Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuna cikin mota ina zaku ne"
"Zamuje Honeymoon"
"Ho..ney..moon "
"Eh ".
" To babbar magana "
"Tunda kukayi aure bakuje ba sai yanzu "
Ashe maganar da take ta fito a fili
"Maganar ki haka taki Mom lokacin munyi aurene Don Karata daga Sadiq yanzu kuma muna son junan mu"
"Ah lalai Baby Baka da kunya to Allah ya tsare Hanya " ta tsinke wayan
Kallon Sa tayi shine bazaka gaya man inda zamuje ba na hada kaya na kada ki damu ae nasaka maki idan ma basuye maki ba sai ki saya a can"
"ohk"
"Private flat suka shiga"
"Baby tsoro nakije ".
" idan ina tare dake ki dai najin tsoro kinji "
Rungumeshi tayi sosai har suka isa Singapore........
Da saukan su suka kama daki wanka sukayi "Baby muje muga gari ko"
Murmushi tayi "Thanks"
Hanun Sa ya daura kan lips inta "kar in saki ji"
Ya jata suka fita sunyi yawo sosai domin Haneefa taga abunda bata taba gani a rayuwan ta ba kuma taji dadi sosai da Haneef ya kawo ta Singapore koma wa sukayi dakin sun daga missalin karfe 8:30pm yayi wanka ya fito daure da towel ita ma ta shiga ta fito daure da towel "wai haryanzu Baka saka kaya ba "
"Eh ki naki jira ya mak'ile mata ido ".
" Cream ta dauko ta zaunar da shi nasan ko shi Baka shafa".
"Ina kuwa zan shafa ina tare da ke ae kema kinsan aikin ki".
" Shafa masa tayi to nima sai ka shafa min"
Ya amsa ya fara shafa mata ".
" Cewa nayi fa ka shafa min ba cewa nayi ka kama shafan min jiki ba "
Murmushi yayi "ae naga wanan jikin Nawa ne ko kuma na biya Sadaki don haka yau sai an bani kaya na " gaban ta ya fadi tashi yayi ya dauko mata wata Riga Read "kin tuna wanan Riga"
Tunani ta tsaya yi
"Eh nagane wada kace matar ka ka saya ma har na saka ta"
"Eh ita yau ita zaki saka tunda kice Matar".
" murmushi tayi ae sai ka taya ni saka wa ko"
"Why Not jikin Sa har rawa ya kai ya saka mata Bra sa'anan ya saka mata Riga sakin gashin ta yayi ba k'aramin kyau tayi ba ba'a magana"
"Babynah kinga yanda kikayi kyau kuwa " wayan shi ya dauko yayi mata photo kuma sukayi tare "Gaskiya ba k'aramen kyau kika yi ba ya kama yau ki samu *Habib*
" Habib kuma"
"Eh manah Ne Haneef ki Haneefa Shi kuma Habib kinga duk sunan mu da *H* yake fara wa"
"Hakane ama ba ko yau ba"
Jawota yayi har suna jin nunfashin juna "Ba yau za'ayi Me ba"
"Ba yau za'a same Habib ba"
murmushi yayi "Yau kam in ba yau ba to za'a kara ya dawo da *Habib da Hafsat*
Zaro ido tayi " Aa nikam ina tsoron Haihuw fa"
"Ki kwantar da Hankalin ki ae ina tare dake" to Kawai tace masa


Ba abunda zamuce sai Alhmdl A yau ne Haneef da Haneefa suka cika ma'aurata ba'a cewa kome sai dai Allah ya bada zaman lafiya

Tunda safe suka tashi suka yi wanka suka fita
"Baby ina son kamin mu koma nayi ma da su Mom Albishir mai dadi"
"Kamar na me kinan kina da ciki manah"
Murmushi tayi to Allah k'asa yace Ameen

Wasa wasa yau satin su Ukku a Singapore ba inda basu xagaya ba kullum suna video call da Mom da Mama kwance take bisan jikin Haneef "Baby ina son turaren nan Naka sosai shiyasa a kullum nafi son in kwanta a jikin ka "
"Baby kinan to ae ni nakine duk yanda kike so haka za'ayi "

Yanzu dai ki tashi ki muce abinci tashi sukayi ya zauna ta zauna kan cinyan Sa yau me aka dafa mana"..


