Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Shi duk yaran da aka haifa shekaru shabiyar baya ba zai iya banbance kamanninsu da sunayensu ba.
Cikin sakanni goma kwakwalwarsa ta tunar masa sunan yarinyar da kuma ita wacece. SAHLA ce, Fatima Sahla 'yar marigayi Uncle Sulaiman.
Ai dole ma yarinyar nan ta yi karambani. Allah ya jikan Uncle Sulaiman kawai...

Sai yanzu ya tuna yarinyar da kyau. The last time da ya zo garin nan itane ake bashi labarin wai a wata sallar layya Alhaji ya sa anyiwa matansa da Kaka layya kowacce rago ɗai-ɗai. Kawai dan an ɓata mata rai sai ta je ta kira wasu miskinai guda biyar tace su zo Alhaji zai musu kyautan ragon layya. Malamai suka shigo ana tsaka da yanka raguna, suka shiga yiwa Alhaji godiya suna masa kirari. Alhaji ya nemi bahasi Sahla tace ai ita ta kira masa su tunda ya yiwa Allah alkawarin yin sadaka da raguna biyar wannan sallar. Abunka da mai sarauta baya son girmansa ya faɗi a gaban mutane sai kawai ya yarda da haka. Aka gama yanka rago aka mikawa mutanen da Sahla ta kawo sadaka. Allah dai yasa dama akwai Sa da Alhajin ke son yankawa wanda za a rabawa mabukata.
Bayan sun tafi da raguna Alhaji ya tambayeta dalilin wannan karya tace wai Kaka ce tace bana ba zata ba ta naman sallah ba, su kuma sauran matan kowacce da laifin da ta mata shiyasa ta ce bana babu wacce za ta samu naman layya. Maimakon Alhaji yai faɗa kawai sai yayi dariya yace shi kenan kuwa kowa zai karɓi ladan sadakar da aka yi ranan gobe kiyama. Da matan gidan suka ji labarin abinda Sahla ta aikata sai da su ka ji kamar su daɓawa Sahla wuka a ciki ta mutu kawai kowa ya huta. Amma Alhaji ya hana a daketa, yai Allah ya isa wa duk wanda ya daki Sahla akan maganar ragon layya.

Cikin naman Sa da aka yanka aka yankawa kowacce mata kasonta sauran Alhaji yai sadaka da su kamar yadda ya saba.
Ita kuwa Sahla da Kaka ta isheta da mita sai ta tattara kayanta ta wuce gidan Kawunta sai bayan Sallah da sati biyu ta dawo gida.

Gaskiya the girl is incredible ya faɗa a ransa yana daɗa murmusawa.

***

Allah Sarki! Allah Sarki!

A falon Anty Rafee'ah aka killace Amare sai kuka suke kamar wanda aka musu mutuwa. Anty Firdausi kam da warin takalmi ɗaya ta bar wajen taro. Ana ta basu hakuri. Masu Allah ya isa na yi. Ni dai ina gefe ina murmushi. Sai tambaya ake garin yaya Awaki suka shigo gidan ba tareda an sani ba. Nan Adda Sabuwa take faɗin ai har wajen da ake girki Awakan suka shigo. Sai da suka saka aka yi ɓarin miya da kuma kullin masa da aka ajiye na gobe da safe.

"Wallahi ana wannan hayya-hayya ɗin nema. Wasu mata suka shiga store suka sace daron soyayyen nama"

Anty Rafee'ah ta fusata " na shiga uku. Adda Sabuwa ba cewa nayi da an karasa suyan naman nan a kai sashen Mommyn Affan a ɓoye ba. Ba saboda haka ta baki key ba"

"Anty Amarya cewa na yi mu karisa suyan sai a haɗa a kai duka lokaci guda. To muna faman koran Akuyoyi
Wasu sheɗanun mata marasa imanin suka kwashe daron nama biyu"

"Innalillahi. Wannan wani irin abu ne. Allah ya tona asirin wanda ya aikata wannan abu"

Gaba ɗaya falon aka amsa da Amin. Ni kuma a zuciyata na ce ba Amin ba. Sai dai ban gama sauke numfashin Amin ɗina ba Abbas ɗin Ummi ya shigo falon yana kwala sunana.

