Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Amma wani hanzari ba gudu ba. Idan su Alhaji suka ji labari ba zasu bari ba"

"Eh hakane. To ya za ayi"

"Ai ki dage musu kafarki na ciwo kuma kina son ki chanja Asibiti, likitocin Egypt dana Nigeria duk basu iya aiki ba. Ke yanzu wajen Faruku zaki je ya nema miki likitoci masu kyau a Paris"

"Kina ga zasu yarda?"

"Zasu yarda Kaka amma sai kin yi abu ɗaya"

Kaka ta buɗe ido tana saurarona.

"Duk rintsi kice musu da Sahla zaki je. Kice idan ba da ni ba kin fasa"

"Kai amma Sahala Bokon ki yayi amfani. Ai muna zuwa can wajen Farukun sai mu dage sai ya kaini Makkah ko?"

"Peww. Kaka ni da ke sai mu lula Paris kawai"...

Step 1- shine Kaka ta langaɓe ta kuruta ciwonta. Hakan kuwa aka yi da Alhaji ya shigo ta langaɓe tana masa complain iri-iri. Yace bari ya ɗau mota a kaita asibiti tace masa ita ba ta gane asibitin nan. Dake dama ta kwana biyu ba a kaita Egypt ba sai yace zai yiwa Abba magana a fara shirin tafiyarta Egypt.

Step 2- Kaka ta kekasa kasa tace allanfir ta gaji da Egypt ɗin nan. Duk yadda za ayi kawai a chanja Asibiti. Shekara da shekaru tana zuwa Egypt amma sai dai ciwo ya lafa ya sake dawowa.
Alhaji ya nace dai Egypt ɗin za a kaita.

Step 3- Kaka ta fara emotional blackmail ɗinsu. Kun san dai yadda manyan mutane basa wasa da iyayensu. Abba ne ma ya fi rikicewa. Alhaji kaman ya so gano shirinmu amma da Likita ya confirming jinin Kaka ya hau sosai sai ya ɗan saduda.

Step 4- sun amince zasu yiwa Faruku magana, idan ya amince sai Abba ya rakata Paris. Kaka tace sam babu wanda zai rakata sai Sahala.
Alhaji ya ce ai ina zuwa makaranta. Kaka tace kusan wata uku kenan ana yajin aiki wayasan yaushe za a dawo.

Step 5- anyi meeting. Ance Yusuf ko Sulaiman ne zasu rakata. Sulaiman yana law school an cire shi. Yusuf ya bada uzuri saboda shima zai rubuta professional exams ɗinsa na zama cikakken Medical Lab Scientist. Abdullahi ba shi da nitsuwa. Abbas da Abbas ba hankali. Sahla, Sahlan dai to ya za ayi...

Duk abinda ake ciki na yi likimo kaman ban san komai ba har sai da aka gama kai ruwa rana akace an amince zan raka Kaka jinya.

Abba ne ya kaimu Abuja inda za a min passport da sauran documents na tafiya.

Oh my Goodness. Sahla zata je Paris. Let me scream. Jama'a zan je France, zan bar Nigeria zan je Paris, France.

Hanifah har ɗaki ta biyoni tana min kumfar baki. Na mata kwalele nace aga-aga waye zai fara shiga jirgi a cikinmu.

Aka gama kananun maganganu, aka gama gulman aka zuba mana ido. Na zama Sahla ikon Allah.

Ban san ya aka kare da Uncle Faruku ba amma tunda aka fara shirye-shiryen tafiyarmu na san cewa ya amince. To ya ma isa yace bai amince ba.

Ni kam tuni na bazama sunday market na siyo kayan sanyi dayawa. In Allah yasa na bar Nigeria to ni da dawowa sai na kammala karatuna. Ni ASUU zasu ciwa mutunci. Ko sun ki ko sun so sai na kai matsayin Professor.

Anty Amarya da ta zo ta ga kayan tayita min faɗa wai sai kace me shirin kaura. Ai ba haka ake ba. Ta shiga rage min kayan, zuciyata kaman zata fashe. Ko dai itama tana bakin ciki da tafiyata me. Kai amma Anty Rafee'ah bata da mugun zuciya.

Abuja aka kaimu ranan Monday, ni ina tunanin nice zanyi jagoran tafiyar kawai aka taka min birki wai Uncle Faruku na jiranmu a Abuja.

