Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masifar tashi a dik sanda taga ya shiga gurin Haliman ya jima bai fito takan shiga tashin hankali da damuwa saboda tasan yana can yana shiriritar da ya saba da shegiyar yarinyar nan Naja'atu da Babynsa wacce ya sanyawa suna Fatima amma sai suke kiranta da *Saddiqa* dalili kenan da ya sanya take Allah Allah itama ta haihu itama taga yana nuna kulawarsa a kan d'anta.

Haihuwar *Saddiqa* ta janyo masa bud'i da alkairai da yawa, harkokin kasuwancinsa suka bude sosai yake harkar gwangila na gina gidaje da ma'aikatu da sauransu........Wani 'katon gida yake ginawa a cikin unguwar *Danbare* sabuwar unguwa ce da masu kudi suka siyeta suke ta gasar gidana gida a gurin, gaskiya gidan da yake idan aka gama aikinsa babu shakka zai zama abun kallo a gurin jama'a.


Halisa ta haihu lafiya lau ta haifi namiji kamar yanda Scanning ya nuna mata, sai dai kuma cikin ikon Allah kwanan yaron d'aya a duniya ya koma.....Ihu! ta dinga zabgawa tana kuka dan rashin tawakkali cewa take wallahi Halima ce tayi mata asiri d'anta ya mutu saboda tana bakin cikin ita bata haifi d'a namiji ba.
Abba Abbas tun yana rarrashinta har ta si'ke shi haushinta ya rufeshi, ya shiga nuna mata illar abinda takeyi, Allah ne ya bata kuma ya kar'bi abinsa dan me zata d'orawa wani! sai da yayi mata kaca-kaca! sannan ta daina ikirarin cewar Halima ce tayi mata asiri.


***
Bayan shekaru uku Halimatu ta sake haihuwa inda ta haifi 'Da namiji! Wanda wannan haihuwar ta janyo tashin hankali sosai a gidan dan iskokai Halisa ta dinga tayarwa na 'karya dana gaskiya tana yun'kurin kashe maijego da jaririnta......Babu arziki ya tarkata ta ya kaita gidansu dan al'amarin yafi karfinsa haka kawai yana ji yana gani ta illata masa d'ansa.
Ashe iskanci ne Halisa na ganinta a gidansu, sai ta dawo hayyacinta mussaman da mahaifinta ya samo malamai, masu ru'kiya suka dinga jibgarta, babu arziki ta dai-dai ta nutsuwarta ta dinga kiransa a waya yazo ya dauketa taji sauki!
Shi kuwa dama tuntuni ya yanke shawara kan cewar zai raba musu gurin zama, dan gudun aikata mummanan aiki idan baya nan shima ya fahimci duk wani abu da Halinsan keyi sharri ne da ba'kin kishi da ganin kyashi!

Gidansa dake *'Dan bare* suka tare shida Halimatu da 'yayansa kana yasa aka gyarawa Halisan wanda suka bari ta zauna a ciki yana ganin hakan shine yafi alkairi a tare dasu baki daya...
Wannan al'amari ya sanya zuciyar Halisa kusan bugawa, gidan da take kulafucin zama a cikinsa shine zai ce ba zai je da itaba, kuka taci ta koshi tana tunanin mafita babu shakka ta ko'ina Halima tayi mata zarra! ta haihu har sau biyu kuma ta tare a sabon gida. tabbas dole ne ta nemawa kanta mafita yanzu ne ta sake gazgata maganar Yaya Ramlatu inda take cewa mugun sihiri iyayen Halimatu sukayi akan Mijin nata, itama idan hakane to tabbas zama bai kama ta ba.

To da yake yanzu bata da matsalar kudi yasa ta d'auki d'amarar shiga malamai domin bukatarta ta biya, duk ranar da ya kasance ba a gidanta yake ba to idan ta fita tun safe sai yamma zata dawo gida tare suke yawace yawacen malamansu da Yayar mijin nata.....Yaya Ramlatu bata da matsala saboda mijinta matafiyi ne shiyasa takeyin abinda take so a gidan, haka zata fuce ta watsar da 'yayanta a tsakar gida, kishiyarta Sakina mutuniyar kirki ita ke mata dawainiya da 'yayanta tayi da nata, tabbas albasa ba tayi halin ruwa ba, dan da Ramlatu ta gado halin iyayen nata to ba zata aikata abinda take ba.


