Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kamar yanda kika saba domin wallahi bazan daukar makiba a'a yaya ainadena yanzu inaganin kowa da gashi to Allah yasa abin yadore Amin ina hajara tana gidanta Fa'iza waisai yaushe zakiyi Aure tinda kikafito daga gidan mijinki shekara da shekaru haryanzu kinki fidda miji kiyi Aure karka damu yaya domin koyaushe yaya Hajara tanayimin zancan Aure insha Allah nakusa Allah yasa domin akullum naimaki zancan haka kike fada yanzudai da gaske nakeyi to Allah yakawo nagari Amin yaya nizantafi domin yamma tayi sosai duhu yafara yaciro kudi yabata to gawannan kiyi kudin mota tonagode sosai Allah yasaka da alkhairi Amin tatashi tayi tafiyarta anyi kiran sallar magariba yatashi yatafi masallaci baidawoba saida akayi sallar isha sannan yadawo kaitsaye dakin Jamila yanufa yasameta akan gado Nusaiba tanatayi mata fitina yunwa takeji yashigo tare dayin sallama ta'amsa batare data dubeshiba kukanme takeyi yadauketa Nusaiba maikikeso Dady yunwa nakeji bakici abinciba tadaga masa kai alamar eh Jamila maiyasa bakibata abinciba saboda banyiba maiyahanaki ganin dama ok yamakikyau yadauki Nusaiba zaifita tasha gabansa inazska kaimin yarinya bansaniba kinga kijanye kiban hanya yasa hannu yajanyeta gefe yayi tafiyarsa dakin Hajiya Aisha yanufa yasami kofar arufe yabuga tazo tabude masa kaine sannu da zuwa yauwa bismillah yashigo yazauna yanayin dayaganta yasan tana cikin damuwa sosai yasan kuma damuwarta tanada nasaba da zuwan Fa'iza yagirgizs kai batare dayace komaiba yakalleta Fa'iza tazonanko tayi dogon numfashi tare da dagamasa kai yayinda takejin cikin zuciyarta tamkar anayimata azaba da wuta maitafada makine tagirgiza masa kai yayinda hawaye sukebin fuskarta takasa jurewa takuma kasa mantawa tatashi tayi ciki tazauna bakin gado lokaci daya kuka yazo mata yabiyo bayanta Hajiya dan girman Allah da darajar rasullulahi (S.A.W.) kisanar dani abinda tafada maki Nusaiba tace Dady waya daki Hajiya take kuka sai lokacin ta'itayin magana ganin Nusaiba tazo tana share mata hawaye tana tambayarta waya daketa tadaure tayi dan murmushi bawanda yadakeni kinji tomaiyasa kike kuka bakomai kingama nadena to Hajiya zanci abinci zskici abinci eh tomuje kici sunfito tana rike da hannunta taje tazubo mata abinci sunzauna tana bata lokacin Alh Mansoor jikinsa duk yamace yafito yasameta tanaba Nusaiba abinci tanayimata fira tamkar ba'itaba

By. Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:48] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
Part 2
1⃣3⃣
By

Fauziya Usman

Yakaraso gurinsu ya zauna tadago kai takallesa kafito dan Allah kayi hakuri munfito munbarka aciki shidai kallonta kawai yake yayinda mamakinta yacika zuciyarsa yayi ajiyar zuciya maiyasa kebazakici abincinba banajin yunwa a'a idan kinkarasa bata kizubo mana muci a'a baza'ayi hakaba domin idan Jamila taji kaci abinci anan bazataji dadiba kenan kinzabamin nakwana da yunwa ko a'a bana nufin hakan to batayi abinciba shiyasama kikaji Nusaiba tana kukan abinci to shikenan Allah yakyauta bayan takarasa bata abinci taje tazubo masu nasu sunci tare bayan sunkarasa taduba agogo tace yakamata katafi dare yayi sosai zantafi amma kisani jibi zaki koma Kaduna aibikin saura kwana biyar badole sai anyi biki dakeba farin cikinki yafi bukin muhimmanci agurina yana kokarin daukarta tana kiyawa Nusaiba muje kikwanta Dady ni anan zankwana bazakiyi kukaba eh toshikenan Hajiya saida safe to Allah yabamu alkhairi Amin yayi tafiyarsa tadauketa taje tashin fideta sunkwanta lokaci daya taji kaunar yarinyat takara shigarta ya'isa dakinsa yasameta tanata kaida kawo Jamila lafiya kaida kawonme kikeyi tambayanama kake ina 'yata tace acan zata kwana shine saika baromin ita takwana acan eh mana tomiye toni bazan yardaba kakoma kadaukomin 'yata wallahi baki'isaba acan zata kwana kokinaso kibakyaso yatafiyarsa yakwanta

