Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Idan Turaki ba ya nan, hotonsa da ke kafe a falonta ta ke zuwa ta tsaya ta kafa wa ido, komai na halittarsa na kayatar da zuciyar ta. Har ba ta so Batulu ta shigo, don tana katse mata tunanin Turaki, wani abu da ya fi komai yi mata dadi a halin yanzu, ya gusar mata da damuwar fitsarin kwance. Damuwar ta a yanzu na yadda za ta samu Turaki ya so ta ne ba na fitsarin kwance ba.
Batulu ta taba gaya mata Umma tace wai itama har da sakacin ta da Turaki ke yin nesa da ita. Ba ta yi masa abubuwan da mata take yiwa mazan su. Ita kuma Umma kunya irin ta surkunta bata bari ta zaunar da ita ta bayyana mata abubuwa a fili. Sai dai tayi ta yiwa Batulu korafin rashin wayon ta.
Zuciyarta na wani irin azabtuwa idan ta luluka a fagen imaginary life, imagination din ta bana komai bane face nata da Abubakar-Turaki da yayansu in sun haifa. 'Yan dugwi-dugwi dasu kyawawa. Tana so ta rayu da shi, matsayin uban 'ya'yanta rayuwa mai tsayi da albarka. She want to be by his side till eternity. Idan tana da kalubale a cikin gidan, to Turaki ne babban kalubalenta, da yadda zata samu ta karkato da hankalin sa gare ta. Amma bata da sani akan wannan fannin.
Turakin da kamar bai san Allah ya yi ruwan tsirar ta ba, wanda ya nuna bai san tana existing cikin gidan su ba. Maganar fitsarin kwancen ta da ya ji, ya sa ya kara nesan ta kansa da ita. Harkokin gabansa kawai yake na shirye-shiryen tafiyarsa UK. Ba ya Gaya ba ya Abuja. Sau tari ya kan manta da wanzuwar Kulsumu cikin gidansa, sai ya ga giftawar ta ko ya ji motsin rufe kofar ta. Ya riga ya gama tsara yadda rayuwarsa za ta kasance a gaba shi da zuciyar sa, ya tsara yadda zai tsallake Kulsumu ya gudu, ba zai yarda ya dawo ba sai iyayensa sun raba auren nan. Yayin da ita Kulsumu, a nata bangaren, duk wani kyakkyawan tunani nata ya ta'allaka ne kan hanyar da zata bi ta samu zuciyar Abubakar Turaki ya so ta, ta cigaba da rayuwa a karkashin igiyar auren sa har karshen rayuwar ta.

A kokarin Umma na son dasa shakuwa da sabo hadi da soyayya tsakanin Kulsumu da Turaki, sai ta daura mata nauyin karba masa abinci daga sassanta kullum sau uku a rana zuwa sassansu, 'sassan Turaki' kamar yadda ake kiran sassan nasu a gidan, tace da ita ta huta ba sai ta dinga girki ba sai zuwa gaba don abinci wadatacce ake yi a gidan kuma mai kyau. Duk da haka in tana son wani abun zata iya dafawa a kicin din ta.
Rannan Batulu cikin hira ta ce mata Umma ta ce ta zage wajen wanka da kwalliya sannan da tsaftar muhallin su. Ta kasance ma'abociyar kamshi kada ta bari ko yaya mijin ta ya shaqi abinda bai masa ba daga jikin ta. Kuma Kulsumu ta dage da hakan, tana daukar duk abinda Batulu ke gaya mata da muhimmanci, ta san Batulu 'yar uwa ce ba suruka ba, duk abinda take mata da zuciya daya take yi.
Ita ke zuwa sassan Umma ta dauko musu abincin su sau uku a rana, idan ya gama ci sai ta dauka ta tafi dakin ta ta ci sauran. Sannan ta fidda kwanukan Laraba ta wanke. Shi bai san ragowar sa take ci ba, ya dauka a can sassan Umma take ci ita da Batulu. Sabida bai taba ganin ta tana cin abinci ba. Wani irin pleasure take deriving daga cin left-over din Turaki. Umma tace ta dinga wanke masa bayi kullum da safe da yamma amma Turaki baya barin dakin sa a bude sam. Bata san cewa shi baya son kusancin nan da Umma ke son assasawa a tsakaninsu. Abincin ma don ya san ba ita take dafawa ba shiyasa yake ci.
Amma a can karkashin zuciyar sa tana darsa masa tausayin yarinyar, kyakkyawa da ita amma nakasassa ce, fitsarin kwance ta wani fannin za'a iya kiran sa da nakasa. Sannan an nakasa mata rayuwa da auren wuri (a ganin sa). Turaki yana da tausayi, ke dai barshi da ra'ayin rikau irin nasa.
A hankali ya samu kiyayyar da yake yiwa Kulsumu na decreasing gradually (raguwa a hankali). Sakamakon halayen ta da nutsuwarta da ya ankara da su. Sai dai bata kai matsayin da zai dauke ta a matar auren sa ba. Ba don kasancewar ta 'yar talakawa ba, ko don tana da makusa a suffa ko halayya, ko kuma don lalurar ta; sai don ta zo cikin rayuwar sa a lokacin da bai shirya ba, auren ta bai zo a sanda yake bukatar sa ba. Ya zame masa alaqaqai. Sabida a wannan gabar ta rayuwarsa bai shirya aure ba.
Ya yarda yayi auren ne kawai don ya samu albarkar iyayensa su bar shi ya cika burin sa na zama cikakken ophthalmologist. Yana ganin aurenta a matsayin unwanted marriage. He has no feelings akan diya mace yanzu. He's a goal oriented. Yana da muhimman abubuwa da dama a gaban sa da yake son cimmawa kafin ya gina family life.

