Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kai ya hangi mami dake zaune idanuwanta lumshe bakinta na motsi ahankali, it's like she's praying,  Dan murmushi ya saki tare da taba shoulder din Yazid yace
"What is she doing..." Ya tambayeshi kasa kasa.
"Kilan she's praying yau kaka ta manta da lamuranta kar ta tsigeta yau..." Ya amsa mashi shima kasa kasa,
"Shugaba ka bude mana taro da adua...!" Kaka ta fada sounding very angry, nan wani mutun Wanda duk yafisu tsufa ya fara adua cikin sweet tune, sai dai ya gama aka Shafa Sannan kaka ta kalli Mai karanta agenda tace
"Karanto abubuwan da zaa yi yau da ka karanta dazun" kaka ta umarceshi, suhail sai binta yake da kallo yana ji kaman ya shakota daga inda take. Zaune ya lika  ta da kasa, sake kallon mami yayi yaga har lokacin bata bude Ido ba, haka nan sai yaga tayi mashi duhu ta rame, yana Jin Wanda kaka tasa yayi reading agenda data sa shi rubutawa sai yaji ance
"Sannan sai wayanda sukayi rashin kunya a wannan watan..." Yaji an fada, juyowa Yazid yayi ya kalleshi sannan yace
"You're in trouble..." Tsoki suhail yaja yana kallon mami, Shan sai yaga ta bude idanuwa sai yaga her eyes are red,
"Abu na farko da zaa tattauna shine maganar sakin da buba yayi wa matarshi,.." Kaka Tafada ta danyi shuru Sannan kuma tace
"Buba kana abinda zakace game da wannan?.." Kaka ta fada kaman wata Chief Justice, goshi suhail ya dafa yana cewa
"Imagine..tonan asiri gaban yara...this family is the worst ever..." Yafada kasan muryar shi, wani cousin brother dinsu ya kalleshi tare da sakin yar dariya,
"Ni dai bani da raayin fadin abinda ya faru gaban wannan yaran..kawai dai yanda na fada maki haka zancen yake..." Wanda aka Kira da buba ya fada sounding respective,
"Lallai buba..wato bazaka fadi abinda ya faru a gaban yara ba amma ka sake ta?.. To ka maidota...fakat..." Kaka ta fada ataikace, Mutumin kaman bai so ya koma ya zauna bai ce komai ba, kallon treasurer kaka tayi tace ya fadi abinda suke dashi a account.! daman a kaidarsu duk wata in an Zo wajen meeting suna fidda task, like in kana amsar kaman half a million duk wata zaka fidda 50k ka ajiye cikin asusun Tallafin Mai waazi, Duk wanda ke family din indai yana aiki sai ya fidda nor matter little ya saka, kuma kowa da amount da yake fiddawa depending on yawan salary Dinka, cikin kudin suke bawa yaransu allowance duk wata, duk Wanda bai aiki ko yana zuwa school like university zaa bashi 20k duk wata har sai ya gama, in mutum na senior secondary school zaa bashi 10k, sai junior secondary school zaa bashi 7k, sai primary 5k and nursery 3k, haka ake basu duk yawan yaransu, kowanne zaiyi managing nashi ko nata zuwa karshen wata, su matan kudinsu yafi na Maza saboda suna da extra 5k saman Nasu, which yana sa matasan Jin haushi sosai amma sai kaka tace Ai mata sunfi Maza bukatar kudi, kawai sai suce sonkai né Don Tana mace, dukda kudin da ake basu wasu suna karawa yaransu sabida yawancin su masu kudine. Sannan cikin kudin ake daukan wasu kudin da zaa dafa abinci da Kayan da zasu sha during the Meeting. Ahankali mutum da kaka ta tambaya ya Mike Wanda kamanninshi da dad din suhail ya bace ya dad ya bude book yace
