Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi aikin ta ,tunda kinsan ba Wanda zaiyi mata aikinta."

Yana fadin haka yabar mata falon."

zagi ta bisa dashi a zuciya ta juya ta tafi.

Kaya ta duba taga Gaba-daya kayan sun tsufa,wani katon akwati ta duba anan taga sababin kayan ta su less atamfofin shadodi,duk dinkaku,kuma masu tsada,tayi mamaki sosai,zagar kala biyar tayi ,sanan ta d'auki mayuka da sabulu ta fito,masu aikin ada wanda A'INDO take aikin su yanzu wa'inda a yanzu suke wani aikin, su ta gani ta basu wasu yan kudi tace su dinga yima A'indo aikin da take ma oga kafin ta samu lfy."

ba matsala sukace, sanan tayi ficewar ta,tunda aka kai A'indo har yanzu bata farfado ba,nan Mari ta kwana a asibitin,sai dasafe A'indo ta farka,ras taji saukin jikin ta saide rashin kuzari .


Mari take dawainiya da A'indo,yau kwana uku kenan A'indo ta warke tana komai ,tagumi A'indo tayi tana kallon Mari,A'indo tace"nagode sosai Anty, Allah saka miki da Alherie,badan ke ba nasan da yanzu na wula,daga hannun mugun nan."
"Ehee dama ina cewa bara na tambayeki meye hadin ki da wanan azalumin."

"Mijina ne"
A'indo ta bata amsa.

"😱,Miji fa kikace"?
Cewar Mari cik'e da mamaki da kuma razana."

Murmushi A'indo tayi sanan ta ba Mari labarin ta,sosai Mari tayi dariya sanan ta tausaya ma A'indo dan tabas jahilci na dawainiya da ita,dan da ba jahilci ai A'indo mace ce ta nuna ma tsara,kuskure daya akayi da ba'a bata ilimi ba kafin a aurar da ita.

Tabas tanada bukatar taimako.

"Anty Mari wly na tsani soji,anma kuma ina sha'awar nima nayi wanan aikin,Anty inason ilimi ,ina sha'awar zama soja nima."

"To anma kin taba Makaranta kuwa"?
Mari ta tambaye ta .
"Eh nayi primary a kauyen mu."

"Aisha yanzu zaki iya aikin soja,aikin soja fa saida jarumta,kuma Kinga da ace ke ba matar aure bace zan iya taimaka miki,anma Kinga ke matar aure ce."

"Wallahi Anty dagaske nake, inason zama jaruma nima dan na dau fansa,wly Anty ni kaina wani abun idan inayi sai nayi tunanin kamar banida hankali,wallahi inason inyi hankali,nayi ilimi,nima fito soja."

Murmushi Mari tayi tace"kwanta ki huta..

Saida A'indo tayi kwana biyar aka Salamo ta,Sam Alhassan baiyi tunanin ba bata gidan,domin a tunanin sa ita ke aikin da ya bata,tunda ana yin aikin kafin ya fito ,wanan yasa baya sanin mai aikin....


A'indo tayi rama saide cimar da Mari ke kai mata a kwana biyar ta murmuje,kayan da Mari ta kawo mata ba karamin bala'in kyau suke mata ba,saide duk sai taji ta a takure ,batajin dadin sa su.

Taji k'arfin jikinta sosai hakan yasa suna dawowa gidan maida kayanta na da.

Kuma abun burgewa acikin wanan dan zaman da A'indo tayi a asibiti kwararun likitoci suka duba hannun ta inda aka maida mata shi daidai,hanun ta ya koma dai-dai,sanan suka kara bata wasu maganin nika wanda zata dinga sha zaiyi saurin warkewa,Masha Allah ba karamin godiya Mari tayima doctor ta ba,domin shine yayi wanan taimakon .


Mina ce a zaune saman k'afar Alhassan inda take fada masa abinda Mari tayi mata saboda A'indo ran Alhassan a bace yasa a Kira masa Mari da A'indo a tare sukazo ."

Kallon tsana yakai ga A'indo sanan ya juya ga Mari yace"ke har kin isa kina k'arkashi na ki nemi cima Matata mutunci,har ki fada mata magana saboda wanan jakar,wallahi kinci darajar tsohon ki badan haka a yau din nan sai na koreki,

kije kiyi abinda ya kawoki ki tatara tsuman rayuwar ki, ki barmin tawa karki kara shiga Al'amarin rayuwata zaki iya tafiya."

fita Mari tayi ranta ya baci anma ta danne.
Sanan yakai kallonsa ga A'indo yace "kije ki gyara min d'aki na, sanan inason ki sani kika saki kikayi kuskure sai kin gane shafi ruwa ne,sanan ki tabatar bakibar dati ko daya ba,ki gyara komai ,ki wanke na wankewa ,ki gyara na gyarawa.wly idan kikayi kuskure sai na lahira yafiki jin dadi,d'akin sa taje ,duk an birkita d'akin anma kuma tasan anyi haka ne dan ya wahalar da ita,gyaran d'akin ta fara da hannu daya,ta share da k'yar sanan ta dinga nade kayan. , b'andakin sa ta shiga b'andakin ma harda Tv ta bango b'angare guda, b'angare dayan kuma su cumputer ne,da wasu takardu, b'andakin ya hadu matuka ,gyara b'andakin tayi duk da ba wani dati tayi ba,sanan ta wanke , cumputer ta d'auka taga kamar ta danyi dauda sai ta hada ruwa da klin ta sa ta cik'in ruwan ta fara wanke ta,saida ta wanke computer da kyau sanan ta goge ta maida ma'ajin ta,sosai ta gyara ko ina.

Duk ta gaji , gashi dama bata ida warwarewa ba. Alhassan ne ya shigo d'akin ya huce b'andakin dan d'aukan computer sa,aiko sai yaga aika aikar da A'indo tayi masa,zaro idanu yayi yace"what cik'in razana da k'arfi,jiya ya sayo computer dan yasa wasu bayyanai anma sai gashi A'indo ta wanke Masa computer,Idanun sa suka rikida tsabar bacin rai,ita kam A'INDO tuni ta sure,dan tasan wata killa tayi laifi,itakam tasan yau kashe ta zaiyi,wuri daya ta tsamure, cik'e da tsoro abin tausayi,juyowa yayi ya kalleta tuni ya kara jin wata tsanar ta a ransa,"ke!! Wly na tsane ki ayau zanyi ajalin ki uban kowa ma ya huta nima na huta,wuyan ta ya kaima cabka ta baya,ya rikota,ya fara janta,har saida ya sauko falon da ita ya fara marin ta,sanan ya jefar da ita,Allah ya taimake ta ba bisa kararen hanun bane,kuka take sosai tana basa hakuri akan ya yafe mata, k'afafun sa ta rike da hannu daya,tace"dan Allah kayi min rai kayi hakuri idan na maka laifi."

"Dan ubanki har tambaya kike in kinmin laifi,agidan uban wa kika taba ganin an wanke computer."
Duk Mina na tsaye tana kallon su tana dariyar jin dadin bugun da yake ma A'indo,itakam A'indo neman gudu tayi dan ta ceci kanta ,ganin haka ran Alhassan ya kara tunzura,ya kara damko wuyanta ta baya da k'arfi ya buga kanta da bango wata irin razananar kara A'indo ta buga sai gata suuuuu ta fadi,jini ya fara zuba daga goshin ta,salati yaji an buga daga bayan sa,wanda yayyi matukar razana sa,juyawar da zaiyi aiko wa zai gani idan ba Hajiyar sa ba,wato Momyn sa,a matukar ruduwa da firgita ya zaro idanu,da gudu Hajiya ta karaso ita da Mari dan dama a tare suka shigo talabo A'indo Hajiya tayi,ta fara jijigata tana ambatar sunan ta anma ina A'indo ta suma.
"Mari taimaka mukaita asibiti.".

Hajiya tace da Mari,d'aukan A'indo sukayi,aka kaita wata asibiti daban,ba wacan ba,taimakon gagawa aka ba A'indo awa daya aka d'auka a kanta,sanan aka samu ta farfado,anma kuma ga dukan alamu akoi matsala a kanta,domin kuwa har k'wak'walwar ta likitoci suna tsoron idan bata samu matsala ba saboda buguwar da k'arfi ne akayi mata.hajiya na hawaye ta dafa Mari tace nagode ya ta,da Kika kirani,anma dan Allah ki fadamin gaskiyar duk abinda kika san ana mata a gidan,domin na tambayeki a waya kince sai nazo to ki fadamin yanzu."

Sauke ajiyar zuciya Mari tayi,ta fadama Hajiya duk wani abinda ta sani.

Goge hawaye Hajiya tayi,tabas sunyi kuskuren yin wanan hadin,ashe haka Alhassan yake bashida imani,tabas zai gane kuren sa,dafa Mari Hajiya tayi sanan tace "Mari ki kula min da A'INDO zanje na dawo fita Hajiya tayi,ta shiga taxi gidan Alhassan ta koma,yana falon har yanzu, yana nan inda yake, Mina kam ta gudu ta bar sa dan tsoro ,tunda ta fahimci Hajiyar sa ce tazo .

A tsaye Hajiya ta iske sa,bata ko masa magana ba ta basa takarda da biro tace"amshi ka saki A'indo a yanzun nan,idan ko kaki bin Umarni na zan iya tsine maka,hannu na rawa ya amsa ya rubuta ma A'indo saki daya,ya ba Hajiya takardar hannun sa na rawa,"Mom dan Allah tsaya kijiiiii."

"✋ya isa!!! tsayar dashi Hajiya tayi a tsawace,tace"a yau ka nuna mana mu bamu isa dakai ba,cewa nake ko Kashi muka aura ma ka zauna dashi ba tare da ka zalunce sa ba bare dan Adam,ni bazan maka baki ba,anma ka sani wallahi alhakin baiwar Allah nan kadai ya ishe ka,yanzu sai kayi abinda kaga dama ,A'indo insha Allah ta rabu dakai har abada."

Hajiya na gama fadar haka tabar gidan ta nufi asibiti,anma tana zuwa asibiti ta tarar da mumunan labari,zaune suke daga ita har Mari gaban doctor inda yake musu bayani game da matsalar A'indo kamar haka........





Aci gaba da gashi🍇
Maimou love😘
[10/10 à 17:34] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨




*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋




*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚




*DAGA AKALAMIN MARUBUCIYAR*

👇
*YA MACE KOWACE DA IRIN NI'IMAR TA*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*,
_and Now_👇
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*


_kuyi hakuri na rubuta Latifa ina tsaka da editing ya goge_😢



_DEDICATED TO SADJIDA & UMMY ONTOP_





*Page 33-34*




Fita yayi ya barsu,a kyamace Mina ke nuna mata abubuwa cik'in yanga,tanayi mata magana tana done hanci wai wari take,duk A'indo na lura da ita,tabas duk abin A'indo bata zama da kazanta bare wani abu wai shi wari,kaya ne kawai na lefe bata sawa Wanda aka mata,anma tana amfani da mayukan da aka hada mata na gyaran jiki da kuma kamshi,sanan tana amfani da turare,wanda ko ita karan kanta Mina bazata nuna mata kamshi ba....


Girgiza kai kawai A'indo tayi cik'e da takaici,nan ta zuba komai yanda ta nuna mata ta duka ta fara wanke mata kafa,"wai ke wace irin daba ce stupid bakya da laka ne,wawiyar banza ,kina wankin kafa kamar kina susa."

Cewar Mina ta daka ma A'indo tsawa."

"Yi hakuri"

Abinda A'indo tace kenan,nan ta dinga wanke ma Mina k'afa tana zagin ta,bayan ta gama tace A'INDO tayi mata tsifar kitson kanta,mai hade da gashin attachement,kalon ta A'indo tayi tace"kiyi hakuri hannuna daya bayayi ya samu karaya ne."


Fadin haka ya bata ran Mina tace"dan uwarki bakiji abinda mijina yace ba,cewa yayi ke baiwata ce,koda hannun ki yana jan kasa ai kinyi abinda nace,anma tunda naga dama ku yan kauyen nan baku iya samun guri ba,bara kiga."

Waya ta d'auka ta danna kiran Alhassan aiko cik'in yan sakanni sai gashi sai muzurai yake,yace"my wife wa ya tabaki."
Kyabe baki Mina tayi tace"haba my Man ace wai yarinyar nan na sa ta aiki anma taki yi min ,wai taji ciwo a hannu dan munafurci,kamar ni yarinyar nan ta nemi zagi na."


Waro idanu Alhassan yayi tare da cewa "what"? cik'in zaro ido,ransa in yayi dubu to ya baci,dama neman hanyar da zaibi ya bata ran A'indo yake,ya kalli A'indo yace"ke dan ubanki kina matsayin yar Aiki ni zaki kalli Matar da nake so kice bazaki mata abinda take so ba,wai ke hannu, sallon munafurci,hannu ko ,hum bara kiga,hannun ya rike wanda ya karye din,yayi masa wani irin ja da k'arfi,wata razananar kara A'indo ta saki tsabar azaba,sai gata ta fadi sumamiya.

Waro idanu😨 Mina tayi cikin matukar tsoro tace" Man ka fa kashe ta!
"Yau ta mutu mana wa keda asara,kinga fice muje,na kirawo masu fida min ita,ni dama zata mutu da naji dadi mtsssss."
Cewar Alhassan,da k'arfi yaja Mina suka fice daga wurin,gards dinsa Mata yakira,Mari da Jenifer,su suka d'auke A'indo sukayi d'akin ta da ita a some.

Mari Kam yau kuka take sosai,domin tasan cewar matukar A'indo nada rai to ga yanda taga hannun ta sai ta Allah,domin gwiwar hannun ta dan lank'wasa,yau Mai gyaran hannun ta kira direct ,bata nemi saurayin ta ba,ba'a jima ba yazo,a sumen ya duba hannun A'indo ya zaro ido yace"ranki ya dade ya haka ,me yasa aka bari hannun ta yana samun matsala haka,to a gaskiya cik'in biyu za'ayi daya,kodai idan ba'ayi sa'a ba hannun ta ya lalace wanda dole sai an yanke sa,idan kuma na duba Allah ya so ta to ba lallai hannun ya daidaita yanda take a da ba."
Duk a turanci yake wanan bayanin.

"Mari da duk jikin ta yayi sanyi tace"ka taimaka ka duba hannun a yanda take a some domin idan ta tashi zatafi cin azaba."

Nan ya kunce karayar ,ya duba,hannun ya lank'wasa,haka dole ya sake sabon d'auri,wanda azabar hakan ya farfado da A'indo a gigice,ta fara kiran sunan Alhassan da yayi hakuri,tana kara fadin wayyo babana ka taimaka ka kwato ni daga hannun azalumi,Wayyo Allah,Mari ce ta rungume ta,Saida aka kara gyara karayar,saide hannun bai koma dai-dai ba, saboda ya dan gusa,bayan an gama mai gyaran yace"a gaskiya a dinga taka tsantsan da wanan hannun domin anyi sa'a tanada kyan jiki,badan haka ba da wani jikin ne saide a yanke hannun ,anma yanzu ma a kiyaye,domin kuwa idan hannun ya kara tabuwa to za'a iya samun matsala,dan ba fata nake mata ba za'a iya yanke hannun."

Ga wanan maganin a bata tasha."


Mari ta masa godiya ya tafi ,kallon ta takai ga A'indo tace"wai ke me kikema oga yake miki irin wanan horon,ki daina matse masa,ko yi Masa musu dan wly kinji abinda akace idan hannun ya kara tabuwa to fa za'a iya yanke sa,ko kinfi son a yanke,kinga ni yanzu sati yayi min saura na bar kasar nan in koma kasata Niger dama ina sha'awar aikin soja shi yasa mahaifina ya turo ni wanan K'asar domin Karin ilimi bisa kan karatun soji,shine aka hadani da oga Alhassan a wajen sa nake karin koyan abubuwan da ya danganci soji."

Dan Allah ki roke sa ya mayar dake gida,kinga duka gidan nan kusan arna ne,ba wani tausayi garesu ba,suna kallan ki ko zaki mutu ba zasu taimake ki ba."


Kada kai A'indo tayi cik'e da tausayin kanta,zataje ta roke sa ya mayar da ita,anma kuma yanzu mugu mugun tsoron sa take ji ,nan Mari ta barta ta koma taci gaba da aikin ta,A'indo taci kuka kamar ranta zai fita....

Washe gari da zazabi mai zafi A'indo ta kuma tashi,wanda yasa ko tashi bata iyayi,sai tayi yunkurin tashi sai jiri ya d'auke ta,dan haka take kwance,ga muguwar yunwa da ta adabe a,ga amai da yake zuwar mata,tun tanayin na garin rogo har takai in ta duka bata anma komai,saide tayita kakari anma ba abinda ke fitowa, ,cik'in ta ya kulle,a haka da asuba kamar yanda Alhassan ya saba idan ya fito daga Sallah a masalaci yana ganin ta tana wanki motar da zai fita da ita anma yau yaga wayam ba ita ransa a matukar bace,yayyi b'angaren ta,kwance ya isketa tayi lamo,dan yanda taga dare haka taga rana,bai tsaya lura da yanayin da take ciki ba yana zuwa yayi ball da ita dai-dai Allah ya taimaka bai samu hannun ba , saide cik'in ta da ya buga,da kyar A'indo ta iya yin kara wace duk azabar da take ji karar ba zata fito ba saboda ba k'arfi a jikin ta,kuma gashi ba komai a cik'in ta ga bugun da yayyi mata dama ciki ya kulle.

"Dan uwarki ubanwa kike so ya miki aikin naki,kinsa da bana son a saba magana ta shine dan ubanki yau baki tashi Kika wanke min ba."

Kuka A'indo take da kyar muryar ta ke fitowa tace"dan Allah ranka ya dade kayi hakuri wallahi banida lfy ne,nasha kokarin in tashi anma jiri yana diba ta,kayi hakuri ka yafe ni😭😭😭."


Ko kadan bata basa tausayi ba,saima dukawa da yayyi ya ja kunnen ta da k'arfi yace"wallahi baki isa ba ko Zaki mutu sai kinyi ayukan nan."


Cik'in zafin ciwo da kunar zuciya A'indo tace"dan Allah idan abinda nayi maka ne a baya kayi hakuri ka yafe min,wly Allah yanzu a shirye nake da fasa auren ka,wly Allah zan fada ma Hajiya,dan Allah kayi min rai ka maidani kasata."


"Hum yaro yaro ne,daga baya kenan,yanzu kuma ai bakin Alkalami ya bushe,bara kiji ba kin kwanmace ki biyoni ba,hum karki damu,akuba ai baki ma fara ganin komai ba,muje zuwa yan mata,sai na nakasa ki,sanan nayi miki sakin wulak'anci ta yanda a gobe da keda yan iskan iyayen ki ba zasu Kara kokarin yarda su aurar da yarsu ga irin mu masu kudi ba.
Makwadaita kawai ,kuma wly na fito zuwa office banga an wanke min mota ba,hummmm."


Yana gama fadar haka yasa kai yayi ficewar sa."



Duk yanda A'indo taso tashi abin fa yaci tura,domin kuwa ta galabaita iya galabaita,dole tasa ta koma ta k'wanta , tana jiran sakamoko,dan tasan wanan karon kam idasata zaiyi."


K'arfe bakwai Mina ta rako sa,ya fito dan zuwa aiki,turus yaja ya tsaya ganin babu Alamun an wanke motar da zai tafi da ita,domin kuwa ba lema a gurin,in ransa yayi dubu to ya baci,wani abu ya d'auka a mota,ya koma d'akin da A'indo take,isketa yayi a kwance kamar yanda ya barta dazu,kamar guguwa ya karaso inda take,gashin kanta yaja da k'arfi,tayi kara wada bata fitowa,,,
Wani abu ya d'auka irin wanda ake horar da criminal dashi, idan ana tugumar sa da laifi baba ana son ya fada kuma yaki fada,abu ne wanda idan ansa a jikin dan Adam zaiji kamar wutar lantarki na jansa,dan har jinin jikin sa ja yake ,abun yanada zafi."

Murmushin gefen baki yayi yace"wato kin raina ni ko,nasaki aiki bakiyi ba ko,hum zakici ubanki ne."


Nan fa ya fara jona mata,daga ya jona mata sai ta fara karkarwa kamar mai farfadiya,abun zafi garesa sosai,take jini ya fara fitowa ta hancin ta,anma bawan Allah nan bai barta ba,saida ya sumar da ita ,sanan yasa aka kawo masa ruwa masu bala'in sanyi ya sheka mata."


Ta farfado,ya kalleta yace" gobe ma sai ki kara, stupid villageoise girl mtsss."


Kallo daya zakayi ma A'indo ka tabatar da cewar batada wadatacen jini,domin kuwa zazabin da take dama ya shanye mata jini gashi kuma yanzu wanan abun da yayyi mata,tabas idan bata samu taimakon gagawa ba, za'a iya samun matsala dan zata iya rasa rayuwata.......





Muje zuwa......






[10/10 à 21:05] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨




*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋




*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚




*DAGA AKALAMIN MARUBUCIYAR*

👇
*YA MACE KOWACE DA IRIN NI'IMAR TA*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*,
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*





_DEDICATED TO SADJIDA & UMMY ONTOP_




*Page 37-38*





Doctor yace" yace a gaskiya a yanda ta bugu munyi tunanin ma zata samu matsala a k'wak'walwar ta ,anma kuma sai muka samu akasin hakan,saide inda matsalar take shine idan har ba'a bar yi mata abinda bata soba Zuciyar ta na gap da kamuwa da ciwon zuciya ,dan haka a kiyaye abinda zai dinga bata mata rai."


Sauke ajiyar zuciya Hajiya tayi dan a yanda taji doctor ya fara magana tayi tunanin wani mumunan abun ne ya kuma samun A'indo.


Duk a fransanci doctor ke musu bayani suma a yaren suka maida masa cewar yaushe za'a salame su yace yau ma zasu iya tafiya."

A gadon asibiti Hajiya zaune A'indo na kusan ta cik'e da kukan farin ciki,yayyin da Mari ke b'angare daya a tsaye, A'INDO ta tashi ta dan dafa goshin ta da ya dan sara Mata gurin har ya dan kumbura,Hajiya ce ta taimaka mata ta zauna A'INDO rungume Hajiya tayi ta fara kuka tana fadin hajiya dan Allah ki taimaka ki rabani da danki,wly kasheni zaiyi bana son sa,a raba auren😭😭."

Tausayi taba hajiiya ganin yanda A'indo ta lalace ta rame,share mata hawaye Hajiya tayi tace"naji A'indo anma sai kinyi min Alkawarin zakiyi duk abinda nace kiyi,sanan zaki natsu kiyi hankali."

Saurin daga kai A'indo tayi tace"Hajiya wallahi na yarda zan natsu,ai na ma nutsu kuma wly Hajiya zanyi duk abinda kikace ."

"Good yayi kyau ,zan sa Alhassan ya sake ki anma sai kinyi karatu anma idan ba haka to saide na maidoki gidan sa."

"Wallahi Hajiya zanyi ko wane irin karatu ne,indai zaki rabani dashi."


Hajiya takai kallonta ga Mari tace"to Mari ba abinda zance dake sai Allah ya miki Albarka,kuma aikin da kikayi nagode sosai da kika sa min Ido a kansu kamar yanda na sa ki,yanzu zamuje gidan Alhaji da yake anan zamu kwana acan washe gari zamu koma Niger."

Murmushi Mari tayi tace"ba komai Hajiya aike uwa ce,dan haka karki damu."

Murmushi Hajiya tayi tana yaba halin Mari.

Mari dai yar kawarta ce da ta rasu shekaru biyu da suka huce,Yar gidan Alhaji Usman ce,mai Kudi ne a a Niger garin Zinder,Mari zawara ce ,dan ta taba aure,shine lokacin da zataje Karin ilimi akan aikinta na soja sai kuma akayi sa'a Alhassan ne zai kara bata horo hakan yasa Hajiya ta kira ta ,tace"ta kullar mata da A'indo duk da bata fada mata cewar matar Alhassan bace,anma tace yarinyar yar uwarta ce ,
Wanan dalilin yasa duk motsin A'indo a idanun Mari .

To Hajiya ni zan koma bakin aiki insha Allah nima a satin nan zan koma Niger,idan naje zanje can Hajiya saboda akoi magana mai mahinmanci,sannan ta dafa A'indo tace"to kanwata Allah ya baki lafiya sai mun hadu a Niger idan Allah ya kaimu."
Murmushi A'INDO tayi sanan suka rungume juna Mari ta tafi takai bakin k'ofa A'indo tace"Anty ya zancan mu da fa gaske nake,dan a yanzu burina kenan😊."


Murmushi itama Mari tayi tace "karki damu insha Allah burinki zai cika,kiyi kokari ki warke,kuma ki dage ki samu ilimi tukon."

Mari na gama fadar haka ta fita, A'indo kara rungume Hajiya tayi tana sauke ajiyar zuciya,koda doctor yazo ya dudubata sannan ya salameta tare da rubuta mata wasu maganun nuka.


A gidan Alhaji dake garin suka kwana washe gari jirgin su ya daga zuwa Niger.

Gaba-daya Alhassan ya rude ,ya razana ya rasa abinda ke masa dadi,farin cik'in sa guda ne idan ya tuna cewa yanzu fa ya rabu da wanan jakar kuma jahila ,yanzu burinsa daya ne shine ya shawo kan iyayen sa su yafe masa sanan su aura masa Mina ,wanan ne kadai matsalar sa.



Bayan su hajiya sun sauka akazo d'aukan su da mota,abun mamakin da A'indo ta iske bai huce yanda ta tarar da yar uwarta Husseina ba ta fito daga islamiya,ta fara nutsuwa,ita kanta Husseina da gudu tazo ta tarbi A'indo tana murna da farin ciki tare da mamakin ramar da A'indo ,anma jin Hajiya tace "Yi a hankali husseina A'indo karaya ke gareta."sai taja baya ta tsaya,hawaye ne suka fara zuba a idanun ta tace"meye haka hassana

Please Login or Register in order to submit comment