Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daga kasar waje nake nazo gai..." Still bata Bari ya karasa ba tace
"Allah yasa daga lahira kake tashi ka bani waje..." Suhail zai bude baki yayi magana ta nuna shi da yatsa Sannan tace
"Wallahi Ina da mabuga...daman nasan sai Kai...Wallahi in Baka tashi ba sai in sa aci ubanka..jan banza kawai..." Tafada mashi cikin fada, suhail daga idanuwa yayi ya watsa mata harara Sannan ya Mike, wata sanda dake kusa da ita ta dauka ta wulla mashi yayi saurin kaucewa yana cewa
"I wish you're dead..." Yafada kasan makoshin
"Ka zagi munafukar uwarka da munafukin ubanka...Wallahi kasa na dauki wayata sai ranka ya baci..." Tafada mashi sounding so tensed kaman they're enemies, sai Yanzu nagane abinda yasa mami ke fargabar haduwansu, tsoki suhail yaja ya bar falon,
"Allah ya hadani da Kai...Wallahi zamu hadu...kasan dai da hankalina kuma nasan kaine..." Yaji Tana fada da karfi,  tsoki yaja da karfi tare dacewa
"Kanki akeji..." Yafada da karfi yanda zataji da kyau,
"Kan ubanka akeji...allah ya Kai mu gobe...har gidan ubanka zanzo..." Tafada sounding so angry, suhail fita yayi ranshi bace, yana fitowa wajen gate yazid dake jingine da gate yace
"Hope you're satisfied that you touches the lions tail...Wallahi Yanzu sunan ka sorry indai kaka ce..." Ya fada mashi,
"Kai Wannan tsohuwar is something else...Wallahi har cewa tayi gobe zata zo gidan mu..." Suhai ya fada cikin bacin rai,
"Kuma Wallahi zuwa zatayi...kuma she will make sure tasa dad yayi maka abinda zai faranta mata...kawai shawara muje gidan mu har sai tazo ta koma sai In maidoka gida..." Yazid ya fada mashi yana bude mota ya shiga.
"Aa babu inda zani..." Suhail Yafada yana shiga mota shima,
"Hmmm I think Baka San kaka ba...indai tasan saboda humaira kazo Tana iya hanawa ayi maku aure..Kai ba hakuri ita ba hakuri..so kawai lets go home..in taje ta gama rashin mutunci sai in maida ka gida..." Yazid ya fada yana tada mota, suhail bai Kara cewa komai ba Jin an ambaci zata hanashi auren humaira and for sure yana iyawa, yazid barin gidan yayi ya Kama hanyar gidansu, suna daf da shiga unguwar suhail yace
"Wai Ina SIM card Dina Dana Baka ajiya?.."
"It's safe..." Yazid ya fada mashi yana shiga street dinsu, yana zuwa daidai saitn gidan yayi horn Maigadi ya bude mashi ya shiga yayi parking, bedroom din yazid a kasar bane yake while bed na sauran mutanen gida na upstairs sai part din dad dinsu dake waje, fitowa sukayi suka nufi falo lokacin mom bata dade da saukowa daga wajen mami ba, Tana Jin sallama Ta amsa Tana kallon Kofar, suhail né ya fara shigowa, Tana ganin shi ya saki murmushi Tana cewa
"Sannu da zuwa Dana na Kaina..." Da sauri suhail ya karasa gabanta ya durkusa kasa ya gaisheta amsawa tayi tana Shafa kanshi, yazid né ya shigo ya jefa kanshi kan sofa dake kusa da mom dinshi,
"Ya karatu?.." Ta tambayeshi
"Alhamdulillah mommy..." Ya amsa kanshi kasa
"Wai mum Ina aunty?.." Yazid ya tambayi mom dinshi,
"She's upstairs..." Ta amsa mashi, surprise look suhail yayi masu yace
"You mean anty is still in this house..." Ya tambayesu yana mikewa tsaye farin ciki na appearing a face dinshi because he's so close to her, duk sanda suka samu matsala yazid itace ke sasantasu Sannan she's like their second atm machine da duk sanda sukaji su broke or can't go to bank wurinta suke amsar kudi,
"Yes she's upstairs..." Mommy Ta amsa mashi, da gudu ya Kama hanyar upstairs deep down he's thinking wai har yau batayi aure ba? Because first year daya tafi yana kirashi then she later stopped, yasan dakinta so yana zuwa knocking yayi da karfi kaman yanda ya Saba yi mata, Sam mami batayi tunanin shine ba, she thought it's yazid,