"A Yanzu sauran kudin mu bayan duk expenses..." Bai karasa ba kaka ta katseshi dacewa
"Banason son Jin turanci cikin maganar ka..." Ta fada sounding so commanding,
"Tou kaka..bayan duk kashe kudin da mukayi muna da million shidda da yan Kai a  account saboda Yanzu wata biyar kenan bamu bada kyauta waje ba bayan Wanda muke bawa yaran mu..." Mutumin ya fada Sannan ya koma ya zauna,
"Madalla...Yanzu me zamuyi da wannan kudin..." Kaka ta. Tambaya Tana kallo faces Din manyan, dad din Suhail me ha Mike yace
"Ayi kaman yanda aka Saba, a Kai wasu gidan marayu,,,sai kuma a sayi abinci a bawa mabukata..." Yafada Sannan ya koma ya zauna, harara kaka ta watsa mashi sabida haushin shi da takeji tace
"Tou ba haka zaayi ba...wani ya kawo wata shawarar...Wanda yake da yara masu hankali.." Ta fada sounding serious, suhail saya kurawa mami Ido daga Kai ya kalli dad disnhi sai dad disnhi ya watsa mashi harara, mami najin abinda kaka tace ta juya ta kalli suhail a daidai lokacin da shima ya kalleta sai suka hada Ido murmushi ya sakar mata murmushi tare da kashe mata Ido daya, murmushin karfin Hali ya sakar mashi tare da girgiza mashi Kai,
"Tou me zai Hana mu gina wata masallaci a wasu kauyuka da suke da bukata..." Dad din Maryam ya fada
"Kayi magana in ka aurar da tsohuwar diyarka,,," kaka ta fada mashi referring to mami, maganar yayiwa suhail zafi har yaja tsoki Wanda kaka taji amma she's not sure if she had right,
"Pls ka daina..kar kaja mana..." Wani cousin din suhail ya fada sounding angry,
"If you're afraid of getting into trouble then ka tashi..." Shima Suhail ya amsa mashi, mami sadda Kai kasa tayi mata daga kai ba sabida abinda kaka tace, daman tsohuwa take ce mata in public. Suhail kallon ta kawai yake Don ganin reactions dinta amma bata daga Kai ba balle ya gani, Dan juya Kai yayi suka hada Ido da humaira, to he's surprise sai tayi mashi wani irin kallo da bai gane manufarta ba, haka ya mugun bata mashi rai, Kara daurewa yayi yana karkada kafa ahankali, dukkan su babu Wanda ya Kara bada shawara saboda sunsan dole kaka zata samu abinda zata fada kansu, daman da gani yau she's in bad mood, Jin an yi shuru yasa tace
"Yanzu babu. Wanda sai bada shawarar yanda zaayi da kudin?.." Ta fada cikin tsiwa, duk shuru akayi sai suhail dake dariya  hannunshi kan bakinshi,
"Ai shikenan... Dauki rabin kudin a sayawa nene Kayan daki...sai saurin a barsu a banki..." Tafada atakaice, wani irin harara mahaifiyar suhail da mahaifiyar humaira suka watsa mata Sai kuma maman Maryam ta saki murmushi saboda nene is Aisha,  bakin ciki kaman ya kashe mahaifiyar suhail Jin an bawa nene kyautar million uku da wani Abu, kallon juna sukayi da maman humaira duk idanuwa nsu sun sauya kala, magana kaka ta dingayi babu Mai cewa komai, suhail kam bai minti biyu bai kalli mami ba, duk jikinshi sai kaikaiyi yake mashi saboda Rashin wanka, bayan kaman hour daya da rabi sai kaka ta daga Kai ta kalli mami tace
"Sai maganar wanna tsohuwar.,gaskiya ba kuyi min adalci...sai ace duk cikin ku babu Wanda zai nemo koda guturu né a bata?.. Sai a bar ya mace ta tsofe gaban uwar ta?.. Inna lillahi wa'ina ilaihi rajiun...wannan abun bakin cikin zaiy ajalina..kaf danginmu babu Mai wannan nauyin jini haka ..." Tunda ta fara maganar mami ta sadda Kai kasaTana hawaye,
