Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bude, lokacin wajen karfe 9:30 mahaifin suhail bai fita ba, Ana parking kaka ta fito sai zuba ruwan fada take, da gudu alhaji Muhammad ya fito daga part dinshi ya durkusa kasa yana cewa
"Kaka lafiya dai?.. Waya taba mani ke...kaka Ai sai ki Kira inzo ba sai kinzo ba..." Yafada kanshi kasa in a respectful way dukda ba ita bace mahaifiyar shi,
"Ya zaayi in Bari kazo alhalin kun turo fitsararren danku ya zageni tas..." Tafada Tana tafiya zuwa hanyar part dun mahaifiyar suhail, da sauri alhaji Muhammad ya Mike ya bi bayanta yana cewa
"Inna lillahi wa'ina ilaihi rajiun...kaka waye cikinsu?.."ya tambayeta, banza tayi dashi har saida ta shige falon mahaifiyar suhail ya zauna tace
"Hassana fito Dan ubanki...." Ta Kira mahaifiyar suhail dake bathroom, tun inda take taji muryar kaka, da sauri tayi ta fito Tana tunanin yau da akwai matsala saboda kaka bata zuwa gidan kowa sai in da akwai problem, da gudu ta fito Don daman ba shiri suke da kaka ba a Sanadiyar mahaifiyar mami, alhaji na durkushe gabanta yace
"Kaka Ina kwana..." Bai karasa ba ta daga mashi hannu Tana cewa
"Ba gaisuwa ya kawo ni ba...Hassana Wallahi kar ki kuskura in Mike baki iso nan ba Dom sai kin tafi kauye ku yau ba gobe ba..." Ta fada sounding so harsh, da gudu hajiya Hassana ta iso ta durkusa kasa gaban kaka gefen mijinta, nunata kaka tayi da yatsa Sannan tace
"Ki fiddo min danki da kika aiko ya zageni jiya da daddare ko ranki ya baci..." Ta fada mata kaman she's talking to four years old girl,
"Wayyo Allah kaka...Wallahi ban turo kowa ba...ni ban ma San abinda kike cewa ba..." Ta fada kaman zatayi kuka, harara kaka ta wats mata Sannan tace
"Yo min shuru munafuka...wato an samu bakin halinki ya ragu shine zaki turo wannan Dan dake yawo kaman babu jini jikinshi ya zage ni kou....Yanzu je ki fiddo min shi..." Tafada mata atakaice, Tana cewa yana yawo kaman babu jini jikinshi suka gane she's
Talking about suhail
"Wallahi kaka rabona da suhail tun jiya daya dawo..ko hour daya baiyi cikin gidan nan ba suka fita da Yazid...Wallahi maganar da nake maki ba gidan nan ya kwana ba..." Tafada kanta kasa,
"Karya kike munafuka..." Kaka ta fada mata, face hajiya Hassana ta daure Jin Tana kiranta da munafuka, ganin ba Mai kallonta yasa ta watsa mata harara tare da tale baki Sannan tace
"kaka ni ban San abinda nayi maki ba...tun daga yarinta izuwa Yanzu baki amincewa da duk abinda na fada maki...ni kawai baki sona..." Ta fada cikin kuka, afusace alhaji Muhammad ya juya gareta yace
"Ke meye haka?.." Ya daka mata tsawa, Sannan ya juya ga kaka yace
"Kiyi hakuri kaka..Wallahi ko ganinshi banyi ba tunda ya dawo daga waje....kiyi hakuri zanyi maganinshi..." Alhaji Muhammad yafada in a respectful way, hajiya Hassana dake kukan karya harara ta gallawa mijinta ta kasar Ido Jin yace zai hukunta autanta,
"Aa kar ka hukunta shi...Allah ya kaimu karshen wata...ai na isheshi Riga a wando...ni Wallahi duk tarbiyar da wannan shashan matar nan ta bashi né...duk zuriar nan kaf babu Mai maidawa mutum magana sai yaranta...shiyasa tuntuni naso a kora shegiya daga gidan nan..." kaka ta fada Tana mikewa, hajiya Hassana Kara volume din kukanta tayi amma in da zaki ga face dinta babu komai saboda kukan na munafuci né,
"Allah ya huci zuciyar kaka...kaka ki zauna kisha ko ruwa né..." Alhaji Muhammad ya fada mata, tsoki taja Tana cewa
"Allah ya tsareni da Shan abun hannun wannan munafukar..." Tafada Tana dogara sandan ta zuwa waje,  bayanta alhaji yabi suka fice daga falon, hajiya Hassana ta Mike tabi bayan Kofar da harara, Tana cewa
"Useless good for nothing old witch....inda marinki yayi sai kiyi duk abinda zakiy...mata duk tabi ta addabi mutane?.. Kuma mutuwa yaki awon gaba da tsigaggan banza...Allah ya hadaki da balai on your way home ...banza kawai...kece munafuka kuma mutuwar munafurci zakiyi in Allah ya amince..." Tafada Tana komawa cikin dakinta.  
5💙💛❤️💜💛💚
Lokacine
💙💚💛💜❤️💚