"Abunda kika fi so pizza nayi ordering inta naga tunda munka zo kin fi sonta "

"Sosai kuwa Thanks tayi masa kiss " har sauri ta kai ta ci yana Sa mata a baki taji ba dadi kamar abunda yayi shekara Hudu aje da saure ta tashe ta shiga toilet amai ta kamayi Haneef ya Mara mata baya yana ye mata sanu
"Lafiya baby"
"Pizza naji ba dadi kamar ta dade ajiye"
"Wannan ae sabuwa ce muje naci najiya "
Janta yayi ya ci k'adan "ni banji wata matsalar Sa ba "

Da gudu ta tashi ta saki kwara wani Amai "sannu "
"Yauwa ko Warin ta bana son jin "
Daukan ta yayi ya azata kan gado ya dauki pizza ya saka ta a shara " Sannu baby na bare na kira Dr."

"Aa kada ka damu lafiya ta k'alau"
"Shh bana son gardama " kiran Dr.yayi ya Sanar da shi bada jima wa ba sai gata ta iso"
"Dr. Ki duba man ita tin dazu take amai "
"Ohk"
Tayi dubi Dubin ta shikuwa duk Hankalinsa ya tashi sosai
"Dr. Lafiya naga sai murmushi ki kai gani cikin wani hali meki damun ta???

" Congrat matar ka tana da juna biyu"
Rike cewa yayi ya na nuna Haneef "Ciki Dr."
"Eh Don haka ka kulla da ita sosai "
"Insha Allah Dr.nagode sosai".
Hanu yasa cikin Aljihu bai kosan Nawa ne ba ya dam ka mata godiya tayi sa'anan ta wuce

K'arasawa yayi gunta " baby da gaske you are pregnant "
Rufe fuska tayi" Eh"

Ba karamen dadi yaji ba ya rungumeta tare dayi mata kiss waya ya dauka yakira Mom ya gaya mata ba k'aramin dadi taji ba zata ga yan jikokin ta •••••••


*muje zuwa*
🚴🏻‍♀🚴🏻‍♀🚴🏻‍♀🚴🏻‍♀🚴🏻‍♀🚴🏻‍♀
*Lipton and pure*✍🏻






🧚🏻‍♀🧚🏻‍♀🧚🏻‍♀🧚🏻‍♀🧚🏻‍♀🧚🏻‍♀
🧚🏻‍♀🧚🏻‍♀🧚🏻‍♀🧚🏻‍♀🧚🏻‍♀
🧚🏻‍♀🧚🏻‍♀🧚🏻‍♀🧚🏻‍♀
🧚🏻‍♀🧚🏻‍♀
🧚🏻‍♀
AྂUྂRྂEྂNྂ BྂAྂZྂAྂTྂAྂ
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀

LྂAྂBྂAྂRྂEྂNྂ HྂAྂNྂEྂEྂFྂAྂ DྂAྂ HྂAྂNྂEྂEྂFྂ🙆🏻‍♀

W̥ͦR̥ͦI̥ͦT̥ͦI̥ͦNͦG̥̥ͦͦ B̥ͦY̥ͦ K̥ͦH̥ͦḀͦD̥ͦI̥ͦJ̥ͦḀͦ S̥ͦ D̥ͦO̥ͦG̥ͦḀͦR̥ͦḀͦI̥ͦ(L̥ͦI̥ͦP̥ͦT̥ͦO̥ͦͦN̥ͦ)✍🏻

S̥ͦT̥ͦO̥ͦR̥ͦY̥ͦ B̥ͦY̥ͦ H̥ͦḀͦF̥ͦS̥ͦḀͦT̥ͦ M̥ͦU̥ͦH̥ͦḀͦM̥ͦM̥ͦḀͦD̥ͦ (P̥ͦU̥ͦR̥ͦE̥ͦ)✍🏻


​​®🔥E͎L͎O͎Q͎U͎E͎N͎C͎E͎ W͎R͎I͎T͎E͎R͎S͎ A͎S͎S͎O͎🔥​​
________________________________________
Email: eloquencewriter@gmail.com
Facebook: https://mobile.facebook.com/Eloquence-Writers-Association-272714726630585/?5ref_component=mbasic_bookmark&ref_page=XMenuController&ref=opera_speed_dia