"Gaskiya ke kadai zaki bata mana sunan pamili...kowacce yarinya bata wuce shekara 20 zuwa da biyu sunyi aure amma ke gash har zaki Kai shekara arbain bakiy auren ba..duk sabida karatun banza..." Kaka Tafada idanuwanta kan mami dake hawaye sosai har da majina, suhail clinching hannunshi yayi likewise duk Wanda ke hall din Mai son mami, mami daman bata da bakin jini a family sai wajen kaka da kuma mahaifiyar suhail da friends dinta in the family, kaka na fara magana sai ta saki wani irin ajiyan zuciya tare da lumshe idanuwa na Jin dadi da nishadin abinda kaka keyi mata,
"Wai da am fara magana sai ta Kama kukan munafukai..duk kalli wayanda kika girma sunyi aure da yara rututu amma ke sai yawo da gantalin aiki..tou Wallahi kwanan zan nemi wani tsohon in hadaku,,kuma sadaka zan badaki Dan ubanki...kuma Wallahi ko kukan jini zakayi bai hanani cin ubanki duk sanda muka hadu,..in kinga na kyaleki tou Kin fiddo mijin aure...in kuma karuwanci zakiyi sai mu sani..." Wannan Karin very loud mami ta fashe da kuka, afusace suhail ya Mike Yazid yayi saurin rike mashi hannu sai ya fixge yace
"Wai kaka meye haka?.. Ana sayan miji né?.." Ya tambayeta many was very happy with he's confidence but others are sad
"Zauna Dan ubanka..." Mahaifiyar shi Ta fada mashi cikin tsawa Tana mikewa tsaye, kaka baki ta bude face dinta na komawa ja saboda haushi sa bakin ciki
"Kaka In Ana sayan miji ki saya mata...hakan zai nuna kina kau..." Bai karasa ba yaji saukar Mari, ji kake tas kaman an fasa glass, salim né tsaye wato Wanda yaso ya auri  mami tun day one taki shi, duk mikewa akayi, afusace suhail ya rike wuyar rigarshi ya  shakeshi duk aka dauki salati, Kama suhail akayi salim ya Kara daukeshi da Mari yana cewa
"Ni zaka shakewa wuyar Riga?.. " Yafada sounding so piss off sabida akalla ya bashi shekara goma, suhail sai kokarin kwacewa yake yana cewa
"Wallahi Tallahi sai na Rama...in na yarda shege nake...Wallahi Mai raba ni dakai Sai Allah..." Yafada yana kwacewa daga rikon da akayi mashi, duk rigar jikinshi ya yage sabida yanda yake kokarin kwacewa, hajiya Hassana kallo maman mami tayi tace
"Allah yaisa tsakanina dake...kin mallake min da....." Tafada sounding so angry, hajiya rukkaya kam tunda kaka ta fara zagin mami ta sadda Kai kasa Tana kuka Don duk wata take taya yarta kuka, ko kallon hajiya Hassana batayi ba balle ta amsa mata,Baban yazid né ya rike suhail yana cewa
"Kai kana haukane...da wanka zakayi fada?.. Are you mad..." Ya daka mashi tsawa, sai lokacin suhail ya Dan saki jiki idanuwanshi kaman ba nashi
"Wallahi this is not over...sai kaci ubanka Wallahi..." Salim ya fadawa suhail da har lokacin bai bar yi mashi wani irin kallo Mai wuyar fassara ba, kawai he feels like strngling someone, wani né yaso Wanda suke yana yi da shi salim din yace
"What you did was wrong..ya zaayi ka Mareshi...gaskiya you owe him an apology..." Wannan babban mutum dake salki ya fadawa salim,
"Yaya apology fa kace...kana ganin suhail na néman fada Dani kace apology..."
