Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

irin gumi ne ya shiga tsiyaya daga jikin Halisa! "Aure!aure! kalmar ma ba babu dadin ji a kunnanta, wato duk ladabi da biyayyar da take masa da nuna masa kulawar da Halimatu take masa bai sa yaji sha'awar aure ya fita daga ransa ba? ashe duk abinda takeyi masa na kulawa a banza take mutuwar Halima ko sati biyu ba'ayi ba amma har ya fara kokarin aure, shin wai dame ta gaza ne a gurinsa......wasu hawayen takaici da bakin ciki ne suka shiga sauka a kumatunta.....Yaya Ramlatu tace." Ai ba kiyi kuka ba ma tukkuna sai kinji yarinyar da zai aure."! Bakinta na rawa tace."Wacece."? Kai tsaye Yaya Ramlatu tace"Naja'atu ce.'' Sai tayi kasa'ke tana kallonta tunani takeyi wacece ma Naja'atu! dan a lokacin gabadaya kwakwalwarta ce ta toshe ta mance a inda tasan mai irin sunan."
Yaya Ramlatu tace''Kina mamaki! ko da jin wacce mijinki zai aura bari na 'kara tabbatar miki da maganar, Abbas zai auri Naja'atu kanwar matarsa Halimatu yarinyar da ya ri'keta tun tana 'karama yayi mata komai tamkar 'yar cikinsa! shine yanzu zai maye gurbin 'yar uwarta da ita." Halisa ta dinga jin hajijiya tana daga xaune! rintse idonta tayi tana tunano siffofin Naja'atu a idonta!!! a gigice ta bude idonta ta zabura ta mike tsaye tare da cewar "Wallahi ba zaiyi wuba !! ba zan yarda da wannan cin amanar ba! Ni Abbas zaiyi wa haka? me nayi masa a duniya zai had'ani kishi da yarinya 'karama 'yar cikina! kutumar uban nan kayyasa!! sai ta zube kasan kafet ta fashe da wani mahaucin kuka tare d'ora dukkanin hannuwata a kanta.





*GA MASU BUKATAR KARANTA BOOK DIN ZASU TURA #300 SINGLE, VIP GROUP #600 GA ACCONT D'IN DA ZA'A TURA KUDIN.......0542382124.....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATIN WAYA ZAKI TURA KIYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBAR......07084653262.....IDAN KIN SAN BA BIYAN KUDIN LITTAFIN NAN ZAKI YI BA DON ALLAH KADA KI KIRA WAYA TA KO KIYI MIN WATA MAGANA TA WHASAP*

*MUTANAN MU NA NIJAR IDAN KUNA SO KU BIYA KUDIN LITTAFIN ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN NUMBARS.........90899076_88137740 KATIN AIRTAL KO ORANGE.*


