Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kan lalurar diyarsu su ma ba ta yi musu adalci ba. Sannan an ce DA na kowa ne, ba ka san wanda zai amfane ka ba. Za ta karbi Kulsumu a suruka tare da dukkan lalurorinta sabida mutuncin dake tsakanin ta da kakarta. Babu cutar da Allah ya saukar ba tare da Ya saukar da ita tare da maganinta ba. Watakila watarana ta warke. Sannan Turaki kasar zai bari, ba zai yi dogon zaman da zai gane lalurar matarsa ba, zai yiwu ta iya warkewa kafin su yi dogon zama tare insha Allahu. Idan kuma ya gama karatun ya ga baya bukatar auren nata yana da damar auren wasu matan har uku masu lafiya bayan ita. Burin su a yanzu shine kawai yayi auren ya zame musu garkuwa tsakanin su da shi, kada ya tafi babu aure rudin zamani ya rude shi, ko ya manta da gida idan yasan babu nauyin kowa a kan sa, suna son yarinyar da suka yarda da tarbiyya da usulin ta, kuma Kulsumu ce ta cika wannan sharudda.
Da wannan karfin gwiwar Hajiya Rakiya ta dubi kawarta Goggo Shatu ta ce,

Hajiya Shatu, kun amince kun bai wa Turaki auren Kulsumu?

A dan daburce Goggo, wadda ta yi nisa a tunanin hukuncin da Hajiya Rakiya za ta yanke ta juyo, ta ce,
Iyee Naam me ki ka ce Hajiya?
Hajiya Rakiya ta sake maimaita zancenta,
Na ce kun amince kun bai wa Turaki auren jikar ku?
Hawaye suka zubo wa Goggo Shatu, ta ce, Idan har ku kun amince ku karbe ta a yadda ta ke, mu me za mu ce ban da mu bisu da fatan alkhairi?
Hajiya Rakiya ta gyada kai, sannan ta kama hannun Goggo Shatu ta ce,
Ki cire damuwa a ranki Hajiya Aisha, ki bi su da adduar Allah ya ba su zaman lafiya da zuria mai albarka. Dukkanmu masu nakasu ne ta wannan fannin ko ta wancan. Ba wanda Ubangiji ba ya jarraba. Ita Kulsumu jarrabawarta kenan, kuma da sannu Allah zai yaye mata. Zancen nan kuma zai tsaya a sirri tsakanina da ke, ko Maimartaba ba zai ji shi ba, ku ci gaba da nema wa Kulsumu magani, ku kara tsananta addua. Insha Allahu kafin Turaki ya gama karatu ya dawo gida gaba daya Kulsumu ta warke. Ki gaya wa Malam Jibo ya saurari yan aiken Maimartaba.
Hawaye kawai Goggo ke yi tana sauraron Hajiya Rakiya tana gyada kai. Ta rasa a sahun irin mutanen da za ta saka ta. Irinta tsiraru ne a cikin alumma.
Wadanda suka yarda imaninsu ba ya cika sai sun so wa dan wani abin da suke so wa yayansu. Ta gaza cewa komai sai kawai ta saki kuka ta rufe fuska da habar zaninta.
Hajiya Rakiya ta ce, Ki bar kuka, Da na kowa ne. Mu taru mu yi addua mu bi su da fatan alkhairi. Jikina na ba ni alheri za mu kulla cikin yardar Ubangiji.

