Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta, ta zo ta kunna fitilar dakin wanda hasken ya sa dalibai da yawa suka tattashi har Kulsumu. Muskutawar nan da Kulsumu za ta yi ta ji ta cikin lema, sannan cikin dan kankanin lokaci kwakwalwarta ta soma harhada mata abin da ya faru. Jikinta ya yi balain sanyi, tare da wani irin faduwar gaba da ya same ta duka a lokaci guda. A lokacin da ta jiyo muryar siniya Rabia tana fadin, wallahi ta gama zama a makarantar nan, yau aljannu sun mata fitsari a baki ta shanye, sai ta rushe da kuka, Metron da yan dakin me za su yi in ba dariya ba. babu wanda ya bai wa zancenta muhimmanci, haka ta karaci kukanta ko kusa hankalinta bai ba ta fitsarin mutum ba ne, balle ta yi tunanin Kulsumu ce ta yi mata shi a baki ya ratso daga katifarta sabida yawansa ya shiga bakinta. Duk da cewa kuma a washegari ba ta yi fitsarin ba, don ba ta yarda bacci ya dauke ta ba. akai-akai ta ke zuwa bandaki ta kakalo shi ko da ba ta jin yin sa ta yi shi, fargaba da tsoro ba su bari ta samu ta runtsa ba sai gefen asubahi.
Daga ranar Kulsumu ba ta kara bari ta yi dogon bacci ba, sannan ba ta fidda katifarta ta shanya ba, don tsoron kada wani ya gane. Haka ta ke buya a bandaki ta yi kukanta mai isarta. Ta sani duk ranar da wani ya gane tana fitsarin kwance karshen zamanta a makarantar kwana ya zo duk son da ta ke ma karatunta. Tun daga ranar Kulsumu ta shiga wani hali na damuwa da janye jiki daga mutane, karatun ma ba ta fahimtarsa sosai. Ba ta iya cin abinci sosai, duk ta rame ta yi wani haske fayau, ta bushe a tsaye. Allah-Allah ta ke ranar visiting ta zo Allah ya kawo mata Goggo, ta gaya mata farin cikinsu ashe ba mai dorewa ba ne, ashe fitsarin kwance bai barta ba, ashe har abada ba za ta daina fitsarin kwance ba???
Kafin ranar visiting Kulsumu ta gama fyadewa, domin kuwa ta kara yin fitsarin kwance ya jika Siniya Rabia sharkaf! A wannan ranar ne Metron ta zo har kwanar gadonsu don ganin ta ina fitsarin aljannun ke taba Rabia. Rabia na gefe duk ta firgice sai digar fitsari ta ke. Kulsumu da ta farka ta fahimci abin da ya faru ta makure a kan gadonta ko kwakkwaran motsi ta kasa. Hawaye na malala daga gefen idonta. Metron ta leka koina ba ta ga komai ba, kamar an ce ta kai hannunta kasan gadon Kulsumu sai ta taba ta ji lema. Ta kama baki ta ce,
Yanzu yar nan da girmanki haka ki ke fitsarin kwance? Yau na ga abin da ya ishe ni ni Aminatu.
Kulsumu ta saki kukan da ta ke ta makalewa, shi ke nan yau ranar fallasarta da wulakantarta a duniya ya zo. Yan dakin suka hada baki cikin mamaki a lokaci guda suka ce,
FITSARIN KWANCE???

