Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana nuna masa toilet din, Ya rike hannunta yana tofa mata addua tangadi ta shiga yi tamkar 'yar maye ta tafi luuuu! zata fad'i! ba tare da 'bata lokaci ba ya ri'ke ta sosai a jikinsa, cikin tashin hankali da damuwa ya nemi gefen bed ya zauna da ita rungume a jikinsa, ji yayi jikinta na wani irin kyarma! yana rawa kamar wacce take cikin zazzabi mai zafi! babu shakka a firgice take, adduoi ya shiga tofa mata a jikinta yana me tsirawa fuskarta ido, a fizge suna dan kama da Halimatu kad'an, nan ya shagala da kallonta dan gani yayi tana nema ta rikid'e ta koma masa Halimatu.......Lokacin ne kuma ta dan samu nutsuwa ta bude idonta tana ambatar kalmar innalillahi wa'ina ilahi raji'un! Ta mike da sauri ganinta kwance lakadan a jikinsa ga towel din jikin ya sa'bule! brest dinta duk a waje! Da sauri shima ya gyara yanayin sa amma dai duk da haka kana kallonshi sai gane ya hau network, Yayi dan gyaran murya as'usul Yace."Sannu ki dinga yawaita addua ina ganin tunda kin firgita da zaman side din nan zan sa a gyara miki Side din da ya kasance nawa sai ki koma can." Gyara towel din jikinta tayi ta mike daga jikinsa, kayan ta dake kusa dashi ta dauka tana so tasa tana jin kunyarsa, Yace."Ya zaki sa kayan bayan duk ga sabulu nan a jikinki." Cikin rawar Murya tace"Ba zan iya komawa toilet din ba, dan ina wanka naji kamar ana kiran sunana." Ya dinga kallonta abin na bashi mamaki! Mikewa yayi ya rike hannunta yace."Muje na raka ki kiyi wankan." Ma'kale kafad'a tayi tana komawa baya! Yace."Zan tsaya har ki gama fa kuma bazan kalleki ba." Hawaye ta share tace''Na hakura da wankan."Ya girgiza kansa da fad'in "A'a ai bai dace ba kina amarya ki zauna da datti ba zakiyi ba'ki fa." Kallonsa ta dinga yi tana mamakin maganarsa, Tace."Abbah ni d'in amaryar waye."? Ya nuna kansa da hannu da fad'in "Amaryata mana." Taji wani irin ciwo da takaici a cikin zuciyarta, hawaye suka kece mata tace."Kaico da wannan kalmar taka Abbah! Kaico da wannan maganar dake fitowa daga bakin ka, ni ba amaryarka bace 'Yar ka ce." Tana gama maganar ta ta cire hannunta daga cikin nasa ta fita daga dakin, gabadaya ma ji tayi ta daina jin tsoron akan ta zauna a dakinsa yana kiranta da amaryarsa gwara ta fito koma meye ya cutar da ita....
*GA MASU BUKATAR KARANTA BOOK DIN ZASU TURA #400 SINGLE, VIP GROUP #600 GA ACCONT D'IN DA ZA'A TURA KUDIN.......0542382124.....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATIN WAYA ZAKI TURA KIYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBAR......07084653262.....IDAN KIN SAN BA BIYAN KUDIN LITTAFIN NAN ZAKI YI BA DON ALLAH KADA KI KIRA WAYA TA KO KIYI MIN WATA MAGANA TA WHASAP*

*MUTANAN MU NA NIJAR IDAN KUNA SO KU BIYA KUDIN LITTAFIN ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN NUMBARS.........90899076_88137740 KATIN AIRTAL KO ORANGE.*
*🗯️MADADI!!💍*
_(Ba Haram Bane!!)_

