Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dinsa suka lotsa dukan su,yanada kewayayar face,ga dogon hanci,yanada idanu,shanyayu,wanda idan yana magana kamar mai jin barci,bakin sa ma karami ne kewayaye mai kyau,daga ganin sa kaga kakarfan namiji."

Murmushi ya kuma yi yace"kinyi mamaki ko hussy."

" A to dole ai nayi mamaki,domin kuwa ba kowa ke gane mu ba,anma kai da ko ganina ma bakayi ba kasan ko wacece,wanda ko murayar ba kowa ke ganewa ba"

"Karki damu son da nake ma yar uwarki ne yasa nasan komai nata,da kowa nata.

Bismillah kazo,muje tana zuwa tace na shigo da kai."

Ok yace,shi ya shiga gaba,dan bazai soba yaga komai na jikin ta ba,saboda Allah bai halasta masa ba,yayi koyi da Annabin mu.

Can ya dan tsaya yace"anma daddy yana nan kuwa?zan so na fara ganin sa kafin yar uwar ki."

"Eh inajin yana nan,muje na kaika gun sa,har b'angaren su hajiya sukaje,suna zaune ko Hajiya da Daddy,harda idrissa,Husseina ce ta shigo falon,tayi salama,suka amsa ,Hajiya tace"a'a dota na kece."
"Eh Hajiya dama bakon ne na wajen A'indo yace yana son ya fara ganin ku keda daddy kafin ya karasa gurin ta."

"Ayya to shigo dashi."
Cewar daddy.

Dan dama Hajiya ta masa zancan .
Da salama ya shigo ,Masha Allah Hajiya tace a ranta,ganin farko dukan su sukaji yaron ya shiga ransu,gashi daga gani dan gidan manya ne,ga kwarjini,da kamala,,gami daya ya shiga ransu,gaida su yayi suka amsa,sanan yace"Daddy ni sunana Bashir d'a a gun tsohon Minister Al'mansoor kadafi,Allah yayi ma iyaye na rasuwa,ta hatsarin jirgin sama,yau shekara goma kenan, Mahaifiya ta Indira,yar K'asar Mumbai ce,a can indiya, ba'indiya ce,mahaifi na kuma bafulace ne,sun mutu sun barni ni kadai ba uwa ba uba ,na tashi ne a hannun kawuna kanen mahaifi na,dan dukiyar mahaifana ma shi ya kulla da ita,har lokacin da na malaki hankalin kaina, na fara son Aisha wato A'indo ne tun lokacin da tazo wanan gida da sunan aikatau,ban zo nan ba saida na nemi amincewar ta,nasan komai nata,harda auren ta na farko,nace a kawo ni wurin ku ne,kamar yanda Addinin musulmci ya nuna mana da mu fara neman izini ga mahaifi kafin muje ga Yar."
Shine nazo gurin ka daddy dan neman izinin fara zance gun Yar ka."


" Masha Allah yaro naji bayanin ka,kuma Ina maka ta'aziyar mahaifan ka,kwarai nasan Minister,domin kuwa kowa yasan mutunci Kamala,da amana irin nasa,tabas idan kayi halin sa ka dace,dan mutumin kwarai ne,na yaba da halin ka da kuma tarbiyar ka,ni Alhaji Sanmani nace kaje ka nemi soyayar ya ta A'indo matsawar tana son ka to na baka izinin ka turo manyan ka,da zaran kun daidaita."
Godiya Bashir yayi,sanan ya tashi yabar falon cik'e da farin ciki.
Idrissa ransa a bace yace"haba daddy kuda ya kamata ku gyara auren ta da Yaya,anma kuka ba wani izini,."

Murmushi Hajiya tayi tace"hum idrissa baka san abinda dan uwanka yayi ba,da kaida kanka bazaka goyi bayan a maida auren su ba,anma yau dai bara na fada ma abinda dan uwanka yayi, gaba-daya Hajiya ta fada masa,shi kansa idrissa saida yaji wata irin kumyar A'indo ta shige sa ,duk da ba gaban ta yake ba.

