Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

7 ya haɗa da Gionee ɗin ya aika wa Yusuf a Gombe a bawa Sahla.

"Hi Handsome. i'm Noor" muryan wata budurwa ya daki kunnensa.

"Noor Wakili" ta mike masa hannu.

Bai mika mata hannu ba amma ya furta "F Kay Ubandoma" a hankali.

Zama ta yi gefensa sai murmushi take.

"Ina zaka je F K? London?"

Ya kalleta na sakan ɗaya sannan ya kauda kansa ya cigaba da latsa laptop ɗinsa.

Clearly irin matan nan ne da suka saba hitting mi shi. Casa'in da biyar cikin ɗari suna tunkaranshi ne karara da abinda ke ransu. Abinda shi ba zai iya musu ba.
He has stop trying tun kusan shekaru takwas da suka wuce. Lokacin yana shekarun 20's ɗinsa ya biya strip tease, lap dance, anything da zai nuna lafiyarsa but nothing works. So ya hakura ma da tunanin samun nasara. Ba zai iya ba, ba zai iya ɗin ba kenan.

Idan ka ga ya kula mace to ta zo masa ne da taimakon neman aiki ko wani scholarship kuma ya ga cewa lallai abinda ya kawota kenan. Ya riga ya saba da tactics ɗin mata irin su Noor Wakili. From yadda suke magana, yadda suke fari da ido, murmushinsu, tafiyarsu har ma da maganarsu.

Noor ta gaji da shirunsa ta mike tana wani kumbure-kumbure ta koma wajenta na da. Ko baka mata kallon kurilla ba za ka san irin yaran manyan 'yan siyasan nan ne wanda sun saba ana basu attention.

Finally bayan minti talatin da biyar jirginsu ya tashi.

Ahmad ne ya zo ya ɗauke shi a airport. Ya jima bai haɗu da sirikin nasa ba amma duk da haka sai daya ga chanji a tattara da shi. Ya kara tsufa. Babu wannan murmushin nasa
mai kama rai.

"Ahmad is everything OK? Wani abu ya samu Hasinah ne?"

Ka bari mu je gida. Zan yi maka bayanin komai.

Akwai tarin ayyuka a gabansa a Paris amma yanayin yadda Hasinah ta roke shi akan ya taimaka ya zo London koda abinda zai mata na karshe kenan yasa shi fasa tafiya Paris ya nemi ticket ɗin London.

Hankalinsa bai kwanta ba har suka kai gida.
Akwai fa'ida a cikin zumunci. The last time daya haɗu da Hasinah a bikin Mustafah ne. Tunda tayi aure sau ɗaya ya zo gidanta a London lokacin da ta haifi Faisal.

"Hasinah" ya kira sunanta lokacin da Ahmad ya turota a wheelchair.
Ta rame tayi wani fayau da ita.

"Aliyu Faruq" ta faɗa tana ware masa hannunta.
Ya mike da sauri ya rungumeta.

"Aliyu Faruk. Ɗanuwa yaushe rabon da na ganka. I miss you fa"

"Miya sameki?" Maimakon ta amsa sai ta ce " ya ka baro su Maami"

"Ahmad?" ya kalli Ahmad yana neman karin bayani.

Ahmad ne ya iya tsarge masa abinda yake faruwa. Tareda faɗa masa dalilin da ya sa suka kirashi.

"Faruk, Hasinah ba ta da lafiya. Cancer ance ya shiga stage IV. Bayan haihuwan Amir aka diagnosing ɗinta da shi. An treating na shi kuma ance ya tafi but last year abin ya sake dawowa. Za a fara yi mata chemotherapy nan da kwana huɗu. Faisal da Amir ba za su samu kulawa ba, kuma bama so su sani balle hankalinsu ya tashi.

" mun yi tunanin kaisu wajen Sayyidah amma gaskiya Sayyidah ba ta yi nitsuwar da zamu bata kulawar 'ya'ya biyu ba. Ba ma so su koma Nigeria har sai an gama treatment nata. F Kay muna so ka tafi da su Faisal ne"

Bai ce uffan ba har ya gama yi masa bayani. Tun yaushe Hasinah take fama da wannan matsalar amma suka rufe shi.
Abubuwan sun zo mishi bazata. Cancer. Stage IV. Ga Hasinah ko tafiyar kirki bata yi.
Idan ya ɗau yara biyu ya tafi da su Paris ya zai yi da su. Shi ko a Paris ɗinma ba wai yana zama bane a chan dindindin. Mostly sukan yi ziyarar aiki kasashe daban-daban.

Allah ya tsare shi da ɗaukan mai kula da su. Faisal is 10yrs shi kuma Amir shekara 6yrs. Ba zai yi sakacin da zasu samu jarrabawa irin tashi ba.

"Mi zai hana ku kai su wajen Maami a a Nigeria"

"Aliyu, Maami is busy tana koyarwa a Abuja, tana koyarwa a Kaduna sometimes har Fed Uni Lafia take zuwa as a visiting lecturer. Ba zata basu kulawar data dace ba. And ni bana so a kai yarana gidan da za a dinga yi musu kallon Agola."

"And Dad?"

"Seriously! Yarinyar Uncle Sulaiman wa yake kula da ita a gidan nan idan ba Kaka ba. Idan ka cire Anty Rafee'ah matan Dad psychos ne, suna bukatar gyaran kwakwalwa"

F Kay dai ya ɗan yi murmushi.

'Yan'uwan Ahmad ma ba option bane dan shima maraya ne, duk da tarin 'yan'uwa da yake da su babu wani a ciki da zai iya ba shi amanar 'ya'yansa. Ahmad self made millionniere ne. Scholarship ya samu yai karatu, daya gama kuma jajircewarsa da kuma tarin baiwar da Allah ya masa ya kawo shi wannan matsayi da yake ciki a yau.

Dake Faisal da Amir indigene ne na UK basu samu matsalar visa ba. Dama tuni an musu duk wani shiri daya kamata dan sun san da tafiyar.

Kwanansa biyu a London ya ɗau yaran Hasinah suka wuce Paris...


TOP-NOTCH.....the touch of excellence just for you.

✈✈✈SAHLA a Paris✈✈✈

013...My goal..

***
Wayata Gionee ta dawo ga kuma iphone 6. 'Yan bakin ciki sai su mutu arzikin Sahla ya zo.

lokacin dana ɗaura layina a sabuwar waya. Naci karo da texts ɗin Affan guda uku.

1- Sahla dear, i didn't mean to. Ba halina bane, soyayyar dana ke miki ya sa na rasa nitsuwata a kanki. Dan Allah ki kunna wayarki mu yi magana.

2- i'm sorry Amal ta dawo ta ga abincin da kika kawo, na san za ta gayawa Mom. Kiyi hakuri da faɗan da Mom za ta miki. Ki amsa wayata please...

3- kin san ke kanwata ce ba zan taɓa cutar da ke ba. Abinda ya faru was a mistake Dan Allah kar ki gayawa Abbanmu ko Alhaji...

Shege ashe ya ji tsoro. To ko na faɗawa Alhaji ne. To na ce me ?

' Alhaji na kaiwa Yaya Affan abinci shine ya tsareni a ɗaki wai zai ciremin kunya'
Wata zuciya tace min 'Hmm Sahla ki yiwa kan ki faɗa ki rike abin nan a ranki'
Allah zai saka min. Kuma sai na rama koba daɗe koba jimawa...

Ban san ana min bakin ciki ba a gidan nan sai da iphone ta shigo hannuna. Takanas na je falon Alhaji na nuna masa wayar da aka bani na ce ya tayani yiwa Uncle Faruku godiya. Ya ce sai in yi hankali da ita dan iphone ba Gionee bane.

Wallahi ko zaman minti biyar a ɗakin Kaka ba aka aiko wai a kirani.

Mama da Ummi ne suka haɗa zama.
Amal, Hanifah da sauran duk suna nan.

Ina shigowa Mama tace
"Yawwa. Sahla zo nan. Ance Faruk ya aiko miki da waya ko?"

"iphone 6 ya siya mata fa" Hanifah ta faɗa. Da wani katon bakinta a wajen.

"Lokacin da aka chanja muku waya duk tare aka haɗa aka siya muku. Dan haka ba zai yiwu yanzu ace ke kina da sabuwar waya su kuma basu da shi ba. Hanifah kin ce kuɗin wayar ya kai nawa?"

Kafin ta bada amsa Amal tace " Mama wallahi shige masa ta yi, na san rokon Uncle F Kay ta dinga yi. Sahla ba dai kwaɗayi ba. Haka ta samu Akhi wai tana son shi harda kai masa wani shirmen abincinta"

Raina yai matukar ɓaci. Ga ɓacin ran Affan ga kuma wannan fin karfin da ake son yi min.

Na ɗaga musu wayar nace " ga dai wayata nan original iphone 6 ne kamar yadda kuka gani" na nuna musu tambarin gutsirarren apple dake jiki.

"Wacce ta ke ganin roko nayi aka bani Dan Allah itama tayi rokon ta gani ko za a siya mata"

"Waya kuma in banda Alhaji banga wanda ya isa ya hanani amfani da ita"

"Sahla rashin kunya zaki mana. To wallahi sai kin bayar da wayan nan"

"Ayya! Ummi ina ce akwai Likita mai zuwa wajen Hanifah. Ku ce masa ya siya mata iphone"

"Wannan wayar dai farar kafata ce ya kawo min".

Na juya na tafi abina ina jinsu sunata masifa ko a jikina.
Dana shigo ɗaki na fara mamakin ya akayi suka san Uncle Faruku ya siya min waya.

Ikon Allah. Ashe munafurfur ɗin gidan ne. Lokacin da naje Umma Bilki na falon tana yankawa Alhaji lemo.
Munafuka ta je ta gulmata musu ta makale a ɗaki kamar ba ta yi komai ba. Kai ta Allah ba taki ba Umma Bilki...

***
Lokacin da Alhaji ya shigo ɗakin Rafee'ah a zaune ya sameta akan sallaya ta ɗaga hannu tana addu'a tana kuka.

Ya samu bakin gado ya zauna yana jiranta. Bai taɓa nuna mata ba amma ya damu kwarai da rashin haihuwarta. Musamman ma da ya san har yanzu da lafiyarsa tunda ga shi Zainab (Ummi) tana nan da tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe.

Bata daina addu'arta ba duk da kuwa ta ji shigowar shi.

"Allah kai ka bawa Zainab haihuwa har ta buɗi baki take min gori akan baka bani ba. Allah kaine ke bayarwa a lokacin da ka so kuma a yadda ka so, Allah ka bani haihuwa. Allah ko da sau ɗaya ne nima kasa na samu na ɗauki ciki na haihu. Allah kace idan aka shiga cikin kunci a tuntuɓeka domin kaine mai yaye kunci. Allah ka yaye min wannan kunci, ka maida min shi da farin ciki..."

Ta dinga nanata kalamai masu taɓa zuciya.

Alhaji yana zaune yana jinta. Jikinsa yai sanyi. Yayi alkawari yai bayan Maryam ba zai sake saki ba saboda illar sakin daya gani tunda gashi har yau baya da wani iko akan yaran da Maryam ta haifa masa, yana matsayin Uba ne a garesu amma babu shakuwa ta Uba da 'ya'ya a tsakaninsu. The last time da Rafee'ah ta masa maganar mutuwar auren Sayyidah takanas ya shirya ya tafi chan US ɗin. Amma Sayyidah tayi girman da bata bukatar taimako ko soyayyar shi. Kiri da kiri ta nuna mishi ba zata iya zama da shi a Nigeria ba.

"Idan na koma Nigeria bani da 'yanci sai abinda kuka ce kai da Kaka. Na san aure zaku ce zaku mun, ni kuma ba zan iya auren ɗan Nigeria ba. Ba zan iya zama da namijin da mace ɗaya ta masa kaɗan ba. Na saba da nan ba zan iya komawa Gombe da zama ba. Ka yi hakuri ka barni a nan"

Yana kauda kai ne a lamarin Zainabu saboda 'ya'ya dake tsakaninsu. Duk cikin halayenta babu wanda ya ke kyamata sama da sata. Alhamdulillahi yana iya kokarinsa wajen wadatasu da komai duk da 'yankoma baya da aka samu a kasuwancinsa. Amma Zainabu. Yayi masifar yayi hukuncin amma duk da haka lokaci lokaci yana kamata da laifin sata. Akwai lokacin da ya horata kusan shekara ya hanata shiga sashensa, saboda idan kuɗi bai ɓata ba agogo ko hula zasu ɓata. Irin satan da take masa tun farkon aurenta har yanzu yasa shi banbance satan da su Abdullahi da su Abbas ke masa da kuma wanda take yi.

To ya zai yi. Banda hakuri. Shi ya gani yace yana so. Abin kamar magani, tunda ya auri Aishatu sai zuciyarsa ta kwaɗaitu da cika sunnah zuwa mata huɗu. Zainabu kanwar wani abokinsa ne da suka taso tare.

Bilkisu ya haɗu da ita a gidan Radio. Tayi NCE Hausa tana aiki a nan. Bayan aurensu ya hanata aikin saboda wasu maganganu da ya ke ji akanta.

Rafee'ah? A rasuwan Sulaiman ya ganta lokacin tana bautar kasa a Asibitin da aka kai gawar Sulaiman. Sai da yai bincike ya gane ashe 'yar'uwar Maryam ce. Alhamdulillah gasu nan yau aure ya bawa shekara goma shauku baya.

Bai tanka mata ba har ta gama addu'o'inta ta shiga nannaɗe sallaya.

Wayarsa ce ta shiga kara ya ɗauka da sauri ganin mai kiran.

"Eh tana nan. Gamu nan zuwa ranka shi daɗe"

Yana gama wayan ya kalli Rafee'ah wacce itama shi ɗin take kallo.

"Maimartaba ne. Akwai wani case na haihuwa, ana bukatan ki"

Bata tambayeshi karin bayani ba ta cire hijabin sallarta ta buɗe closet dan ta ɗau ko wani hijabin tunda babu halin chanja wani kayan.

***
Tabbas Allah yana amsa addu'a a lokacin da ya so, a yadda ya so.

Rafee'ah ta sake kissing goshin yaron wanda har lokacin bacci yake. Bata taɓa jin karɓan ɗan wani ba. Kanwarta Hadiza ma ta mata tayin Ihsan ɗinta amma ta ki. Idan ta karɓa na kwana nawa ne za a zo a karɓa ko kuma a fara mata gori. Ta jure zama ita kaɗai iya waɗannan shekaru amma tun daga haihuwar yaron nan ta ji son shi ya shigeta. Ya sha wahala sosai.

Ba ta iya shiru ba lokacin da suka baro Asibitin ana maganar za a kai yaron gidan marayu. Tace Alhaji ya mata alfarma ta adopting yaron.

Mahaifiyar yaron mahaukaciya ce. Nakuda ta fara aka kaita Asibiti abin ya zo da complications shine aka gayawa Sarki ana bukatan kuɗin da za a mata aiki.

An mata aikin but she didn't make it. Ta jima tana yawon hauka. Akwai lokacin da aka ce har a Fada tana kwana. Daga baya kuma ta gudu ba a sake ganinta ba kusan shekara biyu sai gata nan kumadu amma wannan karan har da tsohon ciki.

Ta kissing kumatun yaron tareda kiran sunansa 'Ayman'

***
Ina zama a aji na ajiye jakata a gefe ina murmushi. Yau zamu fara lectures. Duk da ban samu course ɗin dana ke so ba amma wannan ɗinma ya min. Zan karanta abinda mahaifina ya karanta kuma sai nayi suna sama da Mahaifina. Ina ga ma yin Allah ne ya sa ban samu first choice ɗina ba sai second choice dana zaɓa wato English and Literature.

Wata budurwa ta zauna gefena tareda mikomin hannu muka yi musabaha.

"My name is Nazifa"

"My name is Sahla"

"Wow nice name"

Nace "Thank you"

Ba a jima ba lecturer ya shigo muka fara lectures ɗinmu na farko.

Kai Jami'a akwai daɗi. Ina tafiya a cikin school ina jin kaina nima wata ce. Ina tsakiyan sabbin friends ɗina Nazifa da Alheri, muna tafiya muna taɗi. Kowa da burin daya saka a gaba.

Ni nawa burin na yi karatu mai zurfi na zama professor of English. Wai! Har na hangoni ana kirana da Professor Sahla.
Wannan burin na saka a gaba kuma sai na cika shi. I will make my late father proud. I will make Alhajinmu proud.

Mun gama lectures fa tuntuni amma muka yita yawo har hostel. So nake na ga Jami'a, Jami'a ta ganni.

Ni kaɗai ne a GSU. Hanifah ta samu ABU amma maimakon Pharmacy sun bata Biochemistry. Ita kuma Safiyya dama JAMB ɗinta bai yi kyau ba balle har tayi tunanin samun admission.
Da farko Hanifah tace ba za ta je ba sai an chanja mata course amma chanjin course bai yiwu ba dan haka da ta bari admission ya wuceta sai ta hakura ta je tayi registration.
Safiyya kuma wai za a nema mata admission a Fed Poly Bauchi.
Ni kam ina ruwana ina son GSU ɗina. In je lectures in dawo gida in haɗu da tsohuwata.

Tun bayan rabuwar mu da Affan na hana kaina kula samari. Shegu kaman ance na shiga GSU dan samari ne. Bini-bini Sahla ina so mu zama friends, Sahla ina son ki. Sahla ki bani chance na zo gidan ku.

A ajinmu idan ka cire Ma'aruf sai kuma course rep ɗinmu Hassan babu namijin da nake kulawa. Kowa sese ne tsakanina da shi.

A gida kuma Yaya Yusuf ne yake takura min. Watarana takanas ya zo ya ɗaukeni bayan mun gama lectures ya kaini wani restaurant har ina tunanin abin kirki yasa shi zuwa ɗaukana ashe da nasa manufar.

Muka zauna ya tsige mun abinda ke ran shi. Wai sona yake. Wai da gaske idan na bashi dama aurena zai yi. Wai ya jima yana dakon soyayyata.
To ni na bashi dakon ne da zan biya. Shi ya ga zai iya shiyasa ya ɗauka.

Ya gama I love, I die, I live, I mad ɗinshi na ce masa yai hakuri ni na dena soyayya. Ko zan yi soyayya ma ba zan kara yi da ɗan gida ba, Allah ya kiyaye, ɗan bakara.

Mun jima a wajen yanata yi min karatun so amma na ki ɗaukan darasi ko ɗaya. Toshe kwakwalwa na nayi karma ta yi munafurcin ɗaukan karatun ba tareda na bata izini ba.

Imba Yaya Yusuf bama, sai daya gama zane nin zai wani biyo baya wai yana dakon soyayya na. Wallahi irin dukan da ya min ko Yaya Mustafah iya kaci.

Cewa yai zai bani lokaci na yi tunani kafin mu kare first semester ɗinmu. Na ce masa kar ya sa rai. Haka kawai, ba a soyayyar dole...

*

Karatu ya fara nisa dan assignment da presentation muke yi ta ko'ina. Book review da ake bamu kuwa kamar bamu da abinyi sai karatun littafi.

Mr Thomas ya bamu review ɗin littafin Jaguar Nana, shi kuma Mr Akilu ya bamu review na Chinua Achebe. Ga Malam Mukaddas ma ya bamu kusan littafi uku yace mu rubuto mishi review ɗinsu.

Yanzu Karatu nake kamar zan yi hauka wani lokaci dai sai ka ganni da novels huɗu a lokaci guda ina karantawa.

Sai da muka shigo tsakiyar semester na gane cewa Jami'a ba wasa bane, ashe daɗin suna garai ba daɗin yi. Ni da Nazifa da Alheri da Ma'aruf muka haɗa clique ɗinmu, muna taimakawa juna da tutorials. Abin dai kamar na hakura da burina. In dai haka first degree yake da wahala to da alama ba zan kai matakin Professor ba. Kai Ya Allah...


TOP-NOTCH.....the touch of excellence just for you.

✈✈✈SAHLA a Paris✈✈✈

014...The Plan...

Ina zaune ina rubuta review Anty Amarya ta yi sallama. Kaka na zaune ta yi nisa da tunani.

"Sahla dan Allah ga Ayman nan ki kula min da shi kafin na dawo. Muna da surgery ne ba zan iya tafiya da shi ba. Akwai abincin shi a nan, idan akwai abinda na manta ban saka ba ga key nan ki je ki ɗauka"

Tab. Anty Amarya ce da barin key ɗin ɗakinta. Kai ashe reno na chanja mutum.

Na karɓi Ayman ina mishi wasa. Lokacin da aka kawo shi Alhaji ya tara dukka gidan aka yi meeting yace mana Ayman ɗan Anty Rafee'ah ne dan haka ɗansa ne. Ko bayan ransa bai yafe ba wanda yaiwa Affan kallon ba ɗan Kabiru Ubandoma bane.
I remember har sunan Ummi da Umma Bilki ya kira ya ja musu kunne akan duk wacce ta yiwa Ayman gorin asali a bakin aurenta. Alhaji yayi faɗa sosai.

A ranan sunansa anyi shagali sosai. Bayan sati biyu da sunan shi Ummi ta haifi 'ya mace. Ta sha burin namiji zata haiho amma Allah ya turo mata 'ya mace.
Tun kafin ayi suna aka fara rikici da ita akan Alhaji ya ki sake hannu ayi shagalin suna kaman yadda aka yiwa Ayman. Rabon da ayi haihuwa a gidan ai an jima. Alhaji yace ba za ayi shagali ba.

Ita dai yarinyar ba a saka mata suna Fatima ba sai aka saka mata Khadijah muna kiranta Baby Dijah...

"Kaka ta yi bacci ne?"

"Ki bar Kaka fa. Kuna magana yanzu zata bige miki da bacci"

Anty Rafee'ah ta fita bayan ta yiwa Ayman kiss a goshin sa.

Yaron kyakykyawa da shi, idan ba a faɗa maka ba baza ka taɓa sanin ba Anty Amarya ta haifeshi ba. Shima fari ne sosai kamarta.

Da na ga yaron zai hanani rubutu sai na ɗaura shi akan gado, ya ɗan yi kuka kaɗan yai shiru ya fara bacci.

Ina rubutu Kaka tace " Sahala yanzu wai Kabiru da AbdulKarimu ba zasu biya mini kujerar Makkah ba. Anya ba zan sai da Tumakai da Awaki na ba?"

Na yi dariya nace " Kaka kenan, kuɗin jirgi fa ba kuɗin motar Gombe zuwa Abuja bane. Kaka kema ki hakura da maganan nan, kwanan nan fa kullum sai kin yi korafin kafanki"

"Kema goya musu baya zaki yi. Ai ina gani a TV masu lalurar kafa na zuwa Hajji, zaka ga ana turasu a keke"

"Kaka idan aka ce za a biya miki kujera ma ni zan ce kar su biya. You are so obssessed..." kwal na ji sanda a kaina.

"Amma Kaka Allah, Allah kina cin zalina, nifa marainiya ce"
Ta ɗaga sanda za ta sake kwaɗamin na yi saurin jan littafina na gudu...

*

Su Abba zasu dawo Nigeria da zama. A bakin Kaka na ji yau dana dawo daga lectures.
Na yi ko oho da labarin. Ni ina ruwana da su, idan ka cire Abba dukkansu ba ruwana da sha'aninsu.

"Ni kam ba zance kuke da Afan ɗinba"

"Allah ya kiyaye na yi zance da shi. Ni fa Kaka ki barni, karatu zan yi mai zurfi sai na ga karshen biro"

"A'a ki zama Alhudahuda karshen karatu kenan. Ke da nake so ki shirya da Yusufa nayiwa Kabiru magana a yi 'yar gida nan da farkon shekara mai zuwa"

"Kaka karatu zan yi. Ba ruwana da aure. Mai ake yi a aure banda cire kunya"

"Auren ne ba amfani. Ita Asiya data sha boko ta koshi gashi har yanzu babu mashinshini. Ina raye ba zaki karisa boko ba sai a ɗakin mijinki. Ba kya ganin Asiya ne"

"Kaka kenan, ke kika ce jifa aka yiwa Anty Asiya yanzu kuma kince boko ya hanata aure. Da aure da mutuwa duk lokaci ne. Ke ya ba ki mutu ba da Inna Sadiyya ta rasu."

"Amma Sahala zan ci..."

"Sulaiman yana can kabarinsa. Kila ma yana jiran zuwanki gobe"

"Sahala!"

Na kyalkyale da dariya. Tsohuwar tawa bata son zancen mutuwa.

Ko sati biyu ba ayi ba da maganan da muka yi da Kaka su Abba suka dawo. Ance Affan yana chan saboda zai karisa masters ɗinsa. Ita kuma uwar yanga Amal ance transfer za a mata ta dawo private university, ko wannene ohon musu.
Da alama Mom ɗinsu ba ta so dawowarsu ba. Daga baya naji gulma a cikin gida wai bata so su zauna a Gombe ne, ta fiso su koma Abuja.
Matar nan tunda suka dawo ita da 'ya'yanta sai sun ga dama suke shigowa su gaida Kaka.

Ni ko ina ruwana babu abinda na saka a gaba sai karatu dan mun kusa fara exams...

Abinka da kawancen munafurci. Ummi da Mama sai da suka yi kaca-kaca akan Mom.

Matar nan sai wani shishshige mata suke yi ita kuma tana koransu kamar kuda. Idan ka cire Anty Rafee'ah babu wacce take gani da wani daraja. Girman kan tsiya ne da ita ga rashin son mutane ko nace talakawa.

Akwai wani rana da kunnena naji Mom ɗinsu Amal tana kiran su Ummi da 'ya'yan matsiyata.
A raina nace madallah, maganin masu kwaɗayi kenan.

*

Alhamdulillahi mun yi jarrabawa mun gama. Kuma ina da yakinin ba zan samu matsala ba dan mahaukacin karatu nayi, duk kwaɗayina da son cin abincina a lokacin exams ɗin nan wani lokaci sau biyu nake cin abinci, kuma ba wani abincin kirki ba.

Muna cikin hutu daf za a yi resuming school ASUU ta fara yajin aiki. Kamar wasa aka yi yajin aikin sati biyu. Sati biyu ya kare aka sake shiga yajin sai Baba ta gani.

Tun ina tsammanin dawowa har na fara jiran maatayyassara kawai.

Ana wannan zaman shirun ne na fara koyon cake a wajen Anty Rafee'ah. Kila nima cake ɗin zan fara tunda boko ya gagara. Ko ince mu 'ya'yan talakawa Boko ya gagaremu.

A wannan zaman ne aka haɗa auren Asiya da wani abokin Baffanmu Abubakar. Ɗan kasuwa ne yana da mata biyu ita zata je ta uku. I'm very sure Anty Asiya ta amince da auren nan ne saboda maganar mutane. Mutumin fa idan bai yi sittin ba to saura kiris, gashi wani luti da shi. Astagfirullah.

Bikin dai anyi ne amma babu wani armashi. Anty Asiya tace ba za ta yi events ba banda walima. Su kuma Mama da Ummi da ya kamata su haɗa kai ayi komai har yanzu basa magana.

Aka gama hidiman biki aka kai Amarya gidan mijinta a chan Kano.

Muka sake zama a gida muna jiran tsammanin Man Rabbuka. Amma shiru.

Ranan kamar an tsikare ni ina zaune ina latsa iphone ɗina wani abu ya faɗo min.

"Kaka" shiru

"Kaka"

"Na'am"
Ta amsa min da kyar.
Allah Sarki, ta saka damuwa sosai a ranta yanzu bata da wani energy kamar da. Idan ana abu a gidan ma ba kasafai take shiga ba.

"Kaka ina da wani plan. Amma sai kin dage plan ɗin zai yiwu"

"Minene kuma pillow?"

"Kaka Plan ba Pillow ba. Ko dai kunnenki ma ya fara taɓuwa ne"

"Bana son shiririta Sahala. Minene?"

"Ba kina son zuwa Makkah ba. To akwai yadda za ayi hakan ta faru"

Kaka ta mike zaune da sauri jin maganan Makkah.

"Kinga Uncle Faruku yana da kuɗi. Idan kika masa magana zai biya miki kujerar Makkah.

2 Comments On SAHLA A PARIS
avatar
mahamane-noura

1 year ago

Reply

Ya sanyi don ?aukar novel dan Allah

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to mahamane-noura

Domin downloading novel na mu dole fa sai kayi subs da mu

Please Login or Register in order to submit comment