"Go away bacci Zanyi..." Ta fada cikin sanyinmurya, ,sake knocking yayi da karfi ta saki tsoki Tana mikewa zaune cikin cotton rigar bacci dake jikinta, 
"Allah this better be good..come in..." Tafada Tana zama bakin gado, yana bude kofa taga suhail tsaye, da sauri ya shigo dakin yana dariya face dinshi dauke da farin ciki,
"I should have known tunda Allah ya maidoka lafiya..." Tafada Tana dariya, takawa yayi zuwa gabanta ya zagaya hannunshi bayan wuyanta yana cewa
"Auntyna nayi missing dinki sosai,..." Buge mashi hannu tayi tace
"Ashe Kay missing Dina and you don't bother to call me even once..ai shiyasa Nima na daina kiranka...I always ask of you a wajen yazid nasan ku kullum jone kuke, dariya ayi ya zauna bakin gado yace
"Haba anty na,,,ba student nake ba?... Kuma Ai kira daga chan zuwa nan yana cin kudi..." Yafada cikin zolaya, harara ta Balla mashi Sannan tace
"Wato daga nan zuwa chan bai cin kudi kou?..Lallai Dan rainin wayau..." Tafada cikin raha, matsawa yayi kusa daita ya Dora hannu a shoulder dinta yana cewa
"Anty what's up...how have you been?.."
"Am fine...ya kake ha karatun?.." Ta amsa mashi cikin kulawa
"Wallahi anty Alhamdulillah...karatu is over..,next week zan fara aiki .." Juyowa tayi ta zuba idanuwanta cikin nashi bakinta bude tace
"Wow kanina am so proud of you...naji dadi sosai...Allah ya taimaka..." Tafada
"Ameen antyna..." Kofa aka bude yazid ya shigo rike da bowl of salad yana ci,
"Anty Ashe bakiyi bacci ba ko wannan shegen ya tasheki?.." Yazid ya fada yana zama kan stool dake gaban mirror yana kallon suhail da hannunshi ke kan shoulder mami,
"Daman am about to naji kaman zaa ciremin kofa..I was thinking it's you...Ashe shine..." Tafada Tana lumshe idanuwa,  dariya sukayi, hira sukayi kaman minti goma Sannan tayi hamma tare da ture hannun suhail dake kan shoulder dinta tace
"Ku tashi ku tafi I want to sleep..." Tafada Masu, dariya suhail yayi ya Mike taganshi wani zankankan gabanta tace
,"wai Kai Ina zaka Kai tsawo?..ji yanda ka karayin tsawo.." Tafada mashi, dariya yayi yace
"Kai anty mami ko kafin in bar kasar nan da tsawo na Ai..."
"Yes I know..amma Yanzu kafi da...you that is very small lokacin..." Dariya duk sukayi suhail yace
"Anty wallahi kin fiya son girma..kina magana kaman yarintar mu...alhaji duk kusan tare muka taso..." Bai karasa ba ta dauki wata small pillow Mai shape din heart ta jefa mashi yayi  grapping yana dariya
"Ai gaskiya na fada..." Yafada mata yana kallon yanda take hararanshi
"Kun Raina min wayau..wai tare muka taso daku...ku da har na shiga secondary kuna yawo da majina..." Bata karasa ba yazid yayi saurin ajiye salad dake hannunshi yana cewa
"Shikenan ban Kara ci..ya fita Raina da Jin majina..." Yafada yana goge bakinshi, dariya suhail yayi yace
"Rabu da anty...kawai Tana fada né Don taji dadi..." Kai mami ta girgiza ganin zasu Raina mata hankali
"Naji ku tashi ku tafi...I want to sleep now..," mikewa yazid yayi Don daman suhail na tsaye rike da heart pillow da mami ta jefeshi dashi, takawa suhail yayi ya ajiye mata pillow din Sannan yace
"Anty sai da safe..." Shima yazid yace mata same thing, hannu ta daga masu Tana cewa
"Allah ya kaimu.." Tafada masu Tana mikewa,
"Bari in cinye tunda ka koshi...," Ta taka zuwa gaban mirror ta dauki bowl da yazid ya ajiye,
"Daman you did that on purpose..." Yazid ya fada yana ficewa daga dakin, shima suhail fita yayi yana tunanin why is he's favorite cousin sister not married yet, suna sauka suka ga mom ta bar falon, zama sukayi yazid ya kuna kallo, suhail shuru yayi yana kallon waje daya for a moment Sannan yace
"Wai besty tunda na tafi anty batayi aure ba?.." Ya tambayeshi cikin sanyinmurya, ajiyan zuciya yazid ya Saki Sannan yace
"Wallahi har Yanzu anty shuru..."
