Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuwa yauwa indo ananan eh Umma fa tana ciki kinga Safna kitashi kobazakici abinciba tokiyi sallah sannan kizo kikwanta kinga lokaci tafiya yake wallahi Aunty Zainab nagaji sosai naji duk dahaka kifarayin sallah sannan kikwanta kinji haba Safna kinfasan sallah tana gaba akan komai maiyasa kike wasa da itane abinda bahalinkiba to bara naje nayi yauwa kokefa taje tayi sallah tayo wanka tashirya cikin riga da wando tayikyau sosai domin ko ita tayaba kanta tafito falo keda kikaje sallah harda wanka tonaji gajiyar tayimin yawa shiyasa nace bara nayi wanka naji kozata rage wai Umma haryanxu bata fitoba lafiya kuwa dan Allah kuyi hakuri wallahi mantawa nayi tafita ina kuma taje ta tafi gidan Hajiya Aunty Safna kinyikyau sosai nagode Ammar ina yaya Safwan ai yafita yaushe yafita bayan nadawo daga school yafita ina kaji yace zaije gaskiya baifadaba suna cikin firarsu saiga Habu yashigo tare da yin sallama bayan yagaishesu yace Zainab kinyi bako dasauri Safna tace kace tana zuwa to shikenan yatashi yafita Zainab takalleta taga tana dan murmushi Safna kinsan da zuwansane eh wayeshi wanda muka hadu dashi ahanya to shine dama yafadamin cewa yana sanki kuma zainemi inda kike yanzu kije kishirya kafinnan nizan fita mugaisa to shikenan tare suka Safna ta'aza after dires tafito tafita tasamesa acikin mota yana ganinta yafito yana murmushi sai fari'a yakeyi sannu da fitowa kanwata yauwa ammafa gaskiya nayi mamaki domin sanda kafadamin abinda yake zuciyarka wallahi banzaci da gaske kakeba aikuwa kinyi kuskure dominni da gaske nakeyi inasanta harcikin raina aika tabbatarmin da hakan domin naga zahiri to ina maku fatan alkhairi nagode toke yasunanki tayi murmushi Safna to yasunan yayan nawa Hafiz suna tsaye Safwan yadawo yashigo yana kokarinyin parking yahangesu atsaye suna fira da dariya yafito da sauri yayinda yake hadeye rai yana bata fuska yakaraso inda suke lah yayana kadawo sannu da zuwa yakalleta ke waye wannan haba yaya Safwan wannan irin bata fuska haka aisai kasa natsorata kinga tambayarki nayi kiban amsa to sunansa Hafiz yazone gurin Auntu Zainab shine nafito mugaisa Kafin tafito yaya Hafiz ga yayanmu sai lokacin yasaki ransa tare da sakin fuska yabashi hannu sungaisa tare da yimasa sannu da zuwa bayan sungaisa yakalli Safna toni nashiga daga ciki sai kinshigo to yayana saina shigo am yaya Hafiz mutafi nakaika masaukinka sunzo takawoshi wani hadaddan guri yazauna takoma ta kawo masa ruwa da lemu mai sanyi tare da dambun naman rago to bara nakirama ita to godiya nake tashigo tasameta takarasa shirinta tayi matukaryin kyau sosai sai kamshi take sunfito tare to yaya Hafiz ga Aunty Zainab ina matukaryin godiyata agareki lah bakomai wallahi toni zanshiga daga ciki tabarsunan tayi tafiyarta yakalleta tabirgeshi sosai yace mata Amincin Allah yatabbata agareki yake wannan kyakkyawar yarinya inagodiya ga Allah dayanunaminke azahurina domin da abarci kikazomin toda bazanso nafarkaba sunana Hafiz Sani nidan garinnanne ina aiki asibiti ma'ana daini doctor ne tinda naganki komai nawa yatsaya domin banaganin kowa saike sanki kawaine yake aiki atare dani dan Allah kidaure kicije kiyarda da soyayyata nikuma nayi maki alkawarin zancika zuciyarki da farin ciki maitarin yawa zansoki fiye da raina zanbaki kulawa fiye da lafiyata nidai burina ki Amince dani amatsayin masoyi domin nassmu nayi rayuwa mai inganci tayi murmushi maitattare da nishadi karka damu domin nima inasanka nayarda dakaine sakamakon yanda naga Safna tayi na'am da zuwanka kai amma yau ina cikin farin ciki Marar misaltuwa haka sukaci gaba da firarsu lokacin da Safna tadawo tasamu Ammar kawaine afalo ta tambayesa ina yaya Safwan yana dakinsa ok tayi Sama tashiga daki tacire abayarta tafito daga harzuwa wannan lokacin baifitoba kaitsaye dakinsa tanufa tabuga kofa yace shigo mana taturo kofa tashigo tamayar tarufe tayi tsaye jikin kofa tanata murmushi shikuwa sai wani irin kallo yake mata sabida shigarta tayimasa kyau sosai yana akwance tashigo baisan sanda yatashiba haryakai inda take yayi tsaye Yana kallonta

By. Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:49] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
Part 2
1⃣8⃣
By

Fauziya Usman

Tasa iskan bakinta tahura masa afuska ya lumshe ido tare da ajiyar zuciya wannan irin kallo haka so kake kaga munina kanwata kinyimin kyau sosai naji amma irin wannan kallo zaisa kaga munina yayi murmushi Safna kenan aida ace zanyi'iya tsayin rayuwata ina kwallonki wallahi bazan taba ganin muninkiba domin bakidashi kyanki na musammanne inagodiya sosai abisa yabani dakake saidai ka'iya bakinka domin idan Aunty Baby taji bazataji dadiba yayi murmushi Safna kenan zokiga yajanyo hannunta sunzo bakin madubi yatsayar da ita kidubeki mana kebakiga yanda kikebane tayi murmushi yayana kenan kana yabani da yawa kanayin duk wani abu dazaisani farin ciki inagodiya abisa hakan wallahi yaya Safwan shiyasa idan bana tare da kai nikawaice nasan irin yanayin danake shiga domin abin bazai faduba kanwata kenan inamatukar san naga kina farin ciki yaya Safwan yunwa nakeji to muje kici abinci sunfito sunje sunci abinci su Zainab sunjima suna fira ganin duhu yafara yayi mata sallama yatafi saidai kafin yatafi yabuda mota yadauko wasu manyan ledodi yabata takarba tayi masa godiya sosai yaji dadi aransa yatafi tashigo tasami su Safna gurincin abinci ta'isa inda suke Aunty Zainab sannu da shigowa yauwa haryatafi eh to yaushe zaidawo gaskiya ban tambayesaba to maiyasa saboda batada surutu irin naki yaya Safwan yanzu danta tambayi lokacin dazai dawo saiyace tacika surutu Aunty Zainab amma gayan yamaki ko domin kunyi kala dashi wannan shi akekira zabin Allah ko hadin Allah waikinsan wani abu a'a wallahi dazu ko badan yafadamin uzurinsaba wallahi dayasha mamakina sosai ainima nayi tinanin haka kuzo kuga abinda yakawomin suntaso sundawo falo sunzauna tanuna masu ledodin Safna ce kebudawa domin suga miye aciki dayar ledar kayan makeup me da turaruka da mansha fawa tare da Sabulu da sauran kayan kyale-kyale na mata dayar ledar kuma kayan chocolate ne masu yawa aciki lokaci daya tadaga kai takalli Safwan yaya Safwan kaima haka kakeyiwa Aunty Baby kallonta kawai yayi tare da yimata murmushi amma baice da ita komaiba itama murmushin take yayana kenan aishiruma magabace gamai tinani Safna tadauki chocolate takira Ammar tabashi itama tasaka ledar agaba saisha takeyi karfe 08:30pm Umma tadawo Abba ne yadaukota bayan sunshigo sunyi masu sannu da zuwa sunzauna sunhuta Safna tace Umma yau bakinan mukayi bako bako kuma eh wane bako konace waye yazo sunansa yaya Hafiz waye maiwannan sunan tadawo kusa da ita Umma kalli Aunty Zainab kigani Umma tadago kai sunyi ido biyu da Zainab da sauri tatashi tayi daki saboda tanajin nauyinsu Abba itakuma Safna sai dariya take Umma kingama kayan da yakawo mata nida Ammar har munsha chocolate Umma tayi murmushi Abba yace waimai kuke fadane Umma tayimasa bayanin komai yayi murmushi to ita Zainab tana sansa eh Abba to Allah yasa alkhairi dama tinda takarasa karatunta nake fatan ganin na Aurar da'ita domin Aure shine gatan duk wata mace saurake Safna tayi dariya sosai nikuma Abba eh kemana domin tare zan Aurar daku a'a Abba saidai ko yayana amma badainiba aini bankarasa karatuna ba tatashi tayi tafiyarta tasami Zainab tana amsa waya daga yanayin dataganta tasan da Hafiz take waya bayan Safna tatashi Umma takalli abba tace Abban Safwan wallahi zsncan da Safna tayi yayi dai-dai da ra'ayina maitafada zancan hada Auran Zainab da Safwan gaskiya inaga hakan za'ayi to Safwan kaji Abba taya zaku biyewa zancan Safna wadda batasan inda yake mata ciwoba nigaskiya bantashi Aure yanzuba yama tashi yayi tafiyarsa Umma tace Abban Safwan anya yaronnan lafiyarsa kuwa shi sam bayasan zancan Aure kaduba kagani Salim yayi Auransa harda 'ya shiko sha'awar hakan sam bayayi gaskiya abin yafara bani tsoro karki damu Hajiya indai Aure zaiyi lokacine kawai baiyiba to Allah yakawo lokacin da alkhairi Amin ya Allah Safwan yanatashi dakinsu Zainab ya'isa yasami Zainab tana waya Safna kuma tana azaune yamata wani irin kallo shiba hararaba shiba murmushiba maiyasa zakiyimin haka yaya Safwan maikuma nayi miye nacewa ahade Auran Zainab dani gashican Umma sai zancan takeyi bayan kinsan nafada maku Wanda nakeso bayanzu zatayi Aureba ko kinasan narasatane a'a banaso to maiyasa kikafada dan Allah kayi hakuri yayana nima wallahi bansan ya'akai nafadi hakanba sai zuwa wannan lokacin Zainab takarasa wayarta gaskiya Safna maganarki tayi yawa shiyasa harkike fadar magana batare da kinsaniba haba Aunty Zainab amaimakon kibashi hakuri sai kuma kiyi kokarin tinzirashi karka damu yayana domin inada tabbacin Umma da Abba bazasu yima dolaba to Allah shine masani yajima suna fira sai karfe :1100pm yayi masu sallama yatafi Zainab takalli Safna gaskiya kirage yawan magana zanyi kokarin hakan insha Allah