Bamu haɗu ba sai safiyar da zamu tafi.

Na gaishe shi ina kokarin yi masa godiyar iphone ya shige mota abinsa.

Inaga jifa aka min daga Gombe. Sai da muka zo airport na tuna cewa ashe baro jakar da aka saka mana documents ɗinmu a gidan Baffanmu Ɗahiru.

"Uncle Farukkk Dan Allah a tsaya nayi mantuwa"
Ba tareda ya juyo ba yace " minene?"

"Visa na manta a gidan Baffa"

"Laa. Sahala ba ance ki bawa Baffanki takardun ba idan muka iso"

"Mantawa nayi Kaka"

Ya ɗau waya ya kira Baffanmu ya gaya masa abinda ya faru. Muka tsaya kusan minti goma kafin ya kira yace an gani za a kawo.

Juyowa yai ya kalleni. Muna haɗa ido na ji wani tsoron shi ya shige ni. Anya banyi kuskuren biyo Kaka ba. What if shima kaman Affan ne, gashi nan tsohon tuzuru da shi.

Allah dai ya taimakemu da aka kawo jakar backpack ɗina aka samu documents ɗin a ciki dan har na fara wasu-wasin ko dai ba a ciki suke ba.

Dake mun ɓata lokaci ko minti goma bamu yi ba aka fara kiran passenger jirgin da zamu shiga. Na riko hannun Kaka muka fara binshi a baya dan tuni yayi gaba ya barmu.
Yau dai zan shiga jirgi, yau dai sai Paris...



015...✈✈✈SAHLA a Paris✈✈✈



***

Ban ɗauka zaman jirgi akwai wahala ba. Na ɗauka kaman yadda nake gani a film ne, wato kowa zai zauna ana kallo ana cin abinci, fuuuu sai ka ji har an yi landing. Probably irin awa biyu ko uku ɗin nan.

Gaskiya na zaunu. Ko dai dan ban taɓa zuwa wani waje mai nisa bane. Iyaka dogon tafiyata Gombe to Abuja ne. Na yi bacci na tashi amma jirgi bai sauka ba.
Kaka kam ko ajikinta, ita da ta saba shiga jirgi kenan. Lokacin da fitsari ya matseni sosai sai na ɗaga hannu sama. Kaka tayi bacci. Wata flight attendant ta zo wajena, nace mata zan yi fitsari. Ta raka ni banɗaki. Ina shiga banɗaki sai amai, duk abinda na ci a cikin jirgin nan sai dana amayar da shi.

Na gama aman na wanke fuskata na fito. Ina takowa a hankali muka haɗa ido da shi. Littafi yake karantawa amma yana ganina ya sauke littafin yai min tambaya da ido irin 'are you OK' ɗin nan. Na girgiza masa kai alamar babu komai. Na koma wajen zamana na zauna, har yanzu Kaka bacci take nima na gyara zama na mike kafafuwana na kwanta.

Kusan awanmu tara ko goma a sararin sama kafin jirginmu yai landing. Zuwa lokacin na yi wani laushi. Gaba ɗaya na kagu mu sauka. Har wani zazzaɓi nake ji. Ga yunwa kamar hanjina zasu tsinke. Na kasa cin komai a jirgin nan har muka isa
Charles de Gaulle airport.

Mun isa Paris da dare. Ina tunanin zan ga anzo an ɗaukemu da wani babban mota amma da muka fito sai naga Uncle Faruku ya tsaida mana taxi.
Aka shigar mana da kaya cikin boot muka fara tafiya.

Ni dai zuciyata ta fara raya mun anya Uncle Faruku na da kuɗi kamar yadda mu ke hasashe. Taya za a ce mun sauka a airport ba za a zo a ɗaukemu ba kaman yadda ake a littafi ko film.

To ko dai direbansa baya nan ne?

Inata sake-sake har mai taxi ya tsaya a a wani katon gida.
Daga korafi sai na koma sake baki galala ina kallon mansion ɗin da aka kawo mu.

"Yanzu wannan gidanka kenan ko Otal?" Kaka ta riga ni furta wannan tambaya dan abinda ke raina kenan.