"Kai kuma miye zaka shigo cikin mutane kana ihu"

"Anty Amarya Sahla ce fa ta shigo da Awakan nan. Yanzu Almajiran da aka kama suke gayawa yaya Mustafah"

Ai kafin ya karisa maganar Anty Amarya ta yo kaina tai min wani damka tareda kifa min wani mari.

Ni: "Allah, Wallahi"

Anty Amarya: "Yi mana shiru"

Anty Firdausi: "Allah ya isanmu Sahla"

Anty Aminah: "Sahla wai mi muka miki ne da zaki mana wannan zalincin?"

Anty Karima: "tashen balaga mana"

Adda Sabuwa: " Ai Sahala farar kafa ce da ita. Kun tuna abinda tayi sallar layyar bariya"

Ban iya tanka musu ba har aka tisa keyata wajen gate inda su yaya Mustafah suke tsare da Almajiran nan.

Ina zuwa aka sake haɗa mini kyawawan maruka guda uku. "Sahla ke wacce irin sheɗaniya ce kam. Kin san irin asaran da aka yi kuwa? kin san mutane nawa suka ji ciwo a dalilinki. Kin san wayoyi nawa aka sace a dalilinki.

"Oya fara tsallen kwaɗo dan ubanki"

Duk da kukan da na ke bai hana ni amsa masa ba. "Ubana Sulaiman? ko Ubana Kabiru?"

"Ke!" Ya kaimin duka na kauce ina shirin guduwa Abbas ɗin Ummi da Abbas ɗin Mama suka kamo ni.

Dana fara tsallen kwaɗon nan na ga ba halin guduwa sai kawai na faɗi yaraf na fara birgima ni a dole Aljanu.

Ina ji yaya Yusuf yana faɗin wai aje a ciro bulali wai yau sai na lahira sun fini jin daɗi. Da na ji batun bulala sai na mike na cigaba da yin tsallen kwaɗon. Yaya Yusuf mugu ne na karshe, gara Yaya Mustafah sau dubu a kansa. Duk cikin gidan shine discipline master. Idan ya kama yaro jibgarsa yake kamar babu gobe.

Tuni Yaya Mustafa ya bar wajen saboda raka wasu abokansa da zai yi. Ina cikin tsallen kwaɗon sai haki nake kamar na yi gudun mutuwa. Tun ina ganin hasken fitilun da suka haska farfajiyan gidan har na koma ganin duhu, har ma na rasa inda na ke, na dai ji kamar a sama na ke tafiya, kamar tafiya nake akan iska.
Kila Babana ne ya zo ɗaukana. "Sahla ki zo mu tafi, tunda ba a sonki a wannan duniya"

"Baba" na furta a hankali sannan idon ya sake rufewa gaba ɗaya...


TOP-NOTCH.....the touch of excellence, just for you.

✈✈✈SAHLA a Paris✈✈✈

***

005 ...miyan kyankyaso...

"Ban yafe abinda kuka yiwa Sahala ba. Gashi nan yarinya ta kasa tafiya tun shekaranjiya"

"Hajiya Kaka wai duk abinda Sahala tayi kina goyon bayanta. Wallahi ko yanzu na sami dama sai na sake punishing ɗinta"

"Koma mi ta yi sai ku karya mata kafa"

"Hajiya babu wanda ya karya mata kafa. Iskanci ne ya hanata mikewa"

"Wallahi ka kiyaye ni Mustafah. Ina faɗa kana faɗa"

"Yanzu dai kiyi hakuri ki saka mana Albarka, yau zan tare a sabon gidana"

"To, to, Allah ya shi Albarka. Shi kuma Farukun yaushe zai aje iyali?"

"Hajiya ki taya shi da addu'a kawai"

"Ina addu'ar zata karɓu ya je ya makale a kasar ɗagutu"

"Hajiya aiki yake yi fa. A UNESCO ya ke aiki)

"Ummisko? A mace yake wa aiki kenan"

"Hajiya ba Ummisko na ce ba kar ki masa sharri"

Fitsari nake ji amma na kasa tashi saboda bana son gaida Yaya Mustafah. Washegarin ranan da suka saka ni tsallen kwaɗo na tashi da kumburarrun kafafu, kafana suka rike, na kasa motsa su. Kaka ta sa aka faɗawa Alhaji. Da kansa ya zo ya ɗaukeni sai da muka fito zamu tafi Abban Egypt ya karɓeni yace ya bari shi zai kaini Asibiti.
Sarai Alhaji ya ji labarin abinda ya faru amma yace a rufe maganar a cigaba da shirye-shiryen ɗaura aure kawai.