*🗯️MADADI!!💍*
_(Ba Haram Bane!!)_

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~



*10*
Wani irin kuka Halisa takeyi tamkar wacce aka aiko mata da mutuwar iyayenta, ta d'ago kanta tana kallon Yaya Ramlatun fuskarta gaje-gaja da hawaye tace"Yaya Ramlatu ina zan saka kaina da wannan abun kunyar! shin wai me yake damun d'an uwanki ne? Ya rasa wacce zai aura sai 'yar cikinsa yarinyar da ya ri'ke tamkar shi ya haifeta amma saboda tsabar abun kunya yace zai aureta tsofai-tsofai dashi zai auri 'yar 'karamar yarinya babu shakka wannan karon komai zai faru tsakanina dashi sai dai ya faru dan na rantse da Allah ba zan bari ya tozartani ya had'ani kishi da matsiyaciyar yarinyar nan da na riga nasan matsayinta a zuciyarsa ba."
Ya Ramlatu ta sauke ajiyar zuciya tana fad'in "Ai shiyasa nima dana ji labarin hankalina ya tashi sosai! Kishi da irin jinin Malam Baba ai bala'i ne wane irin daurin gindi ne Halimatu bata samu ba a gurin Abbas din, ai wallahi kece abar tausayi mutukar kika bari ya auri yarinyar nan to ki rubuta ki ajiye auran ki ya 'kare tsakaninki da mijinki."
Yaya Ramlatu ta 'kare maganarta cikin karfafa maganar ta gami da 'kokarin 'kara ingiza zuciyarta.
Goge fuskarta tayi tace"Yaya Ramlatu ai na fad'a miki wallahi tallahi sai dai ya za'ba ko ni ko yarinyar nan dan ni ba zanyi kishi da Yayarta ba itama nazo nayi da ita ba, wannan karon duk abinda yake ji dashi dai-dai nake dashi zai dawo gidan ya same ni.''
Yaya Ramlatu ta dauki lemo ta kur'ba tace"To ai dik da haka ba zama za kiyi ba dole ki d'an nemi taimako dan baki san irin shirin da iyayen yarinyar suke a kan al'amarin ba, dan wannan tsinannan Malam Baba mugun mutumi ne babu irin surkullan da bayayi." Halisa tace"Yaya Ramlatu ni yanzu gabadaya ma banda kuzarin zuwa gurin wani malami da sunan taimako nifa gabad'aya auran Abbas ya fice min daga rai ya dawo ya sake ni." Ta'karasa maganar cikin rawar murya. Yaya Ramlatu tace"A'a ba za'ayi hakaba ke yanzu idan kika kashe auranki saboda wannan yarinyar ai kin cutar da kanki! kada kice ya sake ki kawai idan ya dawo ki daga masa hankali ke macece kin san hanyoyin da zaka hanashi nutsuwa da kwanciyar hankali gefe guda kuma zamu sa malamai su taimaka miki insha Allah sai zuciyarsa ta karye yaji sha'awar auran ya fita daga ransa da kansa zaice ya fasa."

Halisa tayi shuru tana tunani! Yaya Ramlatu tace"Dole ki futo da kudi aje a taimaka miki ni gaskiya bazan so ki bar dakin ki ba, ki zauna kici ubansu daga shi har yarinyar idan Allah ma ya kaddara sai ta shigo gidan sharri kad'ai ya isheta.
Halisa taja ajiyar zuciya tare dayin 'kwafa, tace"Maganar ki haka take Yaya Ramlatu bari na kawo miki dan abinda ke hannuna dan Allah kiyi min kokari akan al'amarin." Yaya Ramlatu tace"Kada ki damu zan shiga na fita insha Allahu maganar auran zata rushe ke idan ma Allah ya kaddara auran to wallahi ba zamu k'yalesu suji dad'in rayuwa ba." Halisa ta gyada kanta tana dan jin sassauci acikin zuciyarta, bedroom dinta ta nufa, minti biyar ta fito hannunta rike da kudi 'yan dubu dubu. Ta mikawa Yaya Ramalatun da fadin "Dubu ashirin ne zuwa gobe sai ki aiko a kar'bi dubu talatin din zanyi duk yanda zanyi na dauki key din gurin da yake ajiyar kudi na dauka."
Yaya Ramlatu ta mike tana gyara yafan mayafinta tace"Nima daga nan zan wuce gidan *'Yar shagamu* (wata hatsabibiyar 'kawar Ramlatun ce)Ta cigaba da cewa......"akwai wani malami da mukayi hirarsa kwanaki da ita tace ya iya aiki idan dare baiyi ba zamuje idan kuma dare yayi to da sassafe zamu buga sammako dan kada muje mu tarar da mutane." Halisa taji wani sanyi a ranta tace"Yaya Ramlatu nagode kawarai da kaunar da kike nuna min hakika ina alfahari dake a cikin 'yan uwan Abbas kina nuna min kaunar da mahaifiyarku ma bata nuna min."
Yaya Ramlatu ta dafa kafadarta tace"Kada ki damu cikin ko wane irin hali ina tare dake, maganar Hajiyarmu kuwa dama can tafi kaunar Halima a kanki saboda gidan Malam Baba sun riga sun gama dasu daga ita har Alhajin, dan baki ga yanda suke murna da wannan al'amarin ba, Hajiya har da kuka tana 'kokarin yi min baki akan nace auran Abbas da yarinyar bai dace ba, shine fa take kuka har dayi min gorin abinda Abbas din keyi wa Salim."
Halisa ta shiga girgiza kanta, cikin 'kunar zuciya tace"Ai ba sai kin fad'a mun ba dama tuntuni na san Hajiyarku bata sona ko lokacin Halimatu tafi nuna kulawarta a kanta, to kinga kuwa dole taso wannan al'amarin ni na rasa me nayi mata ta tsaneni."
Yaya Ramlatu tace"Wallahi duk sharrin daga gidan Malam Baba yake gabadaya fa sun gama da zuciyoyin jama'ar gidanmu nice kadai na gagaresu." Halisa na jin d'aci a ma'kogwaronta tace"Insha Allahu sai mun karya alkadarinsu."