Washe gari karfe 12:00pm tashiga school tana shiga class Asma'u tace sai yanzu toko namakarane harjin dadin tambaya kike bayan kina da amsar ina Hafsat ne tafita itada Bashir inakuma sukaje sunje gurin Malan mannir ne kardai haryanzu baibasu test dinsuba eh to miye suke wani binsa yana wulakantasu surabu dashi mana yaci yahada da ruwa idan yaga dama toya zasuyi tinda suna da bukata da'ita Asma'u tashi muje mudubasu suna kokarin fitane suka shigo a Safna kinshigo eh aina tambayi Asma'u Ku tacemin kuna gurin Malan mannir nace wai maiyasa bazuhakura da test dinba ko dolane saikun karba ni wallahi banasan harkar Rashin mutunci aidai komai yanzu yagama wucewa tinda yabamu wai mutum bakiwaba Yayi kokarin wulakanta mutane

By. Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:49] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
Part 2
1⃣9⃣
By

Fauziya Usman

Tobayaga yanada oder aizaiyi koma miye kunga yanzudai mumanta dashi dan karya rikita mana lissafi kokuwa hakane Asma'u 04:00pm suka tashi kaitsaye gidan Hajiya tanufa ta'iso tasami kofar arufe tashiga buga kofar takoma daga gefe tayi tsaye kafin azo abude mata wayarta tadau ruri taduba taga Zainab tadaga hellow Safna kina inane dan Allah kizo da sauri inasan ganinki domin nazo school bansamekiba Aunty Zainab lafiya bari idan kinzo kyagani to ganinan zuwa bayanda ta'iya dole tashiga mota tafice bata karasa wucewaba Hajiya tafito saidai ita batagantaba tafice abinta towaye yazo kuma yatafi yarsa koyagaji da jiyane amma naga motar kamarta Zainab amma kuma Zainab aibazatazo kuma tayi tafiyartaba koda sauri take dole zata jirani nafito to Allah shiyasan koma waye takuma ciki Safna tashigo bako sallama tace Umma ina Aunty Zainab lafiya bakomai tana sama da sauri ta"isa dakin tana Shiva tasameta tareda Asiya da Murja sunata firarsu tayi wani dogon numfashi da sauri suka dubeta tace Aunty Zainab lafiya maikika gani kiranda kikaiminne yatayarmin da hankali to kinga kwantar da hankalinki lafiya qlau sai lokacin tazauna tare da gaisawa dasu Asiya Safna ya school lafiya qlau yahidima Alhamdulillah yauwa Safna dama Asiya ce zaki nunawa gidan da akeyimaki lalle gobe takesan taje aimata haba Aunty Zainab maiyasa kikaimin haka maikuma naimaki gaskiya yanda kikakirani abin yadaga hankalina alokacin ina gidan Hajiya kiceyau kinga Hajiya tokinbarni naganta inakofar gidan nabuga mata kofa kika kirani ayya yihakuri kinji toyanzu zamutafi kokuwa kubari nayi sallah taje tayi sallah tadawo tomutafi bakifaci abinciba a'a basainaciba saboda banajin yunwa kinga Zainab kice tafaracin abinci mana karki damu Asiya domin bazataciba yanzu kutashi mutafi sunfito sunfadama Umma inda zasu sannan suka tafi