"Kaka gidana kenan"

"Ya Subhanallahi! Faruku shekara da shekaru kana zama a wannan ɗimemen gida kai kaɗai. Gaskiya ba zai yiwu ba idan na koma dole mu yi zama da iyayenka, dole ne ka ajiye iyali"

Shine a gaba muna biye da shi har muka isa kofar gidan ya buɗe mana kofa.
Muna shiga wani ɗan corridor muka fara gani sannan muka karisa cikin wani makeken falo. Kai! falon nan zai yi falon Alhaji biyu. Falon na haɗe da dinning area. Daga ta jikin dinning ɗin akwai staircase da zai kai ka sama. Komai na falon fari ne da ruwan toka. Curtains ɗin ash ne kujerun kuma farare. Babu wani tarkace a falon dan akwai enough space a wajen. Akwai paintings dayawa da aka saka a jikin bango. Wasu paintings ɗin na flowers ne ko na bishiyoyi sai guda biyu wanda suka fi girma suka fi ɗaukan hankali. Ɗaya painting ɗin na wata tsohuwa ce ɗaure da zani wanda bai gama rufe mata kirjinta ba, tana zaune a bakin wani bukka idanunta cike da damuwa kamar zata yi kuka. Zanen ya tsaya min a rai domin ya fito raɗau kamar hoto Black and white ɗin nana.

Zane na biyu na wani yaro ne da aka rufewa baki daga ta baya. Yaron ya zaro ido kamar yana ihu aka rufe bakin.

"You should go and rest"
Na waigo a tsorace dan ban san yana bayana ba.
Kai Uncle Faruku dogo ne, dana juyo sai dana ɗaga kaina kafin na kalleshi da kyau. Fiskarsa babu fara'a ko kaɗan, kamar dai ba a son ransa muka zo Paris ba.
To ko ma yanene ni kam na zo kenan babu komawa.

"Uncle F Kay wannan zanen yayi kyau" na nuna masa zanen yaron.

"Yayi kyau?" Ya faɗa a fusace.

"Yayi kyau? Ya sake nanatawa. Kamar ya damu sosai da zanen.

"Uncle Faruku ba zane bane? So kake in ce bai yi kyau ba. To bai yi kyau ba shikenan"

"Of course, zane ne, kawai"

Ya juya ya bar wajen.
A'a ku ji min fa. Ba zane bane. Na sake juyawa na kalli zanen. Still zane ne amma ya fito kamar hoto.

"Sahala duba min jakar hannunki ki ciro min Aɗaralbakur in shafa a kafana"

Kaka kam tuni ta samu kujera ta zauna ta mike kafafunta.

"Kaka ni ban ɗauko wani Adaralbakur ba fa"

"Aboniki fa?"

"Kaka babu " na samu na zauna nima ina mike kafafuwana a kan kujerar.
Bacci nake ji, ga kuma uwa yunwa da yake cina tun a cikin jirgi.

Fitowa yai daga wani ɗaki yace "Hajiya ga ɗakin da zaku kwana nan. Ya kamata ku je ku huta"

"Ɗan nan kana da Aɗaralbakur ko Aboniki? Kafafuna kamar zasu karye"

Ina kallonshi ya fara rarraba ido irin bai gane mi take faɗa ɗin nan ba.

"Kaka waya gaya miki akwai Aboniki a nan. Nan fa Paris ne, Paris"

"To 'yar kinibibi, shi Parish ɗin ya kai Makkah ne?"

"Kaka Paris ba Parish ba"

"Ikon Allah. To ni dai Faruku ka nemo min maganin zafi na shafa a kafata"

"Uncle F Kay nikam yunwa nake ji. Hanjina zasu tsinke idan ban ci abinci ba nan da minti biyar"

Ya kalleni kamar zai yi magana sai kuma ya fasa ya juya, inaga kitchen ya wuce.

Lokacin daya dawo har na fara gyangyaɗi. Biscuit ne da cornflakes (cereal) da kuma tea ya haɗa mana. Ina ji yana faɗawa Kaka tayi hakuri babu abinci a gidan kuma ba zai iya order ba saboda dare yayi sosai.

"To babu mace a gidan ina za a samu abinci. Shiyasa kaketa tsayi babu jiki tunda ba abincin matarka kake ci ba"

Na sha tea ɗin sosai dan zafin tea ɗin ya warware min hanji.