*** *** ***
Tun daga wannan ranar rayuwar walwala da farin ciki ta tsayawa Kulsumu a makarantar nan. Sosai yan dakinsu suke nuna mata kyama da hantara, ba mai zuwa inda ta ke, ba mai cin abinci tare da ita. Siniya Rabia da ke sonta a baya ta koma kyamarta da hantararta, da Kulsumu ta doso zata kai hannu ta toshe hanci wai zarni, ta kwashe kayanta daga kwanar ta koma can farkon dakin. Har a ajinsu wata yar dakinsu ta kai labarin fitsarin kwancen ta. Da an ganta sai a ce, Ga mai fitsarin kwance nan. Sai a bushe da dariya. Ta zama kamar wata mujiya a aji da hostel da duk wata mahadar dalibai. Ta yi zuru-zuru ta rame don damuwa da sanya bakin ciki a rai. Haka a daddafe Kulsumu ta samu ta kawo ranar ziyara a Yargaya, ranar da ta ke Allah-Allahn zuwanta don kawai ta ga Goggonta, ta roke ta a cire ta daga makarantar, kada ciwon damuwa ya kama ta.
Don haka ranar visiting ita ce farkon fita bakin get inda dalibai ke tsayawa don tarbar iyayen su. Ba jimawa aka bude get din makaranta iyaye da yan uwan dalibai suka fara shigowa. Kulsumu sai ware ido ta ke a kan duk mai shigowa don ganin ta inda Goggo za ta billo. Ba jimawa kuwa ta hango ta niki-niki da kayayyaki, Kulsumu ta ruga ta rungume Goggo ta saki kuka mai tsuma rai. Goggo ta bambarota daga jikinta tana dubanta ta ga yadda ta rame ta lalace, hankalinta ya yi matukar tashi. Kafin ta ce komai Kulsumu cikin kuka ta gaya mata fitsarin ta ya dawo, kowa ya san tana fitsari a makarantar, kowa hantara da kyamarta yake yi.
Hankalin Goggo in ya yi dubu, to ya tashi, da kyar ta samu ta lallashi Kulsumu ta ce ta yi hakuri har a yi hutu za ta fada wa Baffa a san abin yi kafin ta dawo. Ta lallashe ta ta ci abincin da ta kawo mata ta koshi, ta bude mata robar Yoghurt ta bata. Lokacin da Goggo Shatu ta bar makarantar ko gabanta ba ta gani sabida tashin hankali. Ta zo ta fada wa Baffa komai.

Wannan ne mafarin barin Kulsumu GGSS Yar gaya, ta dawo jeka-ka-dawo a GGSS Gaya. Goggo Shatu ba ta zauna ba ta ci gaba da fafutukar nema wa jikarta magani ganin cewa kullum kara girma ta ke yi. Kulsumu ta taso da damuwar lalurar fitsarin kwance a ranta, wanda ya canza halayenta gabadaya. Ya cire mata walwala. Ya sanya ta tsanar kanta. Ya hana ta shiga cikin tsararrakinta. Ya haifar mata da alienation da inferiority complex. Damuwar Goggo Shatu a kullum shi ne, kada hakan ya taba lafiyar zuciya da kwakwalwarta, domin wani lokacin zama ta ke cikin dare ta hada kai da gwiwa tana kuka, ta ki yin barci duk don kada ta yi fitsari, amma barcin na sace ta ko na awa daya ne za ta farka jike sharkaf. Baffa da Goggo na iya kokarinsu a kan lalurar Kulsumu, duk inda suka ji mai magani sai sun je amma wajen garin Gaya kadai sabida tsoronsu na kada zancen ya fita. Ko Malam Hadi bai san halin da Kulsumu ke ciki ba, lokacin da take wajen mahaifiyarsa Iyatu ya san tana yi amma bai taba kawowa a ransa ya zarce har girmanta ba, ya ga dai ta sauya ta daina walwala. Da ya tambayi baasin dawowarta jeka-ka-dawo Goggo ta ce ita ce ba ta so (Goggon), bai tsawwala ba, amma kwarai ya so Kulsumu ta ci gaba da karatu a makarantar kwana ko don ta san rayuwa ta kuma koyi yin komai da kanta. Gatan da kakanninta ke nuna mata ya yi yawa, kwata-kwata ba ta da wayo irin na tsararrakin ta. Amma fa tana da manyance irin na zama da tsoffi.