"Inna lillahi wa'ina ilaihi rajiun...amma gaskiya am disturbed,,,ya zaayi ace nice woman kaman anty ta rasa mijin aure?.. Kodai something is wrong?.." Ya fadawa cikin damuwa,
"Allah kadai masani...physically nothing is wrong gaskiya....amma wayasan ikon Allah?.." Inji yazid, shuru suhail yayi damuwa na rubuce in his face
"Gaskiya am not happy...am not happy at all...inda Ana siyan miji I will use all I have got to get her the best of them all..amma sai gashi ba'a sayarwa...Allah sarki antyna...I pity her Wallahi..." Suhail Yafada kaman zaiyi kuka,  wata ajiyan zuciya yazid a sake saki Sannan yace
"The worst part is next two months auta zatayi aure...and the most annoying is kaka is on her nerves..." Inji yazid
"Pls forget about that old woman let's say something important Wai you mean auta ma getting married?.."  Suhail ya tambayeshi cikin babban tashin hankali
"yes oo...she's getting married...Yanzu anty kadai zata rage nan gidan tunda Nima bazan Kai one gaba banyi ba..."
"No,,,Insha Allah..in Allah ya yarda anty zatayi aure soon...kawai muyi mata adua..let's pray for her morning and night..." Inji suhail , Dan baki yazid ya tabe yana cewa
"Sai kace wani malami...har saudia an  biya an Kai malamai sunyi mata adua ballekai..." Tsoki suhail yaja yana cewa
"Ai adua bai yawa...kawai lets continue praying..Wallahi it hurt me so much to see her like this...Wallahi da ganin idanuwanta dazun kaman tayi kuka..." Suhail ya fada sounding so disturbed, shuru yazid yayi tare da relaxing yana kallon movie da akeyi, suhail lumshe idanuwa yayi yana wetting lips dinshi da saliva dinshi yace
"Good people always suffer...while bad people are somewhere enjoying themselves..." Suhail ya sake fada, juyowa yazid yayi yace
"Pls ka bar maganar mana..ka rike magana daya sai maimaitawa kake..."
"Wallahi you won't understand how am feeling...anty is a good person that should not suffer lack of husband...Allah am so disturbed..." Yafada kaman zaiyi kuka, ajiyan zuciya yazid ya saki tare da closing eyes dinshi for about two seconds Sannan yace
"I know anty is extra good...amma ya zamuyi tunda haka Allah ke son ganinta...itama she's handling it well..she don't complain about it...muma sai muyi shuru mu zubawa sarautar Allah ido..." Yazid Yafada mashi, zama suhail yayi yana kada legs ahankali sai kuma ya ja tsoki ya Mike ya Kama hanyar dakin yazid, yana shiga ya tube ya shiga bathroom ya watso ruwa ya fito daure da towel, falo ya fito daure da towel yace
"Kai zo ka bani SIM card Dina..." Ya fada mashi Sannan ya juya ya koma ciki, mikewa yazid  yayi ya bi bayanshi ya shiga ya dauko mashi SIM card
"Hope Baka Bari wannan mtn sunyi blocking layina ba..it's a special line ka sani..." Inji suhail, tsoki yazid yaja yana cewa
"Ina using layin time to time.." Yazid ya fada Sannan ya fice daga dakin, suhail kwanciya yayi daure da towel ya bude wayarshi yana saka sim ba Don komai ba sai Don yayi magana da humaira.
