Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka saba.
Idan ka san Kulsumu a baya lokacin da take gaban Kakanninta ita kadai kwal, tana rayuwar kunci da kadaici, ka kuma gan ta yanzu kaga yadda take harka da jama'a a gidan sarauta gaban surukanta abin zai baka mamaki ya kuma baka sha'awa. Ta saki ranta sabida babu mai takura mata ko nuna mata kyara, babu mai hantarar ta, ta kan ce a ranta don basu san lalurar ta bane, sannan Laraba ta rike sirrin ta, mutum ce mai amana sosai.
Kwanakin baya data je ganin gida a garin su Maradi har maganin gargajiya ta karbo mata na fitsarin kwancen, ta tsaya a kanta taga cewa ta yi shi daidai tsayin kwanaki uku. Akwai alamun sauki domin yanzu sai tayi sati ma bata yi ba, amma in zata yin, sosai take yi a lokaci guda har yana malala bisa carpet.
*** *** ***

Lokacin da aka fara daukar dalibai a SS1 Hajiya Rakiya ta tunasar da Maimartaba alkawarin da suka yi wa su Goggo na barin Kulsumu ta ci gaba da karatunta. Don haka ita da Batulu aka nema wa wata makarantar kudi mai kyau a nan kusa da su suka fara zuwa jeka-ka- dawo. Sau tari idan ta zauna ita kadai ba ta komai zuciyarta tuna Turaki ta ke yi. Duk da ta sa shi a rukunin masu manyan laifuka a gare ta, sannan ya yi mata abin da ya dakushe haskensa daga idanunta, wani sako can na zuciyarta with emotion yake tuna shi. Emotion irin wanda babu irin sa a zuciyar ta. Ta kan tambayi kanta ko me yake ciki a halin yanzu? Ko me yake aiwatarwa? Ko ya yi kyakkyawar budurwa yanzu haka? Tunaninnika dai marasa tushe bare makama, wadanda suke tabbatar mata zuciyarta ta ba shi wani kebantaccen matsayi. Matsayi irin wanda babu mai irinshi a tare da ita. Ta kan ji su Umma suna hira ita da yayanta kan cewa, tunda ya tafi sau uku kawai ya taba yin waya dasu. Idan ta zo wajen sai su bar zancensa.
Abin da ba ta sani ba shi ne, iyayensa na cikin damuwa mai yawa a kan rashin ji daga gare shi. Tun bayan da yayi waya yace ya sauka lafiya. Basu kara samun layin da ya kira da shi ba, sun rasa ta hanyar da za su neme shi. Aka kwashe shekarar farko babu wayar Turaki, babu sakonsa. Shekara ta biyu ma haka, a hankali aka gangara uku. Kulsumu tana gab da zana jarrabawar barin babbar sakandire.
A wannan lokacin an samu ci gaba sosai ta fanninta. Ta kara girma ta zama cikakkiyar budurwa yar shekaru goma sha bakwai. Makerin budurci ya gama kera ta. Ilimi na arabi da na boko na shiga kanta, don haka kanta a waye yake, ta yi wayon fahimtar komai in its actual reality. Ta tabbata Turaki sabida ita ya nisanci iyayensa, sabida ba ya sonta. Amma ita din, a duka wadannan shekarun guda uku, ta yi - ta- yi duk iya kokarin ta ta mance shi, ta kuma daina jin feelings din nan masu dadi da sanyaya ruhi da ta ke ji a kansa ta kasa. Ko ta yi kokarin hakan ba ta cin nasara. Kamar tana girma ne ana kara mata emotions a kan sa. Wadanda sun fi kama da shauki na tsantsar SO! Da ace ta san ma'anar su, ba komai bane face SO! Kyautatawar iyayensa da yan uwansa gare ta na shafe damuwar rashinsa a kusa da ita. Tana ji a ranta za ta iya ci gaba da zaman jiran Turaki, daga nan har gaban abada! Idan har zai ci gaba da zama da ita a matsayin matarsa ranar da duk ya dawo.

