Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ci gwaiban na ci biyar ta ci uku.

Da Isha cikina ya ruɗe na nufi banɗaki zan buɗe na ji anyi gyaran murya.

"Kaka ki fito kashi zan yi"

"Nima ita zan amma ta ki fitowa"

"Kaka Allah rabin minti na baki ki fito"

Na tsaya jikin kofa ina ɗan jijjiga jikina kaɗan-kaɗan ko kashin zai tafi. Chan na tuna da wakar da muke lokacin muna yara. Na fara rerawa a hankali.

"Kuliya Kuliya cinye mun kashina"

Na sake buga kofan " Kaka ki fito mana"

Maimakon tayi magana sai tayi gyaran murya.

" Kaka ki fito fa. Zan miki kashi a ɗaki Allah"

Na tsugunna a wajen na rike ciki ina jijjiga jikina ina yin wakar da karfi.
Chan kusan minti goma sai Kaka ta buɗe kofa.

Hawaye na gani a idanun Kaka.

"Dama na gaya miki Gwaiban nan bata gama kosawa ba"

"Kaka ni kam ki matsa"
Na wuceta na shige banɗakin.
Na zauna a toilet seat ɗin ina jira na ji zurrrrr sai na ji wani zafi a takashina. Ina nishi ina tura kashin amma ya ki fita. To ko dai takashina ya toshe ne?
Na sake yin nishi ina turawa amma abu shiru. Can wani mai tauri ya fara fitowa amma sai ya makale shi bai faɗi ba shi bai fito duka ba.

"Wayyo Kaka nima yaki fitowa"

Inaga na yi minti ishirin a banɗakin nan ina nishi, ga Kaka sai buga min kofa take.

Na fito haka nan ba tareda na samu biyan bukata ba.

Ni da Kaka muka tsaya kallon kallo.

"Ke sabulu zamu saka zai fito "

"Sabulu kuma Kaka"

"To ki kunna mana risho mu turara takashinmu da ruwan zafi"

"Allah ya kiyaye Kaka"

Ai kuwa duk option ɗin da Kaka ta kawo sai na ce bai yi ba. Karshe nace barin je na karɓo mana magani a wajen Mama ko Umma Bilki na san ba za a rasa ba.

Na je na karishi zagayena wai babu maganin ciwon ciki.
Na dawo na samu Kaka ta kunna stove ta ɗaura ruwan zafi a tukunya.

Ko mi tsohuwar nan ke shirinyi oho.
Ni dai na tsugunna gefe na cigaba da wakata 'Kuliya Kuliya cinye min kashina"....


007 Sausage...

***

Kowacce rana rana ce ta ambaton Manzo Rasulillahi. Kowacce rana rana ce da za a gode, ayi murna da haihuwarka Aminullahi. Kowacce rana rana ce da za a yabeka ai maka salati sannan a sake yabonka Habibullahi.
A yau ina kara jaddada Salati da yabo gareka ya Manzon Allah.
Allah Albarkacin Sayyidul Mursalina kuma Khatimul Anbiya'i ka amsa mana addu'o'inmu, ka karemu daga dukkan bala'i da jafa'i. Ka kawo mana shuwagabanni na gari masu tausayinmu, masu rikon Amana.
Ya Allah albarkacin LAA'ILAHA'ILLALLAH MUHAMMADUN RASULULLAH, ka sa albarka a rayuwarmu, ka sa albarka a kasuwancinmu, ka yiwa 'ya'yanmu albarka, ka kara mana ilimi, basira, arziki da kuma imani. Ka rabamu da son zuciya da zalunci. Allah ka shiga lamurranmu. Allah ka jikanmu, ka gafarta mana zunubanmu, ka karbi tubanmu ka kuma sa mu mutu cikin imani. Ya Allah kuncin talauci, kuncin zuciya, kuncin matsi, kuncin bashi, kuncin karayar arziki da asara, kuncin jahilci, kuncin rashin aure, rashin haihuwa, rashin kwanciyar hankalin gidan miji ka raba mu da su Yaa Rahimal Masakin, Ya Rabbu Muhammad...