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~~~~~~~~ *16* Ya jima a dakin yana sa'kawa da kwancewa kafin ya fito palon, inda ya sameta a takure a kan kujera har yanzu bata daina zubar da hawaye......Saboda jin haushin maganar data fad'a masa yasa ya kama hanyar fita dan baya so ya zauna a gidan zuciyarsa ta tunzira shi a kanta, dan ya lura koda 'kuruciya a tare da ita to da akwai iskancin dan iskancin ma yafi yawa a tare da ita, gabad'aya ya lura ta raina shi kuma ta daina ganin girmansa, wannan d'abi'un da take masa na 'bata masa rai sosai da sosai! Yana dab da fita yaji ta ri'ke masa hannu, ya juyo fuskarsa babu walwala yana kallonta yace."Me zanyi miki kuma."? Cikin rawar murya tace"Dan Allah zan bika dik inda zakaje kada ka barni ni kad'ai wallahi ba zan iya zama ba." Shuru yayi yana kallonta na minti biyu kafin yace."Jeki dauko hijab din'ki." Da sauri ta saki hannunsa Hijab dinta dake kan kujera ta d'auka tasa ya nuna mata 'kofar fita da hannunsa, da sauri ta fice tana sauke ajiyar zuciya, kwana d'aya tayi a cikin gidan jin ta take tamkar a cikin 'kaya, kulle 'kofar palon yayi yazo shigeta ya nufi motarsa....Bin bayansa tayi da saurin gaske, ta ma rigashi bude motar ta shiga ta zauna tana zazzare ido, sai da ya gama magana da maigadinsa sannan ya shiga motar, yana zama tace."Jakar kayana na manta ban dauko ba kuma tana d'akin Yaya Halimatu.'' Ya kalleta cikin rashin walwala yace."To meye amfanin daukar jakar kaya ke a tunaninki ina zan kai ki."? Tace."Na dauka zaka mayar dani gidan Baba Malam." Girgiza kansa yayi yace."Ba can zan kaiki ba zan kai ki gidan Halisa ku zauna da yara zuwa dare sai mu dawo gidan tare." Fashewa tayi da kuka tace"Dan Allah ka daka mu dawo ni wallahi akan na zauna gidan nan gwara na zauna a gidan Anti Halisan yafi." Yace."Kina ganin zaki iya zama a gidan."? Da sauri tace"Eh zan iya." Ba tare da yace komai ba ya bud'e kofar motar ya fita, cikin gidan ya koma ya shiga, jakar kayanta dake dakin Halimatu ya dauko mata ya fito.Ganinsa dauke da jakar kayanta yasa ta sauke ajiyar zuciya,tana ganin gwara ta zauna a gidan Halisa akan ta zauna ita kadai a wannan uban gidan wanda ake bata tsoro, bayan mota yasa jakar, ya shiga ya zauna ya tada motar ya fita daga cikin gidan........Tana ganin sun hau kan titi ta sauke ajiyar zuciya wacce ta sanya shi dan kallonta da gefan ido, ya dauke idonsa tare da maida hankalinsa gurin draving din da yake.............Motar tayi tsit! na kusa minti goma kafin yayi gyaran murya a nutse ya ambaci sunanta! ta kalleshi tare da amsawa, Yace."Ina so inyi miki wata tambaya bana son ki munafurce ni ko kuma ki 'ki fad'a min gaskiya." Tayi shuru tana wasa da yatsun hannunta, Yace."Me yasa bakya so kiyi rayuwar aure dani."? Kallonsa tayi ya gyada mata kansa a nutse yace."Amsa nake so ki bani bance kuma ki bani amsar da zata 'bata mun rai ba." Tace"Saboda na dauke ka a matsayin mahaifina shiyasa nake ganin kamar haramun ne nayi rayuwar aure da kai." Yace."Waye ya fad'a miki haka? shiru tayi Ya cigaba da cewa" Aure a tsakanina dake ba haramun bane Naja'atu, dan na ri'ke ki kin girman a hannuna hakan ba zai hanani na raya sinnar ma'aiki dake ba mutukar Allah ya kad'dara hakan a tsakanina dake, mutane nawa ne sukayi irin wannan auran na *MADADI* kuma auran yayi albarka, inaso ki sani da badan mutuwa ta raba tsakanina da Halimatu ba to da babu abinda zai sanya ni naji sha'awar auranki, na kwadaitu da auranki ne dan ina ganin kamar zaki maye min gurbin matata ta gurin kyawawan halaye gami da sadaukarwa, ashe ba haka abin yake ba, Allah yasa kun fito ke da Halimatu ta tsatso daya amma kuma halin kowa ya bambanta, shin meye aibuna da bakya so kiyi rayuwar aure dani? ko kina ganin ba zan iya dauke miki dukkanin bu'katunki ba ne? Shuru tayi kanta a kasa tana ta nazarin maganganunsa, Ya cigaba da cewa....."Nasan babu irin sa'ke-sa'ke da zuciyar ki