Bayan mun gama ya nuna mana ɗaki muka wuce. Tuni ya shiga mana da kayanmu ciki. Ɗakin babba ne haɗe da toilet ɗinsa.
Banɗakin na wuce dan na watsa ruwa. Duk kazanta na ba zan iya bacci babu wanka ba, dan jikina ciwo yake min, da zan samu man zafi ko kuma a min massage ba karamin daɗi zan ji ba.

Allah na gani tsabar gajiya ko sallah ban yi ba. Ina ji Kaka tana cewa in tashi in yi sallah kafin na kwanta amma na shareta. Ban taɓa kwantawa a gado mai laushi haka ba. Astagfirullah gadon Anty Rafee'ah ma akwai laushi fa.

*

Da safe muryan Kaka da wasu yara ya tashe ni. Bacci bai isheni ba, ga ciwon kai. Wai ma tukunna wasu yara ne waɗannan?. Uncle Faruku ai bai taɓa aure ba.

" Faisal look at her face" karamin yaron ya faɗa yana taɓa ɗan'uwansa. Kaman dai na so gane fiskar Yayan amma ban tuna a ina bane.

Sai wani dariya suke min. Ko mi suka gani a fiskata oho.

"Kai! Miye kukewa dariya"

Nifa na ɗauka da mun zo Paris babu wani hayaniya kuma. Amma sai ga shi daga tashin farko yaran nan sun sani a gaba suna min dariya.

"Kaka wai su ɗin su waye?"

"'Ya'yan Hasinah"

"Anty Hasinah ta zo ne?"

"A'a"

"To aka yi suka zo?"

"Ki tashi ki zo ki yi sallah"

Na mike tsaye ina tura baki.

*

Lokacin dana idar da sallah Kaka da yaran sun fita daga ɗaki. Tun ina sallah dama wani kanshi ya shake min hanci.

Shine da kansa ke serving ɗinsu, yana sanye da shirt sky blue da jeans dark blue ya saka black apron kamar wani chef.

"Ikon Allah! yanzu kai kake girki kullum. Ni Fatima na ga abu da yaran zamani. Faruku Allah ya hore maka komai amma ba zaka ajiye iyali a gida ba"

Na katse Kaka ta hanyar gaishe shi. Ya ɗaga ido yana kallona dai dai yana zubawa Faisal soyayyen kwai a plate ɗinsa.
Ban san ya akayi idanunsa suka min nauyi ba. Na kauda kaina na zauna kusa da Kaka. Tsohuwar nan tana kwasan abinci tana korafi.

Ban ɗauka Uncle Faruku yana da saukin kai haka ba. Har yana iya yin girki da kansa. Koda yake tuzuru ne fa.

Sai dai duk tarkacen da aka jera babu wanda ya ɗauki hankalina saboda ni yanzu abinci mai nauyi nake so, ko ɗumamen tuwo ko kuma shinkafa da wake da miya. Su wani pancake su wani kwai da toast duk kayan kwalami ne ni kuwa irin yunwar da nake ji ba iya rike min ciki zasu yi ba.

"Uncle Faruk babu ɗan shinkafa ne na ɗan dafa wannan kayan kwalamin ba zai rike ni ba"

Wani irin kallo ya min na yi saurin gutsuro pancake daga plate ɗin Kaka na fara turawa baki da sauri...

*
Ranan wanka dai ba a ɓoye cibi. Bayan mun gama karyawa yaran sun tafi makaranta Uncle Faruk ya zaunad da mu yana faɗa mana tsare-tsaren gidansa.

Daga gobe zai fara zuwa aiki dan haka ba zamu dinga ganinsa kullum ba. Akwai wata mata Mrs Dupont ita ke zuwa ta gyara gida kullum sau ɗaya a rana. Shi yake girki da kansa kuma idan baya nan ya kan order abinci daga African ko kuma indian restaurant ko kuma ya siyawa yaran pizza idan suka bukata.

Yana kawo maganar zuwa Asibiti ni da Kaka mu ka kalli juna. Ya cigaba da cewa ya riga ya yiwa Kaka booking likita ranan Jummu'ah ne appointment ɗinta kafin nan ta huta sosai. Idan suna so suyi girki zasu rubuta list shi zai bayar a kawo musu.

Yace idan babu wata matsala shi zai fita.