® zuwairat (ummumaryam)




5️⃣




Free page

Dedicated to my anty...the wonderful person.

Hajiya Hassana na gama kunduma zagi ta dauki wayar Tana cewa
"nasan wannan yaron yana chan gidan wannan matsiyaciyar matar...yaro ya dawo ko ubanshi bai gani ba yaje ya zauna gidan matar da ko ganina batason yi a wannan family...kuma kayi magana ace kaine Mai bakin Hali...nasan tare sukaje da wannan yaron Yazid amma ba'a ganin laifin shi sai na suhail, saboda uawarshi ta shanye kaka..." Ta fada Tana dailing number suhail,
"Ai kayi aure sai in ga ta yawo...duk tabi ta shanye min da...bai damu da yan gidan nan kaman yanda ya damu da yan Chan gidan ba...inama amfani...mtwssss..." Tafada sounding angry dataji number dinshi not reachable, ajiye wayar tayi looking mad.
Suhail kam yana chan kwance bai farka ba sai wajen karfe 12:30 na rana, baggy a shiga yayi wanka tare da fitowa da alwallah, fitowa yayi daure da towel, bakin gado ya zauna ya dauki wayarshi ya kunna Sannan ya dauki wata riga cikin Kayan Yazid ya saka kasancewan kusan height da weight dinsu daya, sai da ya shirya ya fita zuwa falo, babu kawo sai Aisha dake zaune Tana chatting, Tana ganin shi Tayi saurin ajiye wayan Tana cewa
"Yaya yaushe ka dawo?.." Ta fada sounding so surprised, dariya yayi yace
"Tun jiya...ai nan ma na kwana..." Idanuwa ta zaro Tana mikewa Sannan tace
," Lallai ma yaya...shine ko ka tambayi inda nake...gaskiya nama yi fushi..." Tafada tana komaWa ta zauna tare da harde hannunta a chest dinta Tana turo baki, cikin dariya ya karasa inda take zaune ya zauna kan hannu kujera ya Dora hannu kan head dinta tare da juyo da face dinta yace
"Kiyi hakuri dear...na Tambayi Yazid inda kike yace kinyi bacci...shiyasa...so tell me how are you..." Yafada cikin so da Kauna kaman he's talking to his own younger sister, murmushi Aisha ta saki tac
"am fine yaya..ya karatu..Ina tsaraba ta,.."
"Karatu Alhamdulillah mun gama...tsaraba kuma zan kawo maki..." Yafada yana mikewa,
"yauwa yayana..."
"In da akwai abinci ki tashi ki bani..am so hungry..." Bai karasa ba ta Mike ta Kama hanya kitchen shi kuma ya Kama hanyar upstairs yanacewa
"Bari in gaido mummy..."