*** *** ***
Wasa-wasa karamar magana ta zama babba. Maimartaba ya aiko wakilansa wajen Malam Jibo dauke da dukiyar aure, don Malam Hadi ya ce ya bar wa Baffa wuka da nama, an yi tambaya, an bayar, an biya sadaki naira dubu hamsin cif. A wancan lokacin kudi ne tsugugu ba 'yan kadan ba. Sai kudin gaisuwa da dai sauransu, aka tsayar da ranar daurin aure kwanaki goma sha biyu masu zuwa.
Duk bidirin nan da ake Kulsumu ba ta san wainar da ake toyawa a kanta ba. Daga Goggo har Baffa sun rasa ta inda za su fara billo mata da zancen.
Kwanaki na mirginawa, ranar da aka saka ta daurin aure na kara matsowa. A wannan daren na ranar jumaa da ya rage saura kwana biyu daurin aure, Baffa da Goggo suka yanke shawarar zaunar da Kulsumu su yi mata bayanin komai.
Baffa ne ya shigo dakin Goggo bayan sallar ishai, bai tsaya a majalisar hirarsu ba sakamakon zaman da suka yanke za su yi da Kulsumu yau. Sanda ya shigo ta gama cin abincin darenta, dambun shinkafa ne Goggo ta yi musu ya sha ganyen zogale da gyada. Goggo ta shimfida masa darduma ya zauna, Kulsumu ta fidda kwanon ta dawo ta zauna daga gefen Baffa, ta ce,
Baffa yau tsiren gangare nake shaawa tun safe.
Baffa ya ce, Idan na fita zan samo miki. Har da gasassar kaza mai maiko. Zauna Kulsumu yau magana za mu yi irin wadda ba mu taba yi ba, irin ta kaka da jikanyar sa da yake matukar so.
Kulsumu ta nutsu, ta tattara hankalinta ta mika wa Baffa.
Ya dago ya dube ta cikin ido, ya ce, Kulsumu, idan muka yi hukunci ga rayuwar ki za ki yi mana biyayya ni da Goggon ki da mahaifin ki?
A sanyaye Kulsumu ta ce, Insha Allahu Baffa.
Ya ce, To Kulsumu, aure za mu yi miki. Jibi-jibin nan in Allah ya kai mu. Ki dauki hakan a matsayin kaddara kuma hukuncin Allah a gare ki, kin ji Kulsumu?
Kulsumu ta bata fuska, ta ce,
Ban gane ba Baffa? Wane irin aure?
Baffa ya ce, Auren sunnah, irin wanda ake yi wa kowacce mace idan ta kai munzali. Kamar wanda ke tsakanina da goggonki, kamar wanda ya shiga tsakanin mahaifinki da mahaifiyarki har suka haife ki. Ina fatan kin fahimce ni, kuma ba za ki ba mu kunya ba Kulsumu a idon masoyan mu masu kaunarki fisabilillahi? Za ki nuna tarbiyyar da muka yi miki a duk inda ki ka samu kanki?
Kulsumu ta soma shiga rudu, domin zuwa yanzu ta fahimci Baffa da gaske yake maganganunsa, babu alamun wasa a cikinsu. Hawaye suka ciko idanunta, ta ce,
Baffa sadakata ka bayar? Sabida ina fitsarin kwance?
Ya ce, Ko kusa Kulsumu, aure ne mai daraja, na an gani ana so, sabida an yaba da tarbiyyar ki, har gida aka zo aka roke ni da kokon barar neman aurenki. Aure na mukami da girma!.
Ya karasa da murmushi.
Kulsumu ta bar hawayen da ta ke makalewa suka silalo, wani abu ya dunkule mata a wuya, kafin ta ce,
Baffa wane ne zai auri mai fitsarin kwance? Baffa ina zaman-zamana lafiya don Allah kada ku jawo abin da zai karya zuciyata... da dan sauran karsashin da ke cikinta. Burina in yi karatu mai zurfi Baffa, in zama ma'aikaciyar jinya.....in taimaki al'ummar garinmu da ake wulakantawa a asibiti.... don Allah kada ku raba ni da burina Baffa..... Ta fashe da kuka.
Goggo ta kai hannu gadon bayanta tana bubbugawa tana lallashinta, ita ma nata idanun sun ciko da kwalla, tana hasaso ranar da aure zai raba ta da Kulsumun ta. Hakika aure ya ci sunansa YAKIN MATA, in ba shi ba wa ya isa ya raba ta da Kulsumu?
Baffa ya ce, Kulsumu tuna min, wane irin karatu ma ki ke so ki yi da turancin?
Ta share hawayen idanunta nan da nan jin abin da Baffa ya ce, ta ce, Nursing Baffa.
Ya ce, shine likitanci?
Ta ce, Aa nursing Baffa. Ina so in zamo cikakkiyar malamar jinya, in dinga taimakawa mata a asibiti, don Allah ka bar zancen auren nan. Ni ba ni ma da saurayi, ban taba sauraron kowa ba wallahi Baffa ba ni na turo su ba. Ta sake rushewa da kuka.
Baffa ya ce, Kulsumu ki saurare ni ki ji abin da zan ce miki. Za mu yi miki aure, ba makawa, sannan za ki ci gaba da karatu a gidan mijinki har sai kin ce ya ishe ki, kin amince ko Kulsumun Goggo? Shalelen Baffa?
Ta ce, To Baffa fitsarin fa? Idan ya gane ina fitsari fa? Baffa bana son abin da zai jawo min tozarci da wulakanci, zuciyata tuntuni mai rauni ce ba za ta dauka ba.....!!!
Baffa ya ce, Insha Allahu hakan ba zai faru ba. Ki mika wa Allah dukkan alamuranki ki, bar kowanne tunani mara dadi, ki sa a ranki mutanen kirki masu soyayya ta fisabilillahi ba sa karewa a duniya.