Ni yiwa Kaka signal akan ta masa magana.

Kaka tace " Faruku Allah dai ya maka albarka. Wannan karamci da ka mani Allah ya amsa maka bukatunka"

Ya amsa da Amin.

"Wato maganar gaskiya Aliyu..." ta yi shiru.
Wai yau wace rana Kaka ta kira Uncle Faruku da asalin sunansa. Sunan Baban mijinta ne saboda kunya nasu na mutanen da, yasa ba ta taɓa kiran sunan.

"Ka ga yadda Allah ya rufa maka asiri nake so kaima ka taimaka ka rufa mana asiri. Ba sai mahaifinka ya ji wannan zance ba. Tsakaninmu za a yi komai. Allah kuma zai baka lada"

Cikin kallo dake nuna rashin fahimta yace " Hajiya ban gane mi kike faɗa ba?"

"Ka ga iyayenka sun ki biya mini kujeran Makkah, wai saboda ciwon kafa dake damuna. Ka taɓa jin inda ciwon kafa ya hana aikin lada?.

Ya girgiza kai

"So nake ka biya mini hajjin bana. Yadda Allah ya hore maka nima ka cika min buri na"

"Hajiya ban fahimci maganarki ba"

"Na ce dama ba ganin likita ya kawo mu nan ba. Makkah nake son zuwa, idan da rabo kaga sai na samu tsira a chan"

Like ransa yayi mugun ɓaci, ya juyo ya kalleni fiskarsa a tamke, tamkar ya san cewa ni na haɗa abin.
Tashi kawai yai ya bar wajen ba tareda yace komai ba. Ni da Kaka muka bishi da kallo.

Ganin ya jima bai sauko ba Kaka tace na bishi na bashi hakuri ya sauko ayi maganan.
Na haura saman nima a hankali. Ban san wani ɗaki ya shiga ba na fara buɗe ɗakunan dake saman. Dukka babu wanda ya buɗe sai a na uku.

Babu kowa a ɗakin sai na lura kaman akwai inuwar mutum ta wajen window. Na leka wajen ashe irin balcony ɗin nan ne na gidajen masu kuɗi. Har da kujera da karamin table da litattafai a wajen. Da alama a wajen yake hutawa.
Yana tsaye ya ya rike wani abu a bakinsa.
"Laa!" Na faɗa ina kama bakina.

Subhanallahi! Sigari ne a hannunsa.
Sigari katuwa irin ta masu kuɗin nan"

Ya juyo ya kalleni muka haɗa ido da shi ya zuki sigarin ya furzar min dai dai fiskata

Na ɗan tsorata da ganinsa a haka. Mi kuma yake sha bayan shan sigari?.

Koda yake Abban su Amal ma na shan irinta, na taɓa kama shi yana sha lokacin ina yarinya, i think 7 or 8 yrs haka nan. Lokacin har Kaka na kaiwa gulman nace mata na ga Abbansu Amal yana shan wuta bakinsa yanata fidda hayaki. Kaka ta fara salati.

"You know" yai karamin murmushi irin wanda sai dai kaga gefen bakin mutum ya motsa ɗin nan.

"Lokacin da Dad ya kirani ya min maganar ku sai da zuciyana ya riya min ke ce da wannan aiki. There's no way Hajiya za ta yi tunanin zuwa Paris jinya bayan shekara da shekaru Egypt ake kaita. Unless idan witty jikarta ce ta convincing ɗinta"

"Uncle F Kay..."

"Ba na son mutanen da basu da gaskiya. Ki gayawa Hajiya ta shirya you're going back to Nigeria"

"Uncle Faruk Dan Allah kayi hakuri please. Allah, Kaka ta damu da zuwa aikin hajjin bana, abin kaman ya taɓa mata kwakwalwa har a barci take sunbatun haka. Kayi hakuri na san baka ji daɗin karyan da muka maka ba"

"Mi kuka ɗaukeni? That i'm stupid?"

"Ba hak..."

"Ke!"

Na yi baya da sauri dan a yadda yake na san kiris ya rage ya managare ni.

"I hate liars. Ki je ki maida kayanki cikin jaka yanzu zan kira Dad na gaya masa"

Ya ɗauko waya daga aljihunsa yana shirin dannawa. Na yi karfin hali na cafke wayar. Ina shirin guduwa ya kamani.