Bayan kaman minti talatin yaci ya koshi Sannan ya koma daki ya dauki wayarshi yayi dailing number mom dinshi Tana piçking yace
"My mom good afternoon..." Yafada yana dariya
"Dan ubanka Ina kaje?.. Ka dawo ko uban da ya yayi wahalal karatunka Baka tsaya ka ganshi ba ka Kama gantali kou..." Idanuwa yayi rolling yace
"Mom kaka tazo?..." Ya tambayeta Kai tsaye
"Dan ubanka ta zo mana...me zai Hana tazo ta zageni tunda kaje kajamin magana...an saka gaba kunje amma dayake ni aka tsana a family din ni tazo ta zaga,,," Tafada sounding angry m suhail yasan where her point is going so bai tsaya long talk ba yace
"Mom ga ni nan zuwa..." Yana kaiwa nan ya katse wayar tare da mikewa,daga nan tsaye yayi dailing number humaira yaji switch off , wayar ya maida cikin aljihunshi ya fita, sallama yayiwa su Aisha da momcy Sannan ya Kama hanyar gidansu.

Wajen karfe biyu mami ce zaune a office dinta that looks so cute, tayi tagumi da ganin she's thinking, ba komai take tunani ba sai rayuwar ta, her life seem so perfect from outside but chartered from inside, in taga mata da aure sai taga inama ita, su kuma wasu mutanen in sun ganta sai suce inama su especially saboda yanda take amfani da basirar ta wajen taimakawa na kasa da ita, kofa aka bude amma ko blinking batayi ba balle ta Lura da Wanda ya shigo, she's so lost in thoughts, sallama Mutumin dake sanyi da white shadda Mai tsada yayi amma still bata ji ba, Dan takawa yayi ya shiga cikin office din ya maida Kofar ya rufe Sannan ya sake sallama, afirgice mami ta daga Kai ta kalleshi Sannan ta Mike Tana amsa sallama, the look on her face shows she just get back from another world Don duk idanwanta waje,
"Dr hope dai you're alright?.." Mutumin ya fada mata yana zama kan kujera dake gabanta, Dan murmushin karfi. Hali ya saki Tana zama ita ma tace
"Good afternoon sir..bacci né ya Dan daukeni,.." Tayi mashi karya, murmushi ya saki yana girgiza Kai saboda yasan its a plane lie Don yaganta idanuwanta biyu kawai she's lost in thought né
"Sir yasu hajiya..yau kai kadai kazo kenan?.. How can I help you.." Tafada sounding so friendly Don ta dade sa saninshi da family dinshi, nan suke medical checkup dinsu, and suna mutunci da matarshi sosai, kura mata Ido yayi tare da breathing out loud Sannan yace
"Yau ni kadai nazo...wani Abu ke damuna...I have been trying to keep it because of circumstances amma na kasa..ji nayi in ban fada ba I can't handle myself..." Yafada kanshi kasa kaman yana Jin nauyin ta, da sauri Maryam ta gyara zama tace
"am all ears..." Tada da yana folding hands dinta a kan table with her ears wide open to hear her patients complains, shuru yayi for a moment Sannan ya saki ajiyan zuciya yace
"gaskiya dr Maryam I think am in love with you..." Yafada sounding firm, ahankali Maryam tayi relaxing Tana kallon shi her face full of surprises, she can't believe she's hearing this from this man, the man that duk haihuwar da matarshi zatayi a hannunta take haihuwa, Kai ta fara girgizawa with her eyes closed, zata bude baki tayi magana sai kuma ta rasa what to say,
"Pls you don't have to say anything...zan barki kiyi tunani tukun ...I will come back for your reply..." Alhaji Ahmed ya fada mata yana mikewa ahankali,
"At least you know how I feel about you..." Yafada ma  da har lokacin bata bude idanuwa ba, sai da taji an bude kofa an fita Sannan ta samu ta bude idonta, her heart was beating very fast saboda Abunda ya fada mata, she can't believe Wanda ya San how close she is with he's wife will come and say such words,
"Lallai...ma...I know inason mijin aure but that bazai sa inci amana patient Dina ba..." Tafada ahankali, she's supposed to go back home amma she just want to stay in the office and think about her life, ahankali ta Mike Tana Dora glasses dinta a face dinta Sannan ta dauki car keys dinta ta fito daga office din, she have a good working relationship da Wanda suka aiki tare tunda Tana fita kowa sai Doctor mami Allah ya kayaye hanya kawai suke mata, ita kuma Tana amsawa wearing a smile that makes her looks more beautiful than ever, ko kadan babu Mai taba ganewa wani Abu na damunta, Tana fita ta shiga motar ta tare da sakin wata dogwar ajiya zuciya Sannan ta fara tuki,

