Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Allah sarki Halima tunda Taji labarin Abbas zai auri kawarta sai ta rasa nutsuwa komai nata ya tsaya cak! bata san tana sonsa ba sai da taji zaiyi aure! damuwa ta shiga sosai ta rage walwala har sai da iyayenta suka gane!
Da yake Baba Talatu macece mai saurin fahimtar abu nan da nan ta fahimci abinda ke damun 'yar tata! Ta sameta tayi mata fada da nasiha sosai tace"Kada ta janyowa kanta lalura mutum baya ta'ba auran mijin da bana sa ba, dan haka ta cigaba da addua Allah itama ya za'ba mata miji nagari." Duk da wannan nasihar da mahaifiyar ta tayi ma bai sanya ta daina damuwa ba, ita gani take waye zai aureta tana da nakasa (gurguwa) tana ganin watakila ma haka zata 'kare rayuwarta ba tayi aure ba.
Ita kuwa Halisa tunda ta fahimci Halima na shiga damuwa a duk sanda taje mata da maganar Abbas sai ta dauki d'amarar muzguna mata kullum kan hanyarsu ta zuwa isilamiyya sai tayi mata zancensa da irin soyayyar da sukeyi, Halima tayi shuru bata tanka mata, ita kuwa Halisa tai tayi mata dariya...........Akwai lokacin da Abbas yaje zance gurin Halisa ta tsare shi wai dole sai ya fad'a mata tsakaninsa da Halimatu! mamaki sosai ya kamashi Yace."Halimatu kanwata ce amma babu wata soyayya a tsakanina da ita." Halisa tace"To idan kai baka sonta ita tana sonka dan ba kaga halin damuwar da ta shiga ba lokacin da ta samu labarin abinda yake tsakanina da kai, dan haka gaskiya gwara kayi wa tufkar hanci tun kafin tafiyar tayi nisa duk da take kawata bana tunanin zan iya zaman kishi da ita."
Mamaki ya rufe shi da yake mutum ne mai tsare gida sai yace."Okey yanzu kina so ki nuna min ga yanda zanyi kenan? Idan na fahimce ki kina so kice ke ba zaki zauna da Halimatu ba a matsayin kishiya ko me."? Da sauri tace"Kwarai kuwa ai naga kusancin dake tsakanin gidanku da gidansu ne ina tunanin idan iyayenta suka fahimci halin da take ciki a kanka zasu ce ka aure ni kuma bana so gaskiya shiyasa nake so tun kafin tafiya tayi nisa kayi wa tufkar hanci." Ya girgiza kansa yana kallonta yace."Bari kiji Halisa ni ba irin mazan da mata zasu zauna suna tsarawa magana bane! abinda nasa kaina shi nake yi ke baki isa kice ga yanda zanyi ba, bani da ra'ayin zama da mace d'aya ki rubuta wannan ki ajiye bayan na aureki zan sake auran uku mutukar Allah ya bani iko saboda haka sai ki daura d'amarar zama da kishiya Halimatu kuma da kike magana na jawa kunne a kan tana sona to kin sanya ma naji sha'awar auranta zan aureku rana d'aya tunda dama 'kawayen juna ne." Da jin abinda ya fada sai ta mike a fusace! tace"Wallahi sai dai ka za'ba ko ni ko ita dan na rantse da girman Allah ba zanyi kishi da gurguwa ba."!!! Ya bude bakinsa yana kallonta cikin tsananin mamaki! lallai Halisa muguwar jahila ce yanxu me bambamcin muskini da mai lafiya? saboda jahilci da hauka kishi ma sai ta za'bi da wanda za tayi! Ya mike tsaye fuskarsa a murtuke yace." Tunda kin rantse ba zakiyi kishi da Halimatu ba to nima kuma ba zan janye 'kudirin dana dauka a kan auranta ba, saboda haka sai kije ki r'ike duk wani abu da nasa aka kawo miki da niyyar auranki na bar miki, ki samu wani mijin ki aura ni kuma zanje na auri muskiniya sai naga abinda zai cinye ni." Yana 'kare maganarsa ya futa daga soron gidan nasu. durkushewa tayi kasan soron ta fashe da kuka tana data sanin abinda ta aikata, tun farko ta lura Abbas din ba irin lusaran mazan da mace ke tursasawa bane yana da wani irin baud'addan hali tabbas kamar yanda ya fad'a din babu me sashi yayi abinda baiyi niyya ba mutukar ba iyayansa ba.