*GA MASU BUKATAR KARANTA BOOK DIN ZASU TURA #300 SINGLE, VIP GROUP #600 GA ACCONT D'IN DA ZA'A TURA KUDIN.......0542382124.....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATIN WAYA ZAKI TURA KIYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBAR......07084653262.....IDAN KIN SAN BA BIYAN KUDIN LITTAFIN NAN ZAKI YI BA DON ALLAH KADA KI KIRA WAYA TA KO KIYI MIN WATA MAGANA TA WHASAP*

*MUTANAN MU NA NIJAR IDAN KUNA SO KU BIYA KUDIN LITTAFIN ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN NUMBARS.........90899076_88137740 KATIN AIRTAL KO ORANGE.*


*🗯️MADADI!!💍*
_(Ba Haram Bane!!)_

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~




*PEGEN YAU NAKU NE*

*My Son Najib Sa'id*
*Abue Sale alqurami*
*Bashir Saleh*
*Umar Abbas Yusif*
*Muhammad Karim*

Ina mutukar godiya da kulawarku a kaina da 'kokarin yi min sharing ina rokon Allah ya sadaku da alkairin duniya dana lahira Allah ya za'ba muku abinda yafi alkairi a rayuwarku👏🏻
~~~~~~~~~~~~~~~

*6*
A takaice dai duk wannan fad'in tashin dasu Halisa sukeyi a kan Halimatu ba suyi tasiri a kanta ba, saboda halimatu ta kasance mace mai ibada kuma dukkaninsu bata nufe su da sharri ba shiyasa kullum Ubangiji ke kara kareta daga sharrin su da makircin su, duk wani asiri da sukeyi baya tasiri idan ma yayi baya dadewa yake karyewa, ta inda Halisa take samun galaba akan Abbas din shine ta gurin shaye-shayen magungunan mata to tana d'an janye hankalinsa watarana dan gaskiya irin magungunan da Halisa take sha suna da tsada har dana turawa sha take ita dai burinta ta janye hankalin Abbas din ya wulakanta matarsa uwar 'yayansa, abinda Halisa bata sani ba kuwa shine irinsu Abbas asiri baya saurin kama su idan ma ya kama su to baya wani tasiri a jikinsu zai karye! saboda Abbas mutum ne me yawan azkar da karatun al'akurani mai girma gashi sallahr asubah bata wuce shi, shiyasa duk wani asirin da suke masa baya zama a jikinsa.

Halisa tun haihuwarta ta farko take samun matsala daga zarar ta samu ciki baya yin kwari zai zube, ta shiga tsananin damuwa da tashin hankali! ganin 'Ya'yan Halimatu sunyi wayo har sun soma zuwa makaranta gashi mahaifinsu naji dasu yana yi musu hidima kamar hauka, ai babu shiri ta bazama yawon gidajen masu magani har gurin 'Yan bori zuwa take su bata magani tazo ta jika tasha, ta yini tana amai, da murkukusu, amma taki ta gane hanya madaidaiciya ta fawwalawa Allah domin shine mai bayarwa da hanawa, Kullum kokarinta ya za'ayi ta haihu ko ta halin 'kaka. Abbas ganin ta tashi hankalinta dan har ramewa tayi sai yayi musu viza domin zuwa 'kasa mai tsarki su roki ubangiji hakan be mata dadi ba taso ita ya kaita kasar waje likitoci su dubata idan ma dashe za'ayi mata zata amince ita gani take idan sukaje saudian ba zata sanja zani ba! Gabadayan su dashi da iyalinsa suka nufi kasa mai tsarki, Halisa ta dinga wani iyayi tana shige masa gani takeyi ai saboda ita aka zo kasar! Halima dai sai dai tayi mata dariya kawai dan ita wataran idan Halisa na wani abu har dariya take bata, tana kallonsu zasu shirya su fita ita da Abbas wai zasuje asibiti sai dai tayi musu fatan dawowa lafiya, ta lura shima mijin nasu na biyewa Halisan ne dan kawai a zauna lafiya.