Washe gari Haj Aisha tatashi taje tashiga kicin domin hada abin break fast tagama girkinta tadawo tagyara gidanta tafito daga wanka tana shiryawa Nusaiba tatashi dasauri ta'isa inda take tarikata Nusaiba kintashi tadaga mata kai to muje kiyi fitsari kinji takaita tayi fitsari tayo mata wanka tafito tashirya mata sannan takarasa shirinta tabuda jakar kayanta tadauko wasu riga da siket tasamata dama tasiyo kayanne dan'ita saidai fargaba da shakka yasa bata bataba tasamata kayan sunyi mata kyau sosai sai wani murna takeyi itakuma sai kallonta take yanda taga tanata murna saitaji yarinyar duk tabirgeta to muje kiyi break fast ko tariko hannunta sunfito sunnufi teburin cin abinci

Alh Mansoor bayan yatashi yashirya ya tambayi abin break fast dinsa kaje inda kaci jiya yauma kaci to shikenan zantafi kuma zanci amma kisani kowa yayi dakyau shizaiga dakyau ni natafi adawo lafiya yafito yanufi sashen Haj Aisha yaturo kofa yashigo yahangesu sunacin abinci suna nishadi abin yabirgeshi sosai yakumaji dadi aransa domin yanasan yaga Haj Aisha tana cikin farin ciki ta kallesa lafiya kayi tsaye daga nan kakaraso mana ya'iso inda suke shima tazuba masa nasa abinci suna cikin cin abincinsu Jamila tatuto kofa tashigo tare da yin sallama Haj Aisha ta'amsa a Jamila ce karaso mana kinga dan Allah niba gurinki nazoba ina 'yata itanazo dauka gatanan tanacin abinci takaraso inda suke mama tafada tana dariya na'am 'yata taso mutafi kinbarni nidaya sai maraici nakeyi zomutafi kinji taja hannun 'yarta sunfita tabisu da kallo Allah kenan mai iko akan bayinsa Allah kabani ikon cin'jarabawar daka doramin arayuwa kizauna mukarasa cin abincin mana a'a nakoshi to shikenan nima nakoshi zanfita Allah yakiyaye adawo lafiya yafita yayi tafiyarsa baitsaya ko inaba sai gurin Fa'iza yayi sallama yashigo tafito ta'amsa masa yanda taga fuskarsa tasan ba lafiyaba yaya sannu da zuwa yadaka mata tsawa yashiga yimata fada ta inda yake shiga batanan yake fitaba yamata tas yace kuma baruwansa da'ita yafito yayi tafiyarsa bayan yatashi daga office yadawo gida yadauki Haj Aisha da mota ita kanta batasan inazaikaitaba saida suka iso tafahimci inda yakawita gidansu Lami yace yaje tayi musu sallama saboda gobe zata koma Kaduna batare da wata gardamaba tafito taje tayo masu sallama inna tace gaskiya banji dadiba amma bakomai mungode sosai sunyi mata rakiya harbakin mota sungaisa da Alh Mansoor sundawo gida yatarasu afalonsa yakira sunan Jamila inasan infada maki cewa nanami taransifa ta aiki zankoma Kaduna da wiki domin bazan yarda dake da Fa'iza kutaru kukashemuba zanrika zuwa duk Friday nayi weekend lokacin dakika gane gaskiya kikaji zaki'iya aiki da ita to kofar tuba abude take inasan kisani Fa'iza kanwa tace nasanta sarai batada kirki amma wata rana zaki fahimci hakan da kanki Haj Aisha tanasan tayi magana saidai yahanata washe garin ranar da zasu tafi taje har'daki tayi mata sallama sunyi rabuwar mutunci kamar abin arziki

By. Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:49] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
Part 2
1⃣4⃣
By

Fauziya Usman

Kano

Zaune suke kan tebur din abinci shine kawai yakeci amma ita sam batacin komai ya kalleta yaga tanata bata fuska yasaki ajiyar zuciya tare da kiran sunanta Nafisa waimai yasa bakyasan cin abincine dan Allah kidaure kici ko kadanne kinji Allah yaya Salim bazan'iya ciba tashin zuciya nakeji sainaji banasan cin komai kuma kana ganin yanda bakina yake cika da miyau hakanma yanasa naji bana bukatarcin komai gaskiya Nafisa ina tausayin abinda yake cikinki domin yunwa zata'iya kamashi kekanki ina tausayinki Allah yakawo maki afuwa Amin ya Allah yanzu dauko mayafinki na ajiyeki agidan Ummi sai nawuce office to shikenan taje tadauko mayafinta sunfita sun'iso gidansu Ummi sunshigo sunsamesu suna break fast sannunku da zuwa yauwa Ummi antashi lafiya Abba ina kwana lafiya qlau Nafisa tagaishesu Nafisa yajikin da sauki Abba to Allah yakara sauki Amin Ummi nizantafi office to adawo lafiya yaya Salim Allah yakiyaye Amin yafita yayi tafiyarsa banjima da fitaba Abba ma yafita zuwa office Ummi taje dakin Larai tasameta azaune Larai ko wani abu kikeyi a'a Hajiya tokifito muyi fira mana to Hajiya tafito tasami Nafisa afalo kwance akan kujera Nafisa ashe kinshigo eh Aunty Larai ina kwana lafiya qlau yatsufa yafama da miyau yafama da laulayi kai Aunty Larai wallahi kinfiye zolaya bazancan zolaya bane ni abinda nasani shine da ciki yashiga wata na hudu angama laulayi ammake gaki wata bakwai amma har yanzu kina abu daya Larai kenan kinmanta Nafisa face toya akayi da lafiyar kura balantana tayi hauka wannan ko sanda tana gida yatake kullum tananan akwance ni wallahi tausayinma yarona nake dannasan sauda yawa yaba barci da yunwa koyafita baiyi break fast ba haba Ummi taya zanyi haka wallahi ni sam bana barin yaya Salim da yunws domin banasan naga yacutu ko yanxu bamu fitoba saida yayi break fast tonaji shiyayi kefa kinyi a'a to maiyasa wallahi Ummi banasan cin komai saboda bakina to Allah yakaimu lokacin da za'ahaife cikinnan Amin Larai wallahi nikaina addu'ar danakeyi kenan akowace safiya karfe 04:09pm Salim yadawo yashigo ciki yasami Ummi da Larai afalo sannu da zuwa Salim yauwa Aunty Larai ya gidan lafiya qlau Ummi ina wuni lafiya qlau andawo eh ya'aiki Alhamdulillah Ummi Abba fa ko baidawoba eh to inajin koya biya tawani gurin domin yarigani fitowa suna cikin zancansa yashigo to gashinan yashigo zancanme kukeyi naji anafadar ganinan Larai fadamin gaskiya maisuka fada akaina tayi dariya rankashidade suna maganane akan bakadawoba oho kuntsira bayi tinaninko wani abin kuke fada akaina sai dariyarsa sukeyi to yanzu Abba idanma Ummi zatayi zancanka sai tayi dani eh mana aikai dantane kuma Kaine wanda tayarda dashi fiye da kowa hakama Kaine mutum nafarko dazaifara goyamata baya yayinda tazo