Tofa al'amarin yayi tsanani dan Abbas yaja tunga ya tsaya kan maganarsa kan cewar ya janye maganar auransa da Halisa saboda wasu dalilai saboda haka Halimatu itace matar da ya za'ba a matsayin uwar 'yayansa, Baba malam da Alhajinsa suka dinga bashi hakuri suna rarrashinsa, kan yayi hakuri ya auresu gabadaya, nan ya futo ya fada musu abunda ke faruwa! Yace."Halisa tayi mummunan furuci ga Halima kuma tayi izgili ga hallitar da Ubangiji yayi mata, dan haka to shi ba zai auri macan da zata dinga kokarin nuna masa yanda zaiyi ba, saboda haka shi ya janye maganar auranta Halimatu yake so. Baba Malam da Alhaji Sama'ila ba suji dadin faruwar al'amarin ba kasancewar mahaifin Halisa din mutumin kirki ne duk tare suke zama bakin titi ranar juma'a da yamma, dan haka sai suka yanke shawarar fada masa halin da ake ciki, suna kuma fatan Allah yasa hakan shi yafi alkairi. Koda mahaifin Halisa yaji yanda al'amarun suka kasance sai hankalinsa ya tashi sosai! babu shakka yarinyarsa tayi wa kanta wauta ba kad'an ba ta cutar da kanta kuma shi sam baiga laifin Abbas ba, da irin hukuncin da ya yanke yana bala'in son yaga jajurtaccen namiji mai tsayuwa kan magana daya.............Halisa tasha fada sosai gurin mahaifinta yace."Tunda ba zata auri mai mata ba to taje ta nemo wanda bashi da mata wanda kuma yayi mata alkawarin da ita kadai zai zauna, mutukar ta kawo masa komai illarsa da rashin nagartarsa to shi kuma zai daura mata aure dashi tunda itace taji ta gani.

Hankalinta a tashe ta nufi gidan Ramlatu, tana kuka ta zayyane mata abinda ke faruwa, a ganinta tinda Itace take gaba da Abbas din zata fada masa yaji tace dan Allah ta bashi hakuri yanzu ta yarda zata zauna da Halimatun a matsayin kishiyarta.......Ramlatu ta fusata ta dinga surutai tana aibata Halimatu da iyayenta a cewarta sam Abbas bai dace da auran muskiniya ba, saurayi dashi mai kyau da kudi da Ilimi yama za'ayi ya auri nakashshiya wacce take ci take sha a 'karkashin alfarmarsa dan haka sai ta shiga bawa Halisa hakuri tace ta kwantar da hankalinta za taje ta same shi, insha Allahu zai aure ta.........Da safe da wurwuri ta sauka a gidan kowa yayi mamakin zuwanta, ko gaisawa ba suyi da mutanan gidan ba ta nufi dakinsa, lokacin yana kokarin fitowa da shirin fita kasuwa! Yace."A'a barka da safiya kece a gidan." Tace."Eh gurinka nazo." Cike da mamaki yace."Gurina."? Tace"Eh yace."To Kinga ni yanzu sauri nake zan fita ki bari na dawo ko kuma ki koma gida da yamma idan na dawo zan shigo gidan naki sai naji abinda yake faruwa.