"Yes...Kai kajashi Ai...he's talking to her not you..what kaka is saying is bad..we should be happy he's bold enough to talk to her now apologize..." Senetor Ibrahim Mai waazi ya fada, kaka kam Tana zaune kan kujerar ta, kawai ko uffan bata ce ba, kawai ya jira su gama hayaniyarsu, ita kam mami dafa kunnenta biyu tayi Tana kuka sosai sai shessheka kawai take idanuwanta biyu rufe gam,
"Sorry..." Salim Yafada kaman baiso ya bashi hakuri ba, sai lokacin suhail ya sauke idanuwanshi daga kan salim, Alhaji Muhammad wato mahaifin suhail bai ma Mike ba balle ya saka baki cikin maganar da ake, tamkar ba da danshi ake ba, daman a family dinsu suna da wannan Karan, in Ana wani Abu dangane da danka tou zakayi shuru ka bar saura su yanke hukunci, sai dai in ba manya wajen, Alhaji Muhammad sai karkada kafa kawai yake, hajiya Hassana kam har lokacin da mutane suka fara komawa sit dinsu bata bar fada ba, sai zagi take kasa kasaWai hajiya rukkaya tayiwa danta asiri shiyasa bai ganin girman manya yake mikewa yayi magana just to defend her daughter, dukda an zauna suhail bai bar nishi ba, kawai he's so angry and sad,  mikewa yayi ya Kama hanyar,
"Kai Ina zaka!.." Yaji an fada saga bayanshi bai na gane ko muryar waye ba, amma bai juyo ba,
"Don't you dare step out of here..." Ya sake an fada, takawa kawai yake har saida yazo kusa da inda kaka take ya daga idanuwa ya galla mata harara tare da murmuring witch, baki kaka ta bude Tana kallon ikon Allah, dukda batayi Abunda yace ba tasan he's insulting her,
"Kuma you will be crippled before you die..." Yasake fada idanuwanshi cikin nata, kawai he feels like killing her,
"Wallahi kana fita daga cikin hall din nan you're no more among this family..." Inji first son of the family Yafada, ko juyawa bai yi ba ya fice abinshhi, Yazid gani yayi this s happening because he stood up for he's own blood sister then why will he sit and watch, shima mikewa yayi duk aka kalleshi, yana mikewa wasu cousins dinsu suma biyu suka Mike suka Kama hanyar waje, baki duk manyan wajen suka bude suna kiran yaran su dawo amma basu dawo ba, suka fice, yana Aisha ta Mike tabi bayansu, ataikace bayan fitan suhail kusan 10 members suka fice daga hall din, kaka mikewa tayi ahankali zata fita nan duk yaranta Maza suka zo suna bata hakuri, yau kam she's not harsh like before sabida abinda ya faru surprised her,
"Ban zama waje nan...bai yuwa yan. Yara kanana su nemi su maidani mutuniyar banza..." Tafada Tana kokarin fashewa da kuka, wasu kam adua suke Allah yasa ayi dissolving family meeting kowa ya huta,  suhail na fita ya Kama hanyar gidan wani uncle dinshi Yazid da  sauran family da suka fita Suna biye dashi, 
"Wai Ina zaka?.."  Yazid ya tambayeshi
"Kaya zan saka..haka zan zauna?.." Suhail ya amsa mashi sounding more angry than ever,
"Gaskiya ka burgeni..wannan tsohuwar as been given too much respect that she talks anyhow..yau naji dadi sosai...  " Inji daya daga cikin cousin dinsu, gidan baba usman suka isa kasancewan shi cikin estate yake zaune Sannan danshiu na cikin wayanda ke biye dashi, zuwa yaron ya bude Kofar ya dauko mashi native wear cikin nashi suhail ya maida suka fita, compound din gidan suka koma kowanne da tunanin da yake, cikin hall kam kaka sai kuka take Tana fadin abinda ke cikin ranta, cewa tayi duk su dawo Don tasan if this continues wata rana bazaayi meeting din ba kuma ita batason hakan, wani daga cikin manyan ya fita ya hangesu inda suke tsaye kowa na magana amma Banda suhail, face Dinshi yayi ja,