4💙💜💛❤️💚
Lokacine
💚❤️💙💜💛


® zuwairat (ummumaryam)



4️⃣



Free page


Bayan ya gama saka SIM card dinshi ya kunnna wayar yayi dailing number humaira daya yi saving da mairacutie, yana dailing yaji busy, tsoki yaja yana cewa
"Who's she calling by this time..." Yafada cikin baci rai., still trying yayi  still busy,
"Wai wa take Kira né haka..." Ya sake fada sounding so angry, ajiye wayar yayi har wajen minti goma ya sake Kira still busy, ji yayi he's heart is beating very fast saboda ki shi, ya dai San ba mace yaruwarta mace take Kira ba, the most annoying thing is bayan an fada mata busy zaiyi ringing har ta tsinke bata holding call dinta tayi mashi magana, dailing ya sakeyi still she's on another call, haushi yaji ya wurgar da wayar ya fito falo daure da towel, yazid dake kallo juyowa yayi ya kalleshi yaga yanayin shi ya sauya
"What's up?.." Ya tambayeshi, zama suhail yayi ya dafa goshinshi yaja nishi kaman Dan race, he look so angry and piss of,
"badai anyi blocking layin ba..." Yazid ya tambayeshi,
"Da yafi min sauki.." Suhail Ya amsa mashi cikin bacin rai,
"Then what's happening.." Yazid ya tambayeshi ya zura mashi Ido yana kallon yanda jikinshi ke salki kaman na mace, daman tun asali suhail Dan kwalisane, he's so classy da ko mace bata nuna mashi komai, yanda yake kula da kanshi ba kowacce mace ke kula da kanta haka ba, he gives time for everything, he's hair is he's major concern, then he's skin, amma duk class dinshi bai Wulakanci, he's straight forward and simple but he's a no nonsense person,
"Dan Allah kayi magana mana sai wani kada Kai kake kaman agama lizard..." Yazid Yafada mashi, ajiyan zuciya ya saki yana cewa
"maira Tana son Dora mun hawan jini..."
,"What happened " Yazid ya tambayeshi, daga idanuwa suhail yayi yace
"Am about talking for crying out loud..." Yafada yana zaro idanuwanshi dake kaman white paper Sannan yacigaba dacewa
"Yazid maira na son kasheni...I have been calling her line busy...Wallahi am having a cause for concern..." Yafada kaman zaiyi kuka,
"Kai matsala gareka Wallahi...daga ka kirata kaji  busy sai akace wani Abu take?.. Calm yourself down mana..." Yazid ya fada mashi cikin kwantar da murya
"Ba dole hankalina ya tashi ba?... Who knows is an rudeta...those stupid gold diggers sun hure mata kunne...Wallahi if anything happens to relationships Dina da maira mutuwa zanyi..." Yafada white eyes dinshi na sauya kala, ahankali Yazid ya mike daga inda yake zaune ya koma kusa da suhail ya dafa shoulder dinshi yana cewa
"Haba besty..stop disturbing yourself for nothing mana...babu Wanda zai raba relationship dinku...kawai you're kishine ke damunka..." Suhail relaxing yayi ya Dora Kai saman kujera yana sakin ajiyan zuciya
"Allah Ina Jin heart Dina kaman zai fita...am so angry Wallahi...I wonder abinda suke cewa...kilan ma Saurayin ta né..." Bai karasa ba yazid ya katse shi dacewa
"Please be positive mana...kadai San your happiness lays with humaira and hers lays with you...so ka bar damun kanka..kilan ma wayar da take is not something important..." Yazid ya fada har lokacin hannunta na kan shoulder dinshi, idanuwa suhail ya lumshe yana wetting lips dinshi da saliva dinshi Sannan yace
"Try and call her ka gani...kilan she's still on the phone..." Suhail Yafada cikin tsananin bacin rai, Yazid mikewa yayi ya koma inda ya taso ya dauki phone dinshi yayi dailing number humaira, few ringing tayi piçking, sallama tayi mashi ya amsa tare da saka wayar hands free, amsawa yayi Sannan yace
"Sister how far?.." Yafada mata idanuwanshi cikin na suhail daya kura mashi Ido
"Fine yaya..pls yaya kuna tare da yaya cutest?.. He has been calling kuma Ina waya da wacce muke project tare...Yanzu Ina kokarin kiranshi he's line is not going through..." Tafada cikin calm voice, Yazid zai bude baki yayi magana sai yaji an kwace wayar daga hannunshi, suhail né ya amshe wayar har towel dake waist disnhi na néman kumcewa, dariya yazid ya yayi yana cewa
"Crazy fellow kawai..."