Hafiz bayan yabar gidansu Zainab daya koma gida yasanar da mamarsa cewa shifa yasami matar Aure nanyashiga bata labari saida yakai karshen aya tayi murmushi hafiz kenan to ai Abbanka yananan siyakamata kafadamawa domin shizaije baniba to mama dankirashi to shikenan taje sundawo tare hafiz kadawo eh Abba mamarka tafadamin kana nemana eh Abba togani Allah yasa lafiya dama sai yayi shiru yakalli mamarsa mama kifada masa mana aukai bazaka fadaba saini kunyarsa kakeji nice bakajin kunyata a'a mama bahaka bane waimai yake cewa afadaminne tayi dariya waiyasami yarinyar dayakesan ya Aura kuma yanasan aje gobe-gobe ayiwa iyayenta magana to kafaji Abbansa yayi murmushi to Alhamdulillah hafiz wannan ai abin murna ne agurinmu kuma in Allah yayarda kamar yanda kadafa gobe zanje dominyin magana da iyayenta yayi murmushi yauwa Abbana godiya nake haka kuwa akayi bayan fitarsu Zainab Abba yadawo yasami gidan tsit daga Hajiya sai Ammar yashigo yazauna Ammar yayi masa sannu da zuwa yakalli Umma yace Hajiya yanaganku kubiyu inasauran yaran yanzunnan suka fita zasukai Asiya gidan lalle takawo masa ruwa yana cikin sha aka buga kofa Ammar yaje yabude yadawo yace Abba Habu ne to kace yashigo Hajiya zancan tafiyarmu gobene gobe kuma Abban Safwan eh saiki kasance acikin shiri to Allah yakaimu Amin Amnar yadawo tare da Habu Abba yace Haba ya'akaine Alhaji kayi bakine baki kuma eh tokace ina zuwa ya'amsa dato yatafi bajimawa Abba yafito yasamesu su uku yabasu hannu sungaisa to bismillah yakaisu masauki Alh Sani mahaifin Hafiz yayiwa Abba bayanin komai Abba yajidadi sosai yace to bakomai tinda yara sunasan junansu aishikenan musaidai muyi masu fatan alkhairi Alh abubakar idan badamuwa munasan ayanka mana sadaki to wannan bazai yuwu nayanke hukunci nidayaba duk dacewa 'yatace amma inabukatar shawarar yan uwana dan haka kubari idan munyanka kudin saimusanar maku kamar zuwa yaushe toyanzuni gobe zanyi tafiya zuwa Ummura saidai bazanjimaba sati biyu zanyi kuyi hakuri zuwa lokacin sai muyi magana to Allah yakaimu lokacin yadawo daku lafiya Amin nagode bayan sunkarasa abinda yakawosu sunyi sallama suntafi Abba yadawo ciki yafadama Umma tofa lallai wannan yaron dagaske yake to Allah yashigemana gaba Allah kuma yasanya alkhairi Amin Safwan yadawo yasami falo bakowa yanufi dakinsa yafada kangado ga alama agajiye yake to wadannan yaran ina suka tafi yaciro wayarsa yashiga danna number Safna ringing biyu tadaga yayana kuna ina muna kusa da gida ina kukaje munfita tare dasu Aunty Asiya ne munkaisu gidan lalle amma yanzu gamunan kusa da gida ok ssikun karaso to yayana ya'ajiye wayar Koda suka iso sunsami su Abba suna fira lah Abba kadawo eh sannunku D's zuwa Zainab kirjin biki tayi dariya Abba aidan yana bikin Asiya ne shiyasa nida ita munzama abu daya gaskiya kam hakane aikema kinkusa kizama Amarya nanda lokaci kadan da gaske Abba insha Allah Safna to Allah yanuna mana Amin Abba wai ina Yaya Safwan ne baidawoba a'a Umma yadawo domin naga motarsa to mebi yana dakinsa tomai yakeyi adaki waya sani bandama kinfada wayasan yadawo kaga Ammar jekayo kiransa kaji kacemasa yafito muyi fira to Aunty Safna Abba yakalleta tofa Safna yaukuma Ammar kike aike Abban Safwan kamanta Safna yaubatajin shiga dakin nasa shiyasa Ammar yasami Safwan yanata dannar waya yayi sallama Safwan ya'amsa masa Ammar ya'akaine dama Aunty Safna ce race waikazo sundawone eh

By. Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:50] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
Part 2
2⃣0⃣
By

Fauziya Usman

Tinyaushe ba'ajima sosaiba to kaje kafada mata nace bazanzoba sannan kuma tazo inakiranta yanzunnan kanajina eh tomaza kaje ya'amsa dato yafito yazo yana murmushi Zainab tace Ammar murmushinme kake yaya Safwan ne ya'aikoni gurin Aunty Safna maiyace haka yace wai nafada maki bazaizoba sannan kije yana kiranki yanzunnan Ammar sanda yake fadar maganarsa yakaga yanayin fuskarsa gaskiya fuskarsa adaure take tace waiyoni Allah na nashiga uku aike kikajawa kanki saiki tashi kije haba Aunty Zainab kidena fadar haka mana kinga Aunty Zainab dan Allah muje kirakani kinji bazaniba Safna na'am abba tashi kije abba fada zaiman kiyace narainashi karkiji tsoro kinji tashi kije to Abba tatashi da Zainab da Ammar sai dariya suke mata Umma kinafa ganin sunayimin dariya yitafiyarki kirabu dasu tatafi tatura kofa tashiga jikinta duk asanyaye batare daya dago kai yakalletaba yake magana saiyanzu kikaga damar zuwa a'a tinyaushe nace kizo kobai fada makiba yafadamin sai lokacin yadago kansa sukayi ido biyu yaganta tsaye ajikin kofa jikinta asanyaye to tsayuwarme kikeyi anan karaso mana tazo tazauna akasa taso kihau kujera ta girgiza kai alamar a'a to shikenan barani nadawo akasa yadawo kusa da ita yazauna yaga yanayinta duk sai ahankali yakira sunanta Safna lafiya kike kuwa lafiya qlau nake kifadamin gaskiya maiyake damunki bakomai tanaji maiyasa da kuka dawo bakizo kinfadaminba saidai kika turomin Amnar
[12/19/2017, 11:50] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
Part 2
2⃣1⃣
By