Wata ranar Asabar Kulsumu ta dawo daga Islamiyya, ta cire hijabin ta ta sakale shi a kan kofa, juyawar nan da zatayi taga wasu kyawawan jakunkuna dindima-dindima bakake wuluk Gwaggo ta jingine su a gefe. A hankali ta matsa tana shafa jakunkunan, daidai lokacin da Goggo a shigo dakin hannunta rike da kwano, ta mikawa Kulsumu kwanon wanda ke cike da farfesun kayan ciki, ta sunto habar zanin ta ta ciro kudi ta ce "ungo hamsin kije wajen Sa'idu mai shayi ki amso biredi ki hada ki ci, yau gidan namu cike yake da albarka".
Da mamaki Kulsumu take duban Goggo, don hatta dakinsu kamshi yake yi mai dadi. Ta karbi kwanon da hamsin din daga hannun Goggo tana tambaya a mamakance.
"Goggo wadannan kayan daga ina haka?"
Goggo ta jawo jakunkunan tana budewa. Kulsumu ta kwalalo ido tana shan kallo, atampopi ne manya da shaddoji bandir-bandir da dogayen riguna na 'yammata, ga sabulai sunki-sunki, turaruka da mayukan shafawa irin wadanda Kulsumu bata taba gani ba. Mamakinta ya karu lokacin da Goggo ta dauko wani ambulan ta nuna mata, kudi ne a ciki sababbi fil amma ba irin na kasar nan ba.
Kulsumu tace "Goggo daga ina haka?" Idanunta a warwaje. Goggo tayi murmushi tace "Sako ne daga 'ya ta Nasara, ai na sha baki labarin Nasara diyar Yaya ta Yakumbo Sa'a wadda ke aure a kasar Landan ko?" Kulsumu ta gyada kai "Eh, kina gaya mini, Babar su Sakinah ko?" Tace "to ita ce ta aiko mana, dama ta kan yi min aiken kudi lokaci-lokaci in ta samu mai zuwa Nigeria. Wannan karon kuma kin ga har da kaya fal, tace duka namu ne".
Kulsumu cikin farin ciki tace "shikenan mun samu kayan sallah, bana Baffa ya huta saya mana atamfar idi" ta daga daya daga cikin atamfofin tana karawa a jikin ta. Ta ajiye ta dau doguwar riga tace "Goggo wannan zata yi miki kyau amma tayi miki tsayi" Goggo ta kama baki tace "ina ni ina saka wannan rigar Kulsumu? Ta ce duk rigunan naki ne, shaddojin kuma na Baffa, ni cikin atamfofin zan dinka wasu, sauran duk na bar miki kiyi ta cin kwalliyar ki, don ma dai ba kya son shiga mutane" Kulsumu tace "Goggo kwalliya ai ba don shiga mutane kawai ake yin ta ba, kayi abun ka ma a gida dadi zaka ji a jikin ka. Kai wannan Yaya Nasara Allah yayi mata albarka". Goggo ta amsa "Amin-amin, Nasara ai 'yar albarka ce, ko don saboda zumuncin ta".
Tun daga wannan ranar Goggo ke yawan baiwa Kulsumu labarin diyar Yayarta mai rasuwa, Nasara, tace ita ta yaye ta a nono, har dabdalar kuruciyar Nasara da auren wuri da akayi mata a Kano kafin su tsallaka su bar kasar Kulsumu ta haddace tsaf, tace sama da shekaru ashirin kenan rabon su da ita, tsakaninsu da ita sai dai aike idan ta samu mai zuwa Najeriya, mijin ta ne ma'aikacin matatar man fetur na kasa wato (NNPC) aka turashi wata kasar Turai shikenan basu kara zuwa gida ba, iyayen Nasara duk sun rasu, a dangi Goggon kadai ta rage mata, don haka Nasara bata yada Goggo ba, muddin ta samu mai zuwa Nigeria sai ta yo mata aiken kudi wanda zata dade tana kashewa.
Washegari Baffa ya tafi Kano ya canzo kudin a wafa, da aka basu a kudin Nigeria yawan kudin ya tsorata su, Goggo tace Baffa ya sayi Shanu kawai ya kara a tumakin da yake yi musu kiwo a gonar sa. Sai su ciri wani abu su yi hidimomin gaban su kawai.

Ranar wata alhamis da yamma, Kulsumu ba ta da islamiyya, tana kwance tana tunani a kan rayuwarta, tunanin ta dai a kullum guda daya ne "yaushe ne Allah zai raba ta da wannnan lalura? Yaushe zata daina fitsarin kwance? Shin lalurar ta mai warkewa ce ko kuwa ta har abada ce? Inama zata samu wanda zata iya yiwa wannan tambayar?
Daga kwancen da take ta ga Goggo na shiryawa da alama fita za ta yi, ta dauko sabuwar atamfarta ta can kasan akwati cikin kayan da Nasara tayi musu ta sanya, sai da ta gama shiryawa tsaf ta juya ta dubi Kulsumu ta ce,
Zan je gidan Sarki na duba Hajiya Rakiya, ba ta da lafiya. Yanzu zan dawo, ke da wata mai kuzari ce da kin dora min miyar dare kafin na dawo, amma kina nan kwance kamar ruwa kina tunanin da ba zai amfane ki ba. Komai ya faru da bawa da sanin Allah. Kuma komai Allah ya dora maka Yana sane da kai, ba kuma don ba ya sonka ba ne ya dora maka sai don ya jarrabi imaninka. Ki kwarara imaninki ki daure zuciyarki Kulsumu, ki yi rayuwar farin ciki kamar kowa. Wannan damuwar babu inda za ta kai ki sai dai ta cutar da ke, ta haifar miki da ciwon da ba mu da maganinsa. Ki bar mu mu ji da abu daya. Ni zan tafi sai na dawo, idan na ga gurjiya zan sayo miki.
Kulsumu na son Gurjiya dafaffiya tun tana karama, shi ya sa Goggo ke yawan dafa mata. Ta mike zaune daga kwancen da ta ke, ta bude kwabar kayanta tana fadin.
Bari in canza kaya in bi ki Goggo, bana son zama ni kadai.

