Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hajiya Nasara ta yi murmushi ta ce,
Da da ki ke gidan mijinki su da wa suka zauna?
Goggo ta yi dariya, ta ce, Ai Kusulmu ba ta son mutane, kin ganta nan ta fi son kullum ta kule a daki tana tunanin mijin da ba ya sonta!.
Kulsumu ta yi kasa da kai cike da jin kunyar abinda Goggo tace a kan ta.
Hajiya Nasara ta gyada kai tace,
Kusulm, ita rayuwa da ki ke gani fadi ne da ita. Rassa gare ta kamar ganyen bishiya. Wasu kaddarorin naka ma ba su zo ba, kuma ba su fara ba. Ardullahi waasia (duniyar Allah fadi gare ta). Ki bude zuciyarki ki ba wa sababbin kaddarori damar shigowa, ba ki san wacce ce mafi alheri a gare ki ba.
Ki bi ni in hada ki cikin yaya na kiyi karatun ki. Na yi miki alkawarin watarana sai kin yi alfahari da kanki, Goggonki da Baffa sun yi alfahari da kasancewar ki jika a gare su, sabida ni gidana ba'a komai sai neman ilimi da neman lahira.
Kusulmu ta lumshe idanunta, ta baiwa hawayen da ke son zubowa tana makale su damar saukowa. Ba wai ba ta yarda da kalaman Hajiya Nasara ba ne. Wadda ta kwana da sanin makusanciya ce ta jiki ga Goggo. Tun bata da wayo ta san sunan Nasara a bakin Goggo. Illa ba ta son yin nisa da garin Gaya, Gaya mahaifar ta, Gaya tushen ta, Gaya abar tinkahon ta. Ba ta son abin da zai nesantata da mahaifar Turaki, don ta san ko ba dade ko ba jima, zai dawo mahaifarsa gaban iyayensa.
Haka kawai jikinta ke yawan bata cewa; kaddarar da ke cikin rayuwarsu ita da shi ba ta da karshe, it's infinite, ba ta da iyaka! Aurensu da rabuwarsu is just a link na haduwa ba dai rabuwa ba. Jikin nata na ci gaba da bata akwai uzuri mai karfi da ya hana Turaki dawowa ba ita ce sila ba, ba fitsarin kwancen ta ne uzurin ba, haka ba kiyayyarta ce sanadi ba.
Duk da tana jin ciwon yadda ya karbe ta wasarere cikin rayuwarsa a yar guntuwar rayuwar da suka yi tare, wadda daga haduwar har auren da zaman cikinsa bai fice na 'yan satittika ba. Zuciyarta ta zarme da soyayyar Turaki ba tare da ita kanta ta san son nashi ta ke ba. Soyayyah mai yawa kuma mai tsayawa a zuci. Turaki abin a so ne, ga kowacce diya macen da ta san ciwon kanta.
A dan zaman da ta yi da shi ta fahimci shi din mai tsananin biyayya ne ga iyayen sa, mai son faranta ma mahaifiyar sa. Mai son 'yan uwan sa mai tsantseni a cikin mu'amalar sa da kowa. Mara yawan magana, mai tsafta, mai tsare girmansa. Uwa uba riko da addini; Mai kiyaye lokutan sallah. A dan zaman da tayi dashi bata taba jin sallar asubah ta wuce shi a masallaci ba. Ginshirar sa da sarautarsa na hanawa ka abokantake shi da sauri, sannan suna kara masa kwarjini da ilhama ga duk wanda muamala ta hada su.
A wancan lokacin, ta yi kadan ta san soyayya, amma daga ganinta na farko da Turaki ta san ya zauna mata a zuciya da wani irin feeling da ba ta taba ji a kan kowa ba. Fuskarsa ta zauna a ranta, ta kasa bacewa.
Ranar farko da ya zo gare ta a matsayin sa na wanda zai aure ta ba ta kalli fuskar sa ba sabida rashin wadatar haske, amma ta ji muryarsa har cikin kashi da bargo.
A duk lokacin da ta ji muryarsa samun kanta ta ke da gigicewa. Ita dai ta san wannan ba shi ne karshen kaddarori tsakaninta da shi ba. Haka take so kowa ma ya dauka, saidai da alama ita kadai ke wannan hasashen, daga iyayenta har nasa babu mai mai sauran hope na cigaban auren su, amma barinta garin Gaya na nufin; rufe kofar kowacce sauran alaka tsakaninta da DAN UMMA.
Duk abin da iyayensa ke hange na rashin dawowarsa hasashe kawai suke yi, bai sake ta da kansa ba! Abin da makauniyar zuciyarta mai yawan so ga Turaki ke gaya mata kullum kenan. Bayan a zahiri ga abubuwan nan a fili muraran. Ita dai ta fi yarda da cewa akwai abin da ya hana shi dawowa, amma ba kiyayyar ta ba kamar yadda iyayensa da nata ke hasashe, musamman in ta yi laakari da abin da Batulu ta taba gaya mata na cewa ko a waya Yaya Turaki bai kara kiran kowa ba, tun bayan da ya kira Umma da maimartaba ya ce ya isa lafiya, kuma karatunshi ya kankama, shi ke nan aka daina jin duriyarsa, layin ma ya daina aiki.