Bayan mun dawo daga Asibiti babu inda nake zuwa, ko banɗaki zan je sai Kaka ta dafa min. Duk wanda ya shigo gaida Kaka kuwa sai ya gaya min magana. "Badluck kawai. Mai farar kafa. 'Yar asara" suna dai kala-kala.

Ban san lokacin da Yaya Mustafah ya fita ba, balle har naga shigowan Uncle Faruku.
Marata ya murɗa, na rasa ya zanyi, kamar ma dai wani jiqa-jiqa nake ji a pant ɗina. Da na kasa daurewa sai na tashi zaune.

"Kaka zan yi fits..." na tsaida maganar dai dai lokacin da idanunmu suka haɗu. Yana zaune akan kujerar dake kallon gadon Kaka. Yau bai saka gilashi ba dan haka na samu damar ganin fararen idanunsa.

"Za ki iya tashi ne ko sai na tallafa miki?"

Ban amsawa Kaka ba na diro da kafafuna kasa na fara tafiya. Ina wucewa ta gaban Kaka ta daka salati. "Sallallahu Alaihi Wa Sallam"

Zani ta jawo da sauri ta zo ta rufe min bayana. Ta jawo hannuna muka wuce banɗakin tare.

Yau dai na zama 'yanmata nima. Dama duk cikin sa'annina nice ban fara ba. Haniefah ma dana girma da shekara ɗaya ta fara wancan hutun da suka zo gida.
Sai da muka dawo ɗakin na lura da inda na kwanta ashe duk ya ɓaci da jini.
Na ɗan rufe fiskata. kenan Uncle Faruku ya ga jinin ɗazu dana tashi.

"Shi kuma Farukun ina yai? Ana masa zancen aure ya tashi ya gudu"

***

Malam Salim shine Malaminmu na integrated science. Yana da kyau, ɗan fari da shi, ga gemu da kasumba. Idan yana mana darasi a aji sai na ga kamar ni kaɗai yake kallo. Idan muka haɗa ido sai na ji wani kunyarsa ya kamani.
Malamin Maths ɗinmu ɗan bautar kasa ne. Uncle Zaid shima yana min irin kallon da Malam Salim ya ke yi min. Shima yana burgeni musamman idan ya saka kayansu na bautar kasa. Wayyo ni Sahla! Malaminmu na hadda ma yana burgeni kuma ina son kanshin turarensa. Idan na zo ba da hadda ma sai na matsa kusa da shi sosai dan na shaki kanshin da kyau.

Ban san mi yake damuna ba. Maza masu kyau suna saurin burgeni. Malamin English ɗinmu ne kawai bai min ba. Leɓensa kamar ganda, idan yana darasi na dinga dariya kasa-kasa kenan. Idan ya ce Verb sai kaga leɓen sunyi sama sun baje kasa, kamar yace 'waaab'.

Yanzu ba ni kaɗai ke zuwa makaranta ba. An dawo dasu Haniefah da Safiyya gida bayan Safiyya ta kwaso Aljanu, ita kuma Haniefah ciwon ulcer ya yi mata lahani. Daɗin abinma duka a JSS 3 aka saka su saboda ba su yi junior waec ba a chan makarantansu aka ciresu. Hanifah ba karamin jinya ta sha ba bayan an dawo da su gida, satinta kusan uku a Asibiti, wai ulcer da typhoid suka mata mugun kamu.