Kusan kwanan zaune suka yi su ukun a wannan ranar suna ta lallashin Kulsumu tare da gaya mata falala da albarkar da ke cikin aure. Ita Kulsumu a ganinta daga Baffa har Goggo ba sa hango abin da ita ta ke hangowa, wato babu wanda zai yarda ya zauna da mai fitsarin kwance. Tunda kuwa aka yarda a aure ta da fitsarin kwance ta tabbata mijin ba na arziki ba ne, ko kuma bai sani ba, don babu wani mijin arziki da zai yarda ya auri mai lalurar fitsarin kwance.
Zuwa safe sun samu ta daina kukan da ta ke ta yi, amma ta yi shiru ba ta iya cewa komai. Ko me Goggo ta ce mata sai dai ta gyada mata kai, ba ta umh ba ta umh-umh, ta yi zuru-zuru sai idanduna da siririn karan hancin kadai. Ba laifi Kulsumu na da kyau kamar mahaifiyarta Sugrah, kowa ya san kyau irin na fulanin Gaya, ba ta debo komai na mutanen Yanleman ba, komai nata irin na mahaifiyarta ne, wadda ita kuma Goggo Shatu ta debo a komai. Ba ta da kauri sai tulin gashin kai wanda baya samun kulawa. Ba ta jima da fara kirgar dangi ba, amma kuturinta ya nuna nan gaba kadan za a yi mace lafiyayya daya cikin dubu.
Dan lange-langen jiki gare ta kamar ba ta cin abinci. Bakinta dan karami da shi mai kyau. Tana da dara-daran idanu farare kal, kullum tana lumshe su kamar mai jin barci. Don ma rayuwa irin ta kauye ya boye kaso 70% na hakikanin kyawun da Allah ya yi mata, ya dusashe haskenta, ya kuma boye asalin kalar fatarta.
Zuwa dare sun dan samu Kulsumu ta saki ranta, har ta yarda ta dan tsakuri faten wake da Goggo ta yi musu. Hajiya Rakiya ta gaya wa Goggo, Turaki ba ya garin yana can garin Abuja wajen yin visar tafiyarsa, amma in ya dawo za ta turo shi su gana shi da Kulsumu kafin daurin aure.

A daren ranar da Turaki ya dawo, suna can uwar daka suna fafatawa shi da mahaifiyarsa. Ta ce maimartaba yace lallai ya je su gana da Kulsumu, inda shi kuma ya ce, shi sam ba sai ya je ba, tunda ta yi musu shi kenan su yi komai yadda suke so. Zai yi biyayya. A ganin Turaki wannan auren ba shi da amfani. A auri yar mutane a ajiye ta miji ba ya nan shekara da shekaru. Ya rasa wane irin tunani iyayensa ke da shi, bai ga ta ina wannan auren da suka kitsa rana daya zai amfane shi ba. Kawai don a sa masa takunkumi. A karshe ma sai dai ya zamo takurawa da daukar alhaki ga yarinyar kadai. Ita ba miji ba, ita ba freedom ba. Sannan shi bai shiryawa aure yanzu ba, kum ma wai aure irin na kauye, zai so su bar shi sai ya gama dimbin karatun da ke gabansa ya fara aiki tukunna. Ya zabi yarinya daidai da burin sa. Wannan shi ne aure.
Da ya ga Umma ta dage kan zuwansa gidan su Kulsumu, har ran ta ya soma baci da musun da yake mata, sai ya amsa mata da zai je din, amma sai gobe bayan daurin aure. Umma ta yi tsalle ta dire ta ce, ita a yau komai dare zai je ya ga matar da zai aura, ya ga hannayen ta da 'yan yatsun ta kamar yadda sunnah ta tanadar. Wannan shine umarnin ta da na mahaifin sa.
Umma ba ta barshi ba sai da ta sa shi a gaba zuwa dakinsa ya yi abin da zai yi ya fito, yana ta bakin rai. Ta kira Batulu ta ce ta raka shi gidan su Kulsumu.

