Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Goggo ta taba Kulsumu, ta ce,
Wuce mu je mana Kulsumu, ba ki gaida Yayan naki ba.
Kulsumu ta yi gaggawar dauke idonta daga cikin nasa, ta sunkuya tana saka takalminta jikinta na kyarma. Kyarmar da bata san dalilin ta ba. Still bata bashi hanyar ba sannan bata gaishe shin ba saida ta gama saka takalmin ta. Murya can kasa kamar mai kun-kuni ta ce,
Ina wuni?
Ba za ta iya tantance ya amsa ko bai amsa ba, suka wuce ita da Goggo. Tana jin mahaifiyar tasa na masa bayanin ko su wanene dalla-dalla, uffan bai ce ba. He is not interested at all.
Har suka zo gida jikin Kulsumu rawa yake yi. Ta rasa abin da ya hargitsa ta haka. Ko ma dai mene ne ta san yana da alaka da saurayin nan dan kwalisa da Goggo ta kira da TURAKI. A gabadayan rayuwarta ba ta taba shiga halin da ta samu kanta a yau ba. Har ta zo barci tunanin fuskar Turaki ma'abociyar zati da kamala da wasu irin ilhamomi da bata taba gani a tare da kowa ba, bai bar zuciyarta ko na sakan daya ba.
*** *** ***

An debi satittika da zuwansu gidan Sarkin Gaya, Kulsumu ta ci gaba da zuwa makaranta kuma lokaci-lokaci tana sharkaba fitsarin kwancenta. Zuwa wannan lokacin Goggo da Baffa sun saddakar, sun yi amanna da cewa lalurar Kulsumu ba mai warkewa ba ce kamar yadda mai maganin Durbunde ya gaya musu. Sun yi sanyi da nema mata magani, sun koma addua da gayawa Allah.
Addua suke ba dare ba rana Allah ya yaye wa Ummukulsumu wannan lalura. Ya sa tana da rabon aure a rayuwarta, idan lalurarta ba mai karewa ba ce, Ya ba ta miji na gari, wanda zai kaunace ta domin Allah, ya zauna da ita a hakan da Ubangiji yake son ganinta.

Satittika na juyewa zuwa watanni, yayin da watanni ke juyewa su zama shekara, lokaci zuwa lokaci Goggo da Kulsumu na zuwa wajen Hajiya Rakiya in wani shaani na gidan ya tashi. Amma bata kara haduwa da Turakin da ya zauna mata a rai ba. Wanda har cikin mafarki zuwar mata yake a yanayi daban-daban. Matan Sarkin Gaya ba sa fita don haka Hajiya Rakiya ba ta taba zuwa gidan Goggo ba, amma ta turo manyan yayanta mata Hadiza da Ramla sun gaida Goggo kwanaki da ba ta da lafiya, suka kawo mata buhun shinkafa da katon din taliya. Duk kokarin Hajiya Rakiya na hada kawance tsakanin Kulsumu da autarta Batulu abin ya faskara, domin har gobe Kulsumu ta ki sakin jiki da kowa. Tana nan a yanda take. (Alienated with inferiority complex).
A ganinta bata da lafiyar da zata yi alaqa da mutane, kowa ya fita.... ita bata da daraja.....sunanta mai fitsarin kwance!
Batulu ta zo gidan ba sau daya ba, ba sau biyu ba amma in Goggo ta ce Kulsumu ta je wajenta ita kadai ba ta yarda ta je, sai in tare da Goggon za su je. Sannan in sun je bata yarda ta tashi daga inda Goggo take zaune. Yayin da Batulu tsakani da Allah ta ke son Kulsumu, take son su saba, ta yi iyakar kokarinta don su zama aminai Kulsumu ta ki. A ganin Kulsumu muddin ta yi amintaka da wani, watarana zai san lalurarta ya kyamace ta. Da muguwar rawa.... gwamma kin tashi. Abin da aka yi mata a GGSS Yar gaya ya kasa barin zuciyarta daidai da minti daya. Shi ta ke amfani da shi a matsayin hujja na abin da kowa zai mata in ya zo ya gane tana fitsarin kwance.

