Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kokarin yimata yawa damuwa kuma eh Abba zan'iya ganinta eh sunshigo yaganta yayinda yaketa maimaita abinda aka fada masa to maiyake damun Safna ne harhaka Hafiz waya kawota asibiti suna a waje muje nagansu Sunfito yakaishi gurinsu Hafsat sungaishesa ya'amsa yamasu godiya

Safwan tinda safiya Tawaye ko kasa baisaukoba saboda zuciyarsa kuna take yimasa yana cikin bacin rai sosai baikumayi tinanin Safna ta tafi makarantaba saboda yahangi motarsu acikin get yakai hannunsa ga wayarsa domin ganin wadanda suka kirashi shikashe wayarma zaiyi yahuta yana dubawa yaga missed call da yawa number Hafiz ce asama hakan Yasa yafara kiran layinsa yadaga sungaisa Hafiz kakirani bana kusa eh dama nakurane domin nafadama Safna tana asibiti saboda nakira layin Zainab baitafiba ganin baka dagaba nakira Abba yanzu haka yananan atare da ita Hafiz maiyasami Safna karka damu tana samun sauki tana asibitinmu to ganinan tafe yauwa saikazo

By. Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:52] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
Part 2
3⃣2⃣
By

Fauziya Usman

Lokaci daya yakara shiga tashin hankali da damuwarsa takeru yayinda zuciyarsa yake buga masa da karfi yafito agigice yashiga dakinsu Zainab yasameta akwance tana ganinsa tatashi yaya Safwan kafito eh Zainab dama Safna tatafi school ne eh talura da yanayinsa tace yaya Safwan lafiya yagirgiza kai Zainab Safna tana asibiti batada lafiya innalillahi wa'inna'ilaihiraji'un maiyasameta nima bansaniba yanzu zantafi domin naga halinda take ciki yaya Safwan ina zuwa a'a Zainab domin Umma idan taganmu tare zatayi tinanin gurin Safna zamu tafi to shikenan idan katafi dan Allah kakirani kaji zankiraki yafito zaifita Umma tadakatar dashi ina zuwa zanje wani gurine kacemin zakaje gurin Uwarka to bazakaba a'a Umma wallahi ba school dinsu Safna zaniba wani guri daban zanje dan Allah kibarni nafita to jeka tinda karantsemin yafito yayi tafiyarsa ya'iso asibiti yakira Hafiz sunhadu yakaishi inda Safna take yasami Abba adakin da sauri cikin mutuwar jiki yakai inda take harzuwa wannan lokacin bata farfadoba yana kallonta idansa suna zubar da hawaye Abba sai kallonsa yakeyi irin yanda yaga yashiga damuwa abin akwai mamaki Abba yakira sunansa Safwan dan Allah kafadamin maiyake damun Safna yagirgiza masa kai nima bansaniba Abba to shikenan lokacin salla yayi duk sunfita sunyi gurin salla Abba yacewa su Asma'u sutafi gida haka suma susamu suhuta basuso yafiyaba haka sukahakura sukatafi bayan sunyo salla sundawo lokacin tafara motsawa tana tari ahankali take buda idanta harsuka bude tafashimci ba'a school takeba kuma ba'a agida takeba cantakai kallonta ga Abba taga Safwan da kuma Hafiz tayi dogon numfashi tare da ajiyar zuciya Safna kinfarka yajikin naki nasami sauki Abba sannu Safna yauwa yaya Hafiz takai kallonta ga Safwan taga yanata hawaye suna hada ido yayi saurin sunkuyarda da kansa masa tayi dan murmushin karfin hali yayana lafiya kukanne kake kaga indai dantanice to karka daga hankalinka domin nassmu lafiya yanzu gida zamu Abba mutafi gida a'a Safna kibari kikara samun sauki mana kina bukatar hutu ayanzu tayi shiru nalokaci kadan sannan