Turaki da kanwarsa Batulu suna tafe zuwa gidan Malam Jibo, Batulu rike da ledar kayan da Ummansu ta bayar su kai wa Kulsumu a matsayin kyauta ta farko daga mijin aurenta. Daga gidan Sarki zuwa Maza-Goma ba tafiya ce mai yawa ba, don haka da kafarsu suke tafe, hasken farin wata na haska musu hanya. Batulu farin ciki ya ishe ta, za ta iya cewa ta fi kowa farin ciki da wannan aure, sabida yadda Allah ya dora mata kaunar Kulsumu duk da ba ta samun martanin kaunar daga Kulsumun, ita dai tana sonta, personality dinta na burge ta. Shan kamshi da jan ajinta na bata dariya.
Wani zai yi tsammanin Kulsumu girman kai ne da ita, amma in ka fahimce ta za ka gane personality ne kawai. Tana so ta yi wa yayan nata hirar Kulsumu, amma ganin yadda ya hade rai kamar hadarin da ya nausa ya yi gabas, dole ta killace bakinta.
Ta san halinsa ba karamin aikinsa ba ne ya koma, yanzun ma don Umma (yadda suke kiran Hajiya Rakiya) ta sako shi a gaba ne kamar zata doke shi.
Goggo da Kulsumu na zaune a tsakar gida bisa tabarma suna sauraren radiyon jihar Kano, Baffa bai shigo gida ba tukunna, yana can majalisar hirarsu ta dattijai inda yau ba zancen da dattijan garin ke yi banda na daurin auren jikar Malam Jibo da dan sarkin Gaya, zancen ya yi tambari a garin Gaya kowa na ta mamakin yadda Turaki ya tsallake yayan kowa ya zabo yar talaka irin Malam Jibo. Akwai yayan masu kudi a garin irin mahaifinsa, sannan akwai yayan da suka shafi sarautar gidansu amma duk bai zabo cikinsu ba, sai Kulsumun Goggo wadda ubanta ba ma dan garin ba ne. Wasu sun taya Malam Jibo da maidakinsa murna, wasu kuwa hassada ce fal! Ransu. Ko ma dai mene ne, Malam Jibo da matarsa Goggo Shatu babu kowa a gabansu sai damuwar da ke sasakar kasan zuciyarsu na tunanin yadda wannan aure zai kare, ranar da ya bayyana zahiri ga Turaki abin da mahaifiyarsa ta boye masa.
Daga shi har Goggo Shatu ba su taba tunanin Hajiya Rakiya za ta yi musu wannan halaccin ba. Da gaske ne da aka ce, mutanen kirki ba sa karewa a duniya. Ya maida hankali ga tattara dan abin da yake tarawa wanda da shi ne za a yi wa Kulsumu yan kayan daki, da wanda mahaifinta zai kawo.

