Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ma kike baki shirya ba."🙄

"Bashir Alhassan ya ambata a zuciyar sa,tuni Zuciyar sa ta fara kai kawo."

Da sauri khalissa ta tashi tace"just five minutes my sis wallahi na sha'afa ne."
Halissa tace"to nima ku tafi dani man."

Waro idanu A'indo tayi tace"ki rufa mana asiri kina matar aure Zaki bimu,kekam ai saide a kunkume a cik'in gida,😂
Kinga zamuyi reunion ne da samarin ango,kaima surikina baka shirya ba,anma ba matsala ko kaje ko baka je ba ai duk daya ne,tunda abokan kazasuyi abinda muke so dan haka ka ma yi zaman ka."

Dariya idrissa yayi yace"au abin hakane,ba'ama so dama naje,to bara naje wurin amarya ta Nima,ya tashi ,yabar gurin, khalipha ne yace"tab abin yar wariya ce ,hum ya kalli halissa yace"sis taso muje yawo harda shopping kyale wa'inan."
"Yauwa bro muje kawai."suka tafa A'indo tace "to aso diyawa."

"Anki "
. Sukace da ita tare da yi mata gwalo suka fita suma.

Alhassan kam tunda yaji tace da halissa abun na Yan mata da samarin ango ne yaji Zuciyar sa na tafarfasa,wato itama yan matace kenan.😡kuma uban waye Bashir dinnan?

Ganin duk sun watse sai ita dashi yasa ta tashi zata fita ,yace"da ita kema kenan yan Mata ce,ai inaga dake da halissa matsayin ku guda,Dan me ke zakije cik'in kata wai da sunan reunion."😡

Ya fada kansa na hayaki,Idanun sa har sun canza coulor tsabar masifa.

Mamaki ne ya kama A'INDO,zatayi magana kuma ta fasa dan ba amfanin masa magana,ganin ta kama hanya ta fice yaji wani irin bala'in zafi da Zuciyar sa ta masa, ta ya ma za'ayi ta tafi yana mata magana,a haka take son zuwa cik'in wasu kata,tashi yayi da zafin nama ya fito waje da gudu ,ganin ta yayi zatayi part dinsu,da gudu yazo ya sabe ta,bayan ya rufe Mata baki, yayi saurin yin b'angaren sa da ita.

A'INDO na wule-wule tana ihu,bai dire ta ko ina ba sai d'akin sa ,ya rufe,wata irin faduwar gaba A'indo taji,ranta yayi mugu-mugun bacewa,Idanun ta har sun canza,tsabar masifa da bala'in dake cinta, gaba-daya taji ta kara tsanar sa,tsanar da ko makiyin ta bata fatan tayi masa irin ta.


Alhassan yace"bakida hankali ne Ina miki magana zaki wani share ni dan ki raina min hankali,dan iskanci a haka zaki fita,kuma wai wajen samarin ango uban wa kika tambaya,ke ko kumya bakiji ba zaki fita a haka har kina ikirarin kanki a Yan mata,a haka kike son fita maza suyita kalle ki."

Takaici bakin ciki suka yima A'indo tsaye a zuciya,wuka ta hango a bisa tire mai d'auke da lemo,d'auka tayi rai a bace tace"wallahi Allah idan baka bani hanya na huce ba zan caka maka wanan wukar,an fada ma A'indo ta da ce da ko wane sakarai zai nemi wulakanta ta ,to bara kaji idan acan farko kayi kaci bulus wallahi yanzu bazan barka ba,da kake cewa meye ni Yan mata ce,kwarai kuwa ni yan mata ce tunda har yanzu ina tamaka da abinda yan matan ke tamaka,dashi,har ake kiran su da budurwa,banida igiya,ko nauhin wani a kaina,dan haka dole nayi rayuwa ta yanda nake so,sanan Wanda zan aura ma baiyi min wanan takurar ba sai Kai! kai a su wa.?

"Wallahi ka bani waje idan ba haka ba zan caka maka wanan wukar ."

Ke har kike tambaya ta ni a su wa,dan kin raina min hankali ina matsayin mijinki kike kiran wani zai aure ki."😡 gaba-daya cik'in tunzura da bacin rai yake wanan maganar.

"Miji miji,tuf ta tofar da yawu ,tace "Allah ya kiyaye,ai wallahi da ace har yanzu ina matsayin matarka tabas da ko saide na kashe kaina,dan da in zauna dakai gwara zama da bakin kumurci ina umartar ka da ka bani wuri na huce,dan wallahi idan ka nace zan caka maka wanan wukar.",ko gezo baiyi ba,ya tsaya cak gurin kamar an dasa sa,ji yake ga daya duniya bai tabajin ciwon abu ba, da zafin abu kamar yanda tayi masa wanan maganar wai gwara ta zauna da bakin kumurci da zama dashi,aiko yau zaiga k'arshen kiyayar da take masa,dan bazai gusa a gun ba sai ya tsaya yaga zata caka ko kuwa,a matukar haukace A'indo tayi saiti da wukar ,dan ta d'aukan ma kanta matsawar bai gusa ba wallahi sai ta caka masa ita.......





Aci gaba da gashi🍇
Maimou love😘
[22/10 à 21:02] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨




*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋




*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚




*DAGA AKALAMIN MARUBUCIYAR*

👇
*YA MACE KOWACE DA IRIN NI'IMAR TA*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*,
_and Now_👇
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*





_DEDICATED TO SADJIDA & UMMY ONTOP_



*Assalamu Aleykum,zanyi kira ga wasu marubuta,wa'inda kuma yawanci sababin marubuta ne ke irin hakan,a gaskiya bana jin dadin abinda kuke yi min,ace kaf online kunfi d'aukar min sunan book, duk idan zan rubuta sunan book to sai na zauna nayi nazari nayi bincik'e naga idan ba'a taba irin sunan ba sai na rubuta,ban taba d'aukar sunan book din wata marubuciya ba ko daya ba a Online na rubuta,wallahi duk sunan book din da zan sa babu taimakon kowa ni ke aje hankali na kirkiro sunan book dina,anma abun mamaki shine da farko an d'aukan min sunan book dina Mai sunan *(MAKIRCIN, )anyi sa.nayi shiru banyi magana ba,aka kuma d'aukan sunan book dina (YAN MATAN ZAMANI,)shima nayi shiru,aka kuma d'aukan (HASSADA GA MAI RABO),shi nayi ma marubuciyar magana kuma ta fahimce ni,an d'auki Ina (MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN),shima nayi shiru,kwanan nan daga fara tala book zan fito dashi wata ta gani ,a lokacin ta fara rubuta sa,nayi hakuri,kwatsam yau kuma sai naga an kuma d'aukan saunan book dina mai taken (KAICONA),shi nayi magana anma tace bazata iya canzawa ba,to a gaskiya a wanan karon bazan iya hakuri ba,ya kamata ace wasu marubutan su dinga tunani da lissafi kafin su fara abu, bai kamata ba ace ana rubuta sunayen book sama da uku ba,kuma duka sunaye iri daya,hakan zai sa mu ruda kan Makaranta,ina mai bada shawara ga masu irin wanan abu,idan zaku rubuta litafi kuyi bincik'e da kyau ku tabatar ba mai irin sunan litafin sai kuci gaba,anma ba wai ku d'auki sunan litafin wani ba,gaskiya hakan baiyi ba, idan akaci gaba da haka kunga zan d'auki sunan book din wada ta d'auki nawa Nima na rubuta book din da irin sunan book din da takeyi akafi sanin ta dashi na kunga hakan ba dadi ,dan haka dan Allah mu gyara tun kafin mukai ga haka.*🙏





*PAGE 51-52*




Murmushi yayi wanda yafi kuka ciwo,alhakikanin gaskiya wani irin tararin bala'in sonta yakeji ,wanda shi kansa abin tsoro ya fara basa,bai taba son wata mace ba haka,sanan baisan lokacin da son ya shige sa ba,tafin hannun sa yasa zai janyo ta ,itako idanu a rufe ta yarfar da hanunsa,a inda tsotsayi yaja ta yanka tafin hannun nasa,take jini ya fara zuba, bud'e idanu tayi jin yayi yar karamar kara,jini taga yana zuba a hanun sa,duk da bataji dadiba a k'asan zuciyar ta,saboda har ga Allah bataji dadin abinda tayi ba,saboda ita ba irin sa bace,d'aurewa tayi ta dake,tare da cin fuska ,tace"Wallahi kadan ka gani ma ,idan ka kara gangancin koda taba hannuna ne to wallahi abinda zan maka sai ka kwanmace baka doron duniyar nan."

Mamaki ne fal a idanun sa,kwayar idanun ta ya duba yaga kiyayyar sa fal a idanun ta,gashi har zata iya fido masa da jini,ganin yayi sanyi yasa A'indo yin tsaki tare da buge sa ta bud'e k'ofa tabar wurin.

Doctor ya kira yazo ya duba masa hannun ,akayi bandeji tare da basa maganunnuka,tunda A'indo tasa kai ta fita,hankalin sa ya kara tashi,sam duk zugin da hannun sa ke masa bayaji,domin kuwa a cewar sa baikai zugin da zuciyar sa ke masa ba.

Tunani yake ,yanzu wai cik'in maza zataje ta shiga suyi cudanya dasu,kuma ma wai namiji ne zai kaisu wanda yake tunanin saurayin ta ne,😳waro idanu yayi da ya tuna maganar ta ,ta dazu wai ko mijin da zata aura,to waye wanan kuma?

Gaban sa ke bala'in faduwa,ji yake kamar ya kwala ihu a hankali yake jin kansa na sara masa,tsabar kishin bala'i maganin barci ya balla yasha.

Anma abun mamaki barci yaki d'aukan sa,hanun da akayi ma bandeji ya jimke waje daya,nan take jini ya kuma balewa,anma ina ko ta hannun baibi ba,wani iri yake ji,idrissa ne ya shigo yanata salama yaji kamar ana nishi, sama-sama dan haka da sauri ya karasa d'akin, Al'Hassan ya iske a tsaye,idanu sunyi masa jawur,yayyin da hannun sa ke tsiyayar jini.

"Ya Salam bro meye haka me ya sameka?
Da sauri Alhassan ya karaso ya rike hannun sa yana dubawa,saurin komawa yayi ya d'auko kayan aikin sa yayi dressing din gurin,sanan ya kara nada masa wani bandejin,dago kai yayi zaiyima Al'Hassan magana,kawai sai yaga har barci ya d'auki yayan nasa,gyara masa kwanciya yayi tare da barin d'akin,yana mamakin abinda ya samu dan uwan sa
.


A'indo ko fita sukayi,Bashir ya kaisu,akayi reunion,tsakanin yan matan amarya da samarin ango,duk da Bashir ya hana A'INDO fita daga motar.

Suna zaune a mota suna fira Bashir yace "baby nifa so nake daga an gama auren sisin mu nima na turo,kuma gaskiya bana son asa dogon lokaci wata daya nake son asa ,dan gaskiya bikin bazai d'auki lokaci ba."

Murmushi A'indo tayi tace"ka ganka ko,to naji kai baka ma barin nan da ko shekara ne."
"Kiyi hakuri baby zancan hakuri bai taso ba,naji ance tsohon mijin ki ya dawo,ni kuma a kowace rana cik'in zulumi nake kar ku koma tare,shi yasa nafi son ayi komai a gama."
Nan take annurin fuskar A'INDO ya d'auke ,ranta ya baci,zuciyar ta tayi zafi a k'ankance ta kalli Bashir tace"bash kasan tunda nake dakai baka taba bata min rai irin na yau ba?
Wallahi ka batan rai ,ta ya ma kake tunanin zan koma gidan sa ,Allah ya kiyaye,dan Allah kabar wanan maganar."

Ganin da yayi ranta ya baci yaji shima baiji dadin abun ba,kallonta yayi yace"plz my princess kiyi hakuri,wallahi kishi ne yasa nayi wanan maganar kiyi hakuri bazan kuma ba na miki Alkawari."

"Is ok karka damu,zaka iya turowa da zaran anyi auren Yar uwata."..

Murmushi yayi yace"nagode sosai my princess.

Al'Hassan bai tashi ba sai bayan sallah la'asar,anma kuma koda ya tashi ya tambaya yaji su A'indo sun dawo aka tabatar masa da sun dawo sanan hankalin sa ya kwanta.


Duk wani shirye-shirye anyi,yayin da dangi sukayita zuwa wanan sabga Mina matar A'lhassan kuwa ana saura sati daya tazo biki,da saura sati daya amarya ta shiga lale,

Su A'indo ansha gyara,kamar amarya,domin ta fada ma Hajiya da zaran an gama bikin Husseina Bashir zai turo kuma baza'a a d'auki dogon lokaci ba a cewar sa,Hajiya tace "Masha Allah muma abinda muke jira kenan ,a shirye muke,dan haka tasa har A'indo ayi mata gyaran amare waw idan kunga kyan da A'indo ta Kara ba'a magana,da misalin k'arfe biyar aka fara fulani day,a inda kowa ya halarci gurin,akayi decoration din gurin abin gwanin sha'awa,kowa yayi shirin fulani,hata abokan ango wasu sunzo,yayyin da Alhassan ke rabewa waje daya inda yasan A'indo na bi yana kallon ta,a yanzu bayada aiki daga kallon photon ta a waya sai tunanin ta,yau ma kamar kullum yana daga lungun sa,ya hango suna rawa, Zuciyar sa yake jin tana masa zafi ganin gaban maza ne suke wanan abun,kowa na kallon ta.zai tashi kenan sai ga Mina da yar iskar shigar ta,zaro idanu Alhassan yayi 😳a matukar tsorace yace"ke wai kinada hankali kuwa?
A gidan surukan ki kika fito haka daga ke sai wondo,Wai Mina yaushe zakiyi hankali."

Tsaki Mina tayi tace"kaga Malam wallahi bazan iya ba,dama ka gayatoni nan ne dan ka wulakanta ni,to bara kaji yanda nake shiga ta acan haka zanyita anan ba Wanda ya isa ya hanani,haba dan Allah meye haka, mtsss."

Da sauri tabar wajen zataje wajen wasan da akeyi,har taci rabin tafiya,domin ta kusa kawo gunsu,da gudu Alhassan ya taso yazo ya taro ta,baiyi wata-wata ba ya kwashe ta da mari,bata tsaya tunani ba itama ta kwashe sa da mari a daidai idanun hajiya da A'indo da Hajiya ta fito kiran ta dan ta raraba abinci ......




Kuyi hakuri da wanan oga ya dawo ,banida lokacin baku yanda kuke so
🥰😍😘
[24/10 à 21:29] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨




*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋




*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚




*DAGA AKALAMIN MARUBUCIYAR*

👇
*YA MACE KOWACE DA IRIN NI'IMAR TA*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*,
_and Now_👇
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*





_DEDICATED TO My Kawa Mrs Adam (yar Mutan kagara),&My dota Aisha A Bagudo_




*Page 53-54*




Zaro idanu hajiya tayi,yayyin da A'INDO kuma tayi shu'umin murmushi,daga hannun zaiyi ya kara dukan ta, Hajiya tace"kul ,a koda yaushe kuskuren da kakeyi kenan,kadan ka gani ,wanan kadai ya isheka ishara,ace mace ta d'auki hannu ta doki mijin ta,ai kuwa ba sauran daraja ,mutane kowa hankalin sa yayi gurin, gaba-daya mamaki ake,soja kamar sa mace ta mare sa tab .



Kallon Mina Hajiya tayi tace"ki koma ciki wanan ba darajar ya mace bace,kina matsayin Matar aure duba yanda kika fito."

Murguda baki Mina tayi ,sanan tace"nifa an takura ma rayuwa ta,dan jaraba irin taka saida nace bazan zo ba ka matsa min,gashi nazo kai kana cimin mutunci, mahaifiyar ka ma haka,ni bazan ."
"Kul karki fara karki yarda ki sa min uwa idan kina iskancinki kiyi sa can shida yake dai-dai ke,anma kika yarda kika sa Hajiya a wanan banzan shirmen naki wallahi sai kin gane kuskuren ki."

A'indo ce ke wanan maganar lokacin da take kokarin karsowa kusa da Mina kamar zata duke ta,


Alhassan kam kasa magana yayi tsabar takaici da kuma kumya da yaji,tabas a yau ya Kara dana sanin auren Mina,a yau ya tabatar da Alhakin iyayen sa ke bibiyar sa da kuma na A'indo,domin kuwa da yabi maganar su da yau baiga wanan bakar ranar ba,ya Salam wasu hawaye ne masu zafi suka zubo a kumatun sa ,ita kanta hajiya saida abun ya dan taba ta,domin kuwa wahala bata taba sa danta kuka ba,anma ai shi ya jama kansa,ji tayi gaba-daya A'indo ta kara shiga ranta,sanan yau ta Kara jin dadi da ta kirata da mahaifiya,tabas tasan Alhassan yayi sake,sanan yayi asarar da bazai taba maida makamancin ta ba.


Murmushi Hajiya tayi tace"barta Aisha,ai wanda yasan darajar iyaye shi ke girmama su,karki damu haihuwa ta ja min,dama ance dan kuka mai jama uwar sa jifa......
"Zo muje,kai kuma idan har kana iya d'aukan magana ta karka taba ta,karka duke ta,domin duk namiji mai dukan matar sa ba namiji bane."


Jan A'indo tayi suka bar gurin,itako Mina tsaki tayi tabar gurin.

Shi kam Alhassan tsaye yayi hawayen bakin ciki na zuba a idanun sa,dole ya roki daddyn sa ya taimaka ya barsa ya saki Mina ,idan ba haka ba wallahi kashe sa zatayi da bakin cikin ta....


Da bala'in sauri yabar gurin yayi b'angaren Mahaifin sa,acan ya iske mahaifiyar sa,koda ta gansa tayi kokarin barin wajen Alhassan yayi mazan rike k'afafun ta,Idanun sa na hawaye ya aza kai saman k'afafun ta yana kuka tare da neman yafiyar ta,tare da rokon ta akan ta zauna ta sausauta masa,jikin Hajiya yayi sanyi sosai,domin kuwa bata taba ganin danta Yana kuka ba,domin tunda yakai dan shekara goma Babu abinda kesa shi kuka,ko dukan sa akayi jurewa yake baya
Kuka,saide taurin rai,anma yau gashi yana kuka , Alhaji ta kalla dake zaune ya daga mata kai alamun ta zauna,zaunawa tayi, Alhassan da idanu sukayi masa jawur,ya kamo hannun Hajiya da na Alhaji,ya daga Kai ya kalle su,yace"dan girman Allah ku yafe min Hakika ku iyaye na gari ne ,duk da na bata muku,naki bin umarnin ku,baku taba nuna fishi a gareni ba,tabas na muku butulci,naki abinda kuka so,ada can bansan cewar gata kukayi min ba sai a yanzu na gane kurena,nayi watsi da zabin ku na rike zabi na ,gashi yanzu ina girbar abinda na shuka,abinda ko namiji dan uwana bai taba mari na ba,anma yau mace kuma matata ta mareni a bainar jama'a wane kask'anci ya huce wanan,tabas bayi ganganci,kuyi hakuri ku dubi girman Allah ku yafe min ."


Hajiya ma share hawaye tayi,"tace hakika Alhassan kuskure kam kayi,saide ka nemi yafiya agun wace kayima laifin,mu mun jima da yafe maka,domin da bamu yafe maka ba da wallahi bazaka ga da kyau ba,tsakanin mata da miji a cik'in su duk Wanda ya zalinci daya tofa Allah sai ya saka ma wanda aka zalunta,ka wulakanta yarinyar nan ,kaso yin ajalin ta,Allah ne yayi akoi sauran shan ruwan ta a duniya ,ka zalinci yarinyar nan,anma ba komai kaje ni na yafe maka."

Daddy ma cewa yayi"hakane kam Son ka bata mana sosai anma ba komai kaje nima na yafe maka,kaje ka nemi yafiyar tsohuwar Matar ka.

"Nagode Nagode ya ku iyaye na gari,sai inason daddy ku taimaka ku kuma aura min tshohuwar matata dan Allah daddy Wallahi Allah a yanzu babu Matar da nake so sama da ita,dan Allah ku taimaka ku shawo min kanta,ta kuma bani dama ta biyu ,sanan daddy ku amince na saki Mina domin bazan iya zama da ita ba."

"Hum Soja na kenan ,ai ka makaro,domin kuwa A'INDO yanzu baza mu taba tarbon ta ba da wanan maganar,dan a yanzu haka ta kuma zama ta wani,bayan bikin yar uwarta zamusa auren ta itama.ni da kake gani wallahi ni na haife ka anma a yanzu nafi son A'indo sama dakai ,domin ita din marainiya ce gaba da baya ,iyayen ta sun rasu shekaru biyu da suka huce,nice uwar su,kuma wallahi bari kaji ko ni bazan ba A'indo shawarar ta koma gidan ka ba,domin kuwa ba dan Allah kake son ta ba,a Koda yaushe zaka iya kuma rabuwa da ita,idan so na Allah kake mata tun acan da bata zama mutum ba ya kamata ka nuna hakan anma ba yanzu da ta zama mutum ba.ada can ma ita tabi umarnin mu duk da bamu haife ta ba ta aure ka,kai da muka Haifa ma kaki bin Umarnin mu,dan haka ni shawarar da zan baka kaje kayi hakuri da matar ka,ka dinga mata Nasiha
Wata killa ta shiryu,anma zancan rabuwa bamu amince maka ba.

Kallon daddy yayi a matukar razane,da gigita,ba komai kuma ya sashi a wanan halin illa jin da yayi cewar yayi hakuri yanzu kam A'INDO ta wani ce,wanan abun yasa ganinsa da jinsa na neman d'aukewa,biyu biyu ya fara ganin su,
Tun yana gane abinda suke cewa har ya daina jin komai,sai gani sukayi ya fadi a gurin ba alamun numfashi.

A matukar razana da rikicewa hajiya tayi kansa,ta kama sa ta fara girgiza sa,tana fadin" Alhassan dan Allah ka tashi ,ka taimaka,meye haka,Alhaji baya numfashi fa,shima Alhaji a rude da ganin halin da dansa ya shiga ya d'auki waya ya Kira idrissa ,ko minti goma ba'ayi ba sai ga idrissa da kayan aiki,nan ya fara duba sa,ya gano matsalar,jinin sa ne ya fara hawa,sanan kuma yanzu wanan hali da ya shiga Zuciyar sa ce ta buga ,jin abinda baiyi zato ba,ko kuma zuciyar sa bazata iya d'aukan abinda taji ba ruwa ya hada,ya sa masa.ya samu numfashin sa ya daidaita anma bai farfado ba.


Hajiya tayi tagumi shima Alhaji hankalin sa ya tashi kawai dan yana namiji ne yasa yafi hajiya dauriya.



Idrissa ya dubi daddyn nasa yace Daddy wai meye aka fada masa da ya sashi a wanan mumunan halin?."


"Gaskiya ce kawai muka fada masa"

Cewar Hajiya,domin bazata so yaran ta suji wai saboda A'INDO ya fada wanan halin ba,dan zasu iya fara jin haushin Yar ta itakam abinda bazata iya jurewa bane,bazata so ba ace daya daga cik'in yaran ta basu samun jituwa ,dan haka tace"so ne yake ya saki Matar sa,shine mu kuma muka ki amincewa."

Cewar Hajiya,duk da tasan ba shine musababin fadawar sa cikin wanan halin ba.


"Gaskiya Mom dad ku barsa yayi abinda yake son yi mana, haba wanan ai ba Mata bace,ku duba fa a matsayin ta na matar aure shigar da take yi,sanan ko kadan bata mutunta brother,gaskiya nima ina bayan sa,Mom kawai ku barsa yayi abinda yake so."


"Wanan kuskuren shi ya tafka a farko wanan kam bazan yarda ba,domin kuwa shi namiji idan ya saba da saki kullum hakan zata dinga Faruwa,dan haka zabin sa ne yayi hakuri ya zauna da ita."


Hajiya na gama fadar haka tabar d'akin.


Idrissa ya kalli Mahaifin sa alamun ya tausaya, murmushi Mahaifin yayi yace"idrissa kasan ban taba juyama mahaifiyar ka baya bisa kan gaskiyar ta ba,sanin kanka ne cewar abinda take so shi nake so,domin kuwa duk abinda zatayi da gaskiya take yinsa,dan haka abinda tace nima shi zance ban amince ba da abinda Alhassan ke so ya aikata ba."


A'indo ko yinin ranar cik'in nishadi da farin ciki ta shiga,ganin cewar yau an mari Alhassan ,me yafi wanan dadi a wajen ta.

Yau gaba-daya cik'in nishadi take."


bayan an gama fulani day da misalin k'arfe goma na dare su A'indo suna zaune suna tsara yanda za'a tsara Arabian day gobe , Salma daya daga cik'in kawayen su tace"a'a yau ko kunga abinda na gani kuwa?
Hum wai wanan sojan yayan ango wata ta mare sa,nace tooo duk fuskar sa,da miskilanci ace mace ta maresa."

Mimi tace "hum ai ance Matar sa ce ta maresa."
Salma tace" kai haba dan Allah ,gaskiya batada tarbiya batada mutunci,ace mace da ita ta daga hannu ta mari mijin ta."

"Hum shi mijin ai baku san halin sa ba,baku san abinda yake ba kawai a dai yi sha'ani." Cewar A'indo,da gaba-daya ranta ya fara baci da taji ana maganar makiyin ta.

"Nikam A'indo naga baki son ana maganar sa,ranar ma nace miki nifa ya min,anma naga kin bata rai,kince Kar na kara miki wanan zancan yadai🤔cewar Salma."


"Mtsss dako kinyi zabon tumun dare,domin kuwa wanan Zuciyar sa baka ce ko kadan bayada imani, kamar fir'auna yake, sanan ga wulakanta dan Adam kai wanan yanada mugun hali wly ni dan Allah abar wanan zancan nasa mu kwanta zaifi saboda kunsan gobe munada aiki.."

Shiru sukayi suka kwanta,yayyin da A'indo take ta juye juye,tunanin marin da Mina tayima Alhassan

Please Login or Register in order to submit comment