A wannan shekarar Kulsumu ta gama karamar sakandire (JSS), suka zana placement, suka zauna zaman jiran fitowar sakamakon jarrabawar su don wucewa babbar sakandire.
****
Wata ranar asabar, wadda ita ta bude shafin kundin kaddarorin Ummukulsumu, da suka zamo mujazar faruwar abubuwa da dama da cikin rayuwar ta.
Hajiya Rakiya ce ta aiko Batulu da sakon tana son ganin Goggo da yammcin ranar in ba ta da uzuri. Da Batulu ta zo ta fadi sakon, Goggo ta ce da dai za ta je gaisuwar mutuwa, amma dai za ta bari sai gobe. Ta je ta ce da Hajiya Rakiya da yamma za ta shigo insha Allahu.
Da yamma Batulu na gidan, don Hajiya Rakiya ta kasa hakuri ta sake aiko Batulun ta tunawa Goggo tana jiran ta, da Goggo za ta tafi Batulun ke tsokanar Kulsumu da ke cin gurjiya, tana ta kula ta ita kuma tana basar da ita.
Kulsumu zo mu je gidan mu mana don Allah, an kawo lefen Yaya Harira sai ki gani ke ma.
Kulsumu ta zumburo baki ta ce.
Ba zan je ba!.
Batulu ta wuce tana mata dariya, ko kadan bata ji haushi ba, da ma tsokanar ta ta ke yi, ta san ba za ta je ba din. Goggo ta yi wanka ta shirya ta ce,
Kulsumu shirya mu je tare man? Bana son zaman nan da ki ke yi a daki ke kadai.
Kamar za ta yi kuka, ta ce, Don Allah Goggo ki kyale ni, ki je abinki. Ni na fi so in zauna ni kadai din.
Goggo ta yafa mayafinta tana cewa,
Ai shi ke nan, idan ki ka kulla abota da aljanu ke ki ka sani, tunda kin ki yi da mutane. Yarinyar nan Batulu tana bin ki kina gudunta, ina laifin mai kaunarka?.
Kulsumu ta yi mata shiru.
Goggo ta ce, To ki yi min miyar kalkashi kafin in dawo, da na dawo sai na tuka tuwon masara.
Kanta na kan littafinta ta amsa da,
Toh Goggo, zan yi kafin ki dawo.