*** *** ***
Suna zaune ita da Batulu a falon Umma suna karatu cikin textbooks dinsu, misalin karfe biyar na yamma. Daya na tada daya a kan ilimin chemistry, wato kowacce na yi wa yar uwarta tambaya a kan abin da ba ta gane ba, ita kuma ta na yi mata tambihi. Umma ta shigo dakin kamar an jefo ta, ba ta tsaya wajensu ba kai tsaye uwar dakinta ta shige, da alama cikin tashin hankali ta ke.
Duk sai suka kasa ci gaba da karatun, Batulu ta bi bayan Umma, amma sai ta samu ta rufe kofarta da mukulli. Suka zauna jigum-jigum sai ga Yaya Hadiza ta yi sallama. Duk suka yi mata sannu da zuwa, ta ce,
Yauwa yan bokon Umma, tana ina ne?
Suka ce, Tana ciki.
Hadiza ta karasa ta hau bugawa Umma kofa, tana mamakin dalilin rufe kofar ta da yammaci haka.
Kulsumu ta mike da nufin komawa sashenta don ta kawo wa Yaya Hadiza wani daddadan cake da meatpie da ta yi a safiyar ranar. Ta je ta zubo a faranti ta rufe da foil paper, ta zubo pineapple juice mai sanyi a jug wanda ta hada da kanta ta dawo sassan Umma. Ba ta tadda Batulu a dakin ba inda suke karatu, don haka kai tsaye ta nufi dakin Umma.
Ba a rufe kofar ba, amma an sakayo ta, alamun Hadiza ce ta shiga, sai bata rufe ba, tana gab da shiga dakin ta jiyo muryar Umma tana cewa.....
Maimartaba ya ce, raba auren Kulsumu da Turaki zai yi in ya cika shekara hudu bai zo ba, kuma saura watanni shida yanzu haka ya shekara hudun, ina zan kai kunyar iyayenta Hadiza?
Suna zaman-zamansu da yarsu na je na tattago su ba tare da sun shirya aurar da ita ba. Yanzu kuma in kwashe ta in mayar musu, in ce musu me? Ba ya sonta? Ko ubansa ne ya gaji da ajiyarta ya raba auren?
Turaki ya ba mu kunya Hadiza, ya nuna wa duniya ba wanda ya isa da shi ya wulakanta mu a idanun masu ganin kimar mu, ya banzatar da umarnin mahaifin sa ban yi masa baki ba, amma zai zo ya yi nadama a lokacin da ba ta da amfani".
Sum-sum-sum ta juya ba tare da ta karasa ba, da ta bar sashen Umma da baya da baya da gudu ta karasa falonta. Ta dangwarar da jug din da farantin a nan kan kilishin tsakiyar dakin ta yi daki a guje ta fada rub-da-ciki a tsakiyar gadonta.
Lumshe idanunta ta yi, tana jin wani irin tashin hankali da fargaba na rufto mata. Ita fa ko shekara dari ne a shirye ta ke da ta jira Turaki. Ba zata taba gajiya da jiran sa ba. Ko da kuwa zata tsufa ne a cikin wa'adin jiran nasa. Ba mutane irin sa ke shigowa rayuwar diya mace, su fita da sauki ba.

Tun daga ranar Kulsumu ta shiga damuwa, damuwa matsananciya, ta rage walwala, ta rage karatu. Fitsari tana yin sa jefi-jefi, amma tana tsananin kula da tsaftar muhallinta. Laraba na taimaka mata. Sannan Laraba bata hakura ba, ta cigaba da kokarin nemo mata magani duk sanda ta je gida Maradi.
Cikin wannan halin suka zana jarrabawar kammala makarantar sakandire ita da Batulu, suka koma zaman jiran fitowar jarrabawa.
A wannan dan tsukin, Kulsumu ta soma ramewa babu dalili, dama jikin ba wani jiki ba, zullumi da fargaba su ke ramar da ita, kullum tana kirge da watanni don tsoron zuwan wata shidda. Wata shiddan data ji an ambata a matsayin wa'adin karewar auren ta da Turaki. Wata shiddan da ke nufin karewar farin ciki a rayuwar ta. Domin ta yarda ta amince raba ta da auren Turaki, daidai yake da yankewar duk wani farin ciki nata.
Yadda ba ta walwala haka Umma ba ta walwala, ba komai yafi damun Umma ba irin nauyin kawar ta Goggo Shatu da maigidanta dattijon arziki Malam Jibo da sauran jama'ar gari wadanda basa gani su kyale. Balle abu in na gidan Sarki ne sai kowa ya ji shi a garin Gaya. Batulu na yawan damuwa da sabon yanayin Umma da Kulsumu cikin gidan, wanda ita bata san dalili ba, cikin su ba wanda ya furta zancen ga kowa. Sannan Umma bata san Kulsumu ta ji ba. Amma ita Kulsumu da ta san ainihin damuwar Umman ba ta yi mamaki ba. Don ta san ta da dattaku da gudun magana, da gudun zuciyar duk wanda take alaqa da shi, ga maimartaba baya taba furta magana ya canza, ta kwana da sanin shi kaifi daya ne.

