Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sam bata ta'ba tsammanin haka daga gareta ba...... a nutse yace."Saddiqa kuje ku kwanta kinji ko, dukkaninku ku daina damuwa ku saki jikinku a gidan nan gidanku insha Allah ba zaku samu wata matsala ba." Saddiqa murya na rawa tace"To Abbah." Ya sunkuya yana d'an tashin Mussidiq ya tashi yana mutsika ido, ganin Abbansa yasa ya bude idonsa sosai, Abba Abbas d'in ya rike hannunsa ya mike tsaye.........Shi da kansa ya rakasu d'akin dama gado uku ne mai dauke da madaidaiciyar katifa da pillo da bargo, Mufida ta gyara nata ta kwanta, Abbah Abbas da kansa ya shimfidawa Saddiqa da Mussadiq sabon bedshirt ya gyara musu sosai sannan suka kwanta, Ya tsaya kansu yayi musu addua sosai kana ya fita daga dakin tare da kulle musu kofa.............To bayan barin Abbah Abbas daga gurin Malam Baba shima Abbah Magaji sallama yayi masa kancewar kafin ya shiga gidansa zai tsaya ya siyi dik abinda za'a bukata gurin daurin auran, Malam yaji dadin hakan yace."Dashi kafin ya tafi ya shiga gidan Alhaji domin ya sheda masa abinda ke faruwa, koda Alhaji yaji bayanin da Abbah Magaji yayi masa sai ranshi ya 'baci! ya za'ayi sun riga sun gama magana da Abbah Abbas din kan cewar ya janye maganar auran yarinyar kuma dan yaga baya gurin zai sauya magana, yaji haushin hakan ya dauki laifi kacokan ya d'orashi kan Abbah Abbas d'in, Dan 'kin tsayawa ma yayi ya saurari bayanin da Abbah Magaji ke masa, ya sauko daga samansa, kai tsaye futa yayi daga gidan, Abbah Magaji na binsa a baya........Malam Baba yayi mamakin fusatar Alhajin kasancewar yasan shi d'in mutum ne mai saurin fahintar abu da kuma sau'ka'kawa cikin ko wane al'amari.......Da 'kyar Baba Malam da Abbah Magaji suka fahimtar dashi ya gane cewar ba laifin Abbas din bane sune suka tursashi......Alhaji Sama'ila yayi shuru yana ta nazarin al'amarin, daga bisani kuma addua yayi da fatan alkairi tabbas tunda Allah yayi haka to babu alkairi a cikin auran Naja'atu da Salim d'in,......Shine ya sake 'karfafawa Abbah Magaji, cewar yayi 'kokarin tana dar duk abinda ake bukata a gurin daurin aure tabbas babu makawa gobe auran Naja'atu da Abbas sai ya d'auru.........Sai misalin goma da rabi sukayi sallama da juna kowanne ya shiga gidansa cikin fatan alkairi ga junansu.........Baba Malam kafin ya kwanta sai da ya sanar da Baba Talatu abinda ake ciki na irin hukuncin da suka yanke cewar Za'a daura aure gobe dan jan lokacin bashi da amfani, Baba Talatu taji dad'in hakan sosai kuma tayi fatan alkairi dangane da al'amarin.....Naja'atu dake takure kan shimfidarta a lokan rumfar luf!! tayi kamar mai bacci tana sauraran maganganunsu, sai da taga sun shiga daki, da niyar kwanciya sannan ta mike a hankali ta dauki wayarta dake kusa da ita ta mike ta fita daga dakin ........Daya dakin ta nufa tana shararar da hawaye, xaman 'yan bori tayi tana toshe bakinta domin kada sautin kukan da take ya fita suji, wayar ta kunna hannunta na kyarma ta shiga laluben numbar Abbah Abbas d'in, tana jin idan bata zageshi ba zuciyarta na iya bugawa.........Yana zaune a palo shi kadai da Loptop a gabansa yana duba sa'konnin abokan kasuwancinsa na 'kasashen waje, Kiran wayar ta ya shigo wayarsa dan duban wayar yake hankalinsa na kan typing din da yake cikin loptol din, koda yaga numbar Naja'atun baiyi gaggawar dauka ba, ya janye idonsa ya cigaba da abinda yake Naja'atu! ta dingi kiran wayar tamkar zata kashe masa dodon kunne dole ba yanda ya iya ya daga wayar tare da gyaran murya babu wasa a cikin muryarsa yayi sallama....