Ita kuwa Naja'atu mugun haushin Halisan take ji dan ta soma hankali a lokacin, idan taga tanayi wa mamanta wani abu ranta 'baci yake sai tayi yun'kurin magana sai Halimatun ta hanata, sai dai tayi 'kwafa kawai! ita hakurin mamanta ta har mamaki yake bata, kuma a duk sanda za taga Abban nasu yana magana da Halisa sai taji haushinsa, tashi ma take ta bar gurin, wani lokacin kuma idan taga sun shiga daki da Halisan sun dade kuka take zuwa taci ta koshi! ta fito tana kumbura fuska, Halimatu ta gane yarinyar na kishinta shiyasa takejin ciwon abinda ake mata, ta kuma fahimci yarinyar za tayi kishi sosai dalilin da ya sanya take yi mata 'yar nasiha a fakaice! Naja'atu kam jinta kawai take yi tana ganin kamar wani abun ma itace take bada goyon bayan Halisan nayi mata, 'kiri-kiri sai suna zaune a guri daya Halisa zata tsiri wasu abubuwa wanda suke sawa ta janye hankalin Abban nasu! duk sanda haka ta faru taga ya tashi yabi bayan halinsa ji take kamar zuciyarta zata babbake! ko ya fito bata kulashi idan yazo yana musu magana banza take dashi sai dai yai ta tambayar Halimatu ko wani abun ne yake damunta Halimatu tasan abinda take fad'a masa maganar ta wuce! Naja'atu gabadaya daina walwala tayi ta daina sakin fuskarta, rashin kunya takeyi wa Halisa a duk sanda tasa mata baki a cikin maganarta dan Halisa akwai katsalandan daga zarar tazo taga suna hira da wasa da 'yan uwanta su Saddiqa da Mussadiq sai tazo ta dinga buga musu tsawa tana hantararsu, aikuwa dama a ciki take da ita, tace watarana suna wasa tazo tana yi musu tsawa! Tace"Mu dan Allah ki daina zuwa kina takura mana muna maganarmu ke waye ya takura miki eye? ina cewa abinda kike so shi kikeyi saboda haka ki daina zuwa kina mana tsawa mtwsss!." Takarasa maganar tana jan tsaki.

Halisa ta fusata sosai hannu ta fitar ta tsinka mata mari tana d'ura mata ashar! sai ambato sunanan Baba malam take tana zagi! Naja'atu ta dinga kuka tana fad'in "Allah ya isa ba kakana kike zagi ba naki kike zagi!
Halimatu tazo tana doke bakinta cikin 'bacin rai tace" Ashe baki da kunya Naja'atu." Tana kuka tace"Mamma kina ji fa tana zagin Baba Malam me yayi mata? wallahi sai na fad'awa Abbanmu." Kai tsaye ta nufi dakin da yake kwance yana bacci! Halisa da Halimat suka bita da kallo cike da mamaki! Halisa mamakin yarinyar take na mayar da uban wasu nata komai akayi sai tace Abbanta ko a gidan ubanwa ya zama Ubanta oho.

Yana tsaka da bacci yaji kukanta a kansa, ya bude idonsa da sauri! yana kallonta a tsaye a kansa tana goge fuska hawaye wani na sake zubowa, mikewa yayi zaune ya kamo hannunta ya zaunar kusa dashi.
Cikin tausasawa yace."Waye ya saki kuka." ? Cikin shashsheka tace"Gata can Anti Halisa muna wasa da dariyarmu tazo tana hantarar mu wai sai mun tashi mu bata guri zatayi kallo, shine dan nayi magana ta mareni har da zagin Baba Malam."

Ransa ya 'baci! Yace." Kan wane dalili zata tashe ku a guri kuna wasa? saboda za tayi kallo sai ta hantareku! hannunta ya ri'ke suka mike a tare suka fita palon

Halisa da Halima na tsaye sai musayar yawu suke Halisa na fad'in "Wannan iskancin da 'kanwar taki take yayi yawa haka kawai saboda samun guri ta mayar da uban wasu nata to tun wuri ki fada mata ba ubanta bane kada ma ta dauka tanada gadonsa."

