Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

perfect, he can stand on the street and shout anty is more than a woman, tunawa yayi da ta fidda miji sai yaji gabanshi ya mugun fadi, bayan kaman hour daya messenger ya shigo da abincin daya sayo masu, sai lokacin ta kalleshi Tana cewa
"Ka dauki daya ka bar min daya .." Tafada mashi Tare da yi mashi one second look ta dauke kanta, ahankali ya Mike not knowing if he can eat Don shi kadai ya San how he's feeling inside inshort ya ji haushi zuwan dayayi because he's getting in to more trouble.

Hajiya Hassana na barin gidanta taje gidan hajiya habiba daman tun asuba tayiwa mijinta karyar hajiya habiba bata da lafiya so she's going to see her, Alhaji Muhammad is not that strict but baya daukan rainin hankali. Humaira hajiya ta Kira ta shigo dakin da suke
"Yanzu kina jina zaki shiga ciki ki shirya zamuje gidan kaka..ki fada mata kinga mami Tana lalata da suhail..kinji kou..." Ahankali humaira ta daga wa mahaifiyar ta Kai,
"Maza ki shirya muna jiranki..." Babu musu ta Mike ta  bar dakin, bayan kaman minti biyar ta dawo, mikewa hajiya habiba da hajiya Hassana sukayi suka fita suka saka humaira cikin mota suka bar gidan suna cikin mota hajiya Hassana tace
"Ki ce zindir kika gansu suna aikata alfasha...kina jina?.." Ta fadawa humaira, ahankali humaira ta daga mata Kai,
"Wallahi rukkaya it's me and you a wannan garin yau...lets see yanda zaayi kaka ta goyi bayanki...shegiya kilibabba..." Tafada out of hatred, you know in life you don't have to be bad to have enemies, kawai your good attitude ma zai jama ka makiya that have opposite character like yours, tunda suke a wannan family na Mai waazi hajiya Hassana bata da burin daya wuce taga hajiya rukkaya suffering for no cause, kawai she hates her with passion because she's so perfect, ko abinci suka Kai gidan Mai waazi loKukan uban me kike..." Tafada cikin matsanacin masifakacin kafin kowa yayi nashi gidan ya tashi sai ance na hajiya rukkaya yafi dadi, hajiya Hassana na iya kawo abinci a bar shi nan amma hajiya rukkaya na kawo nata zaa cinye nan take Ana sati lokacin ba kaka kadai bace duk sauran iyayen mijin suna nan, suna nuna kaunar su ga hajiya rukkaya face to face babu munafurci Sannan har yabbing hajiya Hassana suke poor cooking habit dinta, wannan shine sanadiyar data ji ko kadan bata kaunar hajiya rukkaya Don gani take ita har da asiri ta Kama family din miji, Sannan ita hajiya Hassana bata fito daga babban family kaman na hajiya rukkaya ba, hajiya rukkaya yar gidan manyan mutane sai ya kasance Tana yawa yiwa iyayen mijinta kyauta dukda suma babu abinda suka rasa but they love her gifts so much, duk family din kaka bata da wacce takeso kaman rukkaya. Ita kam hajiya Hassana it hurts her so much that kaka and the rest of the family loves her with passion. But finally she have something to rejoice about shine mami da Allah bai bata miji da wuri ba, kullum it makes her happy if ta tuna dole hajiya rukkaya zata shiga damuwa sabida mami. Rayuwa kenan, Yanzu irin su hajiya Hassana suna da yawa cikin alumma, kawai you don't hurt or hate them but seeing you sad gives them total pleasure. Allah ya raba mu da bakin Hali Amin.