'Dif! tayi gabanta na wata irin fad'uwa! sakamakon jin sautin muryarsa mai cike da kwarjini da rashin wasa yasa ta mance abinda yasa ta kiransa a wayar sai mazari jikinta yake tana sha'kar hanci had'e da sauke ajiyar zuciya irin na wanda yaci kuka ya 'koshi........'Dan gyaran murya yayi a karo na biyu yace."Dota ya akayi ne dare yayi baki bacci ba."......Murya na rawa tace"Me yasa ka san ni 'yar kace kake shirin aurena."? Shuru yayi yana nazarin maganarta, Yace."Eh abinda yasa nake kiran ki da Wannan suna (Dota) saboda nasan a matsayin shekaruna da Allah ya bani haihuwa da wuri dana haife ki kamar ki ko wacce ta fiki so ina ganin babu laifi dan na kira ki da wannan suna."!A hasale! tace." To tunda dai da bakin ka ka fad'a cewa a matsayin shekarunka da Allah ya baka haihuwa zaka iya haifeta ko wacce ta fini me zai sanya ka zubar da k'ima da mutunka a gurina ni da ka 'rike kamar 'yar cikin ka, ka sani ba da badan mutuwa ta ratsa tsakanin ka da matarka ba da kowa yana maka kallon matsayin uba a gare ni." Murmushi yayi wanda har sai da taji sautinsa a kunanta Yace."Nifa ban haife ki ba ki daina kirana Ubanki yanzu sunan da yafi kamata ki kirani dashi shine Mijin ki dan gobe idan Allah ya kaimu iwar haka kin zama matata"! Taji tamkar ta d'ura masa ashar! sai dai ta daure taja wani matsiyacin tsaki! mai 'karfi! da fad'in "Amma dai anji kunya wallahi."!! Kit! ta kashe wayar tana wani irin huci!!! Abbah Abbas ya dinga bin wayar da kallon mamaki! Yau shi yarinyar nan take jawa tsaki har tana kokarin zaginsa, Kasa hakura yayi ya sake kiran wayar! A fusace! ta d'aga ta bud'e baki za tayi magana, ya buga mata wata masifaffiyar tsawa! da fad'in " Dan Ubanki ni kike zagi ashe baki da mutunci dama."!? Jikinta ya shiga karkarwa domin tsawar da ya buga mata bata ta'ba saninsa da ita ba, kashe wayar tayi gabad'aya ta kwanta tare da takure jikinta tana kuka mai tsuma zuciya, ta kirasa a waya domin ta farfad'a masa magana mai zafi 'karshe shi ya fad'a mata maganar data ya mutsa mata tunani har da zagin Ubanta..........Abbah Abbas ya ajiye wayarsa a fusace! ya rufe loptop din ya mike ya nufi bedroom d'in Halisa........... *Sorry kuyi hakuri waya ta ta d'an samu matsala wallahi zaku ga yanayin typing din ba irin yanda na sababa........Ina ro'kon Ubangiji Allah ya kawo mana zaman lafiya a wannan 'kasa tamu ta Najeria Ubangiji Allah ka bamu nutsuwa da daidaito a tsakaninmu amin.........MY FANS KADA MU MANTA DA SALATIN ANNABI A WANNAN RANA MAI ALBARKA SANNAN KUMA MU DAURE MU KARANTA ABINDA YA SAWWA'KA DAGA CIKIN SURATUL KHAFI.*
*************************GA MASU BUKATAR KARANTA BOOK DIN ZASU TURA #400 SINGLE, VIP GROUP #600 GA ACCONT D'IN DA ZA'A TURA KUDIN.......0542382124.....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATIN WAYA ZAKI TURA KIYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBAR......07084653262.....IDAN KIN SAN BA BIYAN KUDIN LITTAFIN NAN ZAKI YI BA DON ALLAH KADA KI KIRA WAYA TA KO KIYI MIN WATA MAGANA TA WHASAP