Halimatu ta bude baki kenan za tayi magana ta hango fitowarsu yana rike da hannunta, Halisa ta kallesu ranta idan yayi dubu ya 'baci! Hura hanci ta shigayi tace"Au! zuwa tayi ta taso ka daga baccin."?

Ya 'bata fuska sosai yace."Koda bata tasheni ba dama dai-dai wannan lokacin nayi niyyar tashi, shin me yaran nan suke miki kullum kike matsa musu bakya barin su su huta."!

Halisa ta rik'e bakinta cikin mamaki take dubansa! Yace."Magana nake miki." Ganin yanda yasha kunu ne yasa ta sassauta murya saboda tasan halinsa sai tace"Kawai dan nace su tashi su bani guri zanyi kallo shine fa yarinyar nan ta hau yi min rashin kunya harda zagina."

Da sauri tace"Ni wallahi sharri tayi min ban zageta ba." Halisa tace"To nayi miki karya ko." Zumbura mata baki tayi ta murguda mata shi! Halisa ta shiga jijjiga kanta tana mamakin saken da yarinyar ta samu a gurin maigidan, kauna da son da yakewa yarinyar ta lura ko 'yayansa bayayi wa."

Yace."Kawai saboda zaki zauna kiyi kallo sai ki tashesu mai suka tsare miki! bana so ki sake hantarar min 'yaya duk wani abu da nake nema a duniya saboda su nake nemansa, kafin Allah ya bani sai da na cire tsammani dan haka dole ne na kyautata musu dan bana son abinda zai 'bata musu rai! duk abinda suke su zasuyi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali kamar yanda kema kikeyin abinda kike so."

Halisa takaici kamar ya kasheta, har ta bud'e bakinta zata ce "Ai ita wannan d'in da kake magana a kanta ba 'yar ka bace.......Sai kuma ta sanja shawara, tace" Shikkenan me 'yaya nima Allah ya bani." Tana 'kare maganarta sai ta fashe da kuka ta nufi daki....Jikinsa ne yayi sanyi kuma, Halimatu ta kalleshi murya na rawa tace"Haba Abban Naja'atu ba haka ya kamata ka yanke hukunci ba! kasan kowaye akayi wa haka dole yaji rashin dadi, yarinyar nan Naja'atu itace tayi mata rashin kunya kamata yayi ka fara hukuntata tukkuna."

'Dan ya mutsa fuskarsa yayi kamar zaiyi magana kuma sai ya fasa, hannun Naja'atu dake cikin nasa ya saki ya juya ya nufi dakin da Halisan ta nufa

Ita kuwa Naja'atu bata so hakan da yayi ba taso ya kyaleta taje tayi kuka taji ciwon a ranta kamar yanda take yini tana 'kuntatawa mamanta rai to itama yau ta d'and'ana taji.

Halima ta rufeta da fad'a kan abinda tayi tace"Wallahi duk sanda na sake ganin Kinyi mata tsaki sai ranki ya 'baci ko an fada miki sa'arki ce." ? Kuka tasa ta nemi guri ta zauna tana fad'in "Mama kina ji fa tana zagin mahaifinki Baba malam Kinyi shuru dan nayi magana sai kice nayi laifi ."
Jikinta a sanyaye tace"Dan ta zage shi sai me? ni nasan ba Ubana ta zaga ba nata take zagi saboda haka na fada miki babu ruwanki da ita har mu bar 'kasar nan." Shiru tayi kawai ba tace komai dan gaskiya ita ba zata dauki cin kashi da wulakancin da Halisan keyi mata ba

haka suka cigaba da zaman doya da manja tsakanin Halisa da Naja'atu babu sassauci kowa najin haushin dan uwansa, Naja'atu taci alwashi kan cewar duk sanda Halisa ta sake kuntatawa mamanta rai to itama sai ta 'kir'kiri abinda zai janyo musu fad'a a tsakaninta da Abbansu, Halisa tunda taga take-taken Naja'atu da irin iskancin da take mata sai ta shiga taitayinta ta rage yiwa Halima wasu abubuwan na rashin arziki badan komai ba sai dan sanin matsayin Naja'atu da tayi a zuciyar maigidan nasu, tasan idan ta tsananta ranta ne kawai zai 'baci a banza.