Duk da gidanmu gidan yawa ne, amma har yau bani da wadda muka shaku da ita irin sosai ɗin nan. Nasiba, Safiyya, Hanifah da kuma Zuhriyya duka sun haɗe kansu waje guda. Zuhriyya tana SS 2 mu uku muna JSS 3 ita kuma Nasiba tana JSS 2.
Ni kam daga ni sai Kaka. Duk iya shege na akwai abinda bana iya faɗawa Kaka. Ina so na tambayeta ko abinda na ke ji gameda su Malam Salim dai dai ne. Ina so na tambayeta ko yawan kallon kaina da nake a madubi abin damuwa ne. Ina so na tambayeta ko abinda na ke ji a raina idan nayi mafarkin Affan ko na Uncle Zaid dai-dai ne.
Ina son sanar da su Safiyya amma ina tsoron kada su min dariya. Kada su dinga tsokalata kamar yadda suka saba.
Matan gidan kuwa kowa 'ya'yanta ta sani. Wani sabon salon iskanci da suka samu tunda sun ga na fara ɗan hankali bana kiyuwar yin aiki sai su dinga sani aiki son ransu. Ko Kaka da muke ɗaki ɗaya bata bautar dani kamar yadda su ke yi.

***

Yau kwana ɗaya kenan ya saura ayi Mauludi.
Hajiya Kaka tana celebrating wannan rana a kowacce shekara. Duk da akwai yaran mazan gidan da suke ja da bikin da ake a ranan amma hakan bai hana yin hidima a wannan rana ba a kowacce shekara. Takanas Alhaji ke ware kuɗi ya bawa Hajiya dan ta yi hidima da shi. Ayi girke-girken sadaka da wanda za a raba kyauta wa 'yan anguwa.

Girkin yau ya faɗa hannun Ummi dan haka ita Kaka ta damkawa lamarin girke-girken da za a yi.

Ita da Kaka sai da aka zauna aka yi lissafe-lissafen abubuwan da za a siya da adadin abinda za a bukata amma duk da haka sai da matar nan ta rage abubuwa. Aka ce ta auno shinkafar da za ayi masa da shi mudu goma shabiyu, matar nan ina kallo ta auna mudu tara ta bani. Ban yi magana ba dan bana son zafin kai nima fama nake da kaina, wannan shegen bakon da yake zuwa duk wata ya hana ni sakat.

Naman da aka kawo za ayi miyan taushe da shi. Kaka ta ware wanda za a soya a kawo mata da kuma wanda za a silala a zuba a taushe. Ita kuwa Ummi ta kwashi rabin naman bayan an silala ta saka a wata tukunya tace Hanifah ta kai mata karkashin gado. Muna haɗa ido tace " miye? Na ajiye ne saboda baki na musamman da basa zuwa sai chan yamma"

"Ummi ni ban ce komai ba. Kema kin san in ba dan ciwon kafa dake damun Kaka ba ba zata bari ki gudanar da komai ke kaɗai ba, tunda ta san halinki. Ki yi abinda kika ga dama. Amma kar ki manta dan soyayyar Manzon Allah ake wannan sadaka"

"To Malama Sahala. Ja mana aya ki mana wa'azi"

Na kauda kai na cigaba da yanka Alayyaho. Kwanan nan dubun matar nan zai cika ta ga abinda zan mata a gidan nan.

Karshe dai hidimar Mauludin bana da walle-walle aka tashi tsakanin Ummi da Kaka da kuma sauran matan banda Anty Amarya.

Masan da aka toya bai kai yadda ake yi ba. Jollof ɗin shinkafa itama bata kai ba. Balle uwa uba nama. Mama da Kaka haka suka shiga har kitchen ɗinta suka dinga neman inda ta ɓoye nama amma basu gani ba. Da kamar na faɗa musu a karkashin gado take sakawa sai na yi shiru nace zan yi maganinta ai na san ya take da su. Ko dai ta soya ta dinga ɗauka ɗai ɗai duk lokacin da za ta ci abinci ko kuma ta yi stew da shi ta ɓoye a fridge ɗinta ranan da ba girkinta ba idan an kawo mata abinci ta buɗe stew ta ɗebi nama ta watsa a saman abincinta.

"Sahla dan Allah yi min jajjage mana, zan yi 'yar sos (sauce) ce kaɗan, gobe na ɗan ci shi da biredi. Kwana biyu na gaji da cin biredi da shayi zalla"

Ba musu balle gardama na ce mata to. Yaranta suna falo suna kallo, ni ce boyi-boyinta ko?.