Suna isa gidan kaka suka shiga, kaka dake zaune a falo na ganinsu ta fara balai Tana cewa
"Wallahi in ma Don wannan maganar né munafukai kuka taho Wallahi ku koma...babu dole..." Tafada atakaice, humaira fashewa tayi da kuka as instructed by her mother, kallon banza kaka ta watsa mata Tana cewa
"Wallahi kika koyi halin wannan banzayen iyayen naki na kilibibi kin shiga uku." Ta fada hankalinta kwance, zama hajiyas sukayi kaka ta kalle su Tana cewa
"Wai baku jine?.. Ku bani waje kafin in Kira mazajenku suyi sake ku mu huta da masu bakin Hali....In ba Don tsabagin munafurci ba yara sun nuna basu so.ku kuma dayake kun hada Kai kun like kaman dole.,tou Maza ku bar min gida..." Tafada cikin fada,
"Kaka mu ba wannan ya kawo mu ba...wata magana ce Mai tsananin tashin hankali..." Baki kaka ta bude Tana kallon face dinsu kaman wata police officer,
"Ku fadamin abun tashin hankalin Inji..." Tafada atakaice, Tana Dora kafa daya kan daya, hajiya kallon Humaira tayi tace
"Kiyi shuru ki fada mata Abunda kika gano." Hajiya Hassana ta fada mata.
Ahankali humaira ta goge face dinta Sannan ta fada mata Abunda ya faru which is 98% lies, baki kaka ta bude ta kasa magana sabida danyan labarin da takeji, 
"Inna lillahi wa'ina ilaihi rajiun." Shine Abunda ta fada cikin tsananin tashin hankali, hajiya Hassana da hajiya habiba signaling junan su sukayi suna Mai Jin dadin yanda face din kaka ya sauya alaman maganar ya shige ta,
"Wai kike ce rukkayatu Tana falo kuma?.. Anya dai..gaskiya da wuya in ita kika gani...Don ance wannan Dan tsohuwar Tana aikata hakan babu musu..daman yanda wannan yaron ya zama fitsararre nasan da akwai magana...Kai Inna lillahi wa'ina ilaihi rajiun..." Kaka ta fada Tana kare hajiya rukkaya, hajiya Hassana tabe baki tayi sabida Jin ta kareta
"Wallahi kaka Tana falo...ita tacemin in shiga dakin." Humaira Ta amsa mata cikin kuka dukda she's asked to cry Don kaka ta fi yarda da maganar she wants to cry on her own sabida ko bacci batayi ba sabida tunanin abinda ta gani, kawai tasan suhail na son mami ya yaudareta da yana sonta
"Tou  dai bata San suna hakan ba?.don da ta sani da batace ta shiga ciki ba .." Kaka ta fada masu,
"Tou Nidai na fada maki kar in dauki mataki da Kaina kice na Raina ki...Don haka a bima Dana hakkinshi.?.Ai wannan cin mutuncin yayi yawa..." Hajiya Hassana ta fada, kallon banza kaka tayi mata taja tsoki Sannan ya dauki wayarta ta mikawa Humaira Tana cewa
"Bincikomin lambar yunusa" Ta fada mata, humaira searching lambar tayi tare da dailing Sannan ta mikawa kaka, kafawa kaka tayi a kunne Tana jiran mahaifin mami yayi piçking, yana dauka da sallama ya gaidata amma ko amsawa batayi ba tace
"Inason ganinka da wannan tsohuwar diyar taka Yanzun nan." Tafada atakaice bata jira yayi magana ba ta katse wayar ta. Kara mikawa humaira tayi tace
"Bincikomin lambar Muhammadu..." Ta fada Tana karkada kafa ahankali, kallon mamaki hajiya Hassana tayi mata Sannan tace
"Yo kaka shima sai ya zone...ai nayi tunanin shi ba sai yazo ba?.." Ta fada cikin fargaba, kallon banza kaka ya watsa mata Sannan tace
"Lallai ma..shi dan naki bazaa yi mashi fada ba kenan.shi ba dadin ya sani ba har ya Bari wannan tsohuwar Tana tarayya dashi...ke Dalla fiddo in lambar shi..." Tafada atakaice, humaira fiddo wa tayi ta mika mata, hajiya Hassana sadda Kai kasa tayi Tana fargaban Abunda zai biyo baya Don cewa zaiyi ta tsallakashi ta kawo magana wajen kaka, shima yana piçking kaka, tace
"Ka kawo wannan Mara kunyar Yanzun nan..Ina jira..." Ta fada Sannan ta ajiye wayar. Both side da sukayi receiving wayar kaka sun San da akwai matsala ance in kaji Kira samu né amma Banda kiran kaka,

