Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na Turaki manya-manya, akwai kayan kallo irin na zamanin sai wasu irin manyan dardumai na fata mahadin tum-tum din an manna su a bangon karshe na falon. Kowanne dakin barci yana manne da toilet dinsa. Daki daya aka bari ba a sa wa gado ba kamar yadda iyayen Kulsumu suka roka a bar musu ko da daki daya ne su yi mata jere.
Har kan gadonta Hadiza ta zaunar da ita, sannan ta gabatar mata da mai aikinta guda daya da Umma ta ba ta mai suna Laraba. Ta ce komai ta ke so za ta yi mata, sannan in aike gare ta wajen Umma ta aike ta. Zamanin wayar hannu ba ta zama gama-gari ba, ba kowa ke mallakarta ba sai daidaikun mutane, amma ana amfani da land-line wanda da shi ake amfani a gidan Sarkin Gaya. Dakin Laraba yana daga tsakar gida.
Bayan fitar Hadiza, Batulu ta shigo. Har yanzu da lullubinta ba ta cire ba, ta yi tagumi a gefen gado. Tana saka da warwara game da sabuwar rayuwarta. Wai ita Kulsumun Goggo ce mamallakiyar wannan gidan da ko a mafarki ba ta taba mafarkin rabinsa ba. Sai dai duka wannan ba shi ne a gabanta ba, damuwarta shi ne mijin (Turakin), ya ya zai karbe ta duk ranar da ya gano lalurarta?
Batulu ta sauke mata lullubin, ta ce, in dai Yaya Turaki ne ki daina tunanin sa Allah ya kashe ya baki. Ki tashi ki zagaya ki ga dakunanki. Inda abin da bai miki ba ki fada a gaya wa Umma.
Da sauri ta ce, Ban aike ki ba ni dai.
Batulu ta yi dariya, ta kama hannunta ta mikar da ita. Falo suka fara zuwa, ita dai Kulsumu nata ido, don ba ta taba ganin falon da ya burge ta irin wannan ba. Kujerun masu taushi sun kawata falon sosai. Fentin gidan ruwan madara ne, kilishin da ya mamaye dakin mai taushi kalar kujerun falon. Kulsumu ji ta yi hawaye sun ciko idanunta ina ma ina ma ina ma dakin zai dauwama a matsayin nata? Ina ma lafiyarta kalau ta mori wannan arziki da Allah ya yi mata? Ta yi saurin dauke hawayen idonta da yan yatsunta kafin Batulu ta gani. Jikinta na ba ta rayuwarta a gidan nan ba mai dorewa ba ce daga ranar da suka gano cewa ita din, mai lalurar fitsarin kwance ce.
Ba inda ba su shiga ba sai daki na karshe. Batulu ta murda ta ji ta a rufe, ta ce, May be wannan ne dakinsa, ko me ye na rufewar? Oho!.
Ita dai Kulsumu ba ta ce komai ba, suka koma kitchen, duk da cewa a wancan lokacin kicin din is not very modern amma ba irin na gidansu ba ne. Risho ne mai cin tukwane uku, da duk sauran tarkacen amfanin kitchen. Yaya Hadiza ita ta sayo komai ta zuba daga aljihun Maimartaba. Shi ya yi komai na gidan. A cewarsa an tayar da su auren ya bagatatan bai kamata a daura musu nauyin komai ba.
A karshe a falo suka zauna, Batulu ta hau jona kayan kallo, film din Hausa ta sa musu na dan Ibro da ake kira (chamama), sai babbaka dariya ta ke har da sunkuyawa da rike ciki. Kulsumu dai kallo ta ke, amma sam hankalinta ba ya kai balle ta taya Batulu dariyar da dan Ibro ke ba ta.
Hankalin ta ya nausa wajen tunanin wace irin rayuwa zata yi da Turaki a gidannan daga shi sai ita a matsayin miji da mata? Bata san komai akan rayuwar aure ba, sannan a hannun tsoffi ta tashi, duk wata wayewar zamani akan hikimar zaman aure Kulsumu bata san su ba. Goggo bata mata zancen aure ko da kuskure don ma kada tasa ran ta akan yin sa. Kullum tunanin Goggo shine ita da Kulsumun ta, tare zasu dawwama har mutuwa ta raba su. Bata taba kwadaita mata aure ba sabida la'akari da take da lalurar ta. Don haka Kulsumu ta taso innocent akan komai da ya shafi aure. Yanzu da Ubangiji ya kawo auren afujajan basu samu lokaci da nutsuwar da zata koyar da ita komai ba, bata ma san ta inda zata fara ba, don haka a haka ta kunso ta ta kawo ta gidan mijin.