To sallama sukayi da juna inda Yaya Ramlatu take sake tabbatar mata da cewar yanzu idan ta fita gidan *'Yar Shagamu* zata nufa domin su tattauna yanda al'amarin tafiya gidan malam zai kasance.


Koda Naja'atu ta koma gidan Malam kai tsaye dakinsu ta shige taje ta kwanta kan katifa, ta dinga kuka tana birgima kan katifar! sai sambatun surutai take da kiran sunan Halimatu wai ta mutu ta bar baya da 'kura mutuwarta tana nema ta zame mata barazana ga rayuwarta...........Sautin kukan tane ya cikawa Baba Talatu kunne da sauri ta fito daga kicin ta nufi dakin, nan ta tarar da ita sai burgima take kan katifa tana dukan kanta da kanta kamar wata mahaukaciya sai surutai takeyi da fad'in in dai aka daura mata aure da wani ba Salim ba to sai ta kashe kanta ta kashe wanda aka aura mata......Baba Talatu ta shiga dakin hankalinta a tashe ta birkitota wani wawan mari ta kifa mata a fuskarta tana wani irin huci!! Rintse idonta tayi ta mike zaune hannunta kan kuncinta idanunta a rufe amma hawaye ne kawai yake zurara.

Murya na rawa Baba Talatu tace"Naja'atu idan baki kashe kanki kin kashe Alhaji Abbas ba bakya kaunar Allah! Wai shin ke d'in wace irin yarinya ce butulu mai manta alkairi! yanzu da abinda zaki sakawa da wannan bawan Allahn kenan? wannan wace irin 'kiyayyace kike nuna masa 'karara? meye bai miki ba? ki sani idan da mutuwa bata ratsa tsakaninsa da matarsa ba ke baki isa ya kalleki ba ballanta yace zai aure ki dan saboda baki dace daki auri nagartaccen namiji kamar wannan ba! meye laifinsa? meye kuma illarsa!? Muna tsaka da alhani gami da rad'ad'in mutuwar 'yar mu mai biyayya kina nema ki d'ora mana ciwo! ashe bamu isa dake ba? ashe kuma Halima bata cancanci sakayya al'kairi a gurinki ba? Idan kin auri mijin Halimatu babu wanda zai kai ki Jin dad'i itama kuma zata samu farin ciki alkairin da kikayi mata kin auri mijinta bayan babu ranta kin tallafi 'yayanta! to wallahi duk sanda na kara jin kinyi wani mummunan furuci kan wannan bawan Allahn sai ranki ya 'baci! sai na fad'awa Magaji duk abinda kike yi tunda ni da malam kin raina mu bakya ganin mutuncin mu."!! Baba Talatu ta kare maganarta cikin tsantsar 'bacin rai gami da jin takaicin abinda 'yar tata takeyi.
Baba Talatu fita tayi daga dakin ranta a 'bace! hakika yarinyar bata ta'ba 'bata mata rai ba irin yau! ita rasa gane meye abin gudu a game da wannan auran da suke kokarin had'awa, a iya tunaninta da tsinkayen ta tana ganin kamar gata sukayi wa yarinyar har indai sun had'ata aure da mijin 'yar uwartata dan hausawa na cewa Naji dad'i shine gari ba nasa baba........Baba Talatu na fita daga d'akin ta zame a hankali ta kwanta kasan ledar dakin tana takure jikinta ta cigaba da kukan rashin mafita, a lokacin ji take yi dama Allah zai dauki ranta ta huta daganin wannan masifar.......... Koda Saddiqa da Mussadiq suka shiga dakin suka sameta a kwance tana kuka! Mussadiq ne kawai ya tsaya a kanta yana mata magana ita kuwa Saddiqa saboda tasan ko kukan me takeyi yasa ta juya ta fita daga d'akinta ranta a 'bace! hakika tana jin ba'kin ciki da takaicin irin 'kiyayyar da take nunawa mahaifinta, shiyasa itama ta soma jin haushinta akan irin abinda takeyi kan al'amarin.