*** *** ***
Komai aka sa wa lokaci a hankali komai daren dadewa za ka ga ya zo cikin yardar Ubangiji. Watanni shidan sun zo sun gifta like a blink of an eye (tamkar kiftawar ido). A wannan rana ta litinin, cikin watan Ramadhana mai alfarma, Maimartaba Sarkin Gaya Abdullahi dan Hamza jikan Abdullahi mai Gaya, ya nemi ganawa ta sirri da Malam Jibo da Malam Hadi, Goggo Shatu da matar sa Umma Hajiya Rakiya.
An yi ganawar ne a falon Maimartaba na ganawa da bakin sa na musamman, inda ya fara da bude taron nasu da addua, sannan ya tafi kai tsaye kan dalilin da ya sa ya nemi ganawa da su bakidayan su.
Kamar yadda ku ka sani, mun nemi auren Ummu Kulsumu a hannunku don kauna da gina zuria mai albarka, a yau ma kaunar ce ta sa zan raba wannan aure. Kafin in ce komai ina neman gafararku iyayen ta, a matsayi na na shugaba mai adalci dole ne duk wanda ke karkashina in tabbatar da adalci a kan rayuwarsa.
Hakika Allah ya kawo mu wani zamani da mun haifi yaya ne amma ba mu haifi halinsu ba. Ni bana daga cikin iyayen da za su dinga bin yayansu sai dai yaya su bi ni. Idan kuma sun ga ba za su bi ni ba, to ni kuma zan zuba musu ido ne su yi abin da suka zaba wa kansu, kasancewar ita duniya makaranta ce mai zaman kanta, kuma ta fi bagaruwa iya jima.
Yaro tunda ya tsallake ya tafi karatu kasar Turai bai kara waiwayo mu ba, balle matar sa, ina kuma da tabbacin lafiyarsa kalau, auren da muka yi mishi cikin mutunci da dattaku ne ba ya so. Don haka a addinance mun shiga hakkin yarinya kasanewarta mutum, kuma mai cikakkar lafiya. Ko addini ya bayyana wasu kayyadaddun watanni wadanda in babu auratayya a cikinsu babu kuma wani kwakkwaran dalili wanda sharia ta yarda da shi, aure ya gurbata. Mun kawo yarinya mun kulle tare da mu shekara hudu, alhalin ba za mu sauke mata babban hakkin aure ba, bayan ci da sha. Don haka na yanke shawarar raba wannan aure domin yarinya ta samu damar yin aure mai inganci. Da son ranmu ko babu.
Wannan shi ne adalcin da zan iya a matsayi na na shugaba. Ina so dukkannin mu mu yarda da kaddara, yarinya har gobe ya ce a gare ni, kuma in ta samu miji zan yi mata komai da uba ke yi wa yar da ya haifa. Shi kuma Turaki duk ranar da guguwar zamani ta sake shi na tabbata zai neme mu. A lokacin da ba shi da uzurin da zan karba.
Falon ya dau shiru, ba ka jin komai sai fyace hancin Umma, Maimartaba na son jin ta bakinsu, amma sun kasa magana. Da ya takura Baffa Jibo ya ce "su masu biyayya ne game da duk hukuncin da ya yanke, sai dai su yi fatan Allah ya sa hakan ya zama alheri ga rayuwar yaran gabadaya".
Umma ta nemi alfarmar yin magana, Maimartaba ya ba ta. Ta ce, tana rokon ko da an raba auren a bar mata rikon Kulsumu a hannunta. Amma sai Maimartaba ya ce, hakan bai yi daidai ba, domin manema za su ji nauyin zuwa gare ta tana hannun uwar tsohon mijinta alhalin yana raye.
Don haka Umma ta kara gigicewa, bata san ta shaqu da Kulsumu ba, sai yau da take neman kubuce musu. Goggo tana ta ba ta baki, tana fadin ba abin da zai raba zumuncin su insha Allahu. Daman kuma ba Kulsumun ce ta hada su ba. Ta yi wa Kulsumu kyakkyawan riko wanda ba'a samun irin sa daga surukai a wannan zamanin. Ga kuma babban halaccin data yi musu wanda bazasu manta ba na amincewa auren Kulsumu alhalin ta kasance mai lalura.
Ta kara da yi mata godiya tare da jinjina mata da cewa, ita din adalar uwa ce, kuma irinta tsiraru ne a cikin alumma.
Ba mutuwa ake wa kuka ba, sabo ne. tabbas wannan magana gaskiya ne, domin gaba daya gidan Maimartaba Sarkin Gaya ya rikice da koke-koke a kan tafiyar Ummu-Kulsumu, wadanda suka saba da ita sai kuka suke yi, musamman Batulu da Yaya Hadiza da suke ciki daya da Turaki. Haka tsohuwa Fulani. Amma sun sani Maimartaba ba ya magana biyu ya riga ya zartar da hukuncin da bai yi wa kowa dadi ba.
A yayin da ya sa alkalin fadarsa ya bai wa Kulsumu saki, bisa doron shariah.
*** *** ***