Da sallama a ciki ya shigo falon. A take wuta ta dauke wa Kulsumu, ta soma barin jikin da ta ke yi da zarar ta ganshi ko ta ji husky muryarsa. Batulu ta tsagaita dariyar da ta ke yi, ta juya ta dube shi ta ce,
Sannu da shigowa Yaya Turaki!.
Harararta ya yi, cikin fada ya ce,
Wace irin dariya ce haka ki ke yi kamar mahaukaciya? Tun daga waje nake jiyo ki. Ke wace irin yarinya ce ne mara nutsuwa? Da Allah je ki karbo min abincina wajen Umma, kuma saura ki bata min lokaci, fita zan yi.
Kulsumu ta kara tsurewa, domin fada yake kamar zai rufe Batulu da duka. Barin da jikin ta ke yi ya kara ninkuwa. Tsoron ta Allah tsoron ta abinda zai taba lafiyar jikin ta. Batulu ta mike tana kunkuni hadi da zumburo baki, a ciki take magana yadda ba zai ji ta ba. Amma ya ji tan sabida kaifin jin sa.

Ni na rasa laifin da na yi maka ka ke ta hantara ta kwanan nan Yaya Turaki.

Dakinsa ya bude ya shige, bai bata amsa ba. Abin da bata sani ba shine haushin kowa yake ji, ba ita kadai ba, ita kuma ya lura tafi kowa son auren ma, iyayen ma don babu yadda zai yi da su ne. Sun yi masa katsalandan cikin rayuwar sa. Ko zai yi aure ai ba yanzu ba da tashen balagar sa, ina dalibin likitanci ina aure yanzu sabida Allah?
Satittikan da suka rage zai yi cikin gidan jin su yake kamar shekaru aru-aru. Sai dai kuma ko yaya ne yana jin bazai iya wulakanta yarinyar nan ba. Tana da wata charisma da ba duka mata Allah ya mallakawa ba, tun ganin sa na farko da ita idanun ta na da matukar tasiri ga zuciyar sa akan dalilin da bai sani ba.
Batulu ba ta jima ba ta dawo dauke da katon faranti ta ajiye tsakiyar falon, ta juya ta fice tana ce da Kulsumu,
Ke da ganina sai gobe, ki ji da masifaffen mijin ki, idan kuma ya mammareki gobe zanzo in gasa miki kumatu.
Idanun ta suka yi rau-rau kamar ta saki kuka. Batulu tayi mata gwalo ta fice da gudu. Ji ta yi kamar ta ce da Batulu ta taimake ta ta dawo su kwana tare, amma ta ji ta kasa magana harshenta ya sarke sakamakon fitowar Turaki Abubakar daga dakinsa. Wani kwayan mutum guda daya dake hautsina kwakwalwarta a duk lokacin da ta ganshi. Ya haifar mata da rashin nutsuwa da kasa mallakar kanta. Ya canza kaya daga shadda zuwa kananan kaya, T. Shirt ce ruwan makuba an rubuta NIKE a gabanta da farin rubutu, sai shudin wandon jeans mai kauri. Da alama wanka ya yi, sai kamshi yake yi mai ratsa zuciya. Daga sanin da ta yi masa zuwa yau ta fahimci shi din maabocin son turare ne, sannan kamshin turaren sa is special ba irin wanda ta saba ji ba ne a koina.
Zama ya yi a kan kilishin falon ya ja farantin abincin gabansa, a nitse ya fara cin abincin sa kamar bai san Allah ya yi ruwan tsirar ta a falon ba. Dazu da ya yi mata kallo daya a dakin Umma sai ya ga kamar ya taba ganinta a wani wuri, sai dai ya manta inda ya gantan. Amma kwarai ya gane ya san wannan bafullatanar fuskar. Mikewa ta yi a darare zata wuce zuwa dakinta. Ya daga kai ya bita da kallo daga samanta har kafar ta tana hardewa kamar zata fadi har ta shige dakin. Girgiza kan sa yayi, yarinya kankanuwa wadda ya dace yanzu ace tana aji tana daukar darasi an kakaba mata auren wuri, kawai don a takurawa rayuwar sa. Dan kankanin tsaki yayi ya cigaba da cin abincin sa. Ban da iyaye-iyaye ne wa ya isa yayi masa wannan katsalandan din? Shi dai tunda ya samu zasu bar shi ya tafi karatun sa ai shikenan, aure gashi nan anyi, sai su san yadda zasu yi da surukar su.
Tana shiga dakin ta kwanta rub-da-ciki tsakiyar gadon ta, fuskar Turaki na gilma mata, ta kasa daina tunaninsa. Wani sabon alamari da bai taba faruwa da ita ba akan kowa, ya dinga sakadar ruhin ta, wani feeling ne da baya misaltuwa. Haka kawai ta ji idanunta ba sa gajiyawa da satar kallonsa. He is smart, gentle, and very classy. Duk matar da ta mallake shi a matsayin mijinta tabbas ta taka babbar saa, kuma dole a yi mata jinjinar mallakar gwarzo a cikin mazaje.
Murmushi ta yi da ta tuna ita din dai, ai ita ce matar sa ba wata ba. Murmushin ya yi saurin bacewa daga siririyar fatar bakin ta da ta tuna Turaki fa ba ya yin ta. Ita kadai ta ke kidanta ta ke rawar ta. Matar shige ce ita, tilashin iyaye kan ba yadda zai yi da umarnin su. Kawai sai ta samu kanta da daga hannu a wannan daren tana rokon Allah soyayya ko kaka daga Turaki, ta dasa sallar dare, cikin kowacce sujjadar ta tana rokon Allah ya mallaka mata zuciyar Abubakar Turaki, ko da kuwa ba zai zauna da ita ita kadai ba; ya yarda ya ba ta gurbin matar auren sa.