.


Har Falon baki Husseina takai sa,ta cika gaban sa da kayan ciye-ciye.
"Kinga malama ni ba wanan nake so ba plz kije ki kira min matata,ita nake bukatar gani,kina wani ja min aji."

Ya fada cik'in tsokana,dariya Husseina tayi" tace to masu mata naji."
shima ya fada cik'in raha tare dayin murmushi dimple dinsa suka lotsa."

Tafiya Husseina tayi tana dariya tace"idan naga dama sai na hana ganin ta."
"Oh yi hakuri kanwata,idan Kika hanani ganin masoyiya ta Allah zaku iya rasani. .
"Ah bama za'aje nan ba bara na turo maka ita."

"Yauwa koke fa "☺

Da gudu ta karasa gun A'indo ta rukunkune ta ,tana dariya tace "wallahi yar uwata na tayaki murna,wallahi kinyo baban kamu,ke kin gansa kuwa,wallahi kamar ba'indiye,koda yake ya hada jini dasu,kinsan Allah yafi Alhassan kyau mugun kyau ma,kai wallahi Anty A'indo kinyi baban kamu."

" Iyee to santin ya isa haka,harda kirana da Anty yau ,hum lalai bara naje naga Wanda kike zuzutawa hakan."

" Za ko ki gani ."cewar Husseina.

Fita A'indo tayi har falon ta shigo tayi salama cik'in zazakar muryar ta ."

Yanzu ma tsaye yake,hannuwan sa cik'in aljihun sa,ya juya mata baya,bayan sa kawai ta gani.

Kamshin ta ya bugo hancinsa,yace"ayimin afuwa my wife,idan da hali ki taimaka ki canza kaya,sanan karki sa turare,hakan bai halasta ba,ki bari har muyi aure , please kimin wanan Alfarmar,yana magana ne har yanzu bataga face dinsa ba,bayan sa kawai take gani."


Sakaka tayi da baki.ta tsaya,tare da zumburo baki,shi kuma da salon da yazo dashi kenan,meye haka kuma."


Kamar yasan abinda ta take sakawa a ranta, yace "muyi kokari muyi aiki da Addinin mu,haramun ne ko budurwa tasa turaren da zai tada hankalin wani da namiji,kuma ba muharamin ta ba,ni zan iya sawa,anma dan Allah ki taimaka kiyi abinda nace.

Juyawa A'INDO tayi tabar falon,ranta yadan baci,ta shigo d'akin su,ta fida hijabi tayi kwancin ta,husseina tace"a'a ya na ganki haka kuma."
"Mtsss dan Allah bar dan rainin hankalin nan,yanzu ina wani turaren da nasa da zai tadi hankalin namiji, je kice masa idan ya gama tsayuwar ya iya tafiya ni bazan fita ba.mtsss






Aci gaba da gashi🍇
Maimou love😘
[19/10 à 22:26] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨




*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋




*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚




*DAGA AKALAMIN MARUBUCIYAR*

👇
*YA MACE KOWACE DA IRIN NI'IMAR TA*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*,
_and Now_👇
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*





_DEDICATED TO SADJIDA & UMMY ONTOP_




*Page -47-48*



Murmushi husseina tayi ita sai taga ma yanzu A'indo har tafi ta tsiwa,zama tayi kusa da A'INDO ta dafa ta,tace"haba sis meye haka,a gani na ai gaskiya ya fada,meye a ciki,kiyi kawai abinda ya umarce ki ,idan ba haka ba kuma zan iya cewa har yanzu kina son ya Al'Hassan."

Jin haka yasa A'indo zurmut ta tashi,ta cire hijabi kawai ta sa wani,tana zumbure zumbren baki tabar d'akin,Husseina na mata dariya,domin yanzu ta gano lagwonta.