"Ku dawo ciki dukkan ku..." Mutumin ya fada masu, duk tahowa sukayi Amman Banda suhail dayayi tsaye saboda maganar da big uncle ya fada,
"Bazaka zo bane?.." Mutumin ya fada mashi, ahankali suhail ya bi bayanshi suka koma cikin hall din, zama kowa yayi amma babu Mai cewa komai, bayan kaman minti biyar kaka ta saki ajiyan zuciya tace
"Wato Don Ina am wannan tsohuwar magana Kai Mara kunya da uwarka da ubanka basu Baka tarbiya ba zaka tsaya ya maida min magana?.. Daman kwanaki kazo har inda nake ka zageni...dole zan hukunta ka...zakayi aiki a kampani amma ba'a Baka albashi sai nan da wata uku..." Ta fada atakaice, baki suhail ya tabe, Dan kallon inda mami take yayi yaga har lokacin bata o bude Ido ba sai hawaye yake,
"Sannan kuma na bawa Maryam wata uku ta fiddo miji...in batayi ba zan aurar daita ba driver na..." Tafada atakaice,
"Lallai ma..." Suhail ya fada kanshi kasa,
" ku da kuke ganin Ina matsa mata Ai abun kunya ace yarinyar ta tsufa gidan iyayeta, Don haka wata uku na bata,,in da akwai Mai wani Abu ya fada..." Kaka ta fada atakaice, ahankali baban suhail ya Mike yace
"Maganar auren suhail da humaira...tunda Allah yasa ya dawo sai ki bada izinin ayi masu aure..." Alhaji ya fada as discussed with he's wife, suhail naji Jin haka sai ya kalli humaira yaga ta fashe da kuka, Tana daga Ido ta gan yana kallon ta ta watsa mashi harara tare da murmuring, hannu suhail ya daga alaman zaiyi magana, bai jira an bashi izinin ba ya Mike yace
"Ku tambayeta in bataso kar a matsa mata..." Ya fada ataikace tare da komawa ya zauna,
"Maganar banza...Dan ubanka dole sai an tambayeta...babu wani zancen tambaya..kawai ..." Kaka Bata karasa ba taji kukan humaira da karfi, afusace hajiya habiba mahaifiyar ta ta Mike ta taka zuwa inda humaira take ta dauketa da Mari Tana cewa
"Kukan uban me kike..." Tafada cikin matsanacin masifa
"Lallai ma wannan matsiyaciyar bata da hankali...gabana sai ki Kama dukan yar mutane?.. Lallai zaki ci uwarki..." Kaka ta fada sounding so angry at hajiya habiba, komawa tayi ya zauna Tana fushi sabida tagane dalilin dayasa humaira ke kuka,wato taji maganar aurenta da suhail.

Lets continue some other time
10💚💛💜❤️💙
Lokacine
💛💙💜❤️💚


® zuwairat (ummumaryam)



1️⃣0️⃣


Free page




Kaka sai fada take Tana cewa
"Dan rashin sanin darajan uwarki sai ki Kama dukanta gabanmu?..Wallahi sai nayi maganinki..." Kaka ta fadawa hajiya habiba da har lokacin Tana hucin kukan da humaira take, suhail karkata Kai yayi yana kallon ta, wani irin haushi da takaici yakeji, wato sabida anyi maganar aurensu take wannan kukan, she's showing him publicly, he feels so broken Don tamkar ya Dora hannu bisa Kai ya dinga kuka yake ji, yau is among the hurtful moment of he's life, kaman he's dreaming Don in an fada mashi humaira zata dinga irin wannan kuka sabida maganar aurensu, ahankali ya dafa goshi shi, ji yayi he's head is turning saboda ciwo, humaira sai kuka take da karfi saboda Marin da hajiyarta tayi mata, hajiya Hassana kam ji take kaman ta Shake humaira sabida haushi,
"Mamana..." Kakata ta Kira humaira dake kuka, ahankali ta daga kanta da wet face dinta ta kalli kaka,
"Fadamin meye matsalarki..." Ta tambayeta Tana kallon ta, humaira shuru tayi Tana hawaye,