*MUTANAN MU NA NIJAR IDAN KUNA SO KU BIYA KUDIN LITTAFIN ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN NUMBARS.........90899076_88137740 KATIN AIRTAL KO ORANGE.*


*🗯️MADADI!!💍*
_(Ba Haram Bane!!)_

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~
*13*
Ranshi a 'bace! ya aje loptop din kan wani tevur ya nufi toilet alwala ya daura ya fito ya hau kan dadduma ya tayar da sallahr nafila, raka biyu yayi ya daga hannunsa sama yana rokan Allah ya za'ba masa abinda yafi alkairi a rayuwarsa, kwata-kwata ji yayi auran yarinyar ya fice masa daga rai! a sabili da irin iskancin da wulakancin da take masa da shida 'ya'yansa bai ta'ba tsammin faruwar hakan daga gurinta ba yana ganin barin auranta kamar shi yafi alkairi don baya so da girmansa da komai yarinya k'arama tazo tana fada masa maganar da duk ta gadama, mikewa yayi daga kan dadduma yaje ya kwanta kusa da Halisa, ya d'an janyo ta jikinsa,
Bude idonta tayi ta wani fizge jikinta tana jan tsaki! Al'amarin sai ya bashi mamaki! ganin cewar d'azu suka gama magana da ita kan cewar komai ya wuce amma saboda ya ra'bi jikinta tana fizgewa, bai yi zuciya ba ya sake kai hannu zai janyota ta mike zaune tana 'bata fuska tace"Nifa ba zan sake amincewa da bukatarka ba sai na yankewa kaina hukunci tukkuna dan gaskiya ni maganganunka na dazu basu shige ni ba."
Ya mike zaune yana kallonta cikin d'umbin mamaki! yace." Wane irin hukunci zaki yankewa kanki bayan wanda muka yanke d'azu na dauka yanzu dani dake mun zama d'aya, ashe duk maganar da mukayi dake dazu ta banza ce." Tace."Kawai ka rabu dani na cigaba da tunanin mafita ni ba zan sake amincewa bukatarka ba kaje idan an daura auranka da 'karamar yarinya sai ka sauke bukatarka a kanta." Cikin tsabar takaici yace."Halisa ban ta'ba ganin mara hankalin mace irin ki ba wallahi kin girma amma har yanzu kin 'ki hankali 'Yar cikin ki Mufida ta fiki nutsuwa."
Tace."Duk dai abinda za kace a kaina kace ba zan amince da kai ba wallahi sai yarinyar nan ta shigo gidanka naga irin zaman da zakayi da ita."
Murmushi takaici yayi cikin sigar 'kuntatawa yace."Zanyi zama da ita irin na ma'aurata kuma ba zaki hana ni na ji dad'ina da ita ba." A fusace! taja tsaki! da fad'in "Kana tare da kunya kuwa duk ranar da 'yayanka su kaga ka kwana a d'akin wacce suka d'auka a matsayin yaya a gurinsu, sai ka tanadi abinda zaka fada musu."
Girgiza kansa kawai yayi ya dauki rigarsa yasa a jikinsa ya sauka daga bed din hanyar fita ya nufa jiri naso ya kayar dashi, gabad'aya ji yayi duniyar tayi masa zafi ko ina babu sassauci tabbas sai yanzu ne zai fara kukan rashin matarsa da yayi, a da baiyi kukan rashin Halimatu ba sai yanzu da Halisa da Naja'atu suke gwara kansa a bango....