Yamma lis wajejen karfe biyar Goggo Shatu ta isa gidan Sarkin Gaya, a zauren karshe ta hadu da Hajiya Aina ta yo wa bakuwarta rakiya, uwargidan su Hajiya Rakiya kenan, suka gaisa sannan ta karasa sashen Hajiya Rakiya. Tarba ta musamman Hajiyar ta yi mata kamar yadda ta saba, amma ta yau daban ta ke.
Ta sa masu aikinta suka cika gabanta da soyayyun kaji da dambun nama da drinks na kwali kala-kala, ba wanda Goggo ta tuna a ranta sai Kulsumu, da ta yarda ta biyo ta ai da ta ci, ita ce mai son nama. Hira ta yi nisa tsakaninsu, Hajiya Rakiya ta tambayi Kulsumu, Goggo ta ce,
Tana gida, kin san ta ba son shiga mutane ta ke yi ba. Halin Kulsumu sai ita.
Murmushi Hajiya Rakiya ta yi, ta ce, Ni ai shi ya sa ta ke burge ni, ba ruwanta da kwaramniya, ga nutsuwa ga hankali da rashin hayaniya. Ina za ki hada ta da Batulu sarkin kankanba da giringidishi?
Goggo ta washe baki jin an yabi Kulsumun ta, in da abin da ta ke so, ta ke ji da shi a duniya, to Kulsumu ce.
Hajiya Rakiya ta bar zancen raha ta maida fuskarta serious alamun zancen da za ta yi mai muhimmanci ne. Ta ce,
Abin da ya sa na kirawo ki Hajiya Shatu magana ce mai muhimmanci za mu yi. Amma kafin in yi miki bayani zan so ki gaya min gaskiya, shin ko kun tsayar wa da Kulsumu miji?
Zuciyar Goggo Shatu ta doka, ta sake dokawa, sannan ta kara bugawa, ta yi nauyi mai tsananin yawa. Idan da abin da ba ta son tunawa ko ya shigo cikin tunaninta shi ne; watarana Kulsumu za ta yi aure. Ba don komai ba sai don lalurarta, sun samu yanzu ta rage damuwa ta maida hankalinta kan karatunta. Ba ta son duk wani abu da zai daga mata hankali ko ya janyo mata tozarcin da ta ke guje wa kanta. Goggo ta nisa sannan ta dubi Hajiya Rakiya mace mai tsananin kirki da halayen kwarai, sannan da halin dattako kamar ba matar Sarki ba.
Ta ce, Ranki ya dade, Kulsumu har nawa ta ke? Daga mu har mahaifin ta da ke Yalleman burinmu shi ne ta yi karatun jinyar nan da ta kallafa wa rai. Ba ta da wani saurayi balle tsayayye, kwata-kwata yanzu ne ta cika shekaru goma sha hudu, duk da cewa a karkara irin tamu ta isa aure, amma zancen aure ga Kulsumu tukunna”.
Hajiya Rakiya ta gyara zamanta, sannan ta mika hannu ta kama hnnun Goggo Shatu, murya a raunane ta ce,
Hajiya Shatu, sako ne daga Maimartaba zuwa gare ku ke da Malam Jibo, ku yi mana alfarma ku ba mu Kulsumu mu aura wa TURAKI. Daga yau zuwa sati biyu kacal! Mu kuma mun yi muku alkawarin za mu bar Kulsumu ta yi ta karatunta, ba malamar jinya ba, ko likita ta ke so za mu dauki nauyi da alkawarin hakan. Burinmu ni da Maimartaba shi ne kawai ya yi aure kafin ya tafi kasar Turawan da ya samu tafiya.
A cikin satin nan ya samu nasarar wani tallafin karatu wai cibinin (chevening scholarship), a yadda ya yi mana bayani ba karamin mai saa ba ne yake samu, sannan ba karamar wahala ya sha ba kafin ya samu. Zai tafi karatun likitanci har na tsawon shekaru biyar ko shidda a wata kasar Turawa. Da farko mahaifinsa bai amince ba sabida shekarun sun yi yawa, amma dagewar Turaki da nacin sa kan abin da yake so ya sanya Maimartaba amince masa a bisa yarjejeniyar zai yi aure kafin ya tafi ya bar matar tare da mu, duk karshen shekara ya dinga zuwa gida ya yi hutu ya koma har ya kare.