Kasancewar jiya ba ta samu ta yi barci ba, yau sanda ya fizge ta ya kai ta birnin Sin bai yi shawara da ita ba. Tana kwance ne a tsakiyar gadonta tana tunanin Turaki bayan ta yi sallolin nafila ta gaji ya sadado ya dauke ta. Ai kuwa asubah ba ta yi ba ta ji ta sharkaf cikin laima, tun daga gadon bayanta har kafafunta a jike ta ke. Kuka ta rushe da shi ita kadai a daki. Ta yi kuka-ta yi kuka har ta ji babu dadi. Sai wajen shidda na safe ta samu ta yi sallah bayan ta yi wanka. Ta yaye zanin gadon wanda yake sabo fil mai tsananin kyau amma ta sharkaba masa fitsari, ta hada da kayan da ta tube ta je toilet ta saka su a bokiti ta wanke da omo ta fito tsakar gidan ta shanya su bisa igiyar shanya da aka daura musu. Ta koma ta hada omo da bleach ta sa tawul ta dawo ta dinga goge katifarta tun karfin ta, don ta yi mata nauyi, ba za ta iya fita da ita ba. Ta nemi wasu kayan cikin wadanda aka jera mata a sif ta sanya ta hada kai da gwiwa tana kuka.
Sau biyu Turaki yana jiyo sautin kukanta kafin ya fita zuwa masallaci, a ransa cewa yayi yarinya dole ki yi kuka, tunda rayuwar da iyayen ki suka zaba miki kenan. Wani kukan ma sai ranar da na dawo na auri mai ilmi iri na. Laraba tana can dakinta amma tashin kukan Kulsumu ya hana ta komawa barcin safe.
Bayan fitar Turaki masallaci da jimawa kuma bata daina jiyo kukan Kulsumu ba, sai ta mike ta saka hijabi da silifas dinta ta fito a hankali. Making very sure ba ta yi motsin da zai sa a ji tafiyar ta ba. Kai tsaye ta nufo kofar falon nasu, tana isowa shi ma Turaki yana isowa tunda ya fita sallar asubahi bai dawo ba sai yanzu, har sun kusa yin karo da Laraba wajen shiga falon ta ja baya tare da tsugunnawa tana yi masa barka da asubah. Ta ce,
An tashi lafiya ranka ya dade? Zan duba ta ne naji kamar tana kuka.
Ya dan sosa keya na rashin gaskiya don dai shi rabon da ya sa ta a ido tun jiya da yamma da ya zauna cin abinci ita kuma ta shige daki. Bai kara bi ta kanta ba. Amma ya san ta jima tana kuka tun asubahin fari, Allah yayi masa ji mai karfi.
Bai ce mata komai ba ya sa mukulli ya bude kofar sassan suka shiga a tare. A nan tsakar gida Laraba ta yi arba da shanyar da Kulsumu ta yi, na zanin gado da kayan jikin ta. Tayi mamakin me ya kai ta wankin kaya haka da assalatun fari? Har da zanin gado? To ko dai fitsarin kwance take! Wani irin tausayi ya lullube ta, ta dai tabbata Turaki bai shiga dakinta ba don ta san halinsa tun haihuwarsa a hannun ta ya tashi kuma take bauta ga mahaifiyarsa bai iya yi wa komai karamar kiyayya ba, da wuya ya nemi wannan daga Kulsumu nan kusa. Ba ta ki ba in ta kara girma, ta yi ilimi mai zurfi irin yadda yake son matar sa. Da ya fara tasawa da yake yana shiri da ita ya sha gaya mata shi mace mai ilmi yake so, son samu wadda ilmin su yake matsayi guda. Ita kuma sai take ce da shi ashe 'yar bariki zaka auro mana. Kuna da ilmi matsayi daya ta ina ake zaton biyayya?.
Mahaifiyarsa Haj. Rakiya bata taba daukar zancen sa da muhimmanci ba, ta dauka yana fada ne dai kawai don ya ji dadin bakin sa, yasa tayi ta fada kamar ta ari baki, bata san cewa shi har cikin zuciyar sa yake nufin abinda yake fadi ba.
Kanta tsaye ta nufi dakin Kulsumu, shi kuma ya biyo bayan ta. Juyowa ta yi ta dakatar da shi ta ce ya tafi abunsa ita ba wajensa ta zo ba, in gaskiya ne me ya hana ya duba ta don kansa kafin ya fita?
Murmushi ya yi ya san halin mama Laraba yanzu ta hada shi da Ummah, ya wuce dakinsa. Ba ya so Umma ta ga Kulsumu na kuka ta tahumeshi da yi mata laifi. Laraba ta nufi dakin Kulsumu, tun daga bakin kofa ta ke jiyo shesshekar kukanta, ta murda dakin ta shiga da sauri hade da sallama.
Wata irin zabura Kulsumu ta yi don ba ta taba kawowa a ranta wani zai iya zuwa mata a daidai wannan lokacin ba. Irin lokacin da bata son kowa ya ganta a rayuwarta. Laraba ta kamata ta rike ganin irin firgitar da ta yi. Ta ce,