"Dan Allah ka yi hakuri ka barmu a nan. Wallahi ni da Kaka kowa da mission ɗinsa na zuwa kasar nan. Idan ka koremu dariya za a mana"

"Give me the phone"

"In na koma Nigeria yanzu wuta bal bal. Allah ban zo dan na koma ba. Kayi hakuri kawai ka barmu a nan"

Ina maganan zuciyana yana buga kirjina bukbukbuk kamar zai faɗo. Yau idan ya komar da mu Nigeria ai anyi ba ayi ba kenan. Yaushe ma zan iya ganin idon mutane bayan na je na cika baki a kan zamana a Paris. Ni karya nayiwa su Nazifa ma akan admission za a nema min a Paris shiyasa na zo saboda a min interview.

Kamar wani abu ya cizeshi lokaci guda ya tureni daga jikinsa da karfi sai da na bugu da table ɗin da ke wajen.

Wayyo kaina!

***

Alhaji, Abba da kuma Baffa Abubakar ne ke zaune a wajen wasu kujeru na shakatawa a kofar gidan Abba.
Abba na rike da Ayman yana masa wasa. Ga su dai yaya da kani amma yanayinsu ya banbanta, idan ba kamannin jini ba babu ta inda suke kama. Alhaji ya ɗauko bakin mahaifinsu da tsayin shi, dogo ne sosai dan a wajensa Faruk ya gaji tsayi. Har yanzu da yake cika shekaru sittin da bakwai ba zaka kira shi da mai kiba ba, girma ya saka shi yin nama amma bai ajiye tumbi kaman kaninsa Abdulkarim ba.

Abba shi ya ɗauko farin Kaka. Sosai yake kama da Kaka, dan a nan ya ɗauko gajarcinsa. Sai dai kuma saɓanin Kaka da bata da kiba shi ya je ya ɗebo kiba daga wajen kakarsu mace wacce ake kira Hajja Gambo Allah ya jikan rai.
Hutu da jin daɗi ya sa Abba yai wani mummunan kiba ya ajiye tumbi. Wuyansa kaɗai idan ka gani zaka san Allah yayi mai kiba a nan. Wannan yasa duk yaransa suka ɗauko kibansa idan ka cire Amrah. Matarsa ma tana da kiba dan haka suka complementing juna,.duk da kuwa ita ɗin daga baya ne tayi kiba bayan ta tara yara.

Baffa Abubakar kam yana tsaka tsakiya, ya ɗauko farin mahaifiyarsa Hajia Sadiyya sannan ya ɗauko tsayin mahaifinsu.
A duk katafaren gidan Alhaji da Baffa Ɗahiru ne suke tsananin kama da juna dan duka zubin mahaifinsu suka ɗauko saɓanin sauran wanda sun fi ɗauko ɓangaren iyayensu mata.

Tattaunawa suke mai mahimmanci saboda harkar siyasar da Abba yake son shiga. Shi Baffa Abubakar ya tafi akan babu abinda Abba zai tsinana a siyasa sai bakin ciki da takaici. Sannan yayi kusan fiye da rabin shekarunsa a Egypt, dan haka babu wanda ya san shi a Gombe.

"Alhaji Abubakar kana ganin AbdulKarim Ubandoma zai fito takara jama'ar Gombe su ce basu san shi ba. Har an isa a manta da gidan Muhammadu Ubandoma a garin nan"

"Alhaji AbdulKarim ba wai sunan Ubandoma nake magana a kai ba. Yaren da matasa ke son ji shine mi ka yi musu kafin ka fito takara. Mi ka musu lokacin da kake Egypt. Yaya ka gaya mishi gaskiya, kai ka san abinda mutane ke so tunda kana tare da jama'a koyaushe"

Alhaji ya yi gyaran murya yace "dukkanku kuna da gaskiya. Amma Abubakar ina so ka sani cewa har yanzu ba ta ɓaci ba AbdulKarim zai iya yin wani abu akan wannan. Akwai sauran lokaci. Yana da kyakykyawan manufa ga jihar nan kuma abinda yake gaba da komai kenan"

"Duk da haka Yaya. Siyasa ba a kyakykyawar manufa ta tsaya ba. Mutane ke zaɓe ba manufa ba, su kuma idan basu gani a kasa ba babu yadda za ayi su zaɓe ka"

