Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

uwan nasa yace"Yaya kayi hakuri ka bar zancan tunda kaji abinda Mom tace,dan ko ni nan kafin na fito daga gidan sa saida na bubuge sa,kayi hakuri,mubi umarnin mahaifiyar mu plz."

Sauke ajiyar zuciya Alhassan yayi yace" shikenan."

Dafa sa idrissa yayi yace"brother ka kwanta ka huta,bara na tafi wajen aiki."

Lumshe idanu Alhassan yayi tare da kada Kai.


Tunda idrissa ya fita Zuciyar Alhassan zafi kawai take masa, duk ji yake ba dadi,jin yake kamar shi akayi ma wanan wulak'anci ba A'INDO ba.


*Bayan sati biyu*


Duk wata kulawa da ta dace Hajiya tana ba A'INDO,tana kulla da ita tamkar mai jego,
Sanan duk wani gyara tana Mata,tuni A'indo ta dawo yanda take,ta warware ta cika tayi freshe,Sam ta fida damuwa daga ranta,dan dama zama a gidan Bashir tamkar cik'in kaya take,yanzu ko da suka rabu daidai take Jin kanta,abu guda ne idan ta tuna yake mata ciwo shine yaudarar da Bashir yayi mata,da kuma shairin zina da yayi mata.

A wanan lokacin kuma tuni Bashir ya fara raina kansa,domin kuwa ya saba da cin abincin A'INDO,ya saba da shiga cik'in kogin zumar ta mai dadi,ya saba da adon ta,da yanda take gyara masa gida yayita kamshi,gashi idan yana cinta wallahi wani bala'in dadi yake ji kawai baya Fadi ne,baya sambatu dan karta raina sa,a yanzu bayada aiki sai zama yana tunanin ta.


A yanzu Alhassan kullum yana tare da Halissa zaune idan ya gansu zaune itada A'INDO sai yazo shima ya zauna to daga A'indo taga haka sai ta tashi ta bar wurin abun baya masa dadi, hakuri kawai yake.

Yau ma kamar kullum yazo ya zauna falo suna hira,ita da Halissa.



Halissa ta tashi dan d'aukan wayar ta a d'aki zatayi waya ,itama A'indo tashi tayi zata bar wurin,sai jin muryar Alhassan tayi yace"haba Hassana ko ba komai ai ni matsayin yaya nake a gun ki,me yasa kullum idan nazo kike tashi daga gurin kina kyama ta tamkar kinga Kashi."

"Saboda banga abinda zan tsaya ma ba,me zan maka idan na tsaya,kaga Malam banida wata halaka da kai dan haka ka shafa min lfy."

"Haba Hassana me yasa kin kasa yafe min laifin da nayi miki,karki manta Allah mu ma muna masa laifi kuma yana yafe mana sai mu yan Adam, wallahi hassana na yarda zan d'auki k'addara a duk yanda tazo min anma bazan iya hakurin fushin ki a tare dani ba,Hassana Allah ya nuna min ishara tun daga Matar da nake aure yanzu,zuwa ga kannaina,ga wanan accident din da nayi duk hakkin kin ne ke dawainiya dani,kiwa girman Allah ki yafe min kura kurai na,wallahi Allah hassana tun daga gareki na daina wulak'anta duk wata ya mace,ki taimaki rayuwa ta ki yafe min."😔


Ko kallon sa batayi ba ta buga tsaki tabar wajen,dan ita yanzu kara jin tsanar maza ma tayi,duk da a yanzu bata ma Alhassan kiyayar da take masa ada,anma bata son basa fuska ne har wani shakuwa ya shiga tsakanin su,hakan yasa taki basa fuska ma.


anan tabar Alhassan,kansa na sara masa,ya rasa yanda zaiyi da rayuwar sa,ashe haka ciwon so yake,shikam ji yake da ma ba'a halace sa ba a duniya.


Alhassan sha'awa ta bala'in yi masa yawa,anma baisan yanda zaiyi ba,wanan wace iriyar rayuwa ce haka ace kanada mata anma sam da kaida wanda baida duk daya,shikam dole ya nemi daddy ya gaji da wanan auren .

Tashi yayi jikin sa a matukar sanyaye yabar falon d'akin sa ya nufa,ya d'auki wayar sa number Mina ya lalubo kira daya biyu ta d'auka,tana d'auka ba ko salama tace"ya akayi ."

Rai a bace Alhassan yace"idan kinga dama ki dawo Nigeria,dan na gaji da rainin hankalin ki,idan kuma can zaki zauna to Zan turo miki da takardar sakin ki."

Yana gama fadar haka ya kashe wayar sa.




Aci gaba da gashi🍇
Maimou love😘
[10/11 à 22:14] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨




*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋




*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚




*DAGA ALKALAMIN MARUBUCIYAR*

👇
*YA MACE KOWACE DA IRIN NI'IMAR TA*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*,
_and Now_👇
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*





_DEDICATED TO SADJIDA & UMMY ONTOP_




*Page 69-70*




Mina ko jin kiran Alhassan yasa ta fara tunanin tatara kayanta,saboda har yanzu tana son mijin ta,dan haka ta fara tunanin cirar tiket na jirgi tazo Niger anma ba ta tunanin zata iya wani zama a Niger .

Yau ma kamar kullum A'INDO suna zaune shima Alhassan yana zaune yana karanta jarida,yau dai A'INDO bata tashi ba,wata kawar Halissa ce tun suna yara ,wada kusan a tare sukayi aure da Halissa,saide ita auren ta shekara biyu tayi suka rabu da mijin, dama ba sonsa take ba, auren hadi ne,can dama Alhassan take mugun so,dan har kwana asibiti tayi, saboda ciwon son sa,a yanzu haka da tazo suna yawan waya da Halissa take ce mata itama tazo gida,kuma taji labarin Alhassan shima yazo.shine yau ta d'au wanka cik'in riga da siket na atamfa ja,dinkin yayi mata kyau,dama farida fara ce ,tanada kyanta sosai,kuma diri ma tanada,tayi kyau sosai,salama tayi a falon,da gudu Halissa ta tafo tana murna ta tarbi Farida suka rungume juna,nan suka fara yaushe rabo, Alhassan ya aje jarida yana dan murmushin ganin farida,dan cik'in kawayen Halissa ita yafi sakewa da ita har suna magana ,kawai dai da ta bullo masa da zancan sonsa take yasa ya daina kula ta,anma yanzu da yake tayi aure sai yake ganin ai komai ya huce.

Karasowa sukayi suka zauna ,Farida sai murmushin jin dadin ganin A'LHASSAN take ,yayyin da take kara jin sonsa na linkuwa a zuciyar ta,tace"yaya ina wuni ya bayan rabuwa kuma."

Murmushin sa mai tsada ya sakar mata wanda ya kusan sumar da ita,yace"lafy lau Farida,kun bace kunyi wuyar gani,ya mijin naki kuna lfy ko."

Halissa ce tayi mazan katse ma Al'Hassan hanzari tace"laaa bro yanzu nan kai kallon matar aure kake mata,ai Farida shekara biyu kenan da rabuwar ta da mijin ta,saide in
Kaine zaka maye gurbi😉na yanzun,Halissa ta fada dan daman ta saba tsokanar su.


Rufe fuska Farida tayi wai taji kumya,yayyin da shi kuma Alhassan ya bala ma Halissa harara, wani irin abu A'INDO taji,ya dake ta lokacin da taji ance wai farida da Alhassan.


Kasa controlling din kanta tayi ta tashi tabar gurin rai a matukar bace,wanda duka gurin banda Farida,yayin da Al'Hassan da Halissa suka hada idanu sukayi murmushin,su kam sun gane nufin wanan abun.

Nan Farida sukayita fira,yayyin da A'INDO ta kasa zaman d'akin ta bata d'akin ta bata falon Hajiya duk ta hana kanta sukuni,sai yanma Farida ta shirya komawa gida,daidai shigowar A'INDO,shi Alhassan bai ma yi niyar fita ba,anma ganin A'indo yace"oh bara na kaiki farida ."

Murmushin jin dadi Farida tayi tare da yin fari da idanu dama abinda take so kenan....

Plz zanje nima idan zaka kaita,inason na dan sha ice cream."

Gaba-daya daga Hajiya da ta fito dan suyi salama da Farida,abun yayi bala'in basu mamaki,yanda A'INDO ta tsani Al'Hassan ace wai yau ita da bakin ta take cewar zataje wuri daya da Al'Hassan ,wanda ga dukan alamu ya nuna kishi take ."

Murmushi Alhassan yayi yace"ba damuwa je kisa hijabi sai mu tafi.


Fitowa A'indo tayi,tana jin haushin kanta tare da mamakin kanta,ta ya ma akayi ta kasa controling din kanta,kai anma ta kwafsa,to wai me yasa ma tayi haka ita da ba sonsa take ba,Dan me zataji ba dadi dan yana magana da wata.wayyo Alhassan ko da ya isa d'akin sa wani irin dadi yaji a ransa ,wanda har saida ya taka rawar sojawa .

d'akin,can ya tsaya ya d'auki key ya fito,kusan a tare suka fito shida A'indo ,sai fuska ta kara tamkewa kamar ba ita ba,shi kam dariyar sa yake sha, cik'in Zuciyar sa .


Farida kam tana can ta cika,domin kuwa bata so A'indo tace zata biyo su ba,taso daga ita sai shine ,wata kila yanzu a karo na biyu ya k'arbi soyayar ta dan taga alamu.anma wani irin haushin A'INDO take ji,da tsanar ta,ko wacece ita oho .koda suka dawo falon Hajiya taba farida turaruka,da kayan kwaliya,tayi godiya ta tafi, Halissa taso ta bisu anma Al'Hassan ya bala mata harara shi yasa tayi shiru,tafiya sukayi shi yana gaba,har suka iso motar da zai shiga ya bud'e ya shiga,ganin Alamun Farida zata shiga gidan gaba,da sauri A'INDO ta riga ta tana dan murmushi,kallon A'indo Farida tayi ta kalli Alhassan tace"yaya Al'Hassan wanan wai wacece cewa nake ni zaka kai anma ya naga wanan kamar bata so tana wani shishigi ."


Murmushi Alhassan yayi yace"karki damu farida ki shiga gidan gaba wanan kanwata ce."

"🙄haba Al'Hassan ya haka karka manta fa kusan duk nasan wani naka,kuma wanan bata ma kama da family din ku."

"A'indo zatayi magana dan ranta yayi bala'in bacewa sai Al'Hassan ya riga ta,yace" kinga Farida nine fa nace zan kaiki so meye na wani tambaye tambaye,idan bazaki ba ki fada min nayi ficewa ta."


Ya gama fada ransa a bace,sanin da tayi masa zai iya yin fiye da haka ma dan haka ta hakura ta shiga gidan baya.


Nan ya fara tuki suka fita daga gidan,can sun fara tafiya Farida tace"anm yaya Al'Hassan nace wanan wacece acikin dangin ku,Farida ta fada cik'in siyasa da dariya,baikai gayin magana ba A'INDO tace"kekam kin damu kanki sai kin san ni ko wacece,meye ruwanki ne wai?
Kinga ki fita harka ta na fahimci yar rainin hankali ce ke,bana son shishigi."

Waro idanu Farida tayi tace"ke ni kinsan ko wacece kuwa,ni kike fada ma wanan banzar maganar ."

idanun A'INDO tuni sukayi ja ,ganin shi Al'Hassan baya ma kareta,ko dazu ta fada mata magana anma bai tsawatar mata ba ,da k'arfi tace"ajeni nan,bazan iya tafiya da wanan karyar ba."


A tsorace ya taka burki ganin ran wace yake kauna ya baci yace"haba Aisha me yayi zafi haka kiyi hakuri mana, bud'e k'ofar motar tayi ta fita,wani haushin kanta take ji me ma yasa ta biyo su,gashi yanzu ba abinda zai ja mata bayan raini,ganin da gaske take yasa Alhassan jin zafin Farida ya juyo rai a bace yace"kin gani ko zaki ja min kimin asara ,fitowa yayi daga motar ya bud'e gidan bayan yace"Kinga malama fice ki shiga abun hawa ki tafi gidan ku,dama ni nace zan kaiki yanzu na fasa,kudi ya fido ya jefa mata yace gashinan shiga mota,sa'a kikayi da yanzu bana wulakanta mata saboda wani dalili anma wallahi yau da sai kin raina kanki ,sakaka da baki Farida ta tsaya tana kallon sa cik'e da bakin ciki da takaici,tare dajin muguwar tsanar A'INDO,sanan ta d'auki alwashin sai ta d'au fansar abinda A'INDO tayi mata.ganin ba zata fito ba ya finciko ta tare da watso mata kayan ta.


Ya rufe motar sa tare da janta a tsiyace yabar wurin ya tarar da A'INDO wace take tafiya. bisa hanya,yana isowa daidai wajen ta ya tsayar da motar ko rufe k'ofar baiyi ba ya fito ,"Dan Allah kiyi hakuri,wly banyi haka ba dan wulak'anci ko tozarci,kawai sanin da na miki ne nasan zaki iya gyara ta da bala'in ki ,shi yasa nayi shiru na barki da ita."

"Au dama ka d'auke ni uwar bala'i kenan ."

"Dan Allah kiyi hakuri ba haka nake nufi ba,ina nufin ki mata bala'i,dan Allah ki dawo kamar yanda na d'auke ki na mayar dake."

Ganin yanda ya marairaice yasa ya dan bata tausayi ta juya ba tare da tayi masa magana ba.

Sauke ajiyar zuciya Alhassan yayi,tare da jinjinawa so haka so yake,duba yanda yake rokon ta kamar zai duka mata,tana wulakanta sa anma sam baya ganin laifin ta,saida ta shiga mota da sauri shima yazo ya shiga ya tuka suka fara tafiya,sun fara tafiya tace"zan siye cream glass ."

"To to akoi inda ake saidawa yanada dadi sosai muje na kaiki.",share sa tayi ba tare da ta kuma kulla sa ba,kai kace yar mulki ,suna zuwa wajen suka fito,sukaje inda ake siyarwa,nan yace a basu,ya bada kudi aka basa Glass din kallon sa A'INDO tayi tace"kaga nifa bance ka Siya min ba,me zanyi da abinda ya fito daga hannun ka,juyawa tayi ta fido dubu daya a jakar ta ,ta ba mai saidawa tace a bata.



A wanan karon kam ran Alhassan ya baci, gaba-daya ji yayi kamar yayi kuka ko ya samu saukin abinda yake ji ,me yasa Zuciyar sa ke kaisa inda ake wulakanta sa,shin Allah ma ba ana masa kuskure ba ya yafe,me yasa ita bazata yafe sa ba,ko wanan masifofin da yayita shiga ai ya isa ace zuwa yanzu ta hakura tunda

taga irin masifofin da yayita shiga ta dalilin ta.

Tabas zaije wanjen malami a dinga masa rubutu Allah ya sa masa dangana game da ita,Allah ya raba sa da sonta ko zai huta."


Yanaji yana gani ta siya. gaba-daya tunani ya tafi da hankalin sa,,wanda ya gusar masa da hankali bai ma san ta gama ba,shekeke A'indo ta kalle sa,ganin baida alamun gusawa taja tsuka ta fito waje,keke napep ta tara ta fada masa inda zai kaita ta shiga.


Jin ana fadin "ranka ya dade ga sauran canjin ka,wanan maganar ta dawo dashi daga dogon tunanin da ya shiga,firgigit ya dawo hayacin sa,nan ya fara dube dube da waige waige,yana neman A'INDO anma bai ganta ba,.

Da sauri ya tambayi masu saida S.cream sukace ai ta fita daga nan,da sauri ya fito suna cewa ga canjin sa anma ina ba tasu yake ba.

Fitowa yayi yanata waige waige inda zai ganta anma bai ganta ba ,hankalin sa yayi bala'in tashi dan a tunanin sa ko sace ta akayi,tuni cik'in sa ya kada,nan ya fara duduba gurin da gudu gudu lungu da sako bai ganta ba, nan ya fara tambayar mutane yana nuna pic dinta dake wayar sa,kowa sai yace bai ganta ba,yana ta neman ta aka kira sallah magariba ,gaba-daya ya rikece,wani tunani ya Fado masa ya d'auki waya yayi kiran Hajiya tana d'auka yace "yauwa Mom Aisha ta dawo gida ?"


Hajiya tace"nima kiran da zan maka kenan na tambaye ka me ya tsayar daku har warhaka."

Kashe waya yayi ya aza hannu bisa kai.


itako A'INDO fitarta ta shiga adaidaita, ta fada masa inda zai kaita,wato gida.shigar ta keda wuya ya fara gudu da ita,nan tace" haba malam na fada maka inda zani anma kabi wata hanya sai gudu kake dani.

"Sorry Madam kiyi hakuri,wata tsohuwa ta ce ba lfy shine zan dan bada magani a bata sai na kaiki dan Allah kiyi hakuri da ban fada miki ba."

A'INDO ko jin tsohuwa ce ba lfy yasa ta tausaya ,tace ba komai,abun mamaki suna isowa ba inda suka tsaya sai gani tayi an hangame gat mai adaidaita ya shige da ita,a matukar tsorace take kallon mai Adaidaita ,ji tayi an jawo ta shiko mai Adaidaita ya juya ya fita daga gidan a tsiyace,aka rufe gidan."


Cik'in tsoro A'INDO ta daga kai taga Wanda ya finciko ta a firgice ta ja da k'arfi tayi baya waro idanu tayi a gigice ta nuna mutumin da yatsa tace" dama kaine....."






_Oh Nagode sosai Wanda suka tambayi jiki na da na yarinya ta ,Allah yabar zumunci_🤝🏻🤝🏻
[13/11 à 21:15] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨




*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋




*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚




*DAGA ALKALAMIN MARUBUCIYAR*

👇
*YA MACE KOWACE DA IRIN NI'IMAR TA*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*,
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*





_DEDICATED TO SADJIDA & UMMY ONTOP_




*Page 71-72*




Murmushi Bashir yayi ,tare da kokarin matsowa kusa da ita,da sauri ta kara ja baya tayi tuntunbe da wani dutse ta Fadi a gurin k'afar ta ta fashe.

Anma sam bataji zafin ciwon ba saboda a yanzu ji take wanda ke gabanta yafi zafin ciwon sau dubu.

Dukawa yayi tare da sakin murmushin sa ,yace"welcome baby nayi kewar ki."

Ya fada tare da shafa fuskar ta,runtse idanu A'INDO tayi tare da fadin"karka kara sa wanan banzan hannun naka ya taba min jiki na fada ma mugu."

Gashin kanta ya kama ya jata kiiiiii har saida ya isa da ita k'ofar falo sanan ya sabe ta da k'arfi ya shigo da ita.

Ihu A'INDO take dan neman agaji anma ina ba Hali.

"Bashir kai wani irin mugu ne dan iska,wanda baisan darajar dan Adam ba,kai bunsurun ina ne,to bara kaji na rantse da Allah tun muna shaidar juna ka bani hanya na tafi idan ba haka ba kuma wallahi lahira zatayi bako."


"Hahaha , yarinya kinada abin Dariya,sai ya marairaice fuska kuma yace"haba Aïsha na kira

ki baki d'auka ba nayi miki message bakiyi reply ba, a k'arshe ma kika sa ni a black liss,haba dan Allah Aisha kizo muyi zaman mu,nan Kinga ke ba wani dangi ne dake ba bare a wani damu da bacewar ki,kizo mu zauna na Miki Alkawarin zaman farin ciki a gidan nan kiyi yanda kike so."

Murmushi A'INDO tayi,ta tashi kamar ba ita ba ,tayi dariya tace" Allah ko karka damu anma bara na dan sama mana abinda zamuci yunwa nake ji."

Washe baki yayi yace"Alhamdulillah kin hakura kenan."

"☺me zai hana kuwa Bashir bara dai yanzu na dafa wani abu idan na koshi sai muyi maganar."

Kitchen ta nufa,yayyin da shi kuma yayi wani tsale ya haye saman kujera yana tsalen murna tare da kecewa da dariya yace"ai dole ta so ni kodan kyau na,wly zaman mu zamuyi ba ubanda ya isa ya raba mu.

A'indo ko tana shiga da ma rigar ta doguwa tanada aljihu koda taga yanda mai Adaidaita ya rugo da ita ta d'auki wayar tasa a aljihun rigar ta ,a lokacin da ta shiga kitchen kuka ne ya kusa kufce mata, tayi sauri tayi shiru ta kama bakin ta,sai ta fido wayar daga Aljihu numbers Al'Hassan tasa har mamaki tayi ya akayi ta hadace ta haka.

Kira daya biyu Al'Hassan ya d'auka bayan ya samu gefen titi ya tsaida motar sa dan tunda ya rasa inda A'INDO take yaketa yawon garari Yana neman ta kamar mahaukaci.

Number ta ya gani wace dama yanada ita
Yayi saving dinta,da sauri ya d'auka har bakin sa na rawa wajen magana "hello!

Aisha kina ina kin tada min hankali."

"Yaya Al'Hassan plz kazo ka raba ni da wanan mugun Bashir shine yasa a sato ni gani nan gidan sa ina kitchen plz kazo ka d'auke ni."😭

Idan ran Alhassan yayi yayi dubu to a lokacin ya baci, gaba-daya kansa hayaki ma yake masa, jijiyoyin kansa har tashi suke,Kiran Idrissa yayi bayan idrissa ya d'auka yace"maza ka bani adreshin wanan dan inskan tsohon mijin Aisha."

"Yaya lfy?"

"Kaga nace ka bani ko."
Saurin basa yayi Yana basa ya Kira Hajiya yace"Hajiya maza kije gidan tsohon mijin Aisha dan inaga brother yau Zuciyar sa ta tashi Kar ayi kisan Kai ba alamun lafiya."


"Ya Salam Hajiya tace ta tashi ta hau sama dan d'aukan hijabin ta.
Shi ko Alhassan a dari ya ja motar kamar zai tashi sama,sai gashi a unguwar, k'wank'wasa gidan yayi sai ga Mai gadi ya bud'e ,bindiga ya dungura ma mai gadi ba shiri yayi mazan bashi hanya yana rawar jiki,yana shigowa Mai gadi ya arta a guje yabar gidan.

Shikuwa Al'Hassan da sauri ya karasa falon
Yana zuwa" ya daga murya Aisha kina ina ."

Bashir dake zaune saida gaban sa ya fadi anma ya dake yace " kai Malam lfy zaka shigo min gida ba'a koya maka salama ne ba"

Wani mugun kallon Alhassan ya wurgo Masa Wanda ya kadar da Yan hanjin Bashir,da gudu A'indo ta fito ta nufi Alhassan da gudu ta rungume sa tana kuka.

Tace"kaga wanan mugun ne ya sato ni,kara rungume ta yayi yana shafa kanta alamar rarashi, Bashir ya waro idanu waje yace "dama ke Yar iska ce,shine kika Kira kwarton ki to da yazo me zaiyi wallahi A"indo sai na baki mamaki."

A wani irin k'arfi Al'Hassan ya janye A'indo daga jikin sa ya nufi Bashir baiyi wata wata ba yakai ma bakin sa naushi,ba shiri Bashir ya rike Baki Dan tuni hakorin sa daya ya fita baki ya fara jini,cakumo wuyan sa yayi ya makure Al'Hassan yace"kai dan gidan uban waye ? Wane ganganci yakai ka taba min mata,dan uwarka dama inada haushin ka kyale ka nayi in banda akuyanci ka saki mata sanan ka dinga bibiyar ta,to uwar me zakayi mata ,,Bashir zai kuma magana Al'Hassan ya kuma naushin sa,anan ya makure sa ya fara sakar masa duka tako ina nausan sa yake tun Bashir na iya ramawa har yakai ya kasa,jina-jina da jini Al'Hassan ya Masa,yaji haushi ko gani bayayi aikin dukan sa kawai yake,tuni Bashir ya sume anma Alhassan yaki saurara Masa,A'indo ko kadan bata ji tausayin Bashir ba,illa ma wani so da take ji nasa yana mamaye Zuciyar ta,a yau duk wata kiyaya da take masa ta kawar,ta maye gurbi da so ,Hajiya ce ta shigo gidan ita da idrissa abinda ta iske ne ya tsorata ta,da sauri taje ta ririke Alhassan shima Idrissa haka ya rirke Al'Hassan Hajiya tace"kai wai meye haka?
Kashe dan mutane kake son yi ne Bashir ya debo ruwa ya watsa ma Bashir ya dawo hayacin sa,Hajiya ranta a bace ta tambayi Al'Hassan da har yanzu jikin sa ke rawa gaba-daya baya cik'in hayacin sa,ji yake kamar ya kashe Bashir.

A'INDO ta rugo ta rungume Hajiya tana kuka tace"Hajiya sato ni yasa akayi shine na Kira Yaya Alhassan,dama yana Kira na tare da yi min test akan wai nayi hakuri na dawo gidan sa,ganin ya takura min shine nasa number sa a black liss,shine
Yau yasa aka sato ni lokacin da mukaje wajen siyen ice cream,na fito ina jiran yaya Al'Hassan yasa wani mai Adaidaita ya sato ni ."



Please Login or Register in order to submit comment