Gidan Sarkin Gaya babban gida ne mai sassa daban-daban. Yana da mata hudu da kwarkwarori, yayan Sarkin Gaya mai ci a lokacin duk mata ne, namiji daya ne kuma babba a dakin Hajiya Rakiya. Hajiya Rakiya ita ce matar Sarkin Gaya ta biyu, asalinta 'yar garin Gombe ce, kasuwanci ne da neman abinci ya kawo iyayenta Kano, suka yi muhalli a garin Gaya, kawar Goggo ce tun yammatancin su, haka aure da ta yi a gidan Sarauta bai raunata amintarsu ba, bai sa ta watsar da Goggo ba. Lokaci-lokaci tana aiko 'ya'yan ta su gaisheta kuma tana yi mata aiken abin arziki, sannan tana gayyatarta duk wani shaani na yayansu in ya taso.
Lokacin da Goggo da Kulsumu suka iso kofar gidan, samari ne a zazzaune sun yi da'ira tare da dan Sarkin Gaya, kamar yadda suka saba a kowane yammaci. Duk wasu samari masu ji da kansu a garin zaka same su a wannan dandamalin na dan Sarkin Gaya kullum da yammaci in har yana gari. Goggo na rike da hannun Kulsumu suka bi ta gaban su suka wuce yayin da samarin duka suka yi tsit da maganganun da suke yi suka bi su da kallo. Daya daga cikin samarin ya ce, Wannan salleliyar yarinyar yar gidan waye ban santa a garin nan ba? Katuwa da ita an wani riko hannunta?
Wani daga cikinsu da ake kira Habu ya ce, Kai haba! Yar gidan Malam Jibo manomi ce fa, jikar sa ce yar wajen yar sa Sugrah mai rasuwa, kakar na masifar son ta ne shiyasa bata ganin girman ta.
Sauran har suna hada baki wajen fadin,
Amma dai ba a garin nan ta ke ba ko? Ban taba ganinta ba.
Saurayin mai bada bayani akan Kulsumu ya sake hakikancewa ya ce,
Ai kuwa dai don ba ta shiga mutane ne, watakila shi yasa baku santa ba, amma anan ta girma hannun kakanninta, Babanta ne dai ba dan garin nan ba, ko magana an ce bata cika yi ba, amma a nan ta ke GGSS Gaya, ajinsu daya da kanwata Karimatu.
Na tsakiyar su wanda kallo daya zaka yi masa ka fahimci duk ya fi su aji da kyawun suttura, wanda da alama shi ne dan Sarkin Gaya, duk samarin dake wajen zaman fadanci suke masa, bai ce komai ba, amma tas kunnuwansa suke a bude yana sauraron su. Ya rasa mai yasa yayi developing interest akan hirar tasu, abin da ba ra'yin sa bane hirar 'yammatan gari. Idan suna irin wannan hirar ko sauraron su baya yi. Amma yau har sosai ya bude kunnuwa yana sauraron su. Daya daga cikinsu wai shi Salihu ya ce.
Amma dai Allah ya yi halitta, gaskiya zan leka in buga saata, na samu wannan salleliyar ai rabuwa da Rabi zan yi duk da baikon da ke tsakaninmu, don Allah ya ya sunanta?
Dariya suka fashe da ita.
Mai bada labarin Kulsumu ya ce, Kulsumu sunanta. Kaf! Garin nan ban ga yarinya mai kyau, aji da tarbiyyarta ba. Ni na san ta fi karfina don ba zubin 'yammatan garin nan bace, shi ya sa ban ma taba sa wa a kai na ba. Wannan ai matar manya ce. Ya fadi yana kallon dan sarkin Gaya directly cikin idanun sa. Dauke kai yayi gefe cikin ginshira kamar bai san abinda suke fadi ba.
Gabadaya suka sa masa dariya sabida yadda yayin cikin kasaita ta nuna halin ko'in kula, da yadda saurayin mai bada sharhi akan Kulsumu yake maganar cikin jaddada zancensa idanunsa akan sa.