"Abubakar akwai lokaci. AbdulKarim zai saita lamurra"

Baffa Abubakar yai shiru. So yake yace mutane nawa Abba ya samar wa aiki ko ya ɗau nauyin karatunsu. Mutane nawa ya bawa jari. Wani project yai da guminsa da ake cin moriyarsa har yanzu?.
Ya hakura da tambayoyinsa dan yasan babu amsar su, idan kuwa ya fito da su ba lallai su fahimce shi ba tunda a iya zaman da suka yi a nan ɗin ya karanci kamar Abba na masa kallon tuhuma, ko dai hassada yake da shigarsa siyasa tunda shima Baffa Abubakar ɗin ya taɓa siyasa a baya.

Saɓanin iyayensu mata yasa har wayau da girmansu amma akwai limit a zumunci da shakuwarsu. Duk yadda aka je aka dawo akwai matakin da za a kai kaga waɗannan na ganin kansu a matsayin 'ya'yan Hajiya Fatima waɗannan na ganinsu a matsayin 'ya'yan marigayiya Hajiya Sadiyya.

Bai fi shekara goma ba da dukkansu suka zauna suka yi meeting akan wannan rarrabuwan kan wanda ya samo asali tun suna yara.

A ɓangaren su maza abin da ɗan sauki amma a ɓangaren 'yanuwansu mata abin ya ki chanjawa. Saboda kawo karshen wannan banbancin yasa Alhaji da Baffa Abubakar suka haɗa 'ya'yansu aure. To Alhamdulillah kuma tunda auratayya ta shiga tsakaninsu sai suka sake zama aminan juna.

Allah ya jikan rai, Sulaiman kaɗai ke iya faɗa musu gaskiya duk min ɗacinta. Sau da dama Kaka zata kira meeting iya 'ya'yanta shi kuma ya kira sauran yace su zo. Idan suka zo Kaka ta fara masifa. Shi kuwa Sulaiman yace sanda mahaifinsu ke raye bai sanyawa 'ya'yansa suna Kabiru Fatima Ubandoma da kuma Abubakar Sadiyya Ubandoma dan ya banbantasu ba. Dukkansu sunan mahaifinsu Muhammadu Ubandoma suke ci dan haka babu wanda ya isa ya banbanta su.
Kaka tayi ta masifa tana Allah ya isa.

A cikin sauran 'ya'yan kuma Umar ne shima mai kokarin kawo zaman lafiya tsakaninsu. Baya taɓa banbance 'yan ɗakinsu da 'yan ɗakin Hajiya Sadiyya. Har ya rasu ba shi da wani amini daya wuce Abubakar, duk wani sirri nashi a Abubakar yake faɗawa. Dama can basa shiri da AbdulKarim, Alhajinma ba sosai ba.

Allah Sarki! yau ga shi da Umar ɗin da Sulaiman ɗin duk suna cikin kasa.

"Ina wuni Baffa" muryan Amal ya katse tunaninsa.

"Lafiya Fatima Amira ko?"

Ta yi murmushi tace " Fatima Amal ne"

"Masha Allah! Ina 'yar'uwarki?"

"Amrah tana ciki"

"To Allah ya muku Albarka"

Amal ta amsa da Amin.

Peppered chicken ta kawo musu haɗe da soyayyen plantain. Bayan ta gama jera musu ta sake gaishe su sannan ta wuce.

"Ni kam yaushe Amal zata fara karatu ne?"
Alhaji yai wannan tambaya.

"Har yanzu ba a gama working transfer ɗinta ba. Ina ga dole sai na sake zuwa Egypt da kaina"

Alhaji yace "Wani tunani ya faɗo min. Na jima ina jujjuya shawaran a raina amma kuma ban tsaida magana ba. Da ina tunanin Sahla amma na yiwa kaina alkawarin ba zan yi aurawa Sahla kowa ba sai wanda take so"

Ya ɗan kurɓi juice yace " mi kuka gani

2 Comments On SAHLA A PARIS
avatar
mahamane-noura

1 year ago

Reply

Ya sanyi don ?aukar novel dan Allah

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to mahamane-noura

Domin downloading novel na mu dole fa sai kayi subs da mu

Please Login or Register in order to submit comment