Cikin d'aga murya kamar wata uwarsa tace"Yanzu kai Abbas ka rasa wacce zaka aura sai Halima muskiniya nakashshiya ashe dama anan ruwan idonka zai 'kare gaskiya ka bani mamaki wallahi! Ga Yarinya mai hankali da nutsuwa 'yar gidan mutunci mai kaunarka amma kace ka fasa auranta ka koma gurin wata banza wacce take ci da sha a 'karkashin mahaifin.......'Daga mata hannunsa yayi fuskarsa a murtuke yace."Wallahi ban san sanda zakiyi hankali ba! kullum kina girma kina cin 'kasa! Yanzu ke ko kunya baki ji ba ki shigo har dakina kina daka min tsawa da nuna min yanda zanyi, haifata kikayi da zaki dinga yi min haka? ina ruwanki da aurena da Halimatu idan ba zaki saka albarka ba to kiyi shuru da bakin ki dan ni wallahi duk abin nan da kuke yi 'kara mun 'karfin gwiwa kukeyi babu gudu babu ja da baya sai na auri Halimatu in yaso ku kasheta saboda 'kiyayyya." Fashewa tayi da kuka tana nuna shi da hannu tace"Ni kake zagi ko Abbas dama ai baka da mutunci baka dauke ni a bakin komai ba kuma kai dama ba'a fada maka magana kaji." Yace."Da kinzo min da lisilama zan fahimce ki amma kinzo kina yi mun hayagaga! a kunne ai kin san halina ni ba'a haka dani." ratse ta yayi ya futa dada dakin, kallo ta bishi dashi tana jijjiga kanta, dama tun yana yaro bata iya lankwasa shi gwara Alhasan shi tana fada masa magana yaji amma banda Abbas futo na futo yake da ita girgiza kanta tayi ta futa daga dakin.

To haka al'amura sukayi ta kasancewa kowa na fadar albarkacin bakinsa kan wannan auran yayin da Abbas ya shafawa idonsa toka ya tsaya kai da fata sai da yaga auransa da Halimatu ya tabbata sannan hankalinsa ya kwanta.

Gida gudu biyu iri d'aya Alhaji Sama'ila ya mallakawa Abbas da Magaji Gidajen nasu na cikin unguwar *Gwangwazo* wajejen gidan Sarki.
kowanne ya tare da matarsa a ciki, Maryam matar Magaji 'yar cikin gari ce dai-dai gwargwado tana da hankali da nutsuwa shiyasa tasu tazo d'aya da Halimatu suke zamansu lafiya, kamar yanda mazajensu ke zaune da juna lafiya suma haka suke mutunta junansu...



*GA MASU BUKATAR KARANTA BOOK DIN ZASU TURA #400 SINGLE, VIP GROUP #600 GA ACCONT D'IN DA ZA'A TURA KUDIN.......0542382124.....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATIN WAYA ZAKI TURA KIYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBAR......07084653262.....IDAN KIN SAN BA BIYAN KUDIN LITTAFIN NAN ZAKI YI BA DON ALLAH KADA KI KIRA WAYA TA KO KIYI MIN WATA MAGANA TA WHASAP*

*MUTANAN MU NA NIJAR IDAN KUNA SO KU BIYA KUDIN LITTAFIN ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN NUMBARS.........90899076_88137740 KATIN AIRTAL KO ORANGE.*

_*Bata sati da gama book zata fara wani kan san kud'inta za'a daina san book dinta ni DA WATA A 'KASA Ma dana siya ko pege d'aya ban karanta ba, bata nazari gurin rubutu sai tazo tana rubuta 'karya bata ganin yanda su Billyn Abdul suke ita da Hugama suna Nazari kafin su fara littafi amma ita san kudinta yayi mata yawa😅😅😅*_
*KAJI!! UWAR IYA MAI ZANI BA 'DAN CIKI 🥱INA RUWAN KI ME YA DAME KI? BINTA TANA SON KU'DI💵💵 🥱KUMA BA ZATA DAINA RUBUTU BA SAI SANDA BASIRAR TA TA'KARE 'KARYA DA RASHIN NAZARI DA TUNANI YANZU TA FARA RUBUTAWA IN DAI ZA'A SIYA MAGANA TA MA'KARE🤣🤣🤣 ALLAH KA TAIMAKI BINTA TA CIGABA DA SHIRYA 'KARYA DA RASHIN NAZARI DA TUNANI, A SIYA A CIKA MATA ASUSUNTA😇 MY REAL FANS A CIGABA DA KARANTA 'KARYA DA RASHIN NAZARI IN DAI ZAKU KARANTA KU NISHAD'ANTU NI KUMA BA ZAN GAJI DA TSARA MUKU 'KARYA BA🤗🤗*
*RUBUTU BAYAYI WA BINTA WUYA SABODA TANA DA MATAYA👺*