"Nace ki fadamin damuwarki..in  baki son wannan Mara tarbiya bazan ga bakinki ba...babu Wanda zaisa ki dole...don haka ki fadi abinda ke damunki .." Kaka tafada mata, daga Kai suhail yayi da red face dinshi ya Mike yace
"Nima..." Bai karasa ba hajiya Hassana ta ce
"Kai!!!!.." Ta daka mashi tsawa,
"Wallahi ranka in yayi dubu zai baci...in kara Jin one word from you..." Ta fada cikin tsananin bacin rai, ahankali ya koma ya zauna, amma he's boiling saboda abinda ke faruwa, gani yake it's better shi ya fara cewa bai aurenta da ita ta disgashi,salati kaka ta dingayi Tana cewa
"Yau dai dukkanku shaidan ya sauka gidan nan da ko darajata baku gani kowacce sai haukarta take...Wallahi zakusha mamaki...." Kaka ta fada cikin haushi da takaici abinda akeyi yau,  mami kam tunda kaka ta zageta bata Kara bude Ido ba balle taga abinda ke faruwa, kawai ji heart dinta dake neman fita take, tasan yau da kyar ta iya mikewa daga inda take zaune saboda ciwon  da take ji,
"Ki fadamin mana..." Kaka ta fadawa humaira cikin lallashi, humaira nason magana amma Tana tsoron mom dinta data zuba  mata idanuwa, sai kuka kawai take hannunta kan cheeks dinta,
"Ikon Allah.." Kaka tafada cike da Jin haushin humaira,
"Tou shikenan tunda baki da abun cewa kiyi shuru ko insa ayi maki shegen duka Yanzun nan..." Kaka tafada mata, shuru tayi amma hawaye bai daina zuba ba,
"Yanzu dai na yanke hukuncin zaa hada auren wannan shegen da humaira lokaci guda da na nene..."kaka ta fada, Ai Bata karasa ba humaira ta fara
"Wallahi banson shi,,,ni Yanzu bashi nake so ba..." Ganin hajiyarta ta Mike yasa tayi wajen kaka da gudu Tana kuka, har lokacin bata bar cewa
" Ni ban so...kaka banso..." Tafada Tana boyewa wajen kaka, iyayen Maza wani ya Mike yana cewa
"Humaira kina hauka... Har kin isa ki ce baki auren suhail..." Inji wani kanin abbanta, afusace suhail ya Mike yana cewa
"Wallahi in na aureta shege nake..." Yafada a zuciye, hannunshi Yazid ya rike saboda yanda yake na magana cikin rawar jiki kaman zai fadi,
"Wallahi sai dai ka zama shegen..amma aurenka da humaira babu fashi,,," Inji hajiya Hassana Tafada cikin matsanacin bacin rai, juyawa yayi gareta yana cewa
"Wallahi mom ban aurenta..ko Itace autan mata na hakura..." Yafada face dinshi kaman ba nashi, baki duk suka bude sabida yanda yake magana kaman bashi ba, fada dad dinshi ya haushi dashi kaman zai bugeshi, kaka shuru tayi Tana kallon yanda koina ya kashame da hayaniyarsu har sai da komai ya lafa Don tunda suke meeting ba'a Taba samun tsabani irin wannan ba,  duk yanda take takama da fadanta yau shuru tayi yana kallon su,
"Ya isheku?.." Ta fada cikin bacin rai lokacin da kowa ya samu ya zauna, har lokacin humaira ya kasa komawa wajen zamanta saboda kar mamanta ta zaneta, hajiya Hassana kam kaman ta hadiye zuciya ta mutu, tasan in har kaka tace baayi to shikenan ta zauna, hannu ta daga Sannan ta Mike,
"kaka Dan Allah kiyi hakuri da Rashin kunyar yaran nan..." Bata karasa ba kaka ta watsa mata harara tare dacewa
"Ashe ranshi kunyar yara..ke ba Yanzu kika gama naki haukan ba..dalla koma ki zauna banason ganinki..." Kaka ta daka mata tswa, ahankali ta koma ta zauna gabanta na faduwa Don ba karamin tashin hankali zata shiga muddin akace suhail bai auri humaira ba, ita kadai tasan irin shirin da sukayi da aminiyarta kan maganar auren yaransu, gyarar murya kaka tayi Sannan tace
"Na yanke hukuncin kowa ya nemi Wanda ya dace dashi..." Kaka ta fada atakaice, salati both parents din suka saki saboda tashin hankali, mahaifin suhail né ya Mike yana cewa