ba tayi miki a kaina, kina ganin kamar nazo da son zuciya a cikin al'amarin a matsayina na babba ba yaro ba na aure ki, kina ganin tamkar na cutar da rayuwarki ne tunda na hanaki auran saurayi wanda ya dace da rayuwarki ko ba haka bane".? Kasa magana tayi, Ya cigaba da cewa" Nasan kin san da cewar Annabi Muhammad (slw) ya auri Nana Ayshatu tana 'yar shekara tara, yayin da shi kuma yake da shekara Hamsin, to kuwa idan hakane aurena dake babu haramci a ciki tunda wanda akayi duniya dominsa ma ya auri 'yar 'karamar yarinya wacce bata kai matsayin shekarun da kike ba a yanzu, ina ganin ni na aikata sinna mai kyau tunda nayi irin abinda Annabi ya aikata."......Naja'atu duk jikinta yayi sanyi da maganganunsa, Ya cigaba da cewa" Inaso ki san da cewar abinda kike tunanin wani saurayi mai tashen balaga zaiyi miki a zamantakewar aure to Matashin mutum kamata dan kimanin shekara hamsin zaiyi miki abinda yafi wanda kike tunanin shi saurayin zaiyi miki." ajiyar zuciya ya sauke kafin ya cigaba da cewa" Mafi akasari 'yan matan yanzu abinda ke damunsu kenan.... ((('kalubale gare ku 'yan mata masu tashe saboda ku na zauna nayi wannan littafin, dan akwai masu 'karamar 'kwa'kwalwar da za suce su baza su auri tsoho ba sai saurayi, toh wallahi bari na fad'a muku a wannan zamanin ba'a tsayawa za'ben miji, idan kikace xaki tsaya za'be-za'be to zaki tsufa baki yi aure ba, idan magidanci mai mata yazo auranki idan har anyi binkice mai kyau a kansa an gane cewar yana tsaye a kan gidansa da kula da iyalinsa to ki lalla'ba ki shiga daga cikin, idan kin tsaya kince ke sai saurayi to zaki iya auran saurayin kuma ki kasa samun biyan bukatarki, Samarin yanzu duk 'yan bana bakwai ne kuma mafi akasari auran sha'awa suke daga zarar bukatarsu ta biya shikkenan zaki fuskanci kalubale, bance duka aka taru aka zama daya ba amma dai abinda yake faruwa na fad'a, idan kuwa kika auri wanda ya dan kwana biyu to shi yasan menene aure saboda ya dade a cikin inuwarsa zai ri'ke ki da kyau kuma duk wata soyayya da kike tunanin saurayi zaiyi miki to sugar Dady d'in da kika raina zaiyi miki wacce tafi ta saurayin domin shi tsohon hannu ne a harkar😁)))) Abba Abbas ya cigaba da cewa" Abinda yake damun su kenan sai suce su baza su auri tsoho ba dan suna ganin kamar idan sun auri mai shekaru baza su more kuruciyarsu ba, wanda kwata-kwata ba haka bane sunyiwa abun mummunar fahimta ne, inaso ki zauna kiyi tunani mai kyau a kan wannan maganganun da mukayi dake, Na farko ni ban haife ki ba, ballanta ki dinga ganin kamar kin aikata haramci dan kinyi mu'amular aure dani! Na Na biyu kuma wad'annnan abubuwan da kike yi sun soma isata idan baki gyara ba to zan dauki mataki a kanki, ni ba yaro 'karami bane ballanta ki dinga yi min iskancin da duk kika ga dama, a yanzu ni ina a matsayin mijinki ne ba Ubaba kamar yanda kike dauka a da to yanzu ba haka bane! Wallahi! duk ranar da na sake jin kin fad'i wata mummunar magana a kaina da aurana sai na 'bata miki rai! na dauka kuruciya ce ke damunki sai kuma daga baya na gane rashin arziki ne, to ni ba lusarin namiji bane ke zaki fadawa kowa hakan tunda kin taso a gidana kinga yanda nake zamantakewar aure da mataye na, suna bani girma suna mutuntuni babu wacce take fad'a min bakar magana ko kuma taja min tsaki! dan haka nake gargadinki ki kiyaye aikata abinda zai janyo miki 'bacin raina."
Tun kafin ya gama maganarsa ta rufe fuskarta cikin hijabi tana kuka, shima tunda ya gama maganarsa bai sake cewa komai ba ya cigaba da draving dinsa, daf da zai shiga cikin unguwar ne kira ya shigo wayarsa, koda ya duba sai yaga numbar Halisa a nutse ya daga wayar, Tace"Abban Mufida ya kuma ka fita baka karya ba."? Kai tsaye yace."Naje duba Naja'atu ne yanzu ma dai ganin zuwa tare da ita ta kasa zaman gidan." Da sauri tace."Kamar yaya."? Yace."Idan nazo zanyi miki bayani." Kashe wayarsa yayi dan ganin kamar zata 'kara masa wani 'bacin ran! Yana ta jin shashshekar kunanta sai damunsa take kawai dai yayi mata shuru ne yasan dole idan ta gaji zata daina........Halisa kuwa kasa'ke tayi da waya a hannu shin me hakan yake nufi da zai dauko mata yarinya ya kawo mata gida! cika tayi ta batse ta hard'e a kan kujera tana jiran zuwansu.........