Ni ce Kulsumu, ki yi hakuri na tsorata ki.
Sannan ta sake ta tana kare wa dakin kallo. Idonta ya sauka akan katifar dake jike sharkaf. In ka san wani abu wai shi karshen tashin hankali to shi Kulsumu ta shiga a wannan lokacin, katifar a jike ta ke sharkaf da fitsari da ruwan omon da ta wanke ta. In Laraba ta tambaye ta ruwan mene ne haka, me za ta ce mata?
Laraba ta ciccibi katifar duk nauyinta ta yi waje da ita. Kulsumu ta rasa me za ta ce don mamaki da fargaba. Ta tsaya a tsaye a inda ta ke ta kasa ko kwakkwaran motsi. Zuciyar ta kamar ta faso allon kirjin ta ta fito. Laraba ta dawo ta ce da ita, idan katifar ta bushe zata dawo ta maido ta, kuma za ta kawo mata mai leda karama ta dinga kwana a kai. Zata bayar a dinka mata.
Kunya, nauyi, mamaki, alajabi, fargaba da tuajjibi suka taru suka yi wa Kulsumu lullubi. Ashe Laraba ta san komai! To wa ya gaya mata? Ashe Umma ma ta sani kenan? Ashe a haka ta karbe ta a matsayin suruka? Ya ilahi!
Hawaye na sauka a kan kundukukinta ta ke duban mama Laraba. Laraba ta dafa gadon bayanta tana bubbugawa, sai kawai ta fashe da kuka.
Daina kuka haka, kin ji Kulsumu? Za ki samu sauki insha Allahu. Lalurar fitsarin kwance ba kanki farau ba. Akwai wata diyar Yayata ita ma haka ta ke, kuma ta samu magani ta warke daga baya. Yanzu yayanta biyar ke nan da mijin ta. Insha Allahu sai inda karfina ya kare wajen nema miki magani, daga nan har garin mu Maradi, kafin Turaki ya san lalurarki kin warke insha Allahu!!!

