wa Magaji, har jama'ar unguwa na surutu kan cewar ba haka kawai Baba Malam ya barshi ba wasu suna gani kamar yayi masa asiri ne domin ya mallake shi shida dukiyarsa, wannan cece kucen da mutane keyi bai dameshi ba, dan saboda yasan Malam baba ba zai ta'ba cutar dashi da zuriarsa ba.


Mama Ramlatu babbar Yaya gasu Abbas tayi aure a cikin unguwar dan gaba dasu kadan cikin unguwar Tudun wuzurci! wanda ta aura yana da rufin asiri dai-dai gwargwado amma tana da kishiya, Ramlatu wata irin mata ce mai izzah da ta'kama! bata da hali mai kyau! Tayi ta wulakanta kishiyarta kasancewar ta yar talaka gorin yau daban na gobe daban! a duk sanda Alhaji Sama'ila zaiyi mata aiken kud'i ko kuma tufafi sai ya had'a da kishiyarta kafin ta bawa kishiyarta sai ta gama yi mata gori sannan! Ita kuwa da yake mai hakuri ce sai dai kawai ta girgiza kai ta kyaleta, gabadaya Ramlatu bata dauko halin mahaifinta da 'yan uwanta ba.
Lokacin data haifi 'Danta na fari! sosai Mahaifinta ya gatantata daki guda aka cika mata da kayan barka, shi kuwa maigidan mota guda ta kayan abinci ya sauke masa, aikuwa Ramtalu ta samu abunda take so shiga take tana fita tana sakin habaici da gori! Cewar da abincin ubanta mutum ke rayuwa sannan kuma da tufafin ubanta mutum ke tun'kaho! Allah Sarki Sakina kishiyarta tasan da ita take, sai ta shiga daki taci kunanta ta koshi kuma ta dauki aniya kan cewar idan mijin nasu ya dawo zata fada masa abinda ke faruwa a gidan dan gaskiya ita ta gaji da wulakancin da matarsa keyi mata, gabadaya ta lura Ramlatu bata san mutunci ba ba kuma tasan mai kyautata mata ba, tunda ta haihu take hidima da ita ta kasa zama ta hutu kullum a tsaye take amma babu sannu bare nagode kullum cikin fada mata bakar magana take to gaskiya ta gaji hakurinta yazo karshe kudi ai ba hauka bane.

Maigidansu na dawowa bayan yaci a binci ya huta sai ta shiga fada masa abubuwan da suke ta faruwa a gidan wanda shi bai san dasu ba, tabbas ransa ya 'baci sosai kuma ya sheda halin matarsa Sakina tana da hakuri sosai da kawaici ba zata takali Ramla da rigima ba duk da cewar itace Uwargida amma ta hakura da komai burinta ta kawo zaman lafiya da daidaito a gidin! Yace."Kiyi hakuri insha Allahu zan sameta nayi mata fad'a amma kada irin haka ta sake faruwa kiyi shuru da bakin ki duk abinda ke faruwa tsakanin ki Ramla ki sameni ki fada mun zanyiwa tufkar hanci." Tace."To insha Allah."