Mussadiq ya 'karaci maganarsa ko kallonsa ba tayi ba haka ya fita daga dakin jikinsa duk a sanyaye! haka suke shiga damuwa koda can idan sun ganta tana kuka ko rashin lafiya daga su har mamansu da Abbansu duk su damu duk da bashi da wayo sosai shima ya fahimci cewar Antin tasu bata 'kaunar zaman aure da babansu........Zama yayi kusa da Saddiqa tana gyarawa Baba Talatu wake suna hira jefi-jefi ya kalli Baba talatu da fad'in "Baba me akayiwa Yaya Naja'atu take kuka."? Baba Talatu tace." Kyaleta Mussadiq ka fita daga sabgarta kaji ko." Mussadiq yayi shuru jikinsa duk yayi sanyi.........To Har aka idar da sallahar azuhur Naja'atu na kwance a daki tana juye-juye zazza'bi me zafi ne ya rufe ta wanda ya hanata mikewa taje tayi alwala tai sallah.

Saddiqa ta shiga dakin domin yin sallah ta kalleta itama ta kalleta babu wanda yace komai a tsakaninsu, Saddiqa ta gyara dadduma ta tayar da sallaharta, koda ta idar mikewa tayi ta fita daga dakin ba tare da tace komai ba, to sai hakan da tayi ya bata mamaki sosai! kuma ya nuna mata cewar yarinyar fushi take da ita, jikinta ne yayi sanyi sosai ta rinste idonta murya na rawa tace"Ba laifi na bane laifin zuciyata ne Saddiqa bana 'kin mahaifinku sai dan zuciyata ta riga ta gama makancewa da kaunar Salim, a dai-dai lokacin da muke sanya rai da bukatarmu zata biya a dai-dai lokacin kuma za'a kawo mana cikas a rayuwarmu ha'kika rayuwarmu nida Salim na cikin kalubale mai girma mutukar akace baza'a daura mana aure da juna ba."
Muryar Mussadiq taji a kanta, tayi saurin bude idonta tana kallonsa......Mussadiq duk yaji abinda take fad'a ya fahimci wata maganar wata maganar bai fahimce ta ba, Yace."Yaya Naja'atu ki tashi kiyi sallah kici abinci mu tuntuni munyi sallah munci abincinmu.

Hannunsa ta ri'ke ya zauna kusa da ita murya na rawa tace"Mussadiq bani da lafiya zuciyata na daf da tarwatsewa."!! Da sauri yaron ya d'ora hannunsa saman goshinta yana fad'in "Yaya Naja'atu kanki ne yake ciwo ? sannu bari na kira Abbanmu a waya ya kawo miki magani." Girgiza kanta tayi tana kokarin mikewa zaune tace"Mussadiq wannan ciwon nawa Abbanmu shine ya haddasa mun shi dan Allah kace dashi yayi hakuri ya k'yaleni." Mussadiq ya dinga kallonta cikin mamaki yace."Yaya Naja'atu Abbanmu ba zai cutar dake ba kiyi hakuri ki aureshi ki zauna dashi."! Taji wasu hawaye na kokarin kufce mata, wai kowa sai yace tayi hakuri ta zauna dashi to wai ta yaya zata iya zama dashi alhalin bata sonsa kuma a matsayin Uba take kallonsa, abunfa da wahala wai (gurguwa da auran nesa) mikewa tsaye tayi a hankali ta fita daga dakin, Shi kuma Mussadiq din ya dauki wayarta ya nemi numbar Abban nasu ya shiga kira.