"Wayyo maira kin kusa saka mun hawan jini yau..." Yafada mata yana komawa cikin dakin hannunshi daya rike da towel dake néman faduwa Sai Dayan rike da wayar, yar dariya humaira tayi Sannan tace
"Why yayana?.." Ta tambayeshi cikin sexy voice, mika suhail yayi yana cewa
"Wallahi I was about going crazy Dana kira naji busy...baby da wa kike magana?'"
"Yaya da Wacce  muke project ce..sorry yayana..." Ajiyan ya saki yaja kwantawa kan gado yace
"Now am happy...baby yau munsha drama da kaka..I went there amma banda ruwan rashin mutunci babu abinda ya zuba min..." Yafada yana dariya, itama yar dariya tayi before saying
,"drama queen kenan..ai halin kaka kullum Kara worst yake...ni Wallahi har banason karshen wata yayi saboda ita,,,I don't want to see her at all..." Tafada Tana dariya, shima dariya yayi yace
"shiyasa muke same team...Nima I hate her...halinta baiyi ba...am sure ba haka sauran grandparents dinmu suke ba...mutuwa ta dauke mana masu kirki ya barmu da wannan Allah kakai..." Yafada yana dariya,
"Hahh yaya ace Yanzu taji kace mata Allah Kakai..Tana iya sawa a koreka daga cikin Mai waazi family..the most annoying thing is kaman ta shanye parents dinmu..komai tace shi sukeyi,,," tafada sounding angry,
"Hmmm Ai nasan gobe da akwai drama gidanmu Don dazun naji tana cewa sai taje gida gobe..shiyasa na bar masu gidan na dawo gidan su Yazid..." Ya fada mata,dariya tayi da karfi tace
,"yayana matsoraci..."
"Ai wannan matar abar tsoroce..." Yafada yana gyara kwanciyar shi, shuru né yadan biyo baya Sannan yace
"Maira I love you..I don't know what will become of me if I don't have you..." Yafada mata cikin Chanjin voice, yar dariya tayi tace
"yayana kenan..." Tafada mash kawai, he was angry at her response but pretend not to care
"Baby you're the missing part of my rib..Allah without you am incomplete...Dan Allah baby Don't break my heart..." Yafada kaman zaiyi mata kuka,
"Yayana ka zama poetic...it sounds sweet..." He wasn't expecting that as an answer but h
Still he maintains,
"baby na...I can't wait mu hadu wajen meeting in fadawa kowa it's time for us to get married...all baby I can't wait anymore...am so eager to be with you ..." Yafada cikin voice da ba kowa zaiji ba sai humaira an me that is standing writing,
"Wayyo yayana...nidai in kana yiwa Allah kayi hakuri har sai na gama...duka sauran one year fa..." tunda tayi wannan maganar yaji ranshi ya baci, shuru yayi yana girgiza Kai kaman Wanda akayi remoting
"Yayana..." Ta kirashi Jin he didn't reply her,
"Naam..." Ya amsa mata atakaice,
"Wallahi yaya na zamu fi Jin dadin aure in na gama karatu...I don't have to be going out kullum..iyaka in zauna gida in kula da Kai..." Jinta kawai yake saida ta gama Sannan yace
"Hmmm maira you're surprising me...wato inyi hakuri har nan da one year muyi aure...baby indai Don kula Dani né kar ki damu... I promise I won't complain...kawai let's be together..if you like ko first night kar muyi har sai kin gama karatu if you're scared of pregnancy...kawai all I want is in ganki at anytime tare dani...kuma next week Nima zan fara zuwa office...kinga ba'a gida zan zauna ba har kiji kin bar angonki gida...nidai pls karki Kara..." Bai karasa ba tayi saurin cewa
"abokiyar project Dina is calling..let me get back to you..." Ta fada mashi atakaice, zai bude baki yayi magana sai dai yaji an kashe,
"Kan uban nan...this girl is up to something...Lallai ma  humaira Yafada cikin bacin rai while sitting up, yafi minti talatin yana dailing number yana ringing but busy
"who ever is wannan Mai project din she's more important than him