tace nasamu sauki yaya Hafiz ba'abinda yakeyimin ciwo ajikina hutu kuma dakake magana ina samunsa fiye da tinanina dan haka kabarni natafi gida to tinda kinmatsa Abba zaku iya tafiya amma gaskiya tana bukatar hutu dakuma kulawa to shikenan bayan ruwan sunkare suka fito suka tafi motar Abba tashiga suna cikin tafiya Abba yakira sunanta Safna dan Allah kifadamin abinda yake damunki kinji tayi yar dariya kaima kafara yarda da zancan asibiti to niko mezai dameni awannan lokacin Abba dan Allah kayarda banda damuwar komai araina to shikenan acan gida bayan fitar Safwan baifi mintuna biyarba Salim yazo gidan yashigo yasami Umma itakadai afalo bayan sungaisa yace gurin Safwan yazo aikuwa yanzunnan yafita Umma dama lafiyarsa qlau eh to maiyasa baitafi office ba to Salim saikunhadu saikaji Umma Safna fa tana mskaranta ok toni zantafi to Salim kagaida gida sunyi sallama yatafi Safna takalli Abba tace Abba dan Allah idan mukatafi gida karka fadi cewa daga asibiti muke ko maiyasa domin nasan Umma da Aunty Zainab zasu sakani agaba da tambayar da banida amsarta to insha Allah bazan fadaba Safna na'am Abba idan kinhuta kikira kawayanki domin sunjima asibiti saida nace dasu sutafi sannan suka tafi to Abba insha Allah ina shiga gida zankirasu sun'iso gida sunshigo saidai basuga motar Safwan ba to ina yatsaya sunshigo sunsamu bakowa Umma tagaji da zama tayi dakinta yau kuma falon bakiwa mebi sungaji da zama suntafi sukwanta Abba ninatafi sama to kifito kici abinci kinji Abba kamanta ina axumi kinga Safna azuminnan tinda bana farilla bane ki'ajiyeshi to Abba yauwa kokefa Allah yaimaki albarka Amin Abba tayi tafiyarta shima yanufi dakinsa Safna nashiga tasami Zainab sai zagayen daki takeyi ga alama tinani takeyi bata masan tashigoba tadan dafata tajuyo afirgice da sauri tawani zaro ido Safna kece eh Aunty Zainab lafiya kike kuwa Safna inafa lafiya nasami labarin kina asibiti kinga Aunty Zainab karki wani daga hankalinki domin nasamu lafiya to Allah yakaro afuwa Amin ina yaya Safwan nima bansan yana inaba kamarya baije gurinki bane taje saidai baiyimin maganaba da zamu dawo kuma motar Abba nashiga inajin koyabiya tawani gurin suna cikin maganarsa yaturo kofa yashigo yasami guri yazauna jikinsa asanyaye yake magana yakira sunanta Safna yajikinki nasami sauki talura da yanayin dayake ciki tace kaga yaya Safwan dan Allah kadena saka kanka acikin damuwa domin wannan gaddara tace nakuma yarda da ita baikamata kuma kukasance acikin damuwaba domin ganin damuwa atare daku tana fada tana kuka yazanyi banda wata mafita hakama banda wata fargaba face kaddarata banda kowa aduniya faceku sai kuma yayana Wanda bansan koyana rayeba koya mutu kune gatana daku nake tutiya domin kungama min komai arayuwa kinga Safna maganar ta'isa haka kiyi shiru kukanma ya'isa kibarshi haka kinga ko lafiya bakida kar damuwar tayimaki yawa kinji to Aunty Zainab nadena taje takawo mata abinci da ruwa itace take bata da kanta kadanci Kazan tatafi tayo alwala tayi sallah takira Hafsat da Asma'u tayimasu godiya daga bisani tasha magani takwanta sai barci

By. Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:52] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
Part 2
3⃣3⃣
By