_Banyi niyyar typing ba yau amma saboda na mayar da martani yasa na dau'ki al'kalamina🖊️_

*3*
Halisa hankalinta yayi masifar tashi ganin irin uban gidan da'a kai Halimatu ga uban lefen da Abbas yayi mata atampopi da lesuka masu tsada kuka ta yini tana yi ta rasa nutsuwarta, mahaifiyar ma ba'kin ciki ne fal a cikinta zuciyarta tana aikace-aikacen ta na yau da kullum ta nayi wa 'yar tata fad'an wautar da tayi, in banda rashin tunani da kuma jahilci ina kai ina kushe hallitar Allah alhalin kaima baka wuce Allah ya mayar da kai wata hallitar ba, gashinan lokaci guda Allah ya juya al'amarinsa, tayi kuka tayi nadama gami da dana sani wanda hausawa suke kira da 'keya ce.

Zama mai tsafta ne yake wanzuwa a tsakanin Abbas da Halimatu! tawayarta bata hanata sauke hak'kokin mijinta dake kanta ba, Tana kula dashi sosai dan wani sa'in idan yaga tana hidima dashi har tausayi take bashi dalili yanayin tafiyarta da rashin kuzarinta ma abin tausayi ne, amma abin na bashi mamaki sosai! kafin ya dawo daga kasuwa ta gama komai na gida tayi masa kwalliya mai burgewa. duk sanda ya shigo gidan yayi tozali da ita wani farin ciki ne yake rufeshi, wai shin meye aibunta ne? Halimatu bata da wani abu ko nakasu a gurinsa tinda duk wasu hakkokinsa tana saukewa kwata-kwata nakasarta bata dameshi ba zahirinta yake so ba wani abu na jikinta ba, zaman lafiyar da suke da juna ya sanya yake ji a cikin ransa zai iya zama da ita har'karshen rayuwarsa.

*****
Wata goma cif da auransu Maryam matar Yayanta magaji ta haifi d'a namiji, murna da farin ciki a gurinta tamkar ita ta haihu kullum tana gidan tare da mai jego tayi ta hidima da ita da jinjirin 'Yan uwan Maryam suyi ta tausaya mata idan sunga ta wani abun na wahala sai suce ta zauna, murmushi kawai take musu ta rabu dasu idan kuma sun matsa mata takan ce dasu itafa babu abunda ba zata iya ba saboda haka su daina yi mata kallon mara lafiya da rashin kuzari! To suma ganin ranta ya 'baci yasa suka daina cewa da ita komai! kafin ma suzo ta shiga gidan ta gyara tsaf ta gyara yaron sannan ta had'awa maijego abun kari, sannan ta dawo gidanta tayi wanka ta shirya ta sake komawa, haka ta dinga zurga zurga har sai da akayi suna inda yaron yaci sunan Maigidanta Abbas sai take kiransa da Amir...................KullumAmir a hannunta yake wuni sai dare take mayar dashi ko kuma idan ya bukaci nono sannan, gabadaya dai ita Maryam haihuwar yaron tayi amma raino yana gurin Halimatu, idan ta dauki yaron tun safe to sai dare ita dashi.
Abbas bashi da matsala ta 'bangaran wannan dan shima mutum ne mai son yara duk sanda ya dawo ya tarar da ita tana fama da takwaransa yakan ji dadi yayi ta addua Allah suma ya basu nasu mai albarka.

Shakaru uku da auransu Halima bata ta'ba 'batan wata ba, gashi har anyiwa Amiri 'kanwa Ilham, Abbas tun yana daurewa dai har ya kasa hakuri yace ta shirya suje asibiti a dubasu, koda sukaje likita ya dubaso gabadayansu babu abunda ke damunsu kawai dai lokacin haihuwarsu ne baiyi ba, likita ya rubutu musu magani mai kyau yace suje suyi amfani dashi insha Allahu za'a dace.....Dukkaninsu a sanyaye suka koma gida, kuma ba suyi 'kasa a gwiwa ba suna amfani da maganin kuma suna sake kula da kansu.