*Page 50*



Shirye shiryen koma wa gida sukeyi gobe zasu bi jirgin farko

"Baby ina son kamin mu wuce mu Dan je mu shakata kuma ina son shan ice cream"

"Angama yanzu nan ki shirya ma muje murmushi tayi baby kana ji da babyn nan Naka"
"Ba baby ka dai ba har da mom in su"
Ya kyala mata ido daya "bari na shirya ko"
"Ohk"
Bada jimawa ba ta shirya fitowa sukayi ya rike Hannunta har su ka kai bakin Mota bude mata k'ofa yayi shima ya zagayo ya shiga ya rungumeta Sai driver dake Jan su dayake ya gaya mashi inda zasuje
Dai dai gurin shan ice cream suka tsaya suka shiga fara sha sukayi suna ta firan su abun sha'awa shafa masa ice cream tayi a fuska kallon ta yayi wayace ki shafa man shi ya zaro mata ido
"Kana tunanin zanji tsoron wanan idon Naka " ta aza masa dariya
"Eh manah"
Tasowa tayi ta zauna kan k'afarsa harshen ta tasa ta shanye Wanda ta shafa masa"
Kallon ta yayi yaga mutanen dake zaune wurin sai kallon su a kai
"Baby ana kallon mu fa"
Juyowa tayi ta kallesu "so what ai kai mijina ne ba wani ba don haka ba ruwana da su"
Sakin baki yayi yana kallon ta ita da Tafi kowa kunya yau ita ke ce wa hakan
Daukan spoon tayi ta ba shi shima ya bata tashi sukayi suka wuce Rike yake da hanunta ya bude mota mota zata shiga Kawai wata mata ta shiko da gudu ta bangaje Haneefa da Haneef bai yi saurin rike ta ba da ta fadi
"Sannu baby baki jemu ba dai ko???
" k baki da Hankalin ne zaki kashe man mata ne eh ko bakijin ana yi maki magana ne"
Ita kuwa wannan matar ko kallonsa bata yi ba tana can tana kallon bayan
Jawota yayi da karfi "baki da Hankalin ne ne" ya daga hanu ya mareta tsaya wa yaye cak kamar Wanda aka tsaida wuri daya
Bakin sa har rawa yakeyi ya ce "Balkisu kece???
Sai a lokacin ta dago ta kalle Sa
" Haneef daman kana duniyar nan"
Da karfi wani mutum ya jawo Balkisu ya wanka mata mari "Don Uban ki ni zakiyi wa sata"
"Sata Haneef ya furta"
"Mallam me ta sace maka ne"??
" nafidda kudi zan sayi abinci shine ta kwashe ta wazgo da gudu"
"Balkisu meyasa zakiyi sata ina iyayen ki ne kuma meki kiye a garin nan"
"Idan baki bani kudi na ba sai na yanke ki"
"Mallam Dan Allah rika " ya saka hanunsa a aljihu bai masan nawa ne ba ya bashi
"Kinyi sa'a wlh ya ceceki" ya Tafiyan Sa
"Magana nakiyi maki"
"Bayan tafiyan ka na rasa Wanda zai aure ni na shiga yawon karuwanci har na dauki ciki Baba naganewa ya koreni yace ba zan ja masa abun kunya ba a gida shi ne dalilin da ya Kore ni daga gida har ka ganin ne wanan gari naci abinci ma gagarana yake yanzu haka kwana ukku banci abinci ba"
Subuhalilah Haneefa ta furta
Juyowa tayi ta kalleta "wanan kuma wacece "?
" matar da na aura ce "
"Allah sarki Allah ya Baku zaman lafiya"
Ta k'arasa gurin ta ki roka min yafiya a gurin Sa baiwar Allah duk da nasan baki sani ba ".
Murmushi tayi " nikuwa na sanki"
"Kuma kada ki damu indai baby na zai yafi maki"
Kallon ta yayi "baby muje kada mu rasa flight in mu"
K'arasowa tayi kusa garisa ta reki hanunsa "Haba sweetyna ka yafi mata manah"
"Na yafi mata Happy"
"So Happy kuwa thanks" tayi masa kiss
"Zamu iya Tafiya???
" Haba baby ya zamuje mu barta cikin wanan halin mu tai maka mata manah"
"Sam wanan abun ba zai yuwu ba"
"Baby daman akwai abunda zan tambaye ka naki samu".
" Bazaki gane bane taimakon ta dai kk son ayi ko "
"Eh"
"Mota ya bude ya dauko cherk ya rubuta 1million inaga 1million zai isheta duk wani Abu da zatayi idan kinyi tunani ki sayi abunda zai amfaneki in kuma yawon ki zakiyi suka k'are ke kika sani"ya mika mata