Cikin zuciyarsa ya maimaita sunan, UMMU-KULSUM suna mai maana da dadin fadi.
Duk da bai bita da kallon mayata kamar yadda sauran abokan sa dake wajen suka yi ba, ya dan saci kallon ta ta kasan idanunsa, sa'ilin da suke wucewa ta gaban su, inda yayi nasarar hango sassanyan murmushin ta ga Kakarta.

A cikin gida, su Goggo na dakin Hajiya Rakiya, ta yi musu lale marhabin, ta shimfida musu darduma suka gaisa da Goggo, ta ce ai ta ji sauki sosai, da ma hawan jini ke damunta. Kuma an samu ya sauka. Hajiya Rakiya ta dubi Kulsumu ta ce,
Ba dai yar wajen Sugrah ba ce ta girma haka?
Goggo ta yi murmushi tana duban Kulsumu (affectionately) ta ce,
Ai ko dai ita ce, Kulsumu, kin san girman ya mace ba wuya.
Hajiya Rakiya ta ce, Tabarakallahu masha Allah, Kulsumu ta girma, zata yi sa'ar Batulu, in ce ko Hajiya Shatu za ku barta ta yi karatun sakandire kafin ku yi mata aure?
Kulsumu ta sunkuyar da kanta kasa jin Hajiya Rakiya ta yi zancen da bata so (aure). Cike da alfahari Goggo ta ce,
Ai ko dai Kulsumu mai son karatu ce, daga na boko har na Arabi, ga haddar hizfi talatin a kanta, ta ce min karatun aikin jinya ta ke so ta yi.
Hajiya Rakiya ta kama hannun Kulsumu cike da nuna kauna ta ce, Allah ya yarda Kulsumu, aiki mai dumbin lada kike so kenan.
Haka suka ci gaba da hirarsu ta aminai, Hajiya Rakiya ta kawo musu kayan zaki na gidan sarauta irin wanda ta ke yi a matsayin sanaa, wato su alkaki, dubulan, nakiya, bakilawa da gireba suna ci suna hira, Kulsumu gutsura daya ta yi wa nakiya ta rike ta hannunta ta koma gefe ta takure amma ba ci take ba.
Tunda ta shigo gidannan wani irin bakon yanayi ya bakunci jikin ta. Ta rasa yadda zata fassara shi.

Daga bakin kofa ya yi sallama da wata murya mai zurfi da rashin amo (husky), kamar baya son yi, wankan tarwada mai tsayi da rashin kauri, dogo ne sosai, shi ba fari ba shi ba baki ba, gashi nan dai ruwan kasa mai daukar ido, complexion dinsa tun a wancan lokacin mai ban sha'awa ne, yana da dogon hanci da madaidaitan idanu ma'abota zara-zaran gashin ido, masu yalki da yawan lumshewa. Siririn gashin bakin quarter million ya zagayo daga saman bakinsa zuwa habarsa. Ba shi da kauri sai fadin kirji (physique). Duk inda ake neman zaratan matasa masu jini a jika a wancan zamanin zai kasance cikinsu, yana sanye da kaftani na shadda milk colour wadda aka yi wa kayataccen aiki na 'ya'yan sarauta da zare ruwan kasa. Duk inda ake neman namiji mai aji za'a sanya shi ciki a jerin farko. Daga ganinshi bai da son kwaramniya kuma ba mai yawan walwala ba ne.

Goggo da Hajiyar suka amsa sallamarsa, ya rage tsawo ya gaida Goggo a gajarce, sannan cikin wata irin nutsuwa da zuzzurfar muryar sa ya ce,
Umma, mukulli na zan dauka.
Ta ce, Duba kan firji, nan na ce Batulu ta ajiye maka.
Bayan juyawarsa zai fita bayan ya dauki mukullin Goggo ta ce.
Ranki ya dade ba dai TURAKI ba ne wannan?
Hajiya Rakiya ta yi wani murmushi na alfahari irin wanda ta ke yi a matsayinta na wadda ta haifa wa Sarkin Gaya da namiji kwaya daya jallin jal a cikin tarin yayan gidan mata.
Ta ce, Shi ne fa, shi ma karatun likitanci yake yi a jamiar Ibadan. Bai faya zama a garin nan ba, yanzu ma duba ni ya zo, kwana uku zai yi ya koma can Ibadan din.