Ramlatu kuwa a duk sanda suka had'u da Halimatu a taro sai ta zage ta tayi mata gorin rashin haihuwa, duk taro na family dinsu sai ta tara mata mutane tayi ta nuna ta tana fad'in mugwayen kalamai a kanta, wata irin tsana Ramlatu keyi wa Halima ko ta mece oho! dan akwai ranar da tazo har gida taci mata zarafi da fad'in sun gaji da jiran gawon shanu dan su duk irinsu babu mara haihuwa saboda haka sun gaji da daci da ita idan ba zata haihu ba to zasu kawo wacce zata cika musu gida da 'ya'ya.'

Wannan cin zarafin ya 'bata marai rai sosai ta yini tana kuka dan ki girki ba tayi ba ballanta tayi wanka ta shirya kamar yanda ta saba, koda maigidan ya dawo rasa gane kanta yayi, tambayar duniya tayi masa shuru sai kuka take yi, tsayin shekaru uku da auransu bai ta'ba fuskantar irin wannan matsalar daga gurinta ba, da kyar ya samu yayi wanka ya futo palon tana dai zaune a inda take tana kukan da take, zama yayi kusa da ita yana sake rarrashinta kan ta fada masa abinda ke faruwa, da kyar tayi masa magana tana hawaye gwanin tausayi tace ita taga ji tunda bata haihuwa ya 'kara aure ko kuma ya saketa dan cin zarafin da Yayarsa take mata ya isheta.
Ransa idan yayi dubu ya 'baci! shin wai me yake damun Ramlatu ne? ina ruwanta da matarsa ina kuma ruwanta da rashin haihuwarsa, idan zai mutu bai haihu ba bai dameta ba shine yaga zai iya zama da matarsa a haka, shi kam ya rasa wace irin 'kiyayya Ramla keyi wa Halimatu, hakuri ya bata sosai yace zai same ta yaja mata kunne kan kada ta sake zuwar masa gida.
Jin abinda ya fad'a yasa hankalinta ya tashi sai ta dinga bashi hakuri tana nuna masa illar abinda zai aikata, mutukar ya tunkari Ramlatu da wannan maganar to babu shakka ya sake rura wutar gaba mai zafi a tsakaninsu, kuma ita ba zata so su samu matsala da 'yar uwarsa ba, Nuna mata yayi ya hakura ba zaije gidan Ramlatun ba........Washe garin ranar kafin ya tafi kasuwa sai da ya tsaya gidan Ramlatun sukayi ta babu kyau babu dad'i a tsakaninsu, dan ya nuna mata mahimanci da matsayin Halima a gurinsa kuma ya nuna mata cewar itama ta tsaya a matsayinta na 'yar uwarsa mutukar tasan wata fitina ce zata kaita gidansa to kada ta sake zuwar masa gida, dan tuntuni shi ya riga yasan Allah ne ke bada haihuwa ba wani mahaluki ba! Ramlatu kuka taci ta 'koshi 'dan uwanta da take alfahari dashi shine yazo ya ci kata mutumci a gaban kishiryata lallai babu shakka dole sai ta tashi tsaye kan Halima dan da alama Iyayenta suna tsaye a kanta gurin ganin ta mallake mata d'an uwa.
*Kaji rigima ta Ramlatu ke ba uwar Abbas ba komai ba amma kina kishi da matarsa, Uwar miji aka sani da kishi da matar d'anta Uwar mijin ma irin wacce bata san abinda take ba.*

Abbas zuciyarsa wasai yaje kasuwa yayi harkokinsa......koda suka tashi daga kasuwar kai tsaya 'Kofar Na'isa suka nufa dan ji yake idan bai fad'awa mahaifiyarsu abunda Ramla ke masa ba za'a iya samun matsala nan gana gwara ya fada mata ta kira ta ta ja mata kunne.

Hajiya Abu ranta ya 'baci sosai tace"Ni dik abinda ke faruwa a tsakaninsu ban sani ba wallahi amma Wannan yarinya anyi babbar kwabo wallahi dan taga matar taka mai saukin hali ce shiyasa take mata cin kashi a ko'ina amma kayi hakuri ka kuma bawa Halimatun hakuri insha Allah zan aika yara har gidanta su kira min ita zan mata tsakani da matarka duk sanda ta sake zuwa gidanka domin ta kuntatawa matarka to babu shakka na samu labari da Alhaji maihifinku zan had'ata....