'Bangaran Naja'atu kuwa yanda taga rana haka taga dare daga zarar ta tuna da cewar gobe za'a daura mata aure da Abba Abbas din sai gabanta ya fad'i ta hau takure jikinta, ta jima tana sa'kawa da kwancewa da tunanin mafita a gareta, tana so gari ya waye ta kira Salim a waya ta sheda masa hukuncin data yanke.......Aikuwa tana idar da Sallahr asubahi ta shiga kiran wayar Salim din inda akaci sa'a yau ya tashi da wuri, ya dauki wayar cikin mayaudariyar miryarsa yace.."My Princess kin tashi lafiya."? Murya a 'kasa tace"Lafiya kalau my prince." Ya wani narke murya irin yanda yake mata yana kashe mata jiki yace."My Prince jiya kwana nayi da tunanin ki da begen ki har mafarki nayi dake muna kwance a gado d'aya kina bani kulawa."
Ta rintse idonta hawaye na zuba tace."My Prince Abba Abbas naso ya yanke mana jin dad'inmu bana tunanin zan iya mallakawa wani da namiji kaina sai kai! bana sha'awar kowa sai kai soyayyar ka kawai nake muradi! amma ina tunanin mafarkina dakai ba zai tabbata dan ganin yanda magauta suke 'kokarin kassara mana rayuwarmu." Mikewa zaune yayi yace."My princess ki fad'a mun yanzu a wace matsaya aka tsaya dangane da maganar auranki da Abbah Abbas din.
Tace."Komai yazo karshe My Prince jiya da daddare Baba Malam naji yana fad'awa Baba Talatu cewa gobe bayan sallahr juma'a za'a daura aurena dashi, wannan dalilin yasa na yanke hukuncin guduwa daga garin gabadaya su neme ni su rasa."
Salim ya shiga goge gumi ma'kogwaronsa ya bushe sosai, yace."Innalilihi wa'ina ilahi raji'un! abinda ya iya fad'a kenan, murya na rawa yace."My bani da kuzarin yin magana yanzu saboda na shiga rud'u da tashin hankali jin wannan maganar taki, zan kira ki anjima kafin nan nayi nazari kan hukuncin da kika yanke."

Kashe wayar yayi ya zauna yana tunani.......Ashe dai dattijon nan da gaske yake sai ya dasa masa 'kunci da ba'kin ciki! to kuwa in dai ya kasance cewar ya samu nasara a kansa gurin auran Naja'atu to shi kuma zaiyi amfani da damar sa, a gurin ita Naja'atu duk wani abunda yake bukata a gurin yarinyar ba zai same shi ba sai ta zame masa mafisa wanda da kansa zai gaji ya saketa, koda ya saketa shi ba auranta zaiyi ba yana so ya kawai ya dasa masa 'kunci da 'bacin rai kamar yanda ya dasa masa a zuciyarsa.

Mikewa yayi ya shiga cikin gidan...Yaya Ramlatu na kicin tana kokarin kunna wuta, taga shigewar d'an nata, sai da ta kunna wutar ta d'ora ruwan kunu kan murhun, sannan ta bi bayansa, koda ta shiga dakin gani tayi ya takure kansa hade da dafe kansa, Kafin ma tayi magana taga yana hawaye.
Tace."Salim lafiya me yake faruwa."? Cikin tsabar bakin ciki yace."Yaya 'Dan uwanki bashi da kirki ya kasance mutum mai son kansa, ya cuce ni ya cutar da rayuwata kuma ya yaudare ni da yasa na amince masa na daukeshi a matsayin uba ya ha'ince ni, yarinyar dana 'kwallafa raina a kanta yau xa'a daura masa aure da ita, ba zan ta'ba mantawa da wannan mutumin ba."

Yaya Ramlatu ta dinga mamakin maganar tace."Kai waye ya fad'a maka yau za'a daura auransa da Naja'atu da har kake wannan maganar......A fusace! yace."Ita yarinyar ce ta fad'a min yanzu ta kirani a waya tana kuka tare da sheda min hukuncin data yanke kancewar zata gudu daga garin gabadaya."

Shuru Yaya Ramlatu tayi takaici da bakin ciki kamar ya kasheta, lallai Abbas bai da alkawari kamar dai yanda Salim din ya fada hakane Abbas yafi son kansa akan kowa bai duba soyayyar dake tsakanin Salim d'in da Naja'atun ba sai da ya shiga ya fita ya raba tsakaninsu......Tace."To shikkenan sai ka hakura ka fawwala wa Allah tunda Allah yasa ya samu nasara a kanka, maganar Naja'atu zata gudu ta bar gari bata taso ba dan idan hakan ya kasance to kowa zai d'ora zarginsa a kanka, dan haka kace mata baka amince ba, dan bana son abinda zai janyo min 'bacin ran iyayena."
Yace."Idan ya kasance Naja'atu ta tare gidan Kawu Abbas wallahi tallahi nayi al'kawari sai na 'kunsa masa ba'kin ciki da takaici kamar yanda ya 'kunsa min, tunda dai Naja'atu ni take so ai magana ta 'kare zuciyarta tana hannuna shi kuma yana tare da gangar jikinta."
Yaya Ramlatu tace"Duk wani iya shege da rashin arziki da zaka yi masa ban hanaka ba, kaje kayi domin shima yaji idan da dad'i abinda yayi maka d'aurin aure suje suyi babu inda zanje." Yace."To dama me zaki je kiyi a gidan gabad'aya ma da Alhajin da ita Hajiyan basa kaunarki da suna kaunar ki ba zasu bari haka ya faru ba, sunfi kaunar Kawu Abbas d'in saboda yana da kud'i." Yaya Ramlatu ta dinga girgiza kanta takaicin da ba'kin ciki dik ya cika mata zuciya.

