Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iko da kanka kuma kafi kowa sanin halin da nake shiga idan ina cikin wannan halin dan haka ni ba zan iya sauraran komai ba sai na samu biyan bukatata." Kallonta kawai yake dan shi ya rasa ma abinda zai ce mata, yana jinta tana ta shashshafa jikinsa tana masa salo iri-iri to abinka da wanda dama yake a bukace a take ya bada kai bori ya hau, suka shiga biyawa junansu bukata...

Gabad'ayansu har ita suka fito palo suka zazzauna suna hira kar'fe takwas shuru basu ga gilmawar masu gidan ba, tara ma tayi shuru, basu fito ba, A hankali ta kalli Mussadiq tace"Ko Abbanku ya fita ne."? Yaron ya girgiza kansa da fad'in "Wallahi ban sani ba dazu dai da muka shiga gaishe da Mommy na ganshi a dakin."

Shuru tayi tana nazarin maganar yaron, ta kalleshi cikin sanyin jiki tace"Kana jin yunwa ko."? Kai ya d'aga mata, mi'kewa tayi ta kalli Saddiqa da Mufida tace"Kuzo ku nuna min kicin din na had'a muku break fast." Suka mike da sauri suna murna, tare suka shiga kicin din nan suka shiga aiki kowanne ta bashi abinda zai taimaka mata dashi..............Halisa ta samu abinda take so sosai ta ri'ke wuta ta'ki barinsa ya huta shi kuma jinta zam-zam! ya dinga d'imautar dashi ya kasa hakura da ita suka dinga abu daya kamar jaraba koda yake dama can sun saba tunda jajayen sawun su......Sai kusan goma da rabi ya fito daga dakin, lokacin su har sunyi break dinsu suna zaune dai a palon suna hira wanda take saka musu baki jefi-jefi......Ido suka had'a ita dashi lokacin da ya fito daga dakin Halisan duk sai ya diririce! lokaci guda ta gane rashin gaskiyarsa kuma ta gane abinda suka dade sunayi a dakin, wace irin magana ce za'ace an shiga daki sama da awa uku anayi ai da akwai alamun tambaya.........'Dauke kanta tayi sam bata wani ji ciwo ba dan ba wai sonsa take ba ballanta taji haushin abinda sukayi mata, cigaba tayi da dan dudduba wayarta dake hannunta, Shi kuma da sauri yake kokarin shiga dakinsa.....Mussadiq yace."Yawwa Yaya Naja'atu ga Abban namu ya fito dama nace miki bai futa ba."
Da sauri ta kalli yaron tana d'an hararasa! Shi kuma Abbah Abbas din tsayawa yayi yana kallon Mussadiq din yace."Waye yazo nema na."? Shuru tayi, Mussadiq yayi karaf yace." 'Dazu ne Yaya Naja'atu take tambaya ta wai ko ka fita saboda munji shuru bamu ga ka fito daga dakin ka ba shine nace mata kana dakin Mommy."
Naja'atu taji kamar ta kwad'awa yaron mari! kada fa Ya d'auka ko sonsa take shiyasa take tambayarsa

Shi kuwa Abbah Abbas murmushi yayi yana dan shafa gemunsa ya kalleta a nutse yace."Ina tare da Halisa muna tattauna magana mai muhimanci insha Allah anjima zakuje tare dake da ita ki za'bi irin kayan da kike so domin ita na wakilta ta had'a miki lefe." Tsakaninsa da Allah ya fad'i maganar dan shi yana ganin meye a ciki dan Halisa ta had'a mata lefe ai duk a zaman d'aya!