Saboda yasan zai samu matsala daga gurinta yasa ya shiga gidan fuskarsa a murtuke dan baya so tayi masa rashin arziki ya lura ba tayi maraba da zuwan Naja'atun ba......Mussadiq na ganin Naja'atu tare da Abbansu ya tashi a guje yaje ya rungumeta, Allah sarki yaro kenan har ya mance abinda tayi musu, tsugunawa tayi ta rungumeshi tana sumbatarsa a fuska, Abba Abbas kuwa bai tsaya ba kai tsaye dakinsa ya nufa, Halisa ta mike ta bishi tana huci!! Dama ya tsammaci shigowarta, ya tsira mata ido yana kallonta ganin yanda idonta yayi jajawur lokaci guda, Ri'ke 'kugu tayi tace"Nifa bangane ba meye amfanin kawo ita gidana naga harda jakar kayanta." Yace."Eh kamar yanda na fad'a miki a waya hakane tana jin tsoron zaman gidan ita kadai shine dalilin da yasa na daukota na kawo ta ta zauna nan kafin na yanke hukunci." Murya na rawa tace"To ba sai ka kai mata su Saddiqa su taya zama ba, meye sai ka kawo min ita gida." Yace."Ina tunanin ko ta ganta tare dasu Saddiqar ba zata samu nutsuwar da ake bukata ba." Tace"To naji a'ina kake shirin ajiyeta." Cikin jin haushin titsiyen da take masa yace."A duk inda nayi ra'ayi gidana ne ai." Ganin ya fusata! yasa ta dan sassauta tace"Sai dai a gyara mata d'aya sashen ta zauna dan ni bana jin zan iya zama tare da ita." Yace."Ai dama ba'ace dole ki zauna da ita ba tunda ita tafi so ta zauna anan ke yanzu zanyi duk yanda zanyi cikin satin nan a gyara miki inda zaki zauna a can gidan." Girgiza kanta tayi tana 'kas-'kas! da cingum! din bakinta tayi wani murmushi tace"Ba zai yiwu ba! ai na fad'a maka ba zan amince da wannan rabe raben gidan ba, nima ina nan babu inda zanje." Daga mata hannu yayi yace."To magana ta 'kare kada nan gaba kice min zaki koma can dan ba zaki koma wallahi." Tace."Ai duk inda kake ina nan idan ka tattara ka koma can nima zan tattaro nawa nawa na biyo bayanka." Shuru yayi mata ya zauna gefan gado, ta juya ta fita tana fadin "Bari na kawo maka kayan break din." Tana fita ta gansu zaune a kujera sun kewaye ta har da Mufida sai murna sukeyi tamkar sunga wata sabuwar hallita, ita kuma sai murmushi take musu.....Halisa taja tsaki cikin tsawa tace"Ke Mufida me kike anan zo nan ki taya ni 'aiki." Yarinyar ta mike da sauri! Halisa ta nuna mata hanyar kicin tana fad'in "Bana son shashanci ni kun wani zauna kuna dariyar banza." Naja'atu dasu Saddiqa suka bita da kallo tana kokarin shiga kicin tana surutai.........Bayan shigewar Halisan, ta kalli Su Saddiq tana nazarinsu, kwana biyu da bata gansu ba sai taga kamar sunyi rama ta rike hannun Mussadiq tare da fad'in "Kayi rashin lafiya ne."? Girgiza kansa yayi yace." Yaya Naja'atu kema kin dawo nan kenan na dauki akwatin kayan ki na kai miki dakinmu."? Kanta ta d'aga masa idanunta na kawo ruwa, da sauri yaron yaje ya shiga jan jakar kayan Saddiqa ta mike taje tana taimaka masa, Naja'atu binsu tayi da kallo hawaye ya zubo mata tausayi yaran suka bata, tana ganin ko dan saboda su zata dinga adduar Allah ya sanya mata dangana domin ta zauna tare da dasu.......Halisa ce ta fito daga kicin hannunta ri'ke da tire jere da kayan tea ko kallon inda Naja'atun take ba tayi ba tayi ba ta nufi dakin maigidan, Naja'atu ita dai binta da kallo kawai take..........
Yana zaune 'kasan kafet ta shiga dakin, ajiye tiren tayi ta zauna tana kokarin had'a masa tea din yace."Ki bawa Naja'atu abinci dan bana tsammanin taci wani abu tun jiya." Kallonsa tayi kamar za tayi magana kuma sai ta fasa, ta hada masa tea kana ta zuba masa farfesun kayan cikin rago wanda yaji magani! ta mike ta fita daga dakin...........Saddiqa ta kalla tace"Ke Saddiqa ki shiga kicin ki girka muku abinda zaku ci dan ni ba baiwar kowa bace."! tana gama maganarta ta shiga dakinta......