Koda yaga Numbar Naja'atu na kiransa bai 'ki dauka ba, sai dai babu walwala a tare dashi yayi sallama! sai kawai yaji muryar Mussadiq yana fad'in "Abbanmu nine Mussadiq na kira ka da wayar Yaya Naja'atu." Murmushi yayi yana jin wani farin ciki yace."Na gane ka Magajin Abbah Ina fatan lafiya ina Naja'atun take."? Mussadiq yace."Yanzu taje yin sallah bama ta da lafiya sai kuka takeyi tana cewa wai dan Allah ka 'kyaleta."!! Shuru yayi yana nazarin maganar yaron daga bisani yace."To shikkenan kace mata na kyaleta tunda bata son Allura ba zan kawo likita yayi mata ba." Mussadiq yace."Ba wannan ba Abba naji tana cewa kada ka aure ta ita tafi so ta auri ancle Salim Abbanmu tunda bata so ta zauna tare da kai ka kyaleta ta auri wanda take so."!! Abbah Abbas ya jima yana mamakin maganar yaron, kuma yana mamakin abinda yarinyar take yi na rashin kyautawa! wato yaran take zaunawa dasu tana nuna musu a zahiri bata kaunar Ubansu har tana bawa 'Dansa sa'ko ya bashi! ranshi ya 'baci sosai da sosai! sai kawai yayi 'kokarin bagarar da maganar ta hanyar fad'in "Ina Saddiqa take kace mata nace ku shirya gobe zan aiko Salim ya dauke ku xaku koma makaranta ranar Monday." Yace."Tom zan fad'a mata Abbah." Yace." Yawwa ka gaishe min da Baba Talatu da kyau." Yace." Za taji Abbah." Kashe wayar yayi ya shiga nazarin irin iskanci da wulakancin da yarinyar ke masa, zai iya hakura da duk irin cin fuskar da za tayi masa amma kuma ba zai lamunci ta dinga cin fuskar 'yayansa ba, hakan da take yi zai sanya ransu ya 'baci! su shiga halin damuwa da maraicin mahaifiyarsu.


To da wannan 'bacin ran ya shiga gidansa......In da yaje ya tarar da tashin hankalin Halisa dan ko zama bata bari yayi ba tabi shi d'aki! ta shiga zazzaga masa rashin kunya gami da farfad'a masa duk maganar da tazo bakinta kana kuma tace" Sai dai ya za'ba ita ko Naja'atu dan wallahi ba za tayi kishi da Ya tayi da kanwa ba.