Komai ya zama kamar bai faru ba, komai ya zama kamar ba a yi shi ba, auren da sakin, shekaru hudun da suka dunkule suka shige cikin kundin tarihin Kulsumu, wadanda ba za ta taba mantawa da su ba.

......The beautifull, tall, handsome Turaki, and everything associated with him, will forever remain memorable in her autobiography.

.........Here comes a time when we are bound to think about our travails on earth, the triumphs and travails and...... Most especially to think about those who have wronged our lives in one way or the other, ...... and here is when he comes to her mind; ABUBAKAR TURAKI ABDULLAHI!!!

A karo na biyu yau ga ta a gaban kakanninta a matsayin sakakkiyar Prince Turaki, ko wace irin sabuwar rayuwa za ta fuskanta? Tunda alamu sun nuna rayuwar gabadaya juyawa ta ke kamar wahainiya? Abubuwan cikinta ba sa dauwama? Farin ciki da bakin ciki duka babu dawwamamme. Fitsarin kwance ne ya sa Turaki ya guje ta tabbas! Idan zuciyarta za ta yi mata halacci, to ta taimaka mata ta manta da Turaki kawai, ta yakice komai nasa.
Amma me? Zuciyar ta ki hakan. Ta tabbata ko da ya raba ta da budurcinta ba soyayya ce ta sanya shi yin hakan ba, tursasawar iyaye ce. A yanzu ta yi hankalin da ya isa ta gane fari da baki, ya kamata ta yi wa kanta karatun-ta-nutsu, ta yarda Turaki fa ba masoyi ba ne, bai taba sonta ba!!!
Tana iya tuno kallon KYAMA' da ke cikin idanunsa a duk lokacin da suka hada ido bisa kuskure. Tunda har uwarsa ta sani ba zai kasa sani ba (lalurarta). Watakila abin da ya sa ya gudu ke nan tunda ba zai iya rubuta mata saki ya ba su ba, ya tabbatar watarana za su sake ta da kansu.
Wani kakkarfan kukan tausayin kanta ne ya zo mata. Hakika tana da nakasa, nakasarta shi ne fitsarin kwance. And it is normal maza ba sa son mace mai nakasa balle irin tata so disgusting, ko sai yaushe Allah zai yaye mata? Ko sai yaushe za ta daina fitsarin kwance?
A fili yake idan har ba dainawa ta yi ba dole zaman aure ya gagare ta. Ba a kan Turaki kadai ba, a kan kowanne Da namiji, don haka gatan da za ta yi wa rayuwarta shi ne, ta hakura da aure, ta rufe babin Turaki da duk wani Da namiji daga zuciyarta. Ta tsaya ta nemi ilimi ta samu madafa, madafar da ko ba ta warke ba, to ba za ta wulakanta a idon duniya ba!