Suhail na isa Gida mom dinshi ta dinga fada, ba komai ke bata mata rai ba irin yanda baya Jin magana, ko kanayi he will only pretend to listen to you but ko kadan bai daukar maganar ka, inda suhail najin magana da tuna ya bar tarayya da Yazid amma mom dinshi na gama magana kan wannan family zai Mike bayan kaman minti ashirin yace na tafi gidansu Yazid, ga family din Mai waazi Baka takura yaro, Don in kaka taji kana cikin matsala, she hate yanda duk cikin yaranta suhail kadaine bayajin maganar ta, a family din kaf bata shiri da kowa kaman yanda take shiri da mahaifiyar humaira, ko a wajen meeting kusa da junansu suke zama kiji suna kus kus, basu da gurin daya Kai suga yaransu sunyi aure wato humaira da suhail,
"Wallahi tunda kace bakajin magana jikinka zai fada maka...nasha fada maka gidan nan basu kaunata...matar tunda aka kawoni gidan nan take nunamin kiyayya...har asiri tayiwa kaka Don ta bar ganin laifin ta sai nawa amma dayake kunnen kashi gareka shine daga zuwa danta ya tisa ka gaba kukaje gidan kaka amma ita Ai bata je ta zageta ba...sai ni da aka tsana ..." hajiya Hassana ta fada cikin bacin rai, suhail shuru yayi Yana sauraron abinda take cewa, sai da yaga ta koma ta zauna yace
"Mommy humaira tazo?.." Ya fada so care free, harara mahaifiyar shi ta watsa mashi tace
"wato all my talk babu abinda zakace sai humaira tazo?....you must be out of your mind..." Idanuwa ya lumshe yana cewa
"Mommy ni me zance..tunda Abunda ke tsakanin ku bai karewa...ni tunda nake zuwa gidansu Yazid ba'a taba nunamin wani banbanci ba, ...mommy Tana kula Dani sosai kaman yanda take kula da Yazid...name zan tsaya damun Kaina da what you think..kuma about yesterday ko shiga Yazid baiyi ba..asalima he was begging we shouldn't go..so pls mum keep Yazid out of this..." Hajiya Hassana dake tsaye Tana kallon yanda yake magana kaman baison magana ta Dora hannu bisa Kai Tana cewa
"Allah yaisa tsakanina da hajiya rukkaya...nasan Ai bazata barka haka ba...wato ni kake fadawa why will you disturb yourself with what I said...ni ba mahaifiyarka bace?.. I have total control of what you do..." Tafada cikin bacin rai, suhail na ganin maganar ba karewa zaiyi ba ya Mike ahankali ya Kama hanyar fita daga falonta,
"Dan ubanka come back here right now..." Ta fada sounding so commanding, amma ko juyawa baiyi ba ya fice daga dakin, part dinshi ya koma ya cire Kaya ya rage dagashi sai shorts ya zauna yana jiran zuwan humaira because she promised zata zo.

