Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

barandar ya wuce sashen matan gida.

Kowacce mata sai daya shiga yai mata gaisuwa. Mama ko kallon kirki bata masa ba tana ta faman yiwa yaranta masifa akan abinda Sahla ta yi. Wai ya aka yi suka bari ma Sahla ta buɗe store har ta ɗauko mata kayan abinci.

A wajen Anty Rafee'ah ne ma ya ɗan jima su kan taɓa hira. Duk maganar dai bai wuce yaushe zai yi aure ba. Sai kuma maganar Sayyidahda suka yi. Sun rabu da mijinta amma ta ki dawowa gida Nigeria.

Anty Rafee'ah ta masa nasiha akan ya lallashi Sayyidah ta dawo gida dan Alhaji baya jin daɗin zamanta a America.

Yai mata alkawarin zai yiwa Sayyidah magana. Duk da kuwa ya san taurin kan kanwar ta sa. Shi kuma ga shi mutum ne da baya iya shiga harkar mutane balle har ya takura musu bisa ra'ayinsu.

Lokacin daya fito compound ɗin gidan ya ga jerin Almajirai na shigowa gidan. Tausayinsu ya kama shi. Yau lallai za su ci abinda zai rikita musu ciki. Da wannan ne ma ya fara tambayar kansa wai har yanzu a kasar Hausa ana almajiranci. A bar yaro ya dinga garari a titi neman abinci. Eating leftovers daga ko'ina. Gaskiya Allah ke kiyaye yaran nan, if not da yawansu da sun mutu ta hanyar food poisoning. Yana fata watarana za a samu chanji. Kowanni ɗa zai zauna gaban iyayensa yai karatu. Shi shaida ne na illar rashin kulawar iyaye a kan 'ya'yansu musamman idan suna shekarun kuruciyarsu.

Shi gashi a gaban iyayensa ya taso amma rashin kulawarsu, sakacinsu ya haddasa masa damage ɗin da har yanzu yana fama da shi kuma bai san ranan samun sauki ba.

Lokacin da aka yaye Hasina Maami ta bada rikonta ga yayarta da ke London. Ta focusing hankalinta akan karatunta thinking sai ta gama zata sake haihuwa kwatsam sai ga cikinsa. Tun da aka haife shi ya ke karkashin masu aiki. Infact ance ko nono baifi na wata biyu ta bashi ba ya koma shan madara.

Zai iya kwana biyu, uku bai yi magana da iyayensa ba sama da good morning da kuma good night.
And all of a sudden aka kawo Julius...

Matsalar Sayyidah ma baya rasa nasaba da rashin kulawar iyaye. Bayan rabuwar auren Maami da Dad ɗinsu, kulawarta ya koma hannun babysitters ko kuma gidan makotansu turawa. Maami tana yin degree ɗinta na uku, ga kuma rabuwar nasu ya taɓata.

Dad ya dawo Nigeria da zama gaba ɗaya su kuma sun makale a kasashe daban-daban.
Shi yanzu yana France. Hasina da mijinta suna London. Sayyidah na America.

Idan ya zo Nigerian ma gidan na su ba a haɗe yake ba. Bai taɓa tunanin Dad zai iya ajiye mata har huɗu ba. But then abubuwa da dama sun canja da shi bayan an bashi sarautan Ubandoma.

Sarautan ne ya sa shi kara aure ko kuma dama ra'ayinsa ne? Bai san amsar ba. Bai kuma san ya ake ji idan anyi aure ba balle har yai tunanin wasu mazan ba za su iya rayuwa da mace ɗaya ba.

Yana da burin yai aure watarana, yana da burin ya zauna da mace ɗaya har karshen rayuwarshi. Sai dai kuma wannan buri ne da ba zai taɓa zama zahiri ba.
For now, sai dai ya ga ana aure, ana haihuwa, and the circle continuous.

Bai jima a tsaye ba ya ga almajiran nan na fitowa daga chan gefen Kaka, robobinsu cike da Coustaliye...

Yai murmushi mai tsayi daga chan kasan ransa ya furta sunanta. Sahla..

TOP-NOTCH.....the touch of excellence just for you.

✈✈✈SAHLA a Paris✈✈✈

011...cire kunya...

Soyayya akwai daɗi. Ka so mutum sannan shima ya soka babu abinda ya kai wannan saka nitsuwa da farin ciki. Musamman idan wanda kake so ɗin ɗan'uwanka ne na jini wanda kake ganin duk rintsi zaku kasance tare.
Akwai daɗi ace bayan shekara ɗaya kuna soyayya ta waya zaku
sake haɗuwa da juna. Akwai farin ciki sosai.

Yau su Affan zasu shigo gari. Lokacin rasuwa basu samu sun zo ba sai yanzu. Ga shi wannan karan da su za ayi Azumi har ayi sallah domin sai bayan sallah zasu tafi.

Wannan shekaran Anty Rafee'ah ce da Anty Maryam autar Kaka zasu je Umurah.
Har yanzu Kaka bata huce ba da hukuncin da 'ya'yanta suka yanke mata. Alhaji da Abba sun ce ba zasu biya mata kujerar Makkah ba saboda ciwon kafarta. Kwanakin baya kafar ya sata a gaba sai da aka bata walking stick ta dinga amfani da shi. Ni yanzu ma neman sace walking stick ɗin nan nake, dan da na ɗan yi wani abu kaɗan sai dai na ji sanda a bayana .

Da Allah Annabi Kaka ta roke su akan su bari ta je Makkah bana ko Allah zai sa ta cika a can irin mutuwar Asabe amma sun ki.
Fushi take sosai da su dan har cewa tayi zata kai kararsu wajen Sarki amma ko ajikinsu. Sun tsaya akan babu inda za ta je. Saboda su kwantar mata da hankali ne ma suka biyawa autarsu Maryam kujera dan dama bata taɓa zuwa ba. Duk da hakan Kaka ba ta hakura ba.

Kaka ta zamo kamar mai Aljanu. Abu ɗaya biyu sai ta kawo zancen yanzu ace ta mutu a kasa mai tsarki mana, ai shikenan ta samu tikitin Aljannah. Ba za a tambayeta hakkin kishiyarta Sadiye ba. Tun ina mata bayani akan gafara da rahamar Allah tana iya samun mutum a duk inda yake har na zo na daina. Inaga tsufa ne ya fara taɓata. Kar na biye mata nima ta shafa mun. Yaushe na gama fama da nawa matsalolin. Yanzu ko me na taɓata sai an samu matsala.

Ranan da za ayi masan sadaka matan gidan basa nan aka bar mana ni da sauran 'yanmatan gidanmu. Hmm muka yi kullin masa taki tashi. Ni mai dabara na zuba ruwa a katon tukunyar da ake shinkafar sadaka a ciki na saka bokitin kullin a ciki dan ruwan zafin ya turarashi ya tashi.

Abunka da nayi sabuwar babbar waya. Na tsaya ina chatting a whatsapp ashe ruwan cikin tukunyar ya kone har tukunyar ta fara cin kasan roban shi kuma kulli ya fara dahuwa.
Lokacin dana buɗe tukunya na ga kullin kamar ya fara zama kunu. Hmm ranan dai sadakar buredi aka yi. Sauran kullin da bai lalace ba aka yi sinasir da shi.

*

Yauma dai Allah-Allah nake a raina kar a samu matsala a abinda na shiryawa Affan. Da ke ina taya Anty Rafee'ah aikin donut idan aka kawo mata aikin biki ni ma na iya kwaɓa donut.
Tun jiya na siyo flour da kayan haɗi na ɓoye a cikin akwatina.

Abinka da rashin amana hatta mangyaɗa sai da na siya da kaina. Couscous zan dafa masa da miyar kifi. Bayan na sha faɗa a hannun Alhaji akan Coustaliye dana dafa ranan na samu Anty Rafee'ah nace ta koya min yadda ake dafa couscous. Nifa ranan ɗinma zafin kan registration ne da kuma gajiya. Ɗanbanten wanda ya min registration ɗin ya kama ya min register da sunan Salah Sulayman maimakon Sahla Sulayman. Ɗan iska
Ya sakani asaran dubu biyu kuɗin green card da na siya aka gyara min sunan.

Dake matan gidan sun haɗe baki sun zama 'yan damfara, ni da Kaka ma muka maida ɗaya ɗakinta mini kitchen ɗinmu. Idan abinci bai ishemu ba na kunna stove na dafa mana indomie da kwai mu ci. Wani lokacin ma idan aka yi tuwo da dare bai mana ba sai na ɗan soya mana wainar flour mu ci da shayi.

Na buɗe fridge na fito da ice fish dana siyo jiya.

"Wai ni Sahala wa za ki yiwa girki ne? Saurayinki ne zai zo?"

"Eh. Saurayina ne"

"Yusufa?"

"Waye kuma Yusufa. Allah ya kiyaye na yi soyayya da Yaya Yusuf"

Aikuwa caraf a kunnenshi ya shigo ɗakin da sallama.

Ya kalleni na kalle shi. Ni ina ruwana da shi. Yanzu kam na gama sakandare na kusa shiga jami'a balle yace zai dakeni.

Ai wallahi yadda nake ji da kaina ɗin nan ko Yaya Mustafah ne yace zai dakeni a gidan nan sai anyi daru balle kuma Yaya Yusuf.

Ya tsugunna ya gaida Kaka, maimakon ya tafi sai ya zauna yana jan Kaka da taɗi.

"Yusufa saka mana tashan da suke nuno Makkan nan kaga Azumi ya kusa shigowa"

Uncle Faruku ne ya siya mana TV da Fridge aka saka a ɗakin Kaka. Shine ya sa aka maida ɗakin Kaka ciki da falo, aka kuma gyara barandar sashin nata aka kewaye har da karamin gate.
Kai Allah ya sakawa Uncle Faruku da alkhairi. Shi duk sanda ya zo sai yayi abin alkhairi.

Na shiga kitchen ɗinmu na fara kwaɓa donut. Ina yi ina bin wakar aure ta Nura M Inuwa. Dana gama kwaɓawa na fidda shape ɗin na zo na ajiye tray ɗin a saman fence ɗin barandar mu dan rana ya buga shi ya tashi.

Na wanke hannu na zo na fara gyara kifi.

"Sahla idan kin gama abinda kike yi ki zo ki same ni a part ɗin Alhaji"

Ban ko ɗaga kaina ba nace masa toh.

Na san ba zai wuci faɗa zai min ba akan ban ɗaura ɗankwali ba. Da muna yara ana ce mana sheɗan zai mana fitsari a kai idan bamu rufa kanmu ba. To yanzu mun girma ko oho. Idan ya ga dama yai kashi ma ba fitsari ba. Haka kawai ina cikin ɗaki in yi ta kimtse kaina kamar zan je islamiyya. Allah ya yafe ni amma dan ina ɓangarenmu kam abinda na ga dama zan yi.

Na kammala sauce ɗin kifi na ce barin soya donut tukun kafin nan na zo nayi couscous tunda dahuwar couscous ba mai wuya bane.
Na fito da confidence ɗina na ɗauki tray na cire kyallen dana rufe da shi. Donut yace Hi nace Hello.

Kuka ne kawai ban yi ba amma zuciyata kamar zata fashe. Na shiga kitchen na duba abubuwan da na yi amfani da su. Na saka kwai, magerine, ruwa, sugar. To amma ga chan kullin yeast a leda yana jirana a inda na ajiye shi.

Donut bai tashi ba, gashi lokaci ya tafi. Na yi tunanin mi zan yi na rasa. Na hakura kawai na tari aradu da ka. Ma fara soya donut ɗin a haka.
Kar ma na faɗa muku adadin magerine dana saka a ciki. Flat donut ɗin nan suka shanye min mai tas. Karshe sauran ma kusan gasa su nayi dan mai bai kama jikinsu ba.

Na taɓa guda ɗaya na ji sugar zui. A komai dai ni Sahala bani da sa'a...

*

Soyayyarmu ni da Affan ɓoyayyiyar soyayya ce dan babu wanda ya sani a gidan. Wannan karan ne ma muka yanke zamu sanar a gida. Zan so ganin fiskar su Hanifa da Safiyya. Zuhriyya ta yi aure, idan ka cire Anty Asiya mu ukun nan mune muke tashen 'yanmatancin mu a gidan. Nasiba na SS 2. Fadilah da Nabilan Umma Bilki kuma har yanzu ko JSS 3 basu kai ba. Itama matar tayi-tayi ta kara haihuwa amma abin ya fi karfinta. Na sha kamata tana shan wasu magunguna wai na haihuwa ne.

Matar nan irin magungunan da take ɗirka ko Anty Rafee'ah da bata taɓa haihuwa ba albarka. Dake Ummi da Mama kan yi mata gorin 'ya'ya maza idan ta shiga hannunsu sai abin yabi ya ɗaga mata hankali, musamman daya kasance ta girma, chances ɗinta na sake samun ciki yayi karanci. A aurenta na fari ma 'ya'ya mata biyu ta haifa, nan ma kuma biyun kawai ta haifa. Kowa dai da tasa kaddarar da matsalar da ta shafe shi.
Ita Umma Bilki da take ta kukan rashin haihuwar ɗa namiji ta manta da Anty Rafee'ah ne. Wasu matan ma sai a hankali. Da Allah zai bawa Anty Rafee'ah haihuwa koda gurguwa ce na san da gudu zata karɓa.

Duk yadda nake son yin falli da Affan na rike a raina saboda ina jiran perfect time da zan yi yanga na nunawa hegun yaran nan cewa nima ana sona. Hanifah ce karama a cikinmu amma kamar magani samari sai tururuwa suke mata tun muna SS 2. Yanzu ma wani Likita ne yake pumping mata kuɗi. Ita kuwa Safiyya da Sadiq ɗin Baffanmu Isma'il suke soyayya.

Na gama haɗa abinci na shirya a tray na ɓoye. Couscous dai yayi kyau amma kamar maggie yayi yawa a miyar kifin, ahaf! haka zai ci Da Allah.

Na zubawa Kaka nata ta fara ci tana yi mani tsiya wai duk saurayin dana kawo ba zata bashi ni ba tunda bai taɓa kawo mata kuɗin goro ba.

"Kaka kenan. Ai ke tsufanki bana goro bane. Tsufan nama ne da yoghurt"

Kaka ta kai min duka da sandarta na kauce ina dariya.

*
Lokacin da su Affan suka iso Abba da Affan ne kawai suka shigo gaida Kaka. Mom ɗinsu da sauran yaran suka yi zamansu a ɓangarensu.

Sai bayan kusan awa biyu da zuwansu Affan tukunna Mom ɗinsa da Boy suka shigo. Na tambayi Mom ina su Amal tace sun tafi gidan Aunts ɗinsu.

Ina ta dakon kiran Affan amma shiru. Ni tsorona abincin zai yi sanyi.

Har na fidda rai sai ga kiranshi yace na kawo masa abincin Mom ɗinsu bata nan.

Na shirya abincin a cikin paper bag ɗin da aka raba a lokacin bikin Zuhriyya. Na yafa gyale na cewa Kaka ina zuwa.

"Dama yaron AbdulKarimu kike so"

"Kaka, Affan sunan shi"

"Ke kuwa Sahala ga Yusufa nan yaro mai mutunci ba zaki zaɓe shi ba sai wancan yaron dake barin wandon shi kamar zai faɗo"

"Kaka Swagger kenan, Swagger"

Ni kam na tafi. Na rufo kofa na fita.
Idan zaka bi ta karamar kofa zuwa gidan Abba dole sai ka bi ta gaban sashin Alhaji idan ba haka ba sai dai ka fita ka bi main gate ɗinsu.

Yaya Yusuf na zaune akan kujerar roba yana karanta Qur'ani. Ni sai dana ganshi ne ma na tuna da cewa yana jirana.

"Yaya Yusuf barin kai sako gidan Abba ina dawowa"

Bai ce komai ba ya bini da ido har na zo na wuce.

Sau ɗaya na taɓa shiga ɗakinsu Amal. Duk zuwana gidan Abba iyakana falo.
Affan ne ya buɗe min kofa domin shi kaɗai ne a gidan.

Ya min murmushi nima na masa. Daga shi sai riga mai gajeran hannu da kuma wando three quarter.
A falo na fara zama yace in shigo ɗakinsa zai nuna min tsarabar daya kawo mini. Ban kawo komai raina ba na bi bayan shi.

"My Affan kayi hakuri donut ɗin bai tashi ba a haka na soya"

"Don't worry babez, in dai ke kika girka zan ci"

Na yi murmushi tareda rufe fiskana. Ni kam kona hakura da karatu a GSU ne na amince a mana aure idan muka je Egypt sai na fara karatun a chan.

Na ciro plate na zuba masa abincin na tura gabansa.

"Ba zan iya ci ba" yai maganar cikin shagwaɓa.

"Miya faru? Baka cin kifi ne?"

"Relax. So nake ki bani a baki"

Na zaro ido waje. Na bashi a baki sai kace yaro.

"My Affan ba zan iya ba" na sunkuyar da kai ina murmushi.

"See, ni kinga kunyar nan taki ce bana so. Miye a ciki. Ni ba masoyinki bane. You need to show me love, ba na so kina abu kamar aata 'yar kauye"

Yai ta tsara ni dai har na ɗauki spoon ɗin na fara bashi. Loma ɗaya, loma biyu, loma na uku ya rike min hannu.

"Affan" na faɗa a ɗan tsorace dan wani irin kallo yake mun yana wani lumshe ido kamar mai maye.

"Sahla dear. Ki dena wannan kunyan
Please. Ke kika ce min idan na zo zaki nuna min soyayya. Well this is your chance"

Kafin na yi magana ya ɗauke plate ɗin ga ajiye kasa.

Na yi saurin cire hannuna daga na shi nace "Affan zan koma, Kaka tana jirana"

"Wai kunyata kike ji dan na rike miki hannu. Come on, i thought kin waye Sahla ashe duk baki ne"

Kamin nayi magana ya rungumoni jikinsa.
"Affan ka bar ni"

"Relax, yau zan cire miki kunya. Za ki sake jiki dani yadda ya dace"

Ni da shi muka fara kokawa. Shi yana son turani kan gado ni kuma ina kokarin kwace kaina.

Daya samu ya hankaɗa ni kan gadon na saka kara. " Affan ka barni da kunyana, Wayyo Kaka" na fashe da kuka.
Ya fara kokarin kissing ɗina, na samu na gaftara masa cizo a hanci. Da karfin Allah na cizi hancinsa kamar zan tsinkashi biyu, ya ji zafi ya tashi daga kaina yana rike hancinsa yana " oh shit, shit"

Yana ɗaga ni na ɗau gyalena na ranta a guje.
Allah ya taimakeni Yaya Yusuf baya wajen. Na yi maza na wuce da gudu, ina gudu hawaye na zuba a idona, ko kallon gabana bana iya yi da kyau.

Ina isowa lungun daya haɗa sashen Kaka dana matan gidan na ji gib na buga mutum. Na ɗaga ido na kalleshi, muna haɗa ido na calla kara da duk iya karfina.
Ni yanzu tsoron mutanen kasar waje nake, kar su cire mini kunya...

TOP-NOTCH.....the touch of excellence just for you.

✈✈✈SAHLA a Paris✈✈✈

012...iphone 6...

Na gama soyayya. Na dena soyayya har abada. Koda yake laifina ne ai. Ni ce wawuya. Ranan da ya tambayeni numbar bra ɗina dariya nayi. Na tura mishi emoji na rufe ido haɗe dana dariya.

"I'm serious dear. Na san tiny boobs ba ɗinki ba zasu wuce size 32 ba, ko 34 ne, kai 32/34 nema?"

Dariya nayi ina mamakin ya akayi ya san size ɗina. Ban ɗauki irin wannan hiran a matsayin wani abu ba.
Lokacin da yace yana son mace ta saka jan bra da pant. Har nima na ji ina son jan underwear. Da Anty Amarya ta bamu kuɗin underwear muka je kasuwa da su Safiyya maimakon na sayi bakake kamar yadda na saba sai na sayi jajaye guda shida.

Allah ya tsinewa soyayya. Ba zan sake soyayya ba.
Ni ban gane ba. Dama haka soyayyar take? ko kuwa dai nawa ne ta zo a hakan.

Ɗan iska kawai.

Na cire kayan jikina gaba ɗaya na turasu karkashin gado, anjima zan je na kona su. Rufin asiri na lokacin dana shigo ɗaki Kaka ta shiga banɗaki. Dan haka na samu na ɗaura zani kafin na nemi abinda zan saka.

But it hurts. Ina son Affan. Irin soyayyar da Sharukh Khan ke yiwa Kajol a Kabhi Khushi Kabhi Gham, irin soyayyar da Jack ke yiwa Rose a film ɗin Titanic.
Tunda na amince da Affan ban sake tunanin kowa da soyayya ba.

"Sahala?"

"Lafiya kike kuka?. Wani ne ya dake ki. Faruku ne? dan yanzu ya bar nan"

Na girgiza kai. Idan na faɗa mata gaskiya za ayi tashin hankali a gidan nan. Sannan na san kowa zai yi min dariya. Laifina ne ai, ni na kai masa abinci har ɗaki.

"To miya sameki?"

"Faɗuwa nayi shine abincin dana ɗauka ya zube"

"Shine zaki yi kuka. Hawaye ne ya miki yawa. Matsa ki bani wuri ni sallah zan yi"

Bayan na saka kaya na fara neman wayata dan na jona a chaji. Na duba ɗakin kaf babu waya. Wayyo Allah na! Ko dai na bar wayan a ɗakin Affan ko kuma ya faɗi a hanya.
Ba zan iya komawa ba, ba zan iya komawa ba. Na dafe kirjina saboda wani tsoro daya shige ni lokaci guda.
Ba zan iya komawa ba.
Ba zan iya fita ba.
Na zauna a kasa daɓas ina tunanin abinyi. Ya Allah! Sai yanzu ma na fara jin tsoron abinda ya faru. Da ace Affan ya ci galaba a kaina da shikenan fa. Ba zai taɓa aurena ba, ba zan samu miji ba.

Ko Sallah ban yi ba na kwanta na rufe kaina, ina kwance sai zazzaɓi ya rufeni.
Chan dare Amal da Hanifa suka kawo mana abinci tunda ban je na karɓo ba kamar yadda na saba.

"Hajiya Kaka wai ina Sahla ne?"

"Ku shiga ciki tana kwance zazzaɓi ya rufeta"

Inajin suna shigowa na sake rufe fiskata da kyau.

Hanifa tace "Sannu Cook. Abincinki yayi daɗi fa"

Amal tace " And the donuts..."
Suka kwashe da dariya.

Allah yasa ba su ga wayata ba, dan na san zasu ga texts ɗin dana turawa Affan. Wani lokaci idan na tsinci kalaman soyayya a littafi ko film sai na kwafa na rubutawa Affan na tura masa.

"Mun sani sarai kina jinmu"
"Wai ke duk haukanki ma baki san cewa Affan ba sa'anki bane. Affan yana da budurwa 'yar jami'a, wayayyiya"

"Girlfriend ɗin Akhi a Boston take karatu, sunanta Sarah. Like iyayenta are damn rich. Ki dena bibiyan Akhi ba abinda zai yi dake"

Innalillahi! Wai ni nake bibiyan Affan. Abinda ya gaya musu kenan.

Suna fita daga ɗakin na buɗe fiskata.
Ba zan taɓa Yafewa Affan ba. Kuma sai na ɗau fansar abinda ya min ko ba yau ba.

Shege da yake ya san abinda yayi ko shigowa wajen Kaka bai sake yi ba. Karshema cewa aka yi ya tafi Abuja gidan 'yan'uwan Mom ɗinsu.

Ni dai wayata ta bi ruwa. Na duba hanyan dana bi ranan ban ga wayar ba. Ina tunanin idan wani ya gani ai zai kawo mini tunda hotona ne a wallpaper ɗin.

Na kasa zuwa gidansu Amal na dubo wayar. Itama kuma bata ce ta ga wayata ba.

Kaka ma sai da ta noticing bani da waya dan ta ga kwana biyu bana danne-dannen waya. Nace mata faɗuwa tayi ban ganta ba.

Kwana biyu da abin ya faru JAMB ɗinmu ya fito na samu 199. Alhaji yasa Yusuf ya karɓi takarduna akan za a nema mini admission a Gombe State University.

Ban san score ɗinsu Hanifah ba amma na san su BUK da ABU Zaria suka cika.
Oho ni dai na yi alkawarin nima zan zama 'yar Jami'a zan yi karatu mai zurfi, zan zama wayayyiya kuma zan yi kuɗi. Ina da waɗannan suke ganin Affan ya fini.

Ranan da aka ɗau Azumi da rana ina kwance Azumi ya buga ni na ji sallamar Yaya Yusuf. Kaka ma Azumin na jijjigata ta kwanta a kan darduma tana jan carbi bacci ya ɗauketa.

Na ɗaga kai ina gaishe shi.

"Ki fito muyi magana kar mu tashi Kaka"

Ban mike ba sai dana ga ya fita dan vest ne kaɗai a jikina da dogon wando.

Na saka hijabin sallah na fito wajen baranda.

"Miye tsakaninki da F Kay?"

"Miye tsakanina da shi kuma? Ba Yayana bane"

Yai shiru yana nazari sai kuma yace
"Ke kika ce ya chanja miki waya?"

"Ni kuma? Ni ban ma san inda wayata take ba. Ina ga ma a gidan nan ya ɓata ko kuma a islamiyya"

Miko min wata leda yace " F Kay ne ya aiko miki da shi. Na san Yana da yawan alkhairi amma kin tabbata babu wani abu a tsakaninku?"

Ni haushi ma ya fara bani. Miye tsakanina da Uncle Faruku kuma. Ni rabona da shi tun lokacin da muka yi karo da juna. Ranan ko hakuri ban bashi ba na sa ihu na gudu. Ina ji yana tamabayata miya faru amma ban kulashi ba.

Na karɓi ledan ina dubawa.

"iphone 6 ya siya miki"

"iphone 6! Wooow" Na kama tsalle.

Har da tsohuwar wayata a cikin ledan. Screen ɗinta yayi raga-raga. Ashe dai faɗuwa wayar ta yi ranan ɗin.

"Kai Uncle Faruku is the best. Allah ya saka masa da alkhairi"

Yaya Yusuf ya tsaya kallona.

Kai nikam gaba ta kaini, gobarar Titi a Jos.

"Soyayya kuke da Affan?"

"Ya aka yi ka sani?"

"Da gaske soyayya kike da Affan?" Ya tambaya a ɗan tsorace.

Ni sai ya fara ban haushi ma "wayata ka duba?"

"Kin san Affan yana da wacce zai aura"

"Na sani, sai me?"

Na juya na shige ɗaki abina.

Ina shiga na fara kokarin buɗe iphone ɗina. Kai Allah ya sakawa Uncle Faruku...oops F Kay Allah ya bashi mata nan da shekara mai zuwa.

***

Sun samu delay na kusan minti arba'in bisa tsarin tashin jirginsu.
Bai ji daɗin hakan ba. Ya gyara zamansa ya ɗauko laptop ɗinsa ya buɗe ya fara aiki. Hopefully zai iya karisa aikinsa kafin ma jirgin nasu ya tashi.
Dake a ɗakin baki na musamman yake babu wani hayaniya a wajen sai 'yan tsirarun ma'aikata dake yawo suna tambayar mi ake bukata.
Shima ɗin sau biyu ana tambayar shi mi yake bukata ya amsa da babu.

"Shit!" Ya faɗa da ɗan karfi ganin yadda file ɗin daya tura yake pending yaki tafiya saboda network babu kyau.

Ko kaɗan baya son delay. Tun daga gida aka delaying na shi. Sahla. Yanzu kuma Hasinah.

She was so frightened lokacin da suka haɗu. Ta faɗi wani kalma lokacin da ya yi kokarin rikota yana tambayarta mi ya sameta. She murmured something like " Dan Allah kar ka cire min kunya" whatever that means.

Bayan ta gudu ne ya lura da wayarta a kasa. Screen ɗin ya fashe sosai. Ya ɗau wayar da niyyar zai bawa Yusuf ko Abdullahi su gyara mata but ya manta ya tafi da shi Abuja.

Lokacin da yaga wayar the screen was beyond fixing gaskiya. So ya saka Habib step son ɗin Maami ya siya masa iphone

2 Comments On SAHLA A PARIS
avatar
mahamane-noura

1 year ago

Reply

Ya sanyi don ?aukar novel dan Allah

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to mahamane-noura

Domin downloading novel na mu dole fa sai kayi subs da mu

Please Login or Register in order to submit comment