Saddiqa ta mike da sauri tana kallon Naja'atun tace."Don Allah Yaya Naja'atu kada ki kulata." Murmushin takaici tayi tace."Jeki yi aikin ni ba'a gabana take ba ballanta na tanka mata." Saddiqa ta sauke ajiyar zuciya ta wuce kicin din, mikewa tayi ta nufi dakin su Saddiqar nan ta tarar da Mussadiq yana ta jera mata kayanta a cikin wardorbe dinsu, Tace"Mussadiq daka bar kayan ma a jakar da yafi." Yace."Ai akwai guri a wardrobe din shiyasa nake shirya miki kayanki a ciki." Zama tayi tana bin dakin da kallo, gado uku ne kananu irin na 'yan boarding....Mussadiq yace."Yaya Naja'atu zan baki gado na ki kwanta kafin Abbanmu ya kawo miki naki." Tace"To nagode Mussadiq." ya mike da sauri yana fad'in "Bari ma naje na fada masa." Kallo ta bishi dashi har ya fita daga dakin....Dakin Abban nasu yake kokarin shiga Halisa ta hangoshi tsawa ta buga masa da fad'in "Me zaka shiga kayi."? Yace."Zan fad'awa Abbanmu ne cewar Yaya Naja'atu bata da gado." Cikin tsawa! tace"To sarkin iyayi da rawar kai ai ya fika sani." Abbah Abbas din ne ya fito daga dakin nan Halisa ta gyara yanayin fuskarta Tace."Gashinan wai yana so ya shiga yayi magana da kai shine nace masa kana cin abinci sai ka fito tukkuna." Ya kalli Mussadiq din a nutse yace."Menene."? Mussadiq yace."Abbah Yaya Naja'atu bata da gadon kwanciya amma kayanta sun samu guri a wardrobe d'in mu." Murmushi yayi yace."Gaskiya Magaji kana son Yaya Naja'atu sosai kada ka damu zansa a kawo mata gadonta itama." Murmushi yaron yayi yace."Nagode Abbah." Cike da farin ciki ya nufi dakin nasu yana so yaje ya fad'a mata abinda Abban nasu yace..........Abbah Abbas fita yayi daga gidan ya tafi sabgoginsa sai yamma likis ya shigo unguwar kuma bai shiga gidan ba sai bayan sallahar isha'i, Halisa yau ma ta cancad'a kwalliya kamar itace amaryar tana zaune a palo ita da yaran suna kallo kamar jiya, ita kuwa Naja'atu ta kasa zama a palon tana d'aki ta takure kanta sai neman Salim take a waya bata shiga.....Hannu bibbiyu Halisa ta kar'be shi, ta bashi abinci yaci kamar koda yaushe ya dawo palon ya zauna nan yaga babu Naja'atu a gurin, Ya kalli Mussadiq da fadin "Ina Yaya Naja'atu." Mussadiq yace."Tana dakinmu nace ta fito muyi kallo ta'ki." Kai tsaye yace."Je ka kirata." Yaron ya tashi da sauri! ita kuwa Halisa shan kunnu tayi ta wani tamke fuskarta....Da hijab a jikinta suka fito ta zauna kan kujera kanta a kasa tace"Abbah Sannu da zuwa." Ya amsa yana nazarinta yace."Me kike a daki ke kad'ai bayan kowa na palo." Shuru tayi, Ta kalli Halisa a nutse yace."Inaso nayi magana daku a dakina." Mikewa yayi ya nufi dakinsa." Halisa ta mike tabi bayansa, ita kuwa Naja'atu gyara zama tayi dan bata fahimci maganarsa ba, Minti biyar da shigar Halisa dakin nasa Kira ya shigo Wayarta koda taga numbarsa sai gabanta ya yanke ya fad'i! ta dauki wayar Yace."Ki shigo dakina zanyi magana daku." a raunane tace"To." Kashe wayarsa yayi, Halisa kam sai jijjiga kafa take ta cika ta batse sai wani 'kas-'kas take da cingum din bakinta, Ya kalleta cikin 'bacin rai yace."Malama ki cire wannan cingum din na bakin ki." Ta daina 'kas-'kas din tayi ta dauke kanta......Da 'kyar ta iya mi'kewa ta nufi d'akin nasa yayin da yaran suka bita da kallo, Saddiqa dai duk tafi su hankali ta gane Yanzu Yaya Naja'atu dai-dai take da Anti Halisa a gidan to dan ta shiga dakin Abban nasu ba abun mamaki bane.......
*GA MASU BUKATAR KARANTA BOOK DIN ZASU TURA #300 SINGLE, VIP GROUP #600 GA ACCONT D'IN DA ZA'A TURA KUDIN.......0542382124.....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATIN WAYA ZAKI TURA KIYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBAR......07084653262.....IDAN KIN SAN BA BIYAN KUDIN LITTAFIN NAN ZAKI YI BA DON ALLAH KADA KI KIRA WAYA TA KO KIYI MIN WATA MAGANA TA WHASAP*