***

Ina sauri zan shiga sashen Alhaji na ji an kira sunana. "Sahla"
A meeting da aka yi watan daya wuce Ummi tayi maganar ya kamata a siyawa Zuhriyya waya shine Alhaji yace zai siya har da nawa da Safiyya. Hanifah ta ɗaga hannu wai ita fah. Alhaji yace sai wani shekara.
Ni Sahla guda zan yi waya, tawa ta kaina bata aro ba.

"Yaya Yusuf"

Rankwashi yai min a ka, a raina nace Allah ya isa.

"Za ki fito tun daga ɗakin Hajiya Kaka babu hijabi. Idan akwai baki a falon Alhajin fa"

"Yaya kuma sai na saka hijabi kamar wata matar aure, ɗan nan da nan ɗin"

Ya sake kai min rankwashi na kauce sauri.

"Ki dinga saka hijabi Sahla. Kinga yanzu kin girma.

"To na ji ɗin"

Na sauri na wuce shi. Mugu kawai, shi komai sai ya taɓa lafiyar mutum.

Ina zuwa na samu Alhaji yana zaune a falo yana ta lissafin wasu kuɗaɗe.

Na tsugunna na gaishe shi fiskata cike da fara'a.
Bai yi magana ba. Su Safiyya sun riga sun karɓi wayansu tun ɗazu, nima kitso na je shiyasa ba a bani tareda su ba.
Na zauna fa ina wangale ta hakora kamar mai tallen MacClean amma Alhaji bai ko dubi inda na ke ba. Ya cigaba da irga kuɗaɗen dake gabansa yana saka su a wani jaka.

"Alhaji nan ga an bawa su Safiyya waya"

Ya ɗago kai ya kalleni yace " iyi"

Na ɗan sosa kaina nace "Alhaji ba ka ce harda ni zaka siyasa ba"

"Ayya ashe ba su faɗa miki ba. Ai kaf gidan nan sun kawo karar ki sun ce ba kya jin magana. Dan haka ke da waya sai kin nitsu"

"Allah a nitse nake. Wallahi na nitsu. Tunda Kaka ta tafi Umura ba randa bana aiki a gidan nan. Jele na ke tsakanin wajen su Mama, Ummi da Umma Bilki"

"Ao haka ko?"

"Allah ka tambayi su Fadilah ka ji za su gaya maka gaskiya"

"Ina kika tsaya a haddar ki"

Na yi shiru na sunkuyar da kaina. Kusan wata biyar kenan na kakare a suratul Hudu. Da tare muke tafiya tare da Zuhriyya gashi ita har ta kusa karisa suratul Tauba.

"Kin tsaya wasa ko?"

"Alhaji Allah ba haka bane. Ka yi hakuri zan kara himma"

"Kinga iyayenki Allah ya jikan rai duk mahaddata Qur'ani ne. Kinga Sulaiman babu wanda ya kaishi nacin karatun addini. Ba dan Allah bai yi zai yi tsawon rai ba na tabbata da yanzu ya zama babban Malami"

"Alhaji su Kaka suka ce wai Babana yana da faɗa"

Alhaji yayi dariya ya ajiye kuɗin da ke irgawa akan table yace " Yana da zafin rai kam amma idan har aka taɓo shi. Baya son karya ko kaɗan"

Ina jin daɗi idan Alhaji yana bani tarihin mahaifina. Domin a wajen shi ne nake sanin irin rayuwar da yai. A wajen Kaka kuma na san tarihin yarintar shi.

Ance Babana Malamin makaranta ne. Ya koyar da English a makarantun Sakandare dayawa. Kusan duk wanda ya san Babana to ya san shi da inkiyar Sulaiman Dodon English. Gashi ni kuwa turancin jani in jaka muke da shi kullum ina kama shi yana guduwa.

"Sahla mi kike so ki zama?"

"Ina so na zama..." babu, ban san mi nake so na zama ba. Ina son zama wata shaharriya. Amma a me?. Kafin mu shiga SS 1 na rinka jayayya tsakanin zama Likita, Lawyer da kuma Engineer. Ina son zama Dr Sahla, ina son zama Barr. Sahla, ina son zama Engr. Sahla duka a lokaci guda saboda ina jin daɗin haɗa sunana da wannan profession ɗin. To amma da muka fara darasin Maths, Physics da Chemistry sai ido ya raina fata. Duk abinda na ke so sai na ga akwai wahala a tattare da shi. Ni kuma so na ke ni da wahala mu yi hannun riga. Mu tafi in parallel kamar yadda wani malaminmu na maths ke yawan faɗa.