Da asubah da kafin ya tafi massalaci sai da ya shiga ya tashi yaransa domin suyi sallah, koda ya fito daga dakin nasu bai ko kalli dakin Halisa ba dan har yanzu haushinta yake ji yana ganin duk wani kokari da ya kamata yayi a kanta yayi zai dauke mata wuta gabad'aya dan ba zai cigaba da rarrashinta taba tana masa iskancin da taga dama.
Bayan ya dawo daga massalaci ya koma dakin nasu nan ya tarar dasu sunyi sallah suna zaune Saddiqa da Mufida suna magana, dukkaninsu suka shiga gaishe shi ya dinga amsawa cikin nutsuwa da kulawa, ya kalli Saddiqa a nutse yace." Saddiqa ki shiga kicin ki dafa muku tea da abinda kike ganin zaki iya." Tace."To Abbah." Mikewa tayi tana kokarin cire hijab d'inta shi kuma ya fita daga d'akin, Kai tsaye d'akin Halisa ya nufa domin ya dauki loptop dinsa.
Tana kwance kan bed din ta tsirawa rufin dakin ido, da alama ma ba tayi sallah ba, Ko kallon inda take baiyi ba ya dauki loptop dinshi ya kama hanya ya fita daga dakin, Halisa tabi bayansa da kallon ba'kin ciki tamkar ya tarwatsa mata zuciyarta..............Saddiqa na tsaka da aiki a kicin taji an buga mata uwar tsawa! "Ke dan Ubanki waye ya baki dama ki shigo min kicin."!? Jiki na rawa tace." Abbah ne yace na dafa mana tea da indomee." Da hannu ta nuna mata 'kofar fita da fad'in "Fice ki bar min kicin 'yar iska munafuka masu gadon mugun abu." Saddiqa hawaye ne suka tawo mata, tayi saurin mayar dasu tana kokarin fita daga kicin din Halisa ta kai mata ran'kwashi a kanta tana zaginta. Da sauri ta 'karasa ficewa daga kicin din hawayen da take ta kokarin mayarwa suka zubo.......Ganin yarinyar ta fito a firgice yasa ya kalleta yana tambayar ta menene."? Tana share hawaye tace"Babu komai." Tsawa yayi mata da fad'in "Ba zaki fad'a min menene ba."? Tace." Anti ce tace na fice mata daga kicin." Yace."Zoki zauna anan." Kusa dashi ya nuna mata, taje ta zauna tana goge fuska, cikin tausasawa yace."Kiyi hakuri ki daina kuka kinji ko." 'Daga kanta tayi tana goge hawaye, laptop din dake cinyarsa ya ajiye kan kujera ya mike ya nufi kicin din, Halisa na tsaye tana feraye doya ya shiga ya sameta......Babu walwala a tare dashi yace."Me yasa kika hana Saddiqa ta had'a musu abun kari."?
Juyowa tayi dan ba tasan ya shigo kicin din ba, ganin fuskarsa a murtuke yasa itama ta murtuke tata fuskar tace"Ai sai ka tsaya ka gani idan nayi ban basu ba sai ka bata umarnin tayi musu meye wani zaka ce ta shigo min kicin."!! Girgiza kansa yayi bai ce mata komai ba ya juya ya fita daga kicin d'in, sam bai dauka Halisa za tayi abinci ta bawa yaran ba dan ganin irin rigamar da sukayi ita dashi jiya shiyasa ya umarci Saddiqan ta shiga kicin domin ta samar musu da abinda zasu ci........Suna zaune shida yaran Yaya Ramlatu tayi sallama ta shigo, turus tayi ganinsa zaune a palon, shima cike da mamaki yake binta da kallo, har ta'karaso ta zauna kan kujerar dake fuskantarsa, Yaran ne suka shiga gaisheta ta dinga amsawa tana washe bakinta.
