Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta fara shiga gidan,A'indo Kam ta manta da su wa sukazo taja yar uwarta suka shiga gida,aiko tana zuwa da gudu ta auka d'akin mahaifiyar ta kulu,itama ta fito ta rungume yarta, cik'e da farin ciki,Anty ce ta shigo ta shaida Mata da baki suke tare,maraba tayi musu cik'e da farin ciki,Ado ya fito shima yayi farin cikin ganin Yar sa,aiko Anty ta fada musu da maza suke tare,uwayen gidan A'indo ne.

"To to keko kin barsu a waje Safiya,tashi shigo dasu Bari na samo tabarma mu mu zauna a zaure.

Husseina ce taja A'indo gefe tace "ke A'indo wai su waye kuka zo dasu,harda wani na gani mai irin cik'in Mai gari,shima ya kusa haihuwa ko?
Allah dai yasa ba irin cik'in Mai gari bane dan kinga har yanzu bai haihu ba."

"Tab A'indo tace kinga wanan fa har gudu yake har bai tsoron ma cik'in ya zube."

Husseina tace "tab to ai da zai bari mu taba da mun taba."

Wai kus kus kus din me kuke ma mutane,maza ku tashi ku shiga d'aki kun wani tsaya manya na zaune kuna gindin su cewar kulu ta katse musu zance."
Dan tuni Hajiya ta shigo Suma su Alhaji suna zaure.
Hajiya dai kalon su A'indo take gwanin sha'awa sai suka tuna mata yan biyun ta su Alhassan lokacin da ta haife su da abokiyar tagwaitakar sa,kama suke sosai ,haka su A'INDO suka shiga d'aki sunata kus kus din su.hajiya sun gaisa da kulu nan Anty ta gabatar mata da Hajiya tare da nufin su,acan zaure ma Abokin Alhaji ne suke magana da Ado mai saida kifi,ya yaba da kamalar mutanen ,sanan yace tunda harka ta aure ce bari ya Kira mai gari,bayan an Kira Mai gari shiko ya shiga cikin gida tare da kiran Anty da kuma matar sa ,sai kuma A'indo a d'aki,nan Husseina ta fito ta zauna kusa da Hajiya tayi tagumi tana kalon Hajiya ,bayan Kulu sun shiga d'aki Ado ya tatara nutsuwar sa zuwa ga Anty yace"Safiya mu bamu san mutanan nan ba ke Kika san su ki fada mana tsakani da Allah mutanen kirki ne ,me yasa suka tsalake birni suka zo kauye dan neman auren ya ta,wanda kowa yasan halin A'indo,batada nutsuwa."


"Yaya wly wa'inan mutanan ko a birni ansan irin mutuncin su da kuma son talakawan su,ko a birni da kaga yanda A'indo take musu tabara Kai kace Yar su,basu taba nuna kyamar su ba gareta,saima sanyata a jiki da sukayi,suna son dansu ya daina kyamar talaka da kuma yan kauye shi yasa sukace A'indo itace daidai shi,shi yasa yake son ya masa aure ,anma wly yaya basuda matsala."


"To shikenan,ke kulu ya Kika gani."

Nima na yaba da hankalin Matar,kuma ko baya ga haka kaga yaran nan yanda sukayi bakin jini a kauyen nan wata kila dama can haka Allah ya kadarta,dan haka kawai ni a gani na ayi auren ,Allah sanya Alherie."


"A'indo ado ya Kira ta."

"Iye babana!!!😁 A'indo ta fada da k'arfi,girgiza kai yayi yace" kina son wanda akace za'a hadaku aure?

"Hahhh kaji babana da wani zance,ka gansa kuwa,Allah ko maman mu ta gansa sai tace bata son ka shi take so🙄."


Kulu ce ta rank'washe ta a kai tace"ke wai dan ubanki yaushe zaki nutsu ne.?

"Yau"

A'indo ta bata amsa,shiko ado girgiza kai yayi yace"kina son shi."?

Marmadi da idanu A'indo tayi tace"casss ma kuwa Ina son sa😁."

To Alhamdulillah ku tashi kuje wurin hajiyar ni bari na fita waje,Yana fita kuma Yan uwan sa sun zo wanda ya aika su zo,kowa yayi na'am da wanan auren,dan matsawar yaran suka zauna kauyen Nan to komin kyansu baza'a aure su ba,hakan yasa ma auren A'indo mutane dayawa sun amince,sudai fadan su a rage wanan irin,inda mutane wasu suna gulmar cewa wai Ado yaga kudi ya Saida yar sa,wasu kuma suce ai yan mafiya ne,yan yanka Kai wa zai fito daga birni yazo kauye neman aure,haka dai akayita Yan dumumuwa.

Su Alhaji dama tafe suke da komai nasu goro halawa dabino,a k'ofar gida mutane diyawa sun taru Kai kace an jima da fadin aure ,k'ofa ta cika tambal,su Alhaji basu wani nuna kudi ba ,dubu hamsin aka bada a matsayin sadaki abokin Daddy ya bada dubu hamsin kudin sadaki,anan take aka shaida d'aura auren Alhassan,da Hassana,wato A'indo.


Anyi farin ciki Nan maroki ya shaida,da gudu A'indo ta fito tsakar gida,nan fa ta fara rawa,tana girgizawa,tare da fadin an d'aura,an d'aura."💃💃💃💃,


Mutanen da suke gidan kowa ya Kama haba ana kalon A'indo,itama Husseina fitowa tayi ta fara rawar nan fa suka fara rawa,suna fadin "an d'aura 'an d'aura."



rawa suke suna girgiza Anty ce tazo ta jasu,tayi d'aki dasu,Hajiya ta rike hanun kuluwa tace "nasan zaki so wanke yar ki da kanki dan haka zamu barta anan jibi zamu zo sai mu tafi da ita,gashi wanan dubu dari biyu ne ,a Mata gyaran da ya kamata,yanzu suna jira na jibi sai muzo mu d'auke ta,kuma mun gode da wanan ya da kuka bamu,insha Allah nayi Alkawarin rike ta tsakani da Allah tamkar ya ta cikina,sanan Dan Allah Kar kuyi mata komai,domin mu Yar mu kawai za'a bamu akoi komai acan na kayan d'aki."
Murmushi kuluwa tayi tace"nagode,ai mune da godiya kuda baku kyamace mu ba kuka hada zuri'a damu,,to hajiya gatanan A'indo sai Addou'a anyi hakuri da ita domin ba Kaine da ita ba,Hajiya tayi dariya tace"karki damu zata daina kuruciya ce.

Salama sukayi suka tafi ko samun ganin A'indon basuyi ba,Anty ma zama tayi tace"idan za'a Kai A'indo sun tafi tare .


Bayan su hajiya sun tafi su A'indo suka fito a guje zasu bar gidan kulu ta tare su tare da jawo su tace"wai ku kunada hankali kuwa?
Ke A'indo yau fa aka d'aura auren ki gidan uban wa zaki.?

Turo baki Husseina tayi ta jawo hanun A'indo sukayo d'aki,suka zauna Husseina tace"Kai maman mu akoi masifa."

A'indo tace "bakiji sunan ta ba kuluwa mai bakin masifa fa."

Dariya suka kece da ita Husseina tace"yauwa bani labarin birni da mijin ki."

Dariya A'INDO tayi tare da rufe fuska wai taji kumya nan suka fara zancan su .


Bayan kwana biyu duk wani gyara na amarya irin na kauye anyimata harda lale an sata,shima kuma Alhassan an sa Masa lale irin na ko wane ango,duk da tambayoyi ke garesa cik'e a zuciya anma Bai samu fuska tamya ba. A'indo Masha Allah ta kara kyau,da safe sai ga Su Hajiya sunzo d'aukan amarya,aiko husseina tace ina bata yarda ba da ita za'a tafi,kuka harda birgima,ta kalli ubanta tace "baban mu Kai ka min Alkawarin duk ranar da A'INDO tazo zamu tafi tare,nan Hajiya tace "in ba damuwa su tafi tare da Yar uwarta,Ado yace ba matsala Husseina taje ta d'auko kayan ta su tafi.

Aiko da gudu ta tafi harda tsale,kowa na dariya,ashe dama Husseina ta tatara kayan ta,kowa dariya ake mata,kulu har kwala saida ta zubar,haka A'indo ma a ranar tayi sanyi,itama tayi kuka,Husseina kawai ke dariyar ta,nan aka shiga mota suka tafi,bayan A'indo Tasha fada,da Nasiha ta mahaifan ta.


Tun a mota A'indo ta watsake suka fara shirmen su ita da yar uwarta .

Aiko suna zuwa gida A'indo ta fito da gudu tana kwala ma Rabi'u daudu Kira."

Cewa take "kawa kina ina zo kiga yar uwata."

Wai Rabi'u ne take kira kawa.

Rabi'u a kitchen yaji ana kwala Masa Kira ya kuma san A'indo ce,sanin cewar Alhassan baya gari ya tafi Niamey wajen wani meeting ,dan haka ya fito da gudu,irin na mata yana kada kugu,yace"a'a A'INDO tazo ,yana karasowa yaja burki yayi turus,ganin A'INDO ta zamar masa biyu,yace"na Shiga uku🙆‍♂na lalace ,mai zan gani,A'indo ta zama biyu........




Guys yanzu aka fara fa dan sai ku tanadi dariyar ku yanzu za'a fara wasan🍇🥰📚
[10/10 à 17:28] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨




*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋




*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚




*DAGA AKALAMIN MARUBUCIYAR*

👇
*YA MACE KOWACE DA IRIN NI'IMAR TA*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*,
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*





_DEDICATED TO SADJIDA & UMMY ONTOP_





_wayyo cikina 🤣Kai fans ina son ku ,ashe haka kuke son A'indo tab,gaskiya ina jin dadin comment din ku ,yana sani nishadi,tare da kara min k'arfin gwiwa shi yasa nake son nima na dinga faranta muku,dan haka kowace ta shirya A'indo tace zatazo gidan ta mata shara da guga,ta gyara muku falo tasss,har sai yayi walkiya🤪_




*PAGE 19-20*





""""""" Hajiya!
Hajiya! Hajiya! Kina Ina kizo kiga ta'asar da aka miki."
Cewar Rabi'u daudu da yake kwala ma hajiya Kira,Hajiya har ta fara barci ,cikin barci taji kamar ana kiran ta,salati tayi da taji itace din ake kira, tace"la'illaha kai jama'a kaida gidan ka anma bakada damar kwantawa ka huta,kulum cik'in fargaba,to Allah sa dai ba wani abun akayi ba,nikam na d'auko ruwan dafa kaina,ni ya'yan nawa suna wata duniyar wajen karatu na d'auko wasu su ba yara ba anma kulum cik'in firgici nake,bari naje wanan karon kuma mai sukayi."

Tasowa Hajiya tayi,,tun a sama ta fara cin karo da abinda su A'indo sukayi,gasu sunyi cirko cirko da idanu,suna raraba idanu Kai kace sunyi sata,an kama su.


"Innalillahi wa'ina illaihi Raju'un , A'INDO Mai zan gani,yau ta'asar da kukayi kenan,Saida nace ku bar wanan abun kikace a'a yanzu wane abun ne kukayi haka,yanzu saboda Allah ta'asar da kuka yimin kenan,uban wa yace muku haka ake guga ,aiko yau duk abinda kuke ji sai an d'aure min ku,naga alamar kuna bukatar a taba lfy jikin ku, Rabi'u maza fita,Kira min body gard na gidan nan a d'aure min su."


ai jin haka su A'indo a tsorace ita da Husseina sukace kafa me naci ban baki ba,da rarafe suka fita,shiko Rabi'u Jin da yayi keta za'ayi sam ya manta da yanda gurin yake ,riga ya rike a hannu ya fara kokarin fita da gudu dan ya kira wa'inda akace aiko sai ji kake yayi sama sama ya fado kasa tim,"wayyo Allah na mutu na lalace ni Rabi'a,Hajiya wanan yara sun nakasa ni, ya ya zanyi,wayyo😖Wayyo Hajiya ki kawo agaji ,tsaki Hajiya ta buga,dan yau ranta yayi matukar baci,a hankali ta fara takawa har ta fita daga falon, tsinkayo Su A'indo tayi suna gudu,aiko nan tace a kama mata su,anma ina sai anje kama su sai su zile wani kato ne ya fara taga taga da Husseina ya tare mata hanya,in tayi gusum yayi gusum in tayi arewa yayi arewa,da taga yazo gap zai kama ta ,sai ta duba k'afafun sa taga a ware suke ,dukawa tayi da gudu tabi da tsakakanin k'afafun sa,a rashin sani kanta ya bugi wajen bananar sa ta huce,ji kake Kato ya bada tim ya fadi,ya rike kasan wondon sa yana birgima, A'INDO dama sunkai k'ofa gida,lekowa tayi da k'arfi tace"hajiya mun tafi yawo sai mun dawo."

kama hannun juna sukayi da gudu suka bar unguwar,tafiya suke sosai har suka kai dai-dai kan titi,inda motoci ke ficewa sosai."

Waro idanu Husseina tayi tace"A'indo kinsan aradun Allah bazan huce wanan gurin ba , kinaga,masu kafa hudu na ficewa zan bi tanan tab,aikuwa bada ni ba😏.

Wani mai agwalima A'indo ta tsinkayo can tsalaken titi,takai duban ta ga Husseina tace"la Kinga mai agwalima can muje mu saya."

"ba fa zanje ba A'indo🙄"
Cewar Husseina ,A'indo tace"ke dan Allah fice muje tsoron me kike ji,bakauya kawai,kizo muje ni naji da komai🤨."

riko hannun Husseina tayi sai sunzo daidai bakin tsakar titi sai su tsinkayo mota maimakin su huce a'a sai su dawo baya da gudu,sunyi haka kusan sau hudu, Husseina tace" wly A'indo bazanje ba ni na gaji ke kije mana ."

"anji din uwar tsoro😏

"Ke wly ki kiyayeni karkiga kin rigani zuwa bini kimin rainin hankali,kin sanni sarai🤨"
Cewar Husseina.

Kyaleta A'indo tayi dan tasan ba karamin aikin Husseina na ne ba tace suyi dambe anan.

Zuwa tayi ta samu wata bishiya ta zauna tana kalon A'indo tana neman tsalaka titi ,sai taje tsakar titi idan ta tsinkayo mota sai ta komo da gudu ta dawo baya, gaba-daya ta galabaita ,kuma taki hakura, da ta gaji ne ta kwala ma mai agwalima magana cewar "kai mai agwalima,kawo mana mu saya."
Jin haka mai agwalimar ya taso ya tsalako titin,yazo bishiyar inda suke,dan itama A'indo can ta koma,tashi sukayi suna latsawa tare da tambayar nawa,daya A'indo ta d'auka ta fara sha yace"Yan mata ai sai ki fadi ko ta nawa za'a baki sai a baki anma baki fada ba sai ki fara sha."

"Kaga kar ka fada mana maganar banza,munfi k'arfin wanan abun naka,ko duk muka shanye za'a baka kudin ka,ka masan koni wacece a garin nan kasan kasan matsayina kuwa,hahhh yaro idan kaji matsayina aradun Allah sai ka sara min,kaida kanka zakace mu d'auke duka,ni nan sunana A'indo Tantagariyar Yar Aiki🙄"

zuba masu ido yayi,suka d'auka sai sha suke,saida sukasha mai isarsu sanan,yace "to ku bani kudi na."

Wata tsohuwar naira biyar A'indo ta kunto daga harshen zanin ta wada tun zuwanta daga kauye tazo da ita tace"ungo fida kudin ka bani canji"😒

Waro idanuwa mai agwalima yayi yace"kai bana son shashanci kudi na naira dari biyu ne kuzo ku bani wata tsohuwar naira biyar kuma dan ubanku har kuna neman canji."
idanu tsakanin Husseina da A'indo suka hada,sunsan meye ma'anar kalon nasu,dan sunsan matsawar suka tsaya rashin kumya a sheke sai ya sheke su,dan haka kawai sai suka fara ja da baya,
suna ganin sun dan yi nisa dashi suka kali juna,sanan suka juya da gudu suka sa kai suka bar gurin a guje.


mai agwalima zai bisu har zai ruga yabi bayan su kuma sai yayi tsoron karya bisu kuma yabar agwalima sa da kudin sa."


Ji yayi kamar yayi kuka haka ya dawo wurin."



"Abass je te dis que j ne veux aucune fille dans c monde la parc-qu'elles sont tous les même."

sanye yake da gajeran wondo na sojoji,da riga single,tsaye yake bisa kan bene,yana kalon mutanen dake kasa,yayin da yakeda easpice a kunne,daya hanun sa kuma rike da coffee yana sha, hanun sa daya kuma yana cik'in aljihu,tsaye yake daidai window yana shakar iskar dake kadawa a sananin samaniya,bazaka taba tunanin cewar Alhassan bahaushe ne ba saboda tsananin kyan sa ga kuma kwarjini,ga cikar haiba,duk inda dogon namiji kuma cikak'e yakai

Waya ce yake da Abass abokin sa kuma abokin aikin sa, murmushi yayi yace"Abass na fadama ma kuma na kara fada wly ni a nan kasar hausa dai banga macan da ta isa na aureta ba,saboda wanan K'asar ta hausa duk Yan matan ta kauyawa ne basu waye ba ,kana ganin zan iya auren macan da bata waye ba,nida ake yawan gayata cik'in taro ta ya zan auri Mai karancin ilimi muje wajen taro a nemi tayi magana tazo tana ma mutane karancin turancin ta tasani kumya,ina sam bazaiyu ba wly."

Alhassan ya fada tare da tabe baki,ya ciji kuma lip's dinsa lokaci guda.
Dagacan b'angaren Abass yace"kai abokina kar fa ka cika baki wly su daddy su aura maka Yar kauye ba ruwana,ni bana son cika baki."

Jin wanan maganar tasa gaban Alhassan ya buga a take ya bada dum,kashe wayar yayi,dan wani irin bala'in haushin Abass yaji,lalai Abass ba masoyinsa bane,dan duk wani masoyinka ai bazai masa haka ba.kayan dama tuni suna cik'in mota,dan haka ya fito tare da sojawa masu tsaron lfyr sa,yana fitowa suka Sara masa tare da bud'e masa motar da zai shiga , cik'e da takama ya shiga, suka rufe suma suka shiga tasu ,akaja akaje filin jirgi dashi,ya shiga jirgi dashi da mutum biyu masu tsaron lfyr sa sauran kuma a mota zasu huce.......



Hajiya sam ta manta da A'INDO nada aure sai bayan sun tafi ta tuna,nan tasa a nemo mata su,tasa duk wani abu na falon a fida su a kasa wasu sabi,wa'incan kuma aka bada,nace "um kudi masu gidan rana."








Aci gaba da gashi🍇
Maimou love😘
[10/10 à 17:28] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨




*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋




*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚




*DAGA AKALAMIN MARUBUCIYAR*

👇
*YA MACE KOWACE DA IRIN NI'IMAR TA*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*,
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*





_DEDICATED TO SADJIDA & UMMY ONTOP_




*Page 17-18*



_NO EDITING_



""""""""""""kai dan Allah meye na salati,sai kace kaga Aljannu,cewar Husseina cikin tsiwa tare da murguda baki,Hajiya kam falo ta huce dan bazata tsaya shirmen su ba,Dan Aunty har gidan ta aka kaita.

salati Rabi'u daudu yayi yace "ba tantama kece husseina da A'indo ta fada min,dama tace "ke masifafa ce,kuma naga zahiri,ke A'indo zo muje kiban labari akoi zance fa "ya fada tare da juyawa yana kada kugu.jan hanun A'indo yayi ita kuma Husseina ta murguda baki,tace"wly sai na biyo ku nima.

Kan ki akeji ta mahaukaci da ya fada rijiya yace"kanku akeji ,ni wanka na nake."


Tunda suka fara tafiya Husseina keta kauyanci tana hangame baki,duk kuma sai tabi ta tsorata,da gudu taje ta kama hanun A'indo ta k'ank'ame."
"Hahhh kauyawa anzo birni."

Husseina tasan Sarai da ita yake dan haka ta murguda masa baki .

Kitchen suka zauna Rabi'u daudu yace "ke bani labari ashe dagaske wanan mugun Kika aura,tab aradun Allah an hada sa da hauka,ke kuma an hada ki da mutuwar ki .

"

Tashi yayi ya kunna gaz tsab a Idanun Husseina sai gani tayi an kunna wani abu wuta ta tashi ai da gudu ta fita tana ihu,fadi take jama'a ku kawo agaji gobara gobara ,a rikice mutane suka fara fitowa da gudu suka nufi inda take fadi, itama Hajiya daga falo taji,a tsorace ta fito,A'indo da Rabi'u suma tsoro sukaji Kar aje gobara ce akayi cikin gidan ai jin haka shima ya kashe gaz din a rikice suka fito da gudu shida A'indo, Rabi'u daudu yana gudu yana d'aura zani da ya d'aura a a kirji,kai kace mace,A'indo da take bayan sa saida ta huce sa kan gudu ita kanta Husseina da taga sun fito a guje sai tayi tunanin ko wutar ce ta fara fitowa,itama tace k'afa me naci ban baki ba ta bi bayan su a guje,itama tazo ta huce Rabi'u daudu.


Mutanen gidan da suka zo a guje sukayo kitchen din,ganin babu wata wuta kowa ya sauke ajiyar Zuciya,Hajiya ta karaso tana tambayar lfy,akace mata ai A'INDO ce ta kwaso da gudu tana fadin wuta wuta,su duk a tunanin su A'indo ce,dan suna matukar kama da Husseina..

A'indo ko can k'arshen gida suka tsaya suna sauke ajiyar Zuciya, Rabi'u ya kalli Husseina yace " ke wai a Ina Kika ga wutar kika sa mu wanan gudun sai kace masu gasar tsere🤨"

"Kaji min baho ba kai ka kunna wutar ba a can wajen madafa,ai naga kana kunnawa
yau ai Kai ka tada gobarar ."

" Nashiga uku ni Rabi 🤔,anma Allah shi kwashe miki Albarka ,kekam kinfi k'arfin A'indo,yau ni wanan bala'i har ina daga kunna gaz zan d'aura tukunya kawai sai kice gobara,anma Allh ya isa da kika sa ni wanan gudu haka,ah wly Hajiya na fama aradun Allah ,nikam nayi nan sai kuyita tsayuwa ai."

A'indo ma kalon Husseina tayi tace"tab ashe Husseina kema bahuwa ce bakida hankali,inaga sai an Nemo mai gyaran mutane ya duba ki."

Itama da gudu tabi bayan Rabi'u daudu,nan suka karasa wajen da mutane ke tsaitsaye harda hajiya,.

"Hajiya ta kalli A'indo tace"wai A'indo yaushe zaki nutsu?

"Gobe dasasafe"😒
A'indo ta bada amsa.

Hajiya tace"yanzu dan Allah ki rikita mutane a Ina kikaga wuta."

Rabi'u ne ya katse Hajiya yace"ai fa ke Hajiya kin debo ruwan dafa kanki ya aka kare da A'indo din ma bare ga Karin wata Yar uwarta,wly wacan ce tayi wanan bataliyar ba A'indo ba ya nuna Husseina."

Hajiya takai duban ta ga Husseina tace"Husseina Ashe kema baki ida cika ba."

"Tab kaji Hajiya cika sai kace fulawa "🙄 Husseina tace lokacin da ta karaso.


Aifa Hajiya kin d aukan ma kanki zakisha fama,ina aka kare da A'INDO ma bare kuma ga k'ari."
Cewar Rabi'u.

"Kai fa Rabi'u ka raina ni komai sai kace ni yau ni mahaukaciya ce,nasan dai banida hankali,shima kuma da Hajiya ta kira mai gyaran mutane da ya duba ni,Dan ni kaina Ina tantamar hankali na🙄 "

"asha yau ba ga irinta ba" cewar Rabi'u .
Watsewa akayi ana dariyar su,yayyin da ake mamakin su A'INDO sunyi matukar kama,lalai sukam sunga takan su.


"Hajiya ma cewa tayi Allah ya shirye ku ta juya ta tafi."


Bayan kwana biyu Hajiya zaune , A'indo da Husseina zaune kusa da ita,A'indo sai magiya take cewa " Hajiya dan barmu muyi miki guga,aradun Allah ba'a guga mai kyau,kuma ma ai Kinga yanzu na waye na iya ko😁na iya guga,tas ma kuwa Hajiya,"
A'indo ta bata amsa,
"To naji kiyi anma karki sake kiyi irin na ranar ,karki shafa mai,A'indo tace "to Hajiya ,kamar abin arziki ta kawo duk wani abun bukata na guga, ganin haka Hajiya tasa ma ranta kawai ta iya,ta tashi tabar falon ta haye sama saboda tana son yin wani lisafi.

Husseina ta kalli A'indo tace"ya zamuyi abun."

A'indo tace "tab bakauya zuba ido kiga yanda zan wanke falon nan tas,kinaga in aka wanke zaifi kyau sabanin gugar da ake yi, yau wanan ai bata lokaci ne,idan aka wanke falon ai zaifi,bari kiga aiki ba na raago bane,Nan tace "Husseina kiyika yin rarafe ke saiki dinga debo min ruwa ni kuma sai na dinga wankewa,tsuke kugun ta tayi da d'ankwali ta fara diban ruwa tana watsawa a ko Ina na falon,taje kitchen ta d'auko tsintsiya,wajen tafiyar ma sau uku tana faduwa har kuka saida ta danyi,da taga dai tafiyar idan tayi tana faduwa sai ta koma rarafe
Ruwa tasa tana wanke falon,bayan nan ta jika kujerun d'akin suma da ruwa ta fara dirza wai wanke su

Please Login or Register in order to submit comment