Fauziya Usman

Gwambe

Jamila nafalo itada Nusaiba taji anturo kofa anshigo tajuyo danganin waye tayi tinanin maigidantane yadawo abin takaici saitaga Fa'iza takira sunanta cike da mamaki Fa'iza lafiya Jamila kenan maikike mamaki da ganina sabida nafita harkarki Jamila bara kiji aini bansan cewake muna fuka bace saidaga baya dama ashe mahaifarki tasami matsala shine kikawani cemin dan uwana nane bayasan haihuwa to wallahi baki isaba domin dole yaya Mansoor yakaro Aure damacan dankihaifa mana zuri'a aka Auroki badan kizo kiyi zaman jindadiba kina hutawa tayidan murmushi Fa'iza kenan aigarani tinda nahaifa daya kinga nafiki keda kodaya baki ajeba gakinan saikace tsintarciyar akuya ko ina anaganinki agari idan zaman gidan miji banzane kije kiyi mana ina zaman zamana lafiya da mijina da abokiyar zamana lafiya kikaxo kikarikitamin lissafi kikasamin wawan tinani irin naki kika rabani da farin cikin gidan Aure kikasa mijina yatsaneni wallahi kincuceni saina gode Allah da yanunamin gaskiya tinwuri bari kiji Fa'iza nifa bakamar Haj Aisha bace da kika rainaba kina yimata wulakanci tana hakuraba in wallahi bazandauka domin ko tashanci nafiki idan takama mudaku saimu daku da juna domin mucire raini banza shashasha wadda batasan zaman lafiyaba kekamdai wallahi shaidance mai raba mata da miji mairaba daya biyu haka sukayita musayar baki da juna harzuwa wani lokaci bayan Fa'iza tatafi Jamila tayi zaune duk abin duniya ya'isheta dama Haj Aisha tayi-tayi tanuna mata illar Fa'iza amma sam tarufe ido gashinan yanzu tagani amma zata gyaramata zama domin daga yanzu bazata sake shigo masu gidan da zancan cinmutunci ko wulakanciba saita nunamata wuta namaganin roba batan mintuna talatin da tafiyar Fa'iza Alh Mansoor ya'iso tare yake da Haj Aisha sun'iso lafiya Jamila batakoji isuwarsuba sabida bacin ran datake ciki sunfito kaitsaye sashanta tanufa tana Shiga taga dakin duk yayi datti da kura kuma gashi tafiyar dare sukayi tashiga bedroom shima taga yayi datti da kura to yazatayi dole tayi hakuri harzuwa gobe tagyara dak dacewa tafiyar takwana biyu ce tajikuma bazata iya hakura har safiya tawayeba domin bazata iya kwanciya ahakaba tashiga toilet tayo alwala tafito tayi salla tatashi tafara gyaran dakinta Alh Mansoor kaitsaye dakin Jamila yanufa yatura kofa yashigo Nusaiba taje da gudu tarike masa kafafu tanamasa oyoyo yayi dariya yadauketa Sama itama dariyar take Jamila tayi murmushi sannu da zuwa yauwa yazauna yahanya Alhamdulillah yagidan dafatan komai normal insha Allah to madallah takallesa tace ya Hajiya yaji tambayar tamkar amafarki tayi murmushi janajin mamakina ko to kadena dominni ayanzu rayuwata tacanza bakamar yanda kasaniba kuma bana fatan dana kara komawa ayanda nake ta dukursa akasa tare da sunkuyar da kanta kasa tace mijina dan Allah kayafemin kayimin afuwa kagafarceni wallahi nacanza halina nadena duk wani hali barakyau zankasance salihar mace maiyin biyayya agareka mamakinta yakamashi sai kallonta yakeyi yajinjina kai yace tashi kizauna tatashi tazauna Jamila ni bakiyimin komaiba kuma kinsani cinmutuncin Haj Aisha da kikeyi shiya haifar da matsala atsakaninmu amma badan kin aikatamin komaiba da sauri tace wallahi nadena zanbata girmanta zanyi biyayya agareta fiye da tinaninka da gaske kike eh kinyi alkawari eh nayi totashi muje ina kuma zamu kabari kaci abinci kayi salla mana karki damu tashi muje ta'amsa dato tatashi sunfito yana rike da hannun Nusaiba taga sunnufi sashen Haj Aisha saidai tayi shiru batayi maganaba sun'isa bakin kofa yabuga yaji shiru yasake bugawa nanma yaji shiru itadai kallonsa take tare da tinanin tomaizaiyi adakin miye aciki tinda baifada mata cewa tare yazo da Hajiya ba to amma koma miye zata gani ganin ba'azo anbudeba yasa yatura kofar sunshiga ssidai bata falo Jamila tace Alhaji wai lafiya karki damu inazuwa yashiga daga ciki yasameta tanata aiki jinmotsi abayanta yasata juyowa kafin tayi magana yace haba Hajiya miye haka kikeyi kedayaka mata kizauna kihuta saikuma kikama wani aiki tayi murmushi to yana'iya dakinne duk yayi datti da kura wallahi bazan'iya kwanciya ahakaba tonaji yanzudai fito kiga ta'ajiye aikinta tabiyoshi sundawo falo Jamila nazaune tamike dama tare kukazo eh kindai gani Haj Aisha tace Jamila barka da zuwa yauwa ammani yakamata nayimaki barka da zuwa domin kenasha hanya banida nake acikin gidaba yauwa yagidan lafiya qlau Alhamdulillah Nusaiba kina lafiya ya makaranta qlau to Allah yabada sa'a Amin nan suka zauna Jamila taroki Haj Aisha gafara sunyafi juna Alh Mansoor yaji dadi sosai da ganin wannan ranar yatashi toni bata natafi nayi salka to nima zsnkoma bakin aikina Hajiya aiki kikeyi eh Jamila bakiga yanda dakin yayi datti da kura ba to bara natayaki a'a Jamila jeki gurin mijinki kiyi aikin lada nidai gaskiya saina tayaki a'a Jamila nifa bazanbarkiba to kunga Hajiya ninayafe nawa haki tatsaya tatayaki to godiya name yafita Nusaiba tabishi sukuma suncigaba da gyaran dakunan bawani daukar lokaci sukayi suka gama sunci abinci cikin farin ciki da walwala bayan sunkarasa cin'abinci sunzauna sunata fira saida dare yayi sosai sannan Jamila da Alh Mansoor suka tashi zasu tafi domin adakin Hajiya Aisha suke sunyi mata saida safe suntafi anan tabar Nusaiba takwana Haj Aisha tajidadi sosai aranta domin ita tanasan Jamila har cikin ranta haka sukayi kwana biyunsu cikin jindadi ranar da zasu koma Jamila taji tamkar karsutafi to amma bayanda zatayi sunfito tayo masu rakiya harbakin mota saida suka Tafi sannan tadawo ciki saijin ranta takeyi fari kal batada wata damuwa ko bacin rai balantana tinani ya'addabeta zaman lafiya yafi komai dadi arayuwa Allah ya'isar mata da Fa'iza datayi kokarin ruguza rayuwarta me'akeyi da Fa'iza can takarata itadai Allah yanuna mata gaskiya kuma tasa hannu biyu tadauka Wannanma kawai ya'isheta farin ciki arayuwa

By. Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:52] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
Part 2
3⃣4⃣
By

Fauziya Usman

Kaduna

Zaune suke gurin hutawa shikadaine kemagana yayinda ita wani abu daban take tinani abin yabashi mamaki yakira sunanta Zainab maikike tinani haka keda yakamata kikasance acikin farin ciki domin ansaka ranar Auranmu saikuma nasameki bakya cikin dadin rai waimaiyake damunkine kwanakinnan nafahimci sam bakya cikin walwala yakamata kisanar dani ko akwai wani taimako da zan'iya yimaki tayi ajiyar zuciya karka damu Hafiz insha Allah komai zaidai-daita to Allah yasa Amin Zainab niko wai ina Safna najima bana ganinta ko wayarta akakira bata shiga wani lokaci kuma tana ringing ba'a dagawa Safna nanan qlau makarantace take hana aganta sannan kuma wayarta tasami matsala shiyasa sundan jima suna fira daga bisani sukayi sallama yatafi tashigo ciki tasamu Safna akicin tana girki tahirgiza kai yayinda tausayinta yakamata domin ayanzu duk aikin gidan yakoma kanta ita takeyin komai Umma sam bata tausayinta dimin karta sami samat dazatace tanasan Safwan takaraso inda take sannu da aiki kanwata yauwa Aunty Zainab yaya Hafiz haryatafi eh mundai kusa shan biki agidannan Safna bara natayaki a'a kibarshi nagode tayi-tayi amma sam takiyardar tatayata dole tahakura tabarta bayan takarasa tashiryashi akan tebur sannan tayi tafiyarta domin ita sam tadena cin'abinci akullum ako wace rana azumi takeyi kuma idan magariba tayi batacin abinci iya kacinta tasha shayi ko coffee hakan tasa duk tacanza kamannunta tayi baki tarame tamkar ba itaba abin yana damun Abba sosai saidai yakasa samun Wanda zaifada masa haka Safwan shikansa yanayinsa yana damun Abba da Salim wanda yakasance tamkar hussininsa ayanzu Abba baikosan yadawo gida saboda bashida nishadi da farin ciki agidan gidan yakoma tamkar bashiba kowa cikin kunci yake har Umma ssidai zuciyarta tafi karfinta domin tatsayu akan turbar data azata