Kalaman da suka shiga kunnuwan Abubakar Turaki Abdullahi kenan, a lokacin da ya sanyo kai don ya gaya wa mama Laraba cewa zai fita zai je Kano wajen wani abokin karatunsa da za su tafi tare ya dawo zuwa yamma. Bai tsaya da niyyar labe ba, sai don ya saisaita fuskarsa kada Laraba ta gane irin rashin son da yake wa Kulsumu don a fuskarsa ta ke karantar komai nasa tun yana karami. Baya so yayi abinda zata hada shi da Umma. Ya san Umma na sane ta hada su da Laraba sabida ita kadai ce bata shayin sa cikin barorin ta. Yana so ya rabu da ita lafiya cikin dadin rai. Ga shi in ya tafi ba shi da niyyar dawowa nan kusa kamar yadda suka yi alkawari da shi, cewa duk karshen shekara zai zo gida wajen iyalinsa yayi hutu ya koma har ya gama.
Sai ya ji wannan zance mai kama da fadowar aradu a kwanyarsa; Lalurar fitsarin kwance?” Fitsari dai, fitsari wanda ya san kananan yara na yi a kwance? Shi 'yar shekara kusan sha biyar ke yi a kwancen?
Tsakar gidan ya fita sai ya ga inda Laraba ta shanya katifa, har hannu yasa jikin katifar ya taba don dai ya tabbatar, ya ga inda Kulsumu ta shanya zanin gadon da kayan jikin ta. Ashe abin da ya ji daidai ne ke nan. Yau da ba Umma ce ta haife shi ba, sai ya ce ta yaudare shi, ta cuce shi, ta haince shi. Ta rasa wadda za ta aura masa sai mai fitsarin kwance? To ya yi ya ya da ita a rayuwar sa?
Juyawa ya yi sadaf-sadaf ya koma dakinsa, da baya-da-baya ya fada a gadonsa ko takalmin sa bai cire ba, ya runtse idanunsa yana maimaita kalmar innalillahi har zuwa karshenta.
Umma ta san yadda yake da kyama da kyankyami. Ta yadda ko karatun likitanci kafin ya zaba sai da ya tantance ya zabar wa kansa ophthalmology (fannin ido), amma shi ne za ta dauko mai lalurar fitsarin kwance ta aura masa? Sai ka ce ya rasa mata a duniya. Shi Turaki da yammatan jamia suke rububinsa, yarinyar da ko sakandire ba ya jin ta shiga. Umma ba ta yi masa adalci ba, amma tunda ya yi mata biyayya ya yi abin da ta ke so, shi ma zai yi abin da yake so ta hanyar da babu mai ganin laifinsa. In ya tafi bazai dawo ba!

Haka ya fice ya tafi Kanon ba tare da ya iya yi wa Umma sallama ba. Haushinta yake ji sosai, yau da ba ita ta haife shi ba, cewa zai yi ba ta kaunarsa! Sannan ta yaudare shi!!!