da wata bukata tata dan haka batada wsni Wanda zatayi maganata dashi saikai to yanzu mudai bamuyi dakaiba ko Ummina to aini nama kasafadar komai Ummi ina Nafisa tanacan tana barci amma taci abinci kuwa to dakyar nassmu taci kuma badayawaba wallahi Ummi batasan cin abinci haka nake fama da ita kullum agida kadena damuwa da bata ranka nesa tazo kusa data haife shikenan to Allah yakaimu lokacin Amin Abba yayi sama Ummi tace Salim taso kaci abinci to Ummi yaje yaci abinci yadawo yaga harzuwa wannan lokacin Nafisa bata fitoba yatafi dakin datake tasameta kwance tanata barcinta ya dukursa akasa yajanye rigarta sama yarungume cikinta tare da sunbatarsa lokaci daya tayi wani irin dogon numfashi tare da ajiyar zuciya idanta arufe take magana sannu da zuwa yaya Salim yauwa maman Baby barka da tashi yauwa kiyi hakuri natasheki ko a'a bakomai domin kibazoba zantashi nayi sallah yaya Salim danrikani natashi yarikata tatashi zaune wallahi duk nagaji nakawo maki abinci a'a kafin nakwanta saida naci abinci yanzu bara naje nayo alwala to afito lafiya tatashi taje tayo alwala tafito tayi sallah sundawo fali shida ita sai dare sannan suka koma gida akullum akoyaushe zaifita gidan Ummi yake kaita kasancewar bata iya aikatama kanta komai kwance yake yana barci bayan yayi sallar asuba yakoma yakwanta acikin barcinsa yaga kanwarsa cikin wani yanayi naban tausayi cikin tashin hankali sai kuka takeyi tana fadin yayana maiyasa katafi kabarni dan Allah kataimakeni yayana zanmutu Kaine kawai gata agareni dan Allah kataimakeni karkabari narayu baka domin rayuwata tana cikin hatsari sai kuka takeyi sosai shikuwa sai anbatar sunanta yake Safna! Safna!! Safna!!! Wallahi ina tare dake insha Allah babu abinda zaisameki Safna yafadi sunan da karfi Nafisa tatashesa sabida yanayinda tagansa bamaikyau bane yatashi yana fadin kalmar innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un itace kawai abinda yaketa maimaitawa yaya lafiya maiyasameka wacece Safna dasauri yadago kai sunyi Ido biyu yayinda idanunsa suke zubarda hawaye yaya Salim kukanme kakeyi harzuwa wani lokaci baice da ita komaiba Itakuma sai kallonsa take domin jikinta yajima da mutuwa to maiyake shirin faruwane wacece wannsn Safna din maiyasa yake fadar sunanta sannan kuma miye ssnadin kukansa maiyasa bayasan yafada mata komai tabbas da akwai wani abu akasa wanda yake biyemata tomiyeshi yatashi yashiga toilet ya wanko fuskarsa yafito yaganta azsune a'inda yabarta yadawo yazauna yakalleta lokaci daya sikayi ido biyu cikin sarkarkiyar murya yake maganarsa Nafisa kiyi hakuri kinatayimin magana nayi maki shiru wallahi nikaina bansan abinda zaifaru daniba domin komai kikaga nayi ko kiki kaji nafada to mafarkine nayi mafarki da wata yarinya mai suna Safna yarinyar abar tausayi tanata kirana akan nataimaketa saidai abin takaici nagagara taimakonta kinji abinda yake sani zubarda hawaye

By. Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:49] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
Part 2
1⃣5⃣
By

Fauziya Usman

Karka damu yaya Salim ai mafarkine ba gaskiya bane amma Nafisa bako wane nafarki bane yake zama karyaba wani mafarkin yana tabbata karka damu kuma karkasa wannan aranka insha Allah wannan yarinyar da kagani tana neman taimako zata samu wanda zaitaimaketa yayi dagon numfashi tare da ajiyar zuciya Nafisa banasan kifadama kowa wannan zancan kinji insha Allah bawanda zaiji aranar haka yawuni Sam bayajin dadin jikinsa hakan yasa ko office baitafiba sai tinanin yanda yaga kanwansa kawai yake Nafisa tafahimci yana cikin damuwa sosai saidai ko tatambayesa baya fada mata komai ita kanta abin yana damunta ganinsa acikin damuwa kuma batasan dalilin damuwarsa ba sannan yahanata fadama Ummi tomai hakan yake nufi akwana atashi babu wuya agurin Allah yanzu cikin Nafisa yacika wata tara cif-cif koyaushe zata"iya haihuwa ana igobe zata haihu ranar agidansu Ummi suka wuni kamardai kullum da dare dazasu koma yaganta sai ahankali babu kuzari ajikinta ga alama tanajin jiki yace Nafisa anya zaki'iya komawa gida kuwa Salim kenan tomai zaihanata Ummi naga jikin nata sai ahankali batada kuzari karka damu Salim kutafi idan kaga da wani abu sai kamana waya muhadu asibiti kaji to Ummi muzamu tafi Abba saida safe Allah yabamu alkhairi Nafisa Allah yabaki lafiya Amin Abba Ummi saida safe Allah yabamu alkhairi Allah yasaukeki lafiya Amin Ummi sunfito sunyi tafiyarsu sun'isa gida bayan sun kwanta saidai Nafisa tagagarayin barci saboda ciwan marar dayake addabarta Salim shikansa baiyi barciba alla-alla yake akira asuba yana dawowa daga masallaci yasameta ayanda yabarta yarikata sunje tashiga mota suntafi gidansu Ummi sun'iso yasami kofar arufe yabuga Larai ce tazo tabude Salim lafiya wallahi Aunty Larai Nafisa ce tinjiya da mukabar gidannan haryanzu jikinta sai dadagaba yake subuhanalillah to yanzu tana ina tana mota ai asibiti yakamata kutafi bananba bara nasanar da Ummi yaje yabuga masu kofa tafito atinaninta Larai ce tana buda kofa taga Salim dasauri takira sunansa Salim lafiya Ummi Nafisa ce tinjiya haryanzu batada lafiya tana ina gatacan amota to aimuwuce asibiti kawai bara nadauko mayafina takoma tafadama Abba tadauko mayafinta dukansu suka tafi asibiti harda Larai suna zuwa akace haihuwace anshiga da ita dakin haihuwa sukuma sunanan suna jiran afada masu anhaihu tare da yimata addu'a Ummi na zaune tahangi Salim can gefe atsaye taje inda yake tariko hannunsa tazaunar dashi kaga Salim karka saka damuwa aranka insha Allah Nafisa zata haihu cikin koshin lafiya ita da Babynta Ummi naga tin 07:00am mukazo amma har 09:00am tayi amma sai shiru mikeji karka damu insha Allah anakusa kaji to Ummi Allah yasa Amin karfe 10:00am dai-dai tahaihu tahaifi 'yarta mace kyakkyawa nurse tafito tafada masu anhaifi 'ya mace akawo kaya da baby oil Ummi dama tatanadi komai nabukata tamika mata Salim to barka da arziki Nafisa tahaihu lafiya yauwa Abba Salim inamaka murna Allah yaraya abinda akahaifa Amin Aunty Larai kagani ko Salim nafadama dayardar Allah zata haihu lafiya Allah yaraya mana baby Amin Ummi yace Abba inaneman wata alfarma agurinku alfarmarme kake bukata Salim wannan yarinyar da akahaifa inasan nasamata sunan kanwata wato Safna idan bakuda sunan da kukesan asaka mata haba Salim wannan ai bakomai bane mudai fatanmu Allah yaraya mana ita Amin Abba nurse tafito da babyn Abba ne yafara karbarta Ummi takallesa a'a Alhaji gaskiya bazanyardaba agabana zaka dauki wata toni Hajiya ainasami Amarya gaskiya ina wannan Auran bazai dauruba aikagama Aure tinda ka Aureni Salim da Larai sai dariyarsu suke Abba yamata addu'a yabawa Ummi itama yassnya mata albarka Larai takarba taganta tabawa babanta Salim yakarbeta yana kallonta wani farin ciki yakamashi yaji wani San yarinyar da kaunarta suna dada ratsashi yamata huduba tare da yimata addu'a yasanya mata albarka sannan yarada mata suna Safna sunshigo inda Nafisa sunsameta akwance sannu Nafisa yauwa Abba Allah yabaki lafiya Amin Abba Nafisa ansaukeko Allah yayarda Ummi to Allah yaraya mana Safna dasauri tadagokai takallesa yamata murmushi sannu Nafisa Yauwa Aunty Larai yakaraso inda take yana kallonta zuciyarsa cike take da farin ciki sannu da kokari yauwa to yakikejin jikin naki Alhamdulillah to Allah takara lafiya kinga yarinyar kuwa kyakkyawa tamkar ke tayi murmushi aidatayo fuskarka datafi haka kyau domin kasan cewa kafini kyau nesa ba kusaba nidai bansaniba su Ummi sunfita Ummi sai waya take bugawa tana fadama yan Uwa da abokan arziki kinji sunan babyn eh naji toya maki eh yayimin yauwa ninasan cewar zakiso abinda nakeso murmushi kawai take yaciro wayarsa daga aljihunsa yashiga danna number Safwan

By. Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:49] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
Part 2
1⃣6⃣
By

Fauziya Usman

Ringing biyu yadaga tare dayin sallama my friend barka da warhaka yagida ya Amarya lafiya qlau yasu Safna sunanan qlau kwana biyu haduwa tayi wuya wallahi kuwa abubuwanne sunyi yawa to ya'aka iya aisai godiya kawai to Allah yasa mudace Amin kasan mainakira nafadama a'a saika fada Nafisa tahaihu kaihaba Allah kaimasha Allah kace nagirma nazama uba mai akasamu baby girl masha Allah kamasan sunanta har kayinata suna eh yaushe aka haihune yau dinnan yanzu haka muna asibiti toya sunan 'Yar tawa sunanta Safna da gaske eh da gaske kai ammafa naji dadi sunan babbar kanwa to Allah yaraya yasa mata albarka Amin saina shigo toyayi amma dan Allah inagaida Nafisa kafin nashigo to zataji insha Allah dahaka sukayi sallama anbasu sallama sundawo gida saidai gidansu Ummi tadawo harzuwa ayi suna Safwan yafadamasu Umma Nafisa tahaihu kuma sunan babyn Safna farin ciki yakama Safna yayana sunana akasawa babyn eh kai ammafa najidadi sosai Umma takira Ummi tamata barka harta gaisa da Nafisa Zainab da Safna sunyima Salim barka awaya da cewar sai sunshigo suna bayan kwana biyu da sallamarsu Nafisa harzuwa yanzu mamakin sakawa 'yarta suna Safna take kawai daga ganin yarinya amafarki gaskiya ninafara kariya domin zuciyarta takasa yarda da cewa wannan yarinyar amafarki yasanta tabbas akwai wani abu dayake boye mata tana cikin wannan tinanin yashigo yasameta Nafisa maikike tinani bakomai yakai hannunsa yadauki babyn yana yimata wasa lokaci daya kanwarsa tazo masa azuciya sai tinanin yanda yayi rainonta yake saiganin wannan 'Yar yake tamkar Safna ce kanwarsa sai hawaye yakasa hakura yafashe da kuka domin kukan yaci karfinsa tindaga lokacin da yayi mafarki da Safna tana cikin kunci yakasa samun sassauci azuciyarsa kullum cikin damuwa yake Nafisa ce kawai tasani itama dan tana kusa dashi takallesa lafiya maiyafaru kukanme kakeyi nafarin cikine domin bantaba taba tinanin zama uba ba tayi murmushi amma na tambayeka inajinki dan Allah maiyasa kasawa yarinyarnan suna Safna sunan baimaki bane ko daya yamin inadaisan naji dalikinka bakomai kawai nasamata sunanne sabida inasan sunan to Allah yaraya mana Safna Amin ana saura kwana biyu suna yan sokoto sukazo gida yacika da mutane ranar suna su Zainab sunzo harda Ummarsu sai yamma suka koma tare da Safwan sukazo bayan sunada sati daya Nafisa takoma gidanta domin ta warware sarai batada abinda yake yimata ciwo ajiki damuwarta dayace Salim wanda har yanzu yaki fitowa yafada mata asalin abinda yake damunsa hakama duk lokacin da take tambayesa toyafi shiga damuwa hakan tasa tahakura tadena tambayarsa takuma cire abin azuciyarta sabida tasamu suyi zama cikin farin ciki da lumana

