Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Su A'indo harda karya wai ta fito tana jiran Al'Hassan🙄


Ran Hajiya kanta ya baci kallon Al'Hassan tayi tace"kayi min dai-dai,sanan takai kallon ta ga Bashir Wanda ya farfado anma idanu kawai yake binsu dashi dan baida ko k'arfin motsa yatsar sa .


"Bashir ada nayi tunanin Kai dan mutunci ne a yanda ka yaudare mu kaje mana da mayaudariyar fuskar ka,wada tasa muka baka yarinya,Ashe ba haka kake ba,munyi nadamar aura maka Aisha da mukayi tun farko, kai ko tausayin maraicin ka baka yi, gargadi zanyi maka Wanda na farko kuma na k'arshe tun farko yara na sun so rufe ka na hana su dan tausayin maraicin ka duk da abinda kayi ma yarinya ta,ka sani Aisha ya ta ce,wallahi Allah duk ranar da ka kara kokarin koda Kallon banza wa Aisha wallahi Allah kaji na rantse sai ka raina kanka ku fice muje."

Hajiya taja A'indo shima idrissa yaja Al'Hassan suka bar Bashir kwance tamkar gawa.


Bayan sunje gida gaba-daya Alhassan yaki sakar ma A'indo fuska domin cewar sa laifin ta ne da tayi hakuri suka tafi bata fito ba da duk hakan bata faru ba....



Aci gaba da gashi🍇
Maimou love😘
[15/11 à 20:06] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨




*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋




*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚




*DAGA ALKALAMIN MARUBUCIYAR*

👇
*YA MACE KOWACE DA IRIN NI'IMAR TA*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*,
_and Now_👇
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*





_DEDICATED TO SADJIDA & UMMY ONTOP_


*🏵 HAPPY JUMA'A🏵*




*Page 73-74*




Gaba-daya yanzu A'INDO ta damu,Sam batajin dadin abinda tayi masa ,gashinan taurin kai ya ja mata ya fara fushi da ita.


Suna shiga gidan ya fice b'angaren sa,Hajiya tace "A'isha je kiyi wanka kici abinci ki huta,ki fida damuwa insha ba abinda zai kara faruwa."
Gyada kai tayi ta huce b'angaren ta,dan yau acan zata kwana, idrissa ma salama yayi ya koma gidan sa,inda ya tarar da Husseina yake fada mata abinda ya faru.
"Haba ai da kun barsa ya kashe shi ma dan iska duba yanda yazo duk muka d'auka na Allah ne Ashe mugu ne,wallahi Yaya Al'Hassan ya burge ni gwara da yaci uban sa."

Hade fuska idrissa yayi yace"ni kenan ban burge ki ba ranar da na doke sa ko 😕"

"Au afuwa kaima kana burge ni,ai kaima kafi burge ni kaifa jarumin namiji ne,haba dai ya da kishi kuma yayan ka ne fa🤭 "


Rungume ta yayi yace"ba dole nayi kishi da abinci na ba.😉"
"Au nice abincin naka?
Cewar Husseina yace"eh mana kece
Abinci na danye mai dadi ba."

Dariya tayi ya rungume ta tare da fara aika mata sakwanin sa masu rikitarwa.

Dare misalin k'arfe goma sha daya kowa ya kwanta anma banda A'INDO da take da zuwa da dawowa a d'aki,tasan cewar Al'Hassan yayi mata laifi anma kuma ai yanzu ya gane kuren sa me yasa tayi masa haka duk cin fuskar da take masa bai taba bata ransa ba anma yau gashi tanaji a jikin ta kamar ransa ya baci wanan ya hana mata kwanciyar hankali,hijabin ta tasa
Ta fito sadaf-sadaf ta nufi b'angaren Al'Hassan Saida ta isa zata k'wank'wasa sai kuma ta tsaya cak,"me ke damu na ?
Me zanje nace masa,anya nice kuwa?

Ita kadai take tambayar kanta,can dai kawai ta shiga tare da yin Salama,a falo ta iske sa zaune saman kujera yana danna system dinsa, saman carpet ta dan zauna tace"dan Allah kayi hakuri idan na bata ranka,nasan nayi kuskure."

Al'Hassan kamar daga sama yaji muryar ta,abun yayi bala'in basa mamaki,wai yau A'INDO ce ke basa hakuri,tab yau kam yaji dadin sa,ya samu runguma ga kuma bada hakuri,wai yau shine ake bawa hakuri.

aje aikin da yake yi yayi ya tura system din gefe yakai duban sa gareta da kyau,yace"Aisha ba wai nayi fushi bane,nasan duk da ni mai laifi ne a gurin ki anma ki sani nayi miki laifi ne a lokacin ina cik'in fushi,wallahi Aisha idan nace miki ada can wanan abun da nake miki cik'in hankali na nake miki nayi karya,domin kuwa a lokacin ina cik'in fushi abinda iyaye na sukayi min,Aisha ada a shirme na duk macen da ta waye itace komai zatayi ba tare da ta sa ni jin kumya ba ,zan shiga ko ina da ita ,sanan ba wanda zai raina ni a shirme na ,wayewa itace komai,a lokacin bansan so ba ,bansan meye so ba,bansan ya ake yinsa ba
bansan hanyar da zanbi ba na san sa,wallahi duk matan da nake kulawa har ta yanzu wace na aura ba wai dan ina son su bane,nasan zakiyita tunani idan tsakani da Allah nake son ki me yasa tun farko da baki zama haka ba ban nuna miki ba sai yanzu,eh to a zahirin gaskiya a da can ban ma tsaya na zauna dake bare na fahimci so ,ban nutsu ba bare nayi tunanin zan fara sonki,nayi kuskure anma ki yafe min."


Rike hannun sa tayi abun yayi bala'in basa mamaki , murmushi tayi tace"a yanzu kana so na ?

Zaka iya aurena a karo na biyu?
Zaka iya zama dani a ko wane hali"?


Kasa controling din kansa yayi ya washe baki tare da Rungume ta bai shirya ba,"nagode nagode sosai Aisha Wallahi ban taba tunanin zan sameki ba,Allah Kaine abin godiya wallahi nayi miki Alkawarin zaman Amana dake,zan sanya ki nishadi zan zauna dake zama na har abada,zan baki farin ciki,Allah Aisha zaki aureni,zaki sa ni sau daya dai nima na dandana dadin aure.

Kada kai A'INDO tayi tace" Al'Hassan na kuma baka wata dama ta biyu ne dan Allah Karka kara sa na tsani maza,ka nuna min tunani na ba haka ne ba."

Girgiza kai yake yana hawaye na farin ciki tare da kara rungume ta."

Kokarin zame kanta tayi daga jikin sa.
Ta share hawaye da suka zubo mata tace"ni zanje na kwanta dare yayi, murmushin sa mai tafiyar da hankalin yan mata ya sakar mata yace"haba ke kuwa amarya ai kamata yayi ki kwana tunda dai kinzo bikon angon naki😉."

"😳ni din , wato har na zama amaryar taka ,hum karka sa na fasa ma.🙄"



"🙆‍♂ Ki rufa min asiri a yanzu idan kika kara kokarin bari na to tabas gawata za'a d'auka."

"A'a kaiko ana zancan kirki mai ya kawo kuma mutuwa a ciki nidai bana so ka daina."

"😊 To shikenan kiyi min Alkawarin zama dani a kowane irin hali."

"Nayi."

A'indo tace tare da barin gurin da gudu.


Dariya yayi ya koma ya kwanta,ya fara tsale ,rawa kam ranar ya sha ta, gaba-daya farin ciki ya mamaye sa.

Ita kanta A'indo d'aki da ta koma kasa barci tayi sai tunani da nazari take shin abinda tayi yayi ko kuwa tayi saurin bada kanta,anma ita tayi hakane saboda tsoro,tana tsoron kar Bashir ya Kara d'aukan ta dan a zahirin gaskiya a yau kawai k'arfin halin yima Bashir tsiwa tayi anma ta tsorata,tabas yin auren shine zai kare ta daga shairin sa.
Anma zatayi shawara da Yar uwar ta taji.

Washe gari da misalin k'arfe tara na safe A'indo ta shirya tayima Hajiya salama cewar zataje gidan Husseina,Hajiya tace"lala ban amince kije ke kadai ba bara na kira yayan ku ya kaiki idan zaki dawo ma shi zai koma ya d'auko ki,dan wanan yaron bamusan shairin da yake nufin mu da shi ba.bata same sa ba , wayoyin sa a kashe Rabi'u daudu ne ya shigo,Yana tafiyar tasa ,Hajiya tace"yauwa Rabi'u tunda Allah ya kawo ka je b'angaren soja kirawo min shi..."
"😳tab kaji Hajiya da wata magana,yau Allah na tuba na safurce wanan yawan mutuwa da ake ai gwara mutum ya mutum salin alin ba tare da an wahalar dashi ba,kafin ya mutu,yau Hajiya jiya nayi mafarkin mutuwa yau kuma kina ce naje na kirawo mutuwar da kaina,aradun Allah Hajiya idan kin ganni kabari maza suka kaini ba mata yan uwana ba,yau Allah na tuba na kuma tuba a yanda nake ba aukin nan nausa daya zai min naje barzahu,kinga tafiya ta ga balaraba Yar ki nan ta kira miki shi ni nayi nan."
Kada kai Hajiya tayi tace "Allah ya shirya.
Dariya A'INDO tayi Hajiya tace" je b'angaren yayan naku kice nace ya kaiki,bara na baki sako ki kai mata ."

"To Hajiya."

Sama Hajiya ta hau ta harhado ma Husseina kayan mata masu inganci da aka kawo mata ,komai akoi a rubuce,ta fito tace"ungo ki gaida ta,amshi wanan dubu goma ne nasan ki da kwalam wata killa kinga wani abu kiyi
Sha'awa."

"A'a Hajiya a barsu bazan sayi komai ba."

Harara hajiya ta wurgo mata tace"Sai nace A'indo,wai ni na tambaye ki ina dusar da kike tarawa naga har yanzu ba'a sayi ragon ba ko kudin basu taru ba."

Hajiya ta fada cik'in dariya.
Da gudu A'INDO ta amshi kudin tabar falon cik'e da kumya tana dariyar kanta.
Tabdi lalai ta zuba shirme ita kam.
Al'Hassan yanzu ya tashi ,dan bai kwanta jiya ba,saloli yayita yi,yana kara godiya
Ga Allah , shiryawa yayi cik'in kananan kaya,wondo kalar na soja ne anma ba na sojawa bane,ana basu kayan ne saboda zaman gida ko kuma fita yawo haka,yayi kyau sosai fuskar sa sai annuri take tamkar wani ango.

Fitowa yayi falon sa ya zauna saman table dinner ya zuzuba abin karyawar sa ya fara karyawa yanayi yana shan Lipton,da salama ta shigo ,kamshin turaren ta ya sanar da shi itace,lumshe idanu yayi yanajin nishadi,tare da farin cik'in zai fara tozali da k'yakyawar fuskar ta,kafin ta kowa.

Salama tayi ya amsa ta shigo,tashi yayi ya tarbo ta yace"oyoyo my lovely wife,ya kike,kamar kinsan dama tunanin ki naketa yi."

Murmushi tayi tace"good morning,Hajiya tace" wai ka kaini gidan Husseina,nace mata zanje ni kadai tace a'a wai tana tsoron Kar wanan Bashir din ya kuma min wani abu,shine tace nazo ka kaini."

Ta fada cik'in shagwaba wanda gaba-daya ta tafi da imanin sa ,yayi bala'in mutuwan tsaye, domin ta tafi da imanin sa,wani irin shaukin sonta ke kara shigar sa."

Tsayuwa yayi yasa hannu a aljihu,yace"to zan kaiki bara na gama karyawa ya fada yana kwaykwayon maganar ta."

Turo baki tayi kamar zatayi kuka tace"ni bana so ka bari.".
"☺to naji zan bari anma kema sai kinzo munyi breakfast dan na tabata baki ci komai ba wanan cikin a shafe sam na lura baki son cin abinci ko kadan."

Bubuga kafa ta fara tana dan kukan shagwaba tace"ni gaskiya bana ci idan bazaka kaini ba na hakura."

"a'a ba yi hakuri gimbiya ta bara na d'auko key nima na fasa karyawar muje."

"a kayi hakuri ka karya sai mu tafi."

"bazanyi ba tunda kema kinki yi."

"Yi hakuri zanyi muje muci."
"zama sukayi ta zuba kin cin nasa yayi ya matso kusan ta ya sa cokali suna ci murmushi tayi batace komai ba tasan duk neman magana ne.
Saida suka koshi itace ma taci kadan,shi kam bud'e cikin sa yayi yaci ya koshi cik'in nishadi,ga masoyiyar sa kusa.


Bayan sun gama suka tafi,a k'ofar gidan ya aje ta ,zata fita yace"da kin gama ki Kira ni kuma karki jima I love you."

"To tace masa tayi murmushi ba tare da ta maida masa abinda yace mata ba.


Girgiza kai yayi yaja motar sa yayi gaba ita kuma ta shiga gidan, Husseina da sauri ta tarbo ta lokacin da taji. Salamar ta suna murna suka rungume juna.

Shigowa suka suna yaushe rabo,aka cika gaban A'indo da kayan ciye-ciye ,bayan komai ya lafa A'indo take tambayar idrissa Husseina tace ya tafi aiki,bai ma jima da tafiya ba."

"Yauwa cewar A'indo,tace"Husseina shawara nazo muyi dake ke kadai ce Yar uwata plz ki fada min gaskiya idan da kuskure a abinda nayi,nan ta fada ma Husseina komai game da abinda ya faru da irin abubuwan da take ma Al'Hassan,har jiya da fada masa abinda ke ranta."

Suake ajiyar zuciya Husseina tayi tace"to A'indo,nidai gaskiya a yanzu ko daya bana jin haushin Al'Hassan,sanan bana kin auren ku a karo na biyu,lalai ya kamata ki basa dama ta biyu hakan yayi abinda kikayi shine dai-dai,saide ki sani da ba yanzu bane,karki yarda ki d'auki raini ga kowa, Al'Hassan ya cancanta ki basa dama ta biyu kodan mahaifiyar sa,da Mahaifin sa da yan uwan sa yanda suka d'auke mu hannu biyu-biyu basu taba nuna banbanci ba tsakanin mu da yaran su,sanan Hajiya Koda bata fada ba nasan cewar zata so ki komawa danta........


Alhassan ko komawar sa gida ya iske daddyn sa ya dawo da murna ya isa garesa suna zaune shida Hajiya a falo suna kallo.

Zama kasa yayi yace"Daddy ashe ka dawo.?

"Eh wly son na dawo jiya dadare ,ya kuke Kuna dai lfy ko",?

"Lfy lau daddy wly munyi kewar ka ."
Murmushi daddy yayi ya shafa kan Alhassan, sanan Al'Hassan ya gaida Hajiya ta amsa tare da tambayar sa ya tashi lfy,da fatan yakai A'indo yace "Eh Mom na kaita."

Tumbure fuska yayi a shagwabe Hajiya tace"yadai Soja na?

"Mom ni gaskiya ku daina ce mata A'indo ,duk kun bata mata suna,ga sunan ta hassana ko Aisha anma wani A'indo."


Sakaka da baki suka tsaya kallon sa cik'e da mamaki,Hajiya ce tayi k'arfin halin cewa "kai ungo nan🖐."

Dakuwa ta balla masa tace"kaci yan gidan ku,kaine wai zaka gyara mana sunan A'INDO kai a su wa"?


"A mijin ta Mana."

Ya fada tare da cije harshe ya kashe ido daya.
"Mom daddy dama nazo nace muku ne Aisha ta amince da aure na a karo na biyu jiya ita da kanta tace ta yarda na aure ta ,ni kuma nayi mata Alkawarin auren ta da zama da ita na amana.dan Allah Momy kuma kuyi hakuri ku manta komai ku aura min ita a karo na biyu na muku Alkawarin riketa amana."


"Son mai kake cewa Aisha da kanta ne tace zata aure ka"?

Cewar daddy.
"Eh daddy Wallahi ita tace."

"a gaskiya Son banajin zan amince na kara aura maka yarinyar nan a karo na biyu saboda mun maka haka a farko anma ka butulce."

Hajiya tace"ni kaina gaskiya ban goyi baya ba,kuma ban ma yarda cewar Aisha ta amince da wanan batun ba."

Ba yanda A'lhassan baiyi ba anma ina sam suka ki sauraran sa komawa yayi tamkar mahaukaci,Yana ji a jikin sa matsawar suka kara hana masa ita tofa a wanan karon ransa ne zai rasa.


Haka yaje ya dawo da A'INDO wace ko wunin batayi ba.




Suna zaune kawai sai ganin su sukayi, Alhassan yace "Mom ku tambaye ta gatanan kuji idan ba da amincewar ta ba, gaba-daya ya fice a hayacin sa lokaci guda......


Daddy yace "Kai Alhassan meye haka kuma?

rike kai Al'Hassan yayi Jin da yayi yana sara masa yace"dad kun kasa fahimtar irin son da nake mata shi yasa kuke tantama,Hajiya ta yafito A'indo tace"Aisha zo Nan."

Zuwa A'indo tayi ta zauna tare da sunne kai kasa,dan yanzu ta fahimci inda maganar ta dosa.

Hajiya tace"dagaske ne abinda Soja ya fada wai kin Amince da auren sa a karo na biyu"?

Kamar ta nutse kasa dan kumya,da k'yar ta iya bud'e bakin ta tace"Eh Hajiya ni na amince."


"A gaskiya kuyi hakuri Aisha Allah baki wani mijin,anma bazayin sakacin da nayi ba a baya ,gaskiya Allah Baki miji na gari,wanda zai rike ki Amana,anma yanzu bazan kara sakacin da nayi a baya ba, aka wulakanta min ke."


Gaba-daya kan Al'Hassan juyawa yake tun farkon maganar Hajiya,a yanda ya lura Hajiya bazata aura masa A'indo ba ,gashi yasan cewar ko Daddy ne ra'ayin Mom dinsa zaibi tunda basa musa ma juna.



Dafe kansa yayi kawai sai jin sa akayi tim ya fadi a sume da gudu A'indo tayo kansa tana kuka "Wayyo Allah ka tashi,dan Allah karka barni,Hajiya ku taimaka wallahi Ina son sa ,karku rabamu,Wayyo Hajiya gaba-daya ta rikirkice,bata ma san me take fada ba."






Aci gaba da gashi🍇
Maimou love😘








[16/11 à 20:53] Mai Waina: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨




*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋




*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚




*DAGA ALKALAMIN MARUBUCIYAR*

👇
*YA MACE KOWACE DA IRIN NI'IMAR TA*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*,
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*





_DEDICATED TO SADJIDA & UMMY ONTOP_




*Page 75-76*





Alhaji da Hajiya suka hada idanu cik'e da mamakin A'INDO,kasa motsi sukayi,itakuma da gudu ta tashi ta nufi firge ta d'auko ruwan faro ta dawo ta talabo kansa ta aza bisa cinyar ta ta zuba ruwa a hannunta ta shafe masa fuskar,sau uku tanayi tana karanta Addou'a sai can ya fara bud'e idanu a hankali, murmushi tayi ta fara goge hawayen ta,tace" yauwa tashi kaji,kyale su hajiya idan bazasu aurar damu ba,ba sai mu gudu kauyen mu ba, murmushi yayi cik'e da jin wani sonta na karuwa a ransa bayan ya bud'e idanun sa.


Hajiya tace"A'indo a gaban mu kike cewa ku gudu ba ko kumyar mu, to munji ba sai kun gudu ba zamu aurar daku,ke kika sani,dama ke muke ji."


Saurin rufe fuska🙈 A'INDO tayi cik'in jin kumya,sam bata ma san tayi wanan batun ba a gaban su."

Murmushi Alhaji yayi yace"Son wanan duk so ne,kana namiji kana irin haka."

"Zumburo baki yayi yace"daddy so ne ,shi ba ruwan sa da jarumta, zuciya ba'a iya controlling dinta game da so."

Girgiza kai daddy yayi cik'e da farin ci yace"to ai sai ku fara shiryawa tunda batada idda a kanta za'a sa wata daya ayi a d'aura muku mu huta da rashin kumyar ku."

Hajiya ma murmushi tayi yanda taga yanzu suna son junan su matuka,nan suka juya suka haye sama ita da Alhaji."

Kallon ta yayi yace"ashe kina so na haka shine wancan lokacin kika nemi kasheni,da yanzu na jima a kabari."

"Shiiii🤫 bana son haka ,ya zaka mutu bayan baka bani baby ba, k'yakyawa irin ka ,kuma ma ai sai na riga ka mutuwa,nafi so mu mutu tare,ban ma so na riga ka,dan idan na barka mantawa zakayi dani ka auri wata kusha soyaya."

Dariya yayi yace"anya kin barni ma nayi magana da mata ma kuwa?
Wanan kishi,ranar haka kika sa na kori Farida a mota ta."

Ya fada yana tsokanar ta.


Wani nishadi yake jin kansa ji yake kamar ya dawama a cinyar ta,Dan yana jin dadin yanayin.


"To tashi muje muyi shirye shirye Kinga Alhaji yace wata daya za'ayi auren mu,muje musan abin yi ko."
" Har ka warware?"

Ta tambaye sa
lakuce hancin ta yayi yace"ai dama ciwon naki ne, tunda an bani ke ai na warware ko."


Dariya tayi tace"tashi mubar wurin Allah yau nayi rashin kumya fa."

"Share su Mom ai duk cik'in so ne su wa yasan me sukayi tashi muje ,anma sai kin kama ni bana da k'arfi sosai."


Tashi tayi ta kama sa ,suka bar falon cik'e da so da kaunar juna .

Alhaji zaune shida Hajiya a d'aki.

Alhaji yace"a gaskiya yaron mu ya kamu da so sosai fa ,dariya Hajiya tayi tace"hum wa ya fada masa ai ni na jima da sanin son da yake Mata tun fa zuwan sa da yayi,ka manta yanda yazo yana rokon mu kafin auren ta,da yanda ya kwanta rashin lfy,ni ko auren nata na tabata rabo ne ya raba ta da mijin wancan."


"Hum ni ai ban taba tunanin yaron nan zai mana haka ba,anma in halin sa ne zai gani."
. Nan sukayita tataunawa bisa kan auren, daddy ya bada kudi masu yauwa yace"a sayi duk abubuwan da ya kamata.

Koda su Al'Hassan suka isa b'angaren sa suka zauna a falo, A'INDO ta bud'e fruits ta kawo musu suka zauna kasa suka kunna kalo ita ke basa yana sha tana sha, Al'Hassan yace" babyn na 1millions ya ishe ki sabgar biki ko?


"😳 Haba kaima wani irin abu ne haka duk inkai wanan kudin ina haka,gaskiya a'a sunyi yauwa sosai."

"Nidai abinda zan baki kenan idan ma basu isa ba sai a kara, in yayi saura can kisa a account din ki,kina matsayin matata bana son a raina min ke."
. "🙄 to wai kai kudin sun maka yauwa ne?
Idan sun maka yauwa karka ma yara na albazaranci ka bar musu idan sunzo suci dadin su dasu."


"Wai ni sai maganar yara ake min ince dai za'a Haifa min su masu yauwa ko,dan yan biyu biyu Zaki dinga Haifa min,Kinga har na tsufa anma banida dan kaina😔."


"Tab wai ka tsufa a hakan ,ka ganka kuwa wly kamar dan shekara ashirin ,ni baka tsufa ba gaskiya ban yarda ba😙."

Dariya yayi yace"to naji yaushe zamu fara sayaya,ni Paris ma nake so muje ko kuma indiya ko wata kasa daban dai inda zamuyi sayayar mu,anma nasan Mom bazata yarda ba."

*Bayan sati daya*
Cik'in Khalissa kanwar su Al'Hassan ta tashi da bala'in ciwon ciki cik'in dare wanda ya zubar mata da ciki ko kafin idrissa yayi wani abu akai ciki ya zube.....


Su hajiya da A'lhassan A'INDO duk sunje, Khalissa nan tayita neman gafarar iyayen ta ,tare da fadin a Makarantar su ne akayi mata fyade,Nan iyayen suka amshi k'addara suka yafe Mata,aka maido ta gida kamar ba abinda ya faru.

Mijin Halissa ma Ya dawo garin Zinder kullum cik'in zuwa bada hakuri yake,anma anki ma sauraran sa,so ake a tabatar da ya gane kuren sa tukon.


Al'Hassan da A'INDO sun koma tamkar Romio da Juliette,kullum cik'in soyaya suke,har mamakin soyayar su ake.

A yau Mina ta

Please Login or Register in order to submit comment