Doctor mami na isa gidan as usual ta bawa Mai gadi what she have for him Don already it's part of her before abinda taci ta rage take kawo mashi but now dole sai ta biya suya depot ta saya mashi na one thousand Sannan ta dawo gidan she wonders why bai gaji ya da cin Nama Don kullum cikin jira yake at times she will feel like not to buy amma kuma sai ta tunda he will be expecting it kuma tasan it hurts to expect something then loose it, cikin falo ta shiga ta tarda mommy da Aisha zaune, da gudu Aisha ya fada jikinta kaman yanda take when she was a baby, babu abinda ya Chanza a rayuwar Aisha, har shagwaba da takeyi wa dr har Yanzu bata Bari ba, at time sai ta tisata gaba ta dinga yi mata kuka babu gaira babu dalili, she knows zasuyi missing juna sosai in har tayi aure, rungumeta dr tayi har suka kusa faduwa a jikin hajiya, da sauri ta matsa Tana cewa
'"Ku kullum Baku gajiya da wannan abun..." Tafada Tana kallon yaranta with love,
"Mummy Wai meyasa bakison antyna Tana nunamin so..." Aisha ta fada cikin shagwaba m dariya dr tayi tace
"Kar ki damu..ni da ke takalmi kaza...we're stuck together for ever kinji babyna..." Dr ta fada mata,
"Yeeeeyyyy..." Aisha ta fada cikin happiness Tana cewa
"Anty me zakici..."
"Dear don't worry...zo ki zauna muyi shopping a Ali express...tunda delivery zai Kai 3 weeks kinga one month to your wedding everything will be here..." Dr ta fada mata, ahankali Aisha tazo ta zauna kusa daita ita kuma ta dauko tablet daga cikin bag dinta ta shiga Ali express, Kayan gida ta dinga selecting Aisha na cewa
"anty sunyi yawa...ki rage..." Amma ko kallon ta batayi ba ta shiga check out Sannan tayi paying, Sannan ta kalli Aisha tace baby ki Dan hau upstairs zamuyi magana da mom,.." Da sauri with respect Aisha ta Mike ta bar masu falon, tuni hajiya ta gyara zama Tana sauraron abinda mami zata fada mata,
"Yauwa mom kin tuna alhaji Ahmed...wannan Wanda nake fada maki in matar tazo hospital babu Mai dubata sai ni?..kin tuna shi?.." Ta tambayeta, hajiya shuru tayi looking at same spot Don tunawa da Wanda take magana,
"Wanda ya baki Nama cike da Leda da matarshi ta haihu?.."
"Yauwa mom shi..could you believe what he told me today?.." Mami ta tambayi mahaifiyar ta,
"What did he tell you..." Ta tambayeta itama, ajiyan zuciya mami tayi Sannan tace
"Mommy..Wai yau yazo office..Wallahi I was thinking sani Abu yazo yi...sai yace Wai he loves me... I was so surprised..." Tafada still feeling surprised, shuru mahaifiyar ta tayi Sannan tace
"What was your answer?.."
"Mommy Wallahi ni kasa magana nayi...I couldn't say one word...and when I try to talk sai yace I don't have to say anything now..Wai zai bani time nayi tunani.."
"Ikon Allah...amma dear what do you think about it..."mom dinta ta sake tambayan ta
"Well mommy gaskiya ni I can't accept him...matarshi is close to me...kuma sau biyu Ina amsar haihuwar ta..sai in so mijinta ta dinga yadani Wai na gama sanin sirrinta na aure mata miji?.. Gaskiya am fragile...I can't handle any problems..." Tafada ahankali, mom dinta kallon ta kawai take har ta gama magana Sannan tace
"Abut dear is not haram..remember now you don't have time to think about all this stuffs..."
"Yes mommy..nasan time is going amma somethings are better left undone...ni mom yanda na dade banyi aure ba banason inyi in samu matsala..kawai I will tell him I can't yayi hakuri..." Tafada atakaice, hajiya da gurin is tayi aure tace
"Aa dear...ai duk mace Mai hankali tasan mijinta ba nata bane ita kadai...Sannan tasan ko bajima ko badade zai iya auro wata..nidai like he said just think about it..." Tafada mata,
"Nidai gaskiya mom I have nothing to think about...kinga keda mummy suhail ba mijinku daya ba but look at yanda kuke fafatawa...sai inje in auri mijin wacce ta amminta dani?.. Ai duk abinda tayi min ni najawa Kaina..." Tafada mata kaman zatayi kuka
"Aa dear Ai ba duka aka taru aka zama daya ba..mutane kowa da kala hankalinshi...wasu are selfish while wasu kuma selfless, ...it depends which one you want to be..if you're selfless Allah zai kareki daga masu sharri...kinganin nan you know me too well that ni mutum bai dameni ba especially people that don't want peace...Don haka ki sani nawa da Hassana will not make you give up..she might not be sas bad as you think.." Tafada Tana rike da hannunta
"Hmmm nasan you want be to get married amma gaskiya ban da alhaji Ahmed..." Bata karasa ba hajiya tace
"Don't say that..kawai let's pray...in shine Mafin alkhairi Allah yasa ayi  dashi ..." Tafada mata, mikewa mami tayi without saying a word, she knows matar shi will not be happy with her in har ta amince ta aure mata miji, Ai Ana barin halal Dan kunya, Tana ganin yanda take nunawa mijinta Kauna ko a hospital, she loves him so much, dakinta ta shiga ta shiga bathroom ta watsawa kanta ruwa still thinking about it but ko kadan she don't feel she can accept.

