Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ikon Allah yanda ake ji da Alhassan a kasar waje,direct gidan sa dake can ba nisa sosai da barikin sojoji,a barikin sojoji ma yanada katon gidan sa,to anma saboda kar A'indo ta tona masa asiri yasan ba hankali ne da ita ba,shi yasa yace a huce da ita wancan gidan nasa kawai.


Bayan an shigo tafkeken gidan na gani na fada,akayi parking,sojoji mata yasa su d'auko masa A'INDO,saboda barcin da take,aka kawo ta falon,sanan ya salami kowa,johne cucun sa,mai dafa abinci a gidan shine yake jerawa a table,bayan ya gama yayi ma mai gidan nasa barka da zuwa ya amsa ya fice daga falon."


zama Alhassan yayi ,yayi tagumi yana kalon A'INDO,tunani yake hanyar da zai bulo ya rabu da ita,shifa bazai iya zama da wanan yarinyar ba,Yar kauye dakikiya,dole ma ya nemi wata,mai ilimi ya aura,bazai taba zama da jahila ba kuma yar kauye.


Kare mata kalo yayi,sam yarinyar batayi masa ba,ko kadan.

"Mtsssss yarinya zaki gane ne,ubanda yasa kika biyo ni wly sai kin raina kanki, sha'awar sa yaji ta motsa dan haka ya kira Linda budurwar sa, itama da murna linda ta shirya,ta shigo motar ta,ta taho,Linda baturiya ce,tana matukar son Alhassan,sanan tana yaba ma mazakuntakar sa,yanda ya iya love da mace,yanda yake juyata a bed,abun na matukar burge ta, dan ita ida zai amince zata iya auren shi, shigowa Linda tayi ba wanda ya tsayar da ita tunda sun san ta,motar ta ,na shigowa daidai tashin A'indo,kunen ta Alhassan yaja tare da yi mata kashedi,cewar nan ba Niger bace ta kama kanta,fada yake mata sosai,ana cikin haka sai ga Linda ta shigo ,kur a idanun A'INDO,sakin baki galala A'indo tayi tana kalon Linda,can kuma ta kuma kecewa da dariya 😁 tace"la'illaha ilalahu yau ina Rabi'u zo kaga abinda muke kalo a akwati mai mutum,aradun Allah wa'inan fararen mutanen ne,masu jar fata,dama yace mun garin su zamu zo ,tashi A'INDO tayi saman kujera tana tsalo,sanan daga bisani ta duro da gudu tazo ta cukwikwuye Linda ta nannade ta,tana ihu ,aradun Allah bazaki gudu ba sai Rabi'u da Husseina sun ganki,😁."

"Keeee! Wai dan ubanki meye haka cewar Alhassan ya buga ma A'indo tsawa.

Linda Kam ta tsorata da turanci take tambayar sa Ina ya samo wanan mahaukaciyar .

Ce mata yayi yar aiki ce ,da hausa yayi maganar dan A'INDO taji,saboda Linda tana dan koyan hausa kuma tana dan ji kadan kadan
"Murguda baki A'INDO tayi tace"tab aradun Allah acikin makaryatan duniya kaine lamba daya a panin karya,dan kai inajin kakan su ne a karya,kalon Linda tayi dak'yau,tace"ke yar fara ni nan Matar sa ce,kuma sunana A'indo Tantagariyar Yar Aiki,mai zaman kanta,eheee karki yarda a zuka miki karya😏."

Rai a matukar bace Alhassan ya daga hannu zai mareta sai kuma ya tuna gargadin Mahaifin sa,ya sauke hanun sa,nuna ta da yatsa yayi yace "ki Kiyaye ."


Linda na tambayar sa abinda A'INDO take cewa yace ta kyale ta mahaukaciya ce,Kama Linda yayi ya hade bakin su wuri daya,tun a falo suka fara romancing din juna ,"la'illaha😱 ku yanzu bakwa jin kumya kuke tsotse tsotse kamar wasu tsuntsaye,ko kumya bakuji Kuna iskanci,sanan ta bala ma Linda harara ta murguda baki taci fuska tace"ke fuce ki fita daga gidan nan karuwa kawai dan ubanki ki shigo gida na ki Kama min miji na🤨, cik'in ran Alhassan yace thanks good aiko zaki ga iskanci iya iskanci,d'aukan Linda yayi kamar wata baby suka haye matatakala suka haye sama,kuka ne ya kufce ma A'indo ta fadi anan ta fara birgima tana kuka,wayyo Allah ina kike Hajiya kizo za'aci amana ta wayyo Hajiya ki taimaka,ihu take,wani abu ya fado ma A'indo a rai lokaci daya ta tsayar da kukan ihu ta buga ta tashi,sai yanzu ta gama kalon falon irin na turawa ne tsarin wani abun ma sai Wanda ya gani,falon ya tsaru,nan ta shiga zagayen falon tana buga kauyenci har ta gano kitchen aiko
Ta shiga,duk wani abu na kasar hausa da ya danganci kayan miya akoi harda mai,tunawa tayi da sulbin da yaja su hajiya lokacin da tayi guga,dariya ta kece da ita tace wohoho sai ni A'INDO Tantagariyar Yar Aiki,duk wanda yaja dake sai yaga magyarin mutum,eheee😏 Mai ta debo,tazo ta zuba a kasa daidai wurin saukowa daga matatakala,saida ta shafe gurin yanda baza a gane ba,in ba an kure kalon wurin ba,komawa tayi ta zauna ta baza tagumi,bayan awa biyu sai ga Linda ta fara saukowa ita kadai,sai wani farin ciki take ji Alhassan ya jiyar da ita zakin zumar sa.

Takowa tayi tana yanga,har ta sauko,sai ji tayi kamar an ja ta ta bada suuuuuu tim kake ji tayi sama ta fado kasa,dama Linda ba kiba ba, yar siririya,razananar
Kara Linda tayi wanda ya jawo
Hankalin Alhassan da yasa wondo yana shirin sa riga bayan ya fito daga b'andaki yaji wanan karar tata, ai da sauri ya Yar da rigar sa ya nufo falon inda yaji karar,ganin Linda kasa ya firgita da gudu ya sauko shima yana zuwa kasa daidai inda man yake yayi shuuuu shima ji kake tim ya fado sai ya Kara yin gaba da Linda,ita kam Linda kama kugu tayi tare da kara sakin kara, ita kam A'INDO zama tayi tasa su a gaba tana dariya,harda rike ciki....


husseina bayan tafiyar A'INDO kuka tasa harda birgima a kasa,cewa take"Wayyo Allah na higa uku,ni wly ku maido min yar uwata,Wayyo A'indo kina ina ki dawo dan Allah " kukan ta kawai take shirgawa ba k'ak'autawa, Rabi'u ne ya biyo ya ganta tana kuka yace"aaaa yau ni Naga ikon Allah,ke bara in gaya miki idan zaki ware ki ware ayi harkar arziki,kin wani zauna kina shirga mana kuka kamar Allah ya aiko katuwa dake"🙄


Tashi Husseina tayi ta murguda masa baki tace" ina ruwanka dan sa Ido,ai in bazaka rarashe ni ba sai ka bari hajiya ta rarashe ni,anma kazo ka cikani da surutu."

Tana gama magana ta kuma komawa kukan ta taci gaba."


Sakin baki Rabi'u daudu yayi yace"aaa to kanki akeji ta mahaukaci da ya fada rijiya yace kanku ake ji nidai wanka na nake😏,to ai sai ki tsaya kiyita kukan har mahadi ya bayana,nikam kinga tafiya ta bazan iya ba..... "
"Dadyn Alhassan Rabi'u namiji ne ina laifin akai mata yar uwarta inaga hakan zaifi,nima sai yanzu naga gagawar mu,dan A'indo batada ilimi ko ta zauna can ita zata wahala,ni da zakaji shawara ta da an dawo da A'indo anan Nigeria inaga hakan zaifi,saboda mu samu mu bata ilimi,in yaso idan ta samu daidai gwargwado yanda zata fida kanta ta ko Ina ne, sai mu tura masa ita,a lokacin itama zata iya ci gaba da karatun ta,anma kayi tunani sosai."


Tashi Hajiya tayi tabar d'akin tabar Alhaji da tunanin maganganun ta....





Aci gaba da gashi🍇
Maimou love😘
[10/10 à 17:34] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨




*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋




*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚




*DAGA AKALAMIN MARUBUCIYAR*

👇
*YA MACE KOWACE DA IRIN NI'IMAR TA*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*,
_and Now_👇
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*





_DEDICATED TO SADJIDA & UMMY ONTOP_




*Page 31 -32*




,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,Alhassan doctor yasa ta duba hannun Linda,tace gocewa ne tayi,nan aka gyara hannun Linda,sanan aka bata magani.

Ranar anan tare sukayi barci Alhassan da Linda,yayyin da A'indo ke can d'akin kare,wahala da zafi ya ishe ta,domin kuwa Alhassan da kansa ya hana a kunna A.C sanan yace kar a saki a kunna mata panka,idan kaga yanda A'indo ke kuka sai ka tausaya mata,tsabar wahala,in banda sunan Mahaifin ta ba abinda take kira,ita kam yanzu ba abinda tafi bukata kamar ta koma wajen mahaifan ta.

Washe gari Abass ne yazo gidan cik'in shirin sa shima na sojoji,a falo ya tarar da Alhassan zaune yana kalon Tv yana shan coffee.

Ko kalon inda Abass yake baiyi ba,zama Abass yayi yana dariya.yace
"Haba abokina me yayi zafi haka,har kazo gari ba tare da ka sanar min ba,saide naji a bakin wasu,gaskiya banji dadin hakan ba,me yasa baka sanar dani ba"?
"Saboda na tsane ka"

Alhassan ya basa amsa .

Zaro idanu Abass yayi cik'e da mamaki ,yace"Alhassan ni ka tsana bisa kan wane dalili"?
" Wani kallo Alhassan ya watsa ma Abass yace"saboda a ranar da kayi min baki a ranar ya kama ni,yanzu kamar ni ace an aura min yar kauye ,kauyen ma kauyen kayyau,jahila,munana , marar aji jaka,tunkiya,ai wly Abass Allah ya isa tsakani na da kai,saboda na tabata bakin ka ne, anma ba matsala,ni bazan iya zama da ita ba zan barta ne ta wahala,da kanta zata gudu,kowa ma ya huta."


Sake da baki Abass yayi yana kallon Alhassan sanan daga bisani yace"kai ni fa ban gane abinda kake nufi ba,kana nufin aure aka maka"?

"Dan Allah malam bana son munafurci baka saniba,tun a ranar da kayi min baki a ranar Daddy ya sanar min wai ya aura min yar aiki kuma yar kauye jahila."


Me ko Abass zaiyi baicin dariya, dariya yake kamar Allah ya kawo,abinda ya kara kullar da Alhassan kenan,tsaki yayi ya tashi ya bar falon,Abass saida yasha dariyar sa sosai tukon ya tsagaita,yace"tab anma wallahi Daddy ya burge ni,ai Alhassan anyi maganin ka,ace mutum bai d'auki dan kasar sa a bakin komai ba, ace ka raina matan hausawa,bayan taka mahaifiyar bahausa ce,ai wallahi zaka gane."

Abass yana gama fadar haka ya tashi ya fita motar sa ya shiga yayi compagni na sojoji.

Alhassan ma kayan sa yasa na sojoji sunyi matukar kama sa sun masa kyau,dogon mutum,mai kyan sura,a gaskiya kakin ba karamin kyau suke masa ba,ko mazan idan suka gansa burge su yake,bare kuma mata da suke haukan sa.


Shiryawa yayi ko takan A'indo baibi ba ya nufi wajen aikin sa.


A takaice dai A'indo saida tayi sati a wanan d'akin ba tare da wani abincin kirki ba,saboda abinci ma sau daya take ci a rana, gaba-daya zafi ya feso mata da kuraje a jiki,tayi baki ta rame,ga dauda ta kara rine ta.


A yau ne Alhassan yace a fito masa da ita,fido ta akayi duk tayi yaushi ta rame, wulak'antacan kallo ya watsa mata, sakamokon wani wari da yaji tanayi,saboda rashin wanka,done hanci yayi ya nuna ta da yatsa yace"abinda zan fada miki shine daga yau wanan d'akin da kika fito nan ne d'akin ki,na yarda ki dinga amfani da panka,anma banda A.C, kuma duk wani aiki da kika sani kama daga gyaran falo,wankin b'andakin gidan nan gaba-daya har na waje,sanan motocin gidan nan da fulawoyin gidan nan ke zaki dinga wankewa,kiba fulawa ruwa,wankin motoci ko baki iya zaki dinga wankewa ,sanan wankin kayana,akoi mashine a gidan nan anma da hannu zaki dinga wankewa, kuskure daya kikayi sai na saba miki,sanan abinci sau biyu zaki dinga ci a gidan nan,kamar yanda a kauye nasan ance kuna cin rama da tuwo,to akoi su a d'akin da zaki zauna,naso ma ace kin aza a itace,anma bana son a bata min gida shi yasa ga resho can ke zaki dinga yin abincin ki ke kadai,sanan wly wly naji kin bud'e bakin ki kince ma wani ke matata ce to wallahi sai na saba miki,wancan karon sati daya kikayi a duhu da zafi da yunwa ko,to wanan karon wata zakiyi har sai kin mutu an bine ki."kararawa ya danna,sai ga mai wanke motoci da mai ba fulawa ruwa,da mai wankin bayin gidan sunzo,nan ya umarce su da kowanne ya koya ma A'indo aikin sa,idan ta koya su bar mata ita zata dinga yin ayukan,sanan su zai basu wasu ayukan."


Godiya sukayi suka tafi,kallon sa na tsanar ta ya watsa ma A'indo yace"kuma bara kiji b'andakin gidan nan na waje wanda maza suke wanka suyi komai a ciki,to kema can zaki dinga wankan da komai ma,sanan naji ance kin kula wata hallaka da mace ko namiji a gidan nan to wly sai kin azabtu,babu fita,ke ko magana Kar na Kara jin kinyi a gidan nan,kin fahimta"!
Ya daka mata tsawa,a matukar tsorace A'INDO ta kada kai tace "eh" cik'in rudu. domin kuwa yanzu A'indo tayi matukar tsorata,ko kallon sa bata son yi,domin kuwa ya zame mata wani dodo....


Cik'in ranta take ayyana ranshin tausayi da rashin mutunci irin na Alhassan,yanzu ita da karayar ta a hannu yake son tayi wa'inan ayukan,wasu hawayen tausayin kanta suka zubo mata,korar ta yayi daga falon,wai ta bar gurin wari take,har done hanci yake,yana kwagirar ta,tare da kyama,tashi A'indo tayi tabar falon,haka ta tafi b'andakin tasa soso da sabulu na b'andakin da hannu daya ta fara wanka,a haka ta samu ta gurza jikin ta tayi wanka,ta sake kayan da ta taho dasu,na kauye duk da tana jin zugin da hannun ta yake mata haka ta fito,sai ta koma tamkar ba A'indo ba Tantagariyar Yar Aiki,sai ta zama A'indo abun tausayi....

D'akin ta ta zauna ,tayi tagumi,gari rogo ta gani kusan rabin buhu,nan ta ga suga,da garin tuwo,komai dai irin na karkara akoi a gurin,diba tayi ta jika garin tasa suga ta motse ta fara sha,saida taji cik'in ta ya cika tukon ta dan kwanta,kwancin ta keda wuya aka buga k'ofa,a matukar gajiye ta tashi ta fito ,"yauwa oga yace kizo a fara koya miki ayukan da akace ."

Murguda masa baki tayi,tace"hum wly bakuda tausayi,da hannun daya zanyi aiki."

"Ok bari na fada masa."

"a'a yi hakuri muje ."

binsa tayi,ya nuna mata yanda ake wanke motoci,ya kuma nuna mata kowace mota da fanar da ake shigar ta,kuma tun k'arfe shida na safe ake tashi a wanke ma oga motar da zaya fita da ita,ya nuna mata duk sabulan da klin din da ake wankewa ,da kuma yanda ake wankewa....

Saida ya tabatar ta gane,ya nuna mata wace za'a wanke yanzu,tausayi ta basa yace"hannun ki daya bayada lfy ne?

Kai ta kada masa tare da cewa"karaya ce."

Tausayi ta basa yace"kuma a haka zakiyi wankin."
Marairaicewa A'indo tayi tace"to ya na iya."

"Ok karki damu bara na miki,tunda oga yanzu yana wurin aiki,ke kuma ga ayuka sun miki yauwa."


Godiya sosai A'indo tayi,nan mai wankin bayi yazo shikam ba tausayi ya nuna mata komai nan ta fara wankin da k'yar,har saida ta wanke b'andakin gidan kusan guda shida. Sanan ta bawa fulawa ruwa,duk da hannu daya,kuka kam tasha yinsa,wanan bauta ita A'indo take yi duk wani shirme da wawanci ta aje su gefe,nace hum ashe shirme ma wuri garesa,idan kaga yanda A'indo ta dahe ta lalace tayi baki,ko kai waye sai ka tausaya mata,hannun ta kam kullum sai tayi kuka akan sa,saboda badan Allah yana tsarewa ba,da tuni gyaran ya lalace,abinci ko batada wani abinci sai garin rogo,shi take ci tasha.

*Bayan sati biyu*

Alhassan ne yake horn a bakin k'ofa aka bud'e masa A'indo ya hango tana wanke motar sa,take yaji duk wani farin cikin sa ya gushe,motar ya kara ma wuta da gudu yayo kanta, ganin haka da gudu A'indo ta gusa, cik'e da tsoron abinda taga yana shirin mata jikin ta na rawa.

Parking din motar sa yayi ya fito fuskar nan kicin-kicin, gadan gadan ya nufo ta,bai wani tsaya komai ba ya wanka mata mari yace"jahila baki ganin mota ne kika wani tsaya dan kin raina ni."


Hawaye ne suka zubo mata a kunci itakam bataga abun bugu ba ,kuma ai ta kauce kawai yana son cin zalinta ne."

Share hawayen ta tayi tace"yi hakuri."

Murmushi yayi na gefen baki,dan ga dukan Alamun horon da yake mata tana horuwa duba ga yanda ta lalace,ficewa yayi tare da bangaje ta,ta fadi akan hanun da ta karye,ta saki wata Kara saboda azaba,tsaki yayi ya kara wurgo mata kalon tsana yayi gaba, cik'e da farin cik'in yanda yaga ya kuntata mata....


Yau Mari itace da aiki a gidan,dan haka da gudu tazo ta kama A'indo ,tana hawayen tausayin ta,tace"haba,meyasa oga yake miki haka me Kika masa ne?
Share hawaye A'indo tayi tace"wallahi ban masa komai ."


"Ok to tashi muje d'akin ki,Kama ta tayi ta kaita d'akin A'indo ta duba hannun taga kamar ya dan gota kadan,ita ta kara gyara ma A'indo,saida tayi kuka kamar na fitar rai.



Yau Mina ce tazo gidan Alhassan,dan yau da kansa ya gayato ta,nan sukayi iskancin su,bayan sun gama suka fito falo,Mina tace"Alhassan wai dagaske kake zaka aureni"?

"Mina ina sonki zan aureki,zamuyi aure a boye,kaf Yan mata da suke so na kece nake jin zan iya aura,saboda ilimin ki,wayewa ga class ,inason mace haka,dan haka in ba damuwa inason auren ki,yau sati daya kenan da nayima iyayena magana akan auren anma sunki yarda,inaga kawai muyi auren mu ,daga baya sun huce."


Wani dadi Mina taji burinta zai cika,rungume sa tayi tare da cewa ta amince."
Tace"my Man zanje wajen wankin kafa."

"No karki damu bara akoi yarinya anan ta wanke miki k'afar tunda akoi komai na wankin ."

Sa wa yayi aka kira masa A'indo,da kyar A'indo ta tashi saboda zazabin da ya kamata ,jikin ta kamar garwashin wuta,haka ta tashi Idanun ta tuni suka canza kala,zuwa tayi ta duka tare da sunne kai tace"ranka ya dade gani."

Harara ya wurga mata,sanan ya kalli Mimi yace"tashi muje ta wanke miki k'afar ,tashi sukayi a wulak'ance ya kalli A'indo yace"ke!!!
Taso ,binsu tayi,wani baban d'aki ne sukaje ya tsaru gurin,d'akin gaba-daya duk wani abu da ya danganci wankin kai wankin k'afa,gyaran jiki irin na mata akoi sa,mayuka,turaruka,abun wankin kai ,kask komai dai na Salon na gyaran jiki akoi,nan yayi ma Mina kiss a baki sannan yace"yauwa nuna mata duk abinda zata d'auko ta wanke miki k'afar,wanan baiwar ki ce."

Cik'in kyama Mina tace "gaskiya wanan kazama ce ,anma zanyi maneji....





Aci gaba da gashi🍇
Maimou love😘
[10/10 à 17:34] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨




*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋




*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚




*DAGA AKALAMIN MARUBUCIYAR*

👇
*YA MACE KOWACE DA IRIN NI'IMAR TA*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*,
_and Now_👇
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*





_DEDICATED TO SADJIDA & UMMY ONTOP_




*Page 35-36*




Mari ce ta shigo dan ganin yanayin jikin A'indo duk da yau hutu take,anma ta kasa zama saboda itadai bata san me yasa ba A'indo ta shiga ranta,tana jinta tamkar yar uwarta dan haka ko breakfast batayi ba ta taho,a Lokacin tuni Alhassan yabar gidan,iske A'indo tayi rai hannun Allah numfashin ta na zuwa da dawowa,kamar mai asma,a rikice ta rugo da gudu ta iso ta talabo ta ta rungume,fadin take "Aisha Aisha mai ya sameki, innalillahi wa'ina illaihi Raju'un,aisha jini,kardai wanan mugun ya Kara miki wani abu,waya tayi mazan d'auka ta kira saurayin ta doctor,ce musu yayyi suyi mazan zuwa asibitin da yake,dan wanan abu dole sai anje asibiti,fita Mari tayi ta kirawo wata cik'in gards din tace su kama mata tasa A'indo motar da ta taho da ita ta kaita asibiti....


Mina ce ta fito,tana wani cin shuiwingwom tana harare harare, A'INDO taga an fito da ita ,zaro idanu Mina tayi tace"kai gidan uban wa zaku kaita,ku ajeta zan sata wani aiki ne."
Mari tace"kiyi hakuri madame zamu kaita asibiti ne batada lfy."
"🤨 Nace ku aje ta,baiwa dama tanada galihun da za'a kaita wani asibiti ne"?

Ku ajeta zan sata aiki ne."


Dayar ta saki A'INDO yayyin da Mari ta kara riketa gam,tare da cewa" Madame kiyi hakuri a yanzu wanan baiwar Allah tana bukatar ganin likita,idan ba haka ba komai zai iya faruwa."


"Ke har kin isa ina magana kina sa min baki,tare da yi min musu,to ki kiyaye ni, wallahi idan bakiyi abinda nace ba idan mai gidan nan yazo zaki iya rasa aikin ki."

"To sai me?
Ai indai dan zan ceci rai ne zai koreni a shirye nake,kuma ai Allah ba azalumin bawan sa bane,Nan ta fara jan A'INDO rai a hannun Allah,Mina idan ranta yayi dubu ya baci ,dan haka tayima gards din gidan maganar cewar karsu bari Mari ta fita da A'indo,aiko kata biyu suka tsaya a gaban Mari ,tare da maida hannuwa baya,sukaci fuska,dama Mari daga ita sai riga da wondo sanan kuma dama akoi bindiga karama a aljihun ta,fido ta tayi ta nuna su da bindigar tare da cewa "wallahi Allah idan har wani daga cik'in ku ya kuskura ya hanani fita to wly zan iya yin Ajalin sa,dan haka ku bani hanya."
Tabas sunsan Mari kwarara ce,kuma zata iya domin kuwa idan ranta ya baci babu wanda bai san halin ta ba,dan haka ba shiri suka gusa suka bata wuri."


Hucewa tayi tasa A'indo a mota suka bar gidan a guje a tsiyace,Mina kam tsiza yatsa tayi tare da jin haushin wanan Marin sanan ita kadai tasan shairin da makircin da zata kulla mata daga ita har A'indo.


Da gudu sosai suka isa Asibiti,bayan sunje doctor dama yayi komai taimakon gagawa aka ba A'INDO,wanda numfashin ta ma saida akasa mata Oxygen,da k'yar aka shawo kan matsalar ta,an gano cewar yunwa ta mata baban kamu,wanda a lokacin idan aka kara jan lokaci zata iya hadasa mata ciwon Ulcer,sanan kuma saida akayi mata karin jini,saboda gaba-daya jinin ta ya tsotse, kasancewar batacin wani abinci mai vitamin,da kara jini,sai ma gari rogo da take sha.

Dan haka karin jini aka mata, har leda hudu tasha,sanan kuma aka mata karin ruwa,Mari ke wurin ta tun dasafe har dare,ita ta koma gida ta dawo da abinci,da Alhassan ya dawo Mina bata nan tabar gidan saboda Kiran ta da samarin ta ya mata cewar akoi casu,dan haka a bakin masu gadin yaji cewar ankai A'INDO asibiti,bai ko damu ba,yayi gaba abunsa.....

Mari ce ta dawo dan d'aukan kayan A'INDO saboda sai an tsare su.


Ce mata akayi oga ya dawo, direct falon sa ta nufa yana danna computer,yana shan coffee,ba abunda ya sha masa kai,kamar ba shi ba yasa Yar mutane cik'in wani hali,salama tayi tare da sara masa ,tace"sa dama dan nace maka an rike A'INDO so zan kulla da ita a asibitin,dan haka ina bukatar adan bani hutu."


Wani matsiyacin kallo Alhassan yayyi mata yace" Mari kinsan cewar ba'a min katsa landan,dan me zaki d'auki yarinyar nan ki kaita asibiti?da izinin wa?
To bara kiji wallahi kika ja min magana sai na miki hukunci tsatsaura,sanan bayanin d'aukan hutu ruwan ki ne kizo ruwan ki ne ki tsaya,anma ki sani ki tabatar kin dawo da yarinyar nan dan

Please Login or Register in order to submit comment