"Inna lillahi wa'ina ilaihi rajiun..." Mahaifiyar mami ta fada lokacin da kiran yazo, kasancewan suna tare lokacin,
"Alhaji me mami tayi kuma?.. Na shiga uku..." Tafada Tana dafa chest dinta sabida tashin hankali,
"Yanzu wannan yarinyar bata samun kwanciyar hankali kenan?.. Jiya yini kuka tayi and yau kuma nasan dole ba abun arziki bane..." Hajiya rukkaya ta fada kaman zatayi kuka,
"Ya isa haka nan..Bari inje office dinta in dauketa sai mu wuce since its closer..." Alhaji ya fada yana mikewa sai sweating yake sabida one single drop of tears na mami na damunshi amma shi irin matured people masu danne problem dinsu né.
"Alhaj Ai Nima zani..." Ta fada Tana mikewa itama, alhaji baice komai ba ta shiga ciki ta dauko hijab ta saka suka fito sukayi hanyar hospital din mami,

Suhail kam spoon biyar yayi yaji ya koshi da abincin, gefe daya ya tura ya Mike yana cewa
"Anty Bari in tafi gida kar in dameki,,.i will see you tomorrow..." Yafada idonshi kanta,
,"ok..." Ta amsa mashi looking into a file, ahankali ya juya har zai fita tace
"Cutest..." Da sauri ya  juyo kaman he's waiting
"Pls Kayi resuming aiki...kaji..." Ta fada mashi
"Ok anty..I will tomorrow Insha Allah...but it's because of you..." Ya fada mata,
"Nagode...if wata ya kare sai ka bani account number in dinga tura maka wani Abu tunda kaka tace you don't have salary for 3 months..."
"Aa anty.,you don't have to worry about that...if am broke zan fada maki..." Tadaaa cikin sanyinmurya,
"Ok shikenan...thanks for coming..." Tafada kaman he's a patient, idanuwa kawai ya lumshe ya fita tare da rufe mata office din, ko inda motarshi ke tsaye bai Kai ba before yayi receiving call din dad dinshi,
"Inna lillahi wa'ina ilaihi rajiun..." Yafada cikin fargaba.
17💚💛💜💙❤️
Lokacine
💙💜💚💛❤️



® zuwairat (ummumaryam)