"That's if she's a she..." Yafada yana kashe wayar, kwanciya yayi yana aduar Allah yasa it's not what he's thinking Don in har wani né wannan sai ya samu matsalar zuciya, haka dai ya kwanta yana sake sake har bacci ya daukeshi baisan na lokacin Yazid ya shigo dakin ba,

The following day tunda asuba sukayi sallah kowannen su ya dawo ya kwanta amma Banda mami, Tana idar da sallah tayi azakr dinta tare da néman Allah ya biya mata bukatunta na alkhairi ta sauka downstairs ta shiga kitchen ta dora indomie guda biyu on low heat saboda tasan shima Yazid zaici kafin ya tafi office upstairs ta koma ta shiga wanka, da sauri ta fito kanta daure d towel, kaman kullum tasan her noodles will be ready ta sauka daure da towel tayi saurin shiga kitchen ta sauke ta fita da gudu ta hau upstairs, Baka Jin mostin kowa falon sai nata, Tana hawa ta saka Kaya ta shirya tsaf Sannan ta fito  ta shiga dakin mom dinta, sallama tayi mom dinta dake kwance kan praying carpet sanye da hijab ta Mike zaune
"jewel sai tafiya kou?." Ta tambayeta,
"eh mommy Ina kwana?.."
"Alhamdulillah...tou Allah ya kiyaye hanyar..."
"ameen mom...zan sauka in ci abinci I have surgery by 8:30..." Tafada Tana takawa zuwa bakin kofa
"Tou all the best...a dawo lafiya..." Ta fada mata, amsawa mami tayi Sannan ta fice daga dakin,  zuwa dakin Aisha datayi baje Tana bacci, kiss mami tayi mata ta jawo mata blanket Sannan ta fice zuwa downstairs, yayinda take kan dining shima Yazid yana ciki yana shiryawa, suhail dake kwance sanye da jallabiyar Yazid sai tsoki yake yana cewa
,"Duk ka hana mutum bacci Wallahi..sai motsi kake kaman wani bera ..." Yafada idanuwanshi lumshe, dariya Yazid dake daura tile dinshi yayi yana cewa
"Ai kaima next week zakayi kaman beran ne...tunda dole ka tashi da wuri while working in the family company...in ba haka ba kaka ta  kwace maka albarka..." Tsoki suhail yaja ya na mikewa zaune
"Allah har baccin ya isheni da ka Kira sunan kaka..." Yafada yana murza idanuwa, yana zaune yana kallon Yazid har ya gama shiryawa, brief case ya dauka ya kalli suhail that look weak yace
.."dalla malam tashi ka rakani..."  Suhail baice komai ba ya Mike yana hamma tare da salati suka fito falo, lokacin har mami takusa gama cinye Dan indomie data zubo sai gefen ta hot tea né Mai kaurin gaske, suhail na ganinta ya saki dariya yana nufo dining din yana cewa
"Anty wannan early feeding din baki Bari garin Allah ya waye?.." Yafada cikin zolaya, dariya mami tayi ta Kai cup bakinta, saida ta kurbi tea din Sannan tace
"Ai aiki zani...kuma I won't have time for myself in naje office..so dole in  Dan saka wani a ciki na kafin in tafi..." Tafada not looking at him, dariya yayi yace
"anty bakinki zai kone mana..." Ya sake fada mata, daga idanuwa tayi ta watsa mashi harara Tana cewa
"Ka maidani kakar ka kou.?.." Ta fada Tana hararanshi da sexy eyes dinta, zai bude baki yayi magana sai ga Yazid ya dawo da plate dinshi daga kitchen zama yayi yace
"antyna good morning..." Yafada cikin respect kaman bashine Mai bimata ba,
"Morning sweet brother..how was your night..." Ta tambayeshi Tana sipping tea dinta Tana kallon  expensive wrist watch dake hannunta,
"Antyna good morning..." Shima suhail ya fada, idanuwa ya sake dagawa ta galla mashi harara Tana cewa
"Morning..." Aikam sai ya fara buga kafa kasa kaman wani karamin yaro yana cewa
"Daman ni bakisona..shiyasa kirikiri kike nunamin banbanci..." Yafada kaman zaiyi mata kuka, baki ta tabe tace
"Ai shi ba Raina min hankali ba..Kai kam kana fitowa ka fara ce min ina loma da sassafe..."