Auren shi ne kadai sharadin tafiyar, kuma Turaki ya amince. Ba don yana so ya yi aure a nan kusa ba, sai don ya samu yardar mahaifinsa da albarkarsa kan tafiyarsa, mun ce ya kawo yarinyar da yake so, ya ce ba shi da ita, don haka Maimartaba ya ce in ya amince ya yi auren gida shi ne abin da ya yarda da shi, bai yarda ya yi auren bariki ba, yarinya wadda muka san usulinta da tushenta mai cikakkiyar tarbiyya ya amince masa ya aura nan da sati biyu kafin lokacin tafiyar.
Hajiya Shatu na hanga na duba duk fadin garin Gaya ban ga yarinyar da ta yi min ba sai Kulsumun ki. Na yarda da nagartar ta da tarbiyyar da ki ka ba ta. Don haka ga mu da kokon bararmu, ina mai kara jaddada miki za mu rike alkawarin karatunta da hannu bibbiyu, za mu dau nauyinsa idan Allah ya tsawaita mana numfashi. Zan rike Kulsumu da amana kamar yar da na haifa, zan kula da rayuwarta kamar yadda zan kula da Batulu, sannan ba zan nesanta ki da ita ba, duk sanda kike so ki shigo ki ganta.
Kafin Hajiya Rakiya ta dasa aya a kan bayaninta, Goggo ta jike da gumi kashirban. Wannan shi ake kira Ga bikin zuwa, amma babu zanin daurawa”. Tabbas Turaki miji ne irin wanda ba ta taba mafarki wa Kulsumu ba. Duk fadin garin Gaya babu saurayi mai iliminsa. Kowa ya san wannan. Ta sanshi tun yana yaro, ta san kuruciyarsa. Ba shi da abokin fada, sannan ba shi da wani baragurbin hali. Duka halayensa na kwarai ne irin na mahaifin sa a iya saninta kowa yabon sa yake yi a garin Gaya, ana fadin duka halayen mahaifin sa sarki ya kwashe su. Lokacin da yana yaro ya sha ciyo gasar musabaqah a garuruwa daban-daban, duk makarantun da ya yi sunansa fitacce ne a matsayin wanda ya fi kowa kokari da himma. Tarbiyya kuwa duka yayan Hajiya Rakiya sun yi wa kowa zarrah a fadin gidan nan. Ina ma ina ma ina ma Kulsumu na da lafiyar da za ta mallaki miji kamar TURAKI.
Ba ta ankara ba ta ji hawaye sun biyo kuncinta masu dumi da taba zuciya. Ta yi duba ga kaunar da Hajiya Rakiya ke mata shi ne ya sa har ta zabo jikar ta cikin 'ya'ya dubu a garin Gaya bakidayansa don ta aura wa danta namiji tilo, kwaya daya jallin jal! Da Allah ya bata. Wanda watarana shi ne mai sarautar Gaya, idan babu mahaifinsa.
Nisawa ta yi, tare da saurin shafe hawayen idanunta kafin Hajiya Rakiya da ta juya tana magana da mai aikinta ta gani. Bayan Hajiyar ta gama magana da mai aikin ta dawo da hankalinta ga Goggo wadda ta yi shiru kamar ruwa ya cinye ta, deep in thought, inji bature, har ba ta san wane irin tunani ta ke ba.
Ke nake sauraro Hajiya Shatu, shin me ye raayinki?
Goggo ta gyara zamanta, sannan ta ce,
Na gode Hajiya Rakiya da wannan kauna da ki ka nuna wa Kulsumu, kuma na ji duk bayananki. Na fahimce su na yi naam da su. To amma kin sani ba ni ke iko da Kulsumu ba, tunda ba ya ta ba ce, mahaifinta yana raye. Sannan Baffa da ke gaba da ni bai ji zancen nan ba. Don haka ki ba ni kwanaki uku mu zauna mu duka ukun mu yi shawara, ni Baffa da mahaifinta. Duk abin da muka yanke zuwa ranar talata zan zo na fada miki.
Hajiya rakiya ta ce, Gaskiya ne, na kuma yarda da batun ki, Allah ya tabbatar mana da abin da ya fi zama alheri. Amma kwana uku ya yi yawa kamar yadda na gaya miki ne babu isasshen lokaci, saura sati biyar tafiyar tasa, don haka cikin sati biyu muke so a yi komai a gama, ko sa samu su shaku, su fahimci juna kafin tafiyar tasa.
Goggo ta ce, To insha Allahu a yau za a kira Malam Hadi, gobe ya zo mu tattauna, zuwa jibi za ki gan ni da abin da muka yanke. Na gode Hajiya Rakiya. Na gode.