Cikin nutsuwa ya gaisheta ta amsa tana ta dariya kamar wacce ta shigo gidan da abin arziki, Tace."'Dazu Salim yake sheda min cewar anjima wai za'a daura auranka da Naja'atu hakane ko." ? Yace."Eh insha Allah bayan an sakko daga sallahr za'a daura anan massalacin jikin gidan Alhaji."
Tace."Allah ya sanya alkairi yasa haka shi yafi alkairi, amma banji dadi ba da baka fad'a min ko a waya ba sannan daga can gidan Alhajin ma babu wanda aka turo domin ya fad'a mun sam ba'a daukeni a bakin komai ba, ace maganar daurin auren ma sai a bakin Yarinyar mukaji dan da asussuba ta kira Salim tana kuka tana fad'a masa cewar za'a daura auran kuma idan an d'aura to zata gudu ta bar gari a neme ta a rasa, wannan maganar ta tayar min da hankali sosai saboda nasan yarinyar nan ta gudu to da kai da Salim zaku shiga cikin masifa, dalilin da yasa na umarci Salim din maza ya kira ta a waya sheda mata cewar bai amince da 'kudirin data dauka ba, Kuma nace ya fad'a mata cewar shi tuni ya cire ta a zuciyarsa, dan haka ta daina tunanin guduwa a kansa ta zauna a gidan mijinta tayi zaman aure mai tsafta."
Abbah Abbas ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Yaya Ramlatun yace."Dukkanin abinda ki kaga yana faruwa to dama can haka Allah ya 'kaddara zai faru, ko a mafarki ban ta'ba tsammanin wai zan auri yarinyar nan ba, sai dai kuma babu yanda Allah baya tsara al'amarinsa, mutuwar Halimatu ta janyo min sha'awar auran yarinyar domin ina ganin yarinyar tarbiyar tace kuma zata zame min *MADADIN TA* ta gurin kyawawan halaye da sauransu, sai dai kuma ashe ba haka al'amarin yake ba , Allah shine ya hallici Halimatu ya kuma Hallice Naja'atu a bigire d'aya, sai kuma ya bambamta musu halaye, Halin Halimatu daban Halin Naja'at daban, A jiya mun zauna da Alhaji mun tattauna magana kan cewa na janye bukatata tasan auran yarinyar, zan kuma shige gaba gurin ganin Salim ya mallaketa, a lokacin da naje wa da Baba Malam da maganar shi kuma ya nuna bai amince ba, yace yarinyarsa bata da miji sai ni saboda ni yayi ra'ayin bawa auran 'yarsa, dik yanda naso na fahimtar dashi ya kasa fahimta, haka nayi musu sallama na dawo gida ina fatan Allah yasa hakan shine alkairi a gare mu baki d'aya."