Ita kuwa Naja'atu maganar ce ta girmi tunanin ta wannan ma ai rainin hankali ne da zaice Halisa ta had'a mata lefe kuma har ya iya fad'a mata da bakinsa, zuciyarta tace mata "To ke meye abin damuwa ai ba sonsa kike ballanta na dan yace Halisa ta had'a miki lefe kiji haushi!!! " Eh duk da ba sonsa nake ba amma ai hakan bai dace ba abin kamar yazo da cin fuska a ciki, to idan ya kasance tana sonsa kuma haka zai dinga d'ora kishiyarta kan al'amuranta abinda ba zata iya jurewa ba kenan don ita ba Yaya Halimatu bace...........Dauk'e kanta tayi ba tare da tace masa komai ba, shi kuma yanayin yanda yaga ta nuna sai yaji wani farin ciki ya lullu'beshi yana addua Allah yasa yarinyar ta soma sonsa......Yana shiga daki, Ita kuma ta shiga fad'a da zuciyarta ganin kamar tana so ta takura mata gurin ganin kamar anyi mata rashin adalci a gidan zuciyarta sai ingizata take akan ta dauki mataki ta bishi daki ta tambaye shi me tsaya yayi a dakin Halisa har tsayin awa uku alhalin yasan a cikin kwanakin auranta yake, sannan kuma tace ita bata yarda Halisa ta had'a mata lefe ba!.....Allah mai iko! abinda zuciyarta keta sa'ka mata kenan duk ta kasa samun nutsuwa a gurin sai kallon kofar dakin nasa take tana tununin taje ko kada taje? Mikewa tayi ba tare da dogon nazari ba ta nufi dakin nasa har tasa hannu zata bude kofar sai kuma ta fasa, ta juya cikin sanyi jiki ta nufi dakinsu Saddiqa kwanciya tayi ruf da ciki kawai ta tsinci kanta da fashewa da kuka.


*Tofah!🤔 Ko kukan me Naja'atu take? Ita da take ikirarin bata kaunar Abbah Abbas din to meye najin haushi dan ta ga ya dad'e a dakin matarsa? Lallai akwai alamun tambaya dangane da Al'amarin.................Akwai-Akwai_Akwai!! Rikita_Rikita anan agaba! Wai shin ya zata kaya ne a tsakanin Abbah Abbas da Amaryarsa? Shin zai samu nasarar kar'bar budurcinta ko kuwa? Salim zai kyale Naja'atu tayi rayuwar aure da Mijinta Kuwa? Wane Babban kuskure Naja'atu zata tafka anan gaba? Meye makomar Yaya Ramlatu da Halisa? akwai sauran labari anan gaba!!!! Ga duk wanda yake da ikon biyan kudin littafin nan ya biya ya karanta #300 ko #600 basu isa su biya kudin littafin nan ba😅 Koda yake ai 'KARYA ce amma dai ni nasan 'karyar tawa tana Tasiri a wani gurin dan haka da kai da ke ina so duk ku biyo ni domin a cigaba da tafiyar daku Single #300 Vip #600 Babu tsada🤗 Kada ki nuna ganin 'kyashin biyan kudi ki karanta kice bari ki bari idan an sato ki kiranta Allah ya isa! Idan anyi magana kice kema gani kikayi an turo shiyasa kika karanta, to duk wanda ya'ki sharar massalaci zaiyi ta kasuwa!🤗*


*Masu had'a min decoment na books daga zarar na gama bazan ce komai ba sai dai na ro'ki Allah ya tattara muku zunuban da na d'auka gurin rubuta littafin ya d'ora muku a kanku😅Shikkenan sai a raba mana zunubin tare daku kun rage min nauyi.*


*Masu tambayar wai ni bana littafin free ne sai na kudi: Amsa To farkon littafina Nana Khadija Free ne zagi da 'korafi gami da rashin hakuri irin na redars yasa na mayar dashi na kudi, tun daga haka shikkenan na daina littafin kyauta amma akwai book dina RUWAN DARE free ne book1 yana nan yana yawo a groups ga duk mai bukatar karantawa sai ya tambaya a groups insha Allah idan na gama rubuta littafin MADADI zab cigaba da typing d'insa RUWAN DARE free ne bana kudi bane! idan na gama Madadi zan cigaba da rubuta muku shi🤗*

*Masoya masu sahihiyar kauna Ina alfahari daku♥️*


*GA MASU BUKATAR KARANTA BOOK DIN ZASU TURA #300 SINGLE, VIP GROUP #600 GA ACCONT D'IN DA ZA'A TURA KUDIN.......0542382124.....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATIN WAYA ZAKI TURA KIYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBAR......07084653262.....IDAN KIN SAN BA BIYAN KUDIN LITTAFIN NAN ZAKI YI BA DON ALLAH KADA KI KIRA WAYA TA KO KIYI MIN WATA MAGANA TA WHASAP*

*MUTANAN MU NA NIJAR IDAN KUNA SO KU BIYA KUDIN LITTAFIN ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN NUMBARS.........90899076_88137740 KATIN AIRTAL KO ORANGE.*


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


2 Comments On MADADI
avatar
sumayya-1-4

7 months ago

Reply

Hw can I get the complete text please

avatar
abasu-kala

7 months ago

Reply

Replying to sumayya-1-4

You have to pay 1k first for subscription in order to download our novels

Please Login or Register in order to submit comment