Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

watanni bakwai ɗin nan.
Sai ga shi son zuciya da kwaɗayin abin duniya sun rufe masa ido har yana shirin sakata aikata babban zunubi.

"Rafee'ah it's just for one night. Babu wanda zai sani. Wallahi ba ki ga yadda na shawo kansa akan deal ɗin nan ba amma ya ki. Yana ganinki kuma yace idan zai sameki zai sa hannu a deal ɗin. Rafee'ah we are talking about millions of naira"

"Mansur karuwa zaka maida ni. Kana ma da cikakken hankali kuwa. Wani irin giya ka sha yau ɗin?"

Akwai abubuwa da mata ba su faɗa, idan da zasu fito su faɗa babu wanda zai zage su. Amma ance a rufa musu asiri.
Babu wanda ya san wannan labarin. Babu wanda ya san wannan shine dalilin mutuwar aurenta. Kowa abinda ya ɗauka shine ta kaso aurenta ne saboda Mansur Madaki ɗan giya ne.

Aurenta da Alhaji Kabiru ba auren soyayya bane. Aure ne na biyayya da kuma karamci. Lokacin da girmanta, da iliminta da kuma wayewarta amma kalamen Maimartaba suka sa ta mika wuya ta amshi auren hannu bibbiyu.

Tana shiga falon Hajiyarta ta tsinkaye su suna hira.
Ta risina ta gaida Hajiya sannan ta gaida Adda Maryam duk ta cikata da kwarjini.

Ta shige ciki ta je ta chanja kaya ta fito. Har lokacin hira suke sosai da Hajiya.
Ta zauna suka sake gaisawa da Adda Maryam ɗin. Bayan kaman minti biyar sai Hajiya ta basu waje.

"Wajen ki na zo Rafee'ah"

Rafee'ah ta yi murmushin yake.

"Ance wai kusan wata biyar kenan kina gida. Ban zo dan na san dalilin zuwan ki gida ba. Amma mun yi waya da Sayyidah take gaya min wasu maganganu.

"Rafee'ah kin san mi ya fitar dani daga gidan Kabiru?. Kishi da girman kai. Ban jima da haihuwan Sayyidah ba na ji labarin har an saka ranansa da Aishatu. That illiterate. Abinda na faɗa masa kenan.

"Ban taɓa sanin cewa mahaifina ne ya bashi ita ba. Ban taɓa tsayawa na saurare shi ba. Ni duk abinda nake gani shine cin amanata ya yi, yana son kara aure ne saboda an bashi sarauta.

"I couldn't bear it. Especially lokacin da ta haihu. Na zaɓi na rabu da shi sama da nayi kishi da wacce bata kaini ba. Alhamdulillah kaddara ta riga fata. Amma na tafka kuskure, yanzu ga shi gidan da nake aure nice ta biyu a cikin mu uku.

"Dan Allah ki koma gidan ki. Ba zan ji daɗi a ce yau saboda 'yata Sayyidah kin rabu da mijinki ba. Sayyidah 'yar ki ce. Nima da kike gani auren Sayyidah babu yadda na iya ne tunda yaran nawa taurin kai garesu. Yanzu auren kan shi ba jin daɗin shi take ba, maganan da muka yi jiya ma shine za su yi divorce"

Rafee'ah ta zaro ido cikin mamaki.

"Kema kin yi mamaki ko. Auren da babu albarkan iyaye dama sai a hankali"

"I'm sorry Adda Maryam. Wallahi ban sani ba"

"Ba komai kaddara kowa da irin tashi. Ni yanzu ma so nake idan kin koma ki lallaɓa Alhajin ya je chan Detroit ya ɗauko Sayyidah idan an raba auren na su. Tana bukatan kulawar shi"

"Adda zan yi tunani a kai"

"Nagode Rafee'ah. Nagode sosai"



TOP-NOTCH.....the touch of excellence just for you.

✈✈✈SAHLA a Paris✈✈✈

009...Ta'aziyya...

Tun talatainin dare na tashi, na kasa komawa bacci sai juye-juye nake akan gado. Idan na juya ta wajen Kaka ta sa hannunta ta makeni.
Ina SS 3 mun kusa fara rubuta jarrabawar WAEC. Har wannan lokacin ban gama nitsuwa akan abinda nake son zama ba. Ina tunanin zama Lawyer ko kuma 'yar jarida. Yayinda chan kasan zuciyata kuma ke min kwaɗayin zama matar Affan AbdulKarim Ubandoma. Ina yawan mafarkin mun yi aure, gamu nan mun koma Egypt da zama, gamu nan mun haifi kyawawan 'ya'ya masu dogon gashi irin na larabawa.

Har zuwa wannan lokaci hiranmu da Affan ya karkata ne ta chatting a facaebook. A yanzu bana tunanin kowanni ɗa namiji sai Affan. Wancan wawan dake turomin text tuni na blocking ɗinsa, sai daya chanja nambobi har uku yana turomin sakon ban hakuri amma ban unblocking ɗinsa ba.

Abin mamaki ko Kaka ban gayawa soyayyata da Affan ba. Duk yadda hakan ke cina nayi shiru na ki gaya mata. Affan yace kar na bari kowa ya sani dan za a min faɗa tunda ban gama sakandare ba.

An kawo kuɗin auren Zuhriyya. Wannan yasa sauran matan suka buɗe chapter Anty Asiya wai ta fara tsufa babu mashinshini. Duk da Ummi tana jin daɗin bikin Zuhriyyar da za a yi hakan bai hanata damuwa da rashin saurayin babbar 'yarta mace Asiya ba.

Dake Asiyar boarding school ta yi tun daga JSS 1 har ta gama shiyasa bata wani saba da 'yan gidan ba. Lokacin data gama kuwa tashi ɗaya ta ci Jamb ta samu admission a ABU Zaria, ni ban ma san mi take karantawa ba sai kwanan nan da ake tseguminta wai itama idan ta gama karatun likitancin nata karshe ko ta yi aure ba haihuwa zata yi ba tunda ga zahiri sun gani, Anty Rafee'ah ta karashi dogon karatun bokonta yau aure samaa da shekara goma amma ko ɓari bata taɓa yi ba.

Ta wani ɓangare na ji daɗin yadda matan gidan suka kauda hankalinsu daga kaina. At least nima zan samu sa'ida.
Wani ɓangaren kuma sai na ji tausayin Anty Asiya. Gata mace har iya mace amma babu wanda ya taɓa zuwa gida nemanta koda cikin 'yanuwa ne. Kila tanada samari a can Zaria, to amma in dai akwai, ya kamata ace yadda aka tsangwama matan nan ta turo wani ya zo gida.

Oho, ni kam dai bani da matsala, tuwona maina za a yi. Ko yanzu muka buɗa baki muka faɗa yanzu za a fara shiri...

"Sahala nace ki tashi ki dafa min ruwan shayin nan ko baki ji bane"

"Kaka ke kam da shayin nan sai kace an miki jifa. Ba dama mutum ya zauna sai ki ce shayi"

"Zan make ki Sahala. Tashi ki kawo min shayi ko na haɗa ki da Yusufa"

" kai Kaka. To barin gama tura sakon nan"
Na turawa Affan reply sannan na mike idan ba haka ba sai Kaka ta ɗaga min hankali akan shayin nan. Tinda suka dawo daga Egypt ta kawo saran shan shayi safe da rana da dare. Wani lokaci sai ta sha shayi sau biyar a rana.

Dana dafo shayin na kawo na tarar da Kaka ta zabga Uban tagumi.

"Kaka miya faru? Baki da lafiya ne?"

Ta ja numfashi "hmm"

"Kaka dai"
Na ajiye shayin na hawo gadon na sakala hannuna a kafaɗanta. Duk iya shegena ina son Kakata sosai, bana so na ganta cikin damuwa.

"Kaka wani abu kike so ne?, kaza kike son ci?"

"Ana ta mutuwa wa ke ta kaza Sahala. Ni yanzu ki dubeni. Sadiye ta rasu, Laminde kawata ta rasu. Goggonku A'i ma ta rasu. Jiya-jiyan nan Kabiru ke faɗa min wai Asabe ta cika a kasa mai tsarki. Asabe fa. Yadda mutuwa ke ɗauki ɗai-ɗai ɗin nan yaushe na san zan zata ɗaukeni"

"Haba Kakaaa, ai da sauran shan ruwanki a duniya. Ai sai kinga 'ya'ya har da jikokina kafin ki tafi"

"Munafuka. So kike na ruɓe a raye ko"

"Haba my Kaka. So nake ki jima kina shan shayi da jar miya" na rungumeta ina dariya.

"Yanzu Sahala idan Allah ya kamani da hakkin Sadiye fa?. Kina ganin duk sharrin dana kulla mata Mala'iku zasu bari na haye siraɗi?"

"Kakaaa, kar ki wani ɗaga hankalink. Shi Allah mai yawan gafara ne, ki roki gafararsa zai yafe miki"

"Ba zaki gane ba Sahala. Akwai wata rana girkin Sadiye ne, ta ɗaura miya ta shiga banɗaki na ɗau gishirin naira biyu na juye mata a cikin miya. Ita kuwa al'adarta ce bata taɓa ɗanɗana abinci idan tana girki. Ranan jummu'a ne Malam yayi baki aka kawo musu abinci suka ci gishiri. Da baki suka tafi Malam yai ta mata faɗa"

"Kai! Kaka, ashe kema tyrant ce"

"Ai Sahala abinda na yiwa Sadiye sai dai Allah ya yafe mini kawai. Amma ta ji jiki a hannuna"

"To ba kin ce ta yafe miki ba"

"Cewa ta yi ta yafewa kowa, ai bata kira sunana ba. Kina ga zata yafe mini duk abubuwan dana mata"

"Tunda ta yafe wa kowa ai kina ciki"

"Ni Fatima ina zan shiga da hakkin Sadiye. Dama zan yi irin rasuwar Asabe ai dana huta"

"Kaka ki kwantar da hankalinki ba za ki mutu yanzu ba kinji"

"Sannu Azara'ilu"

Dariya nayi nace " ance ba sunan mala'ikan mutuwa ba kenan"

"To karatun Malam na Lago karya kenan?. Kin san sittin nawa ya sauke? Ance harda sittin mai hayaki ya sauke fa"

Na fashe da dariya harda rike ciki.
Wayyo Kaka zaki kasheni. Miye kuma sittin mai hayaki.

"Ni kam miko min shayi na kora"

***

Yadda ake haihuwa ayi murna ayi suna. Haka nan ake mutuwa ayi kuka ayi zaman makoki. Tunda nayi wayo banda lokacin da Ummi ta haihu ɗan ya koma ban sake ganin anyi mutuwa a gidanmu ba. Kwanaki dai Allah yaiwa matan Baffanmu Ahmad rasuwa. Saboda matarsa basa shiri da Kaka ko gaisuwa Kaka bata je ba.

Gaskiya dai kam kamar matar ta shanye Baffa Ahmad. Duk cikin 'ya'yan Kaka dama 'ya'yan Sadiyya babu wanda baya zuwa gaida Kaka duk nisan da yake kuwa. Amma shi Baffa Ahmad tunda yai aure ya koma Kaduna aka dena jin ɗuriyarsa, ɗansu ɗaya da matar, a lokacin sunan yaron da su Mama suka je da Kaka suka dawo da takaicinsu a hannu. Wai matar da 'yan'uwanta ba karamin walakanci suka musu ba.

Ba a dai cire 'ya'ya a rai ne amma na sani ko Baffan mu Abubakar yafi Baffa Ahmad samun matsayi a wajen Kaka. Shifa duk meeting ɗin da ake na 'ya'yan Ubandoma baya zuwa.
Shiyasa ba a wani ji zafin mutuwar matarsa ba. Bayan rasuwar Kaka tace a bar mata ɗansa Khalifah ta goya shi, Baffa Ahmad yace wai ai ya riga ya mikawa Maman matarsa. Kaka tace a sauka lafiya.

Ranan Lahadi ina tsaka da wankin kayan Kaka gangamin mata suka shigo sashinmu suna kuka. Mama ce da Umma Bilki a gaba suna kuka suna ihu kamar wasu yara kanana. Kai wani lokacin ilimi ma da ranansa. Babu yadda za a yi Anty Amarya tayi wannan haukan koda kuwa Alhaji ne ya rasu.

Kaka tana baccinta kururuwan matan nan ya tasheta.

Na bi bayansu ina ganin ikon Allah dan ni bama mutuwar da sukewa kuka ya dameni ba illa gangancin da suke shirin yi, yadda suka jewa Kaka ai sai su sa tayi kashi a wando ko ta suma saboda firgici. Gashi kwanan nan tsoron mutuwa take kamar me.

"Waye ya rasu? Waye?, Kabiruna ne?"

Mama ta riketa tana faɗin a'a Hajiya.

Umma Bilki tace " Alhaji Umar ne da iyalinsa suka yi hatsari"

"Umaruna ya mutu ko, ya mutu ko" luuuu ta yi kasa.

Ni na san waɗannan annamiman sun zo ne su karisa Kaka. Wani irin sakon mutuwa ne wannan...

Haka Allah ke lamarinsa, duk yadda ake son mutum haka mutuwa zata zo ta kwace muku shi.
A lokaci ɗaya Allah ya ɗau ran Baffa Umar da matansa da yaransa uku. Ɗansa Al'amin kaɗai ya rage shima kuma dan yana makaranta a Maiduguri ne. Allah sarki ko sati biyu bai yi ba da komawa Makarantan iyayensa suka rasu.

Muna cikin wannan shock ɗin, kafin ayi sadakan bakwai Allah yai wa Hajiya Bintu rasuwa. Itace 'yar fari a jerin 'ya'yan Kaka da suke raye. Tana aure a Dukku. 'Ya'yanta tara duk sun girma sun yi aure.
Wannan ya sake tada hankalin Kaka. Dama tunda aka yi rasuwan farko take kwance.
Babu wanda ya san matsalar Kaka sai ni. Ita damuwarta hakkin kishiyarta ke bibiyanta shiyasa 'ya'yanta ke mutuwa akai-akai.

Dama ga shi karatun Malam na Lado ne a kanta har yanzu, shiyasa duk wa'azin da za a mata baya shiganta. Ita dai bata yadda kaddararsu ce ta zo a haka ba.

Ni kam addu'ata Allah ya sa kar ayi wani mutuwar nan kusa dan Kaka zata iya samun heart attack ta mutu. Allah yasan karfin zuciyar Kaka ba dan haka ba ai ance jininta ya hau sosai lokacin da aka kaita Asibiti.

A hankali komai ya fara dawowa dai dai dan kuwa wata biyu kenan da rasuwan da aka mana. A sannan nema aka saka bikin Zuhriyya saboda manajan banki ya matsa ayi biki.

Ni da Anty Asiya muka zamo abin tsangwama a wannan lokacin. Gashi ana strike balle Anty Asiya ta fake da makaranta. Ni kam na dena damuwa da maganganun 'yan gidanmu. Damuwata shine na ci jarrabar WAEC ɗina. Alhaji yace idan jarrabawar yai kyau zai chanja min waya. Nima zan yi babbar waya.

Har yanzu da nake gab da rubuta jarrabawar JAMB na kasa samun matsaya akan abinda zan karanta. Affan yace na zaɓi abinda na ga dama. Yaya Mustafah yace na zaɓi Law.
Malaminmu na English ya bani shawaran na zaɓi Mass Com. I'm confused.
Da aka fara registration na JAMB Alhaji ya sake tambayata mi nake son zama nace masa ban gama tunani ba. "Istikhara za ki yi Sahla. Ko ba a koya muku Istikhara a Islamiyya ba?"

"An koya mana"

Da wannan nima na yi Istikhara har sau biyu. Bayan na yi Istikharan na zauna nayi tunani, idan na fara karatun Law na je na kakare a hanya ya zan yi? Duk da Yaya Sulayman yana cewa akwai sauki amma ban ji zan iya haddace constitution ba. Haddar Qur'ani ma ya muka kare balle wata shegiyar littafi wai constitution. Sai kaji ana sashe kaza a cikin shafi kaza na kundi kaza. Kai su ci kayansu ba zan yi ba.
Mass Communication ne ya ɗan kwanta min, koba komai nima akwai surutu. Da wannan na samu confidence akan abinda nake son karantawa, na je na samu Alhaji na gaya masa.

Ni da su Hanifah da Safiyya ya bamu kuɗin registration na Jamb amma 'yan duniya suka samu driver ya kaisu su kaɗai tun kafin na gama shiryawa.

Na fito kenan na ga wayam an fita da motar gida. Baba Maigadi yace wai an fita da su Safiyya.
Na ce su jirani fa, kawai kaya zan chanja na ɗan shafa powder saboda passport ɗina yai kyau. Amma dan bakin ciki suka tafi suka barni.

"Sahla ina zaki je"

Yaya Yusuf ne ya fito da machine ɗinsa roba roba yana shirin fita.

"Zan je registration ɗin Jamb ne, su Hanifah sun tafi sun barni. Dan Allah ka kira Adamu Direba kace ya dawo ya ɗaukeni"

"Zo ki hau na kaiki"

A zuciyata na ce hi'inn.

"Ki zo ki hau mana"

Na tura baki nace "Yaya kawai sai na hau machine bayan akwai mota, salon a raina ni a Cafe ɗin"

"Za ki hau ko na yi tafiyata?"

"Ni kam Yaya Yusuf"

Yawwa ga mota na faɗa with so much excitement dan tunanina ma Alhaji ne.
Sai dai ba motar Alhaji bane. Ni ban ma taɓa ganin irin jeep ɗin ba.

"Barin gaisa da F Kay sai na kaiki"

Ya aka yi ya gane shi?. Shi kullum baka sanin zuwansa ko tafiyarsa. Tun ranan da ya ceceni daga hannun Yaya Mustafah rabona da shi.
Kusan shekara guda kenan.

Ina ganin motar tayi parking na yi sauri na karisa gaban motar ina jira ya fito.

Takalminsa na fara gani. Shi kam kaman kuturu kullum sai dai ka ganshi cikin cover shoe. Kai amma gaskiya takalmin yayi kyau, sai kace da gold aka yi shi sai kyalli yake yana haske.

Bai fito daga motar ba kafarsa ɗaya ce kawai a waje.

"F Kay Sir. Sai ka zama DG na UNESCO Insha Allahu"
Yaya Yusuf ya mika masa hannu suka gaisa.

"Alhaji yace wai jiya da dare ka shigo Abuja. Ya hanya"

"Alhamdulillah. Ya aiki"

"Alhamdulillahi. F Kay wannan ce latest ɗinka kenan?" Yai maganar yana nuna motar.

"Na Alhaji ne"

"Masha Allah. Kai Allah ya kara buɗi"

Dama shi ya siyawa Alhaji mota shekaru biyu da suka wuce. Ba zan manta ba a lokacin ne Alhaji ya sakewa Yaya Mustafah motar da yake hawa.
Kai wannan mota ba dai kyau ba. In Allah ya yarda ni zan fara shiganta.

Na yi caraf na ce " Uncle F Kay sannu da zuwa. Dan Allah tunda baka riga ka fita daga motan ba ka rage min hanya manaaaa" na yi maganan ina kama kofar motan. Saurin cire hannunsa yai a wajen kamar irin an ɗoɗana masa marar tuwo mai zafi ɗin nan.

"Kayi hakuri" har ga Allah ban san hannunsa na wajen ba.

"F Kay ka barta. Yanzu zan kaita a machine"

Ina jin haka na sulale na je na buɗe kofar baya na shiga, Allah ya taimakeni motar a buɗe take.

"Sahla shi sa'anki ne. Ki fito daga motan nan"

"Ai Wallahi sai dai a fita da gawata. Ga sanyin AC, wayyo daɗi kasheni"

"Sahla zan ci ..."

Inaga ɗaga masa hannu yayi dan bai karasa maganar ba.

Ina gani Yaya Yusuf ya min alamar sai ya yanka ni. Ni kuwa na mishi gwalo.

Yana rufo kofar yace min " i'm not your driver ki dawo gaba"

"Tab! Na fita ka kulle kofa ka hanani shiga. Wallahi inada wayo"

Na cire takalmina na cillashi gaba na mika masa file ɗin hannuna nace ya rikemin kafin in shigo. Kaman da ice nake magana ko kulani bai yi ba.
Na ajiye file ɗin a kujeran gaba. Na sa kafa na tsallako gefensa har da buge masa kafaɗa.
Na samu na gyara zamana da kyau sannan nace " na dawo"

Tsayawa yai yana kallona da munakufin bakin glass ɗinsa.

"How old are you?"

"17" ya gyaɗa kansa. Dan kar ya raina ni nace " amma na kusa cika 18 fa"

"Still a baby" ya faɗa a hankali.

"Ni kam ba baby ba ce. Baby sai kace 'yar yaye"

Muna fita daga gidan na sake gyara zamana na baje cinyoyina dan na cika waje. Ai yau sai na yiwa su Hanifa gori. Ni na fara shiga motan da Uncle Faruku ya kawowa Alhaji. Kar ma su ce karya ne na fidda wayata na juya camerar na ɗauki hoto kyat!

Na kalli hoton yayi wani duhu, rabin fiskatane ma ya fito sai keyar kujerar motar. Dole ma a chanja min waya.
Ina ganinsa yai wani karamin murmushi. Wato dariyan wayata ya ke yi.

Shegiyar waya duk yadda na juyata na ɗau hoton sai kaga rabi na fito.

"Uncle F Kay ka bani aron wayarka nayi hoto Dan Allah"

Ko kallona bai yi ba balle nayi tunanin zai amsa min.

Har na hakura da hakan sai kuma na kai hannu zan zaro wayar daga aljihunsa. Aikuwa ina kai hannu ya damke min hannu.

"Kayi hakuri ba sata zan maka ba hoto zan ɗauka"

"Kar ki sake taɓa ni"

"Ni ban ce zan taɓa ka ba fa. kar ka min sharri nima ina zuwa Islamiyya"

"Ina zaki je?"

"Barin kira Safiyya ta gaya min cafe ɗin da suka je"

Muna zuwa nayiwa Safiyya flashing. Na tsaya cikin motar na buge da dube-duben takardu. Sai da na ga Safiyyah ta fito daga shagon tukunna na cewa Uncle Faruku nagode na fita daga cikin motan.

Da sauri Safiyya ta kariso gaban motar tana gaida shi ranta duk a ɓace.
Ni kuwa na ɗaga masa hannu ina faɗin Uncle F Kay bye, bye bye.

Itama ɗaya munafukar ta fito daga shagon da gudu, har da wani Sahla karanmu kika kai wajen Alhaji. Na ɗaga kafaɗa na shige cikin shago abu na...




TOP-NOTCH.....the touch of excellence just for you.

✈✈✈SAHLA a Paris✈✈✈

010...Coustaliye...

***

A inda Faruk ya ajiye key ɗin mota ko kallon wajen Alhaji bai yi ba.

"Aliyu aure nake so kayi. Duk wani Alheri da zaka min ba zan ji daɗi ba kamar ka ajiye iyali. Ka kalleka, ka kalli kaninka Mustafah. Ba ka ganin nitsuwa a tattare da shi. Kwanan nan ya saka Kamal ɗinsa a makaranta. Aliyu ba mota nake so ba, ba gida nake so ba, ba kuɗi nake so ba. Aure nake so kayi. In dai farin cikina kake so to aure zaka yi."

"Dad ka dena comparing ɗina da Mustafa. Kowa da kaddararsa. Zan yi aure idan Allah ya nufa"

"Haka kake faɗa duk shekara. So kake sai an yi auren su Abbas kafin kai kayi aure. Minene matsalar ne?"

"A kara min lokaci. Zan yi aure"

"Al'amarinka Faruk sai addu'a. Ni kam babu abinda za ka yi ka burgeni sama da aure. Da Allah nake rokon ka idan akwai wata matsala ne da bamu sani ba ka gaya mana"
Faruk ya girgiza kai.

Alhaji ya cigaba "An nuna maka 'yan mata cikin dangi da abokai amma duk babu wacce ta maka. Ance ka fitar da mace ka ki. So kake da girmanka mu maka auren dole ne"

Faruk yai shiru. Babu abinda zai iya cewa. Ba za su gane matsalarsa ba. Kila aure baya cikin kaddararsa.

Yana fitowa daga sashen Alhaji ya wuce sashen Kaka. Itama ɗin ya san duk kanwar ja ce. Dan duk abinda Alhaji ya faɗa itama shi zata maimaita. Amma dolensa ne ya je ya mata ta'aziyya tunda shine musabbabin zuwansa kasar.
Ya so zuwa a lokacin rasuwan amma babu dama saboda aikinsa, infact a South Africa yake lokacin da aka yi rasuwar.

Kaka na kishingiɗe akan tabarma hannunta da mafifici tana fiffita. Ya tsugunna ya gaisheta.

"Faruku ne?"

"Kaine a gidan namu. Sannu da zuwa"

Ina Sahala take ta ɗauko maka kujera a ciki.
"Sahala" ta kwala mata kira. Amma shiru

"Haka nake fama da ita fa, yanzu haka kallo ta je yi a ɗakin Rafee'atu"

Ta ɗan tashi ta zauna tareda mika masa mafificin hannunta.

Gaskiya rasuwan 'ya'yanta biyu ya taɓa Hajiya Kaka. Gaba ɗaya ta rame masa compared to wancan zuwan da ya ganta.
"Na ce ko zaka zauna a tabarma kafin Sahala ta zo"

Ya girgiza kai, bai saba zama a kasa haka ba. Yana mamakin yadda mutane ke iya zama a kasa har su harɗe kafafunsu. Shi idan ka ga ya zauna a kasa to sallah ne.

"Hajiya yaya hakuri"

"Hmm Umaru da Bintu sun tafi saura ni. Ance Umaru da shahada a bakinsa ya cika. Kaga kuwa ya huta. Allah yai musu gafara"

Faruk ya amsa da Amin.

"Yanzu Faruku kai kenan haka zaka cigaba da zama babu aure. Ko dai.. Sahala, ya haka?"

"Wallahi sai dai ayi asaran abinci a gidan nan. Haka kawai ku maida ni 'yar iska. Wallahi sai anyi meeting a gidan nan yau. Babu 'yar iskar da zan sake yiwa aiki"

Tana tafe niki-niki da katuwar tukunya akanta ta yi wani katon gammo da gyalenta.

Shi da Kaka suka zuba mata ido. Tana zuwa tsakiyarsu tace Kaka Dan Allah tayani na sauke wannan tukunyar.
Kaka ta mike da sauri ta kama mata suka sauke tukunya.

Kaka ta buɗe marufin tukunyar, tururi ya baza wajen.

"Minene wannan Sahala?"

"Ba Mama bace za ta maida ni taɓaɓɓiya. Na dawo daga wajen registration ɗin JAMB da uban yunwa wai abinci ya kare. Tace na je na dafa mana couscous guda biyu ni da su Abbas da su Hanifa dan suma ba su ci abinci ba. Shinefa na ga ta ɗaura ruwan kayan miya a wuta yana tafasa. Da farko dana zuba ledan couscous biyu a ciki sai naga yayi ruwa, shine na shiga store na ɗauko biyu na kara a kai, shima couscous ɗin kamar magani ya ki shanye ruwan. Ni kuma na ɗauko ledan taliya guda uku na juye a kai.

"To wai yanzu sai dai ni na cinye abinda na dafa, kuma zata faɗawa Alhaji na mata almabazzaranci da abinci. Wallahi ta faɗa, nima zan faɗi abubuwan da take mini, ai na jima ina tarata"

Faruk yai murmushin gefen baki. Yarinyar nan ba randa zai shigo gidan nan bata saka shi dariya ba. Idan za ta fara comedyza ta yi kasuwa.

Ga dai gwaten taliya da couscous yana kallon Kaka da Sahala suma suna kallonshi.

"To yanzu Sahala da kika cicciɓoshi kika kawo nan ya kike so ayi da shi"

"Cewa ta yi idan ban ɗauke daga kitchen ɗinta ba zata zuba min wanka da shi"

"To shiga ciki ki kawo min cokali na taɓa na ji ko zan iya ci"

Da Kakan da Sahlan duk sammakal. Kaka ta taɓa abincin tace "amma Sahala wannan abincin ai ba zai ciwu ba. Taliyar fa bata dahu ba"

Sahla ta karɓi cokalin ta ɗebo abincin ta kai baki. Shi ba kunu ba, shi ba gwate ba, ga shi nan dai.

"Yanzu ya za ayi da abincin nan. Kema Sahala baki kyauta ba"

"To Kaka sai kin faɗa a gaban shi ne, salan ya je ya gayawa Yaya Yusuf"

"Kawai barin je na samu Baba Maigadi nace ya nemo mana almajirai. Yau za su ci coustaliye. Uncle Far, ai, Uncle F Kay sunan abincin yayi kama da abincin 'yan Paris ko?"

"Hajiya barin shiga na gaishe da mutanen gida" yai maganar yana ajiye mata kuɗi damin dubu ɗaya.

"To Faruku Allah ya maka albarka. Allah ya sa ka auru kwanan nan"

"Kaka ya auru kuma sai kace mace"

"Yo tunda ya ki neman auren ba sai na masa addu'ar Allah yasa mace ta auro shi ba"

Shi kam tuni ya bar

2 Comments On SAHLA A PARIS
avatar
mahamane-noura

1 year ago

Reply

Ya sanyi don ?aukar novel dan Allah

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to mahamane-noura

Domin downloading novel na mu dole fa sai kayi subs da mu

Please Login or Register in order to submit comment