*GA MASU BUKATAR KARANTA BOOK DIN ZASU TURA #300 SINGLE, VIP GROUP #600 GA ACCONT D'IN DA ZA'A TURA KUDIN.......0542382124.....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATIN WAYA ZAKI TURA KIYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBAR......07084653262.....IDAN KIN SAN BA BIYAN KUDIN LITTAFIN NAN ZAKI YI BA DON ALLAH KADA KI KIRA WAYA TA KO KIYI MIN WATA MAGANA TA WHASAP*

*MUTANAN MU NA NIJAR IDAN KUNA SO KU BIYA KUDIN LITTAFIN ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN NUMBARS.........90899076_88137740 KATIN AIRTAL KO ORANGE.*

*🗯️MADADI!!💍*
_(Ba Haram Bane!!)_

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~

*14*
Yaya Ramlatu zagin Baba malam kawai take a cikin zuciyarta amma a Zahiri dariyar ya'ke tayi tace"To ai shikkenan ni a gurina da kai da Salim din duk d'aya ne, kuma na zaunar dashi nace masa ya cire yarinyar daga cikin ransa gabadaya domin kai ba tsaransa bane ballanta ya had'a neman aure da kai."" Abba Abbas yayi murmushi yace."Kwana biyu ma bana ganinshi a kasuwa ko kiransa nayi a waya baya d'auka nasan duk akan hakane." Tace."Ai yanzu komai ya wuce na nuna masa dama can kai kafi cancanta daka auri yarinyar." Murmushi yayi yana girgiza kansa, gaskiya bai tsammaci zai zauna da Yaya Ramlatu haka suyi magana ta fahimta ba yaji dadi sosai da sosai data fahimce shi.

Yaya Ramlatu a gidan ta karya kummalo suka shiga daki ita da Halisa, suna 'kulle-'kullensu, Halisa ta fad'a mata duk yanda sukayi da mijin nata da maganar zai bata kudi ta had'o lefe kuma zai sanja mata mota bayan haka kuma yace ta fadi duk abinda take so zai bata kudi ta siya.....Jin haka yasa Yaya Ramlatu tace"Kinga aikin malam ya fara yi ko ai dama na fad'a miki sai Abbas ya dawo tafin hannunki sai yazo yana miki rawar jiki, dan haka ki daina d'aga hankalin ki kan auransa da yarinyar nan nasan idan muka ri'ke Malam mai al'mutsutsai! a hannunmu to bukatar mu zata biya dama kuma babban burin ki shine ki mallaki Abbas a hannu ina ganin nan da 'kan'kanin lokaci zaki mallake shi da duk wani abu nashi tunda har ya bud'e bakinsa yace miki dashi da duk wani wanda yake 'kar'karshinsa a 'kasan ki suke to kinga kuwa ai sai ki godewa Allah ki sake tanadar kudi masu kauri domin tukwici ga malam bisa ga aikin alherin da yayi miki." Halisa tace."Nifa Yaya Ramlatu sai nake gani kamar dan zai yi aura ne yasa yake kwantar da kansa ba wai asiri ne yayi tasiri a kansa ba, ki duba fa ki gani tsayin shekaru nawa muka dauka muna yawan bin malam tun Halimatu na raye asiri baya tasiri a jikinsa, sai yanzu."

Yaya Ramlatu ta 'bara rai tace"Kada ki sake wannan maganar, wato duk kokarin da nake miki bakya gani sai kin 'karya ta ni! kin 'karya ta aikin malam to babu ruwana wallahi idan kika lalata a aikinki, kada ki sake cewa na taimaka miki, inaso ki sani ko wane malami da irin kalar aikinsa, wani da ruhainai yake aiki wani kuwa da turawan aljanu yake aiki wani kuwa da ba'ka'ken aljanu yake aikinsa, to shi mai al'mutsutsai da ba'kaken aljanu yake aikinsa, idan kin san ba'kar wuyar da muka sha nida 'Yar shagamu kafin mu je zauren malam d'in sai kin tausaya mana, amma kin samu aiki yayi shine kike 'karyata wa to wallahi babu ruwana."

Halisa ganin ran Yaya Ramlatu ya 'baci sai ta shiga bata hakuri tace"Ba wai ina karyatawa bane nasan kina kokarina akaina kiyi hakuri dan Allah." Yaya Ramlatu tace"Koda can ma ba wai asirin ne baya tasiri a jikinsa ba yana tasiri sai dai yana saurin karyewa ne saboda yawan addua da zama da alwala dashi mijin naki yake, amma nasan wannan aikin da akayi masa zai dade kafin ya bar jikinsa."
Halisa ta sauke ajiyar zuciya da fad'in "To shikkenan insha Allahu zanyi kokarin ganin na kauda duk wani abu dake raina dangane da auran, ammafa nace ban yarda ya raba mana gida ba dan ina ganin kamar za'a

2 Comments On MADADI
avatar
sumayya-1-4

7 months ago

Reply

Hw can I get the complete text please

avatar
abasu-kala

7 months ago

Reply

Replying to sumayya-1-4

You have to pay 1k first for subscription in order to download our novels

Please Login or Register in order to submit comment