Ko da Goggo ta dawo gida ta tadda har tuwon Kulsumu ta tuka mata, gabadaya jikinta a sanyaye yake, ta ji dadin girkin da Kulsumu ta yi mata don da ba za ta yi shi ba, ba ta jin tana da kuzarin da za ta iya yi. Ta kasa hakurin jiran Baffa ya dawo, ta aika yaron makotansu ya kira mata shi a inda suke zaman hirarsu shi da dattijai yan uwansa, wato dandamalin gidan wani makwabcinsu Malam Ayuba.
Baffa ya shigo hannunsa dauke da bakar leda ya zo kofar dakin Goggo yana fadin, Kulsumu zo ga balangunki ki ci da zafi-zafinsa.
Kulsumu ta fito daga uwar dakin Goggo, da alama yanzu ta idar da sallah, da hijabi jikinta da carbi a hannunta, tana murmushin murna ta karba ta ce,
Baffa na gode, kuma yau insha Allahu girkina za ka ci, ni na tuka wa Goggo tuwon dare, na yi miyar kalkashi mai shegen dadi.
Ya ce, Ki ce yau zan ci jagwalgwalon Ummukulsumu kawai, me ki ka iya ban da kwanciya jikin Goggo da cin nama kamar mage?
Kulsumu ta shagwaggwabe fuska tana fadin, Allah Baffa na fi matarka iya tuwo, kuma za ka ce na gaya maka.
Goggo dai sai kallon Kulsumu ta ke, tana ta kissima abubuwa masu yawa a ranta. Kalaman Hajiya na ta yawo a cikin kanta.
Sai da Baffa ya ci abincinsa sannan Goggo ta shiga turakarsa, ta gaishe shi ta nemi gefensa ta zauna. Kallo daya ya yi mata ya san cewa, magana ce damkam a bakinta. Ya ture farantin tuwon bayan ya wanke hannunsa a silba, Goggo ta kira Kulsumu ta zo ta fidda kwanukan. Ya maida hankalinsa kanta ganin tana hawaye.
Ya ce, Subhanallahi! Me ya faru Aisha?
Goggo ta soma shesshekar kuka, ta ce, Baffa ALHERI ne ya samu Kulsumu, amma ba ta da halin karbarsa, shi ne nake kukan tausaya mata.
Baffa ya ce, Sai dai in ba rabonta ba ne, idan rabonta ne kuwa za ta same shi. Idan ba rabonta ba ne Allah zai musanya mata da mafi alherinSa insha Allahu. Gaya min me ke faruwa?
Tiryan-tiryan Goggo ta kwashe sakon Maimartaba Sarkin Gaya da matarsa Hajiya Rakiya da yadda suka yi da Hajiya Rakiyar na cewa za su yi shawara ta gaya masa. Baffa shiru ya yi ya kasa cewa komai, daga bisani ya ce,
Na ji dadi da ki ka ce mata za ki yi shawara ba ki yi saurin yanke hukunci ba. Lokaci ya yi da mahaifin Kulsumu zai san halin da diyarsa ta ke ciki. Ranar wanka ba'a boyon cibi, daga nan sai mu yanke shawara a kai. Yanzu zan aika a gaya masa ina kiransa gobe. Ni da ke kuma mu yi istikhara a daren yau mu roki Allah duk abin da ya fi zama alkhairi ga rayuwar Kulsumu.