"Kaka wannan yaran fa mu muka haifesu..bai taba yuwa ace sai Abunda suke zasuyi...dole subi umarnin mu...ai mu iyayen su né...Don haka kaka kiyi hakuri...kar ki raba aurensu..." Yafada mata Sannna ya koma ya zauna,
"Wai so kuke su kashe kansu?.. Ya zaayi duk basu so kuma ayi masu?.. Ai in kunga anyi to daya yana so amma wannan duk basu so ..wancan shegen am cewa yayi in ya aureta shege yake...gaskiya bazan iya bada izinin wannan hadin ba, Don haka kuyi hakuri...Allah ya bawa kowa rabonshi..." Kaka ta fada,
"Nidai kaka kar ayi ma yaran nan haka..kowa yasan suna kaunar junansu...Don haka ki barsu suyi aure..in sun gandama su kashe kansu..." Inji wani uncle dinsu, humaira dake kuka har lokacin ta fara cewa
"Kaka aa...ni wani nakeso..." Ta fada cikin low voice while crying, kowanne mikewa yayi yana tofa albarkacin bakinsa, ita dai kaka bata yarda da maganar aure ba, shi dai suhail  ya riga yayi mading up he's mind, babu abinda zai sa ya auri humaira, ko me zaayi ba zai aureta ba, she have broken he's heart beyond repair, in an fada mashi humaira zatayi humiliating dinshi haka he will never believe it, Idanuwa ya rumtse trying to control tears dake néman zubo mashi, humaira dake labe bayan kaka ya kalla sai kawai ya fara hawaye,
"Haba meye haka...Dan Allah ka goge kar kowa ya gani..." Yazid ya rada mashi, sadda Kai kasa yayi allowing he's tears to flow freely, yasan in har bai zubda hawayen ba he will land in the hospital, shi kadai yasan irin ciwon da heart dinshi ke mashi. Hajiya Hassana kallon hajiya habiba tayi ta watsa mata harara, kawai jira take su fita daga wajen ta fada mata abinda ke cikin ranta, she hates her so much Don a gabanta humaira ta fara bin wani kuma bata Hana ba despite sunyi planing hada yaransu aure, ita kam duk sanda sukayi waya da suhail abinda take fada mashi is he should always remember humaira the way he remembers her, kar ya kuskura ya bawa wata zuciyar shi sai humaira, amma shine Yanzu zaa mata haka, ba komai take wa takaici ba sai yanda take tunanin hajiya rukkaya zatayi mata dariya wato mahaifiyar mami, ita kam hankalinta bai wajen duk wani magana da suke, kawai kallon mami take taga if she's doing alright Don ba wuya ciwon zuciyarta na iya tashi,
"Yanzu dai zaayi bincike...kan Wanda take so..,indai ba'a ganshi da wata matsala ba dole kuyi hakuri ta auri Wanda take so..,shi kam wancan Mara kunyar yaje chan ya gane..." Inji kaka, wannan maganar ya batawa suhail rai sosai, wato in akayi bincika bai da halin kirki sai a hadashi daita,
"that will be over my dead body..." Yafada cikin ranshi, ahankali ya daga Kai bayan ya goge face dinshi, kiran sallah zuhr akayi duk Kowa ya mike har da Yazid, matan ma fita sukayi don suyi sallah, mami kam ji tayi her legs can't carry her, Tayi kokarin mikewa taga zata fadi dole ya koma ta zauna, kawai she's thinking Yanzu kaka zata aurar daita at her age with her class ga driver dinta, tasan confirm muddin bata kawo miji ba kaman yanda ta bukata she's going to marry her off to her driver, Dan sautin kukanta saki Wanda yasa suhail dake zaune far away from  her kallon ta, he's so sad and angry amma yasan she's more hurt than him, shi ko yau ya gandama zai auri the most beautiful girl around, amma ita fa, she's waiting for a man to come ask for her hand in marriage, ahankali

Please Login or Register in order to submit comment