Hajiya Nasara ta dafa bayanta ganin ta luluka a duniyar tunani.
“Kusulm, ina kara gaya miki kin yi kankanta da sanya soyayya a ranki, musamman soyayyar da ba za ki samu martaninta ba. Yara kamar ki kamata ya yi a ce a wadannan shekarun suna kokarin gina rayuwarsu ne ta yadda watarana za su taimaka wa iyayensu a lokacin da karfinsu ya kare. Ki bi shawarata ki bi ni, ni da Goggonki duk daya ne. Ko ban maye miki gurbin Goggonki ba zan kamanta. Ni dai so nake in ga kin fidda damuwar tsohon mijinki a ranki, kin kama abin da zai amfane ki.
Kunya ta kama Kulsumu, ya ya aka yi duk suka san tana da damuwa a kan Turaki ne? Ita da bakinta ba ta taba yin zancen da Goggo ba, amma kullum Goggo ta tashi yi mata fada in ta tashi barci ta ganta a zaune, cewa ta ke tana tunanin Turaki, kuma kwarai abin da ta ke yi din kenan Goggo ba ta yi karya ba.
Tunanin Turaki dadi yake mata, duk da babu wani positive relationship da zata iya dorarwa a takaitacciyar rayuwar ta da shi. Ban da ma rashin imanin da ya gwada mata ya raba ta da diyaucin ta alhalin ya san ba shi da burin ci gaba da rayuwa da ita.

Hawaye ne suka cicciko idonta, ta rusunar da idanunta kasa tana jin rarrashin da Hajiya Nasara ke mata. Tana auna kalamanta a mizani na hankali da tunani, duk abin da ta ke fadi wanda zai amfane ta ne, amma ba zai amfane tan ba sai ta manta da Turaki. Sai ta haka rami ta binne dukkan memories dinnan masu alaqa da shi da duk abin da ya shafe shi.

Hajiya Nasara ba ta gushe tana lallashin Kulsumu da jan raayinta kan neman ilmi da son ta maye mata gurbin uwa ba, har sai da Kulsumu ta amince za ta bi ta din, zuwa inda ba ta san ko ina ne ba. Haka nan dai ta ji Hajiya Nasara ta kwanta mata, ba ta taba haduwa da wayayyiyar mace mai magana kai tsaye cike da ilimi kamarta ba.
A gabadayan kalamanta akwai concern da nuna kauna. Babu takurawa ko son yi mata dole. Misalai kawai ta ke kawo mata na hanyoyin da za ta bi rayuwarta ta inganta, kada ta bari zawarci ya kashe mata rayuwa, idan ta amince da hakan ita kuma za ta taimaka mata ta gina rayuwarta, amma fa sai ta yi mata alkawarin za ta manta da "Turaki".
Idan Baffa ya amince in bi ki, kamar yadda Goggo ke so zan bi ki. Amma za ki dinga kawo ni akai-akai ina ganinsu. Ni kuma na yi miki alkawarin zan manta da shi, zan tsaya in yi karatu.
Masha Allahu!.
Goggo da Hajiya Nasara suka hada baki suka fada.
Hajiya Nasara ta jawo ta jikinta tana bubbuga bayanta, Allah kuma zai dube mu, Ya ba ki miji na gari, wanda ya fi Turaki komai da komai!!!.
A can kasan ranta ta san ta binne Turaki ne ba don ya mutu ba, sai don ta bi shawarwarin da wadanda suka fi ta hankali ke ba ta. Ta kuma yi ilmin da ko ba ta koma matsayin matar Turaki ba, za ta rike Goggo da Baffa a sauran shekarun tsufan su, ko bata daina fitsarin kwance ba, zata samu abin yi wanda zai dinga mantar da ita lalurarta! Amma ba ta da wani buri na samun mijin da ya fi "Turaki". Aure kuma ta gama shi ke nan har karshen rayuwarta!!!

Ko da Baffa ya dawo ya ga Hajiya Nasara ya yi mamaki. Ya kuma yi murna. Su biyu suka rage wa junan su a zuriyar su kaf! Ita da Goggo. Ta gaya musu tunda suka tafi kasar Ingila bayan haihuwar 'yar ta ta biyu Sakinah inda aka tura mijinta aiki ba su kara zuwa Nigeria ba sai yanzu da mijinta yayi ritaya suka dawo gida Nigeria gabadaya, shekaru ashirin da biyar ke nan cif! Su kuma ba waya ba balle ta dinga kiransu don su dinga jin lafiyar juna, a lokacin waya bata zama gama-gari ba, amma yanzu ga wayoyin hannu na zamani ta zo musu da su, za su kasance tare ko yaushe. Ta gaya wa Baffa bukatarta na a ba ta rikon Kusulmu, tana so ta sa ta a makaranta kafin Allah ya ba ta mijin aure.
Baffa ya ce, Da ma ta zo min da zancen tana son ci gaba da karatun aikin jinya a Kano, na ce ta saurare ni ne don hankalina bai kwanta da tafiyarta wani gari ta zauna babu idon kowa ba kuma babu aure. Amma yanzu hankalina ya kwanta tunda tana tare dake, na san zaki kula da ita kamar Goggon ta, Allah ya tabbatar da alkhairi.
Da fatan dai Nasara ba za ki kara dadewa ba ki zo ba, kada ki dawo ki tarar ba ma raye, shekarun kullum kara turawa gaba suke yi, karfi na kara karewa.
Goggo ta fada cikin karyayyiyar murya.
Insha Allahu Yaya Aishatu hakan ba zai sake faruwa ba, ko don Kusulmu dole zan dinga kawo ta akai-akai. Mun riga mun yi (retire) ai, Abba ya dawo gida kenan din-din-din.

Kwanan Hajiya Nasara uku tare da su, suka yi haramar tafiya. Direbanta da ta sallama ya dawo daukanta ranar asabar. A cikin kwanaki ukun Kusulmu na kimtsawa a hankali. Saboda jikin ta gabadaya a mugun sanyaye yake. Bata farin - ciki haka bata bakin - ciki. Abubuwa ne da yawa cunkushe a zuciyar ta; Ga kewar rabuwa da Goggo, ga kewar barin garin Gaya bakidayansa, garin da tun haihuwar ta in ba 'Yalleman zata je ba bata taba barin sa ba, ga kuma zullumin wace irin rayuwa kuma zata je ta taras a gidan Haj. Nasara? Duk dadewar da Nasaran ta yi bata tare dasu bata tashi zuwa ba sai a wannan gabar, gabar da rayuwa ta yi mata zafi. Wannan kadai ya isheta isharar cewa Allah ya jefo Haj. Nasara ne a daidai wannan lokacin don ta tallafi rayuwar ta.


Washegari lahadi suka kama hanya Haj. Nasara na daga barin dama na motar Kulsumu na daga barin hagu, ta manne a jikin kofar motar tana kallon waje, idanunta kurr! Akan hanya tana kallon yadda suke barin yashi da kwazazzabon garin Gaya. Ji take tamkar in ta tafi ta tafi kenan bazata dawo ba.... Soyayyar mahaifar ta da tunanin dabdalar kuruciyarta na kara mamaye zuciyar ta.... Har suka bar kwazazzabo suka hau kwalta mikakkiya motar ta soma wuce bishiyun gefen hanya suka nausa can wani yanki na tsakiyar Najeriya....!!!

Masha Allahu laquwwata illa billlah!
Mu karasa a littafi na biyu.
Tare suke
Taku har abada,
Takori


Ga masu bukatar tsofaffin littatafaina zaku iya samunsu a softcopy, ku tuntubeni a wannan lambar 07030137870.

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


4 Comments On KULSUM
avatar
zainab-salisu-kasim

1 year ago

Reply

I luv dis book

avatar
zainab-salisu-kasim

1 year ago

Reply

I luv dis book

avatar
amina-abdul

1 year ago

Reply

love it

avatar
aysha-abubakar

12 months ago

Reply

I like the book

Please Login or Register in order to submit comment