Kamar yadda Baffa ya bada sakon kiran Malam Hadi, washegari kuwa sai ga shi ya zo. A falon Goggo ya karya kumallo, Kulsumu sai murna ta ke na ganin Babanta, ta kawo masa wannan ta kawo masa wancan. Ta rasa ina taka saka ina taka aje da shi. Ya kawo musu tsarabar kauyen Yalleman iri-iri, ciki har da gurjiyar Kulsumu, da yazawa da gwaza da goba da su dinya. Sannan ya kawo wa Kulsumu sabon takalmin roba daidai kafarta. Sai da ya gama cin dumamen da Goggo ta ba shi da kunun tsamiya, sannan ya tadda Baffa a turakarsa. Ba jimawa Goggo ta bi shi. Sake gaisawa suka yi, Baffa ya tambaye shi lafiyar iyali. Daga nan kai tsaye Baffa ya gaya masa komai da Goggo ta gaya masa jiya, ya kare zancensa da cewa.
Abin da ba ka sani ba Abdulhadi, abin da ba mu taba gaya wa kowa ba don mu kare mutuncin Kulsumu kai kuma mu raba ka da damuwa irin wadda muke ciki shi ne, Kulsumu tun haihuwarta har yau da ta ke shekaru goma sha hudu a duniya ba ta bar fitsarin kwance ba. Ba irin neman maganin da ba mu yi ba, a karshe muka gaji muka bar wa Allah ikonsa.
Ba karamin firgita Malam Hadi ya yi ba. Ba karamar damuwa ya shiga ba. Bai boye ba ya nuna musu rashin jin dadin sa da ba su gaya masa ba, da ba'a yi haka ba tuntuni. Baffa ya ba shi hakuri, ya kuma gaya masa ba don komai suka bar zancen a tsakaninsu ba, sai don guje masa damuwa yana fama da hidimar iyali. Suka gaya masa wannan ne ma dalilin barinta makarantar Yar gaya. Malam Hadi ya nisa, sannan ya dubi surukan nasa cikin ladabi, ya ce.
Ni a shawarata Goggo, dole ki gaya wa matar Sarkin Gaya gaskiyar halin da Kulsumu ke ciki, sabida baki da uzurin da zaki bata na hana su auren ta bayan wannan kauna data nuna miki, in sun ga za su iya aurenta da lalurarta kuma su barta ta yi karatun kamar yadda suka yi alkawari, ni na amince, duk da na so Kulsumu ta yi nisa da karatun gaba da sakandire kafin ta yi aure. In kuma sun ga ba za su iya ba, kin ga shi ke nan ba mu yaudare su ba, sai a bar zancen cikin mutunci Kulsumu ta ci gaba da karatunta.
Ni kuma daga yau sai inda karfina ya kare wajen nema wa Kulsumu magani, insha Allahu. Allah zai yaye mata.
Gabadayansu sun yi naam da shawarar Malam Hadi, duk da Goggo tana cikin zullumin ta inda za ta iya bude baki ta gaya wa wani wannan babban sirri na Kulsumu. To amma an ce, ranar wanka ba a boyon cibi, kuma tsira da mutunci ya fi tsira da kudi, ba za ta so abin da zai bata zumuncinsu da Hajiya Rakiya ba, ko a cikin mutane Hajiya Rakiya mutum ce har da rabin mutum, wadda ta cancanci kowanne irin kyautatawa daga gare ta.
Ba ta kwanta ba a daren ranar, sai da ta yi sallar istikhara kamar yadda Baffa ya umarce ta. Shi ma Baffa a wannan daren ko na minti talatin bai runtsa ba, kwana ya yi sallah yana roka wa Kulsumu alheri a kafatanin rayuwarta. Haka mahaifinta Malam Hadi, shi ma a wannan ranar kwana ya yi yana yi wa yar sa da ya fi so addua. Sosai tausayin Kulsumu ya nannade shi, don haka ne yau da zai taho bai iya tsayawa sun yi sallama ba, tana bandaki ya sanya takalmansa ya wuce, yayin da Kulsumu ta kwana cikin fitsari sharkaf! Na yau har ya fi na kullum yawa.
Da ma dai ta dade da daina kwana a kan katifar Goggo, a kan tabarma da leda da zani da ta ware musamman don kwanciya barcinta kadai ta ke kwana, da safe ta wanke su ta shanya, don haka dakin Goggo ba ya zarni. Sosai Kulsumu ke kula da tsaftarsa da sanya turaren wuta akai-akai.
Washegari, wato ranar da Goggo ta yi alkawarin komawa gidan Sarkin Gaya, tun karfe hudu na yamma ta tafi, ta kasa bari yamma ta yi sosai sabida yadda ta matsu ta san matsayin Kulsumu.
Sosai Hajiya Rakiya ta karbe ta yau ma kamar kullum. Suka kule a uwardakin Hajiyar suna hirarsu ta aminci, duka a kan matsalolin yayan Hajiya Rakiya na gidan aure. Suna kulla shawarwari, daga bisani Hajiya Rakiya ta nemi jin shawarar da su Goggon suka yanke a kan maganarsu.
Da fari Harshen Goggo Shatu ya yi mata nauyi, amma daga bisani ta ture komai ta labarta wa Hajiya Rakiya rayuwar Kulsumu tun haihuwarta da tasowarta, da halin da ta ke ciki a yanzu.
Wuta ta dauke wa Hajiya Rakiya, ta dade shiruuu! Tana tunani cikin zuciyarta...Turaki ko a cikin yayanta daban yake wajen tsafta da gayu, ga shi da kyankyami, ga shi da son kamshi. Gashi da gudun wari komai kankantar sa. In abinci ya kwana ba ya cin sa, ba ya sharing komai nasa da kowa, hatta kofin shan ruwansa shi kadai yake amfani da shi, kuma ba ya raba shi da dakinsa. Yawan tsaftarsa kan sa a yi tunanin yana da aljanun tsafta, komai nasa tsaf! Yake. Jikin sa fes yake, tufafinsa karkar kullum cikin wanki da karin guga, dakinsa neat & tidy. Ba ya yarda sauro ya cije shi, kullum sai ya feshe dakinsa da insecticide sannan yake iya kwana a cikinsa. In ka ji shi yana fada da kannensa mata, to a kan tsafta ne. Ba ya cin abincin kowa a gidan sai na mahaifiyarsa, tsammani za ka yi shi din babban maaikacin NAFDAC ne. Idan ta aura mishi mai fitsarin kwance anya ta yi masa adalci?
To amma mutanen nan ta riga ta gama jin sirrinsu, idan ta juya musu baya a

4 Comments On KULSUM
avatar
zainab-salisu-kasim

1 year ago

Reply

I luv dis book

avatar
zainab-salisu-kasim

1 year ago

Reply

I luv dis book

avatar
amina-abdul

1 year ago

Reply

love it

avatar
aysha-abubakar

12 months ago

Reply

I like the book

Please Login or Register in order to submit comment