Lokacin da ya shiga dakin Ramlatu tana zaune gefan gado taci uwar kwaliya da less an turo dauri gaban goshi kana kallonta zaka fahimci 'Yar Alaji ce hannunta da kunnata gami da wuyanta duk Gold ne sai walwali take...Zama yayi kusa da ita ya mika hannu ya kar'bi yaron dake hannunta da ta gama bashi nono ya tofa masa addua kana ya kwantar dashi ya fuskanceta.......Babu cikakkiyar walwala a tare dashi yace."Yanzu Ramlatu abinda kikewa Sakina a gidan nan ya dace."!? Wani irin shan kunu tayi ta kumbura fuska tace"Me nayi mata ashe! zaunar da kai tayi tana fad'a maka karya da gaskiya ko."? Yace."Abinda Sakina za tayi nasa ni haka kuma abinda Ramla za tayi nasa ni dukkanin ku nasan halin ko wacce ba wai ina so nace Sakina tafi ki a gurina ba A'a dik matsayin ku d'aya a zuciyata, amma ki sani abinda kikewa abokiyar zamanki bai dace ba! wace iri ce ke mai manta alkairi? menene Sakina ba tayi miki ba, ina cewa gabadaya sai da kika daina girki sai dai ta dafa ta kawo miki har d'aki kuma hakan bai hanaki kwana da miji ba! idan muguwa ce ai zata hanaki ki kwana dani ba tunda itace take girki amma ta dafa ta baki kici kina kwance kuma ki rasa sakayya da zaki mata sai irin wannan."!! Fashewa tayi da kuka tace"Shikkenan to ai ba sai ka futo fili ka nuna kafi kaunarta a kaina ba, amma meye haka daga zuwa babu tambayar ba'asi sai ka kama wasu maganganu ai bani ce nace tayi min girki ba ita taga zata iya ta dauka tayi ni ba burgeni tayi ba, kuma koda ba tayi min girki ba zansa a turo mai aiki daga gidanmu tazo ta kula dani har na haihu."
Yace."Ni dai na fad'a miki wallahi duk sanda kika 'kara ci mata fuska ko kikayi mata gori kan wani abu da aka kawo shi gidan nan sai ranki ya 'baci!! Cikin 'bacin rai tace"To ai shikkenan tunda uwata ce ita sai na kwanta ta takani saboda tana da daurin gindi a gurinka, akan me? kai da ita kuna cin arzikina amma kuma kuce sai nayi muku biyayya wallahi ba zai yuwu ba.""! Takarasa maganar tana buga cinya."! Cikin fusata yace."Zanyi maganin ki ai shashasha mara tunani meye abinci da kike gori a kansa, meye kuma tufafi wanda zasu lalace su barki da mutum! to zanje na samu Alajin da kaina zan fad'a masa bana bukatar k'wayar abincinsa a gidana ko ya aiko dashi na dawo sai an mayar." A fusace ya mike ya futa daga dakin....Shuru tayi tana tunani addua take kada Allah yasa yaje gurin mahaifinta da wannan maganar tabbas tasan idan yaji matsalar daga gurinta ne to babu shakka ranta sai ya 'baci.

Aikuwa misalin karfe biyar da rabi na yamma ta fito daga wanka kenan wani yaro ya shigo gidan yana fadin "Wai Ramlatu tazo soro mahaifinta ne yazo.
Gabanta ya fadi da sauri tasa kayanta ta futa da tabarma a hannunta, tana zuwa soron sai taga Sakina a durkushe suna gaisawa da Alhajin, shuru tayi tana jinsa yana bata hakuri dangane da abubuwan da suke faruwa, koda ta gaishe shi 'kin amsawa yayi ya rufe ta da fad'a sosai yace kuma ta bawa abokiyar zamanta hakuri! tana kuka ta shiga bawa Sakina hakuri! Tace " Babu komai ta mike ta shiga gidan, Alhaji ya kalleta da fad'in "Wallahi Sakina duk sanda mijinki ya sake kai 'karar ki gurina to babu ni babu ke! dama ashe mugun hali ne dake ko? to na kara jin na kawo muku wani abu gidan nan kiyiwa wani gori ranar sai na 'bata miki rai! Hakuri take bashi tana share hawaye, ransa ya a 'bace! ya futa daga soron ya barta a tsaye hannunta ri'ke da tabarma.......To tun daga ranar Sakina ta samu lafiya a gidan Yanzu Ramlatu ta daina yi mata gori da kallon banza amma dai duk da haka idan 'yan wulakancin na kusa tana ta'bawa sai dai kawai ta kau da kanta domin dai a zauna lafiya.

****
Irin kulawar da Abbas keyi kan Halimatu ya sanya iyayensu suka ga kamar sonta yake yi, shi kuma ba haka bane a zuciyarsa kawai yana tausaya mata ne a matsayinta na mace kuma mai nakasa, Halima bata da lafiyar k'afa sosai kafarta ta dama ta samu tawaya tun tana yarinya anyi magani na hausa dana Asibiti tafiyarta bata dai-dai ta ba, sai kawai suka hakura suka bar mata hallitarta da alama haka Ubangiji ya hallice ta, kafarta ta dama itace take da nakasa ta inda in tana tafiya take jefata, Amma a fuska Halima bata da muni kyakkyawa ce sosai mai madaidaicin tsayi! komai nata cikin nutsuwa take gudanar dashi.

Magaji ya fitar da matar aure A lokacin da iyayensu suka bukata, shi kuma Abbas din har yanzu ya rasa wacce zai tsayar a matsayin uwar 'yayansa! Mutum ne mai ruwan idon tsiya ko wace mace ba tayi masa ba! Da kyar da ya tsayar da Halisa a matsayin matar da zai aura gidansu na bayan layi! kuma Halisa kawar Halima ce tare ma suke tafiya makaranta,

2 Comments On MADADI
avatar
sumayya-1-4

7 months ago

Reply

Hw can I get the complete text please

avatar
abasu-kala

7 months ago

Reply

Replying to sumayya-1-4

You have to pay 1k first for subscription in order to download our novels

Please Login or Register in order to submit comment