To tun daga wannan rana Halimatu ta samu lafiya Ramlatu ta saurara mata da gorin haihuwa ammafa sa'i da lokaci suka had'u a wata sabgar sai ta yar mata da habaici al'amarin Ramlatu sai addua.

*****
Halisa ce ta shiga kara kaina a gidan, mussaman ranaku guda biyu Juma'a da Lahadi ranakun da ta tabbatar da cewar maigidan nan bai futa sai taci uwar kwalliya ta sanyo turare mai 'kamshi tazo ta yini a gidan! idan sun had'u dashi tana nuna masa kamar babu wani abu a ranta, ta hakura dashi kawai ta zuwa ziyara ne gurin 'kawarta! Sai dai ya girgixa kansa kawai ya shareta dan shi ba yaro bane ballanta ta raina masa hankali.........Ita kuwa Halima zuciyarta ce ta shiga sa'ka mata wani abu! tana ganin tunda dai har yanzu Halisan bata da tsayayye mai zai hana ya aureta ya had'asu tunda ta lura da Halinsa tayi hankali kuma duk wasu alamu da take nunawa a kan mijin nata ta gane sabida shi take zuwa gidan........Koda ta sameshi da maganar cewa yayi zaiyi shawara zai fada mata kome ya yanke!
Kwana biyu ta sake tuntu'barsa da maganar ya dinga kallonta yana mamakinta yace."Ke kina ganin idan na auri Halisa na had'aku babu matsala kuma zaki iya zama da ita."?
Cikin farin ciki tace"Zan zauna da ita tsakani da Allah nasan ko ta nufe ni da sharri zai koma kanta tunda ban cuce ta ba, sannan kuma ina so ka aureta kaga tanan za'a tabbatar da rashin haihuwar mu shin waye yake da matsala tsakanina da kai."! Wannan magana da tayi sai ta sake sa masa 'kwarin gwiwa shima yana so ya tantance waye mara lafiya a cikinsu, kai tsaye ya tunkari Halisa sa maganar, ranar kamar ta zuba ruwa a 'kasa tasha dan farin ciki! ta dinga murna da godewa Allah! Yace."Ina so ki zauna lafiya da Halimatu dan da yawun bakinta nazo nan neman auraki kada ki shiga gidana ki tayar mana da hankali mun gina rayuwarmu cikin mai kyau da inganci" Halisa taji wani irin d'aci a ma'kogwaronta! wato ma ba'a karan kansa yazo neman auranta ba sai da izinin matarsa! 'kwafa tayi a cikin ranta! a zahiri kuwa cewa tayi" Haba Alhajina kada ka damu zan zauna lafiya da ita ai ko lokacin baya ma kuruciya ce ta janyo nayi wannan furucin amma ka daina kokwanto da shakku a kaina."
Yaji farin ciki ya kamashi dama can yana son Halisa halinta ne baya si to tunda dai yanzu tayi hankali zai aureta su zauna tare cikin inuwa daya.

Ba'a wani ja dogon lokaci ba aka d'aura aure Halisa ta tare a dakinta, da yake gidane mai dauke da bangare uku sai kowa ya dauki d'aya, kasancewar babu yara a gidan yasa maigidan ke bin 'Dakunan matayen nasa bai tare a nasa part ba din sai ranar da ya tara iyali tukkuna.