Suhail na kwance yana jiran zuwan humaira har karfe biyar yayi, he's so angry because har lokacin Her line was not going through, face dinshi daure ya shiga bathroom ya fita ya saka wasu English wears da suka amshi jikinshi sosai, yana fitowa motar dad dinshi na shigowa, sai lokacin ya tuna tunda ya dawo bai ganshi ba, gefe daya ya koma yana jira driver yayi parking dad dinshi yafito, saida driver yayi parking alhaji Muhammad ya fito da sauri suhail ya zo wajen dad dinshi da face dinshi babu walwala yayi hugging dinshi not caring about how he looks,
"Daddy nayi missing Dinka sosai..." Yafada yana rungume dashi gam har motsi bai iyayi, idanuwa alhaji Muhammad yayi and rolling zaiyi magana suhail yayi saurin sakinshi ya amshe briefcase dake hannunshi yanacewa
"Dad ya aiki ya komai da komai..." Yafada yana saurin juyawa Don yasan he's dad will surely spark him for misbehaving with kaka,
"Lafiya..." Ya amsa mashi yana biye dashi zuwa falonshi, suhail na ajiye briefcase din yayi niyyar juyawa sai yaji dad dinshi yace
"" me kayiwa kaka jiya?.." Ya tambayeshi sounding so angry, idanuwa suhail dake kallon kofa yayi rolling alaman despite all my efforts, ahankali ya juyo wearing a killer smile yana cewa
"Daddy ko ya karatu Baka tambayeni ba...ko ya results Baka tambayeni ba sai maganar kaka..." Bai karasa ba dad dinshi yace
"You're very stupid for saying that..Kai ka jira ka ganni before kaje daukar magana?.. Now let me warn you for the last time..kar in karajin kaje gidan kaka if not for something good...kowa najin yiwa kaka rashin  kunya amma Banda Kai...four good years ka bar gida ka dawo wth same stupid attitude...to Wallahi ranka zai baci..." Alhaji Muhammad Yafada mashi cikin tsawatawa, sai da ya Kai aya Sannan suhail yace
"Ni dad Wai kuna ganin zai iya zagin kaka né?.."
"Karya tayi maka kenan..kana ganin baiwar Allah nan ko breakfast batayi ba tazo nan gidan saboda ka bata mata rai..." Ahankali suhail ya dawo ya zauna yace
"Nifa dad ban zageta..kawai I went to discuss something important with her..sai maigadin ta yace kar a shiga, ni kuma sai na shiga...that's all fa...take cewa na zageta..." Tsoki alhaji yaja yace
"Ai tunda maigadin yace kar ka shiga kasan it's her instructions..so if you violate it means and insult, Don haka kadai shiga hankalinka..." Ya fada mashi atakaice,
"Hmmm this people...wato she always right...Allah ka kawo ranar fidda wannan matar daga wannan banzar family..." Ya fada cikin ranshi Sannan yace
"Ai dad Baka tambayeni important issue daya Kai ni gidan wannan matar ba..." Kai alhaji ya daga ya watsa mashi harara, yace
"Wato halin ka nan...Kai bazaka fadamin ba sai na tambayeka?.. You're not serious..." Yafada not too harsh,
"Naji dadi but ask me tou..." Yafada cikin shagwaba, banza yayi dashi ya Mike ya shiga one of he's bedroom, kafa suhail ya Dora kan juna yana jiran fitowanshi, mum dinshi ce ta shigo da food of basket ta jera kan dining, ko kallon inda suhail yake bata kalla ha balle tayi mashi magana, shigewa tayi bedroom din alhaji suhail yace
"Muma dai zamuyi auren..ehe.." Ya fada yana kar kada kafa.