Babu Abinda yace mata ya shiga bandaki domin yin wanka zuciyarsa tamkar zata tsaga kirjinsa ta fito dan tsananin 'bacin rai!!!! Koda ya fito samunta yayi a kwance 'kasan ties tana kuka had'e da wata iriyar fuffuka tana burgima 'kasan ties kamar mai iskokai! Ya shirya tsaf ya tsallaketa ya fita ya barta a dak'in! Bin hanyar da yabi tayi da kallo hawaye na sharara ta mi'ke zaune tana cizon tsaya wato Abbas ko gani yayi zata mutu ba zai tanka mata ba kenan ballanta ya fada mata magana mai dad'i! aikuwa a zuciye ta mi'ke tsaye! tana rangaji! da had'a hanya, ta nufi kicin d'inta.
Yana zaune gurin cin abinci yaga fitowarta kallo ya bita dashi yana jan tsaki a fili ya shiga bude kwanonin abincin da ta jera kamar gaske! wayam! babu komai a ciki amma saboda tsabar iskanci da iya shega na Halisa ta shirya tevur kamar ta shirya lafiyayyan abinci......Takaici ne ya kamashi ya tsirawa hanyar data bi ido, kawai sai ya hangota ta fito daga kicin d'in hannunta ri'ke da shar'be'biyar wu'ka sabuwa dal da alama daga cikin kwalinta ta cire, kai tsaye ta durfafo inda yake jikinta na tsuma da rangaji! take fad'in "Wallahi yau koni ko kai a gidan nan Abbas na gaji da wannan abun da kake min ni ka sake ni ma na huta da ganin wannan takaicin auran wannan yarinyar da zakayi masifa ne a gare ni da kai baka sani ba sai sanda nayi maka illah a rayuwarka sannan zaga gazgata maganata." ..........Mufida ta shigo palon tana sanye da uniform na makaranta ta hango abinda ke faruwa, a guje ta jefar da jakarta tayi kan mahaifiyar tata dake dumfarar mahaifinta da dalleliyar wu'ka! tana nema ta caka masa! " Cikin karaji!! tace" Mommy meye haka? me za kiyi? Wayyo Abbanmu ka gudu."!! Tafad'a tare da zuwa ta rungumeshi tana jansa wai ya gudu. Shi kuwa yana tsaye turmin danya bai razana ba, wato wai-wai d'in da yake ji a gari a na cewar mata na kashe mazajen su idan za'ai musu kishiya abun yazo kansa, jira kawai yake ta 'karaso da wukar yaci ubanta! Halisa ido a rufe ta 'karasa inda suke Mufida na kuka tana jansa da fadin "Abbah mu gudu kada ta caka maka wu'ka Abba me kayi mata n...........Gani tayi ya kama duka hannuwan Mahaifiyar tata ya murd'e da iyakacin karfinsa Wu'kar ta su'buce ta fad'i 'kasan gurin! Ya kai mata wani lafiyayyan mari! da bayan hannunsa, wani 'karamin jini ne ya fito daga hancinta, kafin ma ta dawo hayyacinta ya sake kifa mata wani a d'aya gefan, sai kawai yaga ta yanke jiki ta fad'i ta shiga turje turje tana taune harshenta..........Aljanunta ne suke ka da ita a gurin ta dinga turje-turje tana taune harshenta farar kumfa nata fitowa daga bakinta, Halisa na 'karyar aljanu ashe dama tana dasu da gaske! sosai take burgima a gurin tana ta wasu gwalantu wanda ba wanda yake ganewa a cikinsu, Mufida ta nufe ta tana kuka zata ta'ba ta, ya hanata Yace." Je ki cire uniform din'ki idan ta gaji da iskancin da take zata tashi."
Tsakanin Uwa da D'a sai Allah tace"Abbah duba fa kaga abinda take wannan abun ba 'karya bane dan Allah kayi wani abu kai."
Tsayawa yayi tsai yana nazarin Halisan da abinda takeyi Eh kwarai kuwa wannan abun da take yasha bambam dana ko yaushe dan haka sai ya umarci Mufidan ta kawo masa ruwa a kofi, da sauri ta taje ta dauko masa, ya kar'ba ya shiga tofa ayatul'kursiyu da fala'ki da nasi 'kafa bakwai bakwai kana ya iske inda take, ruwan tofin ya guntsa a bakinsa ya shiga fesa mata a jiki, sai da yayi haka sai uku tukkuna sannan ta daina burgimar da take yi ta daina gwalantun surutan da take yi jikinta ya shika sosai tayi lakaf gumi duk ya jika mata jiki, Mufida na kuka taje ta rungumeta tana kiran sunanta................




_*Ana samu mata marasa hankali da tunani irinsu Halisa wanda suka maida kishiya abokiyar gaba suke ganin zasu iya jefa kansu ako wace irin masifa saboda namiji da kishiya, Allah ya sawa'ke wa duk macan da take haukan kishi kan mijinta zai 'kara aure! Wallahi garin tsabar haukan ki zaki je ki jefa kanki cikin masifar rayuwa gami da nadama.*_




*GA MASU BUKATAR KARANTA BOOK DIN ZASU TURA #300 SINGLE, VIP GROUP #600 GA ACCONT D'IN DA ZA'A TURA KUDIN.......0542382124.....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATIN WAYA ZAKI TURA KIYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBAR......07084653262.....IDAN KIN SAN BA BIYAN KUDIN LITTAFIN NAN ZAKI YI BA DON ALLAH KADA KI KIRA WAYA TA KO KIYI MIN WATA MAGANA TA WHASAP*

*MUTANAN MU NA NIJAR IDAN KUNA SO KU BIYA KUDIN LITTAFIN ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN NUMBARS.........90899076_88137740 KATIN AIRTAL KO ORANGE.*
*🗯️MADADI!!💍*
_(Ba Haram Bane!!)_