*** *** ***

Da yamma Laraba ta kawo mata katifar da ta yi mata alkawari, irin ta 'yan makarantar kwana an dinketa cikin leda, ta kuma gaya mata kafin ta tafi dazu ta ware zannuwan gado biyu marassa nauyi ta dinga amfani da su su kadai a lokacin kwanciya. In yaso da safe sai ta wanke mata su ta shanya tasa turaren wuta a dakunanta. Kulsumu ta rasa ta cewa, da halin tawaliu da YAKANAH na wannan baiwar Allah. Ta yarda komai lalacewar zamani mutanen kirki masu tausayi ba sa karewa a duniya.
Turaki bai dawo gidan ba sai wajen karfe takwas na dare, ya tadda su suna cin abincin dare ita da Batulu a kwano daya. Wani kyankyami ya kama shi kamar ya ce da Batulu ta cire hannunta. Shi ba wani kwakkwaran kallo yake mata ba don yanzu haka in za'a ce ya zayyano kamanninta in ta bata ba zai iya ba. Babban abinda yake hana shi kallon ta shine idanunta; suna da wani irin effect na halitta sosai akan mai kallon ta. Wannan ne dalilin da yasa ya kasa dauke idanun shi a kanta rana ta farko da ya fara ganin ta a rayuwar sa. Allah-Allah yake kwanakin tafiyarsa su zo ya haure ya bar kasar, yayi nisa da wadannan idanun masu maganadisu akan sa da duk mai kallon su, ya san kafin ya dawo watakila sun gaji da jiransa sun san yadda suka yi da mai fitsarin kwancensu.
Suna gama cin abincin Batulu ta yi mata sallama ta tafi. Laraba ta kwashe kwanukan, daki ta koma ta yi wanka don ta ji dadin barci, rigar barcin da ta zabo cikin kayan lefenta da aka jibge mata take, masu bukatar dinki duk a dinke suke, dinkuna na alfarma, domin kuwa telan da ke yi wa yayan Sarkin Gaya dinki shi ya dinka kayan. Ta shimfida katifar ta a kasan dakin ta yi shimfida, ta yi adduointa sannan ta kwanta.

Washegari da hantsi karkashin rakiyar Batulu ta je ta gaida Umma har dakinta, sannan kakarsu Fulani da sauran matan gidan. Fulani ta ce, ta dinga shigowa suna hira in ba ta komai. Ba ta san cewa ita ba maabociyar hira ba ce, ta fi so ta zauna shiru ta yi ta tunanin Turaki, sabida ta ganshi ta ke zama a falo kullum idan yana rubuce-rubucen sa. Yana yi yana hararar ta in sun hada ido sabida baya son nacin kallon nan da take masa. A ran sa yana fadin "muguwa, ana gudun idanunta tana mannawa mutane su kamar ta cinye su".
Ta cirewa ranta tsoron sa, kallon sa take ta more, don Batulu ta gaya mata tafiya zai yi. Don haka kallo harda na ramako take masa.
Ita dai idaniyarta ba sa gajiyawa da kallonsa. Yana da wani irin sassanyan kyau, wanda yawan daukar wanka ke fidda shi sarari.
Bata taba ganin namiji mai class da ilhamar nata mijin ba.... Shi din abin so ne ga duk macen da Allah ya baiwa. Zuciyarta ta riga ta gama zarmewa akan sa, tun a shekarun adolscence dinta.
Bata san so ba, bata san ma'anar soyayya ba, babu kuma wanda ya taba zama da ita ya bayyana mata, bata taba karantawa a kowanne littafi ba, amma ta tabbata zuciyar ta zama infatuated akan mijin ta. Zuciyar ta na ragaita da tunanin baya son ta. Haka tana shiga tsananin fargaba idan ta tuna nan da wani dan lokaci tafiya zai yi ya bar ta. Tana mamakin kanta, tana mamakin alamarin da ke faruwa da ita. Ba abin da ta ke so da gani a yanzu sai Turaki, ba abin da ta ke son ji a yanzu sai muryarsa, ko da kuwa a ce fada ne yake yi wa Batulu.
Fitsari ya zama ba damuwarta ba yanzu, Abubakar-Turaki ya maye gurbinsa. Duk wani fatanta na rayuwa ya dawo kan Abubakar Turaki Abdullahi, yadda ta damu da tunaninsa da son ganinsa, fitsarin yanzu bai dame ta haka ba. Duniyar Kulsumu, ta rikide ta juya zuwa ta SOYAYYAH ba tare da ita din ta san hakan ba.


4 Comments On KULSUM
avatar
zainab-salisu-kasim

1 year ago

Reply

I luv dis book

avatar
zainab-salisu-kasim

1 year ago

Reply

I luv dis book

avatar
amina-abdul

1 year ago

Reply

love it

avatar
aysha-abubakar

12 months ago

Reply

I like the book

Please Login or Register in order to submit comment