Har k'asa ta kai tana zambada godiya haka ma tayi ma Haneefa godiya suka shiga mota suka isa Airport jirgi suka shiga ba wani dadewa ba suka isa
*BAYAN WATA TARA*
"Haneef ne k kai da kawo yana jiran ace an haifu Hankalin shi ba k'aramin tashi yayi ba har dai idan ya tuno da cewa Haneefar Sa tace tana tsoron Haihuwa su Mom ne da Mama suka iso har yanzu daga masu kai yayi don baya ma son magana kai da kawo Kawai yakeyi Mom ce ta k'arasa wurin Sa
" Son kada kadamu ba abunda zai sameta insha Allah kayi mata Adu'a kawai kaji"
"Ohk Mom".
" tun yaushe kuke nan".
"Munyi 30mnt yanzu"
"To fa Allah ya jisuwa lafiya "
Haneefa kuwa tana can cikin labour Room duk tayi zufa ga Marata tanayi mata wani Irin ciwo kuma har yanzu bata haihu ba gado ta rike da kyar ya kira Nurse karasuwa tayi
"Zan iya ganin mijina??
" sorry ma'am ba'a barin namiji ya shigo"
"Dan Allah ki kira min shi idan na mutu fa bangan Sa ba ki kira min shi kamin rai na ya baci".

Ba yanda ta iya ta fita ta kira mata shi don idan ta ta da Hankalin ta zata iya bleeding fitowa tayi da sauri Haneef ya k'araso wurin ta Lafiya nurse "
"Lafiya qlw matar ka nason ganin ka muje dakin can ka canza kaya "
"Ohk jikin Sa na rawa ya bita daga baya".
Da kin da Haneefa ta ki ciki nan suka shigo yana shigowa ta Mika masa Hanu da sauri ya rika Mata Hanu
" Sanu Allah ya jishe ki lafiya "
Da kyar tace Ameen "Baby ciwo zan mutu"
Dora mata Hanu yayi kan lips inta ba abunda zai samiki insha Allah bazaki mutu ki barni ba sai dai muje tare"
Rike shi tayi gam....
"Sannu fa"
Ga badaya ya rasa ma mezai yi mata ga zufan datakeyi da karfi ta mike wayooo Allah na
"Baby sanu"
Girgiza kai tayi "baby I can't"
Shhhhhh ya Dora bakinsan akan nata yana yi mata slow kiss sai jin sukayi kukan jariri duk da hakan bai dai na abunda ya kai ba sai ga kukan wani jariri dauka diyan akayi aka gyarasu su na nan suna kiss sundai ji kukan jariri amma basu San nasu bane jin Kawai sukayi ance Congrat Kun samu yan biyu da sauri ya juyo ya gansu yan biyu ka Sa boye farincikin Sa yayi
"Baby duba abunda kika Haifa yan biyu ne". Ya amshe su ya rike mace ita kuwa ya bata namiji murmushi Kawai Haneef takeyi Alhmdl Allah nagode maka
Kiss yayi mata a goshi Thanks
"Sir zaka iya fita zamu gyara ta "
"Ohk ohk"
Ya amshe namije ya reki su fitowa yayi da su da sauri su Mom suka taso
"Alhmdl masha Allah Allah yayi maku Albarka". Haneef kuwa sai murmushi yakai mom ce tace ba za'a bani jikoki na Nagani ba sai a lokacin ya tuna bai basu ba sa'a nan ya Meka masu daya daya