Da wannan tunanin, Ummukulsumu, ta rufe idanunta hawaye na zirarowa, tun dawowarta gida barci ya karanta gare ta, haka darare ke zuwa suna wucewa tana zaune dungurgur tana saka da warwara a kan makomar rayuwarta, da abin da ya kamata ta fuskanta. Sai a yau ne ta samu ta cimma conclusion na rufe littafin kowanne da namiji daga kan hanyarta, ciki har da dan Umma, TURAKI.
Ta kara sabunta burinta na son zama maaikaciyar jinya, duk da ta san mawuyaci ne Baffa ya barta ta tafi har cikin garin Kano karatu (school of nursing) alhalin ba ta da aure. Amma masu iya magana sun ce da rashin tayi a kan bar arha, kuma a rashin kira karen bebe ya bata, ta san Babanta Malam Hadi zai goyi bayanta.

Don haka a wani maraice ta samu Baffa a turakarsa ta bijiro masa da bukatarta. Baffa da tausayin Kulsumu ya sa ba ya son duk abin da zai bata ranta, ya ce, ta bari ta gama iddah tukunna, zai san abin yi. Amma can a karkashin zuciyarsa ba ya so, ba karatun ne ba ya so ta yi ba, ta bar gabansu babu aure shi ne damuwarsa.

Ranar wata asabar da ta bude wani sabon shafin a rayuwar Ummu Kulsumu, tana kicin tana hura wa Goggo wuta da wani itace mai hayakin gaske, idanunta sun yi jazir sai hawaye suke yi. Tunda tayi aure ta manta da yadda ake girki da icce sai dawowarta gidan su. Goggo na daki tana sallar walha, yayin da Baffa ba ya nan ya je duba amfanin gonarsa.
Lokacin da aka raba auren Kulsumu da Turaki, Maimartaba Sarkin Gaya a cikin adalci irin nasa ya shiga tunanin ta hanyar da zai kyautata wa yarinyar da iyayenta yadda za su rayu cikin wadata. Wata katuwar gona ya bai wa Baffa, sannan ya ce, duk sanda Kulsumu ta tashi ci gaba da karatu zai dauki nauyin karatunta, in ta tashi aure zai yi mata komai da uba ke yi wa yarsa. Don haka Baffa ba shi da abin yi a wannan dan tsukin na damuna da ya wuce kula da gonakinsa. Sosai ake shuka don a samu amfani mai yawa zuwa shekara mai zuwa.
***

Assalamu alaikum.