Batulu ta rangada sallama a tsakar gidan, Goggo ta rage sautin rediyon ta amsa. Ta ce,
Aa Batulu ce ke tafe da daddaren nan, in ce ko ba ke kadai ba ce?
Kulsumu a zuci ta amsa sallamar Batulu ta bi ta da idanu.
Batulu ta iso kusa da ita ta zauna tare da kama hannunta fuskarta fal faraa kamar gonar auduga, ta gaida Goggo, sannan cike da doki ta ce,
Ni da Yaya Turaki ne fa Goggo. Ya zo wajen Kulsumu.
Goggo ta yi maza ta mike, ta ce, Shi ne za ki barshi a waje? Maza je ki shigo da shi dakin Baffa, shi din yanzu ai dan gida ne ba bako ba da zai tsaya waje".
Batulu ta fita ta fada masa sakon Goggo. Harararta ya yi da farko, yana mamakin murnar data ke ta yi kamar itace mai auren, sai da ya ja fasali ya mula kafin ya nuna ya ji abin da ta ce.
Ya daga ido ya kalli kaskantaccen gidan da iyayensa suka nemo masa aure yana mamaki a cikin ransa. Agogon hannunsa ya fara dubawa ya kididdige wa kansa adadin mintunan da zai dauka cikin gidan, don shi bai dauki wannan auren da iyayensa suka dage sai sun yi masa da muhimmanci ba. Yana da nashi plan din, shi dai ya samu a barshi ya tafi karatunsa. Sai sun sake ganinsa nan kusa za su tursasa shi zama da matar.
Ya sa a ransa in yasa kafa ya bar Nigeria sai ya kammala karatunsa tsaf yazama cikakken likita zai dawo gida, ba wani hutu da zai dinga zuwa, in yaso in suka gaji da ajiyar yar mutane su maida ita wajen iyayen ta. Zai dinga jin lafiyar su ta hanyar da su ba za su dinga samunsa ba. Yana dawowa kuma dole su barshi ya auri zabin ransa. Daidai da ajin sa da matakin ilmin sa.
Wata irin ajiyar zuciya ya saki, a lalace ya ce da Batulu.
Mu je.
Batulu ta wuce gaba, ya bi ta a baya.
Goggo ta fito daga dakin Baffa inda ta shimfida masa sabuwar tabarma ta kunna musu fitilar kwai, kasancewar an dauke wutar lantarki.
Ya tsugunna ya gaida Goggo, ta amsa tare da sanya musu albarka bakidayansu, ta nuna masa dakin Baffa ta ce ya shiga, yanzu za ta turo Kulsumun.
Kulsumu ban da dukan tara-tara ba abin da gabanta ke yi. Karo na farko a rayuwarta da za ta kebe da Da namiji wai da sunan zance, sannan kuma wai a matsayin mijin auren ta. Wani abu da ba ta taba yi wa rayuwar ta mafarkin sa ba (aure) in ta yi laakari da halin da ta ke ciki. Aure shi ne abu na karshe da bai taba zuwa cikin mafarkanta ba, sai ga shi ya zo mata bagatatan, kamar saukar aradu. Da ma an ce shi din LOKACI NE idan ya zo tamkar habo yake. Dole sai ya zubo.
Hawaye suka cicciko idanunta. Bata san me zata ce idan ta je ba, bata san tarbar da shi zai yi mata ba. Batulu ta kama hannunta suka shige dakin Goggo.
Ta ce, Don Allah Kulsumu ki yi wa Yayana kwalliya, ki fesa turare kada ki tafi a haka don Allah Kulsumu.
Wata irin harara Kulsumu ta zabga mata, sai kuma ga hawaye sun biyo bayan hararar.
Goggo ta ce, Yau na ga sakarci, za ki karbi kayan nan ki sa ko sai na saba miki? Sakaryar yarinya kawai.
Batulu ta ce, Goggo yi mata a hankali, bana son abin da zai bata ranta. Kulsumu karbi kayan ki sa kada ran Goggonmu ya baci da ke, kin ji?
Sabida yadda ta kwantar da murya tana rokon ta dole Kulsumu ta karbi kayan ta shiga ciki tana sakawa, lakakai-lakakai kamar mai ciwon hannu. Goggo ta shigo tana fadin,
Wallahi Kulsumu ki fita idona in rufe, ya za ki barshi yana jiranki haka, saanki ne? Wane irin saka kaya ne wannan? Ko kuwa don kin ga kanwarshi na lallaba ki? Ina laifin masu kaunarka?
Ta kammala saka kayan tana ta zumburo baki ba tare da ta ce da Goggo komai ba.
Goggo ta dauko turaren da Hajiya Rakiya ta taba bata, ta fesa mata, Batulu ta ja hannunta suka fita zuwa dakin Baffa, bayan ta lulluba mata mayafi, kwalliyar dai gata nan ba fasali irin ta 'yammatan kauye, daga can jikin kofa Kulsumu ta rakube kamar a ce kyat! Ta arta da gudu. Batulu ta juya ta koma dakin Goggo.