Da aka zo za a raba mana aji a second term sai na gudu na koma Art class na ce kila dai Barrister ɗin zama. Amma da na tambayi Yaya Sulaiman ya karatun Law yake sai na ji jikina yayi sanyi. Shima Yaya Sulaiman da yake guru yana faɗa min akwai wuhala. Ajinsa uku a jami'ar BUK yana karantar Law.

"Ki fara tunanin mi kike so ki zama tun yanzu kin ji. Wannan zai sa da zaran kin gama secondary school kin san ina zaki faɗa"

Nace masa na gode.

Ya ɗauko kwalin waya a gefensa ya bani.
"Banda kule-kulen samari kinji, ki bari ki gama aji shida tukunna"

"Nagode Alhaji"

Na fito daga ɗaki ina murna.

Yace ya riga ya siya mana sim har an saka mana a ciki.
Wayar Tecno ce karama amma za ka iya yin kusan komai da ita har da facebook da To Go. Ni ba wannan bama, za a turamin indian film ga kuma litattafai da zan dinga karantawa da shi.

Ina shiga ɗaki na buɗe kwalin na fito da wayar na rungumeta a kirjina ina jin daɗi. Ina ma ace Kaka tana da waya, ai dana kirata na ji yaushe zata dawo tunda Alhazai sun fara dawowa.

Na tashi na ɗauko littafin da nake rubuta nambobin kawayena dana 'yanuwan Mamana na fara kwafa ina saving a wayata.

Da dare ina zaune a ɗaki ina kallo a sabuwar wayata sai ga wata numba ta turo min sako.

"Barka da dare Fatima Sahla. Ga kyau ga babban suna"

Na yi saurin taɓa fiskata ina wani jin daɗi, wai ina da kyau.

"Ki kulamin da kanki kin ji"

Ikon Allah. Waye kuma wannan ba suna ba komai. Ni dai na san ban bawa kowa numbana ba tukunna duk dama Alhaji ya saka mana katin ɗari biyar a ciki amma ban kira numbar kowa ba sai ta 'yanuwana musamman wanda bama tare da su.

Na sake karanta sakon ina murmushi. Duk da bansan waye ba amma na ji daɗin cewa da aka yi ina da kyau...

*

Da safe na je karɓan abincina a sashen Mama na ga Yaya Yusuf yana shan kunu da kosai yana ci yana blackberry ɗinsa.
Na gaishe shi nace "Yaya Yusuf Dan Allah ka bani numbar Affan" wani kallo ya watso min sai dana tsorata na ja baya. Bai kulani ba ya cigaba da shan kununsa.
Ko mi ya same shi oho. Na wuce kitchen na je na ɗauki abincina. Zan wuce ya dakatar da ni.

"Daga an baki waya sai ki fara kiraye-kirayen samari, uban me Affan ɗin zai miki idan kika kira shi"

"Daga zan yi zumunci sai ya zama abin faɗa. Allah ya baka hakuri zan kira Yaya Sulaiman na ce ya turo min"

"Har kin fara waya da Sulaiman?"

"Iyi, yace idan zai dawo daga Kano zai kawo min gurasa da nama. Ka san da farko bai gane muryata ba..."

"Wai ba makaranta za ki je ba kika tsaya surutu"

"To ba kai bane na tsayar dani"

"Wuce daga nan ko na zane ki"

Na juya da sauri ina murguɗa masa baki.

To ina ruwansa da wanda na kira.

Ina zuwa ɗaki kuwa na kira Yaya Sulaiman, inaga ko yana wajen lectures ne dan bai kira ba.

Dana gama karyawa na ɗau jakata na kulle ɗaki na wuce sashen Ummi. Yaran nan 'yan duniya ko uniform basu saka ba haka na jira sai da suka gama shiryawa.
Kawata kut da kut a makaranta Hassana sunanta, anguwarsu yayi nisa da mu ai da da ita zan dinga tafiya makaranta.
Su Safiyya idan ni ce na ɗan makarar da su basa jirana sai su kama hanya su tafi, amma idan nine haka zasu yi ta bani hakuri wai na jira su. Kamar dole nima sai na jira ɗin. Mtssw.

**

Yau na yi saurayi a facebook ɗan kasar India, wai sunansa Anwar Khan. Shi a dole wai sona yake, har da cewa zai zo Nigeria. Yace na tura masa hotona na tura masa hoton da na saka a facebook ɗina wanda na ɗauka a sallah da wayar Anty Salima kanwar Mamana. Dake babbar waya ce hoton ya ɗauku, yayi kyau sosai. Ina sanye da kayan sallah na wani material mai flowers ja an yi min riga da skirt. Na ɗaura ɗankwali amma gashina ya fito saboda kitson gaba na yi.

Chan daya turomin reply sai ya turomin wani abu kamar sausage irin wanda Mom ɗinsu Amal ke yankawa ta saka a fried rice.
Na tambayeshi mi ya turo sai yace wai na tura masa nawa. Ni a shashancina sausage yake nufi sai nace ai bamu da shi. A gidanmu ba kowa ke ci ba. Kaka ma idan aka saka a abinci tsincewa take ta zubar.

Sai ya turomin da wani hoto wanda yasa na sake wayar ta faɗi kasa batirinta ya fita.

Ni Sahla nayi gamo. Shege ɗan iska. Raina yai matukar ɓaci. Ni da har ina tunanin ko nima ɗan India zan aura kamar yadda Anty Sayyidah ta auri wani ɗan Pakistan. Nifa har na hango ni a cikin jan sari an min kwalliya irin na amaren indiya.

"Allah ya tsine" na faɗa tareda jan doguwar tsaki.

Ni ban kara bin ta kan wayar bama bayan na haɗata sai chan dare bayan na gama dukkan assignment ɗina na ɗaukota. Kamar kullum wannan mai shegen nacin turo min sakon ya sake turo min wani sako. Ni idan na kira numbar ba za a ɗauka ba, wani lokaci kuma ba ta shiga. Na sha tura masa cewa idan ba zai faɗa min ko shi waye bane to kada ya sake tura min text amma shegen naci baya jin magana.

"Ki kwantar da hankalinki 'yanmata, zan bayyana miki kaina da zaran kin kammala sakandare saura muku term uku ai ko? Mu kwana lafiya...Mai son ki a koda yaushe"

Mtsw in ka ga dama ka bayyana kanka in ka ga dama ka cigaba da zama a duhu...

A facebook na samu nambar Affan. Dana searching suna Affan AbdulKarim Ubandoma sai na ga hotonshi da sunan da yake amfani da shi a facebook wato Appan A Ubandoma. Na tura masa friend request. Na kuma ɗauki numbarsa na saving. Da rana dana dawo daga makaranta dana shiga facebook sai na ga ya accepting ɗina har turamin da Hi dear. Kin yi waya? i miss you. Na ji wani shegen daɗi a raina. Affan yace yayi missing ɗina.
Nima nayi missing ɗinsa dan sallar Azumin bana basu zo Nigeria ba wai Abbansu da Mom ɗinsu sun tafi Umurah shi kuma suna exams.

Kullum na hau facebook ina makale da Affan. Wancan shegen na yakice shi dan kullum sai yai ta turomin hotunan banza. Yaya Sulaiman na tambaya ya koya min yadda ake blocking mutum a facebook.

Mu kan ɗa yi chatting da Yaya Sulaiman ma amma shi mun fi yin hiran karatu da shi musamman da yake daga mun kusa shiga SS 3. Shi yake bani shawaran na yi Law wai zai karɓeni, wai ina raina kaina ne amma ina da ilimi da basiran saurin rike abu.
Ni dai har yanzu ban yanke shawaran mi nake son zama ba. Kila idan muka shiga SS 3 zan samu matsaya akan mi nake son zama...



***

008...hujin ɗuwawu...

Bacci mai daɗi nake aka ɗaka min duka na tashi a gigice. Zuhriyya ce tsaye a kaina.

"Iskancin banza, wa kika fi a gidan nan da zaki baje kafa ki kwanta bayan ga can aiki na jiranmu a kitchen. To Wallahi ki fito ko in haɗa ki da Yaya Yusuf"

"To kuma sai ki ɗake ni?"

"An ɗaka ɗin. Mtsw" ta wani juya ta fita

Ohhhhhhh. Ba dama mutum ya ɗan kwanta sai ace aiki-aiki.Allah dai ya dawo min da Kaka lafiya. Tunda ta dawo daga Makkah ciwon kafa ya sakata gaba. Yanzu haka satinsu ɗaya kenan da Abba ya zo ya ɗauketa zuwa Egypt.

Aikin gidan nan kuwa yanzu baya karewa, musamman yau Jumma'a da ake abincin sadaka.

Tashi nayi ina kunkuni, na ɗauki ɗankwali na ɗaura dan baka isa ka fita nan da nan babu ɗankwali ba yanzu zaka sha rankwashi a wajen Yaya Yusuf.
Doguwar riga na saka na atamfa. Atamfar ma ta ci na kyautar da ita amma na kasa rabuwa da ita. Duk ta koɗe.
Atamfar 'yar amana ce. Da na dawo daga makaranta ita ke saman akwati dan haka sai na ɗauka na saka, ga shi ɗinkin simple gown ne bata kama ni ba kuma bata yi buje dayawa ba, ina sakewa sosai ciki idan na saka.

"Sahlaaaa" ta sake kwala min kira

"Na'am"

Mtsw! Kai Zuhriyya akwai naci. Ni wallahi ban so aka haɗani aiki da ita ba. Gashi komai sai ta bar min ni zan yi.

Na ɗauki wayata na jawo kofar ɗakin na rufe. Na nufi sashin Umma Bilki dan ita ke da girki.

Ina zuwa na samu Zuhriyya tana zaune gaban kayan miyan da za a gyara tana danna waya.
Dama na sani ba zata fara komai ba sai na zo. Duk rashin son aikina Zuhriyya ta ninkani a son jiki.

Ina zuwa na ɗan zunguri keyarta kaɗan, sai ga wayarta ta faɗa cikin kayan miya.
Tasowa tayi ta shako ni.

"Shegiya kika jefa min waya cikin ruwa. Wallahi ba zan yarda ba"

"To nina ce ki tsaya danna waya. Ba aiki aka ce muyi ba"

"Dama Sahla kin rena ni a gidan nan, to yau sai na koya miki hankali"
Muka fara faɗa kicici-kicici.
Ganin ta fara galabaitar dani sai na gaftara mata cizo a wuyanta. Ta saka kara. Na samu na turata da karfi sai gata cikin bahon kayanmiya.

"Wayyooooo Ummina, Wayyo, Wayyo niiii"

Maimakon ta tashi sai ta zauna a cikin bahon tana kuka, sai wayyo take kamar wacce aka kashewa iyaye.

Na ɗauka ko ɗuwawuntane ya makale tunda roban ba wani faɗi yake da shi sosai ba.
Na kama hannunta na jawota da karfi. Aikuwa sai ga jini. Na shiga uku akan wukan dake cikin kayan miyan ta faɗi.
Na saka hannu aka na kwala ihu ina kiran Umma Bilki, dama duk sunan da ya zo min.

Yaya Yusuf aka kira ya cire wukar. Ya mata first aid sannan suka wuce asibiti dan a mata ɗinki.

Kafin su dawo sai da na kwammaci ban zo duniya ba. Ummi kamma cewa tayi wai kishi nake da Zuhriyya, shiyasa nake son nakasa mata 'ya. wai ina bakin ciki saurayin Zuhriyya manajan banki ne.
To ni ina ruwana da saurayinta. Na ce musu ina neman saurayi ne. Ina tareda Affan ɗina mi zanyi da wani kato wai manajan banki.

Da suka dawo daga Asibiti na kukuta na je gaisheta, tana kwance tayi ruff da ciki daga ita sai shirt da bum short.
Ina cewa Zuhriyya ya jiki Ummi ta hayayyako mini.
"Me kuma kika shigo yi?"

"Ummi Allah ba da sani na bane"

"Sahala fita mana daga ɗaki kafin muma ki mana lahani. Mai farar kafa kawai"

Ban iya magana ba, na zame jikina na fita. Kullum maganar kenan, Sahla mai farar kafa. Na koma ɗaki na zauna a kasa na zabga uban tagumi kamar wata tsohuwar data rasa duka 'ya'yanta. Wato nifa yau idan aka ce babu Kaka a gidan nan ba karamin wahala zan sha ba. Babu mai sona tsakani da Allah.
Ni dai Sahla a komai bani da sa'a. Daga faɗa da 'yar'uwata shikenan sai ga ta da hujin ɗuwawu. Wayyo ni Sahla.

Ban yi minti biyar a ɗakin ba Fadila ta shigo wai inje in ji Yaya Mustafah. Tsabar gulma har sun kira shi. Ga shi Alhaji baya gari balle na samu sassauci.

Ni ko in gudu ne? To idan na gudu ma duk inda zan je gidan 'yanuwa ne kuma ina zuwa zasu kira gida su gaya musu. Ko in gudu Jos ne gidan kanin Mamana?
Wata zuciya tace min kije Fada. Ai kuwa tuni na ɗau leda na zuba kayana kala uku a ciki na ɓoye cikin hijabi na saka nikabi na fito. Ina cikin rufe kofa na ji gyaran murya a bayana, nan da nan na yar da ledan hannuna na juyo a tsorace.

"Wayyo! Ashe kaine. Har zaka sa min heart attack"

Ya haɗa hannunsa ya naɗesu a kirji. Yana kallona kamar irin bai ganeni ɗinnan ba.
Na ɗaga nikab ɗin sama nace " Uncle Faruku nine dai. Ka rufa min asiri kar ka faɗawa kowa?"

murɗe min baki yayi yace

"Ni sa'an ki ne?"

Na sa hannu ina kokarin kwace bakina amma na kasa ture katon hannunsa. Kai mutumin nan Basamude ne.
Yama bar ni na tafi ya ki, idan Yaya Mustafah ya kamani a gidan nan kashina ya bushe.
Yana sake min baki na haɗiyi numfashi da kyar. Ko sakan uku banyi ba na hango Yaya Mustafah duguzum- duguzum yana nufo mu.

"Innalillahi" shikenan na shiga uku a gidan nan. Na kama kofan ɗakin ina kokarin buɗewa amma inaa...

"Looking for this?" Ya kaɗa key ɗin a dai-dai hancina.
Na haɗiye miyau makwat dan tabbas yau luguden duka zan sha.

"Yawwa F Kay kama min ita, dama sai da na yi tunanin guduwa za ta yi"

Tun kafin ya kariso na wage baki na fasa ihu "Wayyo Kakaaaaa, Wayyo Alhajina za su kashe niii"

Shi kam tsayawa yai yana kallona. Yaya Mustafah kuwa yana zuwa ya talli kaina tareda fizgar hannuna wai mu je. Yana jana na ji an rike ɗaya hannuna gam. Ban dena kuka ba na juya na kalle shi.

"F Kay bar min ita na je na casata gaba ba zata sake irin wannan gangancin ba. Gaba ɗaya Sahla ta rena kowa a gidan nan"

Bai sake hannuna ba amma shi Yaya Mustafah ya sake min hannu.

"Lokacin sallar jummu'ah yayi. Koma minene ka bari bayan sallar jummu'a sai ayi mata hukunci"

Yaya Mustafah ya kalle shi sannan ya kalleni yace
"Saura kuma in dawo na samu ba kya gidan nan, zaki ga abinda zan miki"

Sai da Yaya Mustafah yai gaba kafin ya sake min hannu. Na shiga yarfe hannun dan kamar an nika mini su tsabar zafi. Wannan Basamuden hannun nasa kamar guduma.

Ina ganin kulewarsu nima na ɗau ledata a kasa na sulale na fice daga gidan. Dake 'yan karɓan abincin sadaka sun fara shigowa babu wanda ya ganni.

***

"Idan na ce ina jin daɗin abinda kake yi to na yi karya. A ce mutum kamarka sai ayita maimaita magana ɗaya duk shekara. Miye amfanin abinda ka yi yanzu. Ka watsa min kasa a ido yanzu kuma kana so ka watsawa Maimartaba kasa a idanu saboda kai ka isa ko"

Alhaji ya gyara zamansa da kyau yace " look at me Aliyu. Ban taɓa yiwa Maimartaba musu ba kuma kaima ba zaka musanta mishi ba. Kamar yadda ya faɗa ka je ka zaɓi ɗaya daga cikin 'yanmatan da ya zaɓa maka. Idan ka ki kuwa babu ni babu kai. Abinda kanwarka ta yi nafila ne akan wanda kai ka ke yi yanzu. Idan kuma Maryam ɗin ce ta muku huɗubar ku bijire mini to sai in hakura da ku"

"Ka yi hakuri. Zan yiwa Baba (Maimartaba) magana. Na san zai fahimceni. I need time, ba zan iya rushing aure ba"

"Tashi ka bani waje"

"Dad"

"Aliyu ka tashi babu amfanin zamanka a nan. Tunda bin umurnin manya ya maka tsauri ka je Allah ya kiyaye hanya. A gaida mutanen Paris"

"Dad" ya faɗa muryansa na rawa. Hannunsa ma ya shiga rawa, yai saurin haɗa hannun nasa waje guda amma duk da haka rawa suke. Kamar karamin yaro yake jinsa. Yaron nan ɗan shekara takwas wanda a karon farko yai niyyar faɗawa mahaifinsa damuwarsa.

"Dad. Dad i want to tell you something. I...Julius..."

Har yau bai iya faɗin abinda aka masa ba. Har yau ɗin kuwa ya rasa ya zai yi ya bayyana matsalarsa.
Gashi dai ya tara shekaru amma idan zaka tambayeshi matsalarsa yanzu zai rikice ya koma ɗan karamin yaron nan da iyayensa suke barinsa tun safe har dare a hannun Julius.

Har Alhaji ya tashi daga falon Aliyu Faruq bai dawo daga hayyacinsa ba.

"F Kay" muryar Abdullahi ya dawo da shi daga duniyar tunani.

"Lokacin sallah yayi"

"Thank you, barin yi Alwala"

***

Dr Rafee'ah na fitowa daga motarta Isiaka ya tareta da barka da dawowa.

"Hajiya Likita yau babban bakuwa mu ka yi a gidan.

"Isiaka waye ya zo?"

"Matar Minister"

"Adda Maryam" ta faɗa a ɗan tsorace.

Tun da ta auri Alhaji Kabiru Ubandoma sau uku suka haɗu gaba da gaba da Adda Maryam ɗin. Ko lokacin da Adda Maryam ɗin ta sake aure bata halarci bikin ba lokacin shekaranta biyu a gidan Alhaji.
Akwai wani cold kishi da ke tsakanisu wanda duk da basu furta ba ka san shine dalilin dayasa suke gudun haɗuwa da junansu.
Adda Maryam has always being her role model tun tana yarinya. Har bayan ta bar gidan Alhaji Kabiru Ubandoma ba su dena zumunci ba. Infact ita ta bata karfin gwiwa akan ta karisa karatunta lokacin da aka sakata gaba akan mutuwar aurenta da Mansur Madaki.

Bata taɓa tunanin zata auri tsohon mijin Adda Maryam ba. Ko lokacin da Alhaji Kabiru ya shigo rayuwarta wannan dalilin yasa ta ki amincewa da auren. Ba dan Maimartaba ne ya shiga lamarin ba da babu wanda ya isa ya convincing ɗinta akan auren Alhaji Kabiru.

Idan ka cire rashin haihuwa da kuma kishi da ba a rasawa lokaci zuwa lokaci. Aurenta da Alhaji Kabiru aure ne na kwanciyar hankali. Lokacin da ta auri Mansur bata wuce shekara shatakwas ba. Ya ɗauketa ya kaita Lagos. Da kuruciyarta yana so ya jefata halaka.

Tunda ta diro garin Gombe bata sake zuwa Lagos ba. Ita tana tunaninma har abada ba zata sake zuwa Lagos ba.

Watansu bakwai da aure. Bata gama sanin kanta ba. Ina yake mata daɗi, ina ke sakata ji kamar zata shiɗe, ina ke sakata farin ciki. Bata gama samun kulawa da soyayyar miji ba.
Mansur kullum cikin meeting da tafiye-tafiye yake. Babu daɗi ka tono abinda ya jima a kasa amma har yau bata manta sau nawa ya taɓata ba a cikin

2 Comments On SAHLA A PARIS
avatar
mahamane-noura

1 year ago

Reply

Ya sanyi don ?aukar novel dan Allah

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to mahamane-noura

Domin downloading novel na mu dole fa sai kayi subs da mu

Please Login or Register in order to submit comment