Na zuba kayanmiya a cikin turmi sannan na ɗauko farar leda dana ɓoye a bayan kofar kitchen ɗinta na zazzage kyankyasan da ke ciki tas a ciki. Dama kyankyasan wanda take kiwo a ɗaki da kitchen ɗinta ne na ke tattara mata su, to yau ga ranan su. Na haɗa su da kayan miya na dake su da kyau suka karawa kayan miyan ja.
Dana gama na zuba a munafukar tukunyarta da take satan nama da shi.
Da na gama na fito falo na ce na gama. Na zauna a falon nima ina kallo zuciyata fal da tsoro. Anya kyankyasai goma basu yi yawa ba? Dan manya ne sosai, sun sha kiwo sun koshi.
Ta tashi ta je ta ɗauko naman da ta ɓoye a ɗaki ta wuce kitchen da shi.
Sai dana tabbatar ta gama miyar sauce ɗin sannan na musu sallama na wuce ɗakinmu.

Da ke Ummi akwai kwaɗayi, tun a daren ta fara taɓa miyar. Ta ci shi da farar shinkafan da ta dafawa yaranta dan ba ayi girki ba yau bayan abincin Mauludi.

Allah ka yafeni. Daga Salamu Alaikum ɗin sallar Asuba aka wuce da Ummi Asibiti saboda gudawan da take tun da tsakar dare.

Na yi kum da bakina. Amma ina addu'ar Allah yasa dai kada ta mutu. Ba abinda ya samu yaranta tunda suma abinda ta basun bai taka kara ya karya ba.
Zuwa karfe shabiyu na rana aka sallamota bayan ta sha ruwa leda huɗu.
Kaka ta dinga yi mata madallah, wai naman sadaka da ta sace ne ya sakata gudawa. Ni dai ina jin su na yi kum da bakina. Da yake na tsorata sosai da aka kaita Asibiti na saci jiki na je sashinsu na ɗauko tukunyar miyar na wanke sauran miyan na zubar. Naman kuma dama saura kaɗan na zuba a leda na fito waje na yar a dustbin ɗin da ke waje.

Matar nan kafin dare ta fara Zage-zage wai an shigo an mata sata a kitchen. Na ce bata daddara ba kenan.
Yanzu ko gaisheta na yi sai na ji dariya ya taho mini idan na tuna cewa taci miyar kyankyaso.


006... "Kuliya Kuliya cinye min kashina" inji Sahla...

Yau Alhamis tunda na dawo daga school na fara kokarin yin assignment ɗin English da aka bamu dan gobe da safe za a karɓa. Ina son darasin English saboda shine kaɗai ko ban yi karatu ba na kan taɓuka abin kirki.

"Sahala tashi ki karɓo min Abinci tunda ke yunwar bata ishe ki ba"

"Kaka Dan Allah ki bari na karisa rubutun nan"

Can kamar minti ɗaya Kaka ta sake yi min magana. Na shareta.

"Sahala wai sai hanjina sun gama nannaɗewa ne kan za ki kawo min abincin ne"

"Kai Kaka" na dangwalar da littafin na je ɗaya ɗakin na ɗauko cooler na wuce sashin Anty Amarya. Na rike ranan girkin kowacce a cikinsu kamar yadda na rike irgen kwanaki.

Ina nufowa ɗan karamin gate da ya raba ɓangarenmu dana matan gidan na fara jin hayaniya. Muryan Anty Amarya ne ke tashi. Ban taɓa ji tana masifa irin haka ba. Ina zuwa kofarta na tarar da kaya jibge a wajen. Hayaniyar ta ciki ne. Na kutsa kai na shiga.

Fitowa kawai take da kayanta daga ɗaki tana jibgawa a falo. Su Mama da Ummi na wajen suna bata hakuri amma sai masifa take.

"Ni zai nunawa ya san Amana. Ya san sarai inda ya ɗaukoni ba gidan matsiyata bane. Aure shekara goma miya tsinana min. Dan ban haihu ba nina ke hana kaina haihuwan ne. Yau zan bar masa gidan. Bani da kowa a gidan nan amma wani irin bauta ne bana yiwa 'ya'yan gidan"

"Sai hakuri dai Rafee'ah" Mama ta faɗa tana kokarin matsar mata da akwati gefe dan Anty Amaryan ta samu ta ajiye jakar da ta fito da shi.

"Zan bar masa gidansa. Alhamdulillah tunda ba wajen zama na rasa ba"

Shegu sai hakuri su ke bata amma babu wanda yai yunkurin hanata tattare kayanta. In da babu munafurci ai Kaka zasu kira ta zo ta hanata tafiya amma suka makale suna bata hakurin karya.