"Tou ban karawa..." Ya fada mata cikin rarrashi,
"Tou naji.." Tafada cikin sauri as in she's in a haste,
"Antyna good morning..." Ya sake fada mata, dariya both Yazid and Maryam sukayi Sannan tace
"Morning my sweet brother how was your night..." Tafada Tana mikewa,
"You will never change..." Inji yazid shima yana cin abinci cikin sauri, cup dinta ya dauka da plate ta nufi kitchen, shikam suhail bin ta yayi da kallo Yana tunanin haka nan ya damu kanshi kan rashin aurenta but she don't look disturbed at all, Tana shiga kitchen ta ajiye ta koma  falo ta nufi dining table sai sauri take ta dauki bag dinta looking so smart and beautiful, suhail sai bin ta  kawai yake da Ido, he admires her a lot,   Zata bar dining din Yazid yace
"anty yau na Jin mance bakiyi min ba..." Yafada mata yana wani turo baki kaman karamin yaro, idanuwa tayi rolling ta dawo kusa dashi ta daga jaw dinshi tayi mashi kiss, wajen suhail taje shima ta daga jaw dinshi tayi mashi kiss a jaw Sannan ya bugi keyanshi ta fice abinta, bayanta yabi da kallo yana cewa
"I love anty mami so much...she's so cute..." Yafada yana murmushi, shima Yazid mikewa yayi yana cewa
"Who wouldn't love personality like her..kaje hospital da take aiki kasha mamaki...har mutane sun  gane in Baka da kudin magani kazo hospital zata yi treating dinka kyauta...har surgery wasu free take masu...my sweet sister is one in a million..." Yafada yana mikewa
"My very own anty kenan..." Suhail ya fada cike da Jin dadi, Yazid hanyar upstairs yayi suhail na biye dashi, dakin mom suka shiga suka gaisheta Sannan  suka fita yazid ya shiga motar shi ya bar gidan shi kuma suhail ya koma dakin ya baje kan gado sai bacci,

A gidan kaka kam duk tasaka maigadin ta Hana kowa shigowa gaisheta Wai a fada masu unguwa zasu, duk Wanda yazo gaisheta yaji Abunda Maigadi yace sai yayi corner Don in har kayi gangancin shiga ciki sunanka sorry. Wajen 8:30 ta gama shiryawa cikin super exclusive Wanda yasha dinkin doguwar riga ta fito face dinta dauke da medical glasses sai hannunta rike da wata modernized walking stick, daman already driver dinta na tsaye yana Jiran fitowanta, da gudu ya bude mata kofa shige yaja motar bayan ta fada mashi inda zai kaita, akan hanya kaka sai zagi kawai take Tana cewa
"Zanga ubanda ya tsayawa wannan Jan yaron..." Ta fada Tana hakimcewa, yan go slow ma bata barsu a baya ba, Tana cikin zagi har suka isa gidan alhaji Muhammad wato mahaifin suhail, horn driver yayi da karfi bisa umarninta Maigadi yazo ya

Please Login or Register in order to submit comment