Sati biyu sukayi a kasa mai tsarki suka dawo gida, Likita ya d'orasu Akan magani, kan cewar in dai Allah ya nufa da akwai sauran rabo a junansu to zasu haihu.............Wata uku da dawowarsu Halisa ta samu ciki murna ta dinga yi tana adduar Allah ya zaunar mata dashi, to shima maigidan yayi farin cikin ganin cikin yayi wata hudu bai samu matsala ba, sai ya umarce data zauna ta daina aikace aikacen gida, mai aiki yace zai dauko mata, tace ya bari zata dauko 'yar yarta sai ta dinga taimaka mata, aikuwa hakane ya kasance Unguwar
Aisami
ya kaita da kansa taje ta dauko Shamsiyya 'Yar yarta budurwa ce 'yar kimanin shakara goma sha hida ta girmi Naja'atu da shekaru biyu, Shamsiyya irin masu shegen iyayi ne gata mummuna amma saboda tsabar shafa mai tayi fari da haske! murna sosai Shamsiyya tayi da zuwanta gidan Halisan tasan kafin ta dawo gidansu sai ta sauya tayi ki'ba dan gaskiya ko zuwa gidan sukayi da ziyara basa dawowa ranar da sukaje sai sun kwana dan har daukar kawayenta takeyi ta kaisu gidan tana musu iyayi kanwar mamanta na auran *Alhaji Abbas Dan kwagila*........To cikin ikon Allah Halisa ta haihu kalau ta samu 'ya mace sai dai ba haka taso ba taso ta haifi d'a namiji dan gaskiya Mussadiq ya tsone mata ido. Ita kuwa Yaya Ramlatu har akayi suna cikin yada habaici take mussaman idan taga Halimatu tazo gidan sai ta tsiri shige da fice tana sakin maganar da duk tazo bakinta........"Duk cikin da ya haifi mace watarana shi zai haifi namiji Halisa ki kwantar da hankali gabadaya dangi munfi bukatar mu samu zuria dake dan haka tunda kin fara dasa 'kwan ki a gidan Abbas to kiyi abinda kike so babu me ce miki don me.!! Ire-iren maganganun da Yaya Ramlatu keyi kenan Shamsiyya na taya ta, Halima bata ta'ba tanka musu ba abinda ya kawota takeyi ta tafi.

Ranar suna da kyar Abbah Abbas ya lalla'ba Naja'atu ta shirya ya kaisu, dan cewa tayi ita ba zataje ba bata da lafiya wanda shi da Halima duk sun san 'karya take yi kawai rashin jituwar dake tsakinta da Halisan yasa tace ba zataje ba.......kwalliya sukayi sosai gabadayan su harshi angon 'karni suna sanye cikin dakakkiyar shaddar galila mai kalar sararin samaniya(sky blue) sun yi iri daya da juna Halima da Naja'atu da Saddiqa! dinki iri daya ne a jikinsu doguwar riga ce wacce tasha uban stone work da aka kashe kudi gurin yin sa
Abbah Abbas shida Mussadiq sunyi iri daya cikin babbar riga da 'yar ciki hularsu iri daya hakanan takalman su iri daya, agogo iri d'aya, sunyi kyau sosai dan kafin su fita sai da sukayi hotona sannan ya kira Salim dan Yayarsa Ramlatu a waya ce yazo ya daukesu.......Salim dan kimanin shekaru ashirin da biyar a duniya matashin saurayi mai jini a jiki d'an kwalisa ne sosai kuma yana kan lokacinsa dan babu abinda Abbah Abbas baya yi masa na rayuwa ya dauki yaron tamkar d'an cikinsa, shine ya tsaya masa kan karatunsa har yayi degree kuma ya d'ora shi kan harkokin kasuwancinsa Salim yasan wasu daga cikin sirrinkan Abbah Abbas amma kuma bai san wasu ba, Salim tun kafin Naja'atu ta kai girman haka yake sonta yana so su kammala secondary tukkuna ya tunkari Kawunsa da maganar tabbas yasan shi zai shige masa gaba gurin ganin ya mallaketa, amma dai duk da hakan yana ta kokarin kafa gwamnatinsa a gurin Naja'atun, itace take nuna masa bata gane me yake nufi ba.