Ana ya gobe Turaki zai tafi, maimartaba ya rusa duk wani planning da ya yi wa rayuwarsa da Kulsumu.
*** *** ***

Umma ta shiga turakar maimartaba ana i gobe Turaki zai tafi. Sun gaisa yadda suka saba idan ba ranar girkin ta bane. Zata fita yace "Rakiya zo in tambayeki Umma ta juyo ta dawo. Yace "tafiyar Turaki gobe ne ko?" Tace "eh, ranka ya dade" yace "ina fatan zuwa yanzu shi da matar sa sun daidaita?" Umma ta gyara zamanta tace "ni ranka ya dade ba shiga shirgin su nake ba, abubuwan gaba na ma sun ishe ni. Amma baya korafi itama bata korafi akan sa, saidai Laraba ta tsegun ta min wai har yanzu zaman 'yan marina suke yi, to me zan yi akai? Tunda itama yarinyar da laifin ta bata san komai ba? Duk wani abu na jan hankalin miji bata san shi ba? Ni kuma ba girma na bane in shiga lamarin su". Maimartaba ya girgiza kai yace " in ya dawo ki turo min shi".

Turaki ne gurfane gaban mahaifinsa a daren ranar, ya kira sunansa ya kara kira har sau uku.

Ya dade yana kallonsa babu ko kiftawa kafin ya kira sunansa na hakika, sunansa na yanka, sunan da baya kiransa dashi ko da da tuntuben harshe.
ABUBAKAR!.
Ba zai iya tuna lokaci na karshe da Maimartaba ya kira shi da sunansa na ainihi ba. Wannan ya nuna ko ma wace irin magana ce ta sa aka kirawo shi, magana ce mai matukar muhimmanci. Kansa a kasa ya amsa,
Naam ranka ya dade?
Maimartaba ya kafa masa ido, kafin ya fadi gundarin abinda yasa ya kirawo shi wanda bai taba zato daga bakin sa ba.
Ka taba sauke hakkin matarka na aure?
A firgice ya dago kai, Iyee? Naam? Allah ya kara maka tsawon rai? Kamar ya ya?
Kai tsaye sarkin Gaya ya ce, Ina nufin ka taba tarawa da ita kamar yadda Ubangiji ya yi maka umarni? Ya kuma dora alhakin hakan a wuyanka a matsayin ka na mijin auren ta?
Wata irin zufa ce ta keto wa Turaki, domin maganar maimartaba ta yi masa nauyi kwarai. Kansa a kasa ya yi shiru bai ce komai ba. Maimartaba ya nuna shi da dan yatsa,
Muddin kana so mu rabu lafiya ni da kai, sannan kana neman albarka ta cikin tafiyar da za ka yi; kana kuma neman ilmi mai amfani cikin tafiyar ka, a daren yau ka tabbatar da aurenka. Ta yadda idan ka mutu za ta yi maka takaba, idan ita ta mutu za ta mutu a cikakkiyar matar auren ka. Rai da rayuwa ba a hannun mu suke ba balle mu tsara wa kanmu rayuwa yadda muke so. Na gaya maka, na kara gaya maka; ka dabbaka sunnarka a yau a bisa umarnina da na Ubangijin ka.
Turaki ya yi mutuwar zaune. Gabadaya jikinsa ya saki. Maimartaba ya bijiro masa da wani alamari mai girma, wanda ya girmi zuciya da kwakwalwar sa. A rasa da wadda zai cire samartakar sa sai da mai FITSARIN KWANCE? Bai ankara ba ya ga maimartaba ya mike ya nufi kofa. Ya bude baki zai roke shi sassauci a cikin umarnin sa, amma harshen sa ya sarke ya kasa fidda kalma. Yana ji yana gani maimartaba ya fice. Da ya ba shi damar yin magana da ya gaya masa, shi fa ko kusa da yarinyar nan bai iya zuwa, yanada kyankyami, sannan sai da so a ke shaawa. Bata taba burge shi ba balle ya yi shaawarta. Yana da taste a kan mace, ba kowacce irin mace zai iya hada jikinsa mai alfarma da ita ba.
Bayan dawowarsa dakin sa, ya kasa ci gaba da hada kayansa, ya zauna a bakin gado ya rafka uban tagumi. Ban da uba-uba ne, kuma ikon sa ya isa iko, wa ya isa ya sa shi cikin matsaloli irin haka? Ji ya yi hawaye sun cika idonsa, na tausayawa kansa, amma ya yi kokarin maida su. In yayi kuka akan takaicin Kulsumu ta yi galaba kenan a kansa!

*** *** ***
Wajejen karfe goma na dare Kulsumu ta yi shirin barci. Wanka ta yi, ta shafa lotion din nan mai kamshi (cocoa butter), duk a cikin kayan lefenta suke. deospray, kawai ta fesa a armpits dinta na dove ta sa rigar barcinta, kafin ta bar gaban madubin ta ji an turo kofar dakinta babu ko sallama, ba karamin firgita ta yi ba, don ta san ba Batulu ba ce, ba mai zuwar mata daki a daidai wannan lokacin.
Ganin Turaki ne sai zuciyarta ta harba fiye da karon farko, wannan ne karo na farko da ya taba shigo mata daki, sanye yake da jallabiyya ruwan madara ta wani yadi mai santsi mara kauri. Kafin ta tattara kalmomin da za su bada maana sai gani ta yi ya kai hannu jikin makunnin lantarki ya latsa shi, fitilu koraye marasa haske suka maye gurbin masu haske.
Tana ganin sanda ya tako a hankali kamar mai counting steps din sa ya iso gabanta. Hannunshi ya kai gareta ya kama hannayen ta ya ja ta a hankali zuwa gadon barcin ta, ba tare da ya ce da ita komai ba. Ita kuma cikin tsoro ta bishi kamar rakumi da akala. Hannun sa ya kai ga zip din rigarta ta baya. Kama rigar ta yi ta rike tamau! Ta ki cikawa, da ta fahimci abinda yake kokarin yi, gabanta na tsananta faduwa irin yadda bai taba yi ba a kafatanin rayuwar ta.
Ya zuge mata zip din riga, for what reason? (A dalilin me)??. Ko dai Turaki ya sha kwaya ne???
Ta tambayi kanta.

Dont fight me, it will not be good to all of us (kada ki yi kokawa da ni, ba zai yi mana kyau ba mu duka).

Tana ji tana gani ya zare rigar barcin tsaf cikin wani yanayi da bazata iya fassarawa ba. Kamar wanda yake yin komai bisa umarni. Kamar wanda ake sarrafawa automatically. Bai zo gare ta don shaawa ba sai don cika umarnin mahaifin sa. Amma jin mace mai laushin fata da tattausan jiki tubus a hannunsa sai komai ya fara canza masacanzawa ta ban mamaki, silently ya dauke ta a hannunsa ya dire a tsakiyar gadonta
Ba romance, babu kissing haka babu burbushin soyayyah ko ta cikin cokali cikin al'amuran sa, sai kokarin kai wa gaci by all means. He is just trying all his possible best to satisfy himself, ba tare da laakari da cewa Kulsumun (virgin) ce ba kuma kankanuwar yarinya da bata san gundarin me auren ya kunsa ba kansa. Rashin tausayin da ya gwada mata ko mai haihuwa uku aka yi wa sai ta ji a jikinta, balle Kulsumun da ba ta san ma mene ne sex ba. Ba ta san ana yi ba, ba ta taba sanin mene ne shi ba. A haka ya tsallake ta tare da rufe ta da bargo ya fice abunsa.
Pillow ta dauka ta rufe kanta da shi, ta dinga gunjin kuka. Kuka ta ke kamar ranta zai fita. Ko dan yatsan kafarta ta kasa motsawa. A haka har aka yi kiran sallar asubahi. Duk wannan son da zuciyarta ke ma Turaki a yan kwanakin nan ya dinga narkewa yana zagwanyewa, yana komawa kiyayyah zallah. Ta tsane shi, ta tsane shi ta yadda ko fuskarsa ba ta son tunowa.
Har zuwa karfe shidda na safe Kulsumu ba ta iya ta tashi ba balle ta yi sallah. Ta rasa wane irin taimako za ta yi wa kanta. Zuwa wannan lokacin Turaki sun shilla sun kusa isa Kano shi da direban gidansu, inda daga nan za su bi jirgi zuwa Lagos, daga nan su tashi zuwa United Kingdom.

Karfe bakwai Umma ta ce yau dai bari dai ta dubo Kulsumu tunda Turaki ya tafi, zata so ganin wani a kusa da ita sabida kewar mijin nata, bata taba taka sassan nasu ba sabida kawaici da jan girma irin nata. Kulsumun ce kullum take shiga ta gaisheta. Yau din ma abinda yasa zata daure ta je din sabida tafiyar Turakin ne. Laraba bata nan ta aiketa Kiru wajen Hadiza tun jiya. Batulu na barci ta fita a hankali don kar ta tashe ta. Bata son kowa ya farga ta shiga sassan Turaki.
Ta yi sallama amma Kulsumu ba ta iya ta amsa ba. Tun daga falo ta ke jiyo shesshekar kukanta. Ta kara sauri ta murda kofar ta shiga. Hannu ta sa ta janye bargon, da sauri ta mayar ta rufe ta tana fadin,
Na shiga uku ni Rakiya, me zan gani haka? Abin da Turaki ya yi ke nan? Wato don an ce ya sauke hakkin aurensa shi ne ya saka miki karfi?
Kulsumu ba ta ce mata komai ba, sai kuka ta ke yi har da hadidiyar zuciya. A gaggauce Umma ta je ta dafa ruwan zafi a kettle, ta koma sashenta ta dauko robar jego ta dawo. Kama Kulsumu ta yi ta daga ta zaune. Wata irin wahalalliyar kara ta saki ta kankame Umma. Umma ta tabbatar Kulsumu ba za ta iya tafiya ba ita kuma ba za ta iya daukanta ba sai ta je ta rufe sassan da sakata ta dawo, ta fiddo ruwan zafin tsakar dakin. Tana kuka da kiran Goggonta haka Umma ta gasa ta, ta karo ruwan zafi ta danna mata jiki da tawul tun daga saman wuyanta har kafafunta exactly yadda ake yi wa masu sabon jego. Ta koma sashenta ta nemo paracetamol ta hado tea mai kauri ta ba ta ta sha. Ba jimawa wani wahalallen barci ya dauke ta. Tana yi tana sauke ajiyar zuciya. Umma ta yi ajiyar zuciya itama tana kwafa ita kadai, ta ce idonta idon Turaki.... Sai ya gwammace bai santa ba (ni kuna nace Turaki ya yi miki nisa Umma, lol, kafin ya dawo kin manta, shaanin uwa da Da sai Allah- Takori).
Ta koma sassanta ta ba wa Abu mai aikinta sallahun irin farfesun da za ta yi mata na kaza, wato ya ji kayan yaji na Hausa da kayan kamshin gargajiya ta kuma dama mata kunun kanwa. Kafin minti talatin Abu ta gama, ta kawo ma Umma cikin karamin flask, kunun kuma cikin tea flask. Sanda Umma ta koma sassan Turaki har zuwa lokacin Kulsumu ba ta tashi ba. Kyale ta ta yi ta yi barcinta, sai wajen azahar ta dawo. Ta samu ta tashi tana zaune gefen gado, ta yi laushi gabadaya, ta zuba tagumi.
Umma ta ce, Kulsumu kin tashi?
Muryarta ba ta ko fita sosai ta ce,
Na tashi Umma, barka da asuba.
Ta ce, Wace asubah kuma ana neman karfe biyu? Tashi ki shanye farfesun nan tun bai huce ba, ki shanye romon gaba daya, sannan ki kara da kunun kanwan nan.
Ba ta yi musu ba don yunwa ce ke sakadarta sosai. Sai da Umma ta tabbatar ta koshi sannan ta ce ta yi sallah ta kwanta ta huta zuwa laasar. Ta aiki Batulu gidan Yayarta Harira don kar ta zo ta dame ta. Dan murushi ta yi ba ta ce komai ba. Umma na bada baya ta kwanta ta bude faifan tunani.

Wato abin da ya faru tsakaninta da Turaki jiya shi ne makasudin auren kenan? Amma babu wanda ya taba zaunar da ita ya yi mata bayani sabida nauyinsa!. Idan shi ko wacce mace ke yi a gidan aurenta hakika ta jinjina wa mata, tunda babu komai cikin auren sai azaba da balai mai barazanar sheka mutum barzahu. Turaki ya cika babban mara imani in ta tuno irin rokon da ta dinga yi masa tare da hada shi da darajar iyayensa ya tausaya mata, amma ko sauraronta bai yi ba. Ita gara ma da ya tafi, idan da a ce zama zai yi ta tabbata watarana gawarta za a kai wa Goggonta. Ta kai bayan hannu ta shafe hawayen idanunta.
Kwana bakwai kenan tana sawa Laraba na kula da Kulsumu ta hanyar yi mata farfesu, kunun kanwa da sauran su, har Laraba ta gane abinda ya faru duk da Umma bata fili ta gaya mata ba, ta tabbatar ba ta samu tear ba daga bakin maaikaciyar jinyar da ta sa aka kirawo ta duba ta. Sannan ne hankalinta ya kwanta.

Sati daya da tafiyar Turaki aka yi mata jere na iyayenta a daya empty room din. Iyayenta sun yi matukar kokari, sun sayi furnitures masu kyau daidai karfinsu. Da ma dakin a malale yake da kilishi, kuma an saka labulaye irin na sauran dakunan. Sun aiko za su kawo gara Maimartaba ya ce, kada su soma, shi ba a yi masa wadannan bidioin.
Zaman Kulsumu a gidan surukanta abun gwanin ban shaawa, ta yi bul-bul da ita a watanni uku. Ranar farko da ta fara jinin haila ta shiga tashin hankali ba kadan ba. Sai da Laraba ta zaunar da ita ta wayar mata da kai, ta nuna mata abu ne da kowace mace ke yi idan ta kai munzalin girma. Kowa a gidan son Kulsumu yake sabida saukin kanta. Ga nutsuwa da hankali, hatta barorin gidan suna jin dadin zama da ita, ita babu ruwan ta kowa nata ne. Hatta abokan zaman Hajiya Rakiya wato sauran matan Sarki suna yabon Kulsumu. Ta kan shiga lokaci-lokaci ta gashe su. 'Ya'yan su duk manya ne a gidan aure basu cika zuwa ba sai wani sha'ani ya tashi.
Wajen kakarsu Batulu wato Fulani nan ne wajen hirar daren ta, tayi ta bata labarin kuruciyar Turaki tana cin dariya. Ta gaya mata da yana yaro tsoron Doki yake, Baban sa kuma ba abinda yake so irin ya dora shi gabansa bisa doki su tafi Kilisa. Yana ihu yana komai a haka suke tafiya kilisar sai kace dole. Tana son zuwa wajen ta don a bakin ta ne kadai zata ji zancen sa. Zuwan Goggo biyu, kuma ta yi farin cikin ganin yanayin da Kulsumu ke ciki, hankalinta ya kara kwanciya, ta tabbatar ko bayan ranta Hajiya Rakiya za ta kula mata da Kulsumu.
*** *** ***

An aiko rasuwar Baffan Hajiya Rakiya a can garinsu Gombe, don haka Maimartaba ya yi mata izinin tafiya taaziyyah, ita kuma ta ce da Kulsumu da Batulu za ta tafi. Murna a wajen Kulsumu da Batulu abin ba'a cewa komai. Kamar ba gaisuwar mutuwa zasu je ba. Musamman Kulsumu da kafar ta bata taba takawa ko'ina ba bayan 'Yalleman. Direban Maimartaba Malam Sule shi zai kai su har can. Tafiya ce za su yi ta kwana uku kacal. Umma ta yi musu shiri sosai na abinci da abin sha cikin coolers, yadda ba za su jigata a hanya ba. Duk da tafiya tsakanin Gombe da Gaya ba wata mai yawa bace can.
Ranar asabar tun asubah suka kama hanya. Zuwa azahar sun shiga Gombe.
A gidan su Hajiya Rakiya da ke Jeka da Fari tarba ta musamman aka shirya musu, babban gida ne mai sassa daban-daban, iyayenta duk sun rasu sai yayyenta da matansu, mahaifin ta na da sarautar Dallatun Gombe, sai kuma Baffan nasu mai rasuwa da matansa biyu. Ya tsufa tuguf kafin rasuwarsa. Matansa ma duk dattijai ne.
A dakin uwargidansa Ramatu suka sauka, jininta ya fi haduwa da Hajiya Rakiya. Kulsumu na kula da komai na Umma cike da kaffa-kaffa kai ka ce mahaifiyarta ce. Kayan sawar Umma, takalmanta, jakar hannun ta, duk suna hannun Kulsumu. Hatta kudin data zo dasu don ta yiwa yan uwanta hidima a hannun Kulsumusuke. Sai dai ta juya tace Kulsumu kirgo naira kaza.
Duk gidan dangin Haj. Rakiya ba inda Goggo Ramatu bata sa an kai Kulsumu an gabatar da ita a matsayin matar Turaki ba. Wannan abu dadi yake yi wa Kulsumu in ta ji ana nuna ta anata kiranta "matar Turaki". Duk da Turaki yayi mata laifin da ya kassara soyayyar sa wani lungu na zuciyar ta na son abun ta.
Laifi daban, soyayyah halittacciya daga Allah daban. Mu'amalar dake tsakani ta da Umma akwai sha'awa a ciki. Umma ba wani sake mata take ba sabida fulatanci amma tana kula da ita. Tana kokari ta ga cewa bata nemi komai ta rasa ba, kuma tana cikin walwala kamar Batulu, sabida a kasan ranta tausayin ta take ji sabida lalurar da Allah ya daura mata.
Bata san me zai faru ba....bata san yaya zata kaya ba...ranar duk da Turaki ya gano abinda ta lullube masa.

Washegarin ranar Umma ta yi sallama da yan uwanta cikin alhinin rabuwa da juna. Suka kamo hanyar Gaya bayan motarsu damkam da tsarabar Gombe. Koda suka dawo gida aka warewa Kulsumu tsarabobin ta zama tayi ta ware na Fulani da duk wanda take mu'amala dashi a gidan ta aiki Laraba ta kai musu. Har sassan ake shigowa yi mata sannu da zuwa da godiyar tsaraba, ranar Fulani da kanta ta tako cikin sassan su sabida jin dadin nono kindirmo da manshanu da tsintsiyar laushi da Kulsumu ta aika mata. Kulsumu ta hau hidima da Fulanin sarki da duk abinda take dashi na ci da sha a kitchen, ranar a nan sassan Kulsumu sukayi hirar daren su yadda

4 Comments On KULSUM
avatar
zainab-salisu-kasim

1 year ago

Reply

I luv dis book

avatar
zainab-salisu-kasim

1 year ago

Reply

I luv dis book

avatar
amina-abdul

1 year ago

Reply

love it

avatar
aysha-abubakar

12 months ago

Reply

I like the book

Please Login or Register in order to submit comment