"Anty Amarya Dan Allah ki yi hakuri"

Allah na gani na fi sonta duk cikin matan gidan nan. Idan ta tafi ya zamu yi ni da Kaka.

"Matsa min a waje kiga" ta ɗan bugeni kaɗan ta wuce da wasu akwatunanta waje.

"Wai ina Hamza ne?"

Mama ta ɗan karkatar da kai wajen Ummi tace " ni kam Akwatunan Rafee'ah nawa ne? Wancan kam ba irin akwatin lefen Firdausi ba"?

"Irinsu ne fa. To yaushe ta sauya akwatuna"

Shigowar Anty Rafee'ah yasa suka yi shiru. Na yi mamaki ma da annamimiyar gidan bata shigo ba, kila bata nan ne.

Na fito daga falon na nufi ɗakinmu. Yadda Anty Amarya ke fitar da kaf kayanta bana tunanin ta yi girki yau.

"Ina abincin? Ko bata gama ba"

Ashe ma na bar kular tamu a chan.

"Kaka, Anty Amarya fa yaji za ta yi. Gata chan tana tattara kayanta"

"Yaji kuma?. Miya faru?"

"Ni ina zan sani"

Kaka ta mike daga tabarmar da take zaune tace mu je. Na bita a baya dan nima ina son sanin abinda ya faru.

Lokacin da muka je Kaninta Hamza ya zo yana ɗaukan mata kaya yana kai mata zuwa motarta. Dama duk gidan ita ke da mota ta kanta, sauran kam sai dai su yi amfani da motan gida na Alhaji.

"Rafee'atu ya haka? Mi ya kawo maganan yaji"

"Hajiya Kaka kiyi hakuri ki tambayi ɗanki"

"Rafee'atu ban san ki da rashin kunya ba. Mu shiga ciki ki gaya min abinda ya faru"

"Babu bayanin da zan miki. Abu ɗaya nake so ki min, Dan Allah ki sa Alhaji ya aiko min da takardata gidanmu"

"Ina shi Kabirun?"

Ummi tayi caraf tace " ya fita tun safe"

"Munafukai, ina gidan nan Rafee'atu tana kwashe kayanta ba za ku zo ku gaya min ba. Aishatu kira min shi Kabirun"

"Hajiya ko an kira shi ma ba ɗagawa zai yi ba kila yana masallaci"

" kira mini shi na ce" Kaka ta daka mata tsawa

"Bari na je na ɗauko wayar"


***

Paris, France


"Aly come here. Come closer. I'm waiting"

Yaron ya ja baya hannunsa na rawa, fiskarsa cike da hawaye yana girgiza kansa tareda faɗin "No, please no"


"Please Nooooooo"

A firgice ya tashi daga bacci fiskarsa ya jike sharkaf da gumi duk da cewa a zahiri ɗakin akwai sanyi.
Ya kunna fitilar ɗakin haske ya karaɗe katafaren bedroom ɗin.
Matashi ne da ba zai wuce shekaru
Talatin da uku zuwa da huɗu ba. Dogo ne kuma ba shi da jiki.

Yaye farin duvet ɗinsa yai sannan ya sauko da kafafuwansa kasa, ya dafa kai yana sauke numfashi a hankali. Kusan sakan goma yana haka kafin ya mike ya wuce banɗaki.
A gaban madubin dake banɗakin ya tsaya yana karewa kansa kallo.
'Komai zai daidaita, abubuwa zasu chanja' abinda yake ta maimaitawa a ransa kenan.
Ya jima a haka kafin ya samu ya watsa ruwa sannan ya fito.
Sai da ya shigo ɗakin ne ya dubi agogo ya ga karfe biyu da rabi na dare shi da bacci kuwa sai wani daren dan idan yace zai sake kwantawa ma ba iyawa zai yi ba. Daga shi sai bathrobe ya wuce ɗakin karatunsa. Buɗe computer ɗinsa yai ya fara aiki. Kusan kowanni dare aikin kenan. Zai kwanta, zai yi mugun mafarki, zai tashi yai wanka ya zo yai aiki ko kuma ya fara karatun littafi...