Koda Salim yayi tozali da Naja'atu kasa nutsuwa yayi ya dinga kallonta yana sosa kansa ga wani shegan mirmushi a fuskarsa, Naja'atu ta 'bata ranta tana kallon Abban nasu dake gyara babbar rigarsa domin shiga mota, murya na rawa tace"Abbah kace ya daina kallona." Abba Abbas na gyara zamansa a motar ya kalli Salim yana d'an 'bata fuska yace."Kai bana son shashanci ka shigo mota mutafi na lura da kai tun d'azu ka damu yarinyar nan da kallo sai wani sosa kai kakeyi na fad'a maka ba zan baka itaba sai da amincewarta." Salim yasa dariya yana kallonsa Yace."Haba Kawu dube ni fa kaga ni da kyau! ni ba irin mazan da mata zasu ce basa so bane, ni nasan nan gaba kadan Ita dakanta zata furta maka ni take so." Abbah Abbas na murmushi yace."Ni dai na fada maka malam ka nemi yardar ta dan cikin 'yayana babu wacce zanyiwa auran dole." Salim yace."Insha Allahu Naja'atu tawa ce." Mussadiq ya rike hannunsa da fadin"Nima ina so ka auri Yayarmu." Rank'washin sa Naja tayi ya shiga motar yana kuka, Halima ta d'auka Abban nasu zaiyi mata fada mai yasa ta dakeshi sai taji yana cewa"Kai Mussadiq bana son rashin kunya ka tsokane ta ta hukuntaka kuma sai ka kama kuka." Mamaki sosai ya rufe Halima! Girgiza kanta kawai tayi dan bata da bakin magana tana iya yiwa Naja'atu fad'a yace dan me shiyasa tayi shuru da bakinta, hakika kulawar da yake nunawa a kan 'kanwartata tana burgeta haka nan suma su Baba malam suna jin dadi yanda Abbas din ya r'ike musu 'yarsu tamkar shi ya haifeta, duk abinda zaiyi wa 'yayansa shi yake mata wani sa'in ma har yana bambamta ta dasu gurin wani abun.


Gabad'aya Naja'atu kasa sakewa tayi a gidan sunan ganin yanda jama'a ke musu wani irin kallo wasu ma sai nuna su sukeyi, dalilin da yasa kenan ta zauna guri guda tana kalle kalle.......Halima kam kasa zama tayi ta mike ta shiga cikin mutane ana hidima da ita duk da irin kallon banzan da suke mata hakan bai sa ta koma ta zauna ba, ta kau da kai tana ta shiga jama'a cikin fara'a ana gaisawa da ita.

Tana zaune a palo wasu 'yan uwan Halisa suka shigo suna she'ka dariya d'aya daga cikinsu tana fad'in "Ku tsaya kuga yanda kishiyar Anti Halisa take tafiya." duk sai su katsaya suna kallonta, sai ta shiga cangala 'kafarta d'aya tana cillata kamar yanda Halima keyi idan tana tafiya! Dariya suka kwashe da ita suna tafawa! Shamsiyya tace"Kuma wai a haka a nakashe take matar so a gurin miji." Duk sai suka ri'ke bakinsu suna kallonta 'karin bayani suke jira tayi musu! Shamsiyya ta bud'e bakinta za tayi magana taji saukar mari a fuskarta!
Naja'atu ce tsaye a tsakiyarsu tana zubar da hawaye itace kuma ta mari fuskar Shamsiyya! Wacce take gwada tafiyar Halimatu ta nuna murya na rawa tace."Yanzu hallitar Allah kike gwadawa? Ke baki ji kunyar abinda kika yi ba Allah yayi hallitarsa yanda yake so kina gwada kuna dariya kema fa baki wuce Allah ya mayar dake haka ba."!! Afusace Shamsiyya tace"Dan kutumar Ubanki ta gwada d'in! shegiya yar karoro! har ni zaki tsinkawa mari! lallai zan nuna miki nafi ki zafin kai!! kafin Naja ta ankara ta rufeta da duka! Sai sauran ma suka shiga taya ta suka rufar wa Naja'atu da duka har sai da ta durkushe a gurin!! Ihu! takeyi tana kokarin kwatar kanta....
Halisa ta fito daga daki a guje! jama'ar dake waje suka shigo palon suna tambayar abinda ke faruwa.
Shamsiyya tana hura huci! ta shiga fada musu karya da gaskiya. Yaya Ramlatu tazo ta tsaya a kan Naja'atu tana zaginta ta uwa ta uba! Naja'atu kasa motsi tayi dan ta daku sosai! Halima ce tazo ta kama hannunta ta mikar da ita, tana kuka itama tana kuka su Saddiqa da Mussadiq na kuka! abin gwanin ban tausayi! Ita kuwa Yaya Ramlatu kamar kara zugata akeyi ta tara mutane sosai sai aibata Halima da Naja'atu take da iyayensu kowa na tofin ala tsine a kansu! Halisa ganin abin ya kwa'be! yasa tazo tana bawa Ramlatu hakuri saboda tasan idan maigidan ya samu labarin abinda ya faru to babu shakka al'amura zasu 'baci! dan rayukan kowa sai ya 'baci! da kyar ta rarrashin Yaya Ramlatu tayi shuru taja tawagarta suka fita harabar gidan domin cigaba da rabon abinci.........Halisa ta dinga yiwa su Shamsiya fada kan abinda suke kokarin janyo mata, dukan Naja'atu da sukayi yana nufin abubuwa da yawa a gareta hakan na iya barazana ga auranta, shiyasa bayan ta shiga dakin tasa Mussadiq ya kira mata Naja'atun! K'in zuwa tayi sai da Halima ta rarrasheta sannan ta shiga dakin.

Halisa ta kwantar da kanta tana fadin "Naja'atu kiyi hakuri kinji ko abinda su Shamsiyya sukayi miki kinga dai a gabanki na hukunta su kuma nayi musu fada dan Allah kada ki fadawa Abbanku." Zum'bura bakinta tayi tace"To me yasa baki rama mun dukan da sukayi min ba! Ni wallahi bazan yarda ba sai na fada masa sun zageshi sun zagi Baba malam sun dake ni kuma sun kushe hallitar Allah."
tana k'are maganar ta ta fita daga dakin, Halisa rakata tayi da kallo baki a sake.

Tana fita daga dakin ta dauki wayar Mamanta wani guri ta 'buya ta kira numbarsa, ganin numbar Halimatu yasa ya dauka da sauri yace"Ranki ya dade yaya ina fatan komai lafiya."? ai kawai sai yaji fashewar kukan Naja'atu a kunnansa! Ya mike tsaye da sauri! Yace''Naja'atu lafiya kike kuka yi shuru ki fada mun abinda akayi miki?" cikin sar'kewa tana jawo numfashi irin na sharri ta shiga wassafa masa abinda ke faruwa a gidan sunan." Ranshi idan yayi dubu ya 'baci! Yace."Daina kuka kinji ko? zan dauki mataki wato Halisa ta tara mutane ne dan ta tozarta ni! babu laifi ki bawa maman taki wayar zamuyi magana." Tana shashsheka da goge fuska tace"To." Zuwa tayi ta kaiwa Halima wayar da fadin "Gashi Abbanmu zaiyi magana dake." Halima ta fita daga cikin mutane ta samu guri tana amsa wayar, Jinsa a fusace! yasa ta sassauta mirya tana so ta fahimtar dashi yaki sauraranta yace."Zai turo Salim yanzu yazo ya daukesu ya mayar dasu gida ita kuma Halisa zata gamu dashi." Kafin ma tace wani abu ya kashe wayarsa.....Kasa'ke tayi da waya a hannunta tana mamakin wannan al'amari! gabadaya idan Naja'atu zata fada masa magana baya tsayawa yayi nazari zai hau kai ya zauna, tabbas ba sune suke da laifi kan faruwar hatsaniyar ba, to amma yana da kyau yabi komai a sannu tasan halinsa da mugun zafin zuciya zai iya aikata abinda ba shikkenan ba.

Aikuwa dai

2 Comments On MADADI
avatar
sumayya-1-4

7 months ago

Reply

Hw can I get the complete text please

avatar
abasu-kala

7 months ago

Reply

Replying to sumayya-1-4

You have to pay 1k first for subscription in order to download our novels

Please Login or Register in order to submit comment