1️⃣7️⃣



Free page



Ahankali ya Kai wajen motar shi ya Dora kanshi saboda yanda numfashinshi ke fitowa not normal,
"Kai...mommy..." Yafada ahankali tare da sakin wani irin nishi kaman Mai Jin wani ciwo cikin zuciyar shi, mota ya bude ya shiga yana tunanin Yanzu mummy dinshi yaje gidan kaka ya fada mata abinda bai kamata ya fita ba, wannan ya Kamata duk uwa ta boyewa danta such issues amma shine ta kaita wajen kaka Don ta yayashi da mami, staring ya buga da karfi yana cewa
"Humaira...humaira..Wallahi ranki in ya Kai dubu sai ya baci...gobe in gulma abinyi né sai ki Kara,..." Yafada yana tunanin abinda zaiyiwa humaira muddin hannunshi ya kamata. Ahankali ta tada mota ya bar hospital premises din ya Kama hanyar gidan kaka trying to drive safe saboda yanda gabanshi ke faduwa, kawai ba Wai yana tsoron matsifsr kaka ba, kawai he's afraid kar mami ya Kara fushi dashi, bayan kaman minti sha biyar da suhail ya bar hospital hajiya da alhaji suka Iso hospital din, hajiya kawai ce ta fita ta nufi ciki while alhaji na bayan da driver a gaba yana jiran su fito, sanda hajiya ta shiga office din mami na zaune da wani suna magana, Tana daga Kai taga mahaifiyar ta gabanta yayi mugun faduwa, da sauri ta Mike Tana Dan squeezing face sabida yanda taji wani Abu ya tokare mata zuciya, sai da ta lumshe Ido ta hadiye wani Abu Sannan ta Dan samu sakin face din, mahaifiyar ta na tsaye Tana kallon ta, murmushin karfin Hali ta saki Tana cewa
"Mommy..kece da kanki...lafiya dai .." Tafada maganar  fita daban daban, Sannan tsoro na kwance kan face dinta, murmushi mom dinta ta saki tace
"Dad dinki ke kiranki..." Ta amsa mata, kura mata Ido mami tayi Tana kokarin gano reaction dinta but nothing, kallon patients din tayi mashi magana Sannan ta Kira wani a waya ta fada mashi fita ya kamata ga patient ya dubashi, Tana magana jikinta sai rawa yake sabida tasan it's about yesterday, bag dinta ta dauka ta kalli mum dinta tare dacewa
"Mum Ina zamu?.." Ta tambayeta
"Wai kaka tace a kawo ki...Dan Allah kinyi wani Abu?.." Hajiya ta tambayeta cikin damuwa, ahankali mami ta koma ta zauna tare da dafa goshinta saboda tashin hankali
"Inna lillahi wa'ina ilaihi rajiun...mummy am sorry..." Tafada Tana kokarin fashewa da kuka, da sauri hajiya ta kamata Tana cewa
"Jewel tell me what's the problem...pls tell me..kar ki boyemin komai..." Tafada Tana kallon mami da duk hankalinta ya tashi kaman an bata death warrant, duk duniya bataki ayi mata duk hukuncin da ake so ba amma kar a hada ta da kaka, kaka bata duka amma bakinta yafi dorina zafi da ciwo, duk sanda ta bude baki ta zageta ba Karamin ciwo take samu aziciyar ta ba, gashi Yanzu an hadata daita with such dirty issue,
"Dan Allah jewel tell me..da gani kinsan dalilin kiran.just tell me...am your mother I will never discriminate you." Ta fada atakaice,
"Mummy..it's nothing serious...kawai am so mad at myself da ban bi umarninki ba...gashi it's getting me into trouble.." Ta fada cikin hawaye,
"Ohhh jewel talk pls...your father is waiting...." Hajiya ta fada mata,
"Mummy..jiya...da suhail ya Dora Kai kan kafata..,da kuka fita..shine humaira ta shigo ta ganmu ahaka...sai ta samu negative thoughts...." Tafada giving her hint of what is happening, there's no way da zata fada mata humaira ta kama su almost mouth to mouth, tasan inda humaira bata shigo at the moment data so ba datayi delay na second biyar da kilan sai dai ta tarda su mouth to mouth.
"Kinga mami if I tell you something I know what am saying....yanda kukeyi da suhail nobody will see I think you're not into something...sai Wanda yake tare daku zai gane gaskiyar...now gashi zaa dragging dinki into mud because of this..." Hajiya ta fada mata not feeling too disturbed, mami ajiyan zuciya ta saki saboda yanda mom dinta bata tada hankalinta sosai ba, it really lessen her burdens,