Shiru suka yi aka rasa mai magana a dakin. Shi ba kallon ta yake ba, domin bai damu ya san kamanninta ba, bai damu ya san wacece ba, agogon hannunsa yake kallo ta dan kyallin hasken kwan fitilar yana kirga adadin mintunan da aka barshi a zaune yana jiranta kamar wani boyi-boyin gidansu. Ba ka ganin ko fuskarta, ta jawo mayafi har kanta ta rufe. Sarauta da aji ke aiki a jikin Turaki, don haka yake fadin ransa yadda yake so, a ganinsa wannan yarinyar ba ta isa ko magana ya yi mata ba.
Kulsumu ta tuna tarbiyyar Goggo shi ne, in ta ga babba ko a ina ne ta fara gaishe shi, don haka ta cije, ta daure ta ce da rarraunar murya,

Ina yini?

Shiru Turaki ya yi mata kamar bai ji ta ba. Daga bisani cikin muryarsa mai zurfi da rashin amo ya ce,
Yanzu ne ki ka san da mutun a dakin?
Kulsumu ta yi shiru.
Ya ce, To rike gaisuwarki bana so!".
Nan ma Kulsumu ba ta ce komai ba.
Ya yi tsaki, ya kara kuluwa da shirun da take masa sannan ya ce,
Yanzu ke da kuruciyarki kin yarda ki auri mutumin da ba zama zai yi ba tsawon shekaru masu yawa, a takure ki cikin gida da sunan aure, alhalin mijin baya nan, maimakon ki maida hankali ki yi karatun da zai amfane ki?
Idanun Kulsumu suka cicciko da kwallah. Kamar shawara ce yake ba ta, kamar kuma shagube ne yake mata. Ta rasa wanne yake nufi a cikin biyun. Ita dai ta san ba kwadayi yasa su Goggo yarda da wannan auren ba, suna da dalilin su. Cikin rawar murya ta ce,
Ni ma ba da son raina ba ne!.
Hawayen da take ta makalewa a idanunta ya gangaro.
Turaki ya kyabe baki duk da ba kallonsa ta ke ba balle ta san ya yi, shima ba kallonta yake ba balle ya ga hawayen da ta ke yi, ko ya kalletan bai ga fuskarta ba ta ja lullubi ta rufe fuskar kirif, ya ce,
Ba da son ranki ba ne amma ki ka yarda? Me ya sa ba ki fito fili kin ce ba ki yarda ba? Sai ki yi shiru a cuce ki for nothing? Anyway tunda kin ji kin gani, Allah ya bada saa!!!.
Yana gama fadin haka ya mike, tare da wucewa ta gabanta cikin takunsa na kasaita gab-gab-gab tafiyar su ta 'ya'yan sarauta. Ko daga bayan sa ka kalle shi ka san wannan namiji ne. Namiji mai matukar aji. Daga dakin bai tsaya a ko'ina ba. Ya fita zauren gidan yana jiran Batulu.
Kulsumu ta durkushe ta rushe da kuka a nan inda ta ke zaune. Ta yi kuka, ta yi kuka har ta ji babu dadi. Ashe ma mijin ba sonta yake yi ba aka tsiri wannan auren? To ina ga ya san ita din mai fitsarin kwance ce?
Muryar Batulu ta ji tana sallama da Goggo, don haka ta mike tana dafa bango domin duhun nan da ke yawan mamayar idanunta musamman da daddare ya rufe ganinta ruf. Ta shige daki, lokacin Batulu har ta kai soro. Yana cika yana batsewa suka kama hanyar gida.

Kulsumu ta tadda Goggo tana fiddo kayan da Batulu ta kawo wai inji Yayanta. Kayan kwalliya ne fal leda da turaruka. Baffa Jibo ya hana a kawo masa lefe ya ce in ta je can gidansu su

4 Comments On KULSUM
avatar
zainab-salisu-kasim

1 year ago

Reply

I luv dis book

avatar
zainab-salisu-kasim

1 year ago

Reply

I luv dis book

avatar
amina-abdul

1 year ago

Reply

love it

avatar
aysha-abubakar

12 months ago

Reply

I like the book

Please Login or Register in order to submit comment