*MUTANAN MU NA NIJAR IDAN KUNA SO KU BIYA KUDIN LITTAFIN ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN NUMBARS.........90899076_88137740 KATIN AIRTAL KO ORANGE.*


*🗯️MADADI!!💍*
_(Ba Haram Bane!!)_

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~


_*Aunty Binta wai dan Allah me yasa duk littafin ki kike bawa maza Power akan mata ni dai duk na karanta novls din 'ki ban ta'ba ganin wanda kika bawa mace power ba*😅_

_*MAFI A KASARIN TAMBAYAR DA MUTANE KEYI MIN KENAN WAI ME YASA NAKE BAWA MAZA POWER! A LITTAFIN NA, TO GA AMSA, BANI NA BAWA MAZA POWER (IKO) BA ALLAH NE YA BASU, NAMIJI IN DAI SUNANSA NAMIJI TO KOMAI 'KAN'KANTARSA SAI YA JAGORANCE KI KODA KUWA KE KIKA HAIFE SHI, TO BALLANTA NAMIJI A CIKIN GIDANSA😅 TO AI NI KO LOKACIN DA NAKE KARATUN LITTAFIN HAUSA DAGA NA FARA KARANTA LITTAFI NAGA AN BAWA MACE POWER A KAN MIJINTA NAKE DAINA KARANTAWA DAN NA TSANI LUSARIN NAMIJI WANDA BAYA IYA JAGORANTAR GIDANSA, MEYE AMFANIN POWER MACE A GIDANTA🤔 IDAN YA KASANCE KINA JUYA MIJIN KI TO ME KENAN AKAYI? AI DUK GIDAN DA KUKA GA MACE NA MULKI A CIKINSA TO TA KAUCE HANYA NE, NI DUK MACEN DAKE MULKI A GIDAN AURANTA TANA JUYA MIJINTA YANDA RANTA YAKE SO WALLAHI BATA BURGENI SABODA NASAN 'KARSHEN TA NADAMA! MATA SU ZAUNA A 'KARKASHIN MAZAJEN SU KAMAR YANDA ALLAH YACE, SU KUMA MAZAN SU KULA DA DUK WASU HAKKO'KIN MATAYEN SU, AMMA BA WAI INA FIFITA NAMIJIN NOVEL AKAN MACEN NOVEL BA INA SO INA NUNA MUKA ABINDA YAKE FARUWA A ZAHIRI SHINE NAMIJI KO MAI 'KAN'KANTARSA JAGORA NE😁*_


*17_18*
Kanta a 'kasa ta shiga dakin da sallama a bakinta, Shi kadai taji ya amsa sallamar dan ko Halisa ta amsa ita dai ba taji ba.
Kusa da Halisan ta zauna tare da sunkuyar da kanta 'kasa, dakin ne yayi shiru na tsayin minti uku kafin yayi gyaran murya kamar yanda ya saba idan zaiyi magana yace." Gabad'ayan ku nasan kunsan abinda yasa na tara ku anan ko."? shuru sukayi babu wacce tayi magana.
Ya kalli Halisa a nutse yace."Tun kafin na kawo miki Naja'atu gidan nan mun gama magana dake ina fatan zaki kar'bi yarinyar nan hannu biyu ki dauke ta a matsayin *'ya* ba kishiya ba, wannan kad'ai za kiyi min ki nuna min ke mai kaunata ce." Halisa ta d'ago kanta da sauri ta kalleshi, lallai sai ta ri'ke yarinyar a matsayin *'Ya* ba kishiya ba sannan zai gane ita mai kaunarsa ce maganar ma mamaki ta bata sosai kuma ta 'kara tabbatar da cewar namiji bashi da kunya, komai 'kan'kantar kishiyarta yaushe zata dauke ta a matsayin *'Ya* wannan magana ma bai mai yiwu bace. To shima dai da ya fad'i maganar yasan abune da ba zai ta'ba yiwu ba dan ya riga yasan yanda Halisa take da masifar kishi ai da wuya ta ri'ke yarinyar a matsayin *'Ya* ko *'Yar uwa*......Hankalinsa ya mayar kan Naja'atu ya dan tsira mata ido na minti biyu kafin ya kira sunanta.
Da sauri ta d'aga kanta tana kallonsa da idanunta da suka soma kawo ruwa.
Ganin ita yake kallo yasa tayi saurin sunkuyar da kanta gabanta na fad'uwa!
Yace."Ke ma d'azu kafin na kawo ki cikin gidan nan mun gama magana dake kuma ina fatan dukkanin abinda na fad'a miki sun shiga kunnan ki kiji ki kuma shiga hankalin ki, zaman aure kika shigo kiyi a gidana ba shirme da shashanci ba, wannan da take zaune tafi kar'fin raini a gurinki." Yafada yana nuna mata Halisa, bata kalleta ba sai sake sunkuyar da kanta 'kasa da tayi
Ya cigaba da cewa"Duk ina sane da rashin kunyar da kike mata a lokotan baya! bakya ganin girmanta duk irin maganar da tazo bakin ki fad'a mata kike bakya gaisheta a duk inda zaku had'u! tsaki! harara duk babu wanda bakyayi mata, to duk nasan da hakan nake kyale'ki koda ita Halisan zata kawo 'karar ki ina bata hakuri saboda a samu zaman lafiya ina kuma nuna mata ke yarinya ce idan kika kara hankali zaki daina.......Halisa tayi hakuri da halayen ki a baya, dan haka a yanzu kada naji kada na gani kin zageta ko kin fad'a mata bakar magana ko kuma kinyi mata tsaki! tsakaninku mutunci da mutunta juna inaso ki dauki Halisa a matsayin Uwa

2 Comments On MADADI
avatar
sumayya-1-4

7 months ago

Reply

Hw can I get the complete text please

avatar
abasu-kala

7 months ago

Reply

Replying to sumayya-1-4

You have to pay 1k first for subscription in order to download our novels

Please Login or Register in order to submit comment