"Mommy am sorry...ni kawai am afraid of me suka fada ma kaka...nasan anyi mani sharri kuma kaka bazatayi bincike ba..." Ta fada mata cikin damuwa,
"Hmmm Ai in hajiya Hassana taji wannan she will make something big out it,,,kawai let's go..keep praying Don nasan it's nothing wrong..." Hajiya ta fada tare da mikewa, ahankali itama mami ta Mike feeling strong, babu abinda take cikn zuciyar sai hasbunallahu waniimal wakil.. Har suka isa gidan kaka, luckily hajiya ma ta fadawa alhaji shima baiga wani Abu cikin issue din ba, suhail kam yaja cikin motarshi suka fito yana kallonsu ya kasa fita, yanda yaga mami yasa ya samu confidence Don she looks so strong, suna shiga gate din kaka shima ya fito ya taka ahankali ya shiga juyowa mami tayi ta kalleshi murmushi ta saki shima ya sakar mata amma he's so afraid, hannu yasa mata a kan lips dinshi alaman she shouldn't say a word, bata amsa mashi ba ta shige falo, mahaifin suhail da sauran yan report né falon sai kaka, alhaji wucewa yayi wajen elder brother dinshi suka gaisa duk alhaji Muhammadu look so angry ganin matarshi zaune, shidai baisan abinda akayi ba amma ganinta makes him so mad, ahankali hajiya tashigo da sallama kaka da alhaji Muhammadu suka amsa, hajiya Hassana binta tayi da harara, gefe daya ta samu ta zauna, itama mami sallama tayi amma babu Wanda ya amsa sai mahaifin suhail, kusa da mom dinta ta zauna
"Watsatsa..." Hajiya Hassana tafada Tana kallon ta, hajiya rukkaya Shafa kan mami tayi ita kuma mami ta sadda Kai kasa Tana wasa da yatsunta, suhail né ya shigo daga karshe ko sallama baiyi ba ya samu waje few inches away from humaira ya zauna yanda zaiji dadin cin uwarta da kyau, ahankali humaira ta matsa away from him, kaka kallon humaira tayi tace
"Ki maimaita Abunda kika ce." Tafada mata, hajiya Hassana kam Sam ba haka taso ba, kawai she was thinking da mami ta shigo kaka zata fara zubar balai kaman yanda ta Saba, humaira daga Kai tayi Sai kuma ta sadda Kai kasa, she can feel suhail temper daga inda take zaune,
"Ke kar ki bata min lokaci...Maza Yanzu ki fadi Abunda kika fada dazun kafin ranki ya mugun baci..." Kaka ta fadawa humaira, cikin rawar murya humaira ta fara cewa
"Jiya ne...nace zanje in bawa yaya hakuri kan abinda nayi mashi ...sai  naje gidansu baya nan..sai mommy tace inje gidansu anty mami kilan yana Chan...sai naje...Ina zuwa na tarda mummy falo da yaya Yazid muka gaisa..sai tace min in shiga dakin yaya Yazid yaya na ciki...sai na Kama hanyar wajen...Ina zuwa....sai naga...naga..?" Sai tayi shuru voice dinta na rawa, suhail kam already ya ware hannu because yasan Mai rabashi humaira yau sai Allah, daman he told her ta fada amma kar ta Bari su hadu, shi kam mahaifin suhail kunnuwa ya bude Don yaji Abunda zatace because baisan labarin ba,
"Ke kar ki bata min lokaci..." Kaka ta dakawa humaira tsawa, cikin rawar jiki da fargaba humaira tace
"Ina zuwa..sai naga..,yaya...da..anty...mami...kwance....babu...komai.jikin..?"  Ai Bata karasa ba taji kaman an dauke mata numfashi sabida saukan Marin dataji a kunnenta, riketa yayi a shoulder ya fara girgiza ta da karfi yana cewa
"Ni zakiwa sharri?.." Suhail ya fada idanuwanshi kaman ba nashi ba, mami kuka ta farayi , while alhaji da Muhammadu da yunusa suka saki salati, hajiya rukkaya ma salati take, kaka kam shuru tayi Tana kallon yanda suhail ke girgiza humaira while hajiya Hassana da habiba suna expecting kaka to do something amma ko ajikinta,
"Ai daman nasan karya take..da dai tace babu kowa gidan sai in yarda amma bazai taba yuwu ace hajiya rukkaya na gidan kuma ayi irin wannan danyan aikin ba...kaci ubanta har saita fadi gaskiya..." Kaka ta fada mashi, afusace hajiya Hassana ta mika ta dauke suhail da Mari tanacewa
"Ka saketa Dan ubanka..." Sai lokacin suhail ya saketa amma bai bar huci ba,