Masha Allahu. In ji Goggo, Allah ya sa mu amfana da su, Ya ba su ilimi mai amfani.

Sun dade suna hirar yayan Hajiya Rakiya na gidan aure, wato Hadiza da Ramla da 'ya'yan su a garuruwan da suke aure, Hadixa na aure a Kiru, Ramla na Kura, sannan Goggo ta yi haramar tafiya. Kulsumu kamar ba ta dakin as if she's not in existence. Tayi wani irin shiru.... tana karbar bakon yanayin dake ratsawa a jikin ta, duk halin da ta ke ciki Hajiya Rakiya na hankalce da ita, ta lura Kulsumu na da damuwa, walwalarta da nutsuwar ta ta banbamta data 'yammata irin ta, musamman da yake tana da 'ya tsarar ta, sannan ba ta cikin farin ciki ko kadan kamar sauran yara tsararrakinta. Da za su tafi, Hajiya Rakiya ta dauko turmin atamfa (Ghana wax) da turare ta bai wa Goggo, ta cika leda da su alkaki da nakiya ta bai wa Kulsumu ta ce, ta ga ba ta ci sosai ba, in ta je gida a nitse sai ta ci. Tunda nan kunya take ji. Kulsumu ta sunkuyar da kai ta ce "nagode".
Suna kokarin fita, cikin duhun da kan ziyarci idanunta lokaci-lokaci ya gusar da ganin ta nawucin gadi, Kulsumu ta ji ta yi karo da mutum a bakin kofa, wanda ke tahowa zai shigo dakin kan sa tsaye. Saura kadan ta fadi, tayi gaggawar rike marikin kofa. Wani kakkarfan (masculine scent) irin na dazun da ya wuce ta gaban ta ya ziyarci hancinta. Tunda ta ke a rayuwarta ba ta taba jin kamshi mai tasirin wannan ba ga kassara jiki da zuciyar diya mace. Dagowar nan da za ta yi da zummar bada hakuri sai idanunsu suka sarke cikin na juna. Ya kalle ta, ta kalle shi with unexpressable lingering look a lokaci guda (kallo mara fassaruwa na lokaci mai tsaho) daya fito kai tsaye daga tsakiyar kwayan idanun kowannen su.
Kallon da ya haifar da darsuwar wani abu mai karfi kamar chemistry din gravity cikin jiki da zuciyar Kulsumu, cikin yan dakikai da ba su gaza biyar ba. Amma ga Turakin, bazan iya cewa ba.
Saidai kuma cikin su babu wanda zuciyarsa ba ta buga fiye da kima ba a dan kallon nan da ya yi wa dan uwansa. Their eyes replenishes suddenly bayan faruwar hakan. Kulsumu ji ta yi gabanta ya tsananta faduwa irin wanda yayi dazu a dakin Haj. Rakiya data ji presence dinsa a kanta zai dauki makulli saman firjin data ke jingine. Duk da alokacin bata dago ta kalle shi ba she feels his presence which overwhelmed her. A lokuta irin wannan da wani bakon al'amari zai faru da ita ta kan ji irin wannan, amma na yau ya fi na kullum.
Shi kuma ya san a kafatanin rayuwarsa bai taba samun irin reaction din da ya samu a wannan karon ba akan mace. Saidai bai danganta shi da wannan yarinyar ba. Wata 'yar ficika da ita. Tsayawa suka yi suna kallon-kallo, ita ta kasa bada hakurin data yi niyya, shi ya kasa cewa ta bashi hanya ya wuce, yayin da iyayen suka yi shiru suna kallonsu. Ganin kallon nasu ba mai karewa ba ne kuma an rasa mai magana a cikin su,

4 Comments On KULSUM
avatar
zainab-salisu-kasim

1 year ago

Reply

I luv dis book

avatar
zainab-salisu-kasim

1 year ago

Reply

I luv dis book

avatar
amina-abdul

1 year ago

Reply

love it

avatar
aysha-abubakar

12 months ago

Reply

I like the book

Please Login or Register in order to submit comment