Thanks
6💛💙💚💜❤️
Lokacine
💙💚💜💛❤️

® zuwairat (ummumaryam)




6️⃣



Free page



Yana nan zaune har dad dinshi ya fito cikin jallabiya mom dinshi na biye dashi, ko inda yake basu kalla ba suka zauna kan dining tayi serving dinshi ya fara ci, suhail kallon su kawai yake yana imagining shi da humaira at this age, but the fact is he can't picture themselves a haka, it looks so blank, ganin babu Wanda ya tanka mashi yaga sun maida shi invisible yasa ya yace
"Duk family in yaransu sun dawo daga abroad suna nuna mashi so da Kauna amma dayake ni ba'a sona ko damuwa Dani ba'a yi " Yafada kaman zaiyi kuka, dad dinshi kallon shi yayi ya tabe baki yacigaba da cin Abincin shi mom dinshi itama ko kallon shi batayi ba, suhail ji yayi ranshi ya mugun baci kawai sai ya tale baki ya fashe da kuka, both parents kallon mamaki suka dingayi mashi without word Don suna ganin kaman he's joking, shima suhail yasan it's a Joke but he tried by all means har saida yayi forcing hawaye down kaman wani Dan film, baki suka saki suna kallon ikon Allah,  cikin kuka yace
"I hate my life...you all hate me..." Yafada yana Mikewa yana kuka,
"Kai !.." Dad disnhi ya kirashi, ahankali ya juyo ya rufe idanuwa gam sai kuka yake Dan hawaye is coming out,
"Meye haka?.. " Inji dad dinshi,
,"dad Baku damu Dani ba...you don't care how I feel anymore...kaman kun mance Dani Wallahi.." Yafada cikin kuka,
"Sit down..." Dad dinshi ya umarceshi, ahankali ya koma ya zauna ita kam hajiya Hassana rasa inda zata saka kanta tayi ganin danta na kuka,
"Now tell me meye damuwanka..." Alhaji ya tambayeshi yana kallon junior him, Don daga behavior har kaman duk nashi né, haka nan yake rufe Ido ya dinga yi mashi fada in yayi ba daidai ba amma yasan shima he was more stubborn than him when he was younger sai dai shi yayi aure da wurin Don at 25 akayi masu aure kusan 4 bayan aure kuma komai sai ya lafa, yasan duk yanda suhail ke rashin ji dayayi aure shikenan,
"Dad Baka tambayeni how is everything...dad Baka sona Yanzu..." Yafada yana Kara volume din kukan shi, idanuwa dad dinshi yayi rolling Sannan yace
"Now tell me how is everything?.."
"Fine daddy..." Ya amsa mashi, abinci bawan Allah zai koma ci suhail ya sake cewa
"Dad Baka tambayeni why naje gidan kaka ba..." Yafada cikin shagwaba,
,"tou why kaje gidan kaka?.." Dad dinshi ya biye mashi, idanuwanshi ya bude ya goge tears dinshi Sannan yace
"Dad naje né inyiwa kaka maganar mu da humaira..,shine.." Idanuwa  alhaji ya zaro yana dafa goshinshi tare dacewa
"Inna

Please Login or Register in order to submit comment