"Wannan yarinyar makira ce...why will she say such horrible word...and my lovely mommy here believes her..."Yafada cikin bacin rai,  alhaji Muhammadu kallon hajiya Hassana yayi ya watsa mata wani irin dirty look dayasa taji hancinta ya kada,
"Humaira tsakaninki da Allah lokacin da nace ki shiga dakin Yazid kin taddasu a yanda kikace?.. Kiji tsoron Allah ki tuna da akwai ranar da bakinki bazai yi magana ba sai gabobin jikinki..." Hajiya rukkaya ta fadawa humaira dake kuka sosai sabida abinda suhail yayi mata, hajiya rukkaya juyawa tayi ga kaka tace
"Wallahi kaka lokacin da humaira ta  shigo gidan banfi minti biyu da fita daga dakin Yazid ba, suhail bai Jin dadi sai Yazid ya Kira mami muka shiga tare, bakin gadon da suhail ke kwance mami ta zauna sai ya Dora Kai kan kafarta ita kuma Tana  tambayanshi ko ta Kira mashi ambulance...ni kuma sai na fita Nayi serving Yazid da bai dade da dawowa daga aiki ba...sai humaira ta shigo." Hajiya rukkaya tayiwa kaka bayani, hajiya Hassana sai kallon banza kawai take mata amma tamkar bata wajen Don ko kallon inda take bata yi ba,
"Wannan zancen haka yake..." Kaka ta fada atakaice, hajiya Hassana ji tayi kaman ta hadiye zuciya ta mutu, suhail kallon mami data hada Kai da gwiwa Tana kuka
"Ke kuma karamin abu sai kuka ...banza kawai..ai inda aure gareki da baki fuskanci wannan matsalar ba,.." Kaka ta fadawa mami,
"Hmmm kaka ki kwantar da hankalinki Yanzu mami ta fidda miji...kwanan nan zaa kawo maki shi.." Hajiya rukkaya tafada Ciki farin ciki, idanuwa kaka ta zaro while shi kuma suhail yaji maganar ko kadan baiyi mashi dadi ba, alhaji Muhammadu ma maganar ya yiwa dad din mami har ya mika mashi hannu
"Kai jamaa da gaske kika ko da wasa?.. Wallahi in da gaske né ku fadamin in nemi hajiya zulaiha Mai zee de mun ta nemo min laci Mai tsada ...da takalma Don har duk tarina sai na bada kyauta ranar..." Kaka ta fada cikin excitement,
"Kaka kenan...ai ki kwantar da hankalinki..."
"aa Ai babu zancen kwantar da hankali..ke Dan ubanki ki fadamin da gaske né?.." Kaka ta tambayi mami, hajiya Hassana gani tayi taron da suka hada Don tozarta hajiya rukkaya and her family ya zama na felicitation, a fusace ta Mike ta dauki bag dinta ta fita itama hajiya habiba ta bi bayanta sai humaira dake kuka sosai itama tabi bayansu,
"ko yaushe wannan muguwar matar zata daina wannan mugun halin oho?sunyi tunanin ni tsohuwar banza ce..shine zasu hada bam...ta Allah ba nasu ba..." Tafada Sannan ta juya ga mami da har lokacin bata daga Kai ba tace
"Bani amsa mana..MAMI  kike ko mama..." Dan murmushi suhail yayi saboda yanda tayi maganar,  ahankali mami ta daga Kai Tana goge face dinta ta amsa da
"Eh.."
"Kai wannan anyi babban banza Wallahi ji yanda take Abu kaman wata yar shekara sha biyar,..mijinki zai sha kilibibi...kince eh...eh din na meye!..yaushe zaki kawomin mijinki?.." Kaka Ta tambayeta,
"In na dawo daga Saudi.zanje sati Mai zuwa...Insha Allah..." Ta amsa mata kanta kasa, suhail kallonta kawai yake bai ko blinking, alhaji Muhammadu dan taba alhaji yunusa yayi ya nuna mashi suhail, kawai yanda yake kallon mami ba blinking says a lot about him,
"Anty Nima Ina zuwa Saudi din...pls,," ya fada yana marairacewa,
"Dalla rufemin baki soko kawai...! Kaka ta hantareshi, haka dai kaka ta saki jiki da mami for the first time tunda delay na aurenta yazo, alhaji Muhammadu da alhaji yunusa fita sukayi suka barsu ya rage daga mami sai mom dinta da suhail.
Alhaji Muhammad lekawa yayi kan kallon so suhail ke yiwa mami shi kuma alhaji yunusa yace aa ba haka bane kawai kallon shakuwa da amintaka yake mata, haka dai suka rabu, alhaji Muhammad na komawa ya nufi part din hajiya Hassana da tayi kuka har ta godewa Allah, Tana ganin ya shigo tayi saurin mikewa, zai bude baki yayi magana tayi saurin rike mashi kafa Tana bashi hakuri kan Abunda tayi, she took full responsibility for what happened, hanashi magana tayi Tana bashi hakuri har ya juya ya fice baice mata komai ba.