Kaduna

Kwanci tashi babu wuya agurin Allah Zainab dai takammala karatunta na jami'a yayinda Safna take ajin karshe bayan tatashi daga makaranta tabiya ta gidansu Asiya daukar Zainab sabida ankusa bikinta kuma Zainab tana daga cikin manyan kawaye ta'isa gidan tashigo tagaisa da mutanan gidan anyimaya iso zuwa indasu Zainab suke tashiga tare dayin sallama kallo daya zakayi mata kafahimci tana tare da gajiya Safna kindawo eh Aunty Asiya Aunty Zainab mutafiko bakisha ko ruwaba a'a Aunty Asiya nagode wallahi duk agajiye nake barci kawai nakesan nayi tamike to Asiya sai jibin to Zainab nafa gode sosai tafiso tayiwa Ummar Asiya sallama sunfito Asiya tayo masu rakiya harbakin mota saida suka tafi sannan tadawo ciki suna cikin tafiya wakai wata babbar mota tazo tafaka agabansu da sauri Safna taja burki ranta yayi mugun baci zatafita Zainab tace a'a Safna rabu dama kowaye kawai jamota mutafi haba Aunty Zainab dubafa kiga abinda yamana wannan ai wulakancine da rashin mutunci nikibarni nafita naji maiyakeji dashi tafito shima yafito yana wani irin murmushi wani kyakkyawan saurayine wanda bazaiwuce shekaru ashirin da bakwaiba sai murmushi kawai yake yayinda itakuma ranta yake abace 'yan mata barka da wannan Lokacin yauwa haba Malan amma kassn abinda kayi baidaceba ko kuma shine zakafito kanayin wani murmushi wannan yana nufin abinda kayi yabirgeka ko a'a Bahaka bane nikaina dolane tasani aikata hakan murmushina kuma yafarane alokacin dayaga wata kyakkyawar halitta acikin motarki tindazu nake binki saidai naga kamar bakiganiba Shiyasa nayi yanda zakigani domin banasan narasa farin cikin danagani atare dake Malan waimai kake nufine domin nidai banfahimcekaba kafitomin amutun tayanda zanfahim ceka to bara kiji zuciyata tanasan kawarki wadda kike tare da ita oho Aunty Zainab ai yayata ce kice kekanwarmu ce kaika iya bakinka daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zaki anfadama ko wace macece ake tara ayimagana da ita ahanya ko anfadama bamusan abinda mukeyiba kinga kanwata wallahi dolane tasani domin yin hakan sam bahalina bane

By. Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:49] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
Part 2
1⃣7⃣
By

Fauziya Usman

To kaji nafadama idan har da gaske kana San Aunty Zainab to kabiyota agida amma ba'ananba to taya zansan gidanku kabiyoni lokacin ne Zainab tafito domin ganin Safna tajima to firarme sukeyi haka yindazu tana fitowa taganta takawo bakin mota yayinda yake biye da ita Aunty Zainab dan Allah kiyi hakuri kinga najima ko tashiga tadauko wani karamin kati tafito tamika masa yayi murmushi yacewa Zainab sannu tare da dagamata hannu yayinda fuskarsa take murmushi ya'amsa masa da yauwa sannu mutafi ko sunshiga mota sunbarshi atsaye yana murmushi yayinda farin ciki yacika zuciyarsa saiyaji yakara santa saboda yafahimci cewa suna da tarbiya tagari daga yanda yake sauraran maganar kanwarta yaje yashiga motarsa yayi tafiyarsa suna cikin tafiya Zainab takalli Safna wai zancanme kukeyi da wannan saurayin kodai kinyi gamone tayi murmushi a'a tomaiya fada maki karki damu zansanar dake komai zuwa anjima yanzu agajiye nake to shikenan sun'iso gida suna shiga falo Safna tafada kujera sannunku da

Please Login or Register in order to submit comment