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~


*11*
Mufida sai tatta'ba jikin mahaifiyar tata take tana kuka had'e da kiran sunanta, Halisa na kwance tamkar gawa wani irin bacci take yi mara dadi...........Ya fito daga daki Cikin shirin fita nan yaga Mufida sai kuka take ta takure kanta a guri guda, tausayi ta bashi sosai kasancewarsa mutum mai son 'ya'ya yasa kwata-kwata baya 'kaunar abinda zai 'batawa d'ansa rai dalili suma yaran nasa dai-dai gwargwado suna masa biyayyar da ta kamata, a nutse ya tsuguna kusa da yarinyar yana kiran sunanta.
A firgice ta d'ago kanta tana kallonsa sai ta sake rurucewa da kuka tana nuna masa Mommynta dake kwance, baki na rawa tace"Abbanmu mommy ta'ki tashi sai tashinta nake yi gashi babu kyau baccin yamma." Yace."Insha Allahu za tashi ki kwantar da hankali yanxu tashi kije ki sanja kaya kizo ki rakani na siyo mana abinda zamu ci." Jiki a sanyaye ta kalleshi kafin tace"Abbah mommy tayi girki gashi can ta jera kan tevur." murmushin takaici yayi yace."Babu komai a cikin kwanukan dake jere a tevur kawai tayi hakane dan ta 'bata min rai." shuru yarinyar tayi tana nazarin maganarsa, babu shakka akwai abinda ke faruwa wanda bata sani ba
Yace."Maza tashi ki sanjo kaya mu tafi kada magariba tayi." mi'kewa tayi ta dauki jakarta ta nufi dakinta, A nutse ya juya yana kallon Halisa dake sheme 'kasan kafet idanunta duk sun zurma ciki lokaci guda duk ta furgice ta rame, tausayi ta bashi kad'an! ya shiga girgiza kansa mamaki yake sosai Halisa ta kai matakin shekaru talatin da biyar a duniya amma har yanxu ba tayi hankali ba, wai wu'ka ta d'auko zata yi masa rauni kawai saboda zai raya sinnar ma'aiki, to meye a ciki kuma meye abun damuwa dan ya auri Naja'atu, sam bai aikata haram ba sai ma sinna daya 'karfafawa kansa dan ya auri Naja'atu tana da shekaru 16 a duniya a ganinsa ba aibu bane, tunda Annabi Muhammad (s.a.w) ya auri Nana Aysha tana da shekara tara, to kuwa idan hakane ai babu laifi gurin auransa da Naja'atu, wani sa'in mutane sunfi girmama al'ada akan addini shiyasa su suke ganin kamar ya aikata haramci! auransa da Naja'atu kuwa yana tunanin babu wani mahalukin da ya isa ya hana, idan ba'ayi ba to babu shakka Allah ne bai so ba


Mufida ta fito a kintse itama tasha hijab dinta har'kasa, haka yake sawa ana d'inka musu hijab manya manya, kasancewar sa mabiyin sinna kai idan kaga yanda yake mu'amula da mutane da yanda ya tsayar da (gemu) zaka fahimci cewar bai yarda da wata bidi'a ba, abokanshi wataran har tsokanarsa suke idan yana kawo musu 'kauli da ba'adi, koda yake irin wannan dama ya saba faruwa a tsakanin mutane kowa da d'ari'kar da tayi masa shi dai Abbah Abbas 'Dan izala ne sosai dan gabad'aya bai yarda da bidia ba shiyasa bai fiye sakin jikinsa da mutane ba.


Da kansa yake draving din yana tunanin rayuwa da abubuwan da suke faruwa dashi da 'yayansa, babu shakka mutuwar Halimatu babban gi'bi tayiwa rayuwarsa data 'ya'yansa da Halimatu na raye babu wanda zai samu dama a kansa, Kira ne ya shigo Wayarsa dake gefansa ya d'an kalli wayar sai yaga My dota na yawo kan screen din wayar......Dauke kansa yayi ya cigaba da draving d'insa, hakika abinda yarinyar nan keyi masa yana mugun 'bata masa rai!

Ita kuwa Naja'atu cigaba tayi da kiran wayar so take ya d'aga ta fad'a masa magana mai zafi dan yanzu suka gama waya da Salim ya sake tunzura mata zuciyarta, ya fad'a mata duk yanda sukayi da Abba Abbas din dazu da safe da zai kaisu kasuwa, shine ya kira wayarta ya fad'a mata komai ya ingizata kan tayi fito na fito dashi tunda shine ya zubda mutuncinsa, lokacin itama zuciyarta ta gama

2 Comments On MADADI
avatar
sumayya-1-4

7 months ago

Reply

Hw can I get the complete text please

avatar
abasu-kala

7 months ago

Reply

Replying to sumayya-1-4

You have to pay 1k first for subscription in order to download our novels

Please Login or Register in order to submit comment