Wata rana Safna tadawo daga makaranta tashigo tasamu Umma tana kokarin fita Safna kindawo eh Aunty Zainab to sannu da zuwa yauwa nagode Umma fita zakiyi eh to Allah yakiyaye adawo lafiya Allah yasa Amin yauwa Safna na'am Umma idan kin ajiye jakarki kije baya kayanacan nasa anjikasu tindazu saiki wanke to Umma Zainab taji wani irin bacin rai tace haba Umma haba Umma maiyasa kike hakane dan Allah kibarta tahuta mana to Uwata yimin fada wallahi Zainab ki kiyayeni tinkafin ranking yabaci aikin banza nasata wanki inkin isa dan Allah kihanata kuma bara kiji wani abu dazanfada maki idan kika yarda kika tayata wankinnan to wallahi banyafe makiba amatsayina na mahaifiyarki tana kai karshen maganarta tafita tayi tafiyarta duk kanninsu hawaye suke zubarwa Safna taje ta'ajiye jakarta da mayafinta tafito Zainab nakallonta amma bayanda ta'iya dole tabarta taje tafara wankin tanayi tana kuka tafada azuciyarta dama rayuwa zata sauya mata haka tana wanki tana kuka abin duniya ya'isheta Zainab tana falo zaune tarasa maiyake yimata dadi Safwan yashigo yasameta yace Zainab ina Safna tana baya baya kuma maitakeyi Umma ce tasata saitafashe da kuka mai Umma tayimatane Ummace tasata wanki kuma gashi azumi take takumace batayafe natayataba Safwan yace wanki fa kikace kaitsaye yanufi inda take yasameta tahade kai da guiwa tana kuka ya dukursa kusa da ita yadafa kafadarta tadago kanta lokaci daya sukayi ido biyu take tausayinta yakamashi baisan sanda idansa suka fara zubar da kwallaba cikin kasa-kasa da murya yace kanwata kigafarceni domin duk halinda kika shiga nine sila saidai kuma nima banda laifi ko ince balaifina bane laifin soyayyarkine domin koda inada laifi to tabbas soyayyarki tafi komai zama laifi saboda itace take sarrafani harma da zuciyata Safna yazanyi da dinbin sosayyarki dake cikin zuciyata hakama kaunarki tayi matukar tasiri acikin zuciyata Safna wallahi soyayyarki tayi yawa atare dani banida abinyi face tinaninki dakuma sanganinki zuciyata har kullum kaunarki takeyi hakama harkoyaushe banajin sankowa sainaki nikaina nakasa fahimtar ya'akai nafara sanki domin kuwa nakasa sankowa saike kekawai nakeso dan Allah kiyarda dani kikuma amince da soyayyata karki juyamin baya domin zan'iya mutuwa idan har narasaki dominke duniyata ce soyayyarki kuma rayuwarace hakama tinaninki kuma ruhinane wallahi banda wani abu danakeso fiye dake kanwata najima inasanki soyayyarki hartakusa ta'illatani narasa yazanyi da raina kitaimakeni kanwata dan Allah kiyimin alkawarin soyayyarki domin samun farin cikina tinlokacin dayafara magana kallonsa take yayinda hawaye kefita afuskarta azahirin gaskiya tanasan Safwan saidai bazata iya baiyana masaba saboda tana matukar jintsoran Umma kuma bazataso wani abu yashiga tsakaninsa da Umma ba koba komai ita Uwace agaresa yatsinke mata tinani tahanyar kiran sunanta Safna dama nasan dole zakiyi tinani akan hakan saboda kina shakkar Umma to inasan kisani wallahi Allah ne kawai zairaba soyayyata dake ta hanyar daukar raina domin nidai harkullum harkoyashe kece ZABINA kenakeso domin dasanki nabude ido dashi nagirma dashi narayu kuma dashi nakecigaba da rayuwa harkawowa yanzu hakama dashi zanmutu kuma inafatan ko alahira Allah yatasheni dashi itadai kallonsa kawai takeyi yayinda manakinsa yacikata

By. Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:52] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
Part 2
3⃣5⃣
By

Fauziya Usman

Tace a'a yayana maiyasa zakayarda da abinda zuciyarka take sakama bayan badai-dai bane kuma bazai taba tabbataba maiyasa jindadi yasa namanta niwacece namanta da asalina yayinda nashagala nakasa tuna matsayina yaya Safwan nida kai munada babnbanci maitarin yawa kai kakasance tamkar sarkine yayinda nake matsayin baiwarka kuma kaskantacciya maragata a'a Safna kidena fadar haka kayi hakuri kabarni nayi magana yaya Safwan ni wallahi banga laifin Umma ba domin tanada gaskiyarta kowace Uwa zataso danta yayi Aure gidan mutunci da asali, nasaba, da kuma nagarta saidaini bandaga cikin wadannan niba kowa bace face tsintarciya abinda Umma tayi shine dai-dai batada laifi ko daya yadakatar da ita tahanyar sa hannunsa yarufe mata baki yagirgiza kai a'a Safna dan Allah kidena fadar haka wallahi banaso kinji raina yana baci sosai dajin wadannan kalaman naki dan haka kidena banaso kinji tadaga masa kai alamar eh yauwa kokefa kinga yanzu abinda za'ayi kibar wankin haka nizan karasa zatayi magana yadakatar da ita bayanda ta'iya dole tabarshi yakarasa bayan sunkammala gaba daya sunyi shanya sundawo falo sunsami Zainab azaune ssidai bata cikin walwala tace Safna sannu kinji yauwa Aunty Zainab Safwan yacema Zainab tazubo mata abinci ta'amsa dato tatashi yayana kamanta ina azumi yayi ajiyar zuciya kinga Safna wannan azumin dakike bana faralla bane maiyasa kiduba kinga yanda duk kikarame kinga dan Allah da girman Allah kibar azuminnan haka to dame zakiji da damuwar dake addabarki koda yunwar dake cikinki wannan ai azabtar da kanji kikeyi gaskiya banaso danyanzuma dole zakici abinci wannan azumin bazanyarda kikaishiba idan kuma kikaki to nima zanyi yajin cin'abinci natsayin wani lokaci tayi dogon numfashi tare da ajiyar zuciya toshikenan zanci yayi dan murmushi yauwa kokefa Zainab jezuba mata abinci tatashi tatafi tazuba anincin ta'ajiye kan tebur tadawo yaya Safwan ga abincincan kan tebur ok sannu Safna mutafi ko ta'amsa dato tatashi lokaci daya taji kanta yasata yayinda zuciyarta take bugamata da karfi Safwan yakalleta lafiya tagirgiza kai bakomai to mutafi tana cikin tafiya taji jiri nadibarta bata ankaraba tafadi akasa somammiya da sauri Zainab da Safwan suka isa gareta yayinda kowannansu yake fadar sunanta tare da jijjigata amma bata iya farfadowaba Safwan yadauketa sunfito yasata mota sunyi asibiti Zainab ce ketuka motar shikuwa Safwan yana rike da Safna abayan mota asibitin su Hafiz suka nufa suna isowa akashiga da ita Safwan da Zainab saikai dakawo suke sunkasa zaune sunkasa tsaye bayan wani lokaci su Hafiz sunfito da sauri Safwan ya'isa garesa yana tambayarsa halinda take cki yayi shiru yagirgiza kai ganin yayi shiru yaki magana yasa Zainab zuwa inda suke tace kaga Hafiz dan Allah kadaure kafada mana halinda Safna take ciki domin shine kwanciyar hankalinmu yace to kubiyoni office bayan sun'isa office dinsa sunzauna yakallesu daya bayan daya yace gaskiya Safna tana cikin rashin lafiya sosai domin ga alama tinani yayimata yawa Wanda yahaddasa mata da damuwa mai tsanani wanda yake samata bugun zuciya ayanzudai daf take da kamuwa da ciwan zuciya mai tsanani domin gaskiya damuwar Safna tayi yawa sosai Zainab tafashe da kuka yaya Safwan munshiga uku yanzu miye mafita kuka takeyi sosai hartamanta da Hafiz shine mijin da zata Aura saboda tashiga tashin hankali Safwan yashiga damuwa matuka dajin wannan labarin yayinda idanuwansa suke zubar da hawaye ba'abinda yake fada face innalillahi wa'inna'ilaihiraji'un azahirin gaskiya yana cikin tashin hankali yanayin da Hafiz yaga sunshiga lokaci daya yadaga masa hankali yatambayesu meke faruwa saidai basu iya cewa dashi komaiba Safwan yafita yabar office din Zainab tabi bayansa hakan yatabbatarwa da Hafiz Cewa akwai matsala nantake yaciro wayarsa yakira Abbansu yasanar dashi halinda akeciki cikin gajeran lokaci Abba ya'iso asibiti kaitsaye office din Hafiz yanufa Abba yashiga tambayarsa halinda Safna take ciki yafada masa komai ba'abinda yaboye masa Abba yashiga damuwa sosai jin halinda Safna take ciki inasu Zainab ko suna gurinta a'a sunadai kofar dakin bazaiyuwu sushigaba ayanayinda suke domin tana bukatar Hutu sosai Abba yace Allah kaba wannan yarinya lafiya Amin Abba toni zaiyuwu naganta eh mutafi sunfito tindaga nesa Abba yahangi Safwan da Zainab cikin wani irin yanayi naban tausayi sunkaraso inda suke Zainab da gudu tazo inda Abba tana kuka duk tausayinta yakamasa yashiga rarrashinta sunshiga inda Safna kallo daya zakayi mata kafahimci tanajin jiki Abba yakira Umma ya sanarmata bawani bata lokaci ta'iso asibiti ita kanta tausayin Safna yakamata dana yaranta sai dai gaskiya batajin zata'iya barin Safwan ya'auri Safna yarinyarda batada asali wama yassni ko shegiyace bata da Uba shine dalilin da yarabata da iyayanta haka kawai yajanyo masu magana agari wallahi sam bazata yardaba dukkanninsu bamai magana hakan yasa dakin yayi tsit shiru daiketashi

By. Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:52] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
Part 2
3⃣6⃣
By

Fauziya Usman

Kano

Zaune suke suna fira Safna tana wasa da kayan wasanta wadanda Safna tasiya mata Nafisa tadauki wayarta tashiga danna number ta amma arufe tayi shiru tanadan nazari Salim yafito yasameta ahakan yadan dafata tajuyo sunkalli juna lafiyarki kuwa maikike tinani harhaka wallahi yaya Salim tinanin Safna nake narasa maiyasami wayartane akullum nakira sai ace layin arufe yake gaskiya abin yana bani mamaki matuka nikaina abin yana bani mamaki amma bakomai insha Allah idan munkoma saimuje mudubata danmusan halinda take ciki ko gaskiya hakan yakamata amma wannan shirun yayi yawa to idan kinshirya mutafi aini tindajimawa nashirya kainake jira sunfito yarika hannun Safna sunshiga mota suntafi sub'iso gidansu Ummi sunshigo Safna tayi gurin Ummi tana dariya domin tasaba da ita sosai saboda kowane karshen sati saisunzo kano sunkwana biyu sunzauna sungaisa da Ummi Nafisa tace Ummi yau kedayace afalo ina Aunty Larai tana ciki nima yanzu nafito Safna tasauka jikin Ummi tayi

Please Login or Register in order to submit comment