Washegari da safe yana haɗawa kansa breakfast wayarsa ta shiga ringing. Sayyidah ce.

"F Kay ka kira Dad ka mishi magana. I can't take it anymore. Zan aikata abinda zuciyata ke so, and i don't give a damn"

"Calm down SD. Zan sake yi mishi magana"

"Iyayen Irfan suna jiranmu. Bamu da lokaci"

"Zan kira shi. Ki kwantar da hankalinki"

Yana ajiye wayar ya shiga nazari. Alhaji yana so Sayyidah ta yi aure amma kuma baya so ta auri mutumin kasar Pakistan, wannan kuma so yake ya take mata 'yancinta na zaɓin wanda take so.

***

Kwana biyar kenan da yajin Anty Amarya. Dake ina makale da Kaka na samu information akan dalilin tafiyarta.
Duk maganar akan Sayyidah ne. Wai ita Sayyidah ta nace wani ɗan India za ta aura ko ana so ko ba a so. Shi kuma Alhaji tunda Uncle Faruku ya masa maganar lokacin bikinsu Anty Firdausi yace bai yarda ba. Ta dawo gida ta auri wanda aka san asalinsa.

To akan maganan ne Anty Amarya ta yiwa Alhaji magana akan ya hakura da zaɓin Sayyidah tunda shi mutumin da take so musulmi ne. Shi kuma Alhaji ya tuhumeta da cewa ita ke hurewa Sayyidah kunne. Shikenan Anty Amarya ta ɗau zafi ta ringa mita, shima Alhajin da yake a tunzure yake sai ya biye mata.
A bisa majiya mai karfi wai Anty Amarya tace tunda ya mata gorin haihuwa ita ba zata dawo gidansa ba sai dai ya aika mata da takardarta.

A wata majiyar kuma ni da Kaka mun samu rahoton cewa shi Alhajin yana neman wata bazawara ne, shine zancen ya isa kunnen Anty Amarya ita kuma ta ɗauka yana mata gorin haihuwane shiyasa yake shirin sawwake mata ya auro wata.

Koma minene dai ni da Kaka muna jin jiki a hannunsu Mama dan yanzu kaf ɗinsu sun haɗa baki wajen rage mana kason abincin da ake zuba mana.

Kaka ta yiwa Alhaji magana akan ya je ya dawo da Anty Amarya amma ya ki. Yace idan ta ga dama za ta dawo da kanta tunda ba sakinta yai ba...

*

"Waye ne a nan? Waye ke kaɗa min gwaiba"

Na yi shiru ina cigaba da kaɗo gwaiba. Ga gwaiba nan sun yi ɓula-ɓula amma Kaka ta hana a cire wai basu gama kosawa ba.
Bishiyar a bayan ɗakinta yake kuma duk cikin bishiyoyin Gwaiba dake gidan wannan ɗin tafi yin mai kyau kuma manya.

Cakwal-cakwal sai ga Kaka ta fito daga ɗaki a fusace ko zani bata gama ɗaurawa ba. Wannan bishiya kamar ranta ne a jiki dan yana ɗaya daga cikin abinda ke haɗamu faɗa da ita.

"Sahala ina magana kina shiru. Ba nace sai karshen watan nan za a cire Gwaiban nan ba"

"Kaka da yau da karshen wata duk ɗaya ne. Ni kam Wallahi ba zan jira ba, kika sani ko na mutu kafin lokacin"

"Sahala ki kiyayeni. Ya isheki haka nan"

Ta kama sandan ta rike.

"Kaka ki bari na kaɗo wannan daga ita shikenan"

"Na ki ɗin. 'Yar banza kina ganin duk nacin Abbas na hana shi taɓa gwaiban nan amma dan munafurci kika biyo baya kina satan min"

"To sai ki yi ai"

Na ɗauki na karshen da ta faɗo na wuce wajen famfo, kamar jaraba Kaka ta biyoni tana faɗin sai na nuna mata nawa na ɗauka.

Da muka gama darun fa da ita aka zauna aka

2 Comments On SAHLA A PARIS
avatar
mahamane-noura

1 year ago

Reply

Ya sanyi don ?aukar novel dan Allah

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to mahamane-noura

Domin downloading novel na mu dole fa sai kayi subs da mu

Please Login or Register in order to submit comment