Fauziya Usman

Ammar wai yakirani kamar wani kaninki dan Allah kayi hakuri yaya Safwan bazan karaba to shikenan yawuce ina Zainab tana falo su Abba suna falone eh to tashi muje sunfito yace Abba sannu da zuwa Umma ina wuni lafiya qlau kadawo eh yaushe kadawo nadawo bajimawa sosai su Safna suka dawo koda nadawo bakowa afalo kuma agajiye nake shiyasa nanufi dakina nadan kwanta to Allah yahutarda gajiya Amin dama inasan nasanar dakai iyayan Hafiz sunzo harsunyi batun ayanka masu sadaki saidai nace subari sainadawo daga tafiyarmu Umura Abba har lokacin tafiyar yayine eh to Allah yasa ayi a'sa'a Zainab Allah yasanya alkhairi gaskiya ina farin ciki sosai Aunty Zainab ashe kinkusa zama Amarya gaskiya zamusha biki agidannan ko Ammar eh Aunty Safna to Allah yakaimu Amin Umma Zainab duk kunya takamata tarashi tayi tafiyarta saidai zuciyarta cike take da farin ciki sabida tanasan Hafiz sosai tana kwance farin ciki duk yakamata taji wayarta tana ringing tana dubawa taga sunan Hafiz tadaga tare da yin sallama ya'amsa barka da warhaka sanyin idaniyata yauwa yakake inafatar kana lafiya lafiyata tana tare dataki idan harkin kasance cikin koshin lafiya tonima haka Hafiz kalamanka suna rikita zuciyata harkasa naji nasaka fadar komai Zainab kenan aini tini zuciyata tariga tamutu da kaunarki tashiga wani yanayi narashin jindadi tashiga halin kakanijayi domin kuwa takasa samun sassauci ko mafita hasalima akoda yaushe sai harzikani take akanki nakasa samun sassauci koda kankani farin cikina akoyaushe nakasance atare dake saboda kunnuwana basa bukatarjin zantukan kowa sainaki saboda kekadai nakeso kuma kece Wanda zuciyata tayarda da ita takuma zabamin amatsayin matar da zan Aura inasan kikasance uwar 'ya'yana dafatan kema kina farin ciki da hakan tayi dogon numfashi tare da ajiyar zuciya cikin kasa-kasa da murya take maganarta Hafiz wallahi kaidaya nakeso bantaba san wani namijiba face kai kuma kaidaya zanso harkarshen rayuwata nayarda dakai nakuma amince da Auranka domin ina farin ciki sossi da samunka sunjima suna firarsu irin tamasoya daga bisani sukayiwa juna sallama