*Rubuta 'karya sakaka! babu tushe ballanta makama ba za tayi armashi ba! My Fans ku cigaba da karanta tushen labari domin shine makamar zance Labari na gaba.*

*🗯️MADADI!!💍*
_(Ba Haram Bane!!)_

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~

_*Allah Sarki My real Fans♥️ kuyi hakuri ban san maganar da nayi zata 'bata muku rai ba, nagode kwarai da kulawa, kamar yanda bakwa so mutumcina ya zube nima bana so naku ya zube, ammafa kusa ni sun d'auke ni sun sani a gruop dinsu dan su samu damar cin mutumcina, To ina ro'kon Allah ya mutuntani wanda yake da tunanin tozarta ni ko yaci mutuncina Allah gaka nan gashi nan........Ke kuma my Aminiya kiyi hakuri kinfi kowa sanin halina yanzu ma raina ne ya 'baci! to amma insha Allah kome zai biyo baya na sharri zan had'a mutum da Ubangijin da ya hallice shi.🤗*_



*Wallahu galibun Ala amrihi👏🏻*


*4*
Sati biyu da shigowar Halisa gidan al'amura suka sauya, Halimatu ta kasa gane kan mijin nata gabad'aya Halisa ta ri'ke masa wuya ko yana kasuwa bashi da nutsuwar kirki mutukar bai dawo gida yayi tozali da ita ba, ranar girkin Halimatu sam bai da wani kuzari da walwala yakan dad'e ma a waje bai shigo ba, idan ma ya shigo d'in babu wani abun arziki da yake tsinana mata ba kwanciyarsa yake yi yai bacci! Halima ta shiga damuwa matsananciya ta rasa wanda zata samu ta fad'awa damuwarta gabakidaya Abbas ya sanja mata baya kula da ita sannan ba ya zama yaci abincinta kamar da idan tayi masa magana sai yace."A koshe yake shine dalili, Ita kuwa Halisa data fahimci rashin jituwa a tsakaninsu sai ta sake zage damtse gurin ganin ta sake mallakarsa, kissar yau daban ta gobe daban, duk abincin da zata bashi sai ta bad'e shi da magani abun mamaki kuma Yayarsa Ramlatu itace ke kawo mata maganin mata dana mallakar zuciyarsa, ita dai burinta Halimatu ta wulakanta a gidan.
Ranar Asabar har ya futa kasuwa da jaraba ta ciwo shi ya dawo gida, a maimakon ya nufi 'bangaran Halimatu tunda Girkinta ne sai kawai ya nufi bangaran Halisa, domin a yanda yake jin kansa yana ganin kamar Halimatu ba zata iya dashi ba, sai yanzu ya gane cewar Halisa ce dai-dai dashi dan tana iyawa da fitinarsa ita kuwa Halimatu rashin kuzarinta a ko'ina ma gwadawa take, ada hakan bai dame shi ba sai da ya auri Halisa ya gane cewar itace zata iya dashi, dan jaraba irin tashi baya tsayawa kan hallitar da Allah yayi masa duk karfi da kuzarinsa sai ya had'a da maganin 'karfin maza, kullum akwai wanda yake kawo musu magani kasuwa suyi ta siya suzo suna gallabar matansu da daddare.

Halisa duk da tasan ba girkinta bane bai hanata nuna masa kulawa ba kar'barsa tayi hannu biyu suka shiga d'aki suka shafe awa kusan hud'u suna abu daya............Halimatu ce ta shiga sashin tana sallama a palon taji shuru idanunta ne ya sauka kan hular maigidan da key dinsa na mota da kuma rigarsa kan kujera.
Tabbas kayan daya sa ya futa dashi ne a dakinta ya shirya kuma asali ma itace ta dauko masa kayan dole kuma tayi mamaki! kafin ta dawo daga tunaninta suka fito daga dakin a tare dashi da halisan daga shi sai gajeran wando, ji tayi yana fad'in "Zo ki bani abinci naci a gurguje na koma kasuwa na bar mutane na jirana." Had'a ido sukayi ita dashi! sai ya wani dake! kamar ba mara gaskiya ba, ya bude baki zaiyi magana kawai sai ta juya ta fita daga palon.
Jikinsa ne yayi sanyi ya zauna kan kujera yana kokarin mayar da kayansa, tabbas yasan wani abun da yake a gidan baya kyautawa sam be san meya sa ba yanzu kwata kwata baya

2 Comments On MADADI
avatar
sumayya-1-4

7 months ago

Reply

Hw can I get the complete text please

avatar
abasu-kala

7 months ago

Reply

Replying to sumayya-1-4

You have to pay 1k first for subscription in order to download our novels

Please Login or Register in order to submit comment