Muryar wata mace maabociyar kamala da kyawun fuska, mai matukar kama da Goggo, wadda a kalla ta yi shekaru hamsin a duniya ta yi sallama a tsakar gidansu.
Daga madafi Kusulmu ta amsa sallamar ba tare da ta fito ba. Goggo ma ta fito tana amsawa, a lokaci guda ta daskare a kofar dakinta ta saki salati ganin mai shigowar, ko ciwo tayi ta warke, haka komai nisan shekaru da canzawar yanayi, bazata kasa gane wannan kyakkyawar matar ba, ta hangame baki tare da cewa,
Wa nake gani kamar NASARA?
Matar da aka kira da Nasara ta karasa shigowa bakinta fal murmushi, ta ce,
Ni din na cika mai dumbin laifi Goggo Shatu, mun dade da dawowa ai, muna settling ne a hankali, sai yau na samu na daure na taso na zo don in wanke laifina a wajenki da Baffa.
Goggo ta ce, lale marhabin, lale da bakin turai, lale da 'ya ta Nasara. Barka da zuwa, shigo daga ciki Nasara".
Ta shimfida mata tabarma a rumfarta, Kulsumu duk tana jin su daga kicin, ta fito daga madafin da sauri data ji wadda Goggo ke ambata, ta je ta wanke fuskarta, sannan ta shigo dakin ta gaida Haj. Nasaran, ba ta zauna a wajensu ba ta wuce uwardakin Goggo. Bakuwar ta bita da kallo sannan ta ce,
Ba dai yar wajen Sugrah ba ce ta girma haka?
Goggo ta yi murmushi, Ita ce dai, Ummu Kulsumu.
Masha Allah tabarakarrahman. Wannan in a hanya na ganta ai ba zan gane ta ba. Ta yi saurin girma. In ce ko tana makaranta?
Har aure an mata, auren bai yi dadi ba, mijin ya tafi karatu ya ki dawowa sabida ba ya sonta. A karshe mahaifinsa ya raba auren, amma har karatun sakandire ta yi a hannunsu, gidan Maimartaba Sarkin Gaya.
Hajiya Nasara cikin tausayi da takaicin yadda aka jaza wa yarinya karama kamar Kulsumu zawarci ta ce,
Amma kam Goggo da ina nan da baza a yi auren nan ba ma, don ba zan yarda a cire ta makaranta a yi mata aure ba. Har nawa yarinyar ta ke? Ga shi an maidata zawara da kankantar shekarunta, yanzu ina amfanin wannan aure? Amma wannan ya cika mara rabo. Yarinya kyakkyawa haka ya ce ba ya so?
Goggo ta yi murmushi kawai, ta ce, akwai dalili, sannan kowa da rubutacciyar kaddararsa. Kuma ba wanda ya tara sani da Allah, amma a lokacin ba mu da zabi ban da mu yi wa Kusulmu wannan auren, sabida darajar iyayen yaron. Kuma dai kamar yadda nace ne akwai babban dalilin da ya sa muka amince. In kin nutsu zamu tattauna ko zuwa gobe ne. Ina ce dai nan zaki kwana ko? Ya ya yaran naki duka? Na san yanzu duk sun tara yara su ma.
Hajiya Nasara ta nisa ta ce, Kwana har uku zanyi anan. Mu kwana mu hantse mu yi hirar da muka yi shekaru bamu yi ba. Yaran daya ce kawai ta yi aure a cikinsu, wato Sakinah, yaranta biyu. Auta Nasma karatu ta ke. Yayansu aikin sojancin ruwa yake. Alhamdulillah ana nan ana ta faman kokarin tarbiyya har zuwa yanzu.
Haka suka yi ta hirar yayan Hajiya Nasara guda uku, tana gaya wa Goggo labarin kowannen su. Da abubuwan da suka faru da ita a shekarun data kwashe a kasar turai. Goggo ma tana bata nasu. Labarin auren Kulsumu da Turaki kaf ta gaya mata da halin da Kulsumu ke ciki. Wani matsanancin tausayi ya kama Nasara, fitsarin kwance? Ta fada ta sake maimaitawa. "To ko shiyasa mijin ya ki dawowa?" Ta tambayi Goggo. Goggo ta ce "Allah masani, don suma iyayen baya neman su. Amma dai maimartaba ya ce yana da tabbacin lafiyar sa kalau". Kulsumu tana daki tana jinsu ba ta kara fitowa ba, sai da Hajiya Nasara ta sa murya ta kira ta, ta ce ta zo kusa da ita ta zauna. A kunyace ta zauna kanta a kasa, Hajiya Nasara ta dafa kafadunta ta ja ta jikinta ta ce,
Kusulmu ki cire damuwar aure a ranki kin ji? You are too young da damuwar Da namiji. Wani hanin ga Allah baiwa ne. Kina so ki bini birni ki yi karatu?"
Da sauri Kusulmu ta girgiza kai, ta ce, Ina so in yi karatu, amma ba zan iya binki in bar Goggo na da Baffana su kadai ba.


4 Comments On KULSUM
avatar
zainab-salisu-kasim

1 year ago

Reply

I luv dis book

avatar
zainab-salisu-kasim

1 year ago

Reply

I luv dis book

avatar
amina-abdul

1 year ago

Reply

love it

avatar
aysha-abubakar

12 months ago

Reply

I like the book

Please Login or Register in order to submit comment