Komawa tayi da salama ta shiga,sai a lokacin ya juyo shima ya amsa salamar tata, cik'in murmushi,kallon sa tayi,ita kanta saida taji wani iri,yanda taji gabanta ya fadi,haka kawai taji gaban ta ya fadi ta kuma rasa meye silar faduwar gaban,domin kuwa kyan nasa har tsoro ya bata,"zauna ko"
Yace da ita cik'e da murmushi,zama tayi itakam sai ya zamana tamkar itace bakuwar bashi ba, gaba-daya ta rasa sukunin ta,haka kawai take jin kamar da akoi wani abu a tatare dashi.

"Yauwa my princess da fatan dai kina lfy ko?
Kuma na same ku lfy,Masha Allah yau dai ga bashir din ki ya bayyana."

Murmushin yake tayi, sanan tace"naga bashir,ashe k'yakyawa ne shi yasa ka boye min kanka."

Murmushi yayi sanan yace"yauwa Aïsha nifa ba wasa ya kawoni ba,kamar yanda kika sani kika sani na kuma fadama mahaifan ki to yanzu ma zan baki cikak'en tarihi na,nan ya fada mata kamar yanda ya fada ma su Hajiya da Alhaji.

Murmushi tayi,sanan tace"Masha Allah
Allah zaba mana abinda yafi Alherie."

Ameen yace,sanan yaci gaba da janta da zance tun bata biye masa sosai har ta saki jiki suka sha fira,anan ne taji ya kuma shiga ranta,anma ta rasa me yasa sam ya kasa kwanta mata sosai,anma kuma tasan cewar tabar ta aure sa tayi dace,dan haka indai su hajiya sun amince dashi zata yarda ta aure sa.

Sunyi awa biyu suna tadi,sanan yayi salama ya tafi tare da aje mata tsaraba ,kin amsa taso Yi saida ya nuna mata bacin ransa tukon ta amshi kayan...

Direct yana tafiya tayi b'angaren su hajiya da kayan,wanan karon hajiya kadai ke falo .

A'indo ta shigo da salama Hajiya ta amsa Mata tana murmushi,A'indo tazo ta zauna kusa da Hajiya tare da dan rungume ta tace"Hajiya na kina hutawa."

"☺ina hutawa ya ta,yaya har kun gama tadin,Kai a gaskiya yaron ya kwanta min Allah yasa siriki na ne."


Sunne kai A'indo tayi cik'e da jin kumya sanan taba hajiya leda ,tace"gashi wai tsaraba ce."


Amsa Hajiya tayi tana murmushi,su turaruka ne manya masu kamshi,da mayuka masu tsada.
Hajiya ta yaba,nan A'indo ta diba musu ita da Alhaji duk da na Mata ne,Hajiya taji dadi sosai.

Sanan tayi salama ta tashi ta koma b'angaren su,Husseina ma tayi murna,sanan ta kara bata shawara akan ta amince ma Bashir kawai,itama kuma tayi na'am da shawarar.

*Bayan sati daya*


A yau ne Alhassan ya shigo jirgi Dan zuwa K'asar sa ta haihuwa,a inda yake tafe da bacin rai,Zuciyar sa na masa wasi-wasi akan matar sa Mina ,hakan ko ta faru ne dalilin fadan da sukayi jiya,na cewar tun kusan sati biyu saura zasu bar kasar yace da Mina ta shirya,sanan akoi auren kannin sa,bata basa amsa ba,saida a gobe zasu tafi yace da ita su shirya su tafi,tace ita ba inda zata yai tafiyar sa,me zatayi a wani Niger,ita ba inda zata a takura mata,ransa yayi bala'in bacewa,sanan yace matsawar bataje wanan auren ba to wallahi zai iya rabuwa da ita,yana gama fadar haka ya gama shirin sa,washe gari k'arfe takwas na safe yayi Shirin sa shi kadai aka kaisa yajirgi ya daga dasu zuwa Niger.



a wanan lokacin kuma soyaya A'indo da Bashir ta bunkasa a zukatan su ,dan a yanda suke son juna abin baya faduwa,wata irin shakuwa ce sukayi,suna ji da juna ,koda yaushe suna like da waya suna fira,idan A'indo zata fita shi ke zuwa ya kaita a cewar sa baya son ana kalle masa mata,in yayi hakan sai yaba A'indo dariya ,tare da cewar "har na ma zama Matar taka kenan."

Sai yace sosai ma.

Ba abinda ke kashe A'indo kamar dimple dinsa.

Shirye shiryen biki ake ba k'ak'autawa,Hajiya ta d'auko mai gyaran jiki ana ma Husseina,itama A'indo ana mata, jikin su yayi luwai luwai yayi kyau ,duk sun raba ma yan Makarantar su katin gayata,dan harda dynner za'ayi, za'ayi shagalilika sosai,dan sai anyi fulani day,indiya day,dadai sauran su,abin ba'a cewa komai,domin A'indo da
Kawayen su na school suke shirye-shirye ba kama hannun yaro,kusan kulum yanzu sai kawayen su sunzo gidan an cika gida ,ayita wasa da raha.

Husseina da A'indo har wani fresh suke abin gwanin sha'awa,sun ciciko sunyi wani irin kyau.

K'arfe hudu jirgin su Alhassan ya sauka ,bai huce gida ba saida ya biya company dinsu,yayi wasu abubuwa,bayan sallah magariba,gards dinsa suka rako sa zuwa gida,shiga sukayi,direct wajen su hajiya ya huce,tarbon sa akayi sosai cik'e da murna,kowa yayi murnar ganin sa,anan akaci abinci,su A'indo dama tunda kawayen su suka fara zuwa wasu hardaga wani gari,sai suka koma cin abinci a b'angaren su.

Dan haka suna b'angaren su tare da kawayen su na school da suka fara zuwa Mimi ,Salma ,da Safna,kawayen su ne yan Niamey,sun shaku matuka hakan yasa suma sukazo bikin,anko ko kusan kala biyar kawayen amarya sukayi,itama A'indo kusan kayan su iri daya dana husseina Saidai banbancin kalla.

Bayan anyi fira sosai wajen k'arfe goma su hajiya suka shiga barci itada Alhaji,yayyin da husseina suke b'angaren falon baki suke tadin su,Alhassan ne zaune a falon baki sanye yake da t-shirt ,da wondo na sojawa iya gwiwa,sunyi bala'in yi masa kyau,fatar sa da ka ganta kasan cik'in hutu yake ,yayi fresh yayi bala'in kyau ,kafa daya kan daya,yana danna computer ,yana shan juis sanye yake da farin gilashi.aiki kawai yake a cumputer.
Salma ce ta kalli A'indo tace "sis dan Allah ki d'auko min waya ta,inajin wallahi mun barta a b'angaren su hajiya dazu,kinsan da mukazo aiki anan nasa caji kuma kinga yanzu inason Kiran Mom."

Murmushi A'indo tayi,sanye take da riga da wondo na kayan barci masu sulbi sunyi bala'in yi mata kyau,sanin cewar a yanzu Hajiya da Alhaji basa falo suna d'aki ita da Alhaji shi yasa kawai ta fita da kayan barcin dake jikin ta da kuma hulla,ta gashi kasancewar lokacin sanyi ne,kayan sunada dan kauri,tasa takalma masu gashi , daga sama, gaba-daya sai tayi bala'in kyau.

Kai kamar wata ba'indiya fitowa tayi ta iso falon su hajiya da siririya salamar ta,ko kadan hankalin ta bai kai a gunsa ba,ganin tayi tunda ta shigo bara ta huce ta aza tea Tasha,shikam tun kafin shigowar ta ya jiyo wani bala'in kamshi mai sanyaya zuciya da ruhi,wanan dalilin yasa ya aje aikin da yake ya zuba ma k'ofa idanu,har ta shigo wani irin dum gabansa ya bada,ganin wanan k'yakyawar halitar a cewar sa,har ta nufi kichen tana shirin shiga Hajiya ta sauko da yake taga A'indo ,tace"a'a A'indo lafiya dai na ganki."

Da murmushi A'indo ta juyo wanda ya kara ma face dinta kyau,tace "là Hajiya kin fito,wallahi Salma ce ta manta wayar ta a caji dazu,kuma abubuwa suka d'auke mana hankali,shine tace nazo na d'auko mata,shine nima nake son hada tea nasha."
"Ayya to yi ki hada,kije kice ma idrissa yabar Husseina yaje b'angaren su,dan in ba haka nayi bazasu iya rabuwa ba har asuba."

" To hajiya ." A'INDO tace tare da shiga kitchen



Sai a yanzu Hajiya ta lura da Alhassan zaune,Wanda ya saki baki cik'e da shagala Yana kallon A'indo wanda Jin an ambaci A'indo gaban sa yaji Yana faduwa,dan kuwa gami daya yaji yarinyar nan ta shiga ransa."

Murmushi Hajiya tayi tace"Ashe kana nan."

"Eh Mom,wacece wanan"?
Ya fada Yana nuna hanyar da A'indo tabi,
"Au wai A'indo kake nufi,ai A'indo ce tsohuwar Matar ka baka gane ta ba"?......."



Aci gaba da gashi🍇
Maimou love😘
[20/10 à 19:40] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨




*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋




*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚




*DAGA AKALAMIN MARUBUCIYAR*

👇
*YA MACE KOWACE DA IRIN NI'IMAR TA*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*,
_and Now_👇
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*





_DEDICATED TO SADJIDA & UMMY ONTOP_




*Page -49-50*



Kallon Hajiya yayi yaga wai ita tayi maganar ko kuwa?

Yace"haba Hajiya wacen yarinyar da take bakauya ya za'a hadata da wanan nutsatsar."🙄

"Hum yaro man kaza ,ai sai kayi,ni zan shiga na kwanta,ka tashi kaima ka koma b'angaren ka."
Hajiya na gama fadar haka ta koma sama,tabar Alhassan cik'e da mamaki ,da kuma tambayoyi a Zuciyar sa.

Fitowa A'indo tayi da cup a hanun ta ,tana tafe tana shan tea ,tana danna wayar ta,dan chatting suke da Bashir,table ta zauna na cin abinci,taci gaba da da chatting dinta tana dariya,inda gaba-daya hankalin Alhassan ya karkata a kanta ,sam bata ma san yana nan ba,sanin da tayi cewar Hajiya ta koma b'angaren su.

Wayar ta ce tayi kara ma'ana Kira ya shigo,dagawa tayi tana dariya,fararan hakoran ta,mai d'auke da wushirya a tsakiya,wace ta kara ma hakoranta kyau suka bayyana,tace"hahhh Kalbi ya dai dagaske nake maka fa,Allah na yarda da zaran an gama auren Husseina kaima ka turo,tunda su hajiya ma sun yarda."

Duk wanan hirar da take a kunuwan Al'Hassan ,ransa yayi bala'in baci,yayin da hankalin sa ya tashi Jin tana cema wani ya turo ,har zai tashi ya nufe ta ,kuma sai ya fasa,zaune yake anma ji yake kamar ana zuba masa garwashi a zuciya,duk da bai yarda cewar A'indo bace,ya ma za'a ce itace,bayan wacan Yar kauye ce,jahila,marar aji kuma mumuna,ya za'a hadata da wanan,daga gani tanada aji,ga ilimi,ga kuma kyau,gata tamkar ba'indiya,Kai ina Hajiya zolayar sa kawai take.
Ji yayi gaban sa ya fadi Jin tana cema wani wai ya turo waye wanan kuma.


Gama shan coffeen ta tayi ta tashi,sai yanzu hankalin ta yakai kansa,ko shekara nawa zatayi bazata taba manta wanan bakin mugun ba,jin tayi gaban ta yayi muguwar faduwa.kenan dai yazo,hum Alhamdulillah tunda dai yanzu ba matar sa nake ba,bai isa ya takurani ba,kuma ma ina ruwana dashi."

Sakin ajiyar zuciya tayi sanan ta daidaita kanta,tazo ta gaban sa ta huce,wanda kamshi turaren ta ya dawo dashi daga duniyar shaukin ta,har takai gurin caji ta zage wayar salma,zata fita taji yace"ke bakisan ki gaisar da mutane ne ba,kina ganin mutane anma bazaki gaida su ba."

Cak A'indo ta tsaya,gaban ta na faduwa,dakewa tayi ta kirkiro murmushin tura haushi na gefen baki,ta juyo,ta zuba masa ido cik'in ido,wanda ya yasa faduwar gabansa dum,ba shaka wanan yarinyar ce,ko gizo ne,kai hakan bazai taba yiwu ba,ta ya ma za'ace itace ina sam bai yarda ba.
"Humm ashe akoi mutum a gun Sorry ban lura bane,ina wuni,anzo lafiya to Masha Allah."

Tana gama fadar haka ta juya tayi ficewar ta,yayyin da Zuciyar ta ke mata tafarfasa.

Wajen su idrissa ta nufa dan fada musu sakon Hajiya,anma ta iske har sun tashi basa nan,hakan na nufin sun gama tadin,tab yau wace rana hum.
.ta fada tayi gaba abunta,barin Alhassan tayi cik'e da baki,shi fa bai gane ba,da sauri ya tatara computer da wayoyin sa yabar b'angaren,ya nufi b'angaren idrissa iske sa yayi ya fito daga wanka.
"a'a bros kaine nayi tunanin ma kayi barci saboda gajiya, murmushi Alhassan yayi sanan ya fido wayar sa da ya d'auki A'indo lokacin da ta fito daga kitchen tana Shan tea bata sani ba,yace"kanina dan Allah wacece wanan,ya nuna ma Idrisa photon ,Idrissa ya duba ,yace Yaya yaushe ka d'auki wanan pic din.

Dazu na d'auke sa ta shigo falo shine nake tambayar Hajiya wai wacece tace tsohuwar matata ce."

Murmushi idrissa yayi yace"bro ai gaskiya ne,itace mana A'indo yar uwar tagwaitakar ta ce zan aura Husseina,itadai ce tsohuwar Matar ka,ai Yaya nayi mamakin da kabar wanan yarinyar,mai sufar indiyawa."

Idrissa na gama fadar haka yabar wurin,dan yanajin haushin dan uwan sa har yanzu.

Wani iri Alhassan yaji jikin sa ya Masa, gaba-daya gabobin jikin sa yaji sun mutu,jikin sa yayi sanyi, Zuciyar sa ta dinga bugawa da sauri-sauri,hankalin sa ya tashi,wani tsoro ya shige sa lokaci daya,firge ya nufa ya d'auki ruwan roba ya shanye gaba-daya,yanzu kam ya yarda photon ya kara dubawa ,duk da acan ba wani kallon ta yayi ba dakyau ya gane cewar itace,idan ko hakane wallahi da sake dole ma a basa matar sa yanzu."

Tashi yayi cik'e da kwarin gwiwa ya koma b'angaren sa,barci dai ranar kaurace ma idanun sa yayi,daga ya runtse idanu zai dinga ganin A'indo tana murmushin ta Mai tafiyar da Zuciyar sa,sai yan juye-juye yake a bisa bed,sai da asuba bayan yayi Sallah barci barawo ya d'auke sa.


Itakam A'INDO da komawar ta ta iske Husseina har tayi barci ,sai sauran kawayen su wa'inda suke tatauna yanda za'ayi choregraphie,wato yan matan amarya zasuyi rawa ranar dinner,wanda kuma harda A'indo,inda tsarin yake yan mata biyar zasuyi zasu jera biyu gaba biyu baya,sai daya a tsakiya,ko kuma a gaba,wada kuma A'indo ce zata tsaya a gaba,nan ta iske su suna ta tataunawa a kai,Salma tace"anma banda uwayen ango ko ?dan gaskiya da yar kumya,A'indo tace a'a dinner su hajiya sunce ta matasa ce,banda uwaye.gobe ma kanwar ango ke zuwa, khalissa muna waya sanan muna chatting da ita,har take ce min harda ita a masu rawar.

Mimi tace"gaskiya gwara tazo mu fara koyan rawar,a fara gaba-daya za'a fi tafiya daidai, yauwa hakan yayi ma.

Duk wani shirye-shirye yana gabata yanda ya kamata,inda khalissa tazo itama autar su Alhassan,suna bala'in sonta,komai take so yi mata suke basa takura ta,da kwana biyu,khalipha yazo shima mai bima idrisa,sai halissa itama a tatare sukazo mai bima khalipha ,wato wada take aure a Niamey,kai gaba-daya family an hadu,kuma dukan su akoi su da son jama'a,ga wani'irin so da suke ma su A'INDO tamkar jinin su ,dan dama koda su A'indo sukayi waya,suka saba da khalipha,Halissa,da khalissa,abun burgewa dukan su, sun d'auki su A'indo tamkar jinin su,hakan yasa da sukazo gida ya d'au hayaniya,domin Suma yan sharholiya ne,akoi su da son sho,Halissa da khalissa kusan kullum suna tare da yan matan amarya wato su A'indo.

Yau kwana biyar kenan da zuwan Alhassan anma abun nasa sai a hankali,dan kuwa kullum cik'in bin A'indo cik'in Siri yake,wani yanayi yake jin kansa wanda ya kasa gane masa, kamar kullum yau ma wajen k'arfe goma na safe suna zaune duka a falo harda Hajiya,da khalipha, Halissa,da khalissa da Idrissa sai Alhassan dake zaune yana duba computer baya ko jin hirar su, Hajiya tashi tayi ta tafi saman ta dan shirye-shiryen su dan bazata iya biye ma shirmen su ba.

A'indo ce ta shigo cik'in siririyar salamar ta, dukan su suka juyo harda uban gayar wato Alhassan,da ya ture cumputer gefe ya zuba ma k'ofar idanu,jin wace yake ishirwar ganin ta shigo,sanye take da dinkin doguwar rigar na bakin less,daga sama matse anyi mai gidan nono,matse yake har wajen bra sai aka sake sa daga sama har kasa ya bud'e ,dinkin yayi bala'in yi mata kyau,ya mata das ,ta dan yafa wani dan shara-sharan gyale,fuskar ta tayi simple make up,sanye take da dogayen takalma masu tsini,bakin ta yasha lips sai walkiya yake,da yar karamar jakar ta,sai ni'imatacen kamshin ta ke tashi a duk inda ta huce sai tabar sanyayan kamshin."


Khalipha yace"hum my sis tun kar ki shigo nasan kece,domin ke dama turaren ki ke fara ma mutum salama kafin ke.

Dariya A'indo tayi,duk da taga Alhassan ta dake tayi kamar batasan yana gun ba,yayyin da shi kuma Alhassan yaji gaban sa ya fadi lokacin da yaji kanin sa yayi wanan maganar.

Wata muguwar harara ya banka ma khalipha,anma ina khalipha ko ganin sa baiyi ba.

Kallon A'indo yake a kaikaice,ina kuma zata tayi wanan Shirin mtsss,salon ayita kalle ta,shi kadai yake wanan maganar a zuciyar sa ,idan ka gansa zaka rantse cewar aikin sa lake bisa laptop,anma ina ba wani aikin da yake sai ma rubutun sakin layi yake yana bata aikin da yayi yana rubuta shirme duk a rashin sani.


Wani kallo A'indo tayi ma khalissa na marairaicewa tace" da khalissa Bashir fa na jiran mu tun dazu ashe ke zaune

Please Login or Register in order to submit comment