Washe gari dasafe su Abba bayan sunyi break fast suka kama hanyar tafiya filin jirgi domin tafiya munrakasu harsuka tashi sannan suka dawo gida karfe 11:00am Zainab tafito tana tambayar Safna yau tanada school eh da yaushe 12:00pm to 04:00pm to shine kuma kike zaune haryanzu bazaki tashi kije kishiryaba aiyanzu nake tinanin natashi todayadaifi to dayaushe zaki tafi kamun Asiya kinsan karfe 03:00pm akasa amma dole za'akai 04:00pm sabida ayi sallah kafin atafi insha Allah inadawowa zanshirya natafi toshikenan Aunty Zainab kitafi da mota idan natashi tafiya sai yayana yakaini aikuwa kinkyautamin sosai idan yaya Safwan yafito kifada masa natafi nashiga dakinsa nasamu yana toilet toshikenan zansanar masa natafi Allah yakiyaye adawo lafiya saina shigo dahaka suka rabu tafita tayi tafiyarta itakuma tayi kwance akan kujera tana chart dinta Safwan yafito yasameta tanata chart dinta taji tafiyarsa tadago kanta sama sunyi ido biyu lokaci daya sukayiwa juna murmushi tatashi zaune sai wani kallon juna suke yazauna sanye yake da kananan kaya shigar tayi matukaryi masa kyau sosai barka da fitowa yayana yauwa sannunki da hutawa tayi ajiyar zuciya tana maicewa tsarki yatabbata ga Ubangijin da yahalitta wannan kyakkyawan saurayin kuma yasashi yakasance yayana yaya Safwan wallahi Allah kyanka yayi yawa waikaganka kuwa barama nafadama wani Abu Wanda yafi wannan wallahi yayana kallonka yana tattare da nishadi shiyasa sam bana gajiya da kallonka domin idan inakallonka farin ciki Danishadi suke kamani harnamanta da wani abu bakin ciki ko damuwa wannan kwalliyar dakayi haka sai ina ko gurin Aunty Baby zaka tinda tafara magana yake kallonta yayinda fuskarsa take aman murmushi yayi shiru baice da'ita komaiba banda kallonta ba abinda yakeyi yaya Safwan kayin magana mana yauwa yaya Safwan intambayeka wani abu zakafadamin yadaga mata kai alamar eh yayana bakai nakesan kadagaminba magana nakesan kayimin yayi ajiyar zuciya to bismillah inasauraranki yauwa kokaifa yaya Safwan waimai yasa idan inayima zancan Aunty Baby ssikayimin shiru baka magana abin mamaki kuma saikayita kallona kobakasan nasantane gaba daya bakayimin zancsnta nikuma idan nama sai kayimin shiru kodai ba'cancanci nasanta bane nifa zuciyata tafara fadamin cewa bakwatare da sauri yazaro ido dan Allah kidena fadar haka aibazan Iya rayuwa ba Baby ba domin ita duniya tace soyayyarta kuma numfashinace tinaninta kuma ruhinane ganinta shine nawa samunta shinake fata rayuwa da ita shine cikar burina banajin zan'iya rayuwa idan har bansametaba koda narayu to inada tabbacin bazsntaba rayuwa maidadiba itace dukkannin wani farin ciki nawa dan haka kidena fadar haka kinji kanwata takallesa tare da girgizs kai to shikenan nadena inama fatan samunta domin inassn karayu cikin farin ciki Allah ya albarkaci soyayyarku yasa Aure yazama alkhairi atsakaninku tana cikin magana wayarta tadau ruri taduba taga sunan Bashir tadaga takara akunne yamata sallama ta'amsa bayan sungaisa yace Safna lafiya bakishigo school ba haryanzu bakomai Bashir yau inadan wani abune bazansami shigowaba saizuwa gobe insha Allah to Allah yakaimu Amin sunyi sallama ta ajiye wayar taga harzu wannan lokacin kallonta yake tass hannunta tarufe masa fuska yasa hannunsa yana kokarin janye hunnunta tasa dayan hannunta tarufe masa fukar gaba daya yanasanyin magana hannunta yahanashi yadan ciji hannunta da sauri tajanye hannayenta taturo baki tana fishi shikuma sai dariyarta yake

By. Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:50] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
Part 2
2⃣2⃣
By

Fauziya Usman
Yaya Safwan maiyasa kacijeni abinda yasa kika rufemin fuska tomaiyasa kakeyimin dariya saboda yanda naga lokaci daya kinjanye hannayanki tatashi zata tafi yariko hannunta inzaki tayi shiru kina fishi dani danna ciji hannunki ko to kiyi hakuri nidawasa nayi idan kuma bazaki hakuraba saina baki nawa hannu kirama amma kafin nan kizauna tazauna tana murmushi tadubi hannun da yaciza tagirgiza kai maikike dubawa inda kaciza kawo nagani gashi yarika hannun yana dan murzawa ahankali lokaci daya yaji wani irin farin ciki yakamata tadan lumshe ido kamar mai barci yalura da yanayinta saidai baice da ita komaiba haka tarikajin wani abu yanayimata yawo ajiki farin ciki yakamata ahankali tajanye hannunta yakalleta akwai zafine a'a to maiyasa kika janye hannunki daga hannuna tagirgiza masa kai yayana kenan alokacin da kake murza hannuna nashiga wani yanayine Wanda idan har nabarka kaci gaba da murzawa to tabbas bazan'iya hakuraba wannan shine yaya Safwan nakasa gane dalilin dayasa duk abinda kayimin nakejin dadinsa kuma nake shiga farin ciki yayi murmushi Safna maiyasa baki shiga school ba yau bakomai a'a kifadamin gaskiya to saboda kaine nikuma eh tadaga masa kai kamarya saboda ni saboda yau kace bazaka office ba shiyasa natsaya domin natayaka fira to godiya nake a'a aikafi karfin haka sunjima suna firarsu karfe 01:00pm Ammar yadawo

Please Login or Register in order to submit comment