Ita kuwa Haneefa aka gyara ta aka k'ara mata ruwa aka sallamesu fitowa sukayi zasu shiga Mota Haneefa ta nufa wurin Motar Haneef mama ce tace mata " ina zaki can kin manta haihuwar farin ce a gida zakiyi ta ".
Kallon Haneef tayi ta marai raice fuska
" Mama Dan Allah Dan Anabi kada ki raba ni da matata 1hour bazan iya yi sai da ita ba ".
Sakin baki tayi tana kallonsa
"Ae dataye Arba'in zan mai da maka abunka kada ka damu".

" no way gaskiya bazan yarda ba a bar min matata tunda ina sonta tana sona kuma za'a raba mu gaskiya sai dai aka wo mata Yar wanka ta rinka yi mata amma ba Inda zata je"
Mama sakin baki tayi tana kallon Sa Jan Hanun Haneefa yayi idan yaran kuke so kowa cen Ku ta dauki daya daya ni kuma Ku bar men matata bai jira amsar su ba ya jata suka wuce ya bar su mama reki da baby
"anya Ko wane Abu bai shiga kan Haneef ba "." To ya muka iya dole mu barta nan gidan Sa sai a dauko Yar wanka "
Ba yanda sunka iya doli suka shiga mota suka wuce da babyn yar wanka aka kai ma haneefa
"Inaa nifa bazan Bari kiyi man wanka gaskiya"
"yar nan ba fa akan ki aka fara ba har iyayen ki ni nayi masu da hanuna"
Haneef ne ya shigo daga dakin "lafiya inna kuke hayaniya??

"wai bazata bari nayi mata wanka "
Kallon ta yayi ta yi marairaice fuska
"Inaa ki jirani a waje"
"to" ta fita
Jawota yayi "meyasa bazaki bari ayi maki ba"
"Haka kawai na bari tayi man wanka"
Jawota toilet ya kai ta yayi mata wanka ya shiryata
Mamaki k'arara a i
don Inaa "diyan zamani sun lalace nikam bazan iya zama a gidan nan ba"
Tana magana tana jinini ta tafiyar ta


Yauce ranar suna diya sunci suna *Hibban &Hafsat* waton Hassan da Hussainah ba abunda zamuce sai Allah ya raya su Haneef da Haneefa kuwa soyaya mai tsanani ta shiga tsakanin su kuma suna ba yayan su kullawa sosai
*ĄɭЂⱮDɭ Ą YĄŲŊĘ ŊĄ ĶĄWo ĶĄŖĄЂĘŊ wannan ɭĮŢŢĄƑĮ WĄŢOŊ ĄŲŖĘŊ ƁĄZĄŢĄ ĄɭɭĄЂ ĶĄ YĄƑĮ ⱮĄŊĄ ĶŲŖĘŊ DĄ ⱮŲĶĄYi Ą ÇĮĶĮ*


*DUMBiN GODIYA GA*
*hαвíвα dαчlíght(mч ѕl)*
*zuwαírα íвαrαhím (hσt kíѕѕ(*
*αctíσn вαвч*
*hαlíѕѕα(líѕѕα)*
*αufαmα*
*mαdєєnα*
*вαѕírα ѕαвσ nα dαmα*
*quєєn nєrdч turαkí*
*fαtímα αвαkαr (dαuthєr)*
*вαlkuѕu чαrí*
*fαtímα ѕ dσgαrαí (mч fαvσurítє)*
*ѕummч ѕ d =вαвч gírl)*
*Mrs.Mubarak*
*MZZ DADDY*
*MAMAN HANEEF*
*QUEEN AYUSHA ILIYASU*
*HAFSAT*
*Na'iki*



αℓℓαн уα вαя кαυиα


мυиα мiкα gαιѕυωα gα мυтαиєи ∂αкe иυиα кulαwα α вσσк ∂ιиqи

*ℓιρтσи αи∂ ρυяє иα мєкα gαιѕυωα*😘

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment