Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗari biyu-biyu guda uku ya bawa Malam Buba.
Ina ji yana godiya na yi caraf na ce masa zan zo na amshi tsire da sauran canjin Alhaji.

"Ni kam Uwata anya ba boarding school zan kai ki ba kuwa, rigimarki yayi yawa"

"Dan Allah Alhaji..." na fashe da kuka na shige gida.
Tab! Ina zan iya barin Hajiya Kaka.
su Safiyya da Zuhriyya da aka kai su boarding school ai ba karamin wahala su ke sha a chan ba, idan suka dawo gida ka gansu a rarrame kamar an tsinto su daga gidan marayu...

***

Yau Asabat ina wanke uniform ɗina a bakin kofar ɗakin Kaka aka yi sallama. Kaka na zaune ɗan gefe dani akan tabarma tana cin goro.

"Wa'alaikumussalamu. Laraba sannu da zuwa. Bismillah"

Ban maida hankali kan zancensu ba na cigaba da wankina, sati biyu kenan da shigata JSS 1. Ina ji da kaina nima. Tsabar an tsaneni sai da aka bari na yi aji ɗaya har aji shida. Hanifa dana girmeta da wata biyar ma a Primary 5 ta zana common entrance ta tafi boarding ita da Safiyya aka barni ni kaɗai a Primary 6 kamar wata mayya.

"Dan Muhammadu kice maganan nan ba gaskiya bane"

Ina jin Kaka ta faɗi haka na karkata kunnena na fara sauraron zancensu.

"Hajiya shiyasa na ce gara na faɗa muku kafin a zo a yi abin kunya"

"To wani abin kunyan ya wuce wannan Laraba" ta ɓantari goronta sannan ta cigaba. "Ai sai ku nema mata magani"

"Iyayen sun ce an nemi magani har an gaji. Wai Aljanunta na gado ne"

"To sai su rasa abin da zasu saka ta sai ɗauke-ɗauke"

"Kaka waye ke ɗauke-ɗauken?"

"Wai fa sarkuwarta da aka kawo kwanan nan"

"Inna Laraba wai Amaryar Malam Hashiru, miye ma sunanta?"

"Kulu"

"Kulu mai sata kenan" Kaka ta kai min duka da tsintsiyar laushi dake kusa da ita, na yi saurin kaucewa ina dariya.

"Dan bantenki cutar ɗauke-ɗauke aka ce take da shi ba sata ba"

Ni kam mi na samu banda dariya. Inna Laraba na fita Kaka ta mike za ta kai rahoto wa matan gidan. Yau Amarya Kulu ta shiga uku a gidanmu. Inna Laraba makotanmu ne suma babban gida suke mai balbali-balbali da yawa. A gidan 'yangidanmu ke kitso. Idan ana wani hidima kuwa sukan shigo kwansu da kwarkwatansu su tayamu aiki...

***

Ina JSS two aka saka bikin Anty Firdausi dana Anty Amina har ma dana Anty Fatima Munnirah 'yar Baffanmu Abubakar. Daɗin abinma tuwona maina za ayi dan biyu daga ciki na gida zasu aura, Amina ce kawai za ta auri wani ɗan Bauchi. Munnirah da yaya Mustafah sai da suka gama kulla soyayyarsu kafin suka sanar a gida. Nan fa Kaka ta fara masifa da korafe-korafenta marasa dalili.
Alhaji kuwa ya dage sai an kulla zumunci wai shi da Baffa Abubakar ɗaya suke. Dake gar ta san gar, duk ta yadda ta fito masa sai ya toshe, karshe ta hakura ta saka musu albarka.

Ba abinda yake mun daɗi irin yadda ake cika a gidanmu lokacin biki. Ka ci ka sha ka koshi son ranka. Gashi lokacine da gaba ɗaya familynmu ke haɗuwa, babu banbanci tsakanin'ya'yan Hajiya Kaka dana marigayiya Hajiya Sadiyya. Balle wannan bikin zai kara karfafa zumunci.
Abban Egypt zai zo da iyalinshi haka nan su Anty Hasinan kasar turai ma duk zasu zo...

Tun ana saura sati biyu 'yan Egypt suka shigo. Su Amal da Amrah an zama 'yan gayu, suna wani turancinsu da larabcinsu na 'yan gayu. Ni kam banda ta'al- zo, na'am- e, babun- kofa da kuma sarirun- gado ba abinda na sani a larabci.
'Yan gidanmu sai nan nan suke da su wai su 'yan gayu. Mtssw.
Har ma danna taɓawa Amal riganta take cewa wai zan shafa mata datti, sannu madara. Mtsww...

Ina zaune a ɗaki nida Kaka muna cin tuwon shinkafa da miyar ɗanyen kuɓewa aka yi sallama aka shigo. Ni da Kaka rige-rigen kai loma muke ko ta kan sallamar bamu bi ba. Miyan yayi daɗi, ko ban faɗa ba kun san girkin Anty Amarya ne. Ga naman kaza a ciki ga hanta an yanka kanana, ga kuma busashshen kifi irin wanda Inyamurai ke siyarwa ɗin nan.

"My Kaks ki ci a hankali mana kar ki shake"
"Sahla dear eat slowly kin ji" ya faɗa yana shafa kumatuna

Affan ne. Affan yayan Amal. Shine ya kirani da DEAR. Duk da dai ban kai su Amal jin turanci ba ai na san wannan kalmar. Kai ina cin 60/100 fa a darasin english kuma duk english novel da aka samu karantawa a makaranta ina karantawa.

Na ɗan sunkuyar da kai ina murmushi. Sai na dena ɗiban katon loma na fara ɗiban karami.

"Sahla kina wani aji yanzu?"

"JSS 2"

"Wow! Kinga nan da shekara huɗu sai a ɗaura mana aure"

"Dalla bani wuri. Waye zai baka Sahalar, da gashinka kamar dambun mahaukaciya"

"Kaks wannan gashin swagger kenan fa"

"Ina uwarka?. Ba za ta shigo ta gaisheni ba"

"Mom tana sashen Anty Rafee'ah. Kaman tace zasu yi maganar event da za ayi a bikin ne"

Ni dai tunda yai maganar za a ɗaura mana aure nan da shekara huɗu sai na sunkuyar da kai ina cin abinci a hankali. Da hakura ma zan yi da abincin sai na tuna idan na hakura dashi Kaka za ta tsame sauran naman ne ta cinye ita kaɗai. Ni da Kakar tawa duk kuraye ne. Son nama ne damu kamar jaraba.

Affan yaita tsokanar Kaka tana biyeshi. Duk cikin 'ya'yan Abba shi kaɗai ne ke sakewa da Kaka. Zai zauna a sha hira da shi. Amma su Amal duk halin Mom ɗinsu suka yi.

Sati ɗaya saura biki su Anty Hasina da Anty Sayyida suka dira a gidan. Anty Hasina har da tsohon ciki za a yiwa Faisal kani ko kanwa. Anty Sayyidah kam ta ki aure har yanzu. Ina ji su Mama da Ummi na gulmanta idan na shiga sashensu.
Ni da su Amal, Hanifa da Safiyya muka ɗunguma sashen Alhaji dan muga Uncle Faruku. Ance ya zo amma har yau bamu gan shi ba.
Har muka karashi ziryanmu bamu ga mai kama da shi ba.
Da muka gama jelarmu bamu ganshi ba sai kowa ya watse. Ina zuwa ɗakin Hajiya na hango wani takalmi irin cover shoe ɗin nan na maza. Sai kyalli ya ke, gefensa kuma wata Akuyar Kaka ce ke Sunsune-Sunsunen abinci. Na kori Akuyar na ɗau takalmi ɗaya ina dubawa dan na ga size ɗin, wannan takalmi ba dai kato ba kam. Kafin na ɗau ɗayan mai takalmin ya fito daga ɗakin Kaka. Dogo ne sosai, fiskarsa babu fara'a ko kaɗan. Yana sanye da blue ɗin riga da jeans 'yan kanti ba 'yan gwanjo ba.

Na ajiye masa takalminsa ina murmushi na fara gaisheshi. Ko ba a faɗamun ba na san Uncle Faruku ne dan suna kama sosai da Anty Sayyidah.
"Ina kwana Uncle Faruku". Faruku Kaka ke kiranshi shiyasa sunan ya bi bakina amma tabbas abinda na faɗa ya ɓata masa rai. Dan kuwa sake haɗe rai yayi kamar ya tauna sabon kashi.

"Takalminka ya min kyau"

Ban ankara ba na ji an shako ni.
"How dare you"
Wallahi irin shakar da ya min sai da na hango iyayena suna min maraba da zuwa Barzahu.

"Faruku kashe min ita za ka yi. Saketa, saketa na ce"
"Mustafah"
Ashe tare su ke dama. Yaya Mustafah ne ya kwaceni daga hannun Dodon nan. Daga gaisuwa.

Sai dana yi minti ɗaya da rabi kafin na fara dawowa dai dai. Sai a sannan nake ji wai ashe Kashin Akuya ce ya gani a cikin takalminsa. To ni na saka a ciki ne?.

Ina ji Kaka na korafi akan koma minene dai bai kai ya kashe mata ni ba. Wallahi na shaku kam, dan har hawayen dole sai da na yi. Ba dan Yaya Mustafah ba kila da yanzu na zama gawa.

Takalmin Yaya Mustafah ya saka ya bar wajen shi kuma Yaya Mustafah ya saka nasa bayan ya karkaɗe kashin Akuyar.

"Allah ya isa, kuma Wallahi sai na rama" na faɗa a fili...

003...Awaki wedding event... Courtesy Sahla ...


'Tashen balaga' wata kalma ce dana tsana a rayuwata. A 'yan kwanakin nan babu abinda zan yi da ba za a jingina shi da tashen balaga ba. Idan Mama ta sani shara na ki yi ko kuma ban yi da wuri ba yanzu za ta fara zagina tana cewa bata son tashen balagan iskanci.
Wai minene Tashen Balaga ne? Oho nima ban sani ba, ina dai jinta koyaushe. Faty kawata a ajinmu ta ce min wai tashen balaga na nufin macen da nononta suka girma. Idan haka ne to Mama tayi karya dan kuwa nonona 'yan mitsi-mitsi ne.

Ban san ya aka yi ba amma tunda Faty ta min wannan fassaran duk lokacin da na shiga banɗaki zanyi wanka sai na shiga da karamin madubi ina kallon kirjina ko nonuwana sun karu ko suna nan dai dai. A fakaice na fara lura da kirjin su Amal. Duk cikin 'yanuwana da muke kusan sa'anni ni kaɗai ce nonuwana suka ki girma. Amal kam dama renon Egypt, ga ta nan ɓulɓul ta cika ta ko'ina.

Tunda Affan ya fara kirana da Sahla dear sai nima na fara jin kaina wata babba. Da na shiga ɗakinsu Safiyya na sato bra ɗinta guda ɗaya. Ina kokarin sakawa amma na kasa. Da ke kullum ina jikin tsohuwa ni ban san ya ake saka shi ba ko Safiyyar ma ita ce ta gaya min da za a kaisu boarding school ne Ummi ta siya musu. Na saka shi ta kai ya ki shiga. Na fara kokarin saka shi kamar yadda ake saka pant amma bai yi ba. Ina ta kici-kicin sakawa dai Kaka ta shigo.

"Miye wannan?"

"Kaka kuma sai ki shigo babu sallama"
"Ungo naki da sallamar. Ni da ɗakina"

"Miye wannan?" Ta sake tambayata bayan ta fizge bra ɗin a hannuna.

"Ina nonuwan da zaki sakawa rigar Mama. Waya baki, Rafee'atu ce ko Bilkisu"

Na tura baki nace "ɗaukowa na yi a cikin kayan Safiyya"

"To maza ki mayar mata. In kin kai ki fara sakawa ni da kaina zan sa a kawo miki"

"Kaka Amal ma fa na sakawa"

"Ji min 'ya. Ina zaki haɗa kajin turawa da ta gida. Wannan yarinya Amal ai nan da shekara biyu ya kamata a kaita gidan miji idan ba haka ba sai ta kamo Uwarta a jiki"

"Ni dai ba zan mayar ba. Sai na saka"

Kaka ta shareni ta shiga sabgarta. Da na ga na kasa sakawa daidai sai kawai na hakura da shi.

***

"Yanzu wannan shi zaku sha ranan da za a ɗaura aure. Ku tabbatar shi kuka fara sha kafin ku ci komai. Yawwa. Wannan kuma idan zaku kwanta zaku sha cokali biyu"

"This is bullshit Anty Rayyanah. Anty Rafee'ah ba za ki saka baki ba. Ke fa likita ce. Tun da na zo gidan nan nake gani ana basu abubuwa suna sha. The other day GrandMa ta kawo wani bakin abu mai shegen wari wai su sha"

Anty Rayyanatu ta ce " Sayyidah ba zaki gane ba. Tunda ba aure kika yi ba ba zaki san gatan da ake musu ba. Wannan ai sirrinsu ne"

"All this ana yi dan namiji ne ko?. Let me tell you one thing, idan kuka ga dama ku yiwa Pussy ɗinsu ado da gold da diamond Wallahi ba zasu taɓa isan mazajensu ba. They will either cheat outside ko kuma su auro mata huɗu kamar yadda Dad yayi"

"Anty Sayyidah Pussy kam ba kyanwa ba ce?"

"Mi kike a nan?"

"Anty Amarya ba ke kika ce na kawo miki kular abincin Kaka ba"

"Tashi ki bamu waje. Manya na magana kina saka baki"

"Anty Amarya to abincin fa. Ko na shiga kitchen na ɗiba" ina maganar ina yin hanyar kitchen.

"Tsaya, tsaya yanzu na gama mopping kitchen ɗina"

"Ni kam Anty Amarya ko da harshenki kike mopping ɗinne?"

Gaba ɗaya falon suka saka dariya. Ina ji Anty Sayyidah na tambayar wai ni 'yar waye ce Anty Rayyanatu tace 'yar marigayi Uncle Sulaiman.

"Oh! Ita ce Sahla"

"Ni ce Sahla, Anty Sayyidah" na amsa ba tareda an yi dani ba. Na karisa na zauna a carpet kusa da kujerar da take zaune.

"Anty Sayyidah jiya na ga Uncle Faruku Wallahi ba karamin kama kuke ba, sai kace 'yanbiyu"

Dariya ta saka tace " you are funny. Ina fatan baki kira shi da suna Faruku ba. Idan kina son ranki da lafiya kar ki sake kiranshi da wannan suna"

"To Anty haka Kaka ke kiranshi"

"Salamu Alaikum. Rafee'atu wai so kike yunwa ya kashe ni ne"

Kaka ta sangalo kafafuwanta cikin falon.

Anty Amarya da ta fito daga kitchen tace " Laifin 'yar ki ce ta kawo kwano ba ta yi magana ba ta tsaya jin gulma"

Kaka ta kalloni ta ce " Sahala maza karbi abincin ki kai mana ɗaki ina zuwa"

Na karɓi abinci na fita ina jin haushin Kaka dan ta ɓata min damata a wajen Anty Sayyidah. Kila idan na lallabeta za ta bani kyautar takalminta wanda ta saka ranan da suka fara zuwa.

Na ɗan laɓe jikin kofa dan na ji wani gulman Kaka za ta yiwa su Anty Amarya.

"Na ce Rafee'atu kwanaki da aka yi biki a gidan nan Aishatu ce ta ja ragamar girki. Ɗan chinchin, Alkaki da su Dibulan na biki duk bata ware min nawa ba. Shegiya har wata uku bayan biki tana nan da su a ɗakinta ta ɓoye. Shiyasa nace tunda shi Kabirun ya baki ragaman biki wannan karan dan Allah ki ajiye min kaso na dan irin mutanen da ke zuwa min barka bayan biki su samu abun taɓawa"

"Hajiya Kaka ni gaskiya ba zan iya miki alkawarin komai ba yanzu. Amma idan aka gama biki abubuwa suka saura tabbas za a saka ki cikin rabo"

"Allah dai ya saka miki da Alkhairi Rafee'atu. Allah yasa nan da wata tara ki samu kazantar ɗaki"

"Amin Hajiya"

"Na ce yau ba ki yi mit faye ɗin bane? (Meat pie)"

"Na dakatar sai bayan biki"

"To to to, barin wuce kar yarinyar nan ta je ta tsame naman cikin abincin nan"

Ina jin haka na ruga da gudu...

***

Kuka nake a ɗaki ina birgima da kafafuna. "Wallahi ba zan saka ba. Dan Allah Kaka taya zaki ce a min irin wannan ɗinkin. Ki ga kayansu Amal masu kyau amma sai ki sa a min riga da zani. Allah ba zan ɗaura sani ba"

"Ja'ira kawai, idan baki ɗaura zanin ba uban mi zaki saka?"

"Allah na fasa saka ankon"

"Wayyo Babanaaaa"

Na cigaba da kukana. Babu yadda za ayi kowa ya saka skirt ni na ɗaura zani a wajen biki kamar wata tsohuwa. Kaka ta cuceni.

Ina cikin kukan Affan ya shigo.

"Wai minene nake jin kukan Baby na tun daga waje"

"Ka tambayeta dai. Yau sakarcinta ne suka motsa"

Ya karitso gabana yana goge min hawaye.

"Tell me, mi aka miki?"

Cikin kuka na sanar da shi abinda ya faru.
Yace kar na damu na ɗau zanin na biyoshi zai kaini shago a maida min shi skirt.
Tuni na mike na fara goge fiskana ina murmushi...

Muna zuwa bakin mota na ga Dodo yana jiranmu. Wannan karan ya toshe fiskarsa da bakin gilashi.
Affan yana shirin yi masa bayani akan zai fita aika da mota amma Dodo ko saurarenshi bai yi ba ya shige motar yai wani wawan reverse ya barmu tsaye kamar wasu shashashu. Dama ni kam tunda muka iso wajen na sha jinin jikina nai wa kaina salamun alaikum kar ya sake shakeni irin na ranan.

Haka dai maganar gyara zani ya lalace dan kuwa shima Affan ɗin kiransa aka yi a waya yace yana zuwa amma har yamma shiru. Duk Dodo ne ya jawo wannan. Da ya bari mun fita da mota da duk hakan ba ta faru ba.

Ina bibiyarsa har ya dawo daga yawon shi. Irin takalmin nan ne dai na ranan ya saka amma irin kalar ta ranan ba. Na dinga binsa a baya har mu ka je sashen Alhaji. Kamar dai ya san ina binshi amma bai juyo ba. Bai cire takalminshi ba a kofar falon, da shi ya shiga. Na san dai Alhaji baya nan, dan jiya ya zo yaiwa Kaka sallama akan zai je Abuja sai gobe zai dawo.

Kashin awaki dana ɗebo a leda na fara barbaɗawa a kofar falon. Duk rintsi dai idan ya fito sai ya taka. Ina gamawa na yar da ledan a wajen na yi gaba ai ban yi taku biyu ba na ji an cafko ni.

"Zo ki share dan Ubanki. Sahla ashe ke shasha ce. Maza ki kwashe da hannunki ko na faffasa miki jiki"

"Ka yi hakuri Yaya Mustafah"

"Wallahi sai kin kwashe da hannunki. Idan tashen balaga kike ji da shi ba a mu zaki yiwa ba. An gaya miki F K sa'anki ne. Shegiya mai ido kamar na mujiya"
Ya karasa maganar da yi min kyawawan rankwashi guda biyu.

Wallahil Azimu haka Yaya Mustafah ya tisani a gaba na kwashe kashin Awakin nan na maida su cikin leda. Zan tafi na ji an ce "tsaya"
Uncle Faruku shine babba amma a girman jik Yaya Mustafah ya fi shi.

"Ki cinye abinda ke ledar nan"

"Qalu Innalillahi. Dan Allah kayi hakuri Wallahi na tuba"

"F K kamin daidai. Oya buɗe ki fara ci"

"Wallahi ba zan sake ba. Uncle Faruku na tuba ba zan sake ba. Ka yafe min Dan Allah"

In takaice muku labari duk magiyar da nake Dodon nan bai saurareni ba, wayarsa ma yake dannawa abinsa. Shi kuwa Yaya Mustafah sai cewa yake wai maganina kenan.

Da na ishe su da kuka sai ya chanja punishment ɗin yace wai na murza kashin na shafa a fuskata.
Allah ya isa Uncle Faruku. Bullukutu, ba zan yafe ba har abada.

Ban san ya aka yi ba su Amal suka ji labari suka zo wajen sai dariya suke min kasa-kasa.

Ina shafa kashin a fuskata aka fara kiran sallar magariba. Yaya Mustafah ya roki Alfarma akan a barni haka nan.

Kafin na karisa ɗakin Kaka ma labarina ya zaga ko'ina. Gashi gidanmu a cike yake da mutane dan saura kwana biyu a ɗaura aure.

Duk ɗokin bikin nan da ake yi sai na ji ya fita a kaina.
Ko mi na Sahla dai akwai rashin sa'a.

Duk wani bidiri da bushasha da ake na biki na ki saka kaina ciki. Na makale a ɗakin Kaka na ki fita ko ina. Ko kayan ankon da aka gyara min ban saka ba. Kaka ta yi korafin ta yi faɗan amma ban kulata ba.

*

Yau za ayi Luncheon da yamma, gobe kuma ɗaurin aure. Gida ya cika sosai. Ɗakin Kaka ma cike yake da tsoffi 'yanuwanta anata shiga da fita da abinci. Rabon dana ci abin kirki tun kafin Dodo ya ci min mutunci.

Tun safe aketa buga tambura. Wallahi idan ban rama abinda aka yi min ba ba zan huce ba. Wallahi sai na ɓata musu biki.
Da Kaka ta dameni akan na je na yi wanka na shirya tunda an kusa fara event ɗin sai kawai na fita daga ɗakin na ce mata zan je sashen su Mama na je na shirya.
Kun san dai idan ana hidima ba a cika damuwa da yara ba. Balle yara 'yan gaban goshi irinsu Amal sun riga sun ɗauke musu hankali.

Na fice daga gidan ba tareda an tareni ba. Gidansu Kulu mai ɗauke-ɗauke na shiga dan rabin 'yan gidansu suna gidanmu anata aikin biki da su. Itama na san saboda matsalarta ne aka hanata zuwa. Ranan da ta zo yiwa Kaka barka lokacin da aka kawo lefen su Anty Firdausi sai da ta ɗauke kwalin lipton, comb da kuma naira hamsin ɗin Kaka.

Na yi sallama muka gaisa. Tace na shigo nace mata ba sai na shigo ba. Kar na shiga ta sace min takalmi ko ɗankwalina. Na ce mata dama tambaya nake ko Awakan Inna Laraba sun tafi kiwo. Tace min sun tafi kiwo amma zuwa anjima zasu dawo. Nace mata to.
Na koma gida na samu su Kaka sun wuce wajen da ake Luncheon. Ya min dai dai dan bana so a ganni. Na je na kunce Awakin Kaka su guda takwas na kaɗa su ta baya inda ake girke-girke, Awakan Kaka kuwa 'yan iska ne ba abinda basa ci. Ga su da ɓarna. Alhaji ya hanata kiwon ta ki. Yace ta kawo su ya haɗa da nasa dake gidan gona ita tace sam ai kiwon dabbobi a gida yana kaɗe fitina.

Na juya na yi tafiyata. Na tsaya ina dakon Awakan Inna Laraba. Ita da yake kiwonta kenan tana da su sun fi ishirin. Na kalli wasu Almajirai guda biyu na ce idan suka koro min Akuyoyin Inna Laraba cikin gidanmu zan basu naira ishirin-ishirin.

Kusan karfe shida saura lokacin Luncheon yayi nisa. Sai ga Awakai sun nufo gida. Ba wasu mutane a gate ɗin sosai. Na wangale musu gate ɗin gidan Almajiran nan suka fara koro min su.

Wata mata na min kai kai, wai kada na bari su shigo nace Awakan gidan ne lokacin shigowarsu gida kenan.
Ni da Almajirai muka shiga koran Awakai zuwa ta wajen parking space inda aka kafa tanti ana event. Kiɗa ke tashi dan haka basu ankara da hayya-hayya da ake ba. Waje ya ɗan fara duhu dan dare na yi da wuri yanzu.

Na koma gefe ina dariya abina. Ba abinda kake ji sai Meee Meee Meee ɗin Awakai. Ana kan koransu suna kara shiga cikin jama'a. Abinka da mata sunfi yawa a wajen sai ihu ake da guje-guje. Akuyoyi da suka ga abinci sai suka kara zagewa suna ta shiga cikin jama'a suna neman abinda za su ci. Wata Akuya har da hawa table tana cin fried rice a cikin plate.

Abin ya zo musu bazata da mazan da matan duk rikicewa suka yi sai neman tsira ake. Meeeh Meeeh Meeeh ɗin Awakai ya cika ko'ina.

Allah ya kaimu gobe a ɗaura aure Lafiya...



***

004 Asirina ya tonu...

Shekaranshi huɗu rabonshi da zuwa Nigeria. Wannan karan ma Mustafah ne ya dage akan lallai sai ya zo bikinsa, ga kuma Alhaji da yake ta damunsa akan maganan auren Sayyidah. "Kai namiji ne Aliyu akwai lokaci a gabanka, amma Sayyidah fa. Tayi degree tayi masters mi kuma take jira?"

Ya san dalilin da ya hana Sayyidah aure, amma kuma ba zai iya faɗawa Alhaji a irin wannan yanayin ba, so yake idan an gama bikin yaran nan kafin su tafi sai ya zaunar da shi ya masa bayani, ya rage na shi yaiwa Sayyidah zaɓin daya dace.

Bai taɓa zuwa garin nan yayi irin wannan kwanakin a gidan Alhaji ba. Duk yawancin zuwansa a Fada yake sauka. Wannan karan ma Mustafah ne yayi sanadin zamanshi a gidan har zuwa wannan lokaci. Duk da ya sani Mustafan yayi hakane saboda wata manufar shi. Duk inda za su shiga haka zai dinga faɗawa mutane wai a UNESCO yake aiki.

Bai taɓa zuwa garin nan ya tsinci kansa cikin nishaɗi ba irin na yau. Tunda suka zo bai taɓa yin dariya ba ma sai yau. To him wannan luncheon da aka haɗa duk shirme ne, shiyasa ma da farko ya ce ba zai attending ba, amma da Mustafah ya nace masa dolensa ya hakura yace zai leka wajen kona minti goma ne.
Kamar yadda Mustafan ya faɗa kuɗine babu a hannun Alhaji shiyasa ya dage akan ba za ayi wani hidima ba.
Dinner da aka saka ma shi ya hana ayi, shine su Anty Rafee'ah suka ce to ayi luncheon a cikin gida tunda akwai fili da zai ɗauki mutane. Ba karamin kuɗi suka tatsa a wajensa ba saboda wannan hidima. But to think that minti takwas da zamansa a wannan waje Awaki zasu invading wajen su kori mutane ya sa shi jin daɗin wannan luncheon da aka haɗa. Ba ma mutanen da ke gudu ne suka sa shi dariya ba. Wata yarinya ya hango sai daɗa kora Akuyoyi take cikin mutane. Ga chan wasu maza a gefe suna poli da Akuyoyin suna koransu ita kuma yarinyar idan suka iso ta wajenta sai ta sake kora su baya, gaba ɗaya dabbobin sai suka ruɗe sai ihu suke Meeeh Meeh Meeeh suna kokarin shiga cikin mutane tunda an hana su karisawa can cikin filin sannan an hana su fita.
Yana gani yarinyar ta shiga kaɗa wata Akuya wacce takalmin wata mata ya makale mata a kaho, takalmin sai reto yake kamar wani crown. A wannan lokacin ne ya ga fiskar yarinyar da kyau. A wannan lokacin ne kuma ya shiga dariya harda kyakyatawa.
Tabbas yarinyar nan ce da wannan aiki, ya sani sarai ita ce ta kaɗo Awakan nan zuwa wajen taron nan. Karfin halinta ya burge shi. A ce yarinya mai shekarunta za ta iya aiwatar da irin wannan abu tabbas abin jinjinawa ne, she's a freaking genius.

Kokarin tuno sunanta yai da kuma 'yar waye ce a gidan tunda ba wai ya gama sanin fuskokin kannen nashi bane. Baya iya banbance asalin kannensa da kuma cousins ɗinsa.

2 Comments On SAHLA A PARIS
avatar
mahamane-noura

1 year ago

Reply

Ya sanyi don ?aukar novel dan Allah

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to mahamane-noura

Domin downloading novel na mu dole fa sai kayi subs da mu

Please Login or Register in order to submit comment