A week later,
Ahmed dai yana cikin nunawa mami how much he loves and cherish her, kullum maganar shi is kawai ta bashi izini ya turo kawai there's no need for any delay ita kuma ta nuna dole yayi hakuri sai ta dawo daga saudi, shi ya dauki nauyin zai biya mata kudin amma tace ta gode ya bar shi, dukda ta dade batayi aure ba ko kadan she's not excited about the marriage issue, at times Tana mancewa sata fiddo miji sai daga baya ta tuna da hakan,. Gobe né tafiyarta, small bag ta hada Wanda Kaya dake ciki baifi guda biyu ba. Karfe biyu zata tashi zuwa Lagos ta Kwana gidan uncle dinta sai su tashi tare.

Suhail kam Yanzu ya fara zuwa aiki tun ranar da yayiwa mami alkawarin zai fara, but the most annoying thing is how he thinks about mami, bai iya yiwa Yazid maganar ta amma kullum Tana cikin ranshi, gashi Yanzu he's always tired sabida aiki balle ya dinga zuwa ganinta, he do call her kullum Suna gaisawa, yau around 10 ya kirata take fada mashi she's getting ready for her trip,
"Anty assuming ban Kira ba bazan San zaki tafi yau ba kenan kou?.." Ya fada kaman zaiyi mata kuka,
"Sorry my bad.." Tafada mashi,
"Anty..let me come and see you before you go..wannan aikin ya Hana ni ganinki two days..."
"Aa..ba sai ka zo ba...kawai dai in na dawo zamu hadu Ai...or during wedding din baby..." Idanuwa suhail ya zaro kaman yana gabanta yace
"Anty you mean baki missing Dina at all?.. Nine fa your cutest,." Yafada yana motsa red lips dinshi ahankali, dariya tayi tace
"Haba my cutest Kayi hakuri...Wallahi am so missing you amma Kayi hakuri..now tell me what do you want me to buy for you..." Tafada kaman She's talking to a baby doll,
"Aa ni dai anty Bari in zo...am coming now..." Yafada yana katse wayar, bai ma fadawa kowa zai fita ba ya fice zuwa gidan su mami, karfe 11 sauran ya isa gidan ya tarda mami kadai a falo kanta babu dankwali kanta Sannan rigar jikinta ba wani Mai nauyi bane sai leggings da ta saka, ta nannade legs dinta Tana operating system dake gabanta, Yanzu it's exactly one week daya ganta last a gidan kaka, she's looking more younger in he's eyes, bata Ankara ba ta ganshi kaman daga sama,
"Mr cute wato sai da ka baro aikinka ka taho..." Tafada Tana maida idanuwanta kan system din,
"Hmmm anty kenan...Yanzu kin manceni sosai...ko kirana ba kiyi saidai ni in kiraki,,,' " yafada yana zama,murmushi ta saki tace
"Am sorry cutest..Wallahi aikin né yana min yawa..ga office, ga tafiya ga preparation na bikin baby,..it's all on me..." Gefen kunnenta ya kurawa Ido tare dacewa
"Hmmm anty despite all this stress you're still looking beautiful...anty pls tell me meye sirrin..." Yafada firmly, dariya tayi sosai Sannan tace
"You're funny...kana ganin yanda kake kuwa?.. Ai ban kaika ba...ni kawai am eager to see your wife..." Tafada Tana dariya, idanuwa ya lumshe kaman an fixgo magana daga bakinshi sai yace
"Ga...ki..."

Nan na kawo karshen free pages Dina, if you wish to continue zaki tura 300 to 0024878383 stanbic sai ki tura screenshot  to 08106102727 ta whatsapp ko kuma ki tura 300 mtn recharge card to wannan number ta sama, duk wacce bata biya ba ta

Please Login or Register in order to submit comment