Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba ta ko me za su ba ta. A haka ma ana yada masa magana a majalisa ina ga an kawo dukiya? Don haka Hajiya Rakiya ta sa yayanta mata suna hada lefen ne da niyyar in an kawo amaryar sai su ba ta.
Kulsumu na shigowa ta daddage ta fadi gaban Goggo ta fasa wani irin kuka. Goggo ta saki kayan hannunta ta kama ta, ta janyo ta jikinta ta rungume tana lallashinta.
Goggo ki taimake ni ki roki Baffa a bar auren nan, wallahi bana so, shi ma ba ya so.
Kuka ta ke sosai tun karfin ta da gunji da kakari wanda ya tada hankalin Goggo. Goggo ta rasa da kalaman da za ta lallashe ta, amma tana ji a ranta ko yankar naman Kulsumu Turaki zai dinga yi kullum ba za ta ce da Hajiya Rakiya a fasa ba. Wannan kaunar da ta nuna musu ta san Kulsumu ba za ta taba samun kamarta daga kowacce suruka ba. Gara ta je din su da kansu in sun ga auren ba mai yiwuwa ba ne sa dawo da ita da kansu, amma ba dai a samu canjin raayi daga gare su ba. Da wannan tunanin ta samu ta lallashi Kulsumu da dadadan kalamai na kwantar da hankali, da nuna mata ta maida komai nata ga Allah. Shi din mai iya canza komai ne.

Washegari kafin karfe takwas na safe mutanen Yalleman maza da mata sun iso tare da Malam Hadi, Bus biyu suka ciko, mata da maza. Cikin tawagar akwai Lami matar Malam Hadi da yayanta gabadaya, sai wata kanwar Baban Malam Hadi, Inna Talatu da kanwar kakarsa Asabe da yayansu. A maza kuma akwai Baffansa malam Samaila da wan mahaifinsa Malam Garba. Sun kule tare da Baffa a daki kafin a fito daurin aure, kowanne ya bada yar gudunmawarsa, Malam Hadi ya kullo kudi masu yawa da ya dade yana tarawa ya kawo wa Baffa, ya ce a saya wa Kulsumu kayan gado da su, abin ne ya zo musu babu isasshen lokaci don haka jere ma sai bayan sati daya za a je a yi mata. Ita Hajiya Rakiya ma ta ce, kada su wahalar da kansu, ba sa bukatar komai daga gare su sai Kulsumu, amma sun ce dole za su yi mata komai yadda ake wa yar kowa a garin Gaya.
Karfe tara Lami duk kiyayyar da ta ke yi wa Kulsumu ta dafa mata ruwa ta kai mata bandaki ta sa ta a gaba ta yi wanka, Goggo ta fiddo mata sababbin kayan da Babanta ya dinko mata, shadda ce fara kal ta sha aiki da zaren silba, an yi doguwar riga mai fadi da dankwali. Lami ta taimaka mata ta shirya ta feshe ta da turaruka cikin wadanda Batulu ta kawo ta takura mata ta shafa hoda, amma ta ki ta yarda ta shafa jambaki, sai ga Kulsumu ta fito fes ta yi fayau da ita, da ma an ce duk munin amarya ranar aurenta kyau ta ke yi, balle Kulsumu kyakkyawa.

Karfe goma daidai jamaar garin Gaya ciki da bai dinta suka shaida daurin auren ABUBAKAR (TURAKI) ABDULLAHI da UMMU-KULSUM ABDULHADI YALLEMAN a kan sadaki dubu hamsin cif, daga nan aka zarce liyafar cin abinci ta maza zallah a fadar Maimartaba Sarkin Gaya, masu kidan kalankuwa da goge kowa ya baje kolin nasa. A cikin gida Hajiya Rakiya da jamaarta sun zarce da wunin biki sai dafe-dafen abinci na alfarma ake ta yi ana fitarwa, baki daga koina cikin garin Gaya wadanda aka gayyata da wadanda ba a gayyata ba sai barkowa suke yi. A can gidan su amarya su ma wunin biki suke, su Lami sai dafa abinci suke kala-kala ana raba wa mutane.
Abokan ango sun yi sun yi da shi su yi hawan angonci kamar yadda aka saba a gidansu, amma ya kekashe kasa ya ki, ya ce ba zai yi ba. Ranar da zai yi aure mai suna aure zai yi hawan angwanci amma ba yanzu ba.
An yi kasaitaccen biki a gidan Sarkin Gaya na tsayin kwana biyu, amma tun jiya aka kawo amarya, an sha daga kafin a iya raba Kulsumu da Goggo, ita kuka Goggo kuka, an rasa mai rarrashin wani, yar nasihar nan Goggo ba ta iya ta yi wa Kulsumu ba, sai cewa ta yi za ta zo daga baya ta yi mata.
Baffa kuwa addua kawai ya yi wa Kulsumu ya ce ta je ta yi hakuri irin wanda kowace mace ta ke yi a gidan aurenta, Allah ya ba ta saa.
Da aka kai ta wajen Malam Hadi albarka ya yi ta sa mata. Ya ce, Kulsumu na sanki ke din yarinyar kirki ce, to ba za a yarda da hakan ba sai kin nuna shi a gidan aure. Ki yi wa mijinki da iyayensa biyayya kamar yadda ki ke yi wa naki. Ki kula da ibada ki kama sallah, sannan ki zamo mai tsafta a gidan aurenki. Tashi ku je, Allah ya yi miki albarka.
Tabbas ba karamin yaki aka yi ba kafin a fidda Kulsumu daga gidansu, Lami goyata ta yi a bayanta sannan aka samu aka saka ta a motar yan daukar amarya wadanda yayyen ango ne mata da yan uwan Hajiya Rakiya da suka zo daga garinsu.
Har uwardakin Umma suka kai ta bisa gadonta, ita ce ta ba su umarnin su kai ta sashe-sashe na matan gidan, sannan su dawo da ita. Hakan aka yi, kowacce cikin matan Sarkin Gaya ta yi wa amarya ihsani, wasu atamfa da kudi, wasu kayan kwalliya da turare aka kai ta bangaren Fulani wato mahaifiyar Sarkin Gaya, ta tsufa sosai amma da sauran karfinta. Ta rungume Kulsumu tana godiya ga Allah da ya tsawaita ranta ta ga auren Turaki, namiji daya jallin- jal a cikin tarin jikokinta wadanda sun kusa talatin. daga nan aka dawo da ita sassan Umma wato uwar mijinta.
Kulsumu ta makure can a karshen gado bayan yan uwanta sun tafi, sawu ya fara daukewa. Babu kowa a dakin sai Yaya Hadiza babbar yar Hajiya Rakiya da Batulu. Yau Umma ce da girki don haka tana can sassan maimartaba ta bar kulawar amarya a hannun Hadiza wadda ita a Kiru ta ke aure sai gobe za ta koma. Ta yi kuka har ta gode Allah ta yi shiru. Wata irin fargaba da wani irin tsoro ke rarake zuciyarta, idan ta yi fitsari a kan gadon surukarta fa? Hankalinta ya dugunzuma ya tashi, ta rasa inda za ta sanya ranta.
Batulu ta janyo manyan (food warmers) tana bubbudewa, ta ce, Kulsumu me zan zuba miki? Akwai jallof din cous-cous da hanta, akwai farfesun kayan ciki, akwai fried macaroni, akwai kuma gasassshen naman rago.
Kulsumu dai ta yi tsumuu! Ta rasa abin da ke mata dadi. Batulu ta sake maimaitawa, amma ba ta tanka mata ba. Yaya Hadiza ta ce, Ke ma dai Batulu da neman zance ki ke. Ina amarya ke wani zaben abin da za ta ci? Kawai in za ki zuba mata ki zuba mata, sai ki zuba mata komai kadan-kadan.
Batulu ta bi shawarar Yayarta, ta zuba kowanne kadan a kan faffadan faranti, sannan ta dauki dan tangaran mai zurfi ta zuba farfesun kayan ciki a ciki, ta sa mata cokali ta kai mata gabanta a kan faranti. Kulsumu ta girgiza mata kai alamar ba za ta ci ba, idanunta sun yi kozai-kozai don kuka. Yaya Hadiza ta ce,
Aah a'ah, kada mu yi haka da ke Ummukulsumu, dauki abinci ki ci kada ki kwana da yunwa, kada in ci amanar Umma kin ga dai ni ta damka wa amanarki.
Cikin siririyar murya ta ce, Wallahi na koshi ne.
Duk sonta da nama yau ko na Dawisu ne ta san ba zai iya wucewa a makogaronta ba, sabida fargabar da ke cin ranta. Haka kawai tana zaman-zamanta cikin kwanciyar hankali a gaban Goggonta, an zo an sa ta a tashin hankali, duk tarin alummar nan da ta gani a gidan nan mai dakuna ba iyaka gobe za su san tana fitsarin kwance. Abinda ba wanda ya sani yanzu kowa zai sani a sata a waka a garin Gaya. Wasu hawaye suka shimfido mata a guje, ta boye fuskarta cikin mayafi tana sharewa.
Yaya Hadiza ta ce, To shi ke nan na kyale ki, daina yi min kuka. Dauki farfesun shi kadai ki sha, ki sha ruwa sai ki kwanta.
Kulsumu ta dauki cokali ta sa a farfesu tana ta juyawa, amma ta kasa kai wa bakinta. Batulu ta hawo gadon ta karbi cokalin ta dauko hanta ta ce, Haa! Bude bakin in sa miki kin ji yar amaryar mu kyakkyawa?
Ta yi wani murmushi har kumatunta na hagu ya lotsa (dimple). Batulu ta sa yatsanta a ramin (dimple) din ta ce, Ko ke fa?! Ai kin yi kuka kin mora sai ki gode Allah haka nan. Yaya Turaki yana da kirki na tabbatar miki lafiya za ku zauna in dai kina kula da tsafta kina wanke masa toilet akai-akai. Kin ga kullum sai na wanke mishi toilet sau biyu in har yana gari, shara da mopping sau biyu nake mishi, fesawa daki Rambo duk magriba, yanzu duk ya koma kanki. Girki ki koyi irin wanda yake so a wajen Umma, wallahi lafiya lumui! Za ku yi zamanku, barin ma in kina cancada masa kwalliya kina fesa sassanyan turare akai-akai.
Yaya Hadiza ta kai mata duka ta kauce tana dariya, ta ce, To aku-kuturu sarkin surutu, fadi ba a tambaye ki ba, tashi ki ba wa mutane wuri.
Batulu ta shagwaggwabe fuska, Kai Ya Hadiza ina ruwanki da mu? Ba tare ki ka ganmu ba kuma tare za ki bar mu gobe-goben nan?
Umma ta shigo dakin ta yi kyau cikin kasaitacciyar kwalliya tana cewa,
Batulu in ce ko ta ci abinci?
Wallahi na yi-nayi ta ki ci Umma.
Ta ce, To hado mata shayi.
Batulu ta amsa tare da mikewa daga gadon. Kulsumu ta kara jan mayafi ta rufe fuska ganin Umma, yau wata mashahuriyar kunyarta ce ta lullube ta. Umma ta ce, Kulsumu daure ki sha shayi sai ki kwanta ki huta.
Da za ta iya daurewa ta yi magana, cewa za ta yi a ba ta ruwan lipton kawai, kada a sa madara don ta samu ya hana ta barci, amma ina! Ba za ta iya ba. Cikin ikon Allah da Batulu ta kawo kayan shayin ba ta hada mata ba, ruwan zafi kwai ta zubo a kofi ta ajiye mata kwalin lipton da sugar da milo da madara a kan tray.
Ta ce, In hada miki?
Kulsumu ta girgiza kai tare da dan janye mayafinta ganin Umma da Yaya Hadiza sun fita. Ta dauki lipton daya ta sa a cup din, ta sa sugar mai kwaya (cube) guda biyu ta shiga motsawa. Batulu sarkin magana ta ce,
Ba za ki sa madara ba?
Daga mata kai ta yi tare da kai kofin shayin bakinta tana kurba a hankali. Rabonta da abinci tun safiyar ranar da Goggo ta matsa mata ta ci waina da miyar taushe kadan da dan kunun tsamiya. Hanjin cikinta har rawa yake sabida yunwa. Tsaf ta shanye shayin ta ce da batulu da ke gyara mata kayanta da aka zo mata dasu na sanyawa tana so ta yi alwala. Batulu ta ce.
"In kin fito sai ki canza kaya ga kayan barci Umma ta ce a ba ki.
Tare suk shiga bayan gidan ta nuna mata komai. Toilet din ba irin na gidansu ba ne, wannan din na zamani ne mai tayal. Don haka da taka tsan-tsan ta yi komai gudun kada santsi ya debeta ta fito daure da alwalarta.
Nan ta tarar Batulu ta ajiye mata wasu sababbin kaya marasa nauyi a gefen gado, ita ma ta sauya kayan jikinta ta kwanta a daya barin gadon yadda ba za ta takura mata ba. Dardumar da ta gani a kan kujera ta dauka ta shimfida ta tada sallah.
Sallar ishai da ba ta yi ba da shafai da wutri ta fara yi, sannan ta fara nafila, sallah kawai ta ke yi ba tare da ta tsaya ta huta ba. fatanta garin Allah ya waye ba tare da ta yi ko gyangyadi ba, balle a kai ga abinda ba zai yi wa kowa dadi ba. Sau uku Batulu tana farkawa cikin dare amma sai ta samu Kulsumu cikin sujjadah, don haka ta kashe fitila mai haske ta bar musu shudiya ta juya ta yi kwanciyarta.
Haka Kulsumu ta kai asubahi dungurgur a kan sallaya. An ce tashin hankali yana hana barci, to hakan ne ya faru da Kulsumu, duk iya samame irin na barci a yau Kulsumu ta yi yaki da shi don tsira da mutuncinta da rufuwar asirin ta a gidan surukanta. Karshen tozarci ke nan fitsari a gadon uwar miji. Gara ma in da a ce dakinta ne ta san yadda za ta yi ta gyara ba tare da kowa ya ji ya gani ba.
A kan kunnenta aka kira sallar asubahi, ta koma toilet ta sake sabunta alwala, ta fito ta tashi Batulu, sannan ta sake kabbara rakaatainil fajri. Daga nan inda ta ke zaune ta ji masallacin gidan sun tada sallah, don haka ta bi su jami.
Karfe shida na safe wani mugun barci ya dinga sakadarta, sai gyangyadi ta ke a kan darduma. Batulu wadda idonta ke cike da barci ta ce, Kulsumu ki kwanta haka, in ba so ki ke ciwon kai ya kama ki ba.
Ta juya ta ci gaba da barcinta.
Haka ta yi ta gyangyadi a zaune tana farkawa. Wajejen takwas Yaya Hadiza ta shigo ta same ta, ta ce, Ai da kin koma kin kara runtsawa Kulsumu, don ki warware gajiyar da ke jikinki sosai.
Kulsumu wadda idanunta suka yi jazir sabida barci da gajiya, ba ta ko iya bude su sosai, ta ce, Aa wanka zan yi.
Yaya Hadiza ta ce, To bari in sa a hada miki ruwan wankan, tashi ki koma daga bakin gado.
Haka ta tashi tana rangaji ta koma bakin gadon ta dan kishingida amma fa kafafunta na kasa. Barci na surarta tana gyagije shi. Yaya Hadiza ta dawo tare da Abu mai aikin Umma tana dauke da bokiti da ruwan zafi a ciki ta kai bandakin ta surka mata ta fita. Yaya hadiza ta ce, ta shiga ta yi wankan. Tana mikewa juwa ta kwashe ta, Hadiza ta taro ta, ta ce,
Anya Kulsumu daren jiya kin yi barci, yadda ya kamata?
Ta yi dan murmushi ta wuce bandakin. Yaya Hadiza ta daka wa Batulu duka a cinyoyinta, ta zabura ta mike, ta ce,
Sannu kasa sarkin barcin tsiya, ki tashi haka ki yi wanka.
Batulu ta zumburo baki, Haba haba Ya Hadiza kin san na gaji fa, jiya na sha wahala sai ka ce biki na.
Murmushi Hadiza ta yi ta ce, Ba sai kin tuna mana ba, muna sane da ke.
Batulu ta zaro ido ta ce, Ba fa haka nake nufi ba, kai Yaya Hadiza. Ta bar dakin tana murmushi.
Kulsumu ta yi wanka da sabon soso da sabulun da ta tarar har sabon brush an ajiye mata. Kayan jikinta ta mayar sannan ta fito. Nan ta samu Batulu ta ajiye mata wata tattausar atamfa mai kyau koriya mai turuwa, ita ba sanin sunayen atamfofi ta yi ba, amma dai ta san wannan mai kyau da tsada ce. Sai wani irin kamshi ta ke yi (English), an yi dinki riga da zani da kallabi daidai jikinta. Ga dukkan alamu da Batulu aka gwada don girmansu daya.
Ta saka atamfar sannan ta yi daurin kallabi ta yafa mayafi mahadin kayan. A lokacin Batulu ta shigo, ta ce, Wannan daurin bai yi kyau ba, zauna in daura miki.
Haka ta zauna Batulu ta hau daura mata dankwali, ta fidda kayan kwalliyarta ta hau fente mata fuska, har jambaki sai da ta shafa mata wanda yammata ke yayi a wancan lokacin. Ba su kai ga gama kwalliyar ba suka ji muryarsa mai zurfi da kauri (husky) tana magana da Yaya Hadiza a falo, kuma kafin dukkansu su ankara suka jiyo takunsa gab-gab-gab yana shigowa dakin. Ya sha farar shadda mai maiko da taushi wadda taji dinkin zare na zamani. Kamshin sassanyan masculine turarensa har cikin zuciyar Kulsumu, ba ta taba jin kamshi mai dadi da shiga rai irin wanda ta ke ji a tare da shi ba a iya haduwa biyu kacal da ta taba yi da shi a rayuwarta. Yana shigowa kallo daya ya yi musu ya kauda kai, ya ce da Batulu,
Ke, ina Umma?
Batulu ta hau gaishe shi bai amsa ta ba, ya ce, Na ce ina Umma wai? Kamar a fusace yake maganar don haka Batulu ta shiga nutsuwarta, ta ce,
Umma ita ce mai girki, ba ta fito ba tukunna.
Tsaki ya yi ya juya ya bar dakin.
Batulu ta ce,
Masifaffe kawai, aniyarka ta bi ka.
Kulsumu dai kanta na kasa, zuciyarta na fat-fat-fat. Kallo daya ta yi masa ba ta kara marmarin maimaitawa ba. Kuma a kallo dayan ta gane shi. Shine mutumin nan dan Umma da ya manne mata a zuciya wata da watanni ya kasa fita daga ganin farko data yi masa. Prince TURAKI, maabocin kwarjini, ilhama da cikar zati, ga wata irin kasaita da yake da ita irin ta yayan sarauta. Hatta magana a kasaice yake yin ta, kamar ba ya so. Kamar an tilasta masa yin ta. Tsayinsa na sa wa sai ka daga ido za ka hango karshen saman kansa. Idanuwansa su ne sirrin kwarjininsa. Wata irin fargaba da tsoro suka taru suka lullube zuciyarta da ta tuna cewa; shi din fa a yanzu shi ne mahadin rayuwarta, sannan abokin rayuwa na har abada a gare ta.
Ta san ba ya maraba da ita, da shigowa rayuwarsa da ta yi, a lokacin da bai shirya ba, idanuwan sa sun fada... bakin sa ya fada. Farin cikinta guda daya ne; soyayya da kaunar da ta lura mahaifiyarsa da yan uwansa na ciki daya na yi mata. Ita ma bata maraba da shi, ko cikakken kallo ba ta fatan ta sake yi masa, bayan wanda ta yi masa tun ganinta da shi na farko, ta riga ta haddace kamannin sa. Tabbas ta ji a jikinta, shi din, wata alaqa zata zo ta sake hada su. Alaqar da bata san wacce iri bace. Amma ta san haduwar su bata kare ba tun a lokacin. Wannan wata baiwa ce da Allah yayi mata.......anticipating of destiny. Faduwar gaban da ta samu a ganin ta da shi na farko ba ta taba yin irinta a rayuwarta ba. Ta dai ji zuciyarta ta sauya bugu at a speedy level irin yadda ba ta taba ji ba.
A rayuwar ta, ba ta taba haduwa da mutum ta ji abubuwan da ta ji irin wanda ya faru a haduwarta da shi ba. Ko da suka koma gida a ranar ita da Goggo, ta dade kamannin fuskarsa ba su bace daga zuciyarta ba. Yau da ya zo gabanta ya tsaya a matsayin sa na mijin ta, duk da bai kula ta ba, samun kanta ta yi da dimaucewa, jikinta ya hau bari kamar haduwar su ta farko. Hatta Batulu ta lura da hakan.
A ranta dai tausayin Kulsumu ta ke, ta sani sarai Turaki ba ya sonta, dole aka yi masa, za ta sanya Kulsumu a cikin adduointa na kowacce sallar farillah Allah ya dora ta a kan Yayanta Turaki, kuma za ta kyautata aminci a tsakaninsu yadda ba za ta barta da damuwa ba har Allah ya karkato da zuciyarsa a kanta.
Ta san dai bai isa ya sake ta ba, gidansu ba'a saki, don haka ya karaci bakin ransa shi kadai Kulsumu ta riga ta zama mahadin rayuwarsa in Allah ya yarda. Ya auro mata uku ma a rana daya ba zai dame su ba, in dai zai zauna da Ummu-kulsumu.
Wajen karfe tara Umma ta shigo dakin har ta yi wanka ta sake kwalliya. A bayanta Abu ce mai aikinta dauke da katon faranti wanda ta jero abincin karin kumallon Kulsumu. Umma da kanta ta zauna ta sa ta a gaba sai da ta ci kwai da dankali da ruwan tea, sannan ta ce ta zama cikin shiri, yanzu za a tafi da ita ta gaida Maimartaba. Bayan Umma ta koma turakar mijinta ta ce Yaya Hadiza ta zo da Kulsumu falon Maimartaba. Haka Hadiza ta kama hannunta ta sha lullubi har tsakar ka, suka tafi turakar Sarkin Gaya.

Yana zaune a wata irin kujera irin ta sarauta, ya tsufa amma ba sosai ba sabida yana samun kulawa sosai daga matansa da likitoci. Umma na gefensa tana masa firfita da wani irin mafici na gashin Dawisu. Daga daya gefen nasa Turaki ne ya tankwashe kafafunsa kansa yana kasa. Hadiza ta yi gaisuwa sannan ta zaunar da Kulsumu kusa da Turaki, ta koma kusa da Umma ta zauna.
Kulsumu ta rasa me za ta ce da surukin nata, sai ta gurfana kadan ta ce, Ina kwana?
Hadiza ta gyara mata, Barka da asuba ake cewa.
Kulsumu ta fadi yadda Yaya Hadiza ta ce, Maimartaba Sarkin Gaya ya amsa mata cikin muryarsa mai dadin sauraro, ya ce,
Barka da zuwa cikinmu Ummukulsumu, da fatan kin wayi gari lafiya?
Ya dubi Turaki ya ce, Ka rike matarka hannu bibbiyu Abubakar, ita din amana ce a hannunka, Allah ya yi muku albarka, Ya ba ku zuria dayyiba. Ummukulsum, ki bi mijinki sau da kafa. Duk abin da yake so ki yi masa, wanda ba ya so kada ki kusance shi. Ki zauna da shi da zuciya daya mu kuma insha Allahu za mu kula da ke yadda ya kamata. Duk abin da ki ke so ki fada wa Ummanku, in kina jin nauyi ki gaya wa Batulu ta gaya mata. Daga nan dakina Hadiza za ta raka ki gidan mijinki, Allah ya yi muku albarka.
Kulsumu hawaye ta ke yi, amma cikin zuciyarta ta ce amin sannan cikin zuciyar tata ta san ita kam ta yi dacen surukai. Mijin ne dai ba ta san wace irin tarba zai yi mata da kutsowarta cikin rayuwarsa ba, a lokacin da ba ya bukata, ko a ce bai shirya ba.
Ba za ta ce ga ta ina aka kukkurda cikin gidan aka shigo sassan da aka kira mallakinta ba sassan Turaki. Haka kowa ke kiran bangaren nasu. Yana daga kusa da bangaren amaryar Maimartaba Hajiya Saratu, kuma babu nisa da sassan kakar su Batulu, wato Fulani. Gida ne guda mai manyan dakunan barci, wadanda aka gina su cikin fankacecen falo, gini irin na sarauta. Kujeru ne na alfarma a falon sai kilishi da tum-tum guda shida. Kana shigowa hoton Maimartaba ne da

4 Comments On KULSUM
avatar
zainab-salisu-kasim

1 year ago

Reply

I luv dis book

avatar
zainab-salisu-kasim

1 year ago

Reply

I luv dis book

avatar
amina-abdul

1 year ago

Reply

love it

avatar
aysha